Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 43
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 43: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 43. A hankali ta saki bakinta da niyar fashewa da kuka, sai dai maganar…
3,343 words
A hankali ta saki bakinta da niyar fashewa da kuka, sai dai maganar da Mama ta yi ya sakata ta jikin kirjinsa da dumin kirjin nasa ke ratsata ta dan waiwayo dan kallon abinda ya saka Maman fadin haka
Da mamaki take kallon irin tsayuwar da irin kallon da matar nan ke yiwa bayan MUHAY wanda ya hadasa mata matsanancin mamaki har Mama ta saje furucin cewa" Useina? Useina? "
Sai kuma firgigit ta zabura wanda hakan ya nuna cewar batama san da ana kiran sunnanta bane kwata kwata
Mama ta maida dubanta kan MUHAY da ya rintse idannuwansa abu biyu na ziyartarsa wa'inda suke da girma sosai da sosai a zuciyarsa
Da kula ta ce" Muhyideen lafiya?"" Domin bayansa ne ake gani ya rufeta sai jikinta dake dan bude kadan haka
Mama gannin bai amsa ba sai ta karasa tana dan jan rigar Shuwwa din tana fadin" Abanta ke son shigowa Nahidt ta karasa ta amso mana abinci a wajen nurse da na saka a dumama mana shi, dago mana me yake faruwa ne?"
Dab tsaki Useina ta yi ta juya da sauri da nufin tafiya, hakan ya saka Mama juyawar itama tana kallonta da mamaki ta kuma fadin" Kai wai meye haka ina magana daga kai din har useinar kun ki bani amsa? Meye haka me yake damun yarinyar? Bayan fitana wani abu ya faru ne?"
Cak Useinar ta ja ta tsaya kafin ta juyo da yannayi na bacin rai har tana dardarwar baki ta ce" Me zai faru a ciki,? Me kike so ya faru ne Hasana? Kina kallo? A gaban idannuwanki?!!!"
Da karfi ya dago yana mayar da Shuwwar kwonce wace ta yi firgigit ta mike daga kwonciyar da ya maida ita wannan karronma tana janye rigarta taa gyara da kyau, sai dai daga ita har Maman a saman hannunsa da ya dora ya damki hannun Useina ya jata ya fita da ita idannuwansu suka sauka kafin su kalli junna sunna masu zarro ido ,
A firgice Mama ke kallon Shuwwa ta ce" Y'ata me yake faruwa ne ? Wani abu ya faru tsakaninki da maman naki ne?"
A hankali Shuwwa ta girgiza kai tana fadin" Mama ko gaisawa bamu yi ba da ita"
Kan mama ya daure sosai, Nahidht na shigowaa da Malan ta ce tana zuwa ta fice da sauri, sai dai du irin neman da ta yi bata gansu ba haka ta dawo tana ta leke leke daidai Malan na basu adu'o'in dake karya sihiri, ayoyi ne kwaya shida na cikin Alkur'ani kamar haka *SURORIN QUR'ANI, GUDA SHIDA DAKE KARYA SIHIR KO ASIRI.*
*1.Suratul Tauba:ayata 14.*
*2. Suratul Yunus ayata 57.*
*3.Suratul Nahli:ayata 69.*
*4.Suratul Isra,i:ayata 82.*
*5.Suratul Shu,ara:ayata 78~82.*
*6.Suratul Fuslilat:ayata 44*
A sanyaye ta zauna samana kujera taba fuskantarsu, gaba daya jikinta tamkar bata da lakkah,
Duda sun gaisa dama, haka Malan ya sake gaisheta a mutunce yana mai sada kansa a gabanta,
Mama ta amsa shi tana sauke gwauron numfashi ta sake dagowa ta kali wajen yan matan, sai ta ga ai ita suke kallo da yannayi na damuwa shinfide a saman fuskokinsu
Malan ya sake sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" Alhmdulilah, Mama Aban ne Allah ya sa na gani, domin ita Maman an shiga ainahin gyarata, in sha Allah zamu sake dukufa da kanmu mu ringa yin adu'o'in nan, sannan zan koma gida dole dab na tatara almajirai a yi ta saukar alkur'ani da dukan abubuwan da Allah ya sa aka sani na karya sihiri, domin dukkan abinda aka fada na faruwa da bawan Allahn nan, koda da firgici to fa akoy abinda ke kada shi gaba......"
Mama ta gyada tana kallonsa ta ce" Allah ya saka da alkhairi Malan, Allah ya biya, mun gode sosai Malan, Allah ya da mu ga hasken lamarin"
Malan ya amsa a nutse kafin ya mike yana yi mata salama dan bashi da sakewar da zai karra jimawa a dakin, duba da yannayinta wanda ga dukkan alamu wannan abu da ya faru yanzu ne da yaronta da matar nan mai kama da ita sosai, ya kula hankalinta du ba a kwonce ba, tana yawan daga kanta ta kalli hanyar fita sai kuma ta dawo da dubanta kansu
Malan na tafiya Nahidht ta raka shi, Shuwwa ta samu damar sake fuskantar Mama
A hankali ta rarafo ta dan dakata tana kallon yannayin maman tana kuma tunanin shin shakuwarsu ta kai idan ta ga tana cikin bacin rai ta yi tambayar abinda yake damunta ko kuma ta koma ta zauna kar ta janyowa kanta fitina?
Sai dai gaba daya sai ta kasa, Shuwwa ce fa, ba zata iya ba gaskiya , hakan ya sa a nutse ta fuskanci Mama ta ce" Mama?"
Mama ta kalleta da sauri tana sauke ajiyar zuciyar dake nuni cewar tana yawan tunani ne
Itama ajiyar zuciyar ta sauke a sanyaye ta ce" Mama me yake faruwa?"
Mama ta yi rau rau da idannuwanta tana shanye abinda ya taru a cikinsu, ta watsa hannayenta ta ce" Nima ban sani ba Shuwwa, ban san abinda yake faruwa ba, na tarar da ita tamkar ta suma ko ta ga bakuwar Halita tana fuskantarku, na ga kuma shi ya rufe ki a kwoncen da kike, gashi da hawaye a saman fuskarki dake nuni da kuka kike, Sannan ya damki hannun Useinata da irin wannan rikon ya fita da ita da karfin da ban san me hakan yake nufi ba......gaba daya kun sakani a duhu gaba dayanku......"...... Ta karashe tana kallon SHUWWA din da ta sada idannuwanta kasa tana tunanin amsar da ta dace ta ba Mama
Mama ta riko hannayenta tana kallonta ta ce" Menene tsakaninsu ne?, Ya dace ace du duniya babu masu ganewa junna irinsu, a lokacin da na haife shi na tafi saudiya da mahaifinsa hutu mun jima a wajenta yake, yar uwar haihuwata ce, tare muka zo duniya da ita, kulun kukana a kansa shine ya yi zumunci da ita, aman kulun bashi da amsar bani, ban taba jin na tsani shiru shirunsa a rayuwata ba irin na a kan yar uwata, gaba daya na fara tsorata da lamarin, wai me yake faruwa ne?....."
A hankali Shuwwa ke girgizawa Mama kai tana kallonta ta ringa harhada abinda zata fada mata duda ta san da wahala ta yarda da furucinta, ita kanta wannan abin ya bata mamaki har yanzu kallon jan da ya mata take yi a idannuwanta, da kuma irin kallon da matar ke masu, abin na son ya dan tsaya mata a rai, aman kuma bata ga dalili ba shi yasa ta fuskanci Mama ta ce" Mama ni cikina ne ya murda min har na fara kuka, shine ya rikeni dan na daina kukan, shine maman itama take min sannu"
Mama ta kure fuskarta da ido, kwarai ta san maganar ba haka bace, aman sai ta samu kanta da son yarda da maganar fiye da sake saken banzan da take yi a zuciyarta, dan haka sai ta ringa sauke ajiyar zuciya itama ta sauko kasan saman tabarmar suka zauna suka zubawa hanyar shigowa ido kowace abinda ke zuciyarta ya fi karfin ya barta ta yi hira a bayane koda kuwa da gangan ne ______________________________________
😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍ALK'ALAMIN KADARATAH
Na
*Sajida*
Page
4️⃣9️⃣
Jan hannunta yake , tana biye da shi tamkar zata kifa domin saurin ba daya ba, haka kuma karfin ba daya, a haka a wulakance har ya samu ya samu dogon corridor din da yakan zama idan ya kawo marar kafiya ya buya a nan ya turata har sai da ta daku da jikin garu kafin ya tsatsareta da idannuwansa da sukai jajajir yana kallonta
Da bacin rai yaa shiga magana yana dago hannunsa da ya wara ya jimke yana fadin" Ki kula idan zaki fuskanci mai daraja ki yi mata magana, ki kiyaye harshen ki wajen yi mata furuci domin kalma daya na iya laladan sauran farin cikin da kike tunanin kina da shi a rayuwa!, Useina ki kiyaye tsawarawa mahaifiyata, domin idannuwanta dake akoy a doron kasa ya saka ban daga ki na murzaki a kas na!, Useina kin zubar da dukan wata kima da nake iya daga maki kafa dominta, ina kauce maki irin ranar nan da zan maki irin wannan kashedin!, Ki kiyaye! Useina ki kiyaye ! Kar ki kuma kiran number wayata, kar ki kuma hadani da mahaifiyata cewar bana zumunci da ke, idan kika kuma zan hadaki da yan barikin daa zasu fitar maki da bariki a ranki, Useina idan kika kuma gigin neman haramci da ni zan goge fuskarki a samab kwalta kafin na dauke kanki da bindiga!, Ki karata da kwaratanki sun isheki , da izinin Allah ba zan yi lalacewar nan da kike burin ki ga na yi ba, ba dai da ke UWATA ba!" da karfi ya karashe maganar yana mai doka hannunsa a jikin garun wanda ita da ya doka a kusa da ita, ita ta tsorata da haka harma ta yi gagawar rintse idannuwanta jikinta na rawa a tsorace ta sake kallonsa da idannuwanta da suka cika da hawaye, bakinta na bari ta ce" Muhay, yaya zan yi? Kadarata ce soyayarka"
Da wani bacin ran a amon muryarsa ya ce" Ki saurara haka, da nake daga maki kafa ban titsiyeki ba ba dan komai bane sai dan jin kunyar zumunta, kadara? Ke taki salon kadarar lalle ina jinjinna mata, kadarar taki ce son kowani gara? Ke Useina yara kannana kike mu'amala da su, mu'amala lalataciya, kin dauka ban sani bane? Ki ce MUHAY kai din son zuciyata ne na yarda wanda kike so ki baje a saman bed dinki zan yarda aman ba kice min ni kadararki bane, ni son zuciyarki ne Useina wanda aikata aikin banza ya saka kike jin sha'awata, ilar aikata aikin banzan da kike yi kennan Allah ya saka maki kwadayin abinda yake guba a gareki, Babar matsalar kuma bayan shirme kin fara hauka a kan lamarinki, USEINA ba zan taba kasancewa mai yi maki biyaya ba ko ki fahimta ta laluma ko duniya ta ganar da ke!"
Daga haka ya matsa ya juya ya barta a wajen, wanda barin nata da ya yi ya sakata dukewa a wajen tana cire dan kwalinta hadi da sakin kuka tana mai rukunkume hannun nata a jikinta
Da dan karfi ta ce" Sai dai ka kashe ni, kana tunanin tunda na tunkari kowa da maganarka zan ji tsoron birgarka ne?, Kennan har dauka kake soyayarka da bukatar da nake biyawa kaina da wasu mazan daya ne?, Zaka gani, yadda ka kawo har yanzu baka mu'amalanci mace ba, ba zaka taba mu'amulantar wata ba, ko yar gidan uban waye!"
Sai da ta ci kukanta sannan ta mike da dan kwalin ta nufi ciki ta nemi wajen ruwa ta kunna ta wanke fuskarta sosai ta gyara daurin dan kwalinta sannan ta juya da niyar fara isar da sakonta a yau yau ba sai gobe ba!
A lokacin da ta shigo Mama ta gama sallar la'asar kennan Shuwwa na tsakar yi ta karaso da sauri ta zauna a kusa da yar uwarta ta riko hanneyenta ta fashe da kuka
Kukan da ya saka Mama zabura a tsorace tana kallonta
A gigice Mama ta shiga fadin" USEINA menene? Tun dazu na fita na nemeku sama ko kasa ban ganku ba menene? Kukan me kike? Ina yake ne?"
Useina ta sake waigawa wajen da SHUWWA ta kai sujadarta ta karshe ta ce" Yanzu Hasana dama SON zai yi auren matar da saboda ita zai nuna min komai na iya faruwa idan har ban fita a harkarta ba?, Dama zan ga irin ranar nan?"
Mama ta kalleta a hankalce ta ce" Useina kin ga, ki nutsu dan Allah ki fada min me yake faruwa yau kuma?"
Useina ta sake yin yadda ta saba dan ta hauda Maman da sirikanta, ba kunya ba jin tsoron Allah bale na Muhay da ya gama ja mata kashedi ta ce" Tunda na shigo dakin nan yarinyar nan ke kin wani irin kallo, tunda ta ji kin yi maganar rigar jikina ta dameni tana gannin kin fita ta ce da ni kamar yar bariki?, Ta dora da fadin bama kama bane yar bariki ce ni, raina ya bace na budi baki da niyar yi mata magana shikenan Son ya tare ya hanna, hakan ya bani mamaki na tsatsareshi da ido uwa uba a gabana ya rukunkumeta ya shiga kissing dinta, Hasana da kika shigo ya saketa ya jani ya gindaya min kashedin a kan matarsa yana iya yanke zumunci da ni kwata kwata, cewar a kanta babu abinda ba zai iya yiwa kowa ba ciki kuwa harda ke da kika haife shi, ya ce yana iya zabarta ya bar kowa, in ina gardama na tambaya ina tsohuwar matarsa?, Hasana kina kallo ya sake auro mana masifa?"
Irin kallon da Mama ke yi mata dole ya saka mutun a cikin tunanin fasarar kallon
Mama ta tsareta da duban nan ne tamkar tana son gane ita din wata irin halita ce?
Tsoro, tashin hankali kala kala suka ziyarceta, Tabas abinda Shuwwa ta fada bata yarda da shi ba domin maganar da ta fada sam karyar bata tsaru ba, ta dai hakura ta bar maganar a haka ne dan ta cire wasi wasi da shakun dake cikin zuciyarta
Sai dai a yanzu wanda kanwarta ta fada ya sakata a cikin tashin hankali Gaba daya maganar da ta fada tana iya zamtowa gaskiya duba da a saman Shuwwa din ta shigo ta same shi, sannan a gaban idannuwanta ya damki hannun yar uwarta ya fita da ita, bayanma wannan a kan wani dalili zata yi masu karya ne? Shin da gaske ne abinda ta fada cewar MUHAY ya fada a kan Yarinyar nan?
Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi har kunnayenta suka jiyo mata salamewar sallar Shuwwa ta juyo da sauri baki da hanci a bude tamkar zata hadiye su da su tana kallonsu da mahaukacin mamakin da ya ki buya
Ta san bata da bakin da zata taro maganar nan, da farkoma ita ta saka kanta a cikin ramin nan, anya kuwa tana iya fitar da kanta?
Mama dake kallonsu jin zuciyarta zata buga ya saka ta mike da sauri ta nufi hanyar fita ba tare da ta yiwa kowa magana ba, wanda hakan ya daka Shuwwa mikewa da sauri da niyar bin bayanta, sai dai riko mata mayafi da akai aka dawo da ita ya sakata juyowa da sauri tana kallon matar nan da fuskarta ta zame mata tamkar ta kumurci
Yar dariya ta yi tana kallonta ta ce" Dama kin yi hakuri kin anfani kyanki ta hanyar da ta dace da ke, da kin guji zakin da ba mahadin Barewa ba to da ina iya yi maki hanyar da zaki mori kyan naki......kina neman yiwa al'amarin da baki da ci a cikinsa shishigi? Meye mahadin hanyar mai cin ciyawa da mai cin nama? Uban dawa yake sai zakanya zata iya da shi ba ke ba!"
Tana gama fada ta zo da niyar wuceta ta tafi, sai dai abinda ya dakatar da ita jin muryar Shuwwa wace ta cika da mamaki da bugawar zuciya tana kallonta ta ce" Ji mana?"
Dan dakatawa ta yi ta juyo tana kallonta da cikaken rashin tsoro irin na rikakiyar yar bariki tana kallon Shuwwa din da jin wata magana ta rainin wayau tana neman yi mata wai ji mana?
Shuwwa ta dan sake dubanta tana kiyasta shekarunta a zuciyarta a nutse ta ce" Mama?, Sorry wacece zakanyar? Wacece barewar?"
USEINA ta yi wani yannayi na ta dan shaka kadan kafin ta dan girgiza kanta a kausashe ta ce" Kece Barewar, da kike nama a gaban zakanya, watau ni!, Da zaki yi biyaya zaki iya tsira da mutuncinki?"
Tabas bata yi hasashen jin cewa Useina ce zakanyar ba, ta zata ko y'arta take YIWA yaki, sai dai da ta fadi hakan kamar ta gaura mata mari ne, domin sai da ta ji kamar zata kifa kafin take iya rike kanta tana kallonta ta ce" Mama, wai ke Zakanya a matsayin uwar zaki kike nufi bakya so danki zaki ya rabi Barewa ko yaya fahimtar da ni?"
Haushi ya saka Useina nunata da yatsa ta ce" Ke saurara min, ba shirme ya tsayar da ni a nan ba, idan baki fahimta ba zaki gane !"
Da sauri Shuwwa ta bi bayanta gannin ta sake juyawa zata tafi da sauri ta saka hannunta ta janyota baya ta yada ta juyo a haukace da mamaki tana kallonta
Tun daga kasa har sama Shuwwa ta daukota da kallo kafin ta sauke a saman fuskarta Yar yatsarta manuniya ta nuna mata zaryan tana kallonta a kausashe ta ce" Ki cewa haukan dake kullawa ko kuncewa a cikin kwakwaluwarki cewar na amshi tayin, ki fadawa rayuwarki cewa da aure ko babu tabas sai na zama Barewar Zakin nan, domin sai ya farauceni ba dare ba rana dan ya ci abinda yake lafiya a gareshi watau ni da nake namana wajenshi!, Ki karra sakawa cikin zuciyarki cewa zaki baya cin zaki bale tsohon nama ai ba na Uban dawa bane!, Ki fadawa kadararki, ko nace gangancinki cewa na siya da farashi mai tsada ba gudu ba ja da baya sai na deba kuma sai na amshi kaya a duk lokacin da hakan ta kama!, Kina iya sakawa a sakeni, aman walahi ki sani sai na haukata duniyar mafarkinki ta yadda zai dawo ya zamto mumunan farkawarki!, Domin ni zahiri ce , kuma na sha iskar duniya sosai ta yadda YAR BARIKI irinki ba zata gigitani ba!, Dama kin kadaice kanki kin sha shinkafar bera an turbune ki da wannan abin kunyar, a gaba ki gani a aikace cewar ya zabeni a kanki!".........
Da mugun mamaki Nahidht ke kallonsu , tunda ta tunkaro take jin maganar Shuwwa a kausashe ya saka ta shigo da sauri
Abinda ta gani ya sakata zubawa Shuwwa ido tanai mata kallon ko ta haukace ne?
Da sauri ta kalli matar da itama mamaki ya nemi halakata ta sake bin yarinyar da ta rainawa ajawali kallo kafin ta fita da sauri tana kai hannunta wajen zuciyarta dake dokawa da gudun balakin tsoron da ya fi na kashedin da MUHAY Ya yi mata karfi
A zabure Nahidt ta juyota tana kallonta kafin ta saketa ta shiga fadin" Shikenan, shikenan, hankalinki ya kwonta, ke wannan fa itace abokiyar tagwaitakar mamansa, me ta maki da zafi da kika nuna mata kalar naki haukan ? Kin san da an sake ki an gama? Mun shiga uku yanzu Shuwwa sai da kika tsinke auren? Tabas Idan mama ta farka sai ta ci uwar ubanmu"
Shuwwa ta kai zaune dabar tana jin wani irin ciwo a zuciyarta wanda bata san dalili ba rai bace ta ce" Walahi, walahi ko ya sake ni sai na bishi irin yadda karya zata bi shi, sai na zamto tamkar bindi a jikinsa, sai ya fuskanceni na gigita rayuwarsa, yadda wannan tsohuwar guzumar take sonsa ba zata taba samunsa ba, ke Nahidt Son Muhay take yi , so irin na soyaya!"
Nahidht ta yi wani irin zabura tana sakin hijab dinta kasa Jikinta na dan rawa ta dauko Hijab din tana kallon Shuwwa ta girgiza kanta ta ce" Ke kin ji me kika ce?"
Shuwwa ta yi wani murmushi mai ciwo tana gyada kanta
Nahidht ta yi gagawar zuwa wajen salaya ta gyara shi da kyau tana fadin" walahi talahi duniya ta zo karshe, bara na yi sallah kar a tasheta da sallah a kaina, Innalilahi Allah ka sa na auri malan kafin a busa kaho, mun shiga uku Shuwwa na shiga uku wannan matar da tsinaniya ce? Ke gaske na kasa gaisheta ashe uwata ce a bariki Innalilahi wa inna ilaihi raj'une.....Shuwwa mun shiga uku...." Haka ta yi ta sambatu, ita kuma Shuwwa din gaba daya jikinta tamkar wace aka zarewa lakkah Ya kasance ne ta kurawa waje daya ido ta kasa fahimtar komai Bata taba jin tsana da kyamatar a rabi abinda take jin a yanzu kamar nata ne irin kar matar nan ta rabe shi domin ai d'an y'ar uwarta ne irin na yau ba
Da wani takaici ta tashi ta fice ta nufi dakin da mahaifiyarta take ta zauna ta zuba mata ido tana kallonta