Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 42
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 42: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 42. Motarsa ce ta dano kai, ba tare da yan tsaro ba, domin sai da ya…
3,339 words
Motarsa ce ta dano kai, ba tare da yan tsaro ba, domin sai da ya sauka a wajen aiki ya je ya dauko Malan da ya sauka shima yanzu yanzun
Tunda suka fito a motar suka gansu, haka suma,
Malan na sanye ne da gari da yar ciki, ya kafa hularsa a kansa hannunsa rike da carbinsa fari kal , haka kuma kafarsa sanye da taklmi sau ciki bakin kirin MUHAY kuwa yau kaki ne gaba daya a jikinsa babu bambanci sama da kasa hakan ya sa yau ya karra cika sosai yake cika ido
Dan tabota ta yi ta sake nuna mata shi, hakan ya sa gabanta sake balewa ya fadi, kuma abinda ya fi saka su kure su da ido shine kamar wa'inda aka dakatar da su bayan sun baro wajen motar kowane na kallon yar uwarsa
Malan ne ya dan kula da yannayin MUHAY, sannan ya tuna cewa shi fa sirikin MUHAY ne kar bege ya saka su mace su lalace a gaban yan yara guni guni haka, hakan ya sa ya dan yi gyaran murya da dan baza babar rigarsa ya daga kafarsa ya shiga gaban MUHAY din irin da karfin halin nan, irin ai shine baban baba a wajen nan dai kau?
Turus ya yi sakamakon gannin NAHIDT ta taho da dan saurinta, sannan ta dan wara hannayenta, uwa uba ta fashe da tabararen kukan da nan take shedan ne? Ko kuma banzan tunaninsa ne? Ya sheda masa cewar idan ta karaso wajen nan babu abinda zata aikata sai rukunkume shi a cikin bainar nasi, a irin wannan rana da ya dauki azumi , sannan ya zo a matsayin siriki watau mutumen da ya dace har ya bar wajen nan ana dubansa da daraja da mutunci, sai dai kasshhhh, wannan lamari da ya fuskanta ya saka shi jin kamar cikinsa zai juya masa Yanzun fisabililahi wannan aikin na adalci ne? Da girmansa da darajarsa? Ba shiri ya dan tatare babar rigar da sauri ya zagaya ya labe a bayan MUHAY dake kallon ikon Allah shima yana jira ya ga wai me zata yi ne haka?
Yana labewar da yaren larabci ya ringa maimaita kalmar sunnanta yana girgiza kansa yana lekenta har ta karaso da mamaki shinfide a saman fuskarta ta ce" Yah habiby yaya haka?"
Ido ya dan rintse dan hanna zuciyarsa fitowa, a hankali ya ce" Yah khalb me zaki yi ne?"
Muhay bai taba jin abinda ya tuko masa dariya ba shiri ba irin na wannan ranar, a hankali ya dantse lebensa na kasa ya baza idannuwansa yana kallon soyayar larabawa a lokacin da Shuwwa ta kyalkyace da dariya har tana dukawa tare da dafe cikinta tana kallonsu, daidai Doctern nan ya fito nurse na rike da takardunsa ga dukkan alamu gida zai je ya hango Shuwwa a duken nan tana kyakyata dariyar nan , hakan ya saka shi sakin murmushi yana sake kallonta kafin ya samu akalar tafiyarsa da juyawa yana nufarta , hakan kuma ya sauka a kan idannuwan MUHAY wanda shima ita din yake kallo harda bin mayafinta da ya fadi dan dariyar ketar da take yiwa Abanta da ya labe, hakan ya bayanar da gashin kanta da yau ta dan caje shi ta saka masa dan ribom, sannan ya sake maida dubansa kan likitan nan dake karasowa daidai NAHIDT ta budi baki tana leken MALAN da ya labe kansa da kafarsa baya so su yi hadewar nan da ta zo masa a kwakwaluwarsa da azuminsa a bakinsa ta ce"ALKALAMIN KADARRATA
PAGE
Na
Sajida
4️⃣7️⃣
*ZO KI JI, KE DAI DAMUWARKI RASHIN SHA'AWA ? KE TUNDA AKAI MAKI AURE KIKE FAMA DA SHI? KIN RASA GANE KANKI?, KE KAWIAI KALLON MUTANE KIKE DU KIN RAME KIN TSOTSE SABODA BAKYA SON ABINDA AKE MAKI MAI SUNNAN JIN DADI?, KE KUMA YAR UWA TUNDA KIKA HAIHU KIKA HADU DA WANNAN DAMUWAR, WATAU TUNDA AKAI MAKI AIKI KIKA RASA WANNAN JIN DADI DA KIKA SABA DA SHI KAFIN AI MAKI AIKIN??????, MAZA JE KI KASUWA HARHADO KAYAYAKI KAMAR HAKA : SOBO JA, GIMJIMBER, QUATRE CÔTÉ, POIVRE SELIM, da Copin ruwa biyu ( ku yi hakuri duk mai so zan turo mata da hotunnan abin domin ni ban sansu da hausa ba gaskiya, ko ku dora a google za'a baku su)....... Zaki hade su ki dafe su gaba dayansu ne, sai ki ringa sha karfe daya kafin lamura su kankama, ko tun da magariba................... Itatuea ne basu da wata matsala, idan kika ga lamuranki sun daidaita kina ita dakatarwa..........*
Ta ce" Ya habiby, me zan yi kuwa? Zan fada maka ne irin halin da Abanmu yake ciki da mamanmu fah"
Kansa ya dan girgiza ya ki ya fito din,
MUHAY dake ta binsa da kallo har ya karaso gannin Nahidt ta dan kare masa sai ya daga kafafuwansa da kyau ya matsa masu ya shiha takawa ya karasa wajen da take kyakyata dariya daidai lokacin da docter ke fadin" Dariya ta fi kayatar da fuskarki yar budurwa"
Da sauri ta dago dubanta kan docter, shi kuma komai ya sauka a cikin kunnayensa Bai ce komai ba ya dan rage tsayinsa ya mika mata hannunsa na dama hakan ya sa ta juyo da wani saurin tana kallon fuskarsa
Gannin fuskar tasa a hade ba alamun ya taba yin dariya ta saka hannunta a cikin nasa, ya cicibeta ya mikar da ita sannan ya jata suka nufi ciki ko kallon likitan dake kwatankwacin abokinsa bai yi ba dan takaicin yarinyar
Yana shigowa da ita ya saki hannunta yana kallonta ya nunata da yatsarsa daya ya ce" Ki kula, kina wasa da igiyar dake wuyanki bayan har yanzu bata tsinke ba, ki kiyaye ki iya bambance igiyar aurena da ta sauran banzayen da kika aura, abayoyinki da hijabanki gaba daya munafukan abin lulubi ne, ban san a kan wani dalili kike son rayuwa irin ta bude jiki!" Ya karashe a kausashe yana dan juyawa ya dafe gaban goshinsa hadi da rintse idannuwansa ya ce" Kin ga, me zai hanna ki rufawa kanki asiri ki kama mutuncin kanki ne? Har hanyarmu ta rabu da ke?"
A hankali idannuwanta dake kallon kasa ta ringa dagosu har ta sauke a saman fafadan bayansa da ya bata baya Kalmar har hanyarmu ta rabu ta ringa maimaitawa a kasan zuciyarta har ta samu ta gane ma'anarta
A hankali ta sake wara manyan idannuwanta a saman bayan nasa daidai lokacin da ya juyo ya sauke dubansa a saman fuskarta
A nutse yana kallon fuskar tata da furucin dake karyata abinda yake son fada, domin ya dace furucin au fito a kausashe da ihu, sai dai gaba daya ya same su da sanyi a gareta yana kallon fuskarta ya ce" Ki yi kokari, ki koyi kilace kanki, ita mace daraja gareta, banzatar da kanta idan ta yi ba shine zai sa a ga kimarta ko a ga kyanta ba, ki kiyaye hulda da kowani namiji har ki samu yancin kanki....."
Ya karashe maganar, aman kuma fuskarta yake kallo sosai ya matse mata waje sosai
A hankali ta ringa hadiye dukan abinda take ji mai kama da tsoron jin furucinsa Menene a ciki? Kar ta manta itama baban burinta bai fi ya sawake mata ba, da farko shi din ba zabinta bane, na biyu shine mutumen da ya wulakantata ya raba mata aurenta, na uku soja yake, wanda bata so ko a hanya su hadu da junna, so meye a ciki?
A hankali ta dan sakar masa sasaukan murmushi tana dan kawo hannunta dan ta tare kirjinsa domin ji take kamar kirjin nasa zai hade goshinta ne irin ya maki goshinta ne
A dan sanyaye ta furta" Ba damuwa........"
Daga haka ta juya ta nufi ciki wajen Mama dake zaune tana waya da yar uwarta tana sheda mata an rike iyayen matar MUHAY a asibiti tun jiya ta mata whatsup ta ga ta bude aman bata ce komai ba?,shine take ce mata ta kwontar da hankalinta yanzu haka ta kusa shigowa asibitin ta taho ai
A hankali ta zauna a gefen Maman tana lumshe idannuwanta
Baki ta tabe a kasan zuciyarta tana ayana' Irin gashi dan gwal din nan, to a kaina za'a fara ko a kaina za'a rufe? Dama me zan yi da namiji irinka?, Allah na tuba na dangana da masu nunan so ma bale mai nunan kiyaya? Kai zanma rokeka ka sakeni da wuri dan na samu wanda zai iya soyaya ba halaya na kiyaya ba!'
Shi kuma a lokacin da ta yi gaba da ido ya rakata har ta bacewa ganninsa kafin ya samu kansa da jan wani dogon tsaki ya juya ya fita ya nufi hanyar da zai iya gannin likitan cen, ya kuka dakiki ne ashe? Ya nuna masa a jiya ashe bai gane ba? To ya bari idan ya saketa sai ya nemeta, aman a yanzu ta fi karfinsa walahi!, Baban abinda ya fi bashi haushi da yarinyar girman kai da nuna ita wata ce, to in takamarta kyau sai ta baza ido ta ga irin matan da ya ringa aura yana saki, dukawa suke yi har kasa sunna kukan ya dawo da su ya kiya, zata yi bayani ne!
Sai da Aban Shuwwa ya samu wajen da ya tabata akoy al'uma dake yawan kai kawo kafin ya iya samun nutsuwar fuskantarta yana murmushi ya ce" Bismillah me yake damun amaryar Muhammad ne?"
Dan murmushi Nahidt ta yi tana dan kawar da kanta dan har ga Allah ta ji kunyar abinda ya fada , sai dai ita bata so ya gane ta ji kunya dan haka sai ta juyo tana fuskantarsa ta ce" Aban Shuwwa a tunaninka a nan din ba zan iya rukunkumekan bane hala?"
Ido ya zarro yana dafe bakinsa ya yi gagawar fadin" Astagfrullah, subahannalah, yah Nahidt ya dace ki karra rike istigfari a dukkan motsinki, sannan ki guji aikata aikin da bashi da kyau komai kankantarsa, fisabililahi wannan aiki ai bashi da kyau, gashi ni azumima nake......"
Murmushi ta sake sakar masa ta gyada kai , kafin ta yi yannayi na hankakinta ba a kwonce ba ta ce" Muhammad, ka san wani abu? Abanmu anya ba ya haukace ba?, Ka ga jiya kafin likitoci su saka shi a cikin barci daga inda muke muke jiyo muryarsa yana ihun shi a fitar da shi daga kasar nan, subahannalah gaba daya tamkar ba mahaifinmu ba mutun mai nutsuwa da izza a jikinsa, mutun mai tarin kamala a tare da shi, a yanzu haka tun barcin nan basa bari ya yi doguwar farkawa domin da ya farka hakan yake ambata......" Ta karashe tana mai sadda kanta
Shima dan tsura mata ido ya yi kafin ya girgiza kansa ya ce" MUHYIDEEN ya ce yana tsantsamin sihiri, idan kuwa aikin sihiri ne in sha Allah zamu samu kansa kin ji? Ki kwontar da hankakinki zamu je na gani idan har sihiri ne ina mai tabatar maki in dai ba a zannen kadararsa ba Allah ya rubuta a cikin yannayin nan zai rayuwa har mutuwa, to fa nan da yan kwanaki zamu ga haske a lamarin, ki daina kukan haka kin ji?"
Kanta ta ringaa gyadawa tana sauke ajiyar zuciya
Shima ya sauke ajiyar zuciyar ya ce" Kin ga, da Malama da furerama suka ce a gaisheki"
Dan tsatsareshi da ido ta yi ta ce" Malan ina amsawa harda na fureran"
Dan kallonta ya yi kadan , sai kuma ya dauke idannuwansa a kanta ya nemi da ta sadashi da mutanen dake ciki, dan ya kula so ake a kure shi sosai, shi kuma in sha Allahu ba za'a kureshi ba yau din nan, kuma azuminsa da yardar Allah sai ya kai abinsa a cike cif ___________________________________
A lokacin da MUHAY ya fito da nashi kalar neman fitinar idannuwansa suka sauka a kan matar dake nufowa inda yake
Har ga Allah sai da gabansa ya fadi sakamakon ganninta a wajen nan, sannan zuciyarsa ta yi bakin kirin da ganninta
A hankali ya juya da niyar barin wajen dan ya cenza hanya, sai dai bai kai ga aiwatar da hakan ba ta yi murmushi tana kawar da makeken gilas din dake saman fuskarta wanda ya cinye rabin girman fuskar mai kalar duhu tana kallonsa da kyau ta ce" Ina zaka je?"
Dakatawa ya yi ya sauke numfashi dan ya daidaita kunar da zuciyarsa ke yi ya juya a saukake ya kalleta sau daya duba irin na ido cikin ido kafin ya ce" Hajia momy ce ke tafe?"
A hankali ta ringa ji ranta na baci da kiranta da sunnan momyn nan da yake yi, sai dai ba komai ta tabata jinkirinta zai zo karshe wata rana, dan haka itama sai dan murmusa masa tana sake binsa da kallon da ya fi tsana a duniya kafin ta ce" Nice kw tafe sweet men"
Baki ya tabe ya juya ya koma ba tare da ya ce da ita ta biyo shi ba, sai itace ta daga kafarta da dan sauri tana biye da shi tare da kallon askin kansa wanda sama sama ne aka aske masa , bakin gashinsa ya samu gyara na musaman sai walwali yake, har zuwa kunnensa da wuyansa
Dakin da Mama take ya tura a hankali ya shiga da salama a bakinsa
A yanzu SHUWWA na kwonce a saman bed din dake dakin, Mama kuwa tana zaunenta ne da carbinta a hannunta tana ja
Murmushi ya sakarwa Maman kafin ya wuce direct wajen da Shuwwa ke kwonce ya zauna a gefenta hakan ya sa ta dan janye kaffafuwanta sannan ta so juwaba barin da garun yake, sai dai dannewar da ya yiwa rigarta ya sa ta kasa aiwatar da hakan sai a haka ta tsaya
Shigowar ouseinarta ta sakata sakin murmushin da ya fito tun daga kasan zuciyarta mai cike da so da kauna harma ta mike daga zaunen da take fuskarta na idasa wadatuwa da farin ciki ta ce" Marhababuki yar uwatah......"
Ouseinarma wani sansanyan farin cikin ganninta ne ya mamaye zuciyarta, tsakani da Allah tama son yar uwarta so daya tak da babu hadi, baban matsalar da yake sakawa take karra yin nesa da ita shine soyayar da take yiwa yaronta mabambanciyar soyayar da ta dace ace tanai masa
Ita da kanta ta sani, ta san cewa abinda take ciki ba alkhairi bane, ta kuma san cewa lalle yaronai mutunci ne da ya kyaleta har yanzu bai tonata ba, aman kuma baban abin Tsoron bata jin Tsoron ya tona tan, ta gaji, ta gaji iya gajiya
Doguwar riga irin yar dubai din nan mai watsetaen stone tun daga sama har kasa wadda a kalla zata ci dubu casa'in ce a jikinta, sai dai dametan da ta yi ne ya saka yar uwarta bin rigar da kallo harma ta kasa hakura ta ce" Kanwa, wannan damamiyar shigar fa?"
Shigar tata ta bi da kallo , sannan ta juya wajen wanda ta yiwa din, abin takaici ko kallo bata ishe shi ba, uwa uba abinda ta gani a bayan wajen da ya zauna ya saka gabanta faduwa da sake zubawa wada ke koncen ido har sai da Mamma ta sake fadin" Haba Ouseina wannan ai ya dame da yawa, da ki hakura da ita ko kuma ki bada a bude maki, idan kuwa in tela ya taba lalacewa zata yi ki ringa saka mata baban hijab a sama, wanann ko a zaman gida bata dace da ke ba Kanwata"
"Zaki fara ko?, Ko zama fa ban yi ba ni yau kin fara kuma, wai wacece ke kwonce haka a bayan Baban yarona?" Ta fada tana mai son nufar Wajen da Shuwwa ke son mikewa dan ta gaisheta aman kuma ya wani danne mata rigarta ta kasa aiwatar da motsin kirki, shi kuma yana sane da dane rigar tata da ya yi, haka kawai yake ji a kasan ransa baya so ta yi mata irin abinda ta saba yiwa sauran matan da ya aura kafin ita
Muryarta cen ciki ta ce" Yalabai ka danen riga ka dagani na tashi......."
Kasancewar Mama ta juya tana fadin" Ina zuwa bara na ga ina Nahidt ta makale ne haka su zo su ci abinci, hakan na nufin ta fita a dakin da gano Nahidt ya saka shi juyowa da kyau ta yadda ya sauke idannuwansa a saman santaleliyar cinyar SHUWWA da take son ya dan daga ta janye rigarta
Ba zato ba tsamani ta ji hannunsa a saman cinyarta daga dan sama kadan ya dora Dorawar da ya yi da niyar ya dan taba wajen ne dan ya isar da sakonsa wa yar uwar mamansa, sai dai a hankali ya samu kansa da dan matsa wajen kadan kafin ya dago idannuwansa ya sauke a saman fuskarta da ta yi tsuru tsuru ta zarro ido cike da mamakin sabon salo wai kiran sallah da usur
A tsorace ta so waigawa dan ta kalli Matar da idan ta fahimta da kyau ana nufin abokiyar tagwaitakar mamansa ce ko menene?, Sai dai baban tashin hankalin da bata taba zato ba, wanda shi kansa bai tana zato ba, wanda ya kusan buga zuciyar ouseinar mahaifiyarsa a lokacin da bataa shiryawa gannin diramar yaron nata har nan ba, domin du ta dauka da gangan yake yi kamar yadda ya saba ja mata kashedi kala daban daban a kan haka, sai dai lokaci daya idannuwanta suka sauka a tashin hankalim a lokacin da ya manta a ina suke? Ya manta me suke yi? , Harma da wa yake? Ya sasauta ya ringyesa ta yadda ya rankwafo mata, gashi ya sake danne mata tifafi ba zata iya ja ba koda ta yi yinkurin hakan, gaba daya yaa halaka mataa tunani a lokacin da ya yi mata rumfa sosai idannuwan nan nata da take zarrowa ya tsayar da su kau kamar ta summa domin ido cikin ido ya saka a nata kafin yake sauke lalausan lebensa a saman nata leben mai dumin tashin hankali , ya ciro da harshensa kadan ya dan lashi leben nata harma ya karra neman sake lasar leben nata sai dai bata bashi dama ba domin jikinta ne ya dauki rawa ta yi gagawar kawar da fuskarta bata san ta yiwa kanta rami bane, domin leben nasa da ya tashi bai sauka a ko'ina ba sai a domin wuyanta hadi da sajensa, shi kuma lokaci daya kanshin turaren kashin kanta da na wuyan nata suka saka shi lumshe idannuwansa yana jin wani takuraren tashin hankali na ziyartarsa harma ya saka hannunsa a hankali ya talafi..................
Mun higa uku😌😌😌😌ALK'ALAMIN KADARATAH
Na
*Sajida*
Page
4️⃣8️⃣
Maganin tumbi.......................
Ki samo KANANFARI, LEMUN TSAMI, SHINKAFA, Ki irga kananfari kwaya goma sha biyar, sai debi shinkafa cikin hannunki, sai ki yayaka lemun tsami biyu manya har bayansa a cikin tukunya ki saka kofi biyu na rufa ki dafa su Sai sun dafe sosai sai ki kawo ki markade ki shanye Kina yi da sasafe, sanann idan zaki kwonta har ya maki daidai yadda kike so😍😍😍😍
A hankali ya saka hannunsa da gashin dake lulube da shi du suka mike sakamakon aikata abinda bai tana aikatawa ba da ya yi , ya tura ta kasan bayanta ya talabeta a jikinsa ta yadda jikinta dake rawa gab gab gab ya hade da kirjinsa a hankali, sannan kanshin da suke bazawa na jikinsu gaba daya ya garwaye waje daya , ya sake lumshe idannuwansa a wuyansa ya shiga dan goga mata sajen dake fuskarsa ba da nufin ya hadasa mata jin kowani irin felling ba, asalima yana yin haka ne dan ya samu ya dan sake nutsar da hankali abokiyar tagwaitakar mamansa da ta yi mutuwar tsaye, kanta ya sara, hankalinta ya tashi, ta zuba masa ido tana son lalle lalle sai ta fadawa kanta cewar ya yi haka ne dan ya bata mata ba dan da wani abu a tsakaninsa da yarinyar da har yanzu bata kalli idannuwanta ziryan ba
Idannuwanta ta rintse, nan take wasu irin hawaye masu dumi suka shiga gangarowa Ba wani abu ya hadasa mata haka ba sai irin bugun da zuciyarta ke yi na bakon lamarin da bata taba fuskanta a rayuwarta ba ko da wasa, namiji bai taba samun kusanci irin yadda bawan Allahn nan ya samu a tare da ita ba kama daga jiya zuwa yau