Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 33
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 33: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 33. Ba komai ya ja haka ba sai gannin jerin motocinsa da ya fita da su,…
3,358 words
Ba komai ya ja haka ba sai gannin jerin motocinsa da ya fita da su, kafin shi dake zaune saman kujera hannayensa rike da jarida ya dora kafa daya kan daya ga Dukan alamu karanta jaridar yake yi, sai ko Wajen kofar da sojoji hudu ke tsaye sunna kikitu da kofar sun rasa ta yadda zasu budeta gashi mai banbare kofar an tafi a dauko shi aman ba'a karaso ba, gaba dayansu jinninsu a akaifa da tarin mamaki da tsoron aikin da matar oga ta aikata yau na kile bangarensu ta tafi da ky, gashi ya dawo a kadan ya yi minti talatin yana jira
"Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, SHUWWAR dan baban babanki hala ky din kofar cen daya tak ne muka kule muka tafi da shi!?"
Shuwwar din kanta cikinta sai da ya juya ta kaleta a zabure ta kada bata amsa, da kyar ta iya yarfe hannunta ta ce" Walahi da na sani da ban aikata haka ba, shi kadaima masifa yake bale an tabo shi, yau Nahidt dukan sojoji ya wajabta a kanmu wayo Allahna"
Nahidt ta zarro ido tana fadin" Ya wajabta a kanki dai kece matarsa, kuma ke kika rufe gidan ai kau? wai tsakani da Allah mema ya dawo da shi gidan nan yau da wuri?"
SHUWWA ta rintse ido gannin motar ta tsaya, sannan ta ji an bude mata bangaren da take kafin ta ji ana magana kamar haka" Barka da dawowa Madame, a kawo ky na bude kofar "
Hannunta na rawa ta wurgawa Nahidt jakar, Nahidt ta bude ta ciro ky din ta mika masa sukai tsuru tsuru sunna kallonsu aka je aka bude masa sannan ya dakatar da su ya amshi kayansa ya masu maganar da ita dai bata jin me yace kafin ya ga gaba dayansu sun sara masa sun fice, nan da nan harta direbobin mazan suka fice suka barsu daga su sai ransu
Gwauron numfashi SHUWWA ta sauke ta fito a motar tana nufar ciki ta shiga ADU'A a bayane tana kallon Nahidht da ta biyota aman ta ki ta bita ciki ta zauna a saman kujerar nan tana saurare
Yawu mai daci ta hadiye ganninsa zaune yana fuskantarta a lokacin da ta shigo
A hankali ta nufo shi, shi kuma kallonta yake yanaa ta maimaita kalaman da suka yi ita da mai kiran nan a waya har lokacin da ta ba yayarta wayar cewar toh ga yayarta zata masa magana suka ringa bada bada da dayar muryar da bai san ko wacece ba sunna durawa mai kiran ashar, har ta karaso gabansa ta zuba gwuiwoyinta a kasa ta hade hannayenta ta ce" Ka mana rai ka yafe mana, bamu san yau da wuri zaka dawo ba, aman gaba idan zan je gari zan tambayeka lokacin dawowarka , ka san abindama ya tsaida mu Nahidht ce, Nahidt ce miji ya fito mata ta masa wulakanci ta ce bata so, an rarasheta, an mata nasihar ta ce bata so, dan Allah ka taimaka ka mata ihu na tabata tana tsoron soja zata maka biyaya, ko auren dole ne a mata da Abanmu yana sonta shi, yadda akai min auren dolen nan itama a yi mata shi dan Allah ........" Ta karashe tana hade hannayenta biyu har tana kokarin zama a kan kafafuwansa sannan tana tare Nikaf dinta dake son dawowa ya rufe fuskarta tana kuma hankalce da hannunsa koda yaka so marintan nan, sai ta yi ta kanta!
Tunda ta fara maganar yake sauraronta, haka kuma yana karantarta har ta dasa aya Sarai ya san dan ta mantar da shi rufe masa faki da ta yi ne ta sako shi a maganarta , aman fa ta ce a aurawa yayarta abansu sai ya samu kansa da mamakinta harma da maimaita kalmar ABANSU?
kafafuwansa ya janye gannin so take ta fada masa a kausashe y💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 3️⃣6️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Kafafuwansa ya janye gannin so take ta fada masa a kausashe ya ce" Ki kula mana ".................sannan ya sake jan bakinsa ya yi gumm yana kallonta
Nikaf din ta cire itama tana kallonsa da kikifta ido, irin alamu na gaskiya da gaskiyar dake tare da ita,
Ajiyar zuciya ya sauke ya sake kallon wajen diner ya ga wayam, yau babu komai, bayan kwana biyu yakan taba dukan abinda ya samu na tabawa, sannan ua dora shayinsa , sai dai yau matar nan ta yi aiki irin na mata bata yi girki ba
Mikewa ya yi ya dauki kayansa ya juya ya shiga haurawa sama, ita Kuma sai ta samu kanta da raka shi da kallo har ya bacewa ganninta tana hangen hanyar da ya bi
Wani gwauron ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da NAHIDT ta ce" Ke Shuwwa"
A dan firgice ta juyo tana kallonta
Murya ciki ciki ta ce" Yaya kuka rabu? "
SHUWWAR ta sake kallon hanyar da ya haye din sannan ta juyo wajen Nahidt tana sauke wata ajiyar zuciyar again ta ce" Cewa ya yi ki kula mana, shikenan ya tashi ya yi tafiyarsa, bayan na barshi da gidansa yana jirana a waje, ya shigo ban yi gyare gyaren komai ba, uwa uba ban yi girki ba, Nahidt anya ba dana min tarko zai yi ta yadda ina shiga sama zan ji kaina ba a jikin jikina ba?, Kin san fa sojoji dukan matansu suke yi, anya ba tarani yake yi ta yadda laifina zai kai na ya batar da ni shikenan kowama ya huta?, Zuwa yanzu na fara tsoron kyaliyarsa da kawar da kansa a kan neman fitinata"
Nahidt ta shiga kwabe hijab din jikinta tana fadin" Yanzun dai tashi kike yi ki fada kicin, ni kuma bara na yi sallah na fito na shiga gyaran falon, Shuwwa an fada maki kowani namiji ne bai san darajar mace ba kuma bashi da ilimin adini ne? Dan kawai yana Soja baa hakan na nufin yadda yake da tsauri da tsagera da mararsa ji a waje zai kasance mai aikata haka wa iyalinsa, mau be kina auren namiji mai daraja, mai mutunci , wanda zai koya maki son kanki da kanki , mutunta kanki da kanki, uwa uba ya koya maki zama da namiji mai daraja , ya karyata hasashenki, ya birkita zuciyarki da dumin kaunar Soja!"
Tunda take kalaman ita kuma kallonta take yi har ta dasa aya Ajiyar zuciya ta sauke tana dan girgiza kanta ta juya ta nufi hanyar kicin din tana tunanin me ya dace ta girka masu sasauka a gidan duba da sun yi dare?
Mayafinta ta cire ta ajiye da jakarta mai dauke da wayarta sannan ta karasa wajen frij mai dauke da danyan nama da su kifi, da su naman talo talo
Naman talo talon ta samu ta ciro da kyar ta nufi wajen ruwa ta dauki roba ta saka shi ta kunna masa ruwa sannan ta barshi ya saki da kankarar da ta dafke shi Wajen dankalin turawa ta koma ta debo mai yawa sannan ta kawo abin bare bayan shima ta ajiye da wata robar da zatana zubawa idan ta bare
Harhada kayan jajage ta yi su tarugu, koren tatasai, da tafarnuwa ta jajaga su sosai sannan ta zuba su a cikin kwalba ta zuba masu Mutarde da mayonaise da garin magin tafi da gidanka da bakin poivre da fari da dan mai ta cakude su sosai sannan ta kawo su ta ajiye wajen kayan aikinta
Naman nan ta cire a ruwan nan ta sake masa wani ruwan, ta samu ta wanke shi tass sannan ta zuba shi cikin abin tsanewa ta sake komawa wajen dankalin nan tana ferewa tana sakawa cikin ruwa da sauri da sauri Sai da ta kusan rabi sannan ta koma wajen naman nan , zuwa lokacin ya tsane ruwansa tassss, hakan ya sa ta shiga tsatsaga jikinsa duba da manyan yanka ne sosai har uku ta ciro, bata cicira shi kannanu ba sai dan tsatsaga jikinsa da ta yi sosai ta kawo wannan jajagen da ta yi ta shiga shafa masa lungu da sako sosai tana shafe shi da shi Su dukansu ta yiwa haka sannan ta dauka ta saka a frij wajen yin sanyi ba wajen yin kankara ba ta rufe ta koma wajen dankalin turawanta
Ba ita ta waiga wajen naman nan ba sai da ta gama bare dankalin turawan nan tass sannan ta yanyanka shi dukanshi, zuwa lokacin ta dauki kusan minti talatin ta zuba dankakin turawan a cikin babar roba mai tiloli dan ya tsane ruwansa shima gaba daya sannan ta koma ta ciro naman nan Anfanin saka naman da ka shafawa jajagen nan a frij shine kayan zasu ratsa shi sosai ta yadda dandannonsa zai fi fitowa sannan zai fi gasuwa komai taurinsa domin hadin nan na saka namaa ya yi laushi ya yi gagawar gasuwa
Abin gashinta ta ajiye ta dauko takardar da ake siyarwa ta gashin nama ko cake t yanka ta saka a cikin abin hashin sannan ta dauki mai ta shafa sosai ta dora yanka biyu ta koma wajen foor dinta da ya gama daukan zafi a 250 wutar sama da ta kasa ta bude shi ta saka naman ta rufe sannan ta rage karfin wutar zuwa 200 dan kar naman ya dauki hanyar konewa bai gasu da kyau ba sannan ta komawarta wajen dankalin nan ta kunna wuta ta dora kasko ta zuba isashen mai sannan ta juya wajen kayan tea dinsa ta shiga harhadowa dasauri da sauri dan ta dora shi gefe shima ya dafa kansa a kan lokaci Man nan na yin zafi ta yanka albasa karama ta jefa cikin man suyar, hakan na saka dankalin turawan bada wani kanshi mai dadi da dandano Zuba mai yawa ta yi tana tsaye a gabansa har ya fara ja ta juya shi ta yadda dayan barinma ya dauko jan sannan ta rage wutar ta kwashe shi cikin abin tsanewa, da gagawa kuwa sai ta kawo gishiri na cikin kwanko garin nan ta dan yayafa da zafinsa ta juya shi ta yadda gishirin zai gamu a jikinsa gaba daya sannan ta zube sauran a man ta bar wanda ta kwashe din ya idasa tsane mansa bayan ta yafa kyale mai tiloli gudun wani abu ya fada kafin ta kawo abin zubawa
Nan da nan ta gama aikinta, a awa biyu danma aikin hannu daya ne kuma sai da ta bari ya gasu sosai , zuwa lokacin har ya dawo daga sallar isha'i yana mamakin aikin da yayarta ke sha ba ji ba gani falon ya dauki kanshi an gyara ko'ina masha Allah ya haye sama yana dan dafe cikinsa domin har ga Allah shi baya wasa da cikinsa sam
A hankali take tafia da kayan da ta jera tana adu'ar Allah kaita dinern lafia har ta fito suka hade da Nahidt A nutse ta ce" Wauh, Masha Allah......Shuwwa wadinnan plat din fa da kayan shayin?"
SHUWWA ta ce" rufa min asiri na ajiye kafin na barar sai na kaiki ki gansu, kulun su ke sake sakani yin sabon girki da su walahi"
Nahidt ta ajiye turaren wutar da take yawo da shi ta kama mata gaban tana fadin " ki rage kayan mana kar garin hawa ki zubar"
SHUWWAR ta ce" Hawa ina kuma? "
Nahidt ta dubeta a tsanake ta ce" saman mana, ko ba dakinsa zaki kai masa ba?"
SHUWWAR ta girgiza kanta Nahidt ta yi Murmushi tana fadin" mu ai a nan zamu ci ko? Muna so muci cikin sakewa ko? Ki kai masa Kawai mu sai mu baje a nan , domin kanshin gashin nan na halaka min yawu"
Yar dariya ta yi ta gyada kanta ta juya hanyar hawan a hankali tana hawa tana adu'ar Allah ya kaita lafiya da tunanin ko ya ci? Har ta haye sannan NAHIDT ta yi murmushi tana girgiza kai a ranta tana ayana'gidan rigima kennan, da ban yi mata dabarar ba, ba zata Kai ba"
A hankali ta samu ta bude ba tare da ta nemi izini ba domin kayan dake hannunta ko budewar Allah ne ya taimaketa ta iya budewar
A hankali ta shiga da salama a saman lebenta kasa kasa ba tun karfi ba dan kar ta saki farantin
Idannuwanta suka sauka a saman kansa yana zaune saman wata lalausar kujera ya mike kafafuwansa da alkur'ani mai girma a hannunsa yana karatu cen cikin kirjinsa
Samun kanta ta yi da zuba masa ido , ga wani sansanyan kanshi na tashi a dakin wanda ga dukan alamu turaren ruwa ne ya saka mai sanyin kanshi dan yaa ji dadin zaman
A hankali ta karasa ta samu ta ajiye masa a gefensa ta sake zuba idannuwanta a saman gashin da ya lulube kafafuwansa Haka kawai ta ringa bin jikinsa da kallo dan neman rigima har sukai ido hudu da shi, wanda hakan ya sakata dan hade fuska tana basarwar nan kamar kallonsa ba dan wata niya ta kalleshi ba ta yatsina fuska tana cije lebenta na kasa hadi da juyawa gaba daya ta mike da niyar tafiyarta dan ta kula kallon nan nasa kamar yanai mata kallon kyama ne!
Ajiyar Zuciya ya sauke yana girgiza kansa kasa kasa ya ce" My bed 🛏️"
Turus ta yi ta juyo ta kale shi na yan sekwani sannan ta cire kanta ta nufi wajen gadon
Yayewa ta yi ta yi mashine wash da su , sai da ta gama wanke su ta fitar ta fito ta bude dayar kofar da igiyoyin shanyan suke ta je ta shanya su Har ta juyo zata filo ta samu kanta da kurawa wajen abin fitila ido Abin ta sake kurawa ido sosai tana kallonsa kafin ta juya ta fito falon daidai ya dasa aya yana rufe alkur'anin ya mike ya nufi wajen ajiyarsa ya ajiye sannan ya juyo yana fuskantarta domin ya tabata tsayuwar nan da ta yi magana ce a bakinta
Ajiyar Zuciya ta sauke tana kawar da kanta gefe ciki ciki ta ce" Am, am, am .............."
Kasa karasawa ta yi, shi kuma ya tsaya ya zuba mata ido har zuwa gaban goshinta da gargasar gashin wajen ke bashi mamaki Idannuwanta ta dago ta dube shi sai kuma ta dubi hanyar da ta fito da hannunta ta dan nuna kafin ta kale shi ta dan shagwaba fuskarta tana sirintar da dubanta ta sake daukan duban nata ta sauke a hanyar da ta fito, hakan ya saka shi gane da abinda take nuna masa
A nutse ya taka ya zo ya gitata ya shige ciki, ya hara mata sansanyan kanshin turaransa da ya sakata lumshe idannuwanta ta bude ta raka bayansa da kallo sannan ta iya cira kafafuwanta da kyar ta bi bayansa
Wajen da ya fi dauke mata hankali ta yi ta nuna masa da idannuwanta har ya ga wajen shima Tsakani da Allah zuwa yanzu ya amshi gayatar wannan neman fitina, zai kuma nunawa mai yi cewar ba sani bane bai yi ba so ya yi ya sirinta, aman tunda wulakancin ya kai haka zai kwatanta masa shi riga yake da ita wace ta bashi damar taka wulakantace!
Da idannuwansa ya mata alamun ta wuce
Wucewar ta yi sumui sumui ta fito a dakin gaba daya
Gannin yana biye da ita ya sakata dan yin sauri ta sauka ta nufi dakin Nahidt domin ta gama komai ta zuba abincinta ta yi shigewarta dan dama babu abinda zata yi jira ai, da gangan ta cewa Shuwwa a nan zasu ci, aman me zasu wani ci a nan? Ai du abinta ta san daidai ta san akasin daidan
A nutse ya bude ya biyo bayanta bayan ta shige
Salama ya yi a saman lebensa sannan ya daga kansa ya shiga bin dakin da kallo kafin ya dawo da dubansa kansu sun yi tsuru tsuru sunna kallonsa gaba dayansu a tsaitsaye
Dan gyaran murya ya yi ya ce" Ku shirya mu tafi"
Daga haka ya so ya juya, sai fai tambayar da SHUWWA ta masa da sauri tana kallonsa cewar ina zasu tafi? ya saka shi juyowa a hankali ya ce" Capital "
A tare suka maimaita Capital?, Yana nufin garin iyayensa kennan fa?, Sai kuma Shuwwar ta ce" Aman yaushe?, Kuma da wa da wa? sannan a me? sai nake gannin dare ya yi ai yanzun?"
Nahidt ta gyada kai domin itama so take ta san amsoshin nan har ga Allah
Dubansu ya yi daya bayan daya Ko dan kwali yarinyar nan bata da shi a kanta, kuma abayar tata daga sama fa ta riketa sosai walahi
Kai ya girgiza yana sake kallonsu ya dubi agogon bangon dakin ya sake dubansu a kausashe ya ce" Now "
Daga haka ya juya ya fice a dakin, hakan ya sa suka kalli junna Shuwwar ta ce" Na ga annabi in na yi hali na gari, ke kuma me yakr nufi? "
Nahidt ta yi sakalau ta ce" Shuwwa ni na sani ne? Kin ga cewa ya yi Now, to yana nufin yanzun yanzu wai zamu yi doguwar tafiyar nan? Ko dai mutuwa aka yi ?"
Rai a hargitse SHUWWA ta💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 3️⃣7️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
*AUNTY SAJIDA NI FARA CE, MATSALATA BAYA KYALI, HAKA KUMA INA DA YARINYA DA NA HAIFA ITA KUMA TANA DA DAN DUHU KASANCEWAR MAHAIFINTA BAKI NE, DU IRIN SANYIN AC DA CIMA MAI KYAU BAMA KYALKYALI IRIN NA YAN GAYU, GAMU A GARI KUSA DA SHUGABAN KASA.......* 😂............................................................................. Amsa " Dan gwada shafa madarar ruwa peak a fuskarki idan da hali har hannayenki, sannan itama ki gwada shafa mata kadan ba da yawa ba, da zarar kin bude ki saka a frij bata komai, idan kun shafa ku barta ta bushe sai ku wanke da ruwa kadai marar sanyi karara sannan marar dumi...........kyalin fata kike so? Zaki bani bayani yar uwa🥰🥰🥰🥰🥰🥰