Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 53

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 53

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 53: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 53. Kallon da Dad ke yi masa, da Mahaifiyarsa ke yi masa, da kuma matar…

2,843 words

Kallon da Dad ke yi masa, da Mahaifiyarsa ke yi masa, da kuma matar mahaifinsa ke yi masa, a gangaro kan sarakuwarsa dake tare da su, da sirikinsa dake gefe yana tofa mata adu'a a bayan an sake suturtata da hijabinta ya shigo shima yana tofa mata adu'a da nema mata sauki a wajen Allah, gaba daya suka zuba masa ido kowane da yannayi na firgicin furucin bakinta da kuma irin yadda ya damke bakin ya rike kam ya kuma hannata karasa furucinta, aman kuma a yadda take kokowar sai ua saketa zaka tabata da zarar ya saki bakin nan komai na iya faruwa ya saka shi sake gyara tsayuwarsa yana sake damkar bakin nata da hannunsa yana rintse idannuwansa ya ce" Kun san zafin ciwon nan babu abinda baya hadasawa, ciki harda dumumuwa kamar yadda likita ya sheda mana yanzu, dan haka nake so dan Allah ku fita ku dukanku waje har ta samu lafiya"

Dad kallonsa yake yi jikinsa na neman fara bari Muryarsa na rawa ya ce" Mu fita waje ko ka saki bakinta?, MUHYIDEEN MUHAY, sake min bakinta now!"

MUHYIDEEN ya sada kansa yana girgiza kansa a sanyaye ya ce" Ka yi hakuri Dad, ba zan iya sakin bakinta ba"

Mahaifiyarsa da ta yi baya baya a hankali ta rike garun dakin ta sake zuba masa ido, sannan ta zubawa matar nan dake kwonce ido, kafin ta lumshe idannuwanta hawayen da take ta sharewa na tausayinta tun dazun wasu suka sake zubo mata masu daci sosai sai kuma ta rike hannun Tinana da ta sake rike hannunta a hankali ta shiga bin bayanta suka fice a dakin kwata kwata suka fice a wajen har suka hade da y'ayanta mata da suka yi zuru zuru an hanna su shiga wajen , Suka wuce su ba tare da sun iya kula tambayoyinsu a kan jikin mahaifiyarsu ba, ya rage sauran mace daya da kuma su Dad, wace itama ta sauke ajiyar zuciya ta girgiza kanta ta juya ta wuce a dakin tana tunanin tabas son zuciya da rashin godiyar Allah sun kai matar nan sun barota , hakan ya rage daga Dad sai Sultan, sai Muhyideen da ya ki sakin bakin nata

Da karfi Dad ya shamace shi ya warce hannunsa a saman bakinta, kamar jira take ta dora da fadin" Ke kuma Salma yadda na haife ki da cikina aman kike juya min baya a kan kudirina da shirina na son kashe dan iskan yaron nan ba damuwa, ai gari da yawa maye ba zai ci kansa ba, da kudina a jakata na tabata zan janyo da yawa da zasu kama min, sai na ga an fita da gawarsa a makara a wulakance zan samu nutsuwar zuciyata, mijina na ni kadai ne sai ko y'ayana, du wanda ya ratso duniyata da mijina sai ya shiga uku wannan alkawarina ne!, Sannan da mijinki ke maganar karra aure ki sani ba zan taba bari a maki kishiya ba, yar iska mai zuciyar mahaukata da baki san ciwon kanki ba bale na uwarki! Ana wulakantani kina nanuke da su ke ga ta kirki ko? In dai mutun ne mugun ice ne,, su ji suke tamkar ki mutu su karra yawon kudin gadon ubanki a kanki............., Ita kuma uwar Uma itama sai na................"

Bakin ya sake damkewa bayan ya bi Father da kallon tausayi yana girgiza kansa ya waiga gannin Aban Shuwwa na kokarin barin dakin a birkice ya ce" Sultan " Wani irin birki mahaifin Shuwwa ya ja ya juyo da sauri yana kallon bayan MUHYIDEEN

MUHYIDEEN ya sake tausasa kalamansa ya furta" Aikinka ne hanna yaduwar fitina ko wace iri ce Abah, ka taimaka ka shiga a matsayin da Allah ya nadaka a kai ba wani dan adam ba, kana da ruwa da tsaki a ciki a matsayinka da Allah ne ya baka, ka dube mu ka kama Abahna, ka kwatanta masa cewar wannan din ba komai bane ba, karma ya daga hankalinsa a irin wannan, Allah ne ya kadara masa haka , wannan al'amari a rubuce yake tun kafin a halicemu, Dan Allah kar ya rikita lafiyarsa ko ya saka a ransa ta yadda zan rasa wani uban a karro na biyu, ya sani wannan din sirrinmu ne na cikin gidanmu, dama ba lale kowa ya zama yadda ake so ba, fatana wannan din shine na karshe a wajenta, Abah ka fada masa bani da karfin fuskantar wani hargitsin bayan wanda na bari a dakina da kuma wanda na tarar din nan a irin wannan lokacin, Aba bani da karfin iya jure haka a irin wannan lokacin Abah....... ba zan iya ba Abah....................." Ya karashe a matukar raunane yana sake kallon yadda take dago kirjinta da karfi tana mayarwa a jigace haka kuma so take ya sakar mata bakin ta idasa tonawa kanta dukan asirin dake ajiye saman zuciyarta wanda ya hadasa mata nauyin zuciya sosai ya hanna mata sukuni take kwana take tashi da shi ( Astgfrullah wa atubu ilaiki )

A hankali ya karra sada kansa yana ta tofa mata adu'a, tun tana yi karfi da yaji har muryarta ta disashe ta dawo yi a hankali , kafin ta yi shiru idannuwanta rintse, watau barci ya yi awon gaba da ita Sai da ta yi barcin nan ne sannan likitocin suka shigo aka shiga jona mata magungunnan du da suka dace da ita domin dama sai abin ya lafa ake jonawar

Ya jima zaune yana kallonta da tunanin yanzun da mahaifiyarsa ce, ko shi kansa ne haka ta faru da shi da yaya zai yi da ransa?, Tabas yana bukatar uzuri haka zai so a yiwa mahaifiyarsa uzuri, zai so koda a kan son zuciya haka ta same shi a yafe masa, shi yasa tunda ya fuskanta ya kuma gane cewar itace ya watsar da dukan kudirinsa na son sai ya yi fito na fito da ita, sannan ya yi ta rokon Allah kar Allah ya bata damar idasa saka rayuwarta a uku ta hanyar samun rayuwarsa, ya yi ta faman nema mata sasauci a wajen ubangijinta, babanma abinda ya bata masa rai shine saka camera a cikin dakin iyalinsa wanda ya gano hakam ya faru ne da hadin baki da taimakon biyu daga cikin yarensa dake gyara masa gida kafin aljanarsa ta dakatar da su suka saka camerar, na bangarensa kuwa lokacin da aka saka masa yana sane, ya dai lalata abin ne ba tare da sun ankara ba, sannan ya yi anfani da damarsu dan ya tantance wace mace ce zata iya zama da shi ba tare da ta nemi rayuwarsa ba komai mugun halin da zai nuna mata a gareta?, A haka suka ringa cin galaba a kan matan da ya ringa jerawa suka mayar da shi tamkar wani dan tasha yau ya dauka gobe ya saki da ita da muryar y'arta wace daga baya ya gane cewar ai itace dayar muryar dake yiwa matan da zai aura barazanar kashe su a kansa, har suka fado kan Aljanarsa da yayunta mahaukata suka rawaito masu ashariya daki daki, daga nan sai suka barta suke bibiyarta da son samun hoton tsiraicinta dan su yi mata anfani da shi, shi yasa ya faukota ya dawo da ita nan domin haka kawai yake ji a cen kasan zuciyarsa idan suka ga tsiraicinta ya wulakanta ba zai iya dauka ba

A hankali ya mike bayan ta shiga barci ya fita a dakin Ya zo ficewa ya hade da y'artata mai dafe mata baya Bai yi wata wata ba ya damketa ya dawo da ita dakin da dayar dake biye da su tana zarro ido a tsorace Da garun dake dakin ya makata ta hanyar hankadata har sai da ta daku da garun a tsorace ta zube kasa tana zazaro ido da kallonsa

A kausashe ya ce" Ruwanki ne ki ci gaba da wulakantar da kanki, ruwanki ne ki yi biyaya ki cenza halayanki, abinda nake so da ke shine ki sake gigin shiga hurumina, a nan ne zan baki mamaki domin ke hargagin karya kike cewar zaki kashe a kaina, ke burga kika iya a kan kowace magana, ki yi komai banda iyalina....dan ni kaina ban gama tantance abinda nake iya aikatawa a kan iyalina ba!"

Daga haka ya fice a dakin ya je wajen doctern da yake sheda masa ai an koma da iyayensa gida, Father ne ya ce su wuce gida gaba dayansu Shi dai bai iya aikata komai ba sai barin salahun su kula da marar lafiyar ya yi ya bi bayan iyayen nasa

____________________________________

Tabas Father ya gigice da jin wannan lamari, ya tsorata da duniya da abinda ke cikinta Da idannuwansa ya yi hawaye mai zafin gaske, ya birkice ya nemi zaucewa, sai dai wace aka fi cutarwa a lamarin bayan ta samu ban baki da nasiha sosai a wajen mahaifiyar Shuwwa sai ta same shi ta nuna masa cewar wannan din ba wani abun bane da ya zarce aikin shedan, ta nuna masa ita ta yafe ta kuma fodewa Allah da abin bai girmama ba, sannan SUKTAN da ya bashi dama ya yi kukansa sosai sai da ya gama ya fuskanceshi ya sanyayar da muryarsa sosai ya ringa tausarsa ta hanyar nuna masa rayuwa da abinda ke cikinta, girman kadara da ladan juriya a haka, ya nuna masa sam kar yace zai yi mumunar magana ya yi mata fatan shiryuwa, dan Adam yanzun abin tsoro ne, tabas dan Adam abin tsoro

Sunna tsaka da haka ya dawo ya same su a bangaren Aban,

Tunda ya shigo SULTAN ya sake kafe shi da ido yana tuna furucin da ya yi a dazu na kiransa da sultan da kuma nuni da ya yi cewar Allah ne ya nada masa abinda yake da hurumi a lamarin kowa, hakan ya sa yake kallonsa ko a yanzun harma ya gaishe shi bai gane ba sai da matarsa da ta cika da mamaki ta sake tabo kafarsa tana nuna masa ana gaishe shine ya ankara harma ya farka a doguwar sumar ko nace kashangar din da ya yi yana mai kallon sojan mijin y'ar tasa da kallon mamaki

Shima ya kula da irin kallon da yake yi masa, sai dia bai nuna ba ya karasa gaban Dad da mama dake zaune sunna binsa da kallo

Dad ya lumshe idannuwansa hawaye na zuba a gurbinsu ya ce" Da na san makashinka yana tare da ni , da ban yarfa an kai yanzu ana wulakantamin kai ba, da na san............"

"Aba...." muhay Ya fada a sanyaye yana katse maganarsa A hankali ya dora da fadin" Wannan din sirrin cikin gidanmu ne, da ya faru a tsakaninmu ne, kuma ba yau ba na yafe mata , sanadiyarta har na gama samun wace............a sanadiyarta har na samu abinda bana tunanin yana samuwa da gagawa a cikin duniyar nan tamu ta yanzu, dan Allah na roke ka, ka yi hakuri ka dubamu dake zagaye da kai, kar ka bari wannan ya daga maka hankali, ka hori matarka son ranka dan gobe kar ta Kuma, aman kuma ba maganar saki ko wulakantarwa domin Allah ya saka albarka a tsakaninku, Abana baka isa ka hanna abinda Allah ya hukunta min ba, inaga farin ciki ya dace ka yi da abin ya zo da sauki ko?"

Father ya lumshe idannuwansa yana jin kaunar yaron a zuciyarsa da na mahaifiyarsa A hankali ya rungume shi a jikinsa yana furta" Haka mahaifinka ya kasance mai matukar hakuri a rayuwarsa, yana iya yafe abu mafi munin da dan Adam ba zai taba tunanin ana iya hakurinsa ba.......... Son Allah ya maka albarka ya karra kiyayemin kai"

Kansa ya sada yana amsawa da kan nasa , ya kalli Mama dake murmushi ta dora hannunta saman nasa a hankali ta dan dadaba kafin ta lumshe idannuwanta tana share hawayenta itama

Murmushi ya yi bayan Dad ya sake shi yana jin zuciyarsa na samun wani gurbi na farin ciki a cikinta

A hankali ya ce" Ya dace ku shirya ku fita ku huta Dad, ya dace ku fita ku yi hutun ajiye aiki Abanah"

Dad ya ringa yar dariya yana kallonsa ya ce" Ban ki ba, aman kafin nan gaskiya sai ka tare a gidanka da iyalinka, ka ga daurin auren yayarta saura sati daya yau, ina so kafin nan ka tare a gidanka da matarka gararambar ya isheni haka"

Kansa ya sada kasa yana sake sauke ajiyar zuciya na jin abinda Dad ya fada, balema da ya ji gaba daya ana dafa maganar ta Dad wace ba yau ba yake so ya ce a yi haka din aman kuma baya fada dan kar su ce ya yi wani hali daban

Kansa a sade yana tunanin lamarin yarinyar a ransa ya ji kamilaliyar muryar Sultan dake murmushi yana kallonsa yana fadin" *TUN DAGA TAUSHE KA SAN CEWA NINE SULTAN UMAR ABDULAHI BINE MUTALAB?* "

DAM DAM DAM DARAM DADARAM, DARAM DAM🥰🥰🥰🥰🥰

Kun san halina idan kuka wankeni da commentma ana iya karowa na wknd din gaskiya, 😂😂😂😂😂 da yawa fa ba wai an tsugul ba🥺🥺🥺💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 6️⃣1️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

A Wajen Maman MUHAY da matarsa ne suka samu kansu da zuba masa ido da ayar tambaya a kansa

MUHYIDEEN ya yi dan murmushi yana sake sada kansa kasa sosai a nutse ya furta" Bincike na yi da magangannun Mama na sake yarda da hakan ne kuma da na bi tsohon tarihin dake birne"

A hankali Tinana ta sake kallon MUHAY, ta juya wajen Maman MUHAY mamakin wani abin kuma , kai gaba daya sai ta fara tunanin wannan rana wace irin rana ce haka mai dauke da abubuwan mamaki ne?, Wai ana so ace da su Wannan shine sarkin........?

Da sauri ta sake fuskantar mijinta da ya yi dan murmushi yana girgiza kansa a sanyaye ya ce" Allah mai iko........., Me ka fahimta a binciken naka ne ?"

Matarsa ta sake kafeshi da ido, aman gaba daya sai ya ki yarda su yi ido hudun da ita domin ya sani sarai in dai hakan ta faru to fa zai bude bakinsa ne ya yi ta bayani ba ji ba gani, yar budurwar tasa ta iya saka shi doguwar magana koda bai shirya ba

Dad ya sauke ajiyar zuciya yana fuskantar Aba ya ce" Allah ya taimakeka, aman baka gane ni ba ko?"

Aba ya yi murmushi yana kallonsa ya ce" Tunda na ganka a cikin hayacina nake son sannin ina na taba sannin mutun mai kama da kai? Aman abin ya shige min"

Yar dariya Aba ya yi ya ce" Dole ya shige maka, ga yannayin girma ya kamani, ga cenjin yannayi, aman nine fa........................" Nan Dad ya bashi sani, ai kam ya sha mamaki matuka har ya kasa boye farin cikinsa ya juyar da kansa ya ce" Allah sarki, ka yi zama na shekara biyu zuwa uku a tare da mu kafin Aba ke shaida mana zaka tafi makarantar sojoji, na ji wahalar rabuwa da kai sosai fa, kawai dai gimbiya ce bata yarda cewar a wahalce nake da rabuwa da kai ba har take cewa wai anya ina son kani kuwa? Bayan nima burina na ga inada yan kanai a gidanmu ba wai ni daya jal uwa rai ba, du inda na motsa idannuwansu a kaina dan an ce abu daya da tsoron bari"

Yar dariya shima Dad din ya yi a sanyaye ya ce" ALLAH ya karra maka lafiya, shin me ya faru da kai ne?, Me ya faru da kai haka? Na samu kaina a cikin hali na tashin hankali da mamakin yadda du muka manta da kai da lamarinka, shin me ya faru da kai ne?"

Sai a yanzu ne ya sauke dubansa a saman fuskar matarsa Irin yadda ya karanci abinda ke cikin zuciyarta saura kiris ya saka dariyar dake cikin zuciyarsa, watau ita dai bata kama da IBTISAM dinsa aman dabi'unsu daya, tai wata kala da ita kamar wata yar 22 yrs

Readers Also Read