Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 44
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 44: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 44. A yanzu tsafta ingataciya na tare da iyayensu, sai ramar da dan ciwon…
3,333 words
A yanzu tsafta ingataciya na tare da iyayensu, sai ramar da dan ciwon da ake magani ba dare ba rana A haka ta tare har yar uwarta ta tardota suka zauna tare ba tare da sun yi tunanin makomarsu a kusa ba, ganni suke koda iyayensu na hali na rashin lafiya a yanzu da suke raye babu mai cin masu, ganni suke dukan wanda zai ki su shikenan ya ki su ai ga mamansu a kwonce ota zata so su! ( Uwa kennan, iyaye kennan, Allah ka gafartawa iyayenmu, ka sa su gama da duniya lafiya,, wa'inda suka rasu Allah ka jikansu, ka basu aljannah ya Allah)
__________________________________________
Bayan sallar magariba
"Ka ga, ai yaren sai ai masu uzuri ko? , Yaren sun cencenci uzuri sosai........, Abinda yake damunahhhhh, abinda na kasa hadiyewa shine zancen gaba dayansa, Meme shin dukkan abinda matanka ke yi mata kafin ka rabu da su gaskiya ne ko kuma ba gaskiya bane?, MUHAY da gaske kaine zaka ce wai saboda matarka nima sai ka bata min?, Ka ga ni fa na haifeka.....gaba daya sai nake kin yarda da maganar ban san ba tsananin sonka ke ya sa haka ko menene?, To aman idan ban yarda da maganar ba da me zan yarda? Kai ka ki zama ka yi maganar da ni..... Sam baka yarda da ni ba, kana boye min damuwarka sosai Muhay....., Shin me yake faruwa tsakaninka da mamanka???? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une MUHYIDEEN zuciyata ciwo take yi, shin ka kai shekarun da dole zan yi hakuri da halayanka na rayu da kai a haka ne ko menene ?, Shin ya kai wajen da zan maka biyaya ne ba ka yi min ba?......"
A sanyaye CHIEF OF ARMY dake kallonta cike da tausayawa , sannan ya kalli MUHYIDEEN dake duke kansa a kasa a gabanta yana sauraronta tana kuka , gaba daya ta rikice ta shiga a duhu, so take sai an fahimtar da ita ko menene, bayan bata san rashin sanninta ya fi sanninta kwonciyar hankali ba
A sanyaye ya ce" Wife....."
Kanta take girgizawa ta ki koda kallonsa
A sanyayen ta ce" Dan Allah Abansa kar ka ce komai ka ji?, Na san so kake ka ce min na bar maganar ko? Kar na takura masa ko? Shi ga wanda ya isa ko?, Shikenan ya tashi ya tafi.....ba zan ji haushin matarsa ba domin yarinyar nan tunda na ganta na ji ina kaunarta a raina, na ji ta kwonta min a matsayin matar d'ana, harma na ji tarihinta na karra jin tausayinta da muradin talaf mata, gashinnan har yanzu bata dawo ba, ta yiwu ta tsorata da yannayina ne, bata san a cikin halin kaka naka yi nake ba, abubuwa sun shige min duhu kuma an ki a fitar da ni..........., Ai ni zan yi farin ciki ka so iyalinka fiye da kowa, sannan ka sawakewa yar mutane da baka kulawa ka barta ta tafiyarta ta samu daidai ita, aman ba zan takura maka ba idan ka ga dama ne Muhay......" Ta karashe tana cicibawa da niyar bara masu wajen, stlll kuma tana kukan
Hankalinsa ya karra tashi, sosai hankalinsa ya tashi
A rikice ya rike kafafuwanta yana sada kansa a jikin gwuiwoyinta muryarsa na fita da kyar dan furucin da zai yi bai san me zai haifar ba , ya dago idannuwansa da sukai jajajir daidai hawayenta sun sauka suka sauka a saman fuskarsa , da gagawa ya ringa girgiza Kansa ya ce"
😭😭😭😭😭😭😭 Oh rainarhhhhhhhh😌😌😌😌🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺😍😍😍😍😍😍😍ALK'ALAMIN KADARATAH
Na
*Sajida*
Page
5️⃣0️⃣
Da gagawa ya ringa girgiza kansa ya ce" Mahmahnah......."
Mama ta sake jin wani takaici na sake tukota dan hakaa ta janye kafarta fahimtar da ta yi baa fada mata ba zai yi ta zagaye shi da sauri ta nemi barin dakin
Chief of army ne ya yi gagawar dakatar da ita ta hanyar ambatar sunnanta kai tsaye sanann ya mike shima jikinsa a mace yana kallon bayanta
Muryarsa a sanyaye ya ce" Na so ki kasance mai hakuri da kawar da kai har Allah ya nuna maki alkhairin abin, domin tsananta bincike bashi da wani alkhairi , bashi da kyau, sai dai kashhh, kin kasance mai yawan son bin didigin abubuwa, gashi yau har kuka kike masa dan yana kare ki da bacin rai?, Hasana yaya zaki yi da gabar dake tsakanin Yaronki da yar uwarki?, Ya nisanta kansa da ita , kin matsa kin kisanto shi da ita, subahannalah, Hasana"
A dan tsorace ta juyo tana kallon Chief of army, sannan ta kalli Muhay da ya kifa kansa a jikin kujerar da ta tashi gaba daya jikinsa na jijiga kamarma wanda yake yin kuka ko menene? Tashin hankali mai girma ta ji na karra ziyartarta, sai dai a yanzu babu gudu ba ja da baya ta riga ta kawo wannan gabar bata da halin yin koma baya
Tana kallonsu Mijinta ya dan sake matsota kadan, a sanyaye ya ce" Zan iya kiran hakan da muguwar Kadara, wace ke sake samun waje a wajen wanda ya yi wasa da fadawa Allah, tabas zuciya ce bata da kashi, aman kuma Allah ya bamu hanyar da zamu iya samun kadararmu da sauki idan har muka kai masa kukanmu, kin ga da ace tun da farko da ta faraa jin irin haka ta yi kokari ta nemi shawara sannan ta sake kusanta kanta da ubangijinta , to da tabas ta samu sasaucin koma menene, sai dai kash, kadara, sakaci, muguwar taraya, son zuciya ne suka hadasa haka, kuma sakaci da adu'a ya sa abun ya sake yin tasiri a kanta....."
Sake kure fuskarsa take da kallo tana ji tamkar ta saka haannunta tta bude masa bakinsa ya yi magana ta yadda zata ji takamaiman abinda yake faruwa, domin a yanzu kwata kwata ya durmiyata a cikin wani duhun fiye da farko
Aa sanyaye ya ce" Tana son sa ne......"
Bakinsa da ya yi furucin ta tsatsare da ido kafin a sanyyaye ta dan juyar da hannunta ta ce" Abansa har yanxu baka fadi laifin ba, ka ce tana sonsa ne ka yi shiru, to wanene bai san cewa Useinata na son Son ba? Matar da a kansa sai ta batawa kowa rai? Ai tana son yarontah......"
Dan sauke ajiyar zuciya ya sake yi zai kuma yin magana Muhay yaa mike tsaye a hankali ya karaso ya kama hannayenta ya nufi wajen zaman da ta tashi ya zaunar da ita kafin ya zauna ya rike hannayenta yana fuskantarta sosai ya sake kallon CHIEF OF ARMY da ya dawo ya zauna a gefenta yana jin tsoron abinda za'a fada mataa domin bata iya tashin hankali ba sam
A sanyaye ya ce" Mahmanah, tun kafin ki haife ni kin san bawa kowa da irin kadarar da Allah ya hukunta zai faru da shi, sannan ina so ki sani cewar abinda yake faruwa launi ne na zane zanen kalar ALK'ALAMIN kadararmu, a cikin lamarin zan so ki dubi wajen dadin fiye da bakin shine cewa har zuwa yanzu makamancin hakan bai faru ba, kennan Allah ya kadarta sannan ya kare mu da kariyarsa........, Baban abinda zamu iya yi shine ci gaba da adu'a, yi mata uzuri, sannan mu ringa nuna mata dan ta bar halayan nan da take yi kwata kwata ta koma ga ubangijinta domin mutuwa ana barin ciki, jariri ya mutuma bale ita, baa lokaci, idan har lokacin yaa yi shikenan baa tsumi ba dabara sai an tafi, shin idan bawa ya je ga ubangijinsa da wannan kayan a saman kansa ina zai saka ransa a kiyama?, Tabas ya shiga uku ya kuma shiga uku, domin ya tozarta komai bayan shi din mai shahada ne a bakinsa........"
" Haba MUHYIDEEN MUHAY, ba zaka fada min ko menene ba sai zuciyata ta buga?, Ka fada min na gaji dan Allah"
Idannuwansa ya lumshe a sanyaye ya ce" shekaru shida da suka wuce ne, a ranar da kika tafi haji tare da Dad, ya kasance bani da wajen cin abinci dole sai a wajenta, da na je cin abinci gidanta ne ta.........." Idannuwansa ya dago a birkice ya zuba mata su yana kallon fuskarta ya ce" a ranar ne ta , ta ce tana sin aurena......." Ta karashe yana mai dantse harshensa yana kuma sadda kansa sakamakon kunya da ta lulube shi bayan furucin nan da ya yiwa mahaifiyarsa wanda Allah yana ganni ya fi jin kunyarsa fiye da komai
Da farko dan shantakai take kallonsa, kafin ta juya wajen mijinta a zabure tana kallonsa
Yannayin da ya nuna ya saka ta gane lalle fa abinda yaron ya fada ne ta ji a kunnenta sannan iya gaskiyar kennan
Da karfi ta so mikewa, sai dai ya riga ya gaje wajen harma ya danne kafafuwanta yana sake sada kansa sosai
Da karfi ta saka hannunta dan ta hankade shi, aman ta kasa domin ya ririketa sosai kansa a kasa
A haukace ta sake ture shi tana mai daga hannunta ta ratsa masa wani ratsetsen marin da ya bada sautin tasssssss a saman fuskarsa sannan ta sake neman dago fuskar tasa, hakan ya sa ya dago fuskar tasa yana sake rintse idannuwansa ya bata dama ta hanyar bata fili ya sakar mata kyakyawa, lalausar, ni'imtaciyar fuskarsa sannan ya ki bata damar tashin dai
A wani haukacen ta sake wanko fuskarsa da mari ta kuma guda, ta daga zata kifa masa na hudu mijinta ya tare yana kallonta muryarsa a rikice ya ce" Me kike yi haka Hasana?"
Da muryar kuka da ihu ihu ta ce" Kai, ka ji me yace? Giya ya fara sha ne? Kana jinsa kuwa? Mamansa fa? Ko ban fahimta daidai bane? Mamansa fa?"
Da sauri ya dubeta a kausashe ya ce" Eh ita din sai me Kuma?, Aka ce Ita din fa sai aka yi yaya? Ko karya akai mata ne? Kina fa gani irin yadda muke kauce maki haka dan mun san ke din nan zuciyarki ba zata dauka ba, a yanzu da kika takura har kika ji sai ki ringa yi masa tankadeta mareta kina cewa ya sha giya? Wace giya kuma da ta fi bayananiya ne?, Hasana ki fuskanci yaronki mana, ke kin san me kika haifa, idan kin san makaryaci kika haifa kuma fine ki karyata maganarsa sannan ki turashi wajenta sai ki rufe taron da fatiha ki kuma tanadi haduwarki da Allah!"
Yana gama fada rai bace ya mike fuuuuu ya fice a falon Sai dai yana fitowa idannuwansa suka sauka a kan yarinyar dake dauke da igiyar auren MUHAY a kanta tana yi masu labe Bata zata wani zai fito a yanzu ba , fitowarsa kuma ya sakata saurin juyawa dan ta basar din nan, sai dai ta makaro domin dama ya shaka ne ya fito kuma sai ta fado a daidai gabar da yake neman abin nema dan ya duba duba na tsanaki A haukace ya damki hannunta ya nufi falonsa da ita, wanda hakan a kan idannuwan matayensa biyu, wa'inda suma sun kasa tsaye ko zaune kowa ya fuskanci baban d'an da mijinsu ke kauna na cikin bacin rai hakan ya sa suma suke shawagi dan gane abinda yake faruwa
MUHAY a sanyaye yake kallonta bayan ta gama maganarta da ihun fadan da ta zuba, fuskarta ta yi jajajir , hancinta ya karra yin tsayi Idannuwanta kuma sun yi wani iri Ta zama abin tausayi ta sake fuskantarsa na dan sakwani, sai kuma ta fashe da kuka tana girgiza kanta ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ya Allah ka sa mu cika da kyau da imani, da ban gaskiya da kalmaru shahada a bakinmu, Allah ka sa karshenmu ya yi kyau ya ubangiji, ko me muke aikatawa ba na alkhairi ba Allah ka sa kafin mu mutu mu tuba, ya Allah ka sa mu din masu dacen kyakyawan karshe ne......."
A hankali ya gyara zamansa yana sake riketa a jikinsa domin ta sauko daga saman kujerar gana dayanta ta zube a kasa hakan ya sa ya riketa a jikinsa sosai yana saurarenta
A sanyaye , muryarta cen ciki ta ce" Tabas tsananta bincike bashi da kyau, ba zan kuma ba Son"
Kansa yake gyadawa a hankali yana karra shafa gadon bayanta
A hankali ta sake fadin" yaya aka yi kana sane ka kyale idan ta ce matar da kake aure ta mata laifi na hau na wulakantar da y'ayan mutane har a je da saki?, Ashe halin kadarar da yar uwata ke ciki kennan?"
A hankali ya ringa shafa gashin kanta daa sanadiyyar take hijabin ya sa ya bayana a birkice take sosai
Wayarsa dake jikinsa ce ke ta vibration tun dazu, da kyar ya iya cirota yana dubawa Gannin Colonel ne ya saka shi dagawa a hankali ya karra a kunnensa yana sauraro
Da kyar ya iya furta magana kamar haka" idan ta ki biyoku ka dauki Sergent Umaimat ta daukota ko a kai ne, kar ta kwana a asibitin nan" Daga haka ya datse kiran yana sake buda idannuwansa a saman mamansa a sanyaye ya ce" Mahmanah"
Mama ta sake rintse idannuwanta ta ce" yaya zan iya rintsawa?"
MUHAY ya ce" zaki iya Mamanah, nima yau zan iya yin barcin sosai fa, domin kin ga ai kin sani, zakuma ki min adu'a kamar yadda kika saba, wada na san daga kin yi Allah zai amsa"
Mamah ta sake sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Zamu yi mata uzuri ko Son? Sanann zamu yi mata adu'a, zan sake kusanta kaina da ita dan n 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 5️⃣1️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Zai kuma yin magana suka ji budewar kofar falon da karfi, Shuwwa ce ta auko kamar an hankadota sannan ta ja wani uban birki tana waigawa ta nuna hannunta ta ce" Ke , ke bari shi wanda ya turo ki ki rikonin nan a kansa zan huce, in ba sai ya fadan in ni y'arsa ce ba shegiya nake yau ga wulakanci ki dagoni gaba dayana ki dura a mota? Kan ubancen kayasa!"
Nahidht dake rike da takalman Shuwwa din da wayarta ce ta shigi itama ta dan dakata ta juya tana dan daga hannunta da yar dariya tana fadin" An fa gode yalabiya, walahi ban taba gannin mace kamar kato irinki ba, kin dai ga kin cicibota cimak kin saka a mota, Allah ya biya, idan Kuma ta ki zama zan saka a taboki ki ci min uwata ko zata shiryu kin ji? In ba Haukan Shuwwa bama ita ai da galihunta ko yanzu aka busa kaho soja zai riko hannunta, Allah ka sa su ji kaina su aura min Malan ko zan je da galihuna...."
Turus sukai sunna kallon su Mama da MUHAY da ya dafe gaban goshinsa bayan ya karewa Shuwwa kallo wace tamkar zata yi dambe dan kwalinta dama tuni ya bar kanta
Bakinsa ya dan tabe a lokacin da ya tsinkayi muryoyinsu sunna gaishe da Mama , irin basu san tana wajen nan ba
Nahidht ta yi yar dariya tana fadin" Walahi mama mun zata a cen zamu zauna ne, sai ga soja yace mu zo gida, to dai itace ta yi gardama , har ya koma yan mintunna sai gashi da wata ta dauko Shuwwa cimak kamar baby, Allah mai iko, a yau na ga abubuwa walahi Mama"
Mama ta yi Murmushi tana mika hannunta ta kamo hannayensu, da kyar ta iya budar bakinta tana fadin " ku yi hakuri y'ayana wani abu ne ya fitar da ni na gagaw akun ji?"
A sanyaye Shuwwa take kallonta, a hankali ta dan karra matsawa kusanta tana sake kallon fuskarta
Mama ta yi masu dan Murmushi ta ce" ku je ku yi wanka maza ku kwonta ku huta zamu yi magana gobe in sha Allah "
Amsata sukai suka mike suka nufi cikin dakin
Sunna shiga wata gardamar suka dora da cacar bakin har dai Shuwwa ta fara shiga wanka ta barta da waya a kunne sunna zantawa da babanta bayan ta gama fadin ta mata shiru zata zanta da tsohonta, ita dai ta shigewarta ciki da mutuwar jiki
A nutse ya sake dan bata lokaci a wajen mahaifiyarsa, ba wani dogon magana suke yi ba, aman dukkan maganar da suke yi na tafe da kula da kauna irin ta d'a da mahaifi, tana dan nuna alamu na ta yi dana sannin matsawa har ta ji maganar, shi kuma yana yin iya yinsa dan ya kwatanta mata cewar in sha Allah komai zai wuce, har dare ya tsala ya kamata ya rakata har cikin dakinta
A lokacin da zai fita daga dakin nata ne ta dan yi murmushi tana fadin" MUhay, yaren nan basa birgeka?"
Dan dakatawa ya yi yana dan juyowa dan ya fahimci wasu yara fa?
Mama ta sake yin dan Murmushi tana cewa" Ina sonsu a raina sosai, ina sha'awar yarintarsu, sannan ina son ci gaba da kula da su sosai, ka ga su fa dole sai anai masu uzuri sunma yi kokari fa?"
Sai a lokacin ya gane wa'inda take nufi, dan Murmushi ya yi mata a hankali ya furta" Allah ya tashemu lafiya Mamahnah"
Mama ta amsa shi itama tana kallonsa har ya fita kafin ta mike jiki a mace ta shiga bayi ta yi wanka hadi da dauro alwallah ta dawo falonta ta cenza tufafinta hadi da daukan dardumarta ta fuskanci gabas ta shiga kai kukanta wajen ubangijinta tun yanzu, domin ita gyara da sauki take nema a wajensa, ta san cewa shine kadai ya isa ya sanyaya mata halin da ta tsinci kanta a ciki, ta kuma san cewa idan kana da damuwa ko baka da damuwa ka kasance mai kai kukanka a wajensa sannan mai gode masa a kowani irin lokaci, shine baya gajiya da baka, baya gajiya da rokonka a gareshi, shine mai mayar da baki fari, ta kuma yarda cewa shi zai mata.
______________________________________
Kofar ya kama ya bude ya shiga ba tare da ya yi salama ba, to koda dai ya yin gaskiya kunnayensu basu jiye masu ba sam sam
A hankali Nahidt ta ajiye man dake hannunta a ranta tana ayana' Toh fa, me muka masa kuma ya shigo ya bamu daidai da kugunmu? Ni fa har ga Allah Tsoron mutumen nan nake shi yasa bana haye masa, Allah dai ya raba mu lafiya'
Mikewa ta yi tana ajiye man a nan ta dauki hijab dinta ta kalli wajen da Shuwwa ke zaune saman madubi tana fesa turare a jikinta su bayan kunnenta ne, au hamatarta ne, da dai sauronsu ta ce" Bara na ga ko zan samu netwrk din nan a waje "
Sai da ta zo fita sai kuma ta ja ta tsaya tana dan kallonsa ta ce" Yalabai, dan Allah na ce dama na fitar da miji a taimaka a daura mana auren nan kafin su Mama su ankare da abinda na aikata , ban san yaya zamu kare ba, kar su tsine min albarka kuma a zo a shiga uku"