Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 69

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 69

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 69: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 69. Ai kam rikicewa iya rikicewa sun rikice, ba mai ba dan uwansa hakuri…

522 words

Ai kam rikicewa iya rikicewa sun rikice, ba mai ba dan uwansa hakuri harda su Malan din A kofar dakin haihuwar suke daf da daf gaba dayansu, abun ne ya hade masu goma da gomiyatara, du irin zumudin da Malan yake ciki sai da ya sare da tsoron haihuwar a ransa Sai dai cikin hukuncin ubangiji ita nata haihuwar bai dauki lokacin na Nahidt ba, domin dama ta jima tana nakudarta a yanzun ta zo kan gaba ne kuma ita jiran ciwon da ya girmi wannan take koda zata ce bata da lafiya dan mamansu fada masu take su iya rike bakinsu a dan kwayam kwayam din nakuda kar su tarawa kansu mutane bayan nakudar bata wani nuna ba a ringa cika asibiti ana yamadidi da su, su a wahalce wanda yake tare da su a wahalce, shi yasa ta dauka cewar nakudar idan ta taso sai ta suma kamar sau bakwai dan azaba, gannin du irin azabar da take ci bata suma ko daya ba sai ta ajiye hakan a matsayin mai zuwan na zuwa a gaba, ashe ita hanya nata budewa bata sani ba, sai a kan gadon haihuwar ne ta ringa salallami da kiran sallah tana fadin kaico rayuea ashe haka ne abin? Toh Allah mun gode maka (😌😂😌 kashhhhh )

A wannan rana daukacin familyn nan uku sun tsincin kawunnansu a matsanancin farin ciki da kukan jarirai hudu ya garwaye kunnayensu yayaryayar yaayayayayayar sunna tsala shi ba ji ba gani sojojin Shuwwa sun bayana yan mata guda biyu tsala tsala hakama na Nahidt jaruman ustazanta guda biyu yan samari tsala tsala, a dole suka rikice da kukan farin ciki kafin duniya ta dauka..................

*sunnah*

An gabatar da taron radin sunnan yaren a baban masalacin fada, inda taro yake gudana a cikin fadar na amaren jegon guda biyu, domin gannin za'a rikice aka hade waje daya ake gabatar da taron A wannan ranar MUhay da Malan baka har hanci, farin ciki suke ciki mai girman gaske sunna kuma godewa Allah da suka wayi gari MUHAY da baby girls dinsa masu sunnan iyayen matarsa da na mahaifiyarsa akai masu inkiya da Ummi da Mami, sai Malan dake da zaratan samarinsa wa'inda shima ya saka sunnan mahaifin Nahidt da nasa mahaifin ake masu inkiya da alhusain da alhasan

Da yama likis akai hawa na dawakai da matasan fada sukaiwa jikokin sarki dan taya murna, a nan zaratan sirikansa suka sako sho tsakiya a saman ingarman dokinansu wa'inda MUHAY ya warci nasa ya neki tafkawa da gudu Malan na murmushi ya ce" Ka ga MUHYIDEEN ka fa kiyaye fa doki ne"

MUHAY ya yi yar dariya kasa kasa a tunaninsa ya ce" Sai kace ba katon Shuwwa ba? Kai dai Allah sa mu cika da imani kawai ................"

Sarki ya yi murmushi yana kawar da kansa a ransa yana godiya da Allah da ya a zanen *ALKALAMIN KADARARSU* ake cakude da farin ciki mai girman gaske, hakan ya sa komai rudanin duhun zanen ALKALAMIN suke fuskantar farin rubutunsa sannan su furta hamdalah a fili da badini wa buwayi gagara misali.....

*Alhmdulilah*

🥰🥰🥰🥰🥰 ALK'ALAMIN SAJIDA NE🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 Na gode sosai da gannin wannan rana

Readers Also Read