Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 32
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 32: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 32. Sake yin dan Murmushi ya yi yana kallonsu aa sanyaye ya ce" Ban ji…
3,321 words
Sake yin dan Murmushi ya yi yana kallonsu aa sanyaye ya ce" Ban ji dadi ba, gaba daya sai Tsoro ya kama ni, na fara tunanin yaya iyalina zasu kasance zuwa gaba ? Bale idan ban yi tsayin rai ba yaya zumunci zai kasance a ahalina?"
Zuwa yanzun gaba daya gaban jikinta idasa mutuwa suke yi, haka kuma karra kallonsa take yi Irin yadda zuciyarta ke bugawa kuma abin nema yake ya fi karfinta bil haki, hakan ya sa a hankali ta ringa ambaton sunnan Allah
A tausashe ya ce" Irin haka babu abinda zai haifar mana sai bacin rai, da tabarbarewar zumunci, da mugun sakamako a wajen Allah, domin kuwa Allah na yafe laifin da ka yi masa ne kai tsaye aman baya yafe wanda ka yiwa bawansa, idan har ka zalunci bawansa ya zama wajibi ka nemi yafiyar bawan nasa koda zai yafe maka ne shima da kansa, hakan na nufin Allah baya so a zalunci bawansa ta kowani siga, sannan ya haramta bawa ya ringa yankewa bawansa hukunci ko yayane..............., Fisabililahi kun kyauta kuwa?"
Gaba daya shiru ne ya sake ratsawa, kafin Furera ta bude bakinta ta ce" Allah ya gafarta Malan , shin da adalci a cikin lamarin nan da ake son nuna min kuwa ? Mata ta tardoni har gidana ta dakeni?"
Kansa ya girgiza a sanyaye ya ce" Ba adalci a hakan ko daya, asalima dukan bashi da anfani, to aman ke me kika yi ne?"
Ido ido suka shiga yi , a dab hade ta ce" koma me na yi ai ban cencenci haka ba"
Shima a dan haden ya ce" Dan su ba mutane bane ya saka basu da zuciyar dake iya hasalasu s Idan suka samu kansu a hali na bacin rai dake iya tunkuda su aikata kowani irin aiki kike nufi ko me?"
Gaba daya sai ta dawo jifansa da kallon dake nuni kamar tana mai tuhumarsa ne da goyon bayansu, shi kuma ya sake daurewa ya ce" Haba Furera, a zaune na fada maki, haka kuma a tsaye cewar koda abinda kike hasashe gaskiya ne ko karya ne baki da hurumin hanna su ziyartata koda a wani irin lokacine, shine zaki wulakantar da kanki har kanwarki ta daga hannu a kanki? Kin san da ba kowa yaa janyo ba sai ke da kanki? Ga yayarki nan, da ta kama girmanta ta mutunta kanta hakan ya sameta ne? Subahannalah yaya kike so na dube ki bayan tun farkon fara furucinki na sanyo kai zan shigo wajen nan nake jin kalamanki na rashin da'a kina furtawa wa yar uwarki? Me ta tsare maki? Idanma abinda kike jifanta da shi ta dawama a ciki Allah ya ce ki ringa jifanta da shi ne? Idan zaki yi mata nasiha ki kwatanta, idan zaki yi mata fada ta sigar nasiha ki kwatanta aman zagin nata da kike yi Furera kin saka hankalina ya tashi bayan na manta cewar Nahidt ta yi rashin ji na ajiye gefe na guji abinda zai daga min hankalina sai gashi kin tuna min kin fada min fisabililahi wannan aikin ilimi ne ko jahilci?"
Kanta ta sake sadawa domin a zamanta da shi, bata taba gannin ya yi mata fada da kakausar murya da dogon zango irin na yau ba, gashi kuma a bayane ransa ya gama baci ne domin abin a bayane yake ba a boye ba, ta gama yarda cewar sai ta tashinwa kanta a kan matan nan, ta gama yarda cewar an shanye mata mijinta malaminta ustazunta
A sanyaye ya kalli gefen da Uwar gidansa take ta sake sanyayar da muryarsa ya ce" Allah ya saka maki da Alkhairi, ya kara shiryar da ke , ya yi maki albarka, ya baki aljannar firdausi ya ke Rabiatu"
A sanyaye ta ringa amsa adu'o'insa tana sake sadda kanta a sanyaye da matukar sannin waye mijinta ta ce" Allah ya huci zuciyarka Allah ya baka hakuri"
Karra cika Furera take tana batsewa tana kallonsu, shi kuma ya sakar mata murmushi a sanyaye ya ce" Dan Allah ki taimaka ki idasa rokar min ita cewa bayan dakinta dake jiranta a gidan nan wanda ya fara tara yanar tautau, ni da kaina na fara gajiyawa da Zaman jiranta, Rabiatuna ki ce mata ta ji tsoron Allah ta dube ni tun kafin karfina ya gaza"
A zabure du sula sake kallonsa, banda ita Hajia Malama Rabi'atu, wace maganar nan irin haka sau uku kennan yana fadarta a gabanta, ta farko ita ce ta tayar masa da balin rigimar ta gaji da ganninsa cikin bacin rai da yawan hadewar fuska sai ya fada mata damuwarsa, ya yi ta kaucewa, ya yi ta kiyawa har ta yi yar dariya ta ce da shi a da dai shi din ba rago bane , aman a yanzu ya kasa fuskantar Nahidt ya fada mata cewar yana sonta? Ita fai ta san mijinta ba rago bane dan haka gaskiya ya daina wannan fargabar a gaban Nahidt ya yi kokari ya fada mata ya taimaketa ya ceceta, ta yiwu sanadiyar haka Allah ya bude masu haihuwarsu, domin su dukansu babu mai matsalar haihuwa sun ga asibiti ba'a ga dalilin da ya tsayar da haihuwarsu ba, sai na biyun ranar da sukai wayar nan ta dare da ta kashe da safe Hamza ke fada masa bata nan ko gidansa ta yi? Ya fice a fujajan ya je tsohon gidanta ya samu gidan a garkame, daga cen wajenta ya yi hankalinsa tashe yake fada mata, daga wannan ranar ta kara daukan aniyae gabatar da tsaftatacen kishi, ba dan bata kishin Nahidt ba, itama mace ce, tana kishin mijinta sosai, aman kuma zata gabagar da tsaftatacen kishin da zai karra mata daraja da soyayar mijinta, shi yasa ta bashi goyon baya a gaban idannuwansa da kuma bayan idannuwansa
A sanyaye ta sakar masa murmushi ta ce" In sha Allah, zata amince ta zama yar uwata, matar mijina, abokiyar tafiyar da zaman lafiyar gidan MALAN Aban SHUWWA"
A hankali Shuwwa ta furta" Muhamadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam" tana kallon Matar malan baki hangame
Furera kuwa a lokaci daya kanta fa idannuwanta suka kwashi zazafan ciwo Da gaske abinda take gani kuma take ji cewar Malan ne ke neman auren wannan karuwar?
A birkice ta mike tana fadin" Malan, anya kuwa kana cikin hayacinka?, Rabi kina cikin hayacinki kuwa?, Ka gane wa kake cewa zaka aura kuwa? Matar da ta gama rabar da dukan wani mutuncin dake tare da ita? Matar da kila wa kala tana dauke da cutar h................"""""" Tsit ta yi tana rufe kumatunta da sauri sakamakon mikewar Da Nahidt ta yi jikinta na dan rawa , dukan gaban jikinta a mace ta tsatsareta da idannuwanta da suka dauki ruwa sosai
A hankali ta lumshe idannuwanta hawayen dake ciki suka zubo saman kumatunta Muryarta a sanyaye tana kallonta ta ce" Daina rufe fuskarki, idan SHUWWA na waje ba zan zane tsageran dake zagina ba na tabata ta fini zafin hannu dan ta taba zabga min mari da na kirayi kaina karuwa, walahi fitsari na yi a wandona a ranar sai daga baya ta bani hakuri na kuma yafe mata, Furera ban san me na yi maki ba, nakan daukanki a matsayin wace ya zama wajibi ta tsaneni dan kina tunanin ina bin mijinki sannan nakan dauki tsanar da kike min da sauki domin a rayuwa babu bawan da zai ce shi lalle kowa dai ua so shi, kin ga dole zaka rayu da wa'inda zasu tsaneka ba tare da ka tsare masu komai ba, bale ke da kike gannin nice damuwarki, Furera bari ki ji, farkon fara masha'ata ya samo asali ne da rashin ci, rashin sha, rashin muhali, da ace da irin mijinki muka fara haduwa da na tabata maki da yanzu ba haka nake ba, da farko tabas kadarar rayuwa ce ta sameni Furera, sai dai shi sabo fara shi ne da sauki, fitarsa Yana da matukar wahala domin daga baya mun samu budi sosai sai dai gaba daya na riga na shiha sai fitar ta gagaremu, aman ki yi hakuri dan girman Allah, kuma ni na yafe maki, hakama kanwata zata yafe maki ko ba yanzu ba, ke zan iya ce maki idan ta kasa yafe maki zaki ganta ta dawo ta nada maki wani dukan dan ta huce domin bata so ta rike mutun a ranta, ta fi gane a yita ta kare da ta rike mutun a zuciyarta, Furera abinda kike yima din fa ni ba zan aikata ba, Furera me gareni da zan iya zama matar sa? Shi din adali ne, ya amshe mu, ya zala uba a garemu, ina zuba masa hauka dan ma ture shi daga rayuwarmu aman shi aikin Allah yake yi, da zuciya daya yake yi, yanzuma abinda ya kawo mu kin ga y'arsa ce ke son ganninsa, ni gabana faduwa yake idan na fiskance shi, bayan wannan sha kuruminki ba zan iya aurensa ba, ba zan taba aurensa ba, ki huta abinki?"
Daga haka ta juya ta fice da gudun tsiya wanda hakan ya saka shi rintse idannuwansa fa karfi ya sada kansa yana sauke numfashin dake fita da gagawa a kirjinsa
Ido SHUWWA ta zarro tana raka Rabiatu da ido wace ta bi bayanta da gudun itama tana fadin baki isa ba walahi! A bayane ta ce" Lah " tana firfito idannuwanta gaba daya da mamaki
Dubanta ta maido kan Furera, kafin kake cewa tak, ta fice itama da dan gudunta har tana waiwayen Shuwwar din, domin ita yanzu ta fara tsoron yarinyar nan, shegiya mai karfin aljannu (😒)💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 3️⃣5️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Sai ya rage daga Malan sai SHUWWA Kansa shi kuma a kasa ya kasa dagowa har sai da Shuwwa ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Abana "
Idannuwansa ya lumshe kafin ya dago a hankali yana kirkirar murmushi yana kallonta ya ce" Na'am Shuwwan Abanta"
SHUWWAR ta ce" Ka san wani lokacin Aunty kan haukacewa kau? Kawai ka hada sadakinmu mu je mu kaima Hamza"
Dan murmushi ya yi yana kallonta ya ce" Shuwwan Abanta idan fa da gaske take? Idan tana tsoron auren wanda baya haihuwa ne?"
"Subahannalah Abanah , subahannalah, dan Allah kar ka saka haka a ranka, na rantse maka tana sonka kuma zaka ganni gannin idannuwanka" Shuwwa ta fada jikinta na yin sanyi sosai
Wani murmushin ya sake yi yana kawar da zancen ya ce" Menene yake damunki? Na tabata akoy damuwar dake damunki"
Kwarai ta so ta bar maganar sai ko zuwa gaba, aman wannan maganarma mai mahinmanci ce, ba zata iya barinta haka ba, kuma ita dai a yanzu shi ne mutumen da zata iya fadawa wannan maganar, dan haka ta fuskance shi a sanyaye ta shiga fada masa dukan abubuwan da suka faru ta dora da fadin" Abahna, gaba daya na shiga hali na zargin kowa da kowa, wanene mai aikata haka? Koma wanene yana da dama a gare shi sannan Yana da kusanci fa shi ta yadda har aka ita shiga dakina aka saka camera, shin kafin ni sauran matansa da haka a dakunannsu? Matarsa dake garinsu itama an kirayeta ne? Ta amince da haka ne? Da wata maganar aka jinginata ne? Shin menene dalilin dake rabashi da mata? Abana gashi mai taurin kan tsiya bale a tambayeshi ya bada amsa cikin sauki, shi yasa na ce kawai mu zo, Nahidhtma ta ce gaskiya mu zo"
Gaba daya abin ya daga masa hankali ta yadda ya yi shiru yana nazari, "Ya salam" shine abinda yake ta furtawa a sanyaye kafin ya dunkule hannunsa ya ce" Mun shiga a cikin tsaka mai wuya IBTISAM, mun shigo a cikin yannayin da ya zama wajibi mu ringa kaye kaye a cikin kwakwaluwarmu, mu ringa zargin kowa, muna duban kowa, sai dai mu tuna cewar zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne........" Ya sakue ajiyar zuciya ya sake fadin" Hasbunnalahu wani'imal wakim, shin tun yaushe hakan ya fara samunsa? Waye abokin hamayar dake neman ransa? Kisa? Me yayi da zafi haka?, Na san cewa ko a sanadiyar kujerar da ya taka , watau matsayin da ya haura yana iya samun abokin hamaya, ta yiwu kuma wani ya taba hukuntawa hakan bai masa ba, subahannalah koma menene me ya kai na shiga hurumin iyalinsa? Wani namijin da a taka lamarin iyalinsa gwara ka kashe shi ya san kashe shin ka yi"
Shuwwar ta dan tabe bakinta ta ce" Ni wollah Abana du sai abin yake min wani iri, wai shi iyayensa da rai kuwa?"
Makan ya kaleta da dan mamaki ya ce" SHUWWA, shin baki zauna da shi ba har yanzu?"
Rashin gane tambayarsa ya sakata tabe baki ta ce" Kai Abana wannan ake wata magana da shi? Shi fa kulun kashedi yake min, dazuma dai ya ce ba'a saka shi magana na kiyaye na ce ka ji dunkum!"..........sai da ta gama zubar kuma ta rufe baki tama fadin" Ba dunkum nake son cewa ba Abana"
Malan ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza kai a nutse ya ce" kina jina?, Ina so ki fuskanceni da kyau sannan ki fahimci abinda nake son fada maki, SHUWWAR ko wanene, ko me yake tare da shi ina so ke ki zamto wace zata gagaresu da karfin adu'a fa gujewa daga wayarsu, SHUWWAR kina jin abinda nake nufi da ke?, Ina so ki ji tsoron Allah, ki sani mutumen nan yana da hakki a kanki, ki kiyaye dukan wani abin da zai zamto cutarwa ne a gare shi, zan je na samu manyana da nake maganar sirri da su na sanar masu damuwarmu ba tare da na basu sunna ba, dan su tayamu fadawa Allah, zamu hanna kanmu barci na tsayin sati biyu mu ga yadda Allah zai yi, idan kuma suka ci gana da kiranki ki yi kirana ki sanar min ko ki zo ki sanar min domin mutanen nan babu abinda ba zasu iya yi ba sunna iya sauraronmu ta waya su gane kin fadawa wani Maganar su maki ila, ki taso ki zo ki sanar min ni kuma na samu mijin naki mu yi maganar in sha Allah, Allah zai toni asirinsu ko su waye da izinin Allah, fatana ba hakinsu ya ci ba suka taso masa"
SHUWWAR ta ringa amsawa, sunna haka Hajia Rabi'atu ta dawo, daidia ana kiran sallah a dole ya mike itama ta dauki Nikaf dinta ta fice tana fada masu gidan Hamza zasu wuce
A lokacin da ta zo cikin motar wani fadan ne suka bude sabo, har suka isa gidan Hamza A nan falon Fauziya suka baje bayan su masu yin sallar sun gabatar suka shiga hira , a nan Shuwwar ke fadawa Fauziya abinda Nahidt ta yi, ai kuwa suka sakota a gaba tamkar zasu cinyeta danya tana kare kanta , har sai da ta gaji ta ce" Ke Shuwwar da Fauziya ku tashi ku ci uwani mana wai? Na ce ba zan auri Muhamadu ba na ga ubanda zai min dole yai ga jaraba ba zan aure shin ba, iskancin banza iskancin wofi , ba zan aure shin ba!"
Ai fa summa suka sameta wannan ya fadi gaskiyarsa, wannan ya fadi tasa, SHUWWAR ta dire magana da fadin" Shi kadai nake da shi ubana a duniya walahi sai kin aureshi dan ba zaki hada masa ciwon zuciya ba ke muguwa!"
Sunna tsakiyar musun ne wayar SHUWWAR ta dauki kuka
Cirota ta yi tana dubawa , lokaci daya ta zarro ido tana masu alamun su saurara sannan da hannunta ta nuna masu mai kiran ko wanene
Saurarawar suka yi gaba dayansu suka nutsu sunna sauraro
Da irin wancen muryar aka ce" Muna fatan kin gama yin tunani, kin gama yanke hukuncin zaki bamu hadin kai mu hadu mu kawar da shi a doron kasa domin zuwa yanzu mun gama sannin cewa har rapping dinki yake kokarin yi a cikin gida, shin zaki amince mana mu cin masa a lokacin da bai yi zaton haka daga garemu ba?"
SHUWWA ta yi dan murmushi ta ce" To wai su wanene ku? Yaya zan yi baban aiki irin haka da ku bayan ban sanku ba?"
Amsa aka bata kamar haka " Ba sai kin sanku ba da zarar mun samu burinmu gaba dayanmu a lokaci daya, kawai ki bamu dama mu kuma zamu ajiye maki abinda zaki masa anfani da shi ki kawar mana da shi ba tare da likita ya gane kashe shi muka yi ba"
SHUWAR ta gyada kai tana kallon Nahidht dake miko mata hannu kan ta bata wayar domin tare suke sauraro gaba dayansu Ta ce" To ga yayata zaku tatauna kan abin"
Bata tsaya jiran ta cewarsu ba ta saka amsa kuwa sannan ta a ajiye
Wani bahagumen , lankwasashen ashar ne NAHIDT ta nado ta nadawa mai maganar bayan ta bambance cewar mace ko namiji da mai maganar take ta dora da fadin" La'anane sai mun ci ...............dinka!"
Tana rufe baki Fauziya ta dauka itama ta bada nata mamakin harda kyatsewa ta dire tana firfito da idannuwanta sannan Shuwwar ta shafa fatiha.........domin a dogon da ta daukoma aka katse kiran sai karan kashe kiran da suka ji ne ya shaida masu an katse
Shiru suka yi sunna kallon kallo, a sanyaye Fauziya ta ce" Yanzun kuma mu duka zai kashe kennan..........mun shiga uku"
Nahidt ta ce" ke bari tsinane, babu abinda ya isa ya yi da mu dan iska, kadanma ya ji na so na masa zagin mahaukata na ce da shi kai Uwaka!"
SHUWWAR ta yi daria tana kwontawa ta ce" Baku da mutunci yan matannan ko kadan............ Da wanna suka shantake, da hira tsakaninsu wace suka jima basu yi irinta ba suka nemi shashancewa sunna shan dariya a tsakaninsu sallar la'asar ta sake tashinsu yi, daga nan suka shige kicin dinta tare suka dafa sasaukan dahuwa ta dauki uban kifi da nama sannan suka baje suka ci aka ringa fitarwa da sojojin da suke tare, wa'inda basu yi tunanin zasu samu abinci a wajen matar uban gidan nasu ba, sai dai fitowar abincin ya saka su maida hankali suka ci abinsu sunna masu jin dadin hakan da tunanin lalle ita din zata zamto uwar sojoji
Ba su su tashi a gidan Hamza ba sai da magariba ta sanyo kai sannan suka shiga kimtsawa suka tarkata sukai mata salama suka kama hanyar tafiya,
Sunna tafe SHUWWA na fadin ta rantse da Allah sai an yi auren nan kwana kusa ma kuwa, in kuwa tsoron Furera Nahidt ke ji ta fito a mutun ta fadi cewar tsoronta take ji
Ita dai ta shaka ta yi mata gummm dan ta fahimci so take ta kaita makura su daku a motar ta yadda zasu bar abin fada
_____________________________________
Tunda motarsu ta sanyo kai a makeken tsakar gidan na LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY gaban dukansu ya yanke ya fadi