Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 68
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 68: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 68. MUHAY ya sake tabe baki yana cewa" Gaskiya gwara kawai ka saketa, kai…
3,240 words
MUHAY ya sake tabe baki yana cewa" Gaskiya gwara kawai ka saketa, kai ni walahi na yi mamaki ko dai auren dole aka yi maka da ita ne? Ina dalili wannan fa ba zaka iya dukanta ba gaskiya tana iya nanaka da kasa baka ganninta ne wai? Yayama kake iya juya abar nan ne? Kai sbahanalahi gwara na auri kamar gajiyarka sau dari da wannan matar, kana gani fa gaba daya ba laushi ba lausasawa, ai da gangan na daga muryata dan na bambance da ihuna da nata wanne ya fi karfi? Wannan ta kwarara maku shi tsakiyar dare ai sai ku zata farmaki aka kawo ko yan fashi ne, inaga ka saketa ka auro wata ya fi alkhairi kawai"
NAHIDt ta yi saurin fadin" Haba yaya MUHAY, Haba abana kai kuwa ya saketa ya kawo wata fa kake cewa, ai ya yi hakuri ya sanyayar da zuciyarsa ya yi adu'ar Allah ya dora shi a kan daidai in sakin nata ne daidai to Allah da kansa zai karrar da zaman ba tare da ya kawo wata ba , idan kuwa ba shi bane Allah ya shiryeta, aman ba ruwansa da fadanmu gaskiya, kai ni nama yafe mata kawai a bar maganar ai dama ba kowa zata birge ba, aman ba sai an kai da su duka bama, duda na yarda da sadaukina ba ita ba ko gaba da ita yana iya horarwa ta kuwa yi la'asar ta yi sanyi walahi, aman bana so ni ma yafe na kuma yafe a bar maganar dan Allah"
Ido da hanci suka zuba mata daga Shuwwa dake jira ace a je a zaneta har mijinta
MUHAY ya juya wajen da nikaf din Shuwwa yake ya dauko yana miko mata da safar hannayenta yana fadin" Dan maimaida kayan nan mu tafi gida kin ji? Inaga Nahidt ta zama munafuka, wai mu zata nunawa zagaye? Ke din? Idan kin tashi yin kokowar dai da ita ki kula fa cikin nan dan idan ta nausa maki hannunta ya bare zan rufe ku ne a matsayin kun yi kisa, yan wulakanci kawai"
Shuwwa din kanta sakawa ta yi cike da mamakin kisar antyn tata, haka dai suka yi tafiyarsu da fada suka barta ta sake rike abinta tana rarashi da nuna masa dole zai ga irin haka, kawai ya kyale maganar cikin a yi fatan Allah raya itama Allah ya bata nata
Shi kam a gaskiya ya zama wajibi ya kaurace mata, ba dan komai ba sai dan kankin kanta, idan ta mike a haka zata fara halaka kanta ne a banza da wofi, gwara ta gane ta yi hankali
..............................................................
*A gurguje*ALKALAMIN KADDARATA
PAGE 7️⃣9️⃣
NA
SAJEEDA
END🤧
Cikin gata da kulawa suke rainon cikinsu abun gwanin sha'awa, duka mazan lallab'a mtan suke dan wani abun idan suka nemi kirtashi dole suke nuna musu sunyi saranda ba dan komai ba sai dan cikunan jikinsu, kowace da na ta kalar laulayin, Shuwwa dai ba mai tsamari bane sai dai kawai canzawae yanayi na kana tare da d'an mutum a jikinka, inda Nahidt kuma har yau baccinta take sha hankali kwance, wanda hakan ba k'aramin shiga hakk'in malam yake ba indai kwananta ne, sai dai ya ya iya? Da ta fara fad'a masa baccin ma ba za'a barta tayi ba dole yake komawa daddab'ata har ta koma baccin, ya d'auki son duniya ya d'orawa cikin nan, fatanshi a yanzu d'aya ne ya ga me za ta haifa, mace ko namiji? Ya ji kukan jariri shima a kunnensa a hannunsa sannan ya ga yan halbe halben hannaye a hannunsa, yana matukar so ya ga budewar ido da Kuma kallon da za'ai masa a hannunsa, yakan ji tsigar jikinsa na tashi idan ya ga tana tube rigarta a gabansa, ba dan komai ba sai dan gannin da gaske jikinta ya fara tasawa ta yadda dole a gane shafafen cikin nan na dauke da dan mutun, domin tun yanzu cikin nata turawa yake yi sosai wanda hakan ya sa yake kan yi mata adu'a ba dare ba rana da fatan Allah ya bata ikon jure dawainiyar cikin da ita da kanwarta wace suke haduwar sati sati ko a gidan Malan din ko kuma a gidan Shuwwa din, ko a je gidan Mama wace ta ja masu kashedon su rage zuwar mata gida kar su jaza mata maganar mutane ace ta aurar da yaren aman kulun sunna gindinta ita kam su yi zamansu a inda suke Shuwwa kam takan zuba tabararta idan ta rayo mata, tun dan zazabin farko farko da ta yin nan shikenan ya bi lafiyar jikinta sai dan karan kwadayi na cin salak wanda ya saka MUHAY koyar wanke salak, domin kadan daga aikinta a talatainin dare ta dan lalubeshi tace cikin nan du ya sakani aiki irin na yan giya, ka ga wai salak........., Sai ya koyi ajiye kayan wankesu a kusa idan ta bukata sai ya fitar da shi a frij domin idan aka saka salak a frij wajen da baya kankara sai ya shafe sati biyu bai yi komai ba, yana wankewa tana darwayewa tana yankawa a gefe ta more sannan ya mori lamari domin bata rowar kam ita, Nahidt ce ta harbu da harbi irin na rowa , mamansa kuwa ta mayar da zuwa abinda ya fi komai sauki a wajenta, dan ta nuna a yanzun a bar Shuwwa da maganar balaguro ita kam bata so, a barta ta reni cikin nan cikin nutsuwar da zata haife shi lafiya ba tare da an shiga wata damuwar ba, duda sun san basu isa su hanna komai ba, aman sunna kamanta kiyayewa
A bangaren Sultanma yana gabatar da mulkinsa daidai gwargwadon iyawarsa, ya saka an fitar da Uncle dinsa Ibrahim an dawo da shi fadar an kebanceshi a waje mai kyau ana ta yi masa dukkan taimaakon da ya dace na sihiri, cikin amincin mai duka kuwa a yanzun ya daina doke doke da neman fita da gudun da yake yi a da, sosai har ya fara kawo hankali a kan kiran sallah yana kamanta son zuwa ya gabatar da ibadarsa, hakan ya sa hankalin Sultan ya karra kwonci ya ci gaba da yin iya kokarinsa dan gannin garinsa ya dan samu daidaituwa, domin gari ne an riga an rushe sai a hankali koda za'a samu kansa, ba laifi samari na jin nasiha sunna kuma kokarin neman aiki hakan ya sa kashe kashe da fadace fadace a kan yan mata du ya ragu, summa yan matan yawanci da suka dakatar da makaranta sun koma bisa nasiha da shirye shiyen da aje gabatar masu a gidan redio na jan hankali da nasiha da nuni cewa kansu suke halakawa ba kowa ba, shi yasa du yawanci wa'inda suke iya jin kira suka sauko suka shiga kimtsa kawunnansu cikin salama sunna dawo da darajarsu koda kadan ne a cikin da yawan
Furera kuwa ta ga rayuwa gannin idonta, domin abu da ya yi abu da kansa ya sakata a mota ua mikata gidansu ya samu datijon mahaifinta ya sanar masa abinda yake faruwa, ya kuma taushi tsohon da ya rikice da tsoron kar aje ya saketa ne? Ya nuna masa ko daya bao saketa ba, zai so ta gyara halinta idan har zata iya zama da shi ta daeo su zauna, idan kuwa ta ga gaba zata karra dan ta samu haihuwar da na kasa bata a gannin shikenan sai a gabatar da komai cikin salama ta yadda zumunci zai dore A nanne mamaki ya cika tsohon yake maganar wace haihuwa? Shin furerar ta manta accident din da ta yi tun tana budurwa wanda ta shiga mawuyacin hali domin cikinta ne ya fi dakuwa da mashin din da ta hau daga makaranta zuwa gida, wanda likita ke fada masu mahaifarta ta tabu ko kuwa bakin kishinta ne ya rufe mata ido? Shi kam malan rasa ta cewa ya yi domin a nan tsohon ya kirayeta ya tunasar da ita maganar da ya ringa mamakin yadda take rusa kuka tana fadin ai likita ba Allah bane bai isa ya yanke hukunci a kan haihuwarta ba Rai bace datijon ya salami malan sannan ya lalubi butarsa ta alwallah ya jefeta da ita rai bace yana fadin" Ki kula, bakinki ya iya magana yanzu dai sai ki shige gidan ki ci abinda muke ci, dama ke kike taimaka mana sai ki tsiro da sana'a sannan ki kasa zaman ki ga idan da riba, ke ba'a guje ki dan halayanki ba kece mai abin fada a bakinki? Hurera ba zan ce maki duniya ba domin idan kuka karra lalacewa a kan haka ni zaki dawo ki kashe, Allah ya ganar da ke da kalar ganiyarsa wace zaki fahimta"
Tun daga ranar take rayuwa a gidansu, rayuwar da ta zo mata a cenji, ba yan aiki ba kudin cefanen Malan bale sansanyar muryarsa da lakausan gadonsa uwa uba abinda takewa kishin babu shi, haka ba cimar da ta saba sannan ba sanyin AC domin gidansu rufin asirin Allah ne Alhmdulilah aman iyayenta ba masu kudi bane, itacema ta gyara gida har suka samu rufin asirin domin ko a anguwar a haka sun fi kowa rufin asiri, shine take baza rashin da'arta son ranta har ta gunduri abokin zaman nata, da kyar da jibin goshi bayan ta cike wata biyu a gidansu aka dawo da ita ta dawo ta ci gaba da zama ba ruwanta da kowa sai mijinta tana kuma gannin yadda cikin mattar da ta tsangwama din ke karra girma da kuma irin yadda kamar da wasa yanzun a anguwar ake mutuntata bayan a da ta dora kowa kan hudubar tsiya ana wulakanta bayin Allahn
______________________________________
*Watani tara da kwana bakwai*
Nishin dake sake tashi a kusa da ita ta sake waigawa tana kallo, a sanyaye sosai ta ce" IBTISAM ko mu koma gida ne? Shin na tabo Mijinki ya maida mu gida ne? Kin ga halin da kike ciki kuma gashi Allah bai sauketa ba har yanzun , bana so ki jigata y'ata" Mahaifiyar MUHYIDEEN da ta dawo gidansu kusan wata daya da sati daya kennan bayan alfarmar da ta nema ta gudo dan zama da Shuwwa din wace ta zama abin tausayi sanadiyar kumburin da cikinta ke sakata, ta sinkime gaba dayanta cikin ya mata girma sosai, tunda suka yi scanning aka sheda masu fa biyu ne a cikin ta kasa hakura sai da ta lalaba mijinta ya bata dama ta dawo kusa da su da zama domin ita dai ko hauka take ba zata taba turo abokiyar tagwaitakarta ba, duda yanzun Useinar ta fara daidaituwa da lamuran da take fama da su dan kuwa da kanta ta nemi da mijinta ya sawaka mata ta kuma nuna cewa aurensu haramtace ne zata je ta kadaice kanta, wannan dalilin ya sa ta daga ta yi tafiyarta kasa mai tsarki ta yanke hulda da kowa kan tana bukatar kusanta kanta da Ubangijinta ko zata samu rabauta ko zata ji zuciyar a sake irin na mai kyakyawar tuba, shi yasa itama ta dawo ta sake rungumar lamarin yaronta da matarsa sai wajen Mama da take zuwa su yi zumunci ta dawo tana kula da Shuwwa sosai A yanzu lokacin haihuwar tata har ya zarce aman kuma shiru, sai Nahidht da itama ta gama ficewa a hayacinta ce nakudarta ta tashi tun da daren jiya har zuwa yanzu karfe goma sha daya na safiya shiru bata haihu ba, gashi likitocin sun nuna cewa nakuda ce take ta zama bata idasa nuna ba sannan sunna kyautata zaton a cikin nan ba daya bane dan irin motsin da abin cikin ke yi bayan girmansa, domin Malan kiyawa ya yi a masa scan ya nuna ya fi so idan lokacin ya yi zai ganni da idannuwansa
Kai ta sake juyawa tana maida hawayen da suka cika idannuwanta ta sake kallon dakin yan haihuwar da Nahidt ke kwonce muryarta a raunane ta ce" Mama, dama kowama haka yake haihuwar ne?"
Hajia da ta dawo da abincin ranar da ta koma ta dauko domin ita Furera bata zo ba tana dai cen tana kula da abincin gidan dan Malan kam ba kanta yana masalacin asibitin koda wani abin cen ake tarda shi ya kasa katabus ta dafata bayan ta nanade mata dardumar da aka shinfida mata a kasa a sanyaye ta ce" Kanwata , kowa da irin yadda take zuwar masa, duda ban taba haihuwa ba aman an haihu sosai a hannuna in sha Allah zata sauka lafiya mu yi ta mata adu'a ta yi kokari sosai domin har yanzun tana ta karra rike kanta sosai "
Mama zata karra mata wata maganar sai ga MUHAY din ya karaso A sanyaye ya sake yi masu wata salamar yana dukawa da ledar dake hannunsa ya shiga budewa yana kallonta ya ce " kin ga na kawo maki yalon nan yau du baki nema ba"
Fuskarsa ta karewa kallo mai cike da haiba , sajensa luflufluf a kwonce, lebunnansa sunna kyalin jansu haka kuma yannayinsa dake tafe da sanyin fa jikinsa yake da shi tun jiyan shima na nakudar Nahidht din da ya tsorata shi har yake tunanin idan ma Shuwwa din ya tashi yaya zai yi da ransa ne? Malan yana masalaci sauka yake yi ba ji ba gani ya kasa cin komai sai karatu yake yi bawan Allah, shi idan tasu ta zo ko yaya zasu kwashe? Likita ya ce lokaci ne bai yi ba da zarar lokaci ya yo zata haihu ba wata matsala a tare da cikinta, wai bata wuce ka'ida ba, aman ai yanzu a satin na wucewar ka'idan take ko? Wanke yake nufin idan bara haihu ba za'a iya yi mata fashi
A sanyaye ta lumshe idannuwanta sakamakon ciwon da ta saba ji mai dantsa mata har bargonta da ya sake tashin mata A hankali take dan numfashi da bakinta idannuwan nata a rintse rufffffffffff har sai da ta ji abin ya lafa mata sannan ta sakar masa murmushi a hankali ta ce" Ka ci abinci ne?"
Ajiyar zuciya ya sake saukewa yana tunanin wai abinci, ita dai a yi sha'ani kawai, shi ba abinci ba yai idonsa idon yan sholisho suka wani kwasa a guje dan sun gansa a lifan dinsa ya yi gaba ko kallo basu ishe shi ba, to ina hankalin kallonsu ne yana ta kansa?
Mama ta sake sauke ajiyar zuciya ta dauki wayarta ta sake kiran Mahaifiyarsu
A sanyaye ta ce" Haba gimbiya wannan wace irin karra ce haka? Ya dace ki zo ki ga Nahidt, yarinyarnan tun jiya take kan gwuiwa, har yanzu shiru, ki zo ki dubata sannan ki karawa yar uwarta kwarin gwuiwa, tunda ta zauna din nan ta kasa koda motsi sai dai ki ga tana rintse ido tana kuma budewa"
Maman ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Aa Umaansu, bayan gaku kuma ni din idan na zo me zan masu? Nakudar wata da har take sati tana ja? Allah ya raba lafiya, sai dai......." Sai kuma ta yi dan shiru
Mama ta ce" Sai dai me?"
Maman Shuwwa ta ce" Ita IBTISAM din, ki dan matsanta mata kan ta mike daga inda take ko ta kwonta ki gani? Idan ta yi to, idan kuma hakan ya gagara fa ina tsoron irin nakudata ce take yi wace sai dai na yi ta surutu a zaune idan kuwa aka yi wasa daga zaune idan har na karkata to dan bada kan d'a ne"
A zabure Maman ta juyo wajen su Shuwwa din tana kallon yadda Muhay ke mika mata hannu yana fadin" Kalleni, bara na kamaki ki mike mu tataka zaman nan bashi da kyau fa kin sanni, tun safe a haka kike fa yau ko ciwon bayan bakya ji?"
Idannuwanta ta kuma rintsewa sanadiya ras ras ras ras din da take ji har kwakwaluwarta ta dan janye hannunta tana dan damkar hijab dinta kadan har sai da ta lafa mata sannan ta ringa sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" ka ga, kafafuwan nawa gaba daya yau basa anfanuwa, haka kuma kamar an girkan duwawun na kasa wani motsin kirki da na ce zan ringesa nan hakarkarina yake rikewa dole dai zan dawo na zauna a haka............ka bari idan Nahidt din ta haihu sai mu shiga "
Mama ta farra zarro ido zata mike likita ta fito da sauri tana fadawa wata nurse kan maza ta kirawo likita kai ya fara badowa
A haukace ta yi baya dan kiran likitar tasu, hakan ya sa Mama mikewa zurbat ta karasa wajen Hajia da ta mike tana fadin" Ya Allah ka rana lafiya alfarmar annabi, ya Allah ka rana lafiya" A dan rikice ta ce" Anya Ibtisamma ba nakudar take yi ba?"
Hajia ta juyo tana kallonta ta ce" Nakuda kuma Hajia? A hakan?"
Mama ta ce" Kinga fa yannayinta fa? Yarinyar nan bata da lafiya zo ki gani"
Sunna karasowa likita na shigewa aka rufu a kan NAHIDt wace karfinta ya gama karewa jikinta a mace ta galabaita ta gama ficewa a hayacinta ta riga ta san tata ta kare wai wani ta nisa? Ta yi me idan ta nisa? Tun dazu ai take nisawar babu abinda ke fita a jikinta gaba daya an gwaleta gaban kowa ana mata nisa, bata san cewa da ake cewa idan lokacin fitowar dan ta yi fitowa yake ba sai yanzu da ta ji wata irin azababiyar nishi ta taso mata daga kirjinta ta fetso aabinda ya tafi da dukan kuzarinta ya yagata tana ju likitar ta idasa janyoshi ta fitar daga jikinta tana kuma neman maida numfashi wata nakudar ta kuma kankama wace ta idasa sadakarwa tana ji ana daidaitata da sauransu da kyar kamar ba zata iya ba sai ga wani dan ya fado duniya mai calarar kuka domin da ihunsa ya diro duniyar yana kukansa tun karfinsa kafin ta nemi tafiya duniyar summa inda suka hannata ta hanyar du da ake hanna mace tafia duniyar summa a irin wannan lokacin domin jinni ke dauka idan ka tafin ta yiwu ka tafin kennan
Ana bidiri ne a ciki a waje kuwa wani bidirin ya barke Da gudu Hajida da ta gama kiran malan a waya cewar ta sauka ta sake duban dayan jaririn da aka kuma fitowa da shi aka nufo wajen da ake auna su a gogoge su kafin a ba masu su su tana zarro ido ta cewa likitar" Likita biyu ne?"
Likitar ta yi murmushi tana gyada kanta lokacin malan ya karaso idannuwansa na zubar da hawaye ta sake maida hankalinta kan Shuwwa da ake kokowar sai ta motsa aman fadi take da bakinta a rikice kamar haka" wani irin juyawa cikina yake yi, abin jinsa nake daf da fita ima tsoron juyawar nan na yi kashi a zaune, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une wayo Allahna cikina bayana, kafafuwana tamkar basa jikina, wayo Mama"
Tashin hankali, a nan fa katonta ya aniyar neman kinkimarta a rikice yana fadin " Ke kin ga ki fa bi tashin hankalina a hankali, mu je gida kawai na shiga uku Mama kin ga ta ki ta motsa"
Da gagawa likitar ta karaso da wanda ke tura gadon nan tana fadin" Ina takardarta ne? A wata na nawa take ne?"
A rikice duka yake dan haka yake fadin" Mu fa haihuwar yayarta muka zo bamu shirya tata ba, kin ga ita ai da tun satin da ya wuce aka ce zata haihu aman bata haihun ba, mu yanzun da haihuwar yayarta muka zo me zai saka mu yi yawo da takardarta?..........." Hannayensa ya dora saman kansa jin abinda likitar ke fadi da karfi cewar" Nakudarta fa ta nuna haihuwa ce fa"