Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 67
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 67: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 67. Shuwwa hankalinta ne ya tashi ta shiga rikota tana fadin" Wani irin…
3,292 words
Shuwwa hankalinta ne ya tashi ta shiga rikota tana fadin" Wani irin shiga gaba, wani irin mutuwa? Ke NAHIDt ke fada min ubanda ya taba ki!"
Mama ta kai hannunta ta bige bakin Shuwwa din tana sakar mata harara, hakan ya saka MUHAY rintse ido domin da farko ya yi dandaja da baki ne yana karra tabatarwa cewa Y'arsa ta kunce, domin a magangannunta babu daya na mai lafiya duka a katse suke,, sai kawai aka dalar masa bakin mata? Yanaga ya dace su koma gida dama ya san wunin nan da wahala a yishi ba'a ci zalin dinta ba Da harare ya kalli Malan, sai ya ga kamar wanda kwallah ke cikawa ido
Sake murje idannuwansa ya yi yana kallonsa da mamaki sai kuma ya samu kansa da yin yar daria a tunaninsa rada zai yi ya ce" Kai wai hala kuka zaka yi?"
Shuwwa da ta turo baki ta juyo tana masa alamun karfa ya kaftta muryarsa bata da sirri
Daidai mama ta kama hijab din ta cire mata domin gaba daya ya nuna a rikice take
A hankali ta dubeta tana sake dubanta
Kasa kasa sosai ta ce". NAHIDt yaishe rabonki da gannin al'adarki?"
Tsoron bada amsa ya sakata yin wuki wuki da idannu, domin ita Al'adarta na mata wasa ne sakamakon dan maganin da ta ringa dan hadiya, wani sa'in sai ta dora mata sati biyu ko uku, a yanzu kuwa ba zata cewa mamanta ta sha maganin hannata daukan ciki ba a da shi yasa al'adarta bata zuwan mata irin na kowa ta kakafta mata mari a wajen nan , domin al'adarta kwata kwata wannan watan batama nuna alamun zata zo ba , a kadan ta yi sati biyar fa domin tana tunanin zuwanta aka yi aurenta yanzun kuwa auren ya kai kwanaki goma sha daya
Inda inda ta fara tana soshe soshe sai kuma ta yi raf da hannun Shuwwa tana fadin"
💃💃💃💃💃💃Saura kiris😆😆😆ALK 7️⃣8️⃣
Inda inda ta fara tana soshe soshe sai kuma tayi raf da hannun Shuwwa tana fad'in "Tuna min k'anwata?"
Da mamaki duk suka kalleta har da Shuwwa kanta, Mama da ta fara wani hasashen na daban ne ta d'an sunkuyar da kai tace "Indai baccin baya sakaki zama da yunwa ai da sauk'i, sai a yi fatan rabuwa lafiya kawai."
Duk ido suka zubawa Mama kamar wacce tayi wani mugun abu, Muhay da shima yake kallon Maman ya kuma kalli Nahidt ne yace "Ita ma cikin ne da ita?"
"Muhammad Rasulillahi sallalahu alaihi wa salam!" Mama ta fad'a tana sinne kanta uwa tana gaban sarki, wata zabura malam yayi ya tsurawa Muhay ido sai kuma ya kalli Mama da kunya ta gama cikata.
Wani uban ihu Shuwwa ta zankad'a tana mik'ewa tsaye har da d'an tsallenta da fad'in" Ciki gareta, wayyo Allah na ji dad'i, kai Allah mun gode maka, idon mak'iya sai dai ya fad'o k'..."
Tun bata rufe bakinta ba Muhay a sukwane yayo kanta yana fad'in" Rufa min asiri Ibtinah daina tsallen kar ya fad'o."
Ita ma sai ya jefata a yanayi irin na Mama ta koma ta zauna ta sadda kanta k'asa suka manne jikin juna da Nahidt.
Tashi ya yi gaba d'aya ya shiga takawa a nutse har ya idasa gaban Mama, zaune yayi irin zaman idan ka idar da sallah, kanshi sadde k'asa cike da ladabi da kunya da kuma rud'un abinda Mama ta fad'a dake son haukata tunaninsa yace "Mama...Mama kina nufin..ciki ne da ita wai?"
Tafin hannu Mama ta saka ta rufe goshinta tana satar kallonsu Nahidt da suke kallonshi suna k'umshe dariya, dan daga baya idan ya tuna abinda yayi zai jima bai had'a ido da Mama ba.
Shirun da Mama ta masa ne yasa shi mik'ewa tsaye ya k'arasa kusa da Muhay yana kallonshi kamar yanzu suka fara had'uwa, sai kuma ya juya ya kalli Nahidt da ita dai kallonshi take tana son gano menene yake damunshi?
Sake kallon Muhay yayi da shi ma ke kallonshi kamar zai tintsire da dariya, ruwan ruwan da ya fara hangowa a cikin idonshi ne yasa ka Muhay dafa kafad'arshi a ganinshi dai ya sassauta muryarsa, sai dai sam ba haka abun yake ba sannan yace "Ka ga malam, wallahi ka daure ka k'urma ihu ko da a harshen larabci ne za ka fi jin garau, haka na yi nima duk na rikice, k'arshe dai sai na rangad'ata da yarbanci kafin na samu nutsuwa..."
Gyara zamanshi yayi yana fad'in "Ai abun dad'in ji ne da shi da saka nishad'i."
Shigowar wata hadima ta shaidawa Mama ta yi bak'in dake son ganinta yasa har ta kusan hadimar fita saboda kunyar da yaran nan suka gama bata, saida ta fita ne malam ya samu ya cira k'afafunshi ya k'arasa kusa da Nahidt ya zauna a d'aya b'angaren hakan yasa suka sakata tsakiya shi da Shuwwa.
Hawayen da suka silalo masa ne yasa shi d'ora kanshi a cinyarta yana sauke ajiyar zuciya cikin rawar murya yake fad'in "Nahidt ciki fa, ashe ni ma zan iya ganin k'waina a duniya? Ashe dama zan iya riskar wannan rana da za'a iya min albishir d'in cewa ni ma zan zama Baba?"
Wata k'akk'arfar ajiyar zuciya ya sauke ya sake dafe cinyarta sosai yace "Alhamdulillah, Allah nagode maka da ni'imomin da ka min, Allah nagode maka, duk da bazata wannan lamari ya zo min, amma ku shaida na yi bakance tsakanina da ubangiji na zan yi azumi uku tare da k'ara aukin tukunyar gidana saboda al'umma, ko da na mutu ban cika wannan alk'awari ba wani ya min wannan k'ok'arin, daga gobe In sha Allah zan kame bakina har na tsawon kwana uku. " Shafa kanshi Nahidt tayi ta d'ora hab'arta a saman wuyanshi tana sauke ajiyar zuciya kafin tace" Za ka ga d'anka Habibina, da yardar Allah ma za ka cika wannan alk'awarin."
A hankali Shuwwa ta zame daga kusansu ta rab'e a jikin mijinta da yayi ram da ita suna kallonsu yace" Iyalinah, ko za mu basu wuri ne?"
Kwantawa tayi jikinshi tana lab'e baki tace" Ni kasan ma me nake sha'awa?"
A kunne ya rad'a mata" Me? Ni ne? To mu samu d'aki ma..."
Rufe mishi baki tayi da tafin hannu ta juya ta kalli su Nahidt da babu wanda ya kula da su, kallonshi tayi tana girgiza kai cikin rad'a tace" Ba fa wannan ba...kuka nake so na yi."
Zaro ido yayi sai kuma ya shiga zura hannu ta k'asan rigarta yana fad'in" Rufan asiri kar kiyi kuka, baki san hakan zai iya shafar lafiyar babynmu ba?"
Sake langab'ewa tayi ta d'an saci kallon Nahidt da har yanzu hab'arta na kan wuyan Abbanta daya kasa d'agowa ita ma har ta fara hawayen na godiyar ubangijinta, irin tarin ni'imar da ya mata sai take sake jin kunya da ta wulak'anta kanta a baya, ta kuma yarda d'ari bisa d'ari Allah ma ji rok'on bayinsa ne sannan mai rahama ne kuma mai jin k'ai, duk irin abubuwan da tayi ubangijinta ya mata babbar ni'imar data samu damar shiga d'akin aure, wanda ko iya haka aka tsaya za ta mutu tana kai goshinta k'asa tana godewa Allah, duba da dayawa da suka tab'a harka irin wacce tayi sun yi mummunan k'arshe, wasu ma idan suka mutu sai dai a jefar da gawarsu a bakin titi har su rub'e su bushe... Amma ita ta yi auren yau kuma gashi har ana alamta mata lallai fa nan da lokaci kad'an za'a kira da Mama ita ma.
Muryarta na rawa ta ce"Aban shuwwa ka daina kuka mana, ka daina kuka, sannan mama hasashe take mana fa? Kar mu kwalafa rai a je ba hakan bane ba......"
Kansa ya dago da sauri yana kallon hawayen dake ziraro mata ya talabi fuskarta yana fadin" Kin san tun ina da shekara ashirin da biyu na yi auren fari? Ba'a taba alakanta min hakan ba domin matana basu taba nuna irin hakan ba, a yau da aka alakanta min zan so ki barni na yi ta motiyar yannayin koda kuwa hasashe ne Nahidt"
Yawu ta hadiye tana talabe hannayen nasa ta ce" Ba nufina ka daina farin cikin hakan bane Aban Shuwwa, Aban shuwwa zan fi kowa farin cikin hakan, aman ina tsoron ka ji ba haka bane kuma tashin hankalim hakan ya fi farin cikin yawa, bayan wannan shin zaka so haihuwa da nine? Zaka so na kasance uwar y'ayanka ne dama? Abam Shuwwa zaka so mace irina ta rike kwonka?"
A hankali ya janye hannun nasa yana kallonta ya ce" Me kike nufi? Ashe baki da yarda da soyayar da nake maki ba?"
Da sauri ta girgiza kanta tana fadin" Ba ba haka nake nufi ba"
Muhay ya tabe baki yana sake kallon Shuwwa dake neman fashewa da kuka ya sake zuba masu ido kamar yadda ya yi shima
NAHIDt ta ce" Allah ya umarceku da ku samawa y'ayanku iyaye na gari ....ni kum...........
"Ke kuma ba uwa ta gari ba?" Ya fada a kausashen da bata taba ganninsa ya yi magana irin haka ba Hannayensa ya dunkule yana fadin" Saurara ki ji abinda zan fada maki, daga yau, daga rana mai kama ta yau, kika kuma budar bakinki kika alakanta kanki da kalma irin wannan Nahidht sai na kaurace maki na tsayin lokaci dan na horar da ke da horon da ya dace da furucinki, idan kuwa wani ne ya fada in ya girme min zan kaishi kotun Allah domin sai na hada shi da Allah, in kuwa nine na girme masa sai na yi masa dukan da ban taba yiwa wata halita a duniya ba! NAHIDt ki kiyaye fushina domin ban iya ba..........."
Kai MUHAY yake gyadawa ya ce" Haka nake son maza Walahi, aman ka wani zaunaa tana raina maka wayo mikon ita na wanwanka mata mari idan ya so sai ta yi hankali!"
Baki sake Shuwwa ta kalle shi, sai kuma ta kankance ido ta ce" Me kake nufi ne MUHAY ?"
Dan tsareta ya yi da ido sai kuma yaa ce" Ni yanzun du kin zama wata mafadaciya, ba damar a ce abu sai ya maki zafi ko ba dake ake yi ba, haka fa jiya kika ce yau za'a zo gidan nan da na ki da na so na fa isheki fa? Hala cikina ne yake saka ki haka? Na ga ai da kyaleni kike yi da halina ko mee zan ce ko?"
Idannuwanta dai na kallonsa ta gyada kai tana kyaftu da sake kallon su Abanta
Murmushi ta yi gannin Nahidt dinta, Nahid dai NAHIDt dinta ta sauko kasa ta duka saman kafafuwanta ta hade hannayenta tana fadin" Dan Allah ka yi hakuri haba bawan Allah mai sanyin hali da zuciyar musulmai, kana gani har an fara son koya maka wani halin daban bayan shi mutun din mijin tace ne? Ka yafewa amaryarka mana haba Muhamaduna"
Du yadda ya so sake cicije mata sai da ya gaza ya juyar da kansa yana dan murmushi
MUHAY ya tabe baki yana rike hannun Shuwwa yana fadin" Sai ka tashi mu je a tabatar mana abinda ke sakata barci, kana gani tana cikin ha'ula'i aman tana nemana masifa, na je na zama mijin tace din in da laifi a ciki a harbeni mana, ku wuce min mu je ni!"
Hakan ne ya kasance, sunna hanyar zuwa clinik din ya shedawa Hajia domin tana ta kirra baiwar Allah, Jin sun tafi clinik ta bi bayansu dan kar aje jikin na Nahidt din ya rikice ne
Da ta zo ta tarda har an yi daukan jinni an kuma ce za'a kawo result nan da minti talatin
Hankali kwonce MUHAY ya kalli docter da ta dawo sanadiyar kiranta da ya yi a office dinta, domin a ciki suke sunna jiran result din ya ce shin za'a iya yi masa abin nan da ake yi dan gannin yaron dake ciki? Allah ya sa sun kai goma
Ita kam ta masa uzuri domin ai na farko ne bai kuma sani ba, inda Shuwwa ta dafe haba , Hajia ta sada kai tana kyakyata daria, Malan kam murmushi ya yi yana sake kallon NAHIDT dake ta jan carbin da Hajia ta zo da shi tana ta hamma baiwar Allah
Dan mintunna tsakani aka fito da result din
MUHAY ne ya karba yana bin kowa da kallo dan sun masa zuru zuru ya bude yana dubawa
Murmushi ya yi yana fadin" Ta tabata ka cika aiki Allah sauketa lafiya"
"Ya salam, ya Allah, ya rahamane, ya Rahim....... Alhmdulilah...... Alhmdulilah............." Yana fada ya mike ya kai sujada goshinsa kasa ya dago yanaiwa Allah godiya da kai dubansa kan Hajia da ta amshi takardar ta karanta abinda aka dora sai kuwa ta shiga hamdallah muryarta sama sama sosai wanda ke nuni da tana cikin farin ciki marar misaltuwa , fadi take" Allah dama bamu cire rai ba, mun san zaka bamu, Allah dama mun san jinkiri ne mai alkhairi, Allah mun san zaka bamu.......ya Allah ka sauke mana ita lafiya ka bata lafiya da ita da abinda yake cikinta ya Allah, dukan abin ki Allah ka karesu da shi ya ubangiji......."
Tabas a yau matar ta karra shiga cikin zuciyarsu baki dayansu fiye da kima, kalaman da take sun saka ta idasa sace zuciyarsu da wannan suka kuma rankayawa gidan Malan, inda sunna zuwa Hajia ta shiga dama madara tana fitarwa ana fitarwa waje ana sadaka, sannan ta fitar da aljihunta makudan kudi ta ba masu aikinta da ta yarda da su ta wakilta su fita neman mabukata su bada, haka su kansa albashinsu aka karra da kuma karin sadakar abinci , kai a ranar dai basu san me ya faru ba aman duba da yadda aka yi baja baja haka sun tabata wani abin farin ciki ne ya shigo masu gidan, duda gidan malan ana sadaka ba rana aman yannayin da Hajia ke shige da ficen hakoranta a washe , haka shi kansa Malan a masalaci da duka je salar azahar shi da MUHAY hakoransa sai hamdallah a waje suke karrara zaka gane farin cikin da yake ciki a yau mai girma ne, ko da ya zo wajen adu'a yana yi a bayane ne sai ga hawaye na wanke fuskarsa, da aka gamama nan aka barsu shi da Soja da ya rafka tagumi yana kallonsa yana zikiri yana dariar farin ciki sai kuma shima ya tayashi dariyar ya ce" Ni Allah la'ila ha ilala malikul mulki na iya...... Da itacema sai na tayaka"
Ai kam ya taya shin, domin ita din suka dauka lamarin ya karra zafi dan kuwa muryarsa ya bude aon ransa ya dagargaji zikirinsa gwargwadon iyawarsa, Malan na yi yana amshe harda su almajirai
Karshe dai a gidan Malan suka yi wunin nasu har karfe shida ta yi, sunna shirye shiryen dagawa bayan sun more da dadaden dan waken da Hajia ta rangada masu mai rai da lafiya sai ga Furera wace tun karfe biyu sukai waya da Malan yake sheda mata ai sun wuce gida hate, zai dawo dai ya dauketa zuwa yama in sha Allah Wani tunani ya fado mata cewa idan jikin na NAHIDHT ne ya rikice ya sa suka dawo gida? Kai shagali, dan haka ta ce da shi ya barshi zata zo da kantama da ta yi sallar la'asar, to shinefa tana zuwa ta ga gidan kamar ana wata sallah kowa bishasha yake ga dukkan alamu yankama aka yi aka shiga aikin naman sadaka sai ta daga kafa da sauri ta karasa bangaren mijinta dan ta tabata a cen zata iske abinda ya dace ta gani
Ido ido sukai da mutanen falon har ta sauke a kan lalausar fuskar mijinta wace a yau annurinta ba boyaye bane ga kuma wani abin kafar karuru ce a saman cinyarsa yana massaging a hankali a hankali
Myrmushinsa ne ya daukaka ya bi kafar tata da kallo da ta janye sakamakon shigowar Furerar domin ko a gaban Hajia bata yarda haka ya faru ba dan zucoya ita bata da kashi, ita kuma ta yiwa kanta alkawari ne yarinyar nan ba zata yi abinda za'a ce eh lalle Nahidht baki kyauta ba a kanta, ta fi so ta yi gigin sake shiga huruminta da kangin kanta ta yadda zata zartar da abinda ta yi niya a kanta da dalili aman ba haka ba kai tsaye
Murmushin dake kan fuskarsa bai gushe ba, haka kuma bai damu da rashin gaishe da mutanen da bata yi ba domin ta yi salama sai dai ta kasa gaida kowa tana dai bin mutane da kallo bayan ta cire nikaf dinta ga karnin ranar da take na wuni a gari tunda bata riga ta yi wanka ba ya ce" sannu da dawowa Furerah........"
Dan murmushin yake ta yi sai kuma ta ce" Barka da yamaci Yah Ustaz....., Shin me yake faruwa a nan ne?"
Carab ya shaida mata abinda yake faruwar, dan shi ai ya dauka Furera da Hajia daya suke kuma zasu iya nuna soyayarsu wa soyayarsa, sai dai kashhhhhhh, hannunta na rawa ta ce" Yah ustaz, kana nufin yarinyar da ka auro jiya, wannan dandin itace ke dauke da cikinka? To wayema ya fada makaa cewar tana da ciki? Me kuma ya tabatar maka naka ne????"
To fa, tunda ta shigo har ga Allah MUHAY kallo daya ya mata ya juyar da kansa wajen wayar dake hannunsa ya danna ya shiga domin shi baya son rashin kunya, fetsarare kuwa kallo daya yake masa ya gane shi, sai yanzu da ta dire maganarta ya sake dagowa ya shiga dumbin yan mamakin jim furucinta
A hankali Malan da maganar ta dake shi yana sake kallonta ya ce" Fure? ......."
Shuwwa ta dantse hakorinta bayan ta ce" Hurera take!"
Malan ya sake fadin" Ki je bangarenki"
Furera duda ta ga yannayinsa haka ta kasa hakura da wutar da ta fara ruruwa a kirjinta a wani haukacen ta bude baki ta kurma ihu tana dora hannayenta duka biyu saman kanta tana fadin" Malan, dama rike cikin ka yi sai a fara zaka ba ba ni ba? Malan dama kana iya yiwa mace cikin ni ka ko bani malan me na tsare maka da ka ba karuwa ciki ni ka hannnnnnnnnnnnjnjj........." Sai kuma luuuuuuuuuu ta tafi ta daku a kasa gaba dayanta alamu na summa suka bayana a tatare da ita
Malan ya lumahe idannuwansa yana girgiza kansa yana kuma jimke hannayensa yana ta ambaton sunnayen Allah da son daidaita fushinsa kafin ya kai gareta
Muhyideen ya sauke murmushi ya dauki ruwan kankarar dake gefensa ya karasa ya maka mata shi yana tsaye a kanta ta farka a gigice da wani ihun ta kuma dora da haukan magangannun mararsa dadin ji har sai da abin ya kai masa makura ya tafka mata wani uban ihun fa ya saka ta zarro ido ta ja baya da sauri tana hade hannayenta a kirjinta tana kallonsa jikinta na bari
A kausashe ya ce" Baki ji Muhamad ya ce ki je bamgarenki ba ko sai an kaiki ne?"
Ido ta ringa kikiftawa tana kallonsa tana kuma kallon Malan da jiran ya yi magana mana waye wannan ya bari ya shiga fadansu na cikin giida? Gannin bai yi niyar yin magana ba ta juya ta fice a dakin da sauri tana mai ci gana da hanna kanta tube komai na jikinta ta fice a gidan tana kurma ihun da kukan nata
MUHAY ya juyo yana fadin" Kaima ba kowa ba ake fadawa irin maganar nan mana, wani fa makiyinka ne baka sani ba"
Malan ya dago kansa yana fadin" MUHYIDEEN Furera ce fa, Furera iyalina? Yau Furera ce ta min min wannan abin? Ashe rashin hankalin nata ya kai haka? Ni walahi ji nake kamar na saketa na huta da shirme irin nata, ina dalili mace ba hankali ko daya? Ka ga har kiranta ta yi da mugun sunnan nan bayan na yi alkawarin du wanda ya kuma kiranta da shi sai na zane shi in dai na fi karfinsa?"