Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 35
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 35: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 35. Cokalin mai yatsu da yar karamar wukar da yake anfani da su ya ajiye…
3,296 words
Cokalin mai yatsu da yar karamar wukar da yake anfani da su ya ajiye a hankali yana kallonta, a nutse ya ce" Mamah, to ni ai ban zauna ba, dazun ne yayar tata ke ta fada cewar su marayu ne iyayensu sun rasu, ni dai daga haka ban san komai ba, ita kuma ai ba'a doguwar magana da ita yanzu aljannunta sa tashi"
Ikon Allah kawai take kallo, wai yaron nan anya lafiyarsa kuwa? Wai yaushe zai fuskanci rayuwa ya ji dadinta? Yanzun yana da mace kamar wannan yana son fahimtar da ita cewar ita dinma yar nesa da nesan ne? Aman gaskiya ba zata lamunta ba, zata kwatanta tata hikimar ko yayane, a nutse ta ce" To dama da yayar tata suka tare ne?"
Kansa ya girgiza yana shan ruwa ya idasa sha a nutse ya ce" Aa, washe gari ta zo , ai inaga ta fitar da miji zan aurarta"
Wani mamakin ne ya sake kashe Mama a zaune, gaba daya komai a dunkule yake bata ya karashe da fada mata shi zai rike yayar matarsa ya aurar? To wai ita din zai zauna da ita din a matsayin iyalin nasa ko yayane? Zata kuma yin magana Shuwwa ta fito tana ta tare abayar da ta doro saman mayafin abayar da ta daura a jikinta domin ba zata iya maida kayan cen ba ta ce" Mama ba'a shigo mana da akwatunnanmu ba?"
Mama ta waiga tana mikewa ta ce" Akwatunna? To ko a mota aka barsu bara na je na gani?"
Da ido ya kalli Mama tana son mikewa a hankali ya ce" Ba'a zo da su ba"
Ido Shuwwa ta kwalalo tana kallonsa ta ce" Na'am ?"
Kallonsa ya maida kanta gannin yadda ta yi da idon da bakin da hannayen har ta saki abayar dake jikinta
Kin bata amsa ya yi ya shiga kokarin mikewa hakan ya sa ta matso da dan sauri tana son yin magana aman sai ta ga ya zagayeta vai bata damar yin maganar ba ya shiga zagaye falon a nutse yana kallon bangon falon, sannan ya nufi dakin da aka sauke su ya dan kwankwasa ya yi salama Sai da Nahidt ta amsa ya tura ya shiga Bai kaleta ba ya ringa bin dakin da kallo, har bayi ko'ina sai da ya duba sannan ya fito ya dawo gaban Mama da itama ke tsayen sunna jiransa da tunanin me yake nema kuma?
Tana gannin ya dawo ta dan gyara tsayuwarta tana cewa" Yalabai , ina nufin akwatunana fa da na aunty da muka kamo ka ce mu bari yarenka zasu dauko, sunne nake tambaya ko sunna cikin mota ne? Duba da komaina a ciki zan cenza na kwonta ne"
Bakinsa ya tabe yana ajiye wayarsa a nan ya juya da niyar tafia bai bata amsa ba hakan ya sa Mama fadin" MUHAY "
Cak ya tsaya yana lumshe idannuwansa ya juyo yana kallonsu ya ce" A ina kika sayi akwatunnan da suke dakinki?"
Tambayar ta zo mata wata iri, hakan ya sa ta dan zuba masa ido kafin ta ce" Ba ni na siya ba, na aurena ne da aka ringa kawo mini"
Da haushi da mamakinta yake kallonta kafin ya girgiza kansa ya ce" Sun haramta a gareki!"
Daga haka ya fice a falon gaba daya, inda ta raka shi da kallo kafin ta karaso kusa da Mama hankali tashe da jin sun haramta a gareta, su wa din? Biyun ko duka? Tana zuwa ta shagwabe fuskarta kamar zata fashe da kuka tana fadin" Lah mama, kayan nawa duka yake nufi? Innalilahi Mama me zan saka to kayana mama, mama kayana"
Mama da wani irin farin ciki ya boye a zuciyarta tana kallon SHUWWAR tamkar ta saka daria a mutunce ta ce" Mu je ki saka wata rigar yanzu, da ke da yar uwarki akoy rigunna dogwaye a nan na anfanina, idan ya so da safe in sha Allah da kaina zan fita da ku Super market ko ku je da yan uwanku, ko a kawo maku ku hada akwatunna idan seti nawa kike so, kar ki damu dama ai bai maki akwatunnan aurenki ba, zai yi su ne ya kuma rama maki naki da ya haramta maki"
Sai a lokacin ta sauke ajiyar Zuciya, aman duda haka ta kasa gane a kan wani dalili zai ce ya bada kayanta? Ina ruwansa da kayanta? Kuma ta tabata wasu kayan har ta mutu ba zata iya maida irinsu ba, haba dai komai kudinsa ai ba zai iya yi mata siyayar maza biyar ba walahi!............(🥺☹️🥺)
___________________________________
"Itace ke tura maka da masu neman ranka son, Ouseina ce ke son kasheka? Idan har Ouseina ce na rantse da Allahn da ya halice ni zan mayar cewa ita din yar uwata ce gefe, na maida raunin yar uwarta gefe, na gurfanar da ita a gaban kotu, domin idan har ita ce ba zan yi sake na barta ba, dan kuwa idan aka kyaleta tabas ni da kaina ba zan samu hutun zuciyata ba da barin bata gari bata zumuncin Allah a gari!" CHIEF OF ARMY Ya fada a kausashe yana kallonsa a cikin masalacin da suke zaune bayan an gama sallar asubahi kowa ya watse ya kasance daga shi sai Muhay sunna zantawa dan har yanzu MUHAY bai rintsa ba sanadiyar kiran yar uwar mahaifiyar tasa da ya samu jin ya shigo gari ta sake jadada masa ko hudu zai aura tana kan bakanta ba gudu ba ja da baya, wannan ya sake daga masa hankali da tunanin yanzu da ya matso kusa da ita zata yi kokarin damun rayuwarsa ne
Idannuwansa ya lumshe a hankali ya bude yana kallon FATHER, a nutse ya girgiza kansa yana kallon gefen dardumar da yake zaune
Idannuwansa ya rintse ransa na kunna ya ce" Da acema wannan ta nema, watau raina ta nema, da zan iya cewa zan yi ta rufewa har mu koma ga ubangijinmu, Dad ba ita ke neman raina ba"
Father da mamaki yana kallonsa ya ce" Ban fahimceka ba son, kana nufin ka san wanda ke neman ranka, kuma a laifin da ya sa baka zumuncin da abokiyar tagwaitakar mahaifiyarka har akoy wanda zai zarce neman kasheka? Subahannalah menene wannan? Kuma su waye masu son ranka? Dan Allah ka fada min yau ko zan samu nutsuwa ka fada min ko zan iya rintsawa, u see ni Abanka ne, Allah ya jikan mahaifinka koda yana raye nine da alhakin nan a kanka domin jine zan hukunta mai neman ranka yarona!"
Fuskantar Father ya yi shima ya gyara zamansa a hankali ya ce " Wani lokacin, shirun ya fi maganar alkhairi, wani lokacin bawa kan rasa ina zai duba ya samu fasarar wani lamarin?, Dama ace abokin hamayar kujerar da nake sama ke nemana da fitina, da na nemi mu yi fito na fito da shi, dama ace wanda na aikatawa wani laifi ke son neman fansa a kaina Father, tabas da na kwatanta bashi dama mun gwabza ta yadda mai iya fida kansa zai fida kansa........sai dai......." Ya karashe yana mai dantse lebensa da yin gum yana dan girgiza kansa
Father da gabansa ke faduwa ya ce" sai dai me?"
MUHAY ya dube shi ido cikin ido ya ce" Sai dai ni dan halak ne, kuma ina bashi dama ko zai fahimta ya gyara, aman ina tsoron na kasa hakuri....Father ina tsoron kokarin cin zarafin iyalina da ake son yi karfi da yaji ya sa na gagara hakura na shiga inda yake na daukoshi a hannuna na maka shi da kasa ta yadda bakinsa ba zai kuma yin wani furuci ba bale har ya kai raini wa ahalina!"
Sosai ya hau a furucinsa kuma kana iya gane abin daga zuciyarsa yake fitowa kuma yana masa ciwo sosai Hakan ya sa Father ya girgiza kansa a sanyaye ya ce" sai na ji na tsorata Muhay, ka san me ya tsoratani? Yadda ka kasa furtan sunnan waye ke neman hakan, hakan na sakani tunanin kowa, ina kamo kowa ina masa kallon nan, na kasa tsayar da tunanina waje daya, sannan ita yar uwar mahaifiyarka menene laifinta a gabar dake tsakaninta da kai? Ka kuwa san girma da darajar zumunci? Allah ya la'anci mai yanke zumunci MUHYIDEEN"
Idannuwansa da sukai ja ya rintse har gaban goshinsa na harbawa da zafi da zafi
Sai da ya sauke ajiyar zuciya ya fi a irga sannan ya bude yanna kallonsa ya ce" Tana fama da tabin hankali ne, rashin hankalin dake damunta ya hadasa mata kudiri marar kyau a gareni, fama take da mugun kudurin da take ikirarin soyaya take ji a zuciyarta ta budurwa da saurayi wa ni, har ya kai ta nuna zata iya barin adininta ta aureni in dai da wani adinin da zai halasta mata hakan a lokacin da muka shiga rigimar maganar nan da take tardani dakina a kowani yannayi ta nunan hali na son kasancewa abu daya da ni, duda na bijiro da son auren y'arta dan ta shhafa min lafiya, harma Mamahnah ta yi farin ciki taa shige gaba aka yi, sai dai da kanta ta fada min cewar ko wa na aura tana kishinsa kuma sai na sake shi, ta nunan sai fa na yi zama irin na aure da ita da auren ko babu, kai a kaina zata iya aikata ko meye ciki harda barin adininta..........Father Uwata?".........ya idasa yana nuna kansa da yar yatsarsa wanda hakan ya saka Father zarro idannuwansa ya mike tsaye jikinsa na rawa yana kallonsa ya ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une Innalilahi wa inna ilaihi raj'une Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, wani irin guri ne shedan ya samu a cikin zukatan al'umar annabi har ya hadasa rauni haka? Hasbunnalahu wani'imal wakim ina zamu shiga da ranmu mu ji sanyi?, Wannan magana ina zan nufa da ita na iya rintsawa? Me ya hadasa haka? Ta yaya haka ya faru? Y'arta? Me ya hadasa haka?"
Kakausan murmushi ya yi yana girgiza kansa ya ce" Shi yasa na rabu da dukan abinda na gada na mika maka dan ka juya ko zan fahimci abinda ya kaita aikata haka, na rasa gane bakin zarren, na rasa gamte dalili, a wuni sai ta yi min kirra ashirin bana dagawa, idan ta gaji ta rikice sai ta fadawa yar uwarta mai rauni cewar na yanke zumunci da ita, ita kuma sai ta rikice ta rikice ta ringa yi min fadan na kiyaye na ringa zumunci da mamana, ta ina zan fara zumuncin da ita? Ta ina zan gane fasarar matsalar nan ni kuma?"
Father abin kam ya dake shi, gaba daya jikinsa rawa yake yi bawan Allah, a hankali ya koma ya zauna yana kallon dan amininsa kuma dan yar uwarsa, yana mai tunanin ta inda zai kama dan ya sasauta abubuwan dake damunsa, ta inda zai kama dan ya hankaltar da haukan abokiyar tagwaitakar mahaifiyarsa, ya tabata tagwaitakar ta taba hankalinta, tabas ta taba hankalinta A sanyaye ya ce" Menene dalilin da ya sa ake neman rayuwarka?, Waye yake haka?"
Muhay ya zuba masa ido, sosai yake so ya buda bakinsa ya ce da shi wane ne, yana so ya sheda masa cewar wane ne Father, sai dai me hakan zai haifar? Idan aka yi nazari aka duba dogon zangon tafiyar tabas akoy cutarwa da jin kunya a ciki, akoy watsewar doguwar alaka a ciki, gani yake yi ya dace a gane cewar albarkacin mai fada a ji ya sa ya kyale, duda yanzun an fara shigar masa hanci da dukunkune sosai,
Dan murmushi ya yi yana girgiza kansa Watau mai aikatawar ya yi ganganci sosai, a tunaninsa har ya kai matsayin da zai iya aikata bincike da aiki ta kasan kasa wa soja? Shima ya iya gane hanyar boye boyen sirri bale soja? Kai ya girgiza yana kallon Father ya ce" Wani lokacin, rufe asiri ya fi Alkhairi kan tona shi Dad, ka min alfarmar dan lokaci, na kwatanta taro mutumen, idan na ga ya fahimci na san shine ya ci gaba da shiga hurumin iyalina.......to tabas zan dago shi na maka shi da kasa, Father tabas zan tona masa asiri a bayane, ba zan iya kyale wannan ba, bale ko dan farcensu ba zan lamunta a taba ba, dan ji nake Uba nake a wajen iyalina wanda ya isa ya kare su!"
Father ya lumshe idannuwansa yana girgiza kansa, yana jin ciwon damuwar yaron a cikin zuciyarsa, yana jin damuwar yaron har bargonsa, zai iya rantsewa matsalar yaron na damunsa tamkar matsalarsa ce, yana so ya talafa masa sosai a rayuwa , sai dai tunda ya nuna a bashi lokaci zai bashi, aman shi ya dauki aniya da kansa sai ya hukunta mai aikata masa haka a bayane dan mai shirin aikatawar ya ji tsoro!, Ko babu alaka ta haihuwa tsakaninsu shi din Soja ne, a karkashinsa yake, yaronsa ne mai amana,, a sanyaye ya riko hannunsa yana kallonsa ya ce💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 3️⃣9️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
A sanyaye Father ya ce" I'm sorry "
MUHAY ya kalle shi da mamakin jin furucinsa
Father zai sake yin magana wani yaro almajiri ya shigo da salama ya duka ya ce" Aba wai maman su Ummi ce ta ce ka zo da gagawa ana fada a gida."
Da mamaki suka kalli almajirin sai kuma zunbur Father ya mik'e yana maimaita" Fad'a kuma?"
Kafin yaron ya bashi amsa har ya kusa fita a masallacin inda MUHAY ke take masa baya saidai tafiyar a yannayi na takama yake yin ta da k'asaita.
Suna shiga gidan idonsu ya sauka kan Umma babar yar Chief of army da uwar gidan MUhay sun kacame junnansu suna dakuwa, wanda ba komai ya jawo haka ba sai labarin da ta ji a bakin mahaifiyyarta cewa ai yau wani wulakancin da suka tashi da shi a gidan nan Muhay jiya ya shigo da matar da ya aura a cen harda yayarta, wannan lamari ya tunzurata ta fito a shiryenta dan ta je ta ga sabuwar yar shigen sauri a fadar da ba tata ba
Had'ewa sukayi da uwar gidan Muhydeen wacce ta shiga jifanta da wani mugun kallo, bata damu da ita ba dan ba ita ce a gabanta ba, har ta d'an wuce cike da izgili tace "Iska dai na wahalar da mai kayan kara, sai rashin zuciya kamar kazar da bata jin as"
Tsayawa tayi tare da dawowa baya ta shiga kallonta a kausashe tace "Bana jin ni da ke muna da bambamci indai a wajen MUHAY ne, dan ga dukan alama ke ma iskan wahalar dake yake sakamakon dakon kayan karmami da kike yi"
A hassale kamar mai jiran tab'i tace "K'arya kike wallahi, dan ko ba komai ni ina amsa sunan matarsa, ke fa ? A cikin gida kike ke ba karuwa ba kuma ba cikakkiyar mace ba mai daraja ba, ke kulun kina jira ki ga motsinsa"
Cike da neman fitina da rashin wayo Umma tace "Sai dai in uwarki ce karuwar amma ba ni ba, jaka kawai, ita matar so d'in ai gashi ya taho da ita har nan, ke fa ballagaza kina zaune ki.."
A tsiyace ta dafe k'irji tace "Ni? Uwata kike fad'ama karuwa?" Ta katse maganar Ummar
Cike da rashin aji da d'aukaka martabarsu ta 'ya'ya mata sai kuwa suka had'e jikinsu da sunnan dambe wanda sam ba tsari a hakan face zubar da mutumci, musamman ma a wajen uwar gidan Muhay wacce da ta san darajarta da kimarta ba za ta yi fad'a da wacce ma ta amsa sunan matarsa bare kuma wannan.
Uwar gidan Father ce ta fara fitowa tana neman rabasu da kwaroroton zancen tana daukaka maganar har maman su Ummi itama ta fito wace ta kwana bata rintsa ba itama da nata kalar bacin ran ta ce "Kai! Kai me kuke yi hakane? Ku saki junanku."
Ba wacce ta san tana yi in banda dambatuwa da suke, sake bud'e murya tayi tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Na shiga uku na lalace, wannan wace irin masifa ce ? Ku kenan kullum a haka akan namiji...wai za ku bari ko sai na had'aku da Chief?"
Duba da babu wacce ta kula da ita yasa ta kada daya daga cikin sojawan dake bada tsaro kan maza ya kira mata CHIEF duda ta sani sarai dokar gidan ba'a aikensu ko nan da nan
Maman Ummi na gannin haka ta hanna ta nufi almajirinsu mai yiwa yaren dan aika wanda sunne suka dauke shi yana ta faman share wajen flowers d'in nan ta turashi ya kira Father.
Father na k'arasowa a tsawace yace" Kai meye wannan kuma!"
Umma ce ta fara kiciniyar raba jikinta da ita tare da dafe kunnenta daya had'e da rigarta, a hankali suka raba jikinsu sai huci suke uwa wasu zakuna suna ta k'ok'arin gyara kayan jikinsu duk sun cimimiye.
Matsawa Father yayi saida ya je gaban Umma ya d'aga hannunshi ya wanke fuskarta da mari, razananniyar ihu ta saki tana d'agowa ya kuma zuba mata wani marin, cikin tsananin b'acin rai da takaici ya juya ga sojawan dake tsatsaye suna kallon ikon Allah, tun farko sun so raba fad'a to amma duk mata ne ba zasu iya kama jikinsu ba, bare fad'an mata da kan k'asa ake kai nushi sai a samu d'an rabo ba gaira ba dalili ga cizo da yakushi, nuna musu Umma yayi a hassale yace "Kai ku d'auke ta ku kai min guardroom d'in nan, sai na tabbatar tayi hankali koda zata fito."
Ya k'arashe da kallonta yana zabga mata harara yace "Yar iska kawai."
Uwar gidansa da abun bai zo mata yanda ta so ba rufe baki tayi jin ya b'aro wannan zagin, dan a saninta da shi ba ma'abocin haka bane, ga kuma wani tashin hankali wai a kai Umma guardroom, to a kan me?
Umma kam fashewa tayi da kuka uwa jiniya ta durk'ushe tana fad'in "Dad ka yi hak'uri dan Allah ba zan sake ba, wallahi ba laifina bane."
A harzuke Father ya nufi part d'in shi ba tare daya kula kowa ba dan idonshi a rufe suke da b'acin rai, ita kanta ba dan yana kallonta a matsayin sarakuwa ba, da sai ya falla mata marin dan ta gane ba'a masa haka.
Shuwwar da Nahidt da ke tsaye kusa da juna wannan hargagin ne na uwar gidan Father ya fito da su dan ko baccin su basu gama ba, dan Shuwwar ma kayanta na jiya ne da ta cire doguwar rigar da ta kwana da ita ta saka su domin sun bushe yanzun watau farin dogon wando da farar riga mai dogayen hannu kanta ko d'an kwali babu sai ribom d'inta daya kusa fita a kan ta.