Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 52
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 52: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 52. Bakinsa ya so budewa dan ya yi kiran sunnanta da kowani irin yare…
3,358 words
Bakinsa ya so budewa dan ya yi kiran sunnanta da kowani irin yare Allah ya sa ya samu hakan, sai dai sunnan nata ya ki fitowa saima ya samu kansa da nauyin baki kamar yadda mararsa tai masa nauyi Hannayensa ya saka bibiyu ya dafe gaban goshinsa sanann yaa dauke wuta Ya jima a haka kafin ya sake dago jajayen idannuwansa ya zubawa kofar ido a cen kasan zuciyarsa yana mai tambayar kansa tambayoyi kamar haka' Me hakan yake nufi? Ko fitsari take ji? Aman da fitsarin take ji ai da ta fito zuwa yanzu ko? Kuma fitsarin a kicin..........' Ya sake tsatsare kofar da kallo ya sake ayanna' Shin guduna ne ta yi? Aman a kan wani dalili ? Ban kai matsayin yi da ita take nufi ba ko me?, .....' gaba daya bayan yannayin da yake ciki sai ya ji kansa na neman tarwatse masa, hakan ya sa ya shiga dadafawa da kyar ya iya mikewa da duku duku ya nufi dakinsa wajen da maganinsa yake ya duba ya ciro har kwaya hudu ya aha maimakun biyun da yake sha ya kora da ruwa mai sanyi sannan ya baje saman kafet din dakin barcinsa yana damke da mararsa yana ta zufar wahala har ya samu ya tafi a duniyar barci mai matukar wahala
Da kyar ta iya lalabawa ta fito ta dauki rigarta da hijab dinta ta zurmuka sannan ta fice a bangaren nasa ta nufi wajen adarta
Tana zuwa ta tarda ita kwonce tana waya da Malan dinta hankali kwonce Fadawa ta yi jikinta ta rukunkumeta still jikinta na rawa sosai tana ta son saka kanta a kirjinta ta labe
A tsorace ta ringa kallonta tana neman zama da son ajiye wayar gefe tana fadin" Shuwwa? Shuwwa ke Lafiya ?"
SHUWWA ta sake komawa jikinta ta labe tana ta sauke ajiyar zuciya hadi da kallon bayanta dan du a tsorace take Hankalin Nahidht ne ya fara tashi da gasken gaske, dama iyayen du basa nan matar Dad an yi asibiti da ita da yarenta dake koke koke sai sune a gidan, sai ta fara jin tsoron ko wani ne ya biyota haka? Ko kuma wani abu ne ya samu mijinta A rikice ta sake riketa tana fadin" Shuwwa wai menene? Wani ne ya biyo ki? Ko wani abun ne ya samu mijinki?"
Shuwwar ta girgiza kai a birkice tana fadin" Ba zan kara ba, na zata zan iya abinda kuke fadi ashe ba zan iya ba, wayo Allahna ni tsoronsama nake ji, kennan ya wulakantani shikenan ya sakeni? Ai gwarama sautan da suke sakina basu yi komai da ni ba!"
Fahimtar inda maganar ta dosa ya saka Nahidt rungumeta a jikinta a sanyaye ta ce" Hey babyn auntynta, wanu irin kar ya taba ki?, Haba autan mama mijinki ne fa , kece fa mai kokari mai jajircewa"
Tana girgiza kanta ta zauna tana kallonta ta ce" Wani irin jajircewa gareni a gabansa?, Burina na faranta masa, ban sani ba ko bani da sa'ar a soni domin Allah ne?, Tubeni fa ya yi yake neman amsar abinda na dade ina rikewa nawa da nufin ya kwace m......" Rufe mata baki da ta yi tana girgiza mata kai ya sakata yin shiru tana jin yadda zuciyarta ke dokawa da karfi sannan ta sake kwontar da kanta a saman cinyar Nahidht dake dan shafa bayanta
Sai da NAHIDHT ta kula ta dan fara dawowa cikin hayacinta kafin a sanyaye ta ce" Sirrinki ne fa, ibtin Aba sirrinki ne wannan, duk matar dake bayana sirrinta da mijinta lalle ta yi asara koda kuwa Allah ba zai hukuntata ba, balatana haramun ne, sannan yaya kike so ne?, Me kike so ne?, Ai yama yi kokari da yake kallonki kina dauke da abinda yake malakinsa , aman bai taba nuna maki yana so ba sai yau, shine kika guje shi, haba yar albarka kin san da ba'a gudun namiji ko? Duk soyayar da yake maki idan dai ke din nan kin zamto wace bata yi masa adalci walahi zai iya hakura da ke ne domin a kan wannan lamari maza basu da hakuri fa, Na san cewa a cikin duhu kike aminiyatah, na san cewa a cikin wasi wasin so ko kiyaya kike daga wannan bawan Allahn, aman zan fada maki wani abu, wasu mazan Allah ya sa kin fi zinari kyali, kin fi gol daraja ba zaki taba ji daga bakinsu sun bude sun furta maki kalmar so ba ko wani abun, su haka Allah ya halice su, ba zaka iya cenza su ba fa, ko me zaka yi ba zaka iya cenza su ba SHUWWA, koyon zama ake yi da su da halinsu sai a ci ribar zama da su, su a aikace suke nuna kalar tasu soyayar, kece baki yarda cewa wannan bawan Allahn na sonki ba, aman mu dake tare da ke mun riga mun yarda, Shuwwa ba zaki iya tantancewa ba, aman idan kina waje idannuwansa a kanki, haka kuma idan ya fuskanci wani na iya kallonki koda yayanmu ne baya iya boyewa, da idannuwansa da kuma motsinsa yake yakin dukkan wani abun da zai rabe ki, aman sai na ga ke sam bakya duba da haka........... Wani irin cutarwa kuma kike magana a kai? Ni fa ina gannin girmansa da kimarsa koda duk duniya zata ki shi, domin shine silar samun farin cikinmu da muka rasa.....shin ke bakya gannin hakan ne kanwatah?"
Shuwwa da idannuwanta ke lumshe tana biye da dukkan bayananyar uwarta ta dan dago ta ce" Nahidht so kike ki ce min shi a haka zan rayu da shi tamkar dutse? Bayan ni burina na rayu da namiji mai min kukan yana sona? Ya ringa min ihun yana so na?,ya zamana tamkar jelata sai abinda na ce ya yi zai yi? Ya nunan so a gaban kowama ya kareni da dukan karfinsa ya shagwabani? Yaya zan iya rayuwa da mutun mai halayarsa?"
Nahidht ta dan zarro ido da mamaki ta ce" Ki ce kawai rayuwar mafarki kike so ko kuma nace rayuwar karya?"
Shuwwa ta ce" Kina nufin babu soyaya a gidan aure? Ko bashi da zuciya ne shi a jikinsa?"
Nahidt ta yi Murmushi tana girgiza kanta ta ce" Babu soyaya ake zaune? In babu soyaya an saka maku wuka a kawunanku ne?, Dukan gidan dake dauke da mace da mijinta da y'ayansu koda tana zaune da shine domin y'ayanta to fa idan aka bincika akoy soyayarma, halaya ne na yau da gobe ke disasheta, da ace zasu kamanta dawo da kyautatawa da zata dawo , Shuwwa da kin fada ya yi uwarsa ce ke?, Ko kuma da kike so ya zamto tamkar jelarki kece mijin ba?, Kin ga ibada ne aure, zama ne na ibada, dukan ibada kuma sai da juriya da hakuri koda za'a kai ga ci, ki sani rayuwa baban nasarar da kika yi a yanzun amsa sunnan matar aure, zaki idasa ga ci ne idan kika yi hakuri kika ci gaba da zama da shi, Allah na tuba rayuwa ai zo mi zauna zo mu saba ne Shuwwa, zaman da yake kulun cikin dariya da farin ciki ina tsoronsa, ai zama dole akoy sabani wani sa'in, aman kuma ana ganewa ana hakuri da junna shine daidai, kin ga ina so ki fahimci wanene mijinki sannan ki masa adalci a zamantakewarku, kar ki yi wasa da damarki, kar ki yi sakaci da aljarki Shuwwa, ba zan so ki kasance mai yiwa mijinki rikon sakainar kashi ba, idan kuwa yana zuwa kina kauce masa babu abinda ba zai faru ba ciki harda daina gannin girmanki da karo wasunki da zasu tarbe shi da zarar ya buda hannayensa., Ba'a barin namiji da yinwa Shuwwa, ba'a yi........"
Fuskarta ta shagwabe sosai tana langwabe kanta ta ce" Ni tsoro nake ji ne Nahidt, walahi tsoronsa nake, kuma yanzunma cewa ya yi yana jin yinwa da ishirwa kin ga baima ci abincin ba inaga ya kwonta barci"
Nahidt ta sake kureta da kallo kafin ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" Mace bata kadan, komai girman namiji kuwa baya fin karfinta Shuwwa, rijiya ce mai daukan guga, haka kuma babu wanda ya girma da dadi koda girman bariki ne, sannan ki kokarta ki koma ki gani ko zai yarda ya ci abincin yanzu kin ji? In bandama abinki mutumen da kece shedar yawun yan bariki a kansa ne kike son yin wasa a lamarinsa?, Koda yake baki san menene kalmar nan ba, bana so ki santa ta tsiya kanwata, bana so ki san sharin yar bariki, domin wata yar barikin komai taurin kan namiji sai ki ga ta shawo kansa cikin sauki bale naki mijin da yake da bukatar hakan? Wai har kin manta niyarki a kan kudurin mamansa a kansa?"
Ido ta lumshe tana sauke ajiyar zuciya tana ta auna magangannun Nahidt din, har aka fara kiraye kirayen sallar magariba Nahidht ta mike tana fadin" Abanki fa gobe zai juya dan ya sanar masu wai da wata magana, ban san ta mecece ba da ba zasu iya bara min shi ya karra kwana biyu a nan ba ni kam"
Ita dai da ido ta rakata har ta shige bayi kafin ta sake gyara zamanta tanaa jiranta
Tana fitowa a bayin itama ta shiga ta kwabe suturarta ta shiga tsaftace jikinta kafin ta dauro alwallah Sai da ta cenza kayanta ta yi sallah sannan ta mike ta koma bangaren nasa da wani hijab din ba wanda ta cire aa jikinta ba
Tana shigowa ya yi daidai da dawowarsa kennan daga masalaci da carbinsa a hannunsa na hagu yana ja a hankali, a hannun damar kuwa waya ce yake ta gwada kiran Dad dan ya ga basu dawo ba, ya yi ta gwada kiran wayar mamansa bata shiga, gashi harda sultan a yan rakiyar bayan yanzu yaronsa ke fada masa tarkonsu fa yana daf da kama kurciya domin wanda aka danama ya. Haukace a kan neman su a cikin garin dan anma buga hotunnan an yadda da sunnan ana nemansu za'a fara kilace mahaukata ana basu kula.....to dai ya yi saken da aka gano sunnansa ne a jikin jaridar dake yada labarun
A lokacin da Dad ya daga wayar muryarsa a matukar sanyaye ya yi sakama kafin ya dan saurara yana jin amsar Dad din sannan ya ce💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 6️⃣0️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
A lokacin da Dad ya daga kiran muryarsa a matukar sanyaye ya yi magana sannan ya saurara yana jin abinda Dad din ke fada kafin ya ce" Ina fata jikin da sauki Aba?"
Dad ya sauke wata irin ajiyar zuciya yana fadin" Ban san yaya zan kwatanta maka abinda yake faruwa ba, an yi faduwa daidai da rashin lafiyarta, wai tana fama da zazafar zazabin nan mai saka surutu, ka ga dai yanzu likita ya jona mata magani jikinta ne ya dauki wani irin zafi sosai Son, na rasa gane menene rashin lafiyar nan kuma......."
Zai yi magana ya ringa jiyo salalamin mutanen dake zagaye da matar Father, sannan ya ringa jin hatsaniya irin sosai din nan, kai harma da furuci kamar haka"Hajia me kike yi haka kar ki cire suturarki mana hajia Innalilahi wa inna ilaihi raj'une menene wannan?"
Da sauri ya kalli wayar domin ba'a yanke kiran ba saima muryar Fathern da ya ji yana fadin" Menene wannan kamar kamun aljannu?, Ke? Ke? Hajia meye wannan kuma?"
Hakan ya sa da dan sauri ya sake kafe fuskarta da kallo yana datse kiran da tunanin abinda ya dace ya yi , ga barcinsa ba wai barinsa ya yi domin maganin yana saka barci sosai, ko yanzu da kyar ya iya mikewa sallar nan
Juyawa ya yi da nufin tafia, sai dai muryarta ta dakatar da shi a lokacin da ta hadasa masa da bugawar zuciya da ta furta" Ina zaka je kuma? Ya ja yaa tsaya yana rike da labulen kofar fitar sannan ya juyo yana kallonta hakan ya sa ta dan daburce kadan tana sosa gaban goshinta ta ce" Gani na yi dare ya yi fa, kuma baka cikin shirin fita aikin dare ko?"
Har ta dire maganar lebenta yake kallo da tuna moment dinsa na dazu da ita A hankali ya saki kofar ya nufota, hakan ya saka gabanta faduwa, sai dai bata gudu ba ta dake tana kuma kallon fuskarsa Yana zuwa ya tsaya yana kallon fuskarta ya ce" Kar na fita ne?"
Dan tsuru ta yi tana tambayar kanta tambayar tasa kamar wace take son gane yaren, sai kuma ta dan gumtse bakinta ta bude ta ce" Gani na yi baka ci abincin da kuma ruwan ba gayacen a rufe yadda na barshi"
Wajen abincin ya kai dubansa wanda sai yanzuma shi ya kula da shi har ga Allah, to in ba ita ba ai wata yinwar ta kori wata gaskiya Bakinsa ya tabr ya juya yana fadin" Cinye abinki na koshi!"
Da ido ta raka shi har ya bacewa ganninta kafin ta sake sauke ajiyar zuciya tana shafa dogon karan hancinta hadi da lumshe idannuwanta ta nufi dakin barcinsa dan gyara masa bed dinsa da tatare gajeran wandonsa dan ta tabata ba zai taba shiryuwa da yarda gajeran wando ba a inda ya cire shi!
______________________________________
Da Mugun sauri ya idasa shiga wajen da likitar sojan ta kawo shi ta nuna masa cewar matar Dad na ciki da likitoci a tare da ita da su Dad din
Hankalinsa tashe ya shiga yana kallon yadda likitan nan ke magana su Dad gaba daya hankalinsu a kansa ga kuma gefe daya likitoci mata biyu da su Mama na ririke da ita tana ta fuzga tana dumumuwa mararsa dadin sauraro masu kamanceceniya da tonon silili da bugun kirji da fitsarar harshe da komai , sannan sai ihun a barta mutuwa zata yi ta yi gunduwa gunduwa take yi, abu shi ba na mai iska ba, shi ba na mai fitar rai ba, shi ba na mahaukaci ba, abu dai abun mamaki da tsoro , abun rikita zuciya tashi daya abun haukata bawa
Likitan ya sake fadin" CHIEF, abinda ke hadasa irin wannan crise din ba komai bane sai rashin lafiya fa muke kira da NERO PALU, shi Nero palu zan iya kwatanta maka shi a matsayin muguwar masasara, watau zazabin dake kama jiki ya cinye karfin jiki har ya haye ya nemi taba kwakwaluwa, tabas wannan zazabi yana da hadari sosai domin bama fatan rashin lafiya ta yiwa mutun yawa har ta kaishi da haka, wannam zazabin idan ya rike mutun mukan hada dukan kokarinmu bayan mun fara rike Allah, domin yana saka mutun ya yi har fiye da haka, ciki harda dabi'u irin na mahaukaci, tube suturar jiki, zage zage, kokowa, neman fita da gudu, sakin kashi a jiki, yakushi ne, dukka ne, magangannu ne masu muni sosai, domin akan shafe dukan wani hankaki na bawa ne a zuba masa rashin hankalin, daidaiku ke yin irin rashin lafiyar nan a cikin hali na summa, dayawansu kuwa idan suka tafi duniyar summan basa dawowa shikenan, wannan zazabi yana da hadarin gaske domin wasun idan suka dawo hayacinsu kwakwaluwarsu na tabuwa, wasu zasu jima sunna yin jinya, wasun kuma sai ka ga Allah ya taimaka sun tashi garas abinsu............ Ba maganar aljannu bane wannan kar ku ce zaku tafi da ita , ku yi hakuri mu daureta haka dan kar ta lahanta jikinta sannan ta lahanta na kusa da ita, in sha Allah zamu bi crise din nan sau da kafa har ta dakatar sai mu saka mata magungunnan fa zasu karra talafa mata wajen sake dawowa hayacinta da samun lafiyar zazabin"
Gaba daya abin wani iri ya zo masu duba da su basu karanta ba, bayan hakan take, Nero palu gaskiya ne, ba cutar iskokai bane cuta ce da zafin zazabi ke hadasa shi har ya haye ya taba kwakwaluwa, daga nan sai abinda Allah ya yi, wasun daga nan ake kwasarsu a kaisu gidan mai rukiya, kana ja da karfi kana kokowa da zazabin da kake fama da shi, malamin na daneka yana tofa maka abubuwan alkhairi yana so ya kwontar da iskokan, wani sa'in akan yi dace Allah ya yiwa abin tsawa, wani sa'in kuma dacen kan hadewa da ALK'ALAMIN kadararka wanda ya riga ya zanna tun kafin a haliceka cewa ta wannan dalili zaka dawo mahaukaci ko ka rasa rayuwarka, ko kuma ka ga baban tashin hankalin da baka taba tunanin akoyshi a cikin duniya ba......kadan daga aikin zafin zazabin nan, baban matsalarsa shine yawanci idan hankalinka ya dauke din nan dukkan wani abu na sirrin ratuwarka ke dagowa ya bayana da bakinka, alkhairi ne ko shari ne, ko menene da bakinka ne zaka fadi cewa ni da nake yin kaza da kaza? ......... Ku tambayi likitoci zasu baku bayani dala dala cewar tabas haka ne kuma hakan ke faruwa Da wannan lamari aka taki rashin sa'a ya fado a kanta, a daidai wannan gaba, a irin wannan babar rana da mijinta ya wayi gari ya sauke dukkan wani nauyi da yake ji ya masa girma a saman kansa, sai ga matsala ta rashin lafiya ta fado, ta kuma zo da karfi, cikin kudurar ubangiji irin wannan,
Da karfi suka kakamata bayan an gyara mata hijabinta Allah ya taimaketa da masu rufe mata suturarta a kusa, suka samu suka daureta a jikin gadon da take kwonce, irin daurin da ba zata iya jima kanta rauni ko ta daki wanda ke gefenta ba, karfi ne tamkar na aljannu ke jan mutun, domin kana iya watsar da mutanen dake gefenka idan abin ya motsa, yana yi ne kuma yana kwociya "Walahi walahi sai na kashe MUHYIDEEN da hannuna, sai na kashe shi , yadda yaron nan da uwarsa suka shigo min rayuwar gidana da mijina ina mulkina son raina aman suka zo suka fi karfina ya zamto mijina ya samu yaron nan a matsayin dan da yake fatan samu namiji aman bai samu ba, shine komai nawa da na y'ayana ya dawo hannunsa harta da shawarar abinda ya shafemu sai ya nema a wajensa uwarsa ta ciri ta kullu tabi bokaye ta shanye mini mijina sai yarda ta yi da shi ita karuwar algunguma mai........" Da sauri ta karasa wajen ya dora hannunsa na hagu a saman bakinta ya damke da mugun karfin da ya sa ta hade da fatar tafin hannun nasa ta gala wani wawan cizon da ya ratsa dukan gaban jikinsa dan azabar zafi harma ya fara ji zufa na neman karyo masa, aman ya danne ya sake dora dayan ya danne bakin nata sosai yana rintse idannuwansa wani irin tsoron Allah na shiga dukkan sasan jikinsa da tsoron haduwa da shi a gobe kiyama da wani laifin, sannan ya sake yarda cewa ko me bawa yake yi a duniya dama Allah ke ara masa , kalilan ke samun dama irin wannan wace zasu bayana kafin su koma ga mahalicinsu, in ka yafe masu to, in baka yafe bama to, dama damarsu basu je a makance ba, watau sunna aikata aikinsu a boye da mugun nufinsu a zukatansu ba