Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 54
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 54: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 54. A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Kamar yadda ka sani a…
3,300 words
A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Kamar yadda ka sani a zamantakewarka da mu a cikin baban gida shine ni daya Allah ya ba Mahaifina a duniya , watau sarki ABDULAHI dan MUTALAB, a sanina suma a wajen nasu iyayen y'aya hudu suka zo duniya, uku sunna uwa daya uba daya da mahaifina, dayan yana dan uwansu aman wanda suka hada uba daya da junna, a cikinsu daya ya koma ga mahalicinsa, saura kwara uku wa'inda biyu ke bima mahaifina , hakan ya sa a lokacin da mahaifinsa ya zo tsufa ya nada mahaifina a masarautar garinmu........" Sasautawa ya yi yana kallonsu ya ce" na zo a tsakankannin soyaya da soyaya ne, du inda na waiga nine dai, a bayana mahaifina ya sake aure aure ko za'a dace? Amaj cikin ikon Allah ba'a samu ba, harma aka fara tunanin anya mahaifin nan nawa yana haihuwa kuwa? A wani dare da kanninsa wanda suke uwa daya uba daya ya jefe shi da wannan maganar cewa anya kuwa ni din nan nasa ne? Hankalin kowa ya tashi domin dai lamarin da mamaki sosai ga jahili mai karamin tunani, ai kam aka fatsama yin gwaje gwaje duba da ci gaba da yake samuwa na rayuwa, aka kuma tabatar cewa ni din kwonsa ne jinninsa ne........" Ya sake fuskantarsu yana fadin" ku gane, ni ban taba gannin kiyaya daga wajen uncles dina biyu ba, hasalima rige rigen nunan soyaya ake yi a tsakaninsu , hakama matayensu da y'ayansu muna da kyakyawar fahimta a tsakaninmu, sai dai da yawancin lokuta nakan tsinci koke irin na jaje da nuni a kan wani dalili mahaifinsu ya fi son mahaifina a kansu? Sukan nuna abin bama dan yana d'ansa na farko bane, kiri kiri ya fi sonsa da su ne, sukan nuna hakan baya yi masu dadi sam, harma baban limamin masalacin masarautar ya taba yin zama da su da Sarkin garinsu watau yayansu, da mahaifansu ya yi masu nasiha mai ratsa jiki da zuciya, bayan sun bar wajen ya fuskanci iyayensu ni kuma ina zaune a saman cinyar mahaifiyar dan uwan mahaifina domin a duniya matar na shagwabani na nunan soyaya tamkar itace kakata ya yi masu nuni da tabas maganar y'ayansu gaskiya ce, a yanzu sun kai gabar tsufa ya dace tun sunna iya dajatar da abin su dakatar su kuma daidaita tsakanin, su boye soyayar yaronsu na farko a gaban sauran yayansu ko dan su sama masu zaman lafiya da jituwa a tsakaninsu, sai dai kashhhhhh , lamarin samun cenji bai samu ba, domin da tsufa ya sake kama su harma suka zamto tamkar yara ko abinci basa yarda su ci in ba shine ya basu da kansa ba, dama dama sukan yarda da uncle dina wanda suke uba daya da mahaifina wani sa'in, a haka rasuwarsu ta zo a jejere domin kuwa maman Uncle Ibrahim ta fara rasuwa, sai maman su mahaifina ta rasu, sai kuma mahaifinsu ya bi matansa............" Ya hadiyi yawu yana kallonsu ya ce" Daga nan girman da komai ya sake hawa kan Takawa, gashi mutun mai son mutane domin ba lokaci Takawa yana amsar baki, ba bambancin kai na kasarsa ne ko bako yakan karama kowa ne shi, haka Allah ya yoshi mutun mai son mutane,............"
Ya fuskancesu ya ce" Mahaifina nada cutar zuciya, wace iya mu ne muka san da wannan rashin lafiya, rashin lafiyar dake hanna mahaifiyata nutsuwar zuciya domin shi ke dauke da cutarsa aman ita ke nisa rashin lafiyarsa, har abin yai mata ilar da babu maganar waiwaye sai dai hakuri da daukan danganaa na rashinta a ranar juma'a da sanyin safiya inda ciwonsa ya tashi sosai ita kuma ta yanke jiki ta fadi, daga wannan lokacin na fara maraicin uwa,............ Sannu a hankali na saba da rashin ganninta na kuma dauki dangana domin ko a lokacin shekaruna sun kai na nema na ciyar da kaina, dan dai na tashi a gida na sarauta ne ya zamto a boye nake , a kilace nake tamkar kwai, bale da kowa ya san cewa nine zan mulki kasata, harma an rigai an min sunna SULTAN tun ban kai ko'ina ba, hakan ya sa ake kakau da ni , balema dan uwan mahaifina Uncle Ibrahim wanda bawan Allahn ke koya min dukan wasu abubuwa da ya dace ace na iya na gidan sarauta ba tare da na fuskanci komai na tsana a tare da shi ba, shi kuma uncle Khamis damaa mutun ne mai matukar iza da sarauta a jikinsa, domin bana tunanin idan har sarkin dake saman sarautar kasata a yanzu ko da matansa yana hira bale y'ayansa harma a zo kaina, shi yasa ni dinma idan da halin mu zanta muke zantawa idan kuma ba halin hakan bana takurawa........"
Ya dafe gaban goshinsa ya ce" Mahaifina ya rasu ne a sanadiyar tashin ciwonsa a daren litinin wayewar talata, wanda muka tashi da gawarsa a gabanmu ana ta yi masa shinfidar kabari........" Ya jimke hannunsa yana kallonsu ya ce" kamar yadda yake kaida haka aka bi da ni, ana dawowa daga suturar sarkina a cen cikin makabartar dake cikin gidanmu aka nadani a sarautar kasata da kannanun shekaruna ko auren fari ban yi ba, sannan aka saka ranar da za'a daura min aure da wace za'a binciko a ga ta dace da ni............." " Na rikice, na dimauce na rasa ina zan dosa na nuna tsantsar tashin hankalina a kan ranar da na wayi gari ake kirana sarki maimakun sarkin garina kuma mahaifina, wace zan je na yiwa kukan ta rigashi kaura, hakan ya sa na kwana cir a saman salaya ina kuka ina fadawa mai duniyar da kiyama cewar zabinsa nake so, karfin gwuiwa nake so daga gareshi,na sake dora kaina na yi kuka na fada masa cewar ba zan iya ba, bani da karfin hakan, aman idan hakan ne zanen rubutun ALK'ALAMIN KADARATAH ya bani ikon cinye jarabawar cikin sauki..............., Ni dai zan iya cewa daga wannan ranar sai samun kaina na yi a garin Manzo, shin ta yaya na zo? Ni na biya ko biya min aka yi?, Ni dai na samu kaina a garin da nake jin nutsuwa a jikina, ta yiwu rabon na hadu da gimbiyar da zan dora kaina a jikinta nai mata kuka ne? Ni dai zan iya cewa babu abinda ya fi daga min hankali irin maganar waye ni, ko kuma a kai ga maganar kasata, harma a san waye asalin ni din, sai kuma ta yarda, ta amince bayan ta fada min abinda ya cirota daga gidansu itama na ji kuma na amince da hakan sai mukai aure muke zaune da junna "
Ya lumshe idannuwansa ya ci gaba da fadin" Shin wanene a cikinsu?, Me yasa ya min haka? Ina cen dinma a labe ya bini ya sake dawo da ni ya rufeni a dakin duhu ya ci gaba da azabtar da ni , ya rabani da y'ayana mata biyu masu kananun shekaru, ya kuma wulakantar min da iyalina .....ya kalleni a hali na hauka , ya ki ya kasheni da wuri wuri ya ci gaba da kallona, ko duk dan Allah ya yi da sauran shan ruwana a doron kasa ne?.............ni dai gani a zaune ina tunanin ina Uncle dina Ibrahim da yake gaba da uncle din Khamis ?, , Yaya aka yi uncle Khamis yake saman karagar mulki bayan Babu wanda ya ji mutuwar IBRAHIM?, shin me yake faruwa a Baban gidanmu?"...........ya idasa yana sake kallon su Dad da Muhay da kowa ya shige a hali na rashin dadin zuciya
A sanyaye Dad ya ce" Ai uncle dinka IBRAHIM yana rufe a gidan mahaukata, zan iya cewa a kadan ya dauki shekara ashirin da bakwai a ciki, domin wayar gari aka yi yana hauka jajir, maganar da nake maka d'ansa daya kawai ke cikin gidan sarautar a yanzu , matansama sun yi wani aurensu sauran y'ayansa mata kuma du basa kasar sai dansa dayan nan , ai yanzu inaga shima ya tara iyali kam"
Sultan ya dan girgiza kansa yana ta ambaton sunnan Allah, sai kuma ya dube shi da dan sauri ya ce" Ko dai Muhsin ne d'an nasa?"
Da sauri Dad ya amsa shi cewar kwarai kuwaa Muhsin sunnansa
Sultan ya fuskanci Tinana da ta yi mutuwar zaune ya ce" An maya, kina tune da wanda ya kawo mana sutura ya bude mana hanya cewa ya yi sunnansa Muhsin? Ko dai shine?"
Tinana ta sauke gwauron numfashi tana sake kallonsa da mamakin wai dama mijinta sarki ne? Sarkinma mai daraja? Ta gyada kanta a sanyaye ta ce" Eh haka yace"
MUHAY ya ce" Koma menene in sha Allah zai fito, a gobe da sasafe zamu juya da LIEUTENANT GANARAL MUJAHEED, option ta gaba da ya gabatar mana shine za'a dauki hoton ABA da rawani sannan a babu rawani , tuni ya sayi baban kampanin jarida ya kuma gana da mai kampanin a boye ya bashi sirrin maganar, daga goben in sha Allah zasu fara yadawa , dama komai dare a yau muka yi niyar fuskantarka da maganar ,sai gashi komai ya zo da sauki in sha Allah....... Zamu fara gannin yaya al'umar kasarka sunna tune da sarkinsu da suka nada ba wanda ya nada kansa ba?, Zamu tsintsinto abubuwan da zasu gabatar na reaction sanann mu watsa a gidajen TV da redio, koma waye a karkashin wannan lamari zai fito fili.....Allah ya bamu sa'a"
Da wannan suka ci gaba da tataunawa har daren ya yi sosai kafin ya shirya cikin dakakiyar shada fara, aka dora masa rawanin da ya saka Tinana fashewa da kuka tana kallonsa, Domin gaba daya ramar ta boye a cikin suturar da ya sha, danma ramar a yanzu gaskiya sai dai ace dan abinda ba za'a rasa ba, da kyar ya iya rarashinta yana binta da kallo akai masa hotunnan yadda ya kamata suka yi kyau sosai, sanann ya cire ya kafa hula nanma aka dauka harda wajen da ya yi murmushi mai kayatarwa duka aka dauka, ana gamawa MUHAY ya masu salama bayan ya furta kalamai kamar haka" Al'umar kasar ce zata sauke shi, sannan ta nadaka, koma wanene boye a bayan lamarin zai fito da kansa ne ko zaman kasar ta gagareshi kamar yadda ya fitar da kai, in sha Allah zai gane tadawar ALK'ALAMIN Kadarra baya goguwa, idan ta zanna ba tsumi ba dabara......"
Hakan ne, a wannan rana SULTAN ya jima rike da matarsa a jikinsa bayan ya samu nutsuwar da rabonsa da irinta har ya manta, harma ya cirewa ransa cewa zai kuma moruwa ta wannan fannin, sai gashi a daren yau sun kule a daka sun kuma yiwa junna tambaya da amsa daidai gwargwado kafin su afka a duniya ta manya, ta yara, watau dai ta masoya.......zai iya cewa ko a haka aka tashi shi kam alhmdulilah😌
Bangaren Muhay kuwa sai da dare ya tsala har kusan karfe biyun dare ya dawo, a lokacin da ya shigo ya sameta ta jima da yin barci kamar jiya a saman cafet ta dukunkune jikinta a cikin hijab dinta Bayan ya gama kimtsa jikinsa ya dauko lalausan bargo ya dawo falon ya rufa mata kafin ya dora yar yatsarsa daya wajen kuncinta a hankali ya dan shafa sannan ya mike ya barta a kwonce ya shige ciki
Washe gari da ta farka ta gama shiryawa bayan ta gama gyaran falon, jin shiru shoru ya saka kawai ta shige ciki dan gannin yana ina ne? Tana shiga ta samu baya nan, aman kuma kanshin turaren dakin ya gama game dakin gaba daya
A hankali ta shiga kokarin gyaran dakin, a saman bed din ta ga takarda da rubutu a jiki Da farko kasa dauka ta yi, domin tsoron abinda rubutun ya kunsa ya kamata, sai dai gannin tana ta tsaye da kyar ta janyo hannunta na rawa rawa ta bude ta zauna tana dubawa
Rubutu ne kamar haka *Ki rufe jikinki koda dakin Mamah zaki je, ta yiwu na yi kwana biyu ko uku....... EBTISEMMMMMMMM, ki kula da kanki*
Shiru ta yi da takardar a hannunta tana tunanin kwana biyu ko uku? Ina ya je ne? Me hakan yake nufi ne?
A hankali ta zauna saman bed din tana dauke gajeran wandon da ya cire na yau, sai ta samu kanta fa lumshe idannuwanta tana jin wani abu a kasan zuciyarta ga tarin tambayoyinta na damun kwakwaluwarta
Sai dai rashin samun amsar ya sakata dunkule takardar ta yar a nan da bacin ran yaya zai dawo har ya yi tafia bai tasheta ya fada mata ba? ta fita ta yi bangaren iyayenta Tana zuwa bata samu mamanta ba, dan haka ta koma bangaren Maman MUHYIDEEN din, domin mahaifintama baya nan
A nan dinma ta tarar ana ta shagulgulan da suka dan daure mata kai Da kulawa Mama ke amsa gaisuwarta sannan ta ci gaba da yiwa mutanen dake zaune bayanu, abinda ta tsinta Maman na fadi cewar aa bata so a yi gyara na fari kadai, su fa kula fa idan gadajen da aka zuba basu yiwa MUHAY ba sun sani sarai na zai yarda ba, gaba daya a yadda ta kula ana cikin shagulgula ne na gyaran gidan CHIEF OF ARMY, dan haka ta silale ta yi bangaren da take jiyo maganar su Nahidht
Tana shiga Fauzy ta ce" Shuwwa, wai dan Allah da color golding da ash color wanne ya fi birge ki?"
Shuwwa ta dan yi tsam ta ce" Ya danganta, idan kamar a sutura ne haka kawai nake son saka color ash color, wasu kalolin kayan jikin Ash color ai sun hadu ne, aman kamar idan harkar cikin gida ne na fi son Golding, domin kalar ta fi jan ra'ayin mutun sosai da sosai, ash color na saurin sakawa ka tsani kwaliyar waje, ko kuma fari, fari kuwa yana sakani gajiya sosai"
Nahidt ta dago daga suyar kifin da take ta ce" Kan balaki, ni zaki saka na ji kunya? Gaskiya baki kyauta min ba Ibti, na dage nake cewa Ash color ta fi birgeki Fauzy ta ce min wai lalle idaj kuwa haka ne ta wannan fannin ban gama karantarki ba, ashe haka din ne"
IBTISAM ta dan tabe bakinta ta duka tana fadin" Na dandana? Wollah yawuna sai tsinkewa yake yi, yadda kika shafa masa jajagen percil din nan na san dandanon sai an tsinke harshe, sai dai ni ba zan taya ku aiki ba gaskiya, ke Fauzy wai me ake yi a falo?"
Nahidt ta yi murmushi ta ce" ki huta a gefe, domin Mama ta tafi da kanta yau kasuwar turaruka zata hado maki aikinki, na tabata sai kin yi juwa dan gajiya in sha Allahu, kuma gyaran gidanku ne ake yi, ni baban takaicina da ba zan yi casu ba, aman ba komai ai in sha Allahu idan bikina ya tashi da Malan dole ne mu kwaso shokiiii"
Fauzy ta dantse lebenta tana kyakyata dariya tana hanna kanta fada mata cewar a yau fa daurin aurenta bai fi saura kwana shida ba, itama Hamza ne ya fada mata ya kuma ce kar ta fada mata domin su Mama basu sanar mata ba tukunnan
A wannan ranar aka fara gyaran gidan SHUWWA, aman sai a washe gari aka gama shi domin gyra ne aka yi na mamaki , kaya ne aka zuba na yar gata
A ranar kwanan na uku biyun suka tashi da daurin kunshin da ta kwana da shi, a ranar ne kuma akai mata Alawa, aka kuma sake yi mata gyaran gashi, sannan ta wuni tana fama da shaye shayen abubuwan da iyayen ke bata, ga kuma yawan hawa saman turaren wuta da sauransu har sai da ta ji ta gaji sosai, aman kuma bata isa ta kusa ba
Zuwa yamma kunshin kafarta da na hannunta ya hudo sosai ya yi maroon sai dauakn ido yake , ya yi kyau sosai kamar ka dauke ka maido shi hannunka, ita da kanta a lokacin sai ya zamto takan yawan jin sha'awar kallon kunshin Dare na yi kusan karfe takwas Maman Muhay da Mama sukai kiransu gaba dayansu watau ita da Nahidt
Nasiha ce sukai masu mai ratsa zuciya, har sai da suka fara tsarguwa da tsorata da nasihar domin idan Mama ta yi ta gama, sai maman Muhay ta dauka, gaba daya nasihar kuma a kan zamatakewar gidan miji ne, da yiwa miji biyaya, da dauka cewar shi aure ibada ne da sauransu a haka har suka gama kafin Maman Muhay a sanyaye ta ce" Nahidt, in sha Allahu yau saura kwana hudu a daura maki aure da malan Muhamad bisa hukuncin da iyayenki maza suka yanke, domin Dad dinku ya matso da auren y'aya matan da zai yi kwana kusa , hakan ya sa suka hade da naki "
Kai ta sada tana jin yadda gabanta ke ta dokawa daf daf daf da tarin jin abubuwa daban dake ziyartarta a wannan lokacin Aurenta? Da Aban Shuwwa? Ya salam, idan ta kurma ihu a wajen nan me zai faru ne?
A hankali ta sake rufe bakinta dan kar ta kurma ihun, sai dai ina dariyar da ta ki boyuea ta tonata, hakan ya sa mamanta maka mata hararar da ta saka ta yi saurin gumtsewa tana mintsinin Shuwwa dake ta washe baki tana fadin" Wayo Allahna dadi zai kasheni"
Maman MUHAY ta yi yar dariya ta ce" Dadin nan kar ya kashe ki daughter, ya barmin ke da ranki"
Sai kuma ta yi kalar serius ta ce" IBTISAM, ban san yaya zan kwatanta maki ba, ban san ta inda zan fara ba, abinda na san zan iya roka a wajenki shine ki yi kokari ki gane wanene shi, IBTISAM kowa da gwaninsa a duniya, kuma ko wanene kai lalle akoy wace ke iya tankwasa lamarinka, sai dau idan baka hadu da ita ba, aman in dai ka hadu da ita to fa komai zai iya faruwa da kai, y'ata, so nake a matsayinki na matarsa ki yi kokari ki koyi zama da shi, ki iya tankwasashi, ki iya daidaita lamarinsa, ki cire tsoro ko shayinsa a ranki, ki jurewa halinsa ki kamanta zama da shi ta yadda zai ..............." Ta dan sasauta ta dora da fadin" Ta yadda zai zama cikaken mutun, ta yadda zai zama mutun cikake Yarinyata, shi din bahagumen mutun ne wanda ni kaina nakan rasa inda ya saka gabansa, sai dai abu daya da na fahimta shine ko yaya yake yakan ja tunga a kan lamarinki, My daughter shin zaki iya yi min kokarin nan?"
Shuwwa ta kalli Mama a sanyaye, sai kuma ta kalli Mahaifiyarta
A hankali Mamanta ta.....🥺ALK'ALAMIN KADARATAH
Na
*Sajida*
Page
6️⃣2️⃣
A hankali mamanta ta dan gyada mata kai tana sake dubanta da kyau, hakan ya sa ta sada kanta tana sauke ajiyar Zuciyar da ta kwace mata, Shin yaya suke so ta fahimtar da su cewar matse masa wajema na hadasa mata da bugawar zuciya da tunani? Yaya zata fada masu cewar shi din mutun ne mai karfin gusa tunaninta ya saka mata wasu abubuwa masu karfin gaske a cikin zuciyarta koda bata shiryawa hakan ba?
A hankali ta dan gyada masu kanta tana karra tunanin kawai sunna son sakata abinda zai hadasa mata ciwon kai ne, summa ya hadasa masu, domin a irin zaman da ta yi da mutumen nan ita kam ta cire tsamanin cewa wai zai iya daidaita lamarinsa a kanta, menene bara kamanta ba? Aman ko kallo bata ishe shi, dan wulalanci fa tafiya ce ya yi ko? Ko irin ya fada matan nan haka ya yi tafiyarsa,
Maman MUHAY ta yi murmushi tana sake kallonta da tunanin kunya ce ta sakata sada kan nan haka , dan haka ta furta" Allah ya maki albarka, Allah ya kama mana"
Da amen suka amsa, hakan ya sa ta mike tana fadin" Bara na baku waje Hajia"
Mama ta yi murmushi ta rakata da kallo har ta bar wajen kafin ta juyo ta fuskance su da kyau ta ce"Ta tafi, kina iya fadan na bakinki"