Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 31

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 31

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 31: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 31. Dagudu gudu ta dauko abayarta lumbukekiya ta lumbuka sannan ta warto…

3,367 words

Dagudu gudu ta dauko abayarta lumbukekiya ta lumbuka sannan ta warto nikaf dinta da safarta ta kafa ta cire wancen ta saka bak'a ta dauki mayafin abayarta ta nanada a kanta sannan ta daura nikaf din ta dauko wayarta da jakarta wace take kyautata zaton da kudi a ciki ta juyo da dan gudu gudu tana fatan Allah ya sa Nahidht ta farka su je su samu dan sahu ya kaisu masalaci

Masu aikinta ta samu sunna ta aiki ba ji ba gani gefe daya kuma Nahidt ce zaune cikin shiga ta bayar itama nikaf dinta a gefe a ajiye tana ta aikin Voice. What's up hankali kwonce

Murmushi ta sakar mata tana fadin" Tashi mu tafi "

Nahidt ta mike tana daukan Nikaf dinta ta ce" Um su Shuwwa an zama hajia a kadan na kusa awa a nan ina jiranki sai yanzu ta nan mijinki ya wuce sai da ya tsuguna har kasa ya gaishe ni, kai Allah dai ya masa albarka"

SHUWWAR da ta farra barawa masu aikinta salahun gyaran da take so su yi mata ta juyo tana kallon Nahidht Kai ta girgiza ta juya tana kare masu kallo Haka kawai ta ji bata yarda da ta barsu a gidan nan su kadai ba, dan ta tabata da dan gida akan ci gida

A hankali ta shiga fadin" Ku tafi kawai, idan muka dawo zamu yi aikinma ai ba yawa"

Su dukansu da mamaki suke kallonta, zasu yi? Gyaran wannan makeken falon? Sai dai basu da damar yi mata musu, kuma sun ga direba da escort din dake jiranta sun san fita zata yi, a dole sukai mata salama suka fice gaba dayansu hakan ya saka Nahidt yin yar dariya tana fadin" Wollah wani lokacin kamar mai hankali idan kikai wani abin"

Sake kyaleta ta yi tana kakarsge dukan wani abin wuta tana cire igiyoyin sannan ta dauki abin rufewa suka fice ta garkame babar kofar kafin ta tsaya tana kallon sojan da ya matso ya sarra mata a ladafce ya ce" Hajia Sir ya ce idan kin fito ga motar da za'a kaiki anguwar cen da eacort"

Daga ita har Nahidt ido sula zarro da mahaukacin mamaki sula juya wajen tsaleliyar farar motar dake ajiye kal tana shinning

Dan ihu NAHIDT ta yi ta nemi yaye Nikaf dinta da kokarin kwaso shoki, da sauri SHUWWAR ta tareta tana girgiza mata kai ta ce"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 3️⃣3️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Dan ihu NAHIDT ta yi ta nemi yaye Nikaf dinta da kokarin kwaso shoki, da sauri SHUWWAR ta tareta tana girgiza mata kai da yaren larabci ta ce" Kar ki yi irin haka a gaban yarensa mana kar su raina mana wayau"

Nahidt ta yi murmushi tana mayar da Nikaf dinta ta hade irin kar a ga damartan nan ta bi bayan SHUWWA da tuni ta sauka ta nufi wajen shiga mota

Budewa suka yi suka shige Direban ya ja su Sai da ya hau bakin titi ya tambayi wajen da suka nufa

Nahidt ta ce" Wajen Masalacin Malan zamu tafi?"

Shuwwar ta kalleta tana girgiza kanta ta yi murmushi ta ce" Kennanma ba karuwan muke ba ko?, " Ta fuskanci Direban a nutse ta fada masa kwatancen gidan malan da hausa sannan ta sake hade fuska tana tunanin wannan amarya ta malan mai kananun iskanci!

Tunda suka nufo gidan ake raka motocin biyu dake dauke da su da kallo har suka karaso kofar gidan malan Makotan gidan Malan du sunna lekowa dan kallon farar motar da kuma motar dake dauke da sojoji a bayan farar motar wadda sunna tsayawa sojojin suka didiro daga bayan motar suka shiga gabatar da aiyukansu na tsaro

Sai da suka bada damar cewa tana iya fitowa daga motar sannan direban da soja daya dake gaba suka basu damar fita

Murmushi Shuwwa ta yi tana girgiza kanta a ranta kuwa ayanawa take yi' Rayuwa mai abin mamaki'

A nutse suka nufi karamin get din sukaiwa mai gadi salama Sarai ya gane su domin ba zai iya kasa gane y'ar Malan da yayunta ba hakan ya sa da fara'a yakr masu barka da zuwa cike da murnar gannin a motar alfarmar da aka kawota harma ya ce" Aaa su y'ar gidan Alama ce?, To ku shigo da motar mana?"

SHUWWA ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" gani na yi da maza , ba'a shedawa matan gidan da baki ba shi yasa baba"

Shima murmushin ya yi yana bude masu da kyau yana fadin masha Allah ai ga kayama ana saukewa

Gaba dayansu suka juya sunnan kallon ikon Allah ana sauke kayan abincin, ai yanzun ba yadda Shuwwa ta iya da Nahidt sai da ta saka buda tana fadin" Duniya labari, ga Shuwwa ta zo gaishe da ubanta an zo da kayan cima, kai Allah mai iko wuce mu je an fara leke"

Itama shuwwar din sai ta ringa jin wani farin ciki daban a zuciyarta ta yi gaba tana salama a bayane ta nufi direct baban falon matan gidan

Uwar gidan Malan ce ta fara fitowa da hijab dinta da carbinta tana amsa salamar Gannin fuskokin su Shuwwa a lokacin da suka cire Nikaf din sai ta ringa sakar masu murmushi tana fadin" Marhababiku"

Shuwwa ta zauna dangalgal saman kujera tana fadin" Barka da safia Hajia "

Da murmushi wadace a saman fuskarta ta amsa gaisuwarta ta juya wajen da NAHIDT ke tsaye bata idasa shigowa da kyau ba ta ce" Yau kuma kece a tsayes a bakin kofa?"

Nahidt ta yi dan murmushi tana fadin" Ai dama rakiya na yi Hajia, shi yasa na tsaya daga nan"

Yar dariya ta yi ta nufi kofar ta kamo hannunta tana fadin" Ki shigo, ko kar ki shigo, ki sani zan je ne da kaina na rarasheki, na duka na baki hakuri sannan na fada maki cewar dakinki ya fara dati, dakinki dake gidan nan yana son fara tara yana, shin yaushe zaki gane ki tataro ki dawo tun kafin Aban Shuwwar ya fara fada ne?"

Da dan mamaki tana kallonta ta budi baki zata yi magana suka ji shewa da tafa hannu sannan ta ce" Ikon Allah, wannan shi ake kira munafurci, ke yanzu Malama kece da budar baki da yiwa wannan matar sannu a cikin gidanki harda tsohon munafurci kike budar baki kika ce ta yi ta zo dakinta na jiranta?, Wani dakin kike bayani a cikin gidan nan? Inace a bangaren nan dakunnan biyar ne daya naki, daya nawa, daya na bakinmu, daya na masu aikinmu, dayan kuma na wada Malan ke kira y'arsa ce, a ciki ba'a ginna dakin kilaki ba ko kin manta?"

Malama ta girgiza kanta tana kallonta bayan ta zaunar da Nahidht dake tsaye da farko ta ce" Ke dai Furera ina so ki koyi iya bakinki, ki kiyaye rayuwa, Furera shin ba'a aurowa ke aka auro min ke kike zaune? Da kike zannen dakin waye, da waye da waye ba shi zai hanna Malan aurar biyu ya cikashe da mu ya jera hudu reras abinsa ya zamo sarki cikaken mutun mu kuwa mu share masa fadarsa ya yada zango, ki kiyayi yowa lamarin ubangiji shishigi na kula Furera idan kina magana kikan yi kokarin nuna kin isa da yannayin rayuwarki!"

Furera ta idasa shigowa tana cire hijabinta taa ajiye saman kujerar tana kallonta ta ce" Ganewa ne baki yi ba, ko da aka auroni aka kawoni gidan nan dama dan kin gaza na zo, a yanzu kuma da ke kike hada mijina da wannan da babu wanda bai bude ya dana ba ina so ki fahimci cewar ni ban gajiya ba, ba kuma zan yarda mijina ya auri sauran gayu ba salon in da wani boyayen lamari a maka mana kau? Ba zai yiwu ba"

Idannuwanta take karra rintsewa da karfi tana cije lebenta sannan ta bude ta kalli Furera ta maida dubanta kan Malama

Malama kam mamakin furera ya kasa barinta, ita takamarta da an yi magana ta ringa hoboro ita ga matar so matar da aka auro mai ganihar kuruciya menene menene, a rayuwarta wannan din shine abinda ta fi kwarewa a shi, domin ko matsalar mijin nata ta kasa fahimta bale har ta yi yaki da son kanta da zuciyarta ta taya shi neman abinda ke kayar masa da gaba, ta kasa fahimtar nacin Malan a kan Nahidt, ta kasa gane cewar Nahidt na iya zamewa rayuwar mijinsu mugun jarabawa ko kyakyawar jarabawa, ta kasa yin irin nata ta koyi hakuri ta koyi kaunar kasancewar Nahidt a tare da su, harma ta fuskanci cewar jihadi ne idan har ya aikata hakan, su kuma idan suka talafa masa zasu samu nasu sakamakon mai kyau, ita abinda ta fi kwarewa a shi shine wannan daga kan da jiji da kai ita ga matar malan, ta bi ta rikita lisafin masu karamar kwakwaluwa na cikin anguwa ta koya masu gori da kadarar mutun, dan rashin hankali ta koya masu abubuwa mararsa ma'ana har sai yanzu da daidaiku ke gane wacece ita suke barin makarantar izgilinta sunna fuskantar rayuwa , A tausashe ta budi baki zata yi magana a tsawace Furera ta dakatar da ita da hannunta tana fadin" Dila Malama kar ki ce min komai a nan, da bana nan da kin ci min amana kin lalumi karuwa an lakawa mijina an ci amanat..............................................."

Tassssssssssssssssstssssssssssss tsadadan marin da ya sauka a kusa da bakinta ya sakata daukewar magana da firgici harma ta juyo a haukace tana kallon wanda ta auna mata tikiten tashin hankalin nan na kakausan mari mai balakin zafin tsiya

Ido ta kwalalona lokacin da ta ga ikon Allah, ba ita ba, harta da Hajia Matar Malan, da Nahidht idannuwan suka zarro a lokacin da Shuwwa ta cire Hijab dinta ta je da gudu ta janyo cazar waya idannuwanta sun kade a haukace ta ce" Baki gane ba Furera, an jima da daina zagi , bara na ci ubanki a cikin gidan naki ki kai karata ke har yar tasha ce a nan? Da nake raga maki kin dauka dan kin isa ne? Tunda baki da hankali bara na gwada maki shegantakama iyawa ce sai ki samu dalilin tsanarmu da zaginmu, banza jahila da kike anfani da laifin wani kina zaginsa da shi bayan ke dinma halita ce da Allah ya halita baki da tabacin yaya gobenki take!" A haukace ta zuga mata zugawa guda ta daga ta sake zabga mata , hakan ya sa da dukan karfinta take kokowar son kwace bulalar sai dai kamar yadda SHUWWA ta fada mata cewa shegantaka iyawa ce, haka abin yake, bata san cewa idan ka tashi neman fitina jinjinar kanka kake yi ta yadda zaka yarda da kanka cewar zaka iya, ta dauko da zafi tana wasa da shi a hannunta ne bata san cewar akoy masu dibansa daga cikin tukunya su kaishi baki ba, ta yi wasa da damarta tun ana bata girma sanadiyar mai girma har ta kai wajen da aka ajiye gefe aka fuskanceta a matsayinta na mutun

Da karfi ta hankadeta hakan ya sa ta maku da jikin garu tana haki ta nunota da yatsarta ta ce" Kin jima kina zaginmu da sunna karuwai, kin jima kina dukan kirjin ke kin isa ba'a isa a auro maki karuwa cikin gidanki ba? Furera an fada maki ban san cewa kece matar da ta bini gidan sarakuwata ta ce ni karuwa ce har mamansa ta saka ya sakeni ba?, Ko baki san cewar na san da kafin na tare kika je kika yi bayanin wacece ni wa Elhaj mai shinkafa ba har ya bani tikitina a cikin mota?, Ko ji kike ban san cewa ke din nan kece wace ta yiwa matar uban mijina bayanin wacece ni ba har aka hanna shi tarewa a dakina har zuwa ranar mutuwar aurena ba?, Ke takamarki musulma ce ke anya kina jin tsoron Allahn da ya haliceki kuwa?, Kin san zaki mutu kuma zaki je gaban ubangiji me zaki ce masa a kan tsangwamarmu da tsanarmu da kika yi dan mun kasance masu aikata laifi wa shi da halicemu maimakun ki yi mana nasiha ne?, A anguwa kin tare gaba kin tare baya kin kula mana shari kala daban daban ya zamto makotanmu bamu da kyakyawar alaka da su dan kin nuna har mata bi muke yi? Ke meye shedar fa zaki bayar a gobe kiyama a kanmu ne?, Furera walahi sai kin mike mun kashe junna yau a falon nan ko ni ko ke!"

A haukace ta sake yin kukan kura ta nufeta tana ihun fadin" Ki tashi na ce ki tashi!"

Dan gyarn murya ya yi yana idasa shigowa ya yi salama a sanyayensa yadda ya saba ya sake sauke idannuwansa a kansu

Kuka ta fashe da shi daga wajen da Shuwwa ta makata da garu tana lankwashewa irin bayantan nan tamkar bayan nata ya kalle tana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une me na maki?, Me na yi maki da zaki dakeni harda hadani da garu bayan kin zageni ta uwa da ta uba? Me na maki ne a rayuwa zaki zo har cikin gidana ki wulakantani da min ikirarin mijin da nake takama da shi kun gama da shi kun shanye shi?"

SHUWWA ta yi murmushi tana juyawa wajen mayafinta da ta cire ta ajiye ta dauka tana maidawa a kan gashin kanta da tuni ribom dinsa ya cire a kasa ta nanada da cazar dake hannunta sai da ta daure da kyau kafin ta juyo wajen da Nahidt ke zaune, ta ga a zaunen dai take tun zarro idannuwan da ta yi bata kuma yinkurin yin komai ba sai uwar gidan Malan ce ta ce" Ki ji tsoron Allah Furera, ki guji kafurin kishi Furera, idan kikai haka jin dadin na kankanin lokaci ne a cikin gidan duniyar, zaki je ki samu ubangijinki a kiyama, ki sani Furera koda jin dadin muzgunawa wani ya zame maki a duniyarki har ki je ga kiyamarki ne to fa da zarar kin mutu kin hadu da sakamakon abinda kika shuka kennan har zuwa tashin kiyama, shin yaya zaki yi idan ubangijinki ya tsayar da ke a gabansa ya tambayeki abubuwan da kika aikata a duniya bayan ya haliceki ne dan ki yi masa bauta me zaki ce? Ke ce hada wannan da wanan, kece zagin kadarar mutun, shin ke kin tabata kin isa ki juya salon rubutun ALK'ALAMIN kadararki ne?"

Malan ya sake furta" ASALAMU ALAIKUM "

Juyowa malama ta yi a nutse tana amsawa kafin ta matsa gaba daya ta bashi hanya ya shigo hakan ya sa Furera sake rakata da mugun harare mai zafi tana ji a cen kasan zuciyarta a duniya idan akoy makiyinta bayan matar nan ne, bata taba gannin mace mai kafurin hakuri da jarababen biyaya irin uwar gidan Malan ba, da ba dan ita ta san me take nacewa a zamanta da Malan ba da ko dan hakurin matar nan ta barshi ta yi tafiyarta nesa da shi, sai dai malan din ne duniya ne, ba zaku gane ba malan duniya ne

A nutse ya masu nuni da wajen zama gaba dayansu

Shuwwa ta cije baki da abin dukanta a hannunta tana jin haushin zuwansa bata farfasawa wannan tsageran jiki ba wai shari ne zata yiwa mutane ikon Allah, tabas sai ta koya mata hankali ko yau ba, wannan alkawari ne ( kai jama'a kamar irin zaka ladaftar da yaron da ka haifa din nan

Da sauri ta zagaye Shuwwar ta karasa wajen zama ta zauna a gantsare dan so take malan ya ganewa idannuwansa cewar mahaukaciya yake neman yin taraya da ita ko me?

Sai da suka zazauna su ukun, dama Nahidt a zaune take, sannan ya karaso saman kujera ya zauna yana dan sauke ajiyar zuciya kafin ya sauke dubansa a kan Nahidt

Ido hudun da suka yin da junna ne ya saka shi sake saka idannuwansa a cikin nata

A hankali yake rage girman💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 3️⃣4️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

A hankali yake rage girman nasa idannuwan a cikin nata, dukkan abubuwan dake cikin zuciyarsa sunna bayanar da kansu a bayanne a cikin nata idannuwan, karara halin da idannuwanta suka nuna tana ciki yake neman kasara dukan tunaninsa da dukan wani yannayi na jarumtarsa A hankali idannuwansa ke isar mata da sakon rarashi duda bata budi baki ta yi magana ba, bata kuma yi rigima da wada ke zaginta ba ji ba gani ba

A hankali ya lumshe idannuwan nasa yana kawar da kansa a bangarenta ya maida kan Shuwwar wace ta tsatsare su da ido tana jin wanu farin ciki a kasan zuciyarta

Kakausan kallon da ya mata ya sakata sada kanta kasa tana boye bulalar a cikin mayafin abayarta a kasan zuciyarta ta shiga ayana' kai, ashe ashe itace na daka kuma ya ganni'

Ya maida dubansa kan uwar gidansa da kanta ke sade , ya samu kansa da yi mata lalausan kallo mai saka Nutsuwa a zuciya sannan ya maida kan Furera Ido hudu sukai da ita, tunda ya fara kallon Nahidht take kallonsa haka kuma take fasara shi a cikin zuciyarta har ya sauke dubansa a kanta Ta so ta yi kisarta da kisisinarta ta hanyar sake lankwashewa, sai dai duban da yake yi mata a bayane yake cewar sam bai yarda da abinda take son nuna masa ba, hakan ya sa ta samu kanta da tsarguwa harma ta kasa kallon cikin kwayar idannuwansa

Ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya ce" Abin alkhairi na ga ana ta shigowa da shi, IBTISAM ashe kece tafe?"

SHUWWA ta kasa cewa komai sai sake sada kanta da ta yi, hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya yana yin murmushi ha ce" Allah ya karra budi, Allah ya saka da alkhairi"

Uwar gidansa ce ke amsawa a nutse da ladabi da biyaya

Readers Also Read