Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 40

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 40

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 40: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 40. Dan murmushi ta yi ta cika kofin ta dan kwanta a saman gadon irin…

3,258 words

Dan murmushi ta yi ta cika kofin ta dan kwanta a saman gadon irin kwanciyar nan ta ruf da ciki ta dan dage kafafuwanta hakan ya sa kwaurinta bayana kuma kafafuwanta babu safa tana rike da kofin tana niyar fara sha mama ta fito Nahidt na biye da ita wace ta sha hawayenta a lokacin da ta hau po din nan ta ringa tunanin yau suma wata ce ta basu abin gyaran da zasu gyara kansu ba su da kansu ne sukaiwa kansu ba, subahannalah ai dole mutun ya yi kukan farin ciki, dole abin nan ya zo masu wani iri

Mama ta dan tsaya ta karewa kwonciyar Shuwwar kallo kafin ta yi murmushi ta karasa wajen kayanta ta bude ta ciro safunna masu tsayin gaske sannan ta dawo wajen gadon

Tana zuwa Shuwwa ta tashi da sauri tana kokarin zama

Mama ta kyaleta sai da ta gama zaburar tata sannan ta ajiye saffunan tana kallonsu ta ce" Irin wannan kwanciyan bashi da kyau IBTISAM, kin ga kwanciyan nan ya nasa maman mace ya tabe ya zube, sannan irin daga kafafuwan nan da kika yi ke ba safa a kafa ba, ke ba irin wandon nan mai saka dumi a jikin mace ba, hanya ce mafi sauki da iska zata samu damar shiga cikinki, iska irin mai haifar da tusar gabar nan"

'Na shiga uku, wai dama haka take Maman ? Tusar gaba kuma? Gaba dama tana yin tusa ne ba sai baya ke yi ba?'......Shuwwa ke ayannawa a kasan zuciyarta cike da jin kunyar maganar

Nahidt kuwa da ta san me hakan yake nufi sai abin bai bata irin kunyar nan ba, ta saka safar Itama kafarta daya ta sauke ta amshi safar ta saka, ta sauko dayar tana kokarin gyara rigarta da ta yi sama har wajen cinyoyinta aka dan kwonkwasa kofar dakin

Ba'a basu damar kimtsawa ba aka sako kai Cikin dakin

Da mamaki yake binsu da kallo a kuryar dakan mahaifiyarsa?, Saima da ya ga irin zaman da suka yi watau Shuwwar da mamansa ya sake binsu da kallo kafin ya maida dubansa kan mahaifiyarsa dake dan Murmushi tana kallonsa

Murmushin ya yi shima wanda iyakarsa saman lebensa kasancewar zuciyarsa na a cinkushe da tunani a sanyaye ya ce" Kys din gida daya nake so"

Mama ta dube shi da kyau da yannayin amon da muryarsa ta bada A hankali ta dan mike tana kallonsa ta ce" Baka da lafiya ne? Wa zai je gidan? Wane a cikin gidajen?"

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon mamansa, ita kam da zarar ta dan rikice sai ta aniya jero tambayoyi

Dan ajiyar zuciya ua sake saukewa yana kallonta

A sanyaye ta ce" Ko da IBTISAM zaku kaura cen din??"

Gabansa ne ya yanke ya fadi jin sunnan da maman ta ambata, duda ba yai ya fara ji ba, a hankali ya sake maida dubansa kanta , daidai gaban goshinta kafin ya dan cije lebensa yana tunanin shin abinda ya yi niyar yi zai aikata ko kuma sai ya katse abinda yake daskare a zuciyarsa na wasi wasi ne?, Niyarsa yaa kaisu daya daga cikin gidajensa, ya kilacesu ya saka masu kulla da su, ya dauko malaman da zasu kula da lamarin datijon nan ko Allah zai sa a ga sauki a al'amuransa, idan ya dawo cikon hayacinsa su zauna ya masa tambayoyi a kan maganar nan, idan har ya fada masa sunnan wanda ya azabtar da shi a fada shi kuma ya je ya kaamo shi ya masa hukunci daidai da laifinsa

Sai dai a yanzu sai yake ji yana son cire wasi wasin haka a ransa, hakan ya sa a dan hankalce ya ce" Ku fito ku dukanku"

Da Maman, su Nahidht din dukansu suka kalle shi, sai dai bai basu damar tambayarsa ba ya ficewarsa a dakin

Kallon junna suka yi,sai kuma Mama ta sauke ajiyar zuciya tana fadin" Ku mu je Allah ya sa alkhairi ne" Shuwwa da jikinta ya mutu jin bakon yannayi ta samu kanta da fadin" Ko wani laifi muka yi?"

Nahidt ta dubeta ta dubi Mama itama abinda take ayannawa kennan

Mama ta yi dan murmushi gannin yannayinsu ta dafa gefen kafadar Nahidt dake tsaye ta ce" Ku saka hijabanku mu tafi, in sha Allah Alkhairi ne" gaba ta fara yi domin itama tana so ta ga abinda yake faruwa, dan fuskarsa a hade take sosai, yannayin maganarsa kuma na fita da sanyi kamar ba danta ba, abinda yake damunsa mai karfi ne gaskiya, koma menene tana fatan Allah ya sa ba wanda zai hargitsa farin cikin marayun nan bane, domin wannan karron ba zata iya barinsa ya saki yarinyar nan ba ko kadan

Gannin waje ya nufa ya sakata dan dakatawa har suka fito kowace tana tafia ne a hankali suka karaso kafin su jeru su fita a falon gaba daya

A irin wannan lokacin kasancewar rana ta fara yin zafi duba da gari ne mai zafin rana ya saka daidaiku ke karkashin ranar nan, sai masu gadin gidan, yawancin mutanen gidan kowace na bangarenta tana hutawa, bama kamar matarsa da rabonta da lekowa tun jiya gaba daya ta tsangwami kanta da nutsuwarta, a tsoracema take da shi sosai, hakan ya sa ta labe a ciki

Gannin ya mike da tafiyarsa ya saka Mama dan daga kafa tana fadin" MUHAY ina zaka je ne haka da mu?"

Dan juyowa ya yi , hakan ya sa ta fuskanci ai waya ce a kunnensa amsa kira yake yi,

Gabanta ne itama ya fara faduwa tana biye da shi ne kawai, har tunani ta fara yi ko wani abu ne ya samu mai gidan nasu?

A hankali Nahidt ta riko hannun Shuwwa tana kallonta, muryarta a raunane ta ce" Shuwwa, kar mu je, dan Allah kar mu je ya sake ki, kin ga mun fara samun soyaya irin ta uwa, mun fara jin dadin uwar da bata haife mu ba aman kuma ta san cewa d'a na kowa ne, kar mu bishi ya sake ki ya katse mana wannan gatan, Shuwwa da ta zare min ido kan sai na koma saman PO din nan kuka na yi, ba na komai ba sai na tuna Mamanmu....."

SHUWWA ta lumshe idannuwanta a sanyaye itama ta ce" Kin ga, abinda ya yi niya zuwanmu ko dakatawarmu ba su zasu hanna shi yi ba, kin san ai yana da gardama sosai, bana tunanin mun isa mu saka shi ko mu hanna shi wani abin, Allah ya zaba mana abinda ya fi zama alkhairi zo mu je kin ga sun bude bayan motar chan"

Kafin suke karasawa suka ga Mama ta juyo a firgi ce tana kallonsu, kafin ta daga masu hannu tana fadin" Kar ku karaso ku tsaya daga cen......"

Gaba dayansu suka ja suka tsaya gabansu na ta faduwa

Mama da jikinta ya dauki rawa ta kalle shi tana fadin" Ka karra ganar da ni abinda nake ganni a kamanin matar nan da yayar matarka MUHAY"

Gwauron numfashi ya sauke ya ce" Kadeta na yi, ................" A sanyaye du ya fada mata abubuwan da suka faru har zuwa yanzu, hakan ya sa a wani firgicen ta sake kallon Matar dake hangensu aman bata jin tataunawar da suke yi, gaba daya kuma ta sake tsurewa da tunanin har an shigo da su wajen da za'a sake salwantar da rayuwarsu kennan

Ta so ta nuna masa idan y'ayan suka ga mutumen nan kuma ya kasance mahaifinsu ne a haka a lalacen nan hankalinsu ne zai tashi sosai

Sai dai kuma ta tabata uwar ba zata yarda a rabata da mijinta ba da wani kwakwaran dalili ba, sannan a yanzu ba zata so ci gaba da ganninsu sunai mata kallo irin na marayun nan da zarar ta kyautata masu ba, haka kawai take jin kaunarsu a cen kasan zuciyarta da son kyautata masu, dan haka ta sake fuskantarsa ta ce" Da ka fadawa Abanku mai yace?"

Hannayensa ya dan watsa ya ce" Yana cikin taro ne, na dan so kwatanta masa na ga zan yi ta magana ne ba zai fuskanci inda bayanina ya dosa ba"

Kai take gyadawa ta nufi motar ta sake bude bayan

Matar ta dan takure jikinta tana kallonta hakan ya sa Mama fashewa da kukan tausayi tana kallonta

A sanyaye da yaren buzanci ta ce" Su waye suka wulakantaku haka har suka saka muku tsoron mutun dan uwanku mai numfashi? Kin ga yaya sunnanki dan Allah? Kama hannayena ki zo ki ga wani abu, taho ki gani kin ji?"

Duda yaren haihuwarta Mama ke yi, sannan kalaman na mama kalamai ne masu saka Nutsuwa da yarda a zuciyar mutun, aman gaba daya sai Manma ta kasance kamar kurma a gabanta sannan ta kasa barin jikin mijinta du sai takura masa take yi bata sani ba

Sosai tausayinta ya karra kama Mama, ta juya wajen MUHAY zata fada masa cewar ta ki yarda ta fito sai ta ga ya juya wajen da suke da hannayensa ya yafito su

Sai da suka kalli junna kafin suka nufo shi kowace jikinta a mace sosai da kuma tsoron abinda yake faruwa

Sunna zuwa wajensa ya saka hannunsa ya kamo na Shuwwa hakan ya sa ta dago tana kallon fuskarsaa hadi da jin faduwar gabanta na tsananta

A hankali ya ce" Yaya sunnan mahaifiyarki?"

Shuwwa ta karewa lebunnansa kallo da ya dire maganar , hakan ya sa idannuwanta suka farra rawa

Nahidt dake kallonsu ce ta kai hannayenta wajen kirjinta tana rungumewa a hankali ta ce" Tsoro nake ji, jikina bari yake yi, Shuwwa tsoro nake ji, wayo Allahna me yake shirin faruwa? Yalabai me kake so da sunnan mahaifiyarmu? Sunnanta TINANA, haka sunnanta yake Shuwwa me yake faruwa ne ?"

Tunda ta fara magana matar ta juyo da karfi tana kallonsu ta madubin motar, kasancewar mai duhun gilas ne sai dai ka ga wanda yake waje ba dai shi ya ganka ba

Kalaman dake fitowa daga bakinta suka saka matar sake kura mata ido har sai da idannuwanta suka fara zafi

A yanzun da kanta ta miko kafafuwanta ta nufo fitowa jikinta na rawa har ta bayana gaba dayanta a waje kafin ta zubawa yan matan ido gaba dayansu

Wajen da ya zubawa ido suka juyo dan gannin me yake kallo ne kuma?

Kallon yan matan take yi itama da wani kallo mai nuni da kamar tama a tsorace da ganninsu a haka ne ko kumaa bata yarda cewa wadinnan din y'ayanta ne da ta haifa a duniya ba duba da ta baro su a cen karshen duniya yaya aka yi suka samu zuwa nan? Kai kwata kwatama ta yaya suka samu kasancewa a nan kai tsaye haka? Haka summa suke masu binta da kallon da ya dakatar da bugawar zuciyoyinsu, ballema Nahidt da wayonta a lokacin ya fi karfin wasa ko yaya mahaifiyarta ta zama ba zata bace mata ba, zuwa Shuwwa din da karfin jinnin haihuwa da kamanin suke ta dawo mata suka sakata daskarewa tana kallon matar da a jikin mahaifiyarsu kamar an raba hudu ne an bata daya, haka farin fatarta ya yi duhu , sannan fatar tata du taa bushe ba kamar matar da sukaa sanni yar gatan mahaifinsu mai kyau da tsari, mace mai lafiya da fara'a ba

A hankali SHUWWA ta ringa lalube a cikin duhu, domin so take sai ta riko hannu a cikin hannunta, aman ta kasa riko hakan har dai Maman MuHay ta fahimci haka ta karasa da sauri kusa da ita ta riko mata hannun tana kallonta hakan ya sa ta juyo, sai dai gannin ba Nahidt din bace sai ta saki hannun da sauri ta kuma damko na Nahidt din tana kallonta a dan tsorace ta ce" Kin ga , kina kuwa ganninta? Nahi itace?"

Nahidt ta juyo a hankali tana kallon fuskar SHUWWAR Da karfi ta janyo Shuwwar suka rukunkume junna ta fashe da kuka mai karfi tana ihun fadin" wayo Allahna wacece wannan mai kama da mamanmu? Wayo Allah mun shiga uku , Mamanmu ba haka kamaninta suke ba, wannan ramamiya ce kuma ....kai wayo Allahna Shuwwa ba ita bace, ba ita bace SHUWWA ba ita bace....."

SHUWWAR dinma da jikinta ke rawa ta sake neman bambarewa daga jikin NAHIDT, sai dai tai mata wani irin riko tana kuma fadin" Ba ita bace, su a saudiya aka ce sun rasu, a saudiya muka baro su, a saudiya aka kamo mu aka baro su, au din ba zasu taba yin nesa da mu su barmu daga mu sai mu a cikin duniyar nan ba, Babanmu ke cewa zai iya yaki da duniya kaf saboda mu, su ba zasu barmu a wulakance ba...... Innalilahi wa inna ilaihi raj'une ki yarda sun rasu, ke ko yarda sun rasu mun fara gannin fatalwarsu ne ko? Du laifinki ne, kece kike taos su daga kabarinsu!"

Matar nan dake kallonsu kamar an dasata idannuwanta ne suka farra gannin dishi dishi

A hankali ta dan sake kallonsu tana ta hanna kwakwaluwarta yi mata cakule dan bata so ta hargitsa mata tunaninta

A hankali ta dan daga kafarta muryarta a cen kurya da yaren larabci ta ce" NAHIDT, IBTISEEMMMM...... "💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 4️⃣5️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

A hankali ta ce" NAHIDT.......IBTISEEMMMMMMM......." Sansanyar, zazakar murya mai irin nata salon da har yanzu babu bawan da ya lakanci sunnayensu kamar wa'inda suka zabar masu su ne suka sake dokar dodon kunnayensu, hakan ya sa a haulace suka saki junna sunna masu zuba mata ido a lokacin da take karasowa tamkar jikinta zai rabe biyu domin har kadawa take yo tsabar rawar da jikin nata ke yi har ta karaso wajensu ta kai kasa kamar yadda suke kasa ta zubawa fuskokinsu ido tana kallo

A hankali ta daga hannunta ta kai daidai fuskar Shuwwa dake kuka tamkar zata side ta shafa gefen fuskar tata a hankali , sai kuma ta saki wani irin lalausan murmushin da ya bayanar da farin ciko, nutsuwar da ta jima bata yishi ba a saman lebunnanta duda a busshe yake kamar yadda hannunta yake bushe kafin hannun nataa ya sakai ya tafi ya fadi kasa , alamu suka nuna kansu na ta suma ne

Ihu suka saka kusan a tare, wanda ya saka Mama zabura daga hawayen da take ta nufo su da sauri tana ambaton sunnan Allah gannin yadda NAHIDHT ke girgizata tana sake girgizata tana ihun fadin" ANNNA,, kar ki mana haka, baki mutu ba tun baya kar ki mutu yanzu, Anna ki tashi ki ji irin rashin jin da muka tafka ki zane mu, Anna kin san da ni yawon banza na ringa yi Ibteen Papy kuma ta ringa aure auren maza? Anna Annannnnnnnnnmmmmmmmmmmm"

Idannuwansa ya rintse a kansu a lokacin da IBTISAM ta mike tana nufo shi da wani irin wawan karfi ta juyo wajen da ya juya ta rukunkume shi a jikinta gaba daya ta fashe da wani karayan kukaa tama sake shigewa jikinsa, hakan ya sa sukai tangal tangal sannan ya sake tsayawa da kafafuwansa yana sake rintse idannuwansa

Muryarta na rawa ta ce" Kana kallo bata motsi Yalabai, dan Allah ka rufa mana asiri ta tashi, koda bata da hankali koda me ta zama muna sonta a haka......ka ga a rashinta babu irin abinda bamu gani ba,, ashe dai da gaske da nake cewa bata mutu ba haka ne? A ina ka sameta? Ina papyna ?"

Hannunsa ya sa a hankali ya baambareta daga jikinsa yana kallonta yadda du ta rikice take son komawa jikin nasa

Kansa ya maida wajen Mama a dan hankalce ya ce" Ku shigo wata motar mu kaisu asibitin kudi,, na so na kilace shi a bashi kulawa irin abubuwan karya sihiri, aman mu je asibitin kawai"

Mama ta amsa shi da kai, shi kuma ya karasa ya saka hannunsa ya dage Nahidt daga zubun matan da ya yi ta mayar da ita gefe sannan ya sake dan rage tsayinsa ya makawa Nahidt din wani kakausan kallo gannin zata sake zubun mata ya saka hannayensa ya dauketa ya nufi motar da ita, inda su kuma suka kasance kamar idan kana son kaza ta biyoka idan ka dauki y'ayantan nan

Sosai ya kwontar da kujerar gaban ya dorata ya saka belt ya daureta kafin ya juyo wajen da suke jira ya basu waje su shiga

Fuskarsa ya hade sosai yana kallonsu kafin ya masu nuni da Mama da ta fito da ky da kanta , masu tsaronta na biye da ita ta dakatar da su ta karaso tana dubaa number dake jikin abin ky din har ta gane ko ta wace mota ce ta dauko dan haka ta zagaya da kanta ta yi Bismillah ta bude ta shiga da tunanin yaushe rabonta da yin tuki

A nutse ta fitar da motar daga layin ajiyeta ta dawo kan hanya, hakan ya sa ya masu nuni da cen zasu shiga

SHUWWA da muryarta ta disashe tana kallon fuskarsa kanta a dage a sanyaye ta ce" Aman me zai hanna ni na shigo nan din yalabai?"

Sai da ya dan rintse idannuwansa kafin ya bude a kan lebenta shima ya furta" Haka na yi ra'ayi !"

Da sauri NAHIDT ta ja hannunta suka koma motar da Mama take suka shiga kowace na dan dagowa tana hangen tasa, har ya gama waya da baban datijon Malamin da yake masa taimako kafin ya koma gaba ya shiga ya tayar yana sauke ajiyar zuciya ya dauki hanya

Sunna isa babar asibitin aka amshe su Likitocin da ya samu mutane ne da suka sanshi suka kuma bashi daraja ba ta karfi da tsoronsa ba, sai ta cencentarsa a matsayinsa na nagartacen mutun mai boyenyen kyakyawan halaya, sun saba amsar marar lafiya daga hannunsa, sun kuma saba bashi kulawa

Sau dukansu sun zauna ne sun yi jigum jigum, uwa uba irin kukan da suka rikice da shi su biyun du sun rikita masa uwa baiwar Allah sai janyo su take yi a jikinta tana faman rarashi da faman bada baki a lokacin da suka ga ashe harda mahaifinsu a cikin motar nan, kuma mahaifinsu dogon mutun mai cikar halita da kwarjini ne ya dawo haka sai gaba daya suka sake rikicewa da wani koke koken wanda yake hahauda ciwon kansa

Gwuiwoyinta a kasa suke, kanta a saman cinyoyin Mama, hannayenta a zagaye da kaffafuwan Maman tana kukanta ba ji ba gani, hakan ya sa jikinta ke rawa, kuma hijabin ya sake dame mata jikin sosai, dama irin mai bin jikin nan ne

Readers Also Read