Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 41
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 41: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 41. Doctern ne ya zo ya dan tsaya a gefensa yana mai yi masa bayani a kan…
3,365 words
Doctern ne ya zo ya dan tsaya a gefensa yana mai yi masa bayani a kan dukkan abubuwan da suka dora su a kai, ya sake yi masa bayani a kan ciwukansu zasu samu sauki idan har sun samu kulawar da ta dace, ya dora da fadin cewa baban abinda ya fi yi masu ila itace yinwa, ya karashe da dora tambayar mamaki yana kallon MUHYIDEEN dake sauraronsa yana kuma amsar dukan takardun da yake miko masa kamar haka" Sir ama da mamaki, bayin Allahn nan a wani daji kuka samo su haka? Kuma na ga yar budurwar nan na kuka kamar ta hada jinni da su, sorry yar kyakyawa zasu samu sauki ai cuta ba mutuwa bace, dama cutar ke samuwa da gagawa lafiya kuma yar a hankali ce in sha Allah.................."
Yar budurwar da ya fada ya nuna ya karashe maganarsa a kanta ya juya ya kai dubansa kanta, hakama Mama dake ta rarashin su ta dago tana kallon Likitan da MUHAY dake tsaye yana sauraron bayaninsa
A hankali ta rage muryarta sosai tana ta ce" Ku yi hakuri da kukan nan haka, kun ji fa likita ya ce zasu samu lafiya kau? Ku mu yi masu adu'a shine zai sa su samu lafiya ba kuka ba............."
Takardar ta karshe ya amsa a hannun likitan ya juya ya fita bai ce komai ba
Likitan ya yi dan murmushi shima ya sake komawa dakin hutun da aka ajiye mutanen kowane da dakinsa, dakunna ne masu tsadar gaske , asibiti ce tamkar a turai, komai abin kallo ne abin ba'a cewa komai, ya sake duduba komai ya gamsu da komai da irin karrin ruwan da aka jona masu mai dauke da vitamine din da zai saka su cin abinci da sauransu sannam ya juyo ya dawo ya wuce office dinsa dan ci gaba da duba mararsa lafiya
An dan dauki lokaci ya dawo da waya a hannunsa ya mikawa Nahidht ita sannan ya kalli Mama ya ce" Ta koma Gida"
Mama ta kalle shi tana ayanna' Zama ka kawo kanka ne' ta dan gimshe tana fadin" Ban fahimta ba"
MUhay ya ce" Ta koma gida ta yi kukan a cen"
Mama ta dan tabe baki tana fadin" Ba zai yiwu ba ai Ka ga ba zata iya nutsuwa a gida ba bayan iyayenta a nan a kwonce"
Dan juyawa ya yi yana kallon yadda yayar tata ke kuka tana ta gyada kai ga dukan alamu rarashinta ne Aban na Shuwwa ke yi domin ya ce yana ta kiranta baya samu hankalinsa a tashe, shine ya bashi ita, kuma ta bude baki sai zayane masa komai take yi hankali kwonce kuma gashi sai ajiyar zuciya take yi ga dukkan alamu rarashinta yake yi, ya cire kansa ya dawo wajen Mama ya budi bakinsa da kyar ya ce" Za, zamu, zamu koma ta cenza kayanta mu dawo Mahmanah........." Irin yadda ya karashe Mamanah din ya saka Mama dan murmusawa a hankali ta dan ringa shafa kan Shuwwa ta ce" Daughter, tashi ku je gida ki yi wanka ki dauko mana abinci da abin bukata, idan kuka dawo sai Nahidtma ta je ta kimtsa ta dawo kin ji?"
Kanta ta dago hakan ya sa ya zubawa fuskarta da ta yi jajajir ido da lebenta da har suka dan tasa dan tsabar kukan da ta ci da ranta
Yar ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya koma bakin hanya yana kallon wucewar mutane har suka gama magana da Mama da kuma Nahidt da ta bata Abanta sukai magana wanda a sanyaye ya ce" Kina ji yar gidan Aba, ba kuka ya dace ku yi ba mana, farin ciki ya dace ku yi, sannan ku godewa Allah, in sha Allah jirgin gobe da ni zai taso zamu zo mu yi ta fadawa Allah, in sha Allah ko menene zai zo da sauki kin ji?"
Kanta take gyadawa tana dan hawayen ta ce " Abahnahhhhh, ba ka ga yadda Abunah ya dawo ba"
Irin muryar nan mai hade da kuka da shagwaba ce ta yi anfani da ita hakan ya sa ya dan sake juyowa yana kallon wayar dake hannunta da kuma kunnenta
Juyar da kansa ya yi har suka gama ta taho tana tafe tana rangaji ga ciwon kai, ga tashin hankali gaba daya sai take wani rangaji tamkar zata kifa haka take ji da kyar ta iya fitowa har ta samu ta bi bayansa dan Mama ta ce shi zai mayar da ita gidan ta cenza kayanta, gaba daya tamkar ba Shuwwa yar rigima da fitina da kaudin tsiya ba, wannan lamari ya sa gaba daya jikinta ya mutu bata da wani karfin aiwatar da komai sai ido
Tunda ya fara tukin bai tsaya ya kalleta ba har suka karaso gida ta bude ta fice ta nufi bangaren Mama
Motar ya rufe Shima ya fito ya nufi bangaren na Mama
Yana shiga masu aikin suka ringa gaishe shi
Sai da ya gama kare masu kallo kafin ya salamesu ya nufi dakinta
Bai tsaya neman izini ba ya tura kofar ya shiga, a lokacin tana daure da tawul a kirjinta
Sosai gabanta ya fadi, harma ta so zabura ta rufe suturar jikinta , sai dai irin yadda sukai ido cikin ido ga rashin karfin jiki ga dacin zuciya sai ta kasa kwakwaran motsi bale har ta aiwatar da abinda ta yi niyya
A nutse yake takowa yana sake saka idannuwansa cikin nata har ya matse mata wahe sosai yana kallon fuskar tata ya ce" Shi din danginku ne?"
Kasancewar bata gane ko wa yake nufi ba sai ta samu kanta da kurawa bakinsa ido tana ta son gane wane?
Huci ya furzar yana kallonta a dan kausashe ya ce" Shi din ta ina ya zama Abanki?!"
Da dan sauri ta kalli fuskarsa, sai kuma ta sada kanta , ta sake dagowa zata yi magana ya daka mata tsawar da ta saka kanta mugun sarawa harma ta saki Tawul din da take rike da shi da hannayenta dan kar ya fadi, sai dai sarawar da kanta ya yi ita kanta bata san a lokacin da ta sake shi ba ta kai hannunta dan ta rufe idannuwanta da shi, hakanma ta ga kamar rufeta zai yi da duka, hakan ya sa ta karaso da sauri a haka din da take ta sake rukunkume shi da karfi ta saka kuka tana goga fuskarta a jikin rigarsa tana mai karra shigewa jikinsa
Watau abu ne da zai sameka da baya yi maka shawara, hakan ya sa gaba daya du irin karfi da irin yadda bawan Allahn nan ya iya rike jikinsa dan kare kansa fadawa ko menene sai gashi ya yi tangal tangal ya hade bayansa da jikin garu da karfin da ya saka shi sauke ajiyar zuciya yana sake zarro idannuwansa da zuba mata ido yana kallonta Kukan da take yi shine abinda ya fi hargitsa dukkan wani kuzarinsa, da dukkan wani tunani nasa A jikinta ko pant babu bale a kai ga maganar bra, ta gama tube dukan wani abinda zai iya tarewa ne zata shiga wanka ya shigo, kuma a halin da take ciki burinta a rarasheta ba a karra firgitata ba, sai gashi ya mata ihun nan da ta ji zata haukace gaba Daya
A hankali ya kai hannunsa bayanta dan ya cireta a jikinsa jama'a rasululahi sallalahu alaihi wa salam yarinyar nan da bata da hankali?, Ya salam, ya salam yaya zata halaka shi bayan babu laifin da ya yi mata? Meye haka? Menene wannan take yi bayan shi tambaya kawai ya mata dan ya ga ai dai idan iyayen nata ne gasu sun bayana menene kuma ya hadata yiwa wancen katon magana da shagwaba me dinta ne? Shine zata auka masa??????
Jama'a ku raba😂😂😂💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 4️⃣6️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
*Aunty ni so nake na yi kiba, nima na ringa juyi ina yada hannu😂, Uhum kanwata kennan ba zaki kasheni da dariya ba, a gaskiya ni dan radin kaina ba zan yi sha'awar na yi kiba ba, kin ga motsawa nake yi sosai dan na zube, domin ita kiba bata da wani dadi, idanma ta yi yawa shikenan ke da kanki kin kashe kanki ne, idan dan mai gidan ne zaki zame masa kaya ne, komai sai ya yi......., Idan dan kawayenki ne zaki dawo abar tausayi domin ko kaya ba zaki saka ki ji dadi yadda kike so ba, sai idan kibar nan ta zame maki dole watau kin yi kin yi aman ina kin yita, to irin wannan zan iya cewa dole ce, ki yi kokari kar ki zaune ki koyi motsawa da dukan karfinki ta yadda kibarki ba zata hanna ki komai ba,aman kin ga? Yin kibar nan ko ga lafiyarki bata da wani kyai, domin shekaru na dan karuwa kin bani kennan, Allah ya daidaita mana yannayin jikinmu....., Aman kuma idan muguwar ramar nan ce ki dan gwada wannan, in sha Allah zaki ga cenji a kwana bakwai ........ Madara ta ruwa ki zuba kopi daya, ki fasa kwai ki yi anfani da yelow din dake cikinsa ki saka cikin madarar ki dan juya sai sun hade jikinsu sai ki zuba cokali daya na zuma ki motsa, ki sha kofi daya kafin ki kwonta barci, daga kin farka ki sha kofi daya, sati daya ki gani idan baki yi jiki ba to gaskiya ki yi hakuri😂*
Hannunsa ya kai kusa da kafadarta da niyar cirota daga jikinsa, a hankali ya dora hannun nasa ya dan nemi janyeta daga jikin nasa, sai dai kamar cingan maimakun ta bambaru daga jikin nasa sai ta kara shigewa tana girgiza kanta da muryar kuka sannan shakakiyar murya ta ce" Abanah ne, ka ga tunda muka zo anguwarsu yake tsaye a kan rayuwarmu, yana mana nasiha sannan shine madaurin aurena, wani abin ne ya same shi shima??????"
Fahimtar da ya yi cewar ta fa shiga hali na kidima ne ya saka shi dan sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Ur nude"
Da rarume rarumen ta dan dakata, a hankali ta sake maimaita abinda ya fada a cen kasan zuciyarta
Da sauri ta rintse idannuwanta, gabanta ya fadi, tsoro da kunya da mamaki suka cikata, mene? Yana nufin ba komai a jikinta? Sai a yanzu ta tuna tawul din da ta rike a hannayenta bata rigai ta daura shi a kirjin nata ba, kennan faduwa ya yi? Aman yaya aka yi bata ji sanyi na dukan jikinta ba? Shin ya salam, ya salam, sai kuma ta yi gagawar dago kanta daga jikinsa sukai ido hudu da idannuwansa da ta kasa tantance jan bacin ran da ta saba ganninsa da su ne ko na menene?
Da karfi ta dan saka ihu kadan ta cika gaban rigarsa da gudu ta yi bayi a haka din domin bata tunanin zata iya kuma daukan tawul din da ya fadi, kafin ta dauka gani take yi dukkan wani asirin jikinta ya idasa bayana kennan, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, yau itace tube zigidir a gaban namiji harma a jikinsa? Ai wayewarta bata kai cen ba, babu namijin da ya taba gannin jikinta haka a bude a bayane, babu shi
Da ido ya raka ukunta dake sama sunna kasa har ta bacewa ganninsa kafin ya maido dubansa a hankali a kan bed din Mama
A hankali ya iya daga kafarsa ya cirata ya koma bakin bed din ya zauna yana hadiye wani abu a wuyansa ya kawo hannunsa ya dafe gaban goshinsa a hankali ya furta" Mahaukaciya ce, ya salam bata da hankali yarinyar nan ko daya"
Gaba daya gannin al'amarinsa na sake hauhawa ya saka shi mikewa da dan hanzari ya fito yana rufo mata dakin sanan ya shiga bin falon da kallo dan sake tabatar da abinda ya gani a shigowarsa shin ana nan ko an fita? Dan idan ana nan ba zai barta da su ba, babu abinda ba zai iya faruwa ba duba da su sun dage a kan son gannin bayansa, ita kuma a irin wannan lokacin ya kula ta samu tabuwar hankali
Sai da ya gama duba ko'ina kafin ya rufe ya fice da ky din falon ya nufo bangarensa dan shima yana so ya cenza kayansa
Ta jima a dakin nata sai da ta gama shiryawa cikin bak'ar abaya da nikaf dinta a hannunta, da kyar ta iya fitowa daga fakin dan wata irin kunya da tunanin yaya zasu iya hada ido da shi ya hannata fitowa kanta tsaye har sai da ta ga lokaci na karra tafiya gashi ko karri basu yi ba sannan ta iya fitowa daga dakin nata
Tunda ta fito kanta sade ta nufi wajen table din da aka jera abinci
A hankali taa ringa bubudewa tana dubawa, har sai da ta gama gannin wanda zata tafi da shi sannan ta shiga warewa gefe tana dan satar kallonsa
Gannin tamkar bai san da ita a wajen ba ya sakata sauke ajiyar zuciya ta dan saki karinta harma ya ware plat ta zuba masa abincin ta dauki ruwa ta dora ta karasa ta ajiye masa ta mike ta yi cikin kicin din dan dauko abinda zata zuba abincin
Da ido ya rakata har ta bacewa ganninsa kafin ya maido idannuwan nasa kan abincin
A hankali ya samu kansa da jin mararin cin abincin domin ba yinwar bace baya ji dama, hakan ya sa ya dauka ya shiga dan ci yana kuma hankalce da shige da fitarta da irin kayan da ta jibgo tamkar wace zata kaura asibitin ko a tunaninta zasu barta ta kwana a cen ne? Bakinsa ya tabe bai ce komai ba, ya dai kula tun dazu bata kuma kallon fuskarsa ba, bayan ita din ba kunya ce da ita ba, bale jikin nata yau aka fara ganninsa ne ba komai a jiki da zata ringa masa wani iya yi? Dadin abin shima kamar yadda ya rike kansa shekara da shekaru a gaskiya ba zai yarda yar hannu ta bude shi a ledarshi ba, gaskiya sai sabuwa.....a kai kasuwa baya so!
Bayan ta gama daga inda take tsaye a kusan table tana hangensa dan bai gama cin abincin ba ta afka a duniyar tunani, shin a ina ya gansu?, Yaya aka yi ya gane sunne? Ya sanmu ne? Dama yana iya gannin mutun ya taimaka masa?, Dama soja na taimako ko menene ? , Tana ta tunani da sakar zuci har ya gama ya mike ya fita, kafin ta gane ta tabe bakinta ta fita ta kirawo masu aikin Maman sauka dauko mata kayan sannan suka fito ta rufe bangaren tanaa sakawa a yar jakarta sukai ido hudu da matar da aka yi dambe da ita jiya a matsayin matarsa
A hankali ta cire dubanta a kanta tana maidawa bakin hanyar da zata bi ta yi gaba, abinda ya tsaye mata a rai irin abinda ta ji a kan matar wanda ta rasa gane me ta yi mata ita kuma da ta ji haushinta haka?, Sai dai ta ajiye hakan a irin kallon wawancin da matar ke yi mata, dama ita ta tsani irin kallon nan sosai, dan bata ga anfanibsa ba gaskiya, kallo kamar na mahaukata a tsareka da ido har a saka ka fadi?
Da wannan suka koma asibitin, yana ajiyeta ya yi tafiyarsa wajen aikinsa, ita kuma tana dawowa Nahidhma ta tafi ta kimtsa din ta dawo , hakama Mama, wace suka dawo da mijinta domin sai da ta koma ta tarda ya dawo kuma yana ta kiranta wayarta a gida hakama MUHAY ya shige cikin aiki tasa bata tare da shi , a dole ya yi jiransu domin mutan gidan sun nuna su basu san inda suka je ba Ai kuwa tana yi masa bayani al'ajabin abin ya kama shi, bai yi kasa da gwuiwa ba ya biyota suka koma tare, suka samu yan matan a nan suka wuni abinsu ga abincinsu a gefe da abin sallarsu Shi ya fahimtar da su ko zaman nan da suka yi ya tabata dan MUHAY ne ya kawo su, domin asibitin nan basa bari ka yi sama da minti talatin a ciki, da zarar ka zo ka ga marar lafiyanka to fa sunna kwatanta maka cewar ka tafi, domin su aikin da suke basa son wannan shige da ficen, Idan wani abin ya taso dole zasu nemeka, aman a yanzu ka basu dama su kula da marar lafiyanka yadda ya dace,
Sunna nan MUHAY ya dawo tare da yarensa uku Sun shigi sun gaisar da su Mama suka ajiye kayan dake hannayensu suka juya, a nan suka sake gaisawa da Father da MUHAY
Sai da ya je ya gama bayani da likita sosai ya sake jadada masa ba zasu kwana ba , sannan ya dawo ya kwatantawa Mama ya yi masu salma ya yi tafiyarsa gida
Da rarashi, da ban baki su Dad suka fahimtar da su kafin suke iya binsu zuwa gidan
Ko da suka koma gidan kadaice kawunnansu suka yi sukai kuka tsakaninsu bayan sun rungume junnansu
Nahidt a tsorace ta ce" Shuwwa, iidan Mama ta san na yi karuwanci ina tsoron idan wahalar da ta mayar da ita haka bata kasheta ba wannan maganar ta kasheta"
SHUWWA ta girgiza kanta a sanyaye ta ce" Ba zata kasheta ba, da izinin Allah ba zata kasheta ba, sai dai tabas ranta zai bace, kuma kin san cewa daga ita har Abui sun nuna mana soyaya aman ba wai sunna kyalemu bane idan har muka yi abinda zasu horamu, shi yasa a kulun nake ce maki, ki fa ji tsoron Allah ki daina, to kin ce Allah zai yafe maki a yanzu kin daina kina nemansa gafara ba ji ba gani, itama zata yafe maki in sha Allah....."
Da wadinnan hirarakin suka yi dare sosai kafin kuma su zarce da nafilolinsu sannan suka cude waje daya suka yi barci
Tunda sasafe suka wuce asibiti, yau harda matan Dad su biyun dukansu domin a jiya da dare yake fada masu cewar su je su ga narar lafiya, iyayen Matar MUHAY ba lafiya Kowace da tambaya a ranta , sai dai kasancewar bai bada damar hakan ba sai kowace ta rike abinta suka kuma bi motocin suka je duba su,
Uwar gidansa da wuri ta dawowarta, mai dakin tsakiyar ce ta zauna ta dan jima kafin itama ta tafi , babu wada ta ga mararsa lafiyan haka suka je suka dawo
Sai kusan karfe goma aka basu damar gannin iyayensu na tsayin mintunna talatin, aka shaida masu cewar baci suke kar su yi hayaniyar da zasu iya tashinsu a barcin nan fa, kafin aka barsu suka shige
Su dukansu sun kasance ne a tsaye a gaban gadajen iyayen nasu da kauna da soyaya, da hawaye irin na soyayar iyayen nasu da tausayin abinda ya mayar da su haka
Daya bayan daya suka je suka gansu sannan suka dawo dakin da aka ware masu
Daidai ana kiran sallar azahar a cikin asibitin, ya kasance cikin gari har sun yi salolinsu , a daidai lokacin ne kuma summa suka fito dan gabagar da alwallah a cen wajen pampunnan balbalin asibitin dan ra'ayi