Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 45
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 45: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 45. Idannuwansa ya dago a karro na biyu ya sake kallonta kafin ya girgiza…
3,210 words
Idannuwansa ya dago a karro na biyu ya sake kallonta kafin ya girgiza kansa bai bata amsa ba yana kallo ta juya ta fita a dakin, ya riga ne ya gama yin waje ya ajiye yarinyar nan cewa akoy wani abu dake damun kwakwaluwarta, koma menene dai akoyshi abin nan
Dan ribom dinta ta saka ta daure gashin kanta sannan ta mike ta juyo face to face da shi
Idannuwanta ta tsatsara a saman fuskarsa kafin ta dan sauke ajiyar zuciya ta ringa takowa zuwa wajen da yake tsaye
A hankali ya ringa kallonta yana fasara me hakan yake nufi? Har ta zo gab da shi sosai tana niyar take taku dayan da ya rage ta auka jikinsa ya samu kansa da dan matsawa yana sake kallonta da mamaki kafin ya ce" Me kike yi haka ne?"
Dan duduba gefe da gefenta ta yi sannan ta sake kallonsa, da zazakar muryarta ta ce" Ban gane tambayar ba"
Idannuwansa ya yiwa micik micik ya ce" Kin ga , karfa ki dauki abinda ya faru a asibiti a matsayin da niya na aikata, na aikata ne dan wani dalili daban ba abinda kike tunani ba"
Idannuwanta ta dan zaro ta ce" Me na ce to ni?"
Da kallon kar ki rainan wayo ya kalleta ya ce" Dama bana so ki ce din, ki kula ni kar ki fada min!"
Bakinta ta dan tabe tana juyawa a hankali ta shiga dan takawa ta ce" Dadin abin jikinka ai ba laushi ne da shi bale a so fadawa!"
Ido ya dan tsura mata kafin ya saka hannunsa ya damko nata ya juyota gaba dayanta yana kallonta ya ce" Me kike nufi?"
Kasa kasa ta kalla wajen kirjinsa sannan ta dago tana kallon fuskarsa , sai kuma ta shagwabe fuskarta sosai ta ce" Ka ga fa damkar min hannu ta yi da karfi ta ciciboni a gaban mutane har sai da rigar dake jikina ta yi sama har ana gannin cinyoyina , yarenka na kallo ta watsa ni a mota ta rufo, fisabililahi kafin mu rabu ai an wulakanta mutuncinka ko?"
Gaba daya sia ya ji har tsigar jikinsa na neman tashi na bacin rai, da sauri ya kalli wajen kaffafuwan nata sannan ya kalleta da kyau Wani kunna ya fara ji ransa na yi masa, harma ya shiga tambayar kansa da Colonel bashi da hankali? Shi ya sa akaiwa matarsa tsirara? Lalle zai koya masa hankali kuwa daga shi har ita!
Rai bace ya ce" kina ji, Mama na cikin bacin rai, ki yi kokari ki dubata kafin ki kwonta, shine kawai ya kawo ni!"
Daga haka ya saki hannun nata da ya damko ya juya har yana hada kaffafuwansa wajen sauri ya ciro wayarsa ya danna kiran Colonel
Colonel na dauka da fada fada sama sama ya shiga fadin" Ashe baka da hankali? Da wa da wa kuka je daukan iyalina har za'a dorota a kafada?"
Da mamaki Colonel ya ce" Sir?"
MUHAY ya yi gagawar katse shi da wani fadan yana fadin" Ka saurara malan, kafar katana a waje a gaban karti? Ku hadu gaba dayanku har ita mai karfin a fada kin dalili!" Daga haka kittt ya kashe yana huci ya juya wajen da ya ga an tsura masa ido
Dan murmushin da ya saka gabanta ya kwonci kwonci ya fadi ya sakar mata , wanda ya sa bayan tsoron gannin an shiga da natar MUHAY din dakin cen, ya karra dora mata Tsoron kar dai gaskiya ne da matar tasa tace ya san ko su wa ke bibiyarsa?
Da sauri ta juya tana barin wajen gabanta na ci gaba da faduwa da tarin tsoro a ranta.......................
Sai da Nahidt ta gama kallonsu kafin ta yi murmushin itama ta koma ciki da wayarta a kunnenta sukai salama ta tura kofar dakin Shuwwa tana mai yin salama a bakinta
Gannin shuwwa tsaye ta rungume hannayenta a kirjinta ya sakata yin dan kasakai tana kallonta, sai kuma ta tabe baki ta zagaya zata haye bed ta ji Shuwwa na fadin" Oh, ban taba jin murya mai dadi irin ta sojan nan ba, kaf duniya babu mai dadin muryarsa wollah"
Nahidht ta mike zaune da sauri tana kallonta da mamaki ta ce" IBTISAM wa kike nufi? Ina fata Abanki?"
SHUWWA ta juyo tana kallonta itama ta dafe habarta ta ce" Abana kuma? Me hadina ni kuma da fadin muryar Abana?"
Nahidht ta idasa zama da kyau ta ce" Ke aman bakya jin tsoron Allah, yanzu wannan muryar marar sirri ce zaki ce ta fi ta Akaramalahu alarama ustazu bawan Allah, murya sam ba sirri ba laushi ba lausasawa?"
Shuwwar ta idasa saman gadon tana fuskantarta ta ce" Me zai hanna kowa kar ya fadi aubun kowa kawai a zauna lafiya? Kin ga dai kar ki sa na ce muryar ubana wata sanyi karai ba wani kazar kazar bayan ana son namiji da zarar ya yi magana a waje, kai ko motsi ya yi a gane ba kawai a ringa rarashin mace ba!"
Ido NAHI ta zarro da mamaki ta tafa hannunta ta ce" zan ga annabi in nai hali na gari, yau kuma ke? Yanzu yaushe kika fara sonsa? Wai son gaske ko karya? Ke bari ki ji karya ne a zagi Malan a gabana walahi"
shuwwa ta tabe baki tana kashe wayarta ta jefa mata tana fadin" dadin abin a nan babu abinda ba'a yiwa uban nawa ba, yanzu a wani ce ana sonmu, kuma da kike cewa ni in so soja kema kin san kin dai fadi ne, maganar gaskiya a yita yana da dadin murya, yana da kanshin turarae dadada fajat aman ba maganar so bata taso ba!"
Daga haka ta juya ta barawa Nahidt dakin wace mamaki ya sakata hangame baki tana tunanin kaf duniya ba wace ta rainata irin kanwar tata.
Tunda ta zo dakin Maman take zaune tana kallonta, sujada ce ta yi kanta a kasa har sai da ta fara jin Tsoron rashin dagowarta, harma ta ambaci sunnan kiranta da sunna Mama? A sanyaye tana kallonta Sai cen Maman ta dago da fuskarta dake cike da hawaye ta yi zaman tahiya sannan ta salame ta juya wajen da Shuwwa ke zaune tana kallonta
A hankali ta dan yafitota, Hakan ya sa ta rarafa ta karasa kusa da ita sosai tana kallonta
Mama ta ce" Baki yi barci ba?, Ina fatan lafiya?"
Shuwwa ta sauke ajiyar Zuciya a hankali ta ce" Mama fada mukai da Nahidt din", ta fadi haka ne dan bata san me zata ce ba, gashi so take ta jima tare da maman, haka kawai take ji a ranta koda bai ce ta lekota ba tana iya kulawa da matar da ta ji tarihinsu ta kuma tausaya masu
Mama ta yi dan kurmushi da shakakiyar muryarta ta ce" Kin sha maganinki kuwa yau?"
Shuwwa ta dan girgiza kanta , domin yau bata sha tsumin nan ba ko diz
Mama ta dan shafa gefen fuskarta ta ce" Maza tashi ki ciro a frij ki sha sai ki kwonta saman gadona"
Shuwwa ta gyada kanta, ta mike ta aiwatar yadda Maman ta ce, duda tana tunanin anya zata iya kwonciya saman gadon kai tsaye haka?, Sai kawia ta jure ta zauna a baki baki tana fadin" mama yaushe zaki kwonta?"
Mama ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" zan kwonta y'ata in sha Allah"
Daga haka Shuwwa ta yi shiru bata kuma cewa komai ba, aman kuma tana kallon Maman ne dake ta adu'a da carbinta har dare ya tsala sosai, sannan Maman kan juyo lokaci zuwa lokaci ta kalleta, gannin a zaune take ya saka ta mike ta sake daidaita alarm dan ta tashi daukan azumi ta je wajen gadon tana fadin" Oya haye cen kurya kar aje ki fado tsakiyar dare, ko bakya gigin barci?"
Shuwwa ta yi yar dariya ta haye cen saman ta ja bargo ta rufa tana jin maman ta gama kimtsawa ta hau gadon itama ta kwonta hadi da rike carbinta tana ci gaba da ja....... Ai kam jin mutun a kusanta ya dan rage mata tunanin, uwa uba ga maganin matsala a hannunta watau carbi, tana tsaka da ja barci barawo yayi awon gaba da ita, zuciyarta sakayau ba nauyi ba komai............ta riga ta fadawa mai magani, ya kuma sanyayar mata da zuciyarta........☺️ _____________________________________
Fitsarin da ta tsilala ya jike mata sket dinta jirgif take dan matsa kafarta a ciki, jikinta na rawa tana satar kallonsa
Tunda ya fito mata kwada kwada cewar shin ita ke neman rayuwar d'ansa ? Ya sakata jin kamar zata summa a zaunen da take , harma ta saki fitsari tana mai gannin mutuwarta a gaban idannuwanta
Jikinta na rawa ta budi baki ta ce"💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 5️⃣2️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Jikinta na rawa ta budi baki ta ce" Sir, na rantse da girman Allah ba ni din ce kai tsaye ke neman ransa ba"
Da karfi ya ce" Ke saurara min, ke mahaukaciyar ina ce da zaki bani amsa irin ta mashaya? Ki fito min a mutun ki min maganar da hankalina zai iya dauka ba shirme ba, idan bakinki ya kuma firtan shirme zan maki aiki irin na shirme, me ya maki? Me ya tare maki?"
"Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, wallahi, wallahi walahi ban san kan zancen ba, kira nake samu da muryar namiji ana ce min idan ban yi biyaya na zuba masa guba ba ni za'a kashe, aka ce in dai shine ba zai taba sona ba ina kallo zai so watana, ba nice ta farko ba , ba zan taba zama ta karshe ba, saima ya lalatan rayuwa ya yi watsi da ni, tun washe garin na tare a gidan nan aka fara yi min haka Aba......." Ta fada tana sake fashew da kuka tana kallon bindigar da ya ajiye saman table kafin ya mata tambayar da yi nara nunin yana iya harbeta a kan maganar nan
Kasancewar dama ya shaki bacin rai ne na matar da yake so, wace bai taba tunanin zai so wata bayan wace ya yiwa soyayar saurayi da budurwa ba, ya fito ya kuma ganninta tana masu labe sai ya hauhawa tamkar fulawa
A kausashe ya ce" Laben da kike yi mana na menene?"
Jikinta na wani rawar ta ce" tun jiya na bar maganar saka masa wani abin a abincinsa Aba, kwana biyu na ga yana fita da wannan bakuwar ne , shine yau ya dawo shi kadai da hajia, shine na je dan na ji ko ya saketa ne?"
Hannunsa yake murzawa yana sake nazartarta da son gane gaskiyar lamarin
A kausashe ya ce" Da wace waya suke kiranki? A ina wayar take?"
Da sauri ta ce" wayar na dakina, da ita ce suke kirana tana saman gadona, tun jiya da na yarda ita na kasheta ban waiwayeta ba"
Da sauri ya mike ya saka daya daga cikin yaransa na amana gadinta ya fito da dan sauri ya nufi dakin, a nan ne ya ga su MUHAY na meeting shi da mutanensa ya tsatsaresu
Da dan mamaki MUhay ya raka shi da kallo gannin yadda yake sauri ya kuma nufi cen bangaren matan gidan
A hankali ya dan girgiza kansa sai kuma ya samu kansa da salamarsu ya koma ya tsaya a hanyar da zai dawo ya wuce
CHIEF OF ARMY na dawowa ya ganshi a nan a tsaye , hakan ya saka shi dubansa har jijiyoyin hannayensa na bali na abinda ke damunsa
Rai bace ya ce"ba dai zaka fada min munafukin dake min zagon kasa a cikin gida ba ko? In sha Allah a yau sai na gane ko waye, kuma da hannuna zan harbe shi da bindigata domin barinsa a doron kasama hadari ne, yana iya daukan rai ba tare da jin kunya ko tsoron Allah ba! Yarinyar nan da ya hada baki da ita ya dauke wayarta da ta bari a dakinta, bai san cewa ya fada a rami ne da kansa ba, na saka cctv tun ranar da mukai maganar nan da kai, kuma a yanzu yanzu zan ga ko waye in sha Allah a yau ba zai kwana lafiya ba"
Da ido yake kallonsa har ya dasa aya kafin ya ce" Aman Dad, yanzu ka gama cewa matarka bincike bashi da dadi, natacen bincike kan haifar da mumunan amsa mai firgitarwa, shin ba zaka yi hakuri har lokacin da na daukar ma mai aikatar ya cika ba?"
A hankali Chief of army ya ce" Yaya zaka min kamawa da abinda yake damuna ne Son?"
A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Dad, a Yanzu zan iya cewa hankalina ya kwonta sosai, da Mama ta ji maganar nan hankakina ya kwonta father, dana shi ya fi damuna fiye da komai fa, tunda har ta ji, ta kuma dauki abun da sauki, sauran du mai sauki ne In sha Allah"
A hankali ya ce" Kana nufin ta hakura da rigimar ne?"
Dan murmushi ya yi dan sarai ya san rikicewar Aban nasa harda fushin mamansa ya karra rura shi, hakan ya sa ya ce" Harma ta kwonta barci Aba"
Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yana sada kansa hadi da girgiza kan nasa
A sanyaye ya ce" Idan mai neman ranka ya fito daga cikin gidana, ban san in har zan iya yi masa hukunci bisa tsarin yadda hukuncinsa zai kama, ina tsoron ko wanene na fara halaka shi da hannuna Son"
Hannayensa ya dan rungume yana kallonsa ya ce" Shima zamu yi masa uzuri ne Abanah, domin ta yiwu nine na ja har ya yi min irin tsanar nan, koma babu abinda na yi masa dole zamu yi masa uzuri in sha Allah"
Chief of army dai sauraronsa yake yi har ya gama sannan ya girgiza kansa ya ce" Yaya matsayin auren yarinyar nan dake kanka? Wannan karron nine ba zan iya yarda ka zauna da macen dake iya yarda ta hada kai da wani dan a kasheka ba, bata da huja koda kuwa yankan namanta kake yi kulun!"
MUHAY ya ce" Dad, na saketa a ranar da na sake bata dama dan na ga ko zata iya jurewa ta ki sake waiwayarsu? Sai dai da kanta ta waiwayesu harma ta amshi maganin ta zuba min a abinci, sani ne basu yi ba gaba dayansu, a tunaninsu motsina suka sani idan na fito waje, basu san cewa ni wanda suke tare da shi ne a tafin hannuna Dad............basu fa da hanyar kubuta bayin Allahn nan, baban abinda ya batan rai har na nufo gida dakin yarinyar cen suka saka camera, kennan har mutuncin iyalina zasu fara shiga? Wannan shine na kasa jurewa Father......... i can't!"
CHIEF OF ARMY ya tsatsareshi da ido sosai yana kallonsa, kafin ya sauke dan murmushi yana dafa gefen kafadarsa ya ce" Alhmdulilah " Daga haka ya yi gaba ya barshi yana tunanin dariyar kuwa ko ta mecece dad dinsa ya yi?
Tun daga wannan rana abubuwa suka cenza sosai a cikin gidan Chief of army
A bayane tsoron masu harin rayuwarsa ke sake bayana daga bakin ranar da suka yarda cewar ya fa san da zamansu, uwa uba hakan ya hadasa rashin yarda mai tsanani a tsakaninsu da makusantansu da suka san da shirinsu a kansa, wannan dalili ya sa da zarar an san ya shigo cikin gidan kowa yake kama kansa, tamkar kowa ne ke labewa, uwa uba matarsa da kanta ta tatara yanata yanata ta bar gidan da kafafuwanta, wadda sai da ta jima gidan yayar mahaifinta kusan kwana biyu sannan iyayenta suka san abinda ake ciki harma suka nemi da sannin dalili? A nan ne Chief of army ya mike da kansa ya same su ya kuma yi masu bayanin da ya girgiza tunaninsu, sunne iyaye na farko da ya rabu da yarsu harma suka san dalilin rabuwar Tabas sun yi takaici da mamaki n yarinyar da suka haifa suka ba tarbiya, ta kuma fara fuskantar izni a wajensu domin su suka haifeta , ko me ta aikata dole sunne dolenta, Allahma ya sa alkalamin KADARArTA bai karasa goga nata bakin penti ba, da ta kashe mutun kamar wannan da ina zasu shiga suma da suke iyayenta a kasar nan bale ita? A haka dinma sun godewa Allah, adu'arsu bata fadi kasa ba, jarabawarta ta zo da sauki, Allah ya bata wani mijin malamuncinta.........
A bangaren Mama da y'ayanta zama suke yi na zumunci, zama na sannin ciwon dan uwa, zama na kula da rayuwar dan uwa A kwana takwas din nan da suka shige bayan kwonciya asibitin iyayensu likita ya nemi da su rage zaman asibitin, danma sunne sun kasance a tare da wanda ya isa a wajen, ama duda ya haka ya nuna masu su bashi dama ya yi aikinsa yadda ya dace, wannan dalilin ya saka Oga kwata kwatan ya dauki decision din bama zasu kuma zuwa kai tsayen nan ba su yi ta zama kamar ba gobe, ya yanke hukuncin gabanan tafiya ta kwana bibiyu ce sannan idan an yita za'a shiga ne a ga jikinsu a koma gida
Sosai hakan bai masu dadi ba, harma sun nuna da bukatuwar a dawo da iyayen nasu a kusa da su mana? Sai dai shirun da ya bi a kan maganarsu ya fahimtar da su cewar bai wani yarda ba, a dole suka kama kansu suka yi biyaya wa maganar
Mama, tunda abin nan ya faru bata kuma daga waya ta yi kiran Useina ba, domin ko a da itace ke kiranta, idan ka ga Useina ta yi kiranta to fa zata kawo mata korafin cewa MUHAY baya zuwa ya gaisheta, baya kiranta ne da sauransu, wani sa'in har sai ta yi dan murmushi a ranta tana ayana ko me yasa ita nata y'ayan itama basa zumunci da ita?, Sai dai ta kore tunanin ta fatatakeshi kan zumuncinsa da mamansa, ashe abin mai boyayan al'amari ne, to fa daga yanzun sai ta ajiye kiran nata ta kuma zuba mata ido har zuwa lokacin da zata waiwayeta da wata maganar , a nan zata bata amsa daidai da maganar da ta zo da ita ta hanyar fara kawo gyara a cikin lamuranta