Kenza eBookz

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 1

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 1

Ana barin halal original by anty nice Chapter 1: Ana barin halal original by anty nice Chapter 1. *👭ANA BARIN HALAL...........*👭

4,449 words

*👭ANA BARIN HALAL...........*👭

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*✍🏻 *®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _(Gaskiya Dokin Ƙarfe🏇🏻Burin Mu Faɗakar Da Al'umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIM*

*PAGE* 1 A hankali Hajiya Ayshaa ta miƙe daga tsakiyan gadon ta jiki duk a sanyaye tayi hanyar window ɗakinta dake kallon haraban gidan ta saka hannun ta wanda yasha jan lalle mai bala'in kyau ta ɗan yaye labulen ɗakinta, idon ta cike da hawaye take leƙen haraban gidanta, inda yake cike maƙil da ƴan kai amaryah, duk da tsiyar da ƙawayenta da suke zaune a ɗakin suke mata na rashin dauriyar da tayi na tafiyan ƴar na ta ƙwaya ɗaya dal kaman rai gidan mijinta, ita dai bata bi ta kansu ba hankalinta yana ga kallon jama'an da ke ta shiga motoci don zuwa kai amaryar gidan mijinta, a hankali ta sauƙe ajiyar zuciya ta juyo tana kallon ƙawarta data dafa Kafaɗanta, cikin ƙasa-ƙasa da murya ta furta, "*Aunty Nice* ban san yayah zanyi na jure tafiyan Maamah ba", lokaci ɗaya kuma idon ta yana ƙara cikowa da hawaye.

Cike da tausayawa na irin soyayyan dana gani a fuskan ta na dafa kafaɗanta nace, "ƙawata ae aure ba mutuwa bace, ba kuma rabuwa bace, ae abun kiyi farin ciki ne ki ƙara godewa ubangiji daya nuna mana auren Maamah, wanda ko wacce uwa take fata da burin taga ta aurar da ƴarta lafiya, mudai fatan mu Allah ya basu zaman lafiya, Allah kuma ya fitowa na baya da mazaje nagari, yadda Maamah ta samu," batare dana bar inda take ba na sake riƙo hannunta nace mata, "haƙuri zakiyi ƙawata, haka aure yake, kuma idan an kwana biyu zakiji sauƙin abun, banda abunki ƙawata ae dama dole mu rabu da ƴaƴan mu watarana," jijjiga kai tayi alaman hakane ta riƙo hannu na tace, "Aunty Nice na shaƙu da Maamah sosai, sai kuma ina ganin kaman bayan zu bane lokacin daya kamata tayi aure". Hararanta nayi cikin wasa, na juya ina duban ƴar'uwarta da suka fito ciki ɗaya, wanda ta shigo tana kallon Aysha tana tambayanta kowa ya fita a ƙawayenta masu zuwa kai amaryar? Ayshaa ta juya ta kalli ƙawayen ta da suke zaune a kan gado wasu a kan kujeru wasu a ƙasa, ta sake juyawa ga ƴar'uwarta tace, " masu zuwan duk sun fita, sune a cikin motan Hajiya Hadiza, dama mutum Uku ne zasuje", Cikin hanzarin sister nata ta juya da fita daga ɗakin tana cewa, "Dama Goggo ce ta ce na tambayeki"

Haka dai muka cigaba da wunin mu har zuwa magrib, inda dayawa aka fara haraman watsewa, inda kowa ka ganni a cikin ƙawayenta hajiyoyin kansu ne, daga wanda driver ke jiranta sai wanda ita da kanta ta tuƙo kanta, biki ne dai irin bikin ƴan boko masu ji da naira, wanda komai kushewan ka kaje wurin wannan wunin sai ya burgeka, ga shi komai cikin burgewa da ilimi akayi shi, wanda duk wadata ta ɗaukaka irin na Hajiya Aysha batayi wani events masu yawa a bukin nan ba, liyafa kawai tayi haɗaɗɗe jiya jumma'a a Event Center na Bauchi, mai matuƙar ƙayatarwa, sai yau da aka haɗa ɗaurin aure da wunin bikin ɗiyarta, *NANA KHADIJAH (MAAMAH)*

Har zuwa gate ɗin gidan Hajiya Ayshaa ta rako mu, tana ƙara godiya wa bakinta da suka zo, a haka kowa zakaga ta buɗe motanta ta shiga, ko kuma drivern ta ya tuƙata, fuska ɗauke da murmushi ta juyo tana ƙara riƙe hannu na tana cewa, "Aunty Nice gaskiya nagode da ƙoƙarin da kika mun, nagode da zumunci Aunty Nice, Allah ya nuna mana auren Nabeelah da rai da lafiya", nima fuska cike da murmushi na dubeta cikin farin ciki nace, "Ameen ya rabbi Ƙawata, fatan mu Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a mai albarka, Allah yasa baɗi mudawo taron suna", Cikin rausaya da yanga wanda na lura halittan Hajiya Ayshaa ne, ta amsa mun da "Ameen ya rabbi ƙawata", sannan nace "tou yanzu ƙawata zan baki sati biyu ki huta, gajjiya ya bar jikinki, sai ki bani labarin da kika mun alƙawari, duk da dai nace nadai na rubutu yanzu" na faɗa fuska na cike da murmushi ina dubanta, Hjy Ayshaa cike da rausayar daya bi jikinta, ta lumshe kyawawan idonta a hankali kuma ta buɗe tana duba na, itama fuskanta cike da murmushi tace, "Aunty nice tawa, ae ko bai kai 2weeks bama zaki ganni, da zaran jama'a sun mun sauƙi xaki ganni har gida insha Allahu, idan kin koma gida ki gaida mun da Ɗana *BAPPAH NUHU, da ƴata NABEELAH* ki kuma miƙa mun saƙo a jama'an mu na *MUYI NISHAƊI DA NOVEL 2, har ma jama'an mu na TABITAL PULAKO* kice musu saura idan sunji labarin suyita zagina", tafaɗa tana ƙara murmushin fuskanta zuwa dariya, nima dariyar nayi nace, "insha Allahu zan ja kunnen su, duk da ma kina group ɗin kina kallon komai da jin komai", mukayi sallama na fito daga gate ɗin gidan, ita kuma ta juya zuwa wurin wasu ƙawayenta cike da rausaya, ni kuma hannu na cike da kayan tsaraban bikin da ta haɗani dasu, dayake ba mota bane gare ni balle driver, sai danayi ɗan tafiya mai ɗan nisa zuwa bakin titi, sbd unguwar tasu ta *G.R.A* wurin babu cikar abun hawa, ina isowa bakin titi na tsaya ina ɗan gyara zaman glashin fuskan na, na duba ƙafana ina kallon takalmina mai kyau na sallan bana da saura kaɗan wata taja mun asara ta sace mun shi, daga ganin jama'anta da suka zo daga cikin gari ne, wanda sukayi maƙil ata can boys quaters, wata taso ta samfe mun shi ta fallashe ni, don ni banyi niyan sayan takalmi a bana ba, atoh yana yin rayuwar nan ae sai kanayi kana tattali, na kalli dogon riga na danaje Hanco ta zizaramun wani haɗaɗɗen ɗinki, zanina dana saya a wurin *JUWAIRI* itama a *MUYI NISHAƊI* take, matar badai iya zaɓawa mutum kalan zani mai kyau ba, ajiyar zuciya nayi na ƙara duban kaina nace, "oh mace har mace amma babu mota", dariya nabawa kaina naƙara gaba kaɗan na tari adaidaita, mun ɗanyi jayayyah da shi akan ina neman ya kaini a ɗari uku, amma firr yaƙi wai sai ɗari bakwai, kaman zanyi kuka haka na shiga, sbd wasu wurin an fara sallan magrib, ina iso gida na zazzage jakan da aka haɗani da shi, cike da farin ciki nace, "shiyasa nake son bikin masu kuɗi ƴan boko, komai nasu a tsare, wato komai dai da kika sani an zuba a ciki, su turmin zani ne sallaya ne, hijab ne, kai komai dai dakika sani an zuba aciki, kuma dama tun ana saura 1week biki ta aiko mun da bocket ɗin su cincin da sauran tarkacen kayan buki, kai matar nan Hajiya Ayshaa babu laifi, dama haka wasu Allah yake haɗaka da su, sai kudawo kaman ƴan'uwa, yanzu sanin da nayi wa Hajiya Ayshaa tun lokacin da nake rubuta *BADARIYYAH* amma ji nake kaman mun shekara 40 tare, Allah kabar mana zumunci Ameen.

Ringing ɗin waya nane ya farkar dani a bacci, wurin ƙarfe 9:46am na safe, narasa dalilin dayasa ban saka shi a silent ba, haka raina bai soba na jawo wayan zan kashe, sai naga *ƘAWATA* ɓalo-ɓalo yana yawo akan screen ɗin wayata, tashi nayi zaune na ɗauki wayan, cike da yangan ta naji muryan ta tana mun sallama, "Aunty nice barka da safiya", nima cikin fara'ar da ta wadata fuskata lokaci ɗaya na maida mata da gaisuwan ta, bayan mun gaisa take cemun yau insha Allahu wajen 11am zata zo idan ina gida, babu ɓata lokaci na dirƙo a gado na nayi toilet, a gaggauce na shiryah mukayi breakfast, a take kuma na ɗaura abincin rana bamai wuya ba saboda na samu daman zama da baƙuwa ta Hajiya Ayshaa, domin hiran da zamuyi da ita yau na musamman ne, duk da wataran takan ɗan tsakura mun kaɗan daga labarinta, muyi shawara a kan wasu abun, nima nagaya mata wasu daga cikin labarina, amma yau na musamman ne, tunda tace mun tun daga ranan haihuwar ta zata bani labarin kanta, har zuwa yau ɗin nan, Rice and stew nayi, sbd ta taɓa cemun favourite ɗinta kenan.

Ayshaa matar arziki matar kirki mai alƙawari mai gaskiya, wuraren 11:00am ɗin kuwa ta tuƙo kanta zuwa gidana, cikin farin ciki na tarbeta har parlor na ta zauna, cike da fara'ar da kullum yake kan fuskanta ta dubeni tace, "Aunty Nice kinsan haka kawai kike burgeni? har wataran nakanji dama ciki ɗaya muka fito, ina son ƙamshi, ina son gayu, gashi Aunty Nice kullum cikin ƙamshi da gayu kike, ni ba gidanki ba kuma ba jikin ki ba, kin san kullum kikaje gida na sai Maamah tace kinzo," ina dariya nace "haba ƙawata ina ƙamshin yake, duk kawu na Tinubu ya takura mu ɗan turaren ma nakasa sayan dayawa yanzu, manage kawai ake ƙawata", Kallo take bin ko ina a falo na takeyi da idon ta, " Aunty Nice kedai ki gode Allah da yayi ki ƴar gayu da son ƙamshi, kinsan ƙamshi rahma ne," "hakane na faɗa ina tashi don zuwa kitchen kawo mata abun sha," "Aunty nice don Allah ga wannan tou ki shiga da shi babu yawa" naji tana faɗa, Bucket ne ɗan madaidaici, wanda yake ɗauke da dambun nama a ciki, ɗauka nayi na buɗe ina nuna mamaki fal a fuskata ina cewa "ƙawata wannan uban naman fa daga ina? Ke baki gajjiyawa ne kam"? "Wallahi wanda nasaka akayi ne wa Maamah na manta ban ɗiba miki ba, kinsan ban nutsuba wallahi sai cikin kwanakin nan nagani, tou dama nayi niyyan keda su Hajiya Hadiza da Zainab zan ɗiba muku, babu yawa ae", inji hajiya Ayshaa, godiya na mata na ɗauka nakai kitchen na adana, bayan na kawo mata abun sha, na nemi wuri a ɗayan kujeran da yake kallonta na zauna, "Ranki ya daɗe ina labari? Na furta ina kallonta fuskana cike da murmushi.

Juya idonta tayi cike da yanga da ruba, a hankali ta maida kallon ta ƙasa, kaman wanda take nazarin wani abu akan carpet ɗin, har zuwa wani lokaci kuma sai tayi dogon ajiyan zuciya, ta ɗago ta kalle ni.

Alhaji Usman Umar shine sunan mahaifin mu, Bafulatanine haifaffen garin *TAFAWA ƁALEWA* da yake garin bauchi, mahaifina cikakken ɗan boko ne kuma ɗan kasuwa ne, wanda yake da matan aure guda uku.

Uwargida Hajiya Khadija itace mahaifiyar mu, itama bafulatana ce, wanda sun fito gari ɗaya da mahaifina, wanda takeda yara guda biyar, Babban ɗanta mai suna Mohd, sai mai bi mishi Ahmad, na ukun su Umar, wanda yaci sunan kakan mu, daga kanshi sai da ta shekara takwai tukun Allah ya bata ni Ayshaa, a lokacin ta cire rai da sake wani haihuwan, sai Allah ya kawo ni, bayan shekara biyu kuma Allah ya bata ƙanwata Hafsat, wanda itace autar mu.

Hajiya Zainab itace matar mahaifin mu ta biyu, ita kuma bafulatanar toro ce, ita kuma Allah bai taɓa bata haihuwa ba, amma tana riƙon ƴar ɗan'uwanta mai suna Adda, takwarar tace amma ana ce mata Adda, ita kuma zata kai sa'ar Yayah Umar.

Hajiya Halima itace matar mahaifin mu ta uku, ita kuma ƴar garin *DARAZO* ne, na jihar bauchi, Hajiya Halima yaranta biyu ne duka mata, babbar sunanta Habibah ita sa'o'i muke da ita, amma ta bani wata uku, sai mai bi mata Raliya ita kuma sa'o'i suke da Hafsat, wacce dayawa muke cemata Hafsy.

Mahaifiyar mu muna ƙiranta Ummi, macece mai haƙuri da kawar da kai akomai, duk abunka da wuya kaji faɗa ko tashin hankali a wurinta, shiyasa abubuwa dayawa zaka ga kaman ana ƙwaranta sbd haƙurinta, acikin ƴaƴanta Yayah mohd da Yaya Ahmad da ni muka ɗauko halinta sak, inda Yayah Umar da Hafsy kuma bansan inda suka ɗauko zafin rai ba, don ko shi mahaifin mu zafin shi ba irin nasu ba, duk da shima mutum ne mai zafi da tsauri, amma ya kanyi wasa da dariya da iyalanshi, amma Yayah Umar kam zan iya cewa hatta matan gidan ma shakkan sa suke ji, ita kuma Hafsy kwata-kwata haƙuri ne bata da shi, ga tsaurin ido da rashin tsoro, don ita hatta Yayah Umar ya mata abu zata yi gaba ta ɗan taɓa gunaguni.

Hajiya Zainab kuma mukan ƙirata da Mama, ita kuma macece mai ɗan fushi, itama bata da faɗa amma abu kaɗan zai tunzurata ta yi fushi, gashi itama bata ɗaukan raini ko kaɗan, shiyasa duk rashin mutuncin Mami, wato Hajiya Halima ta kan ɗan ragar mata, don ita bata ɗaukan rashin mutunci ko kaɗan, don ko Baban mune ya mata abu atake zaka ga fuskanta ya canja, kuma zata fito ta gaya maka gaskiya, macece da bata yadda da wai wata ta fita ba a wurin mijinta, ko dan ganin ita bata haihu ba, tou bai taɓa sakawa taji ita koma baya bace, kuma ɗan kowa nata ne, saidai ita bata cika son taga yara suna raɓanta ba, dayawan lokaci idan jikokinta na wurin Adda sunzo zaka ga tana yawan kora su waje wasa, dayake Adda tayi aure har tana da yara uku, na farinta twins ne, sai yanzu da take goyon namiji.

Mamie kuma wato Hajiya Halima mafaɗaciyace na nunawa a gari, domin ita kullum garin Allah ya waye sai ta nemi faɗa, ba mijinba ba matan ba, ba kuma yaran gidan ba, duk da Yayah mohd da Yayah Ahmad sun girma, amma bata bar su ba, Yaya Umar ne kawai zai shigo gidan kaji ta ɓata shiru, har zuwa yanzu da muka fara zama ƴan mata fitinan ya dawo kammu.

Habiba itama muna kusan yanayi da ita, itama ko kaɗan bata da fitina, idan ka ganta zaka ɗauka Ummin muce ta haifeta, gata ita ma tayi farin mahaifinmu, ga ruwanta na fulani, bazaka taɓa cewa Mamie bace ta haifeta, babu garin Allan da zai waye baka ji faɗan su da Mamie ba, saboda Habiba ita tana da sanyin jiki aiki kaɗan zaka ga ta ɗauki lokaci, wanda hakan zakaji muryan Mamie kaman zata ta yar da gidan don faɗa.

Raliya kuma wayo ne kaman zai kashe ta, kuma ita ta hannun daman Mamie ce, sannan duk wani rahoto ita ke kaiwa Mamie, babu abinda takeso irin taga ana tashin hankali, nan zaka ganta tana fara'a, kaman wata shaiɗan, shiyasa wataran tana shigowa wurin mu, zakiga Ummi tana mata nasiha, kaman gaske zata rusuna, amma bata wani lokacin zata koma halinta, ita da Hafsy ko kaɗan basu zama inuwa ɗaya da Yaya Umar, suma sanin halinsu baida kyau suna ganin yazo hutu zasu rage shigowa parlon Ummi, Raliya munafurci da neman tsokana, hafsy rashin kunya, gashi kullum suna tare, amma baki mintuna kaɗan zakji sun kacame da dambe, akansu kullum sai Mamie ta shigo tayiwa Ummin mu rashin kunya da rashin mutunci.

Gidan mu gida ne mai girman gaske a G.R.A, Sakashim road, kina shigowa gidan filine mai girman gaske, wanda idan nace zai ɗauki mota guda ishirin tou banyi ƙarya ba, don idan ana hidiman biki a sake akeyin komai, duk wani programm a wurin ake yin shi, gidan sama ne side ɗin Baban mu, a side ɗin shi kuma idan kin sauƙo ƙasa akwai wani dogon korido, wanda zai kaiki side ɗin ko wacce mace a cikin su, wanda tanan wurin kowa take shigowa side ɗin Baban mu.

Ta waje kuma agefen dama flat ne guda mai ɗauke da parlor da ɗakunan bacci guda uku, wanda anan ne ɗakun su Yaya mohd yake kafin yayi aure, wanda yanzu daga Yaya Ahmad ne sai Yaya Umar.

Gefen hagu kuma shima kaman na su Yayah Ahmad yake, shima parlo ne da ɗakunan bacci guda uku, shi kuma Kakar mu ce Hajiya Ummah ce a zaune a wurin, amma bata daɗe da dawowa wurin ba, don da tana garin jos ne tana aure, rasuwan mijinta wanda bayan rasuwar kakanmu ta aure shi, bata haihu a garin jos ba, shiyasa yana rasuwa Baban mu ya dawo da ita gidan shi, tunda yanzu *TAFAWA ƁALEWAN* Baffanun mune guda biyu a gidan, wanda suke uba ɗaya da mahaifin mu, shima gidan Baban mu ya gama gyara shi, idan kinje zakiji kaman a bauchi kike, domin bai rasa komai na jin daɗin rayuwa ba.

Baban mu su uku ne a wurin mahaifiyar su, shine Babban cikin su kuma shine namiji a cikin su, sai mai bi mishi ita ce mai sunana, tun tana ƙarama Allah ya mata rasuwa, sai ta ukun su Aunty Rakiya, Mijinta babban mai kuɗine, wanda ya riƙe manyan muƙamai, da suna zaune a lagos ne, amma zuwa yanzu yayi ritire ya dawo bch da zama, inda suka ƙera babban gida a Fadaman mada, Aunty Rakiya akwai kaman ceceniyar hali tsakanin ta da Yaya Umar, gashi dama ɗan gidan tane, domin ɗanta na 2 Ishaq abokin shine, itama babbar ƴarta mace ce, Nana Asma'u, itama ta daɗe da aure a yanzu, sai dai itama ɗanta guda ɗaya dal, Aunty asma'u ma'aikaciyace a CBN, tana zaune a garin Abuja.

Aunty Rakiya mutumiyar Ummin mu ce sosai, domin ita duk wannan aure-auren da Baban mu yayi takaici ta ke ji, domin ita macece mai tsananin kishi, ko kaɗan babu fuska a wurinta idan tazo gidan mu, ko wacce mace kuma Allah yasa suna shakkan ta, domin ita ɗin favourite ɗin Baban mu ne da kuma Hajiya Umma.

A gidan mu akwai parlo guda ɗaya mai girman gaske, wanda yake saman site ɗin Baban mu, parlo ne mai ɗauke da dining section mai girma, shima yana ɗauke da dining table mai girma, mai ɗaukan mutane 12, sannan doka ne a wajen Bban mu duk lokacin cin abincin dare dole ne a haɗu a wannan wajen, aci abinci tare kuma ayi hira tare, wanda rana ɗaɗɗayane mamie baza tayi faɗa da mutane a wajen ba, ƙarshe mama tashi take suyi barambaram ta bar wurin, shi kuma Yaya Umar duk ranan da yazama yana gidan mu tou tabbas idan ranshi ya ɓaci da faɗan su ƙarshe akan Raliya da Hafsy yake sauƙewa, daga nan kuma ya bar wurin ya koma side din Hajiya Ummah, akasarin lokuta shi da Yayah ishaq sun fi zama a side ɗin kakarmu.

Mamie bayan masifah ita macece mai yawon asiri, wanda kowa na gidan yasan da wannan ɗabi'an nata, amma Baban mu kuma baya yarda, don shi yace bai yadda da asiri ba, shiyasa take tsula tsiyar ta yadda taga dama, gashi ko kaɗan Aunty Rakiya basu shiri, inda Allah yayi taimako kuma tsoro da shakkan Aunty Rakiya ta keji.

Yaya mohd muna tsananin shiri da shi, domin komai nashi ni yake nema, muna jss 3 nida Habiba aka fara maganan auren shi da wata budurwar shi ƴar maiduguri, ƙanwar abokin shine, tazo service bch sai ta zauna a gidan mu, sunan ta Bintu, gaskiya zan iya cewa na daɗe banga mace mai kyau da tsarinta ba, gata ƴar gayu na nuwa, naji daɗi da farin ciki danaji Yayah na danafi so zai auri Aunty Bintu, a site ɗin Ummin mu ta zauna, gashi tana bala'in kyautata mana, kullum da safe idan tana shirin fita inda take service bana gajjiya da ganinta, ga wani ƙamshinta kaman nayi yaya nakeji. "Aunty nice ranan dana fara ganin ki naji kaman da Aunty Bintu na haɗu, saboda ƙamshin kanuri da naji kinayi, sai naji kema ina ƙaunar ki kwatan kwacin yadda naso ta" Ayshaa ta faɗa tana kallo na, nima cikin ƙara walwala fara'ar fuskata nace, "Aysha kina koɗani dayawa fa, yanzu matan *MUYI NISHAƊI* idan sunji ki sai su ɗauka haka nake fa da ƙamshi, har naje mrs Al'ameen Da takwararki Aisha jewal, da maman fodio sukawo mun ziyarar bazata" na faɗa ina ƙara murmushin fuskata.

Itama Aysha cike da fara'a a fuskarta tace, '"gaskiya ne ae Aunty nice, nidai haka kawai kina burgeni kuma ƙamshin ki yayi daɗi, dole ma ki haɗani da wacce kike sayan turarenki a wurinta, duk da dai Aunty Bintu bata rageni da turare ba har yanzu.

lokacin da maganan auren Yayah mohd da Aunty Bintu ya taso gadan-gadan, lokacin tagama Service har ta koma Maiduguri, Ummin mu ta wakilta Adda ƴar gaban Mama da wata ƙanwar Ummin mu wacce ake ce mata Goggo, itama anan bauchi take aure, suka wuce lagos domin acan Aunty Rakiya take aure lokacin, acan suka haɗu aka haɗo kayan aure na garari, kinsan auren ƴan maiduguri da ƙaryan kaya dai Aunty nice?

Girgiza kaina nayi alaman hakane,ina ƙara saurarenta, domin ni gaskiya bana gajjiya da kallon Ayshaan nan, don ni mace mai yanga burgeni takeyi sosai, ido na zura mata ina sauraranta.

Kaman tasan abinda yake raina, sai ta sake juya kyawawan idon ta cike da rausaya ta kalleni tana ƙara gyara zaman ta, "kina ji ko Aunty Nice, lokacin da suka dawo daga haɗa kayan auren ranan anyi tashin hankali agidan mu da Mamie, domin dama tana cike da bala'in tafiya da Adda da akayi lagos ɗinnan, tana jin haushi ba'aje da ita ba, ganin kayan kuma ta tada wani bala'in kan wai ana so duk kuɗin Baba ya ƙare, don ita bata yadda Yaya bane ya haɗa wannan uban kayan, ta manta Yaya Mohd a NNPC yake aiki, kuma mutumin nan yakai 5years yana aiki a wurin, gashi darajan Baban mu yasamu wuri mai maiƙo, Yaya Ahmad Barrister ne, shima yana Abuja da zama, Yaya Umar ne kawai ɗalibi, don shi kam da saura. Duk yadda mamie ta kai da son ta raba tsakanin ƙawancen mu da Habibah abin ya gagara, don rana ɗaɗɗayane bata shigowa side ɗinmu tayi masifa wa Ummi, akan dole idan mun shigo Ummi ta kora Habiba, sbd ni babu yadda za'ayi naje side ɗinsu sai mamie ta kore ni, har nadawo ma bana son zuwa, saidai ita Habibah tazo wurina, amma ko sau ɗaya Ummi bata kula ta, watarana ne ma Yaya Umar yazo suna zaune da Yayah ishaq a parlon mu sai ga Mamie cikin bala'inta ta shigo neman Habibah, inda ta shiga batanan ta ke fita ba, gashi bata san Yayah Umar yana ciki ba.

Ranan na tabbatar Yayah Umar gwarzo ne, don tsabar masifah da ƙyar Hajiya Ummah ta shigo da Mamah suka fitar da shi, don rantsuwa yayi akan idan Mamie ta sake shigowa tayi rashin kunya wa Ummin mu ko ta nemi shiga tsakanina da Habiba wlh sai ya mata dokan tsiya, jikin shi har wani rawa yakeyi kaman wani ɗan gunda.

Ita dai mamie jiki a sanyaye taja tsumman ƙafarta ta juya tayi side ɗinta, ƙasa-ƙasa ta ke magana akan yajira dawowan Abban mu, wlh bazata yadda ba, aiko batayi nisa ba, ya biyo bayanta idon shi kaman zasu zazzago yana zare su yace, "wlh ummi na rantse miki da Allah idan baki gayawa Abba baki cika mai sharri ba, kuma ni da kaina zan gaya mishi, ya kuma ja miki kunne akan zuwa gefen mahaifiyata, don wlh idan kowa bai ɗauki mataki ba ni nan".... Yana buga ƙirjin shi da hannu yana nuna kanshi yace "zan ɗauki mataki mai tsauri akan ki da shegiyar munafukar ƴar ki mai kai miki rahoto".. Ya juya da sauri yana neman Raliya.

Ganin haka Ummie ta ƙaeaso wurin ta kama shi, "Umar na baka umurnin ka fita kada ka taɓa yarinyar nan," daga nan ta haɗa hannun shi da Ishaq tace sufita zuwa wurin Hajiya Ummah su zauna, bata son fitina.

Tsaki Mamah taja tana hararan Ummie tace, "amman ummin su ke ina ruwanki ne? Ki bar shi ya chasa mana munafukar yarinyar nan mana, itama uwar munafukan ae shine daidai ita", tana gama faɗa ta juya ta tafi side ɗinta, aka barni nida Habiba muna tsilli-tsilli da idanu, don Allah yana gani muna son junan mu sosai, kuma kullum Abban mu yana nuna muna musu junan mu, yana jin daɗin yadda muke tafiyar da rayuwar mu, haka ma Ummie da Yayah mohd, gashi ko sch class ɗin mu ɗaya sit ɗinmu ma yana bayan nasu Habibah.

Maƙwaftan mu muna da wata ƙawar mu mai suna Maryam, maryam itace sit ɗin mu ɗaya da ita, ita kuma Habiba suna zaune da wata friend ɗinmu Jamilah, ita jamila a fadamar mada suke, maryam kuma unguwar mu ɗaya da ita, wato G.R.A, gida ɗaya ne tsakanin mu da su, kuma tun shigan mu primary class ɗinmu ɗaya sit ɗinmu ɗaya, har zuwa yanzu da muke shirin rubuta junior weac.

Ana gama watsewa a wurin muka haɗa ido da Habiba, kaman wasu dolaye muka kwashe da dariya, Habiba ta matso kusa dani tana zare ido tace, "sis yau kam zanci na jaki a wurin Ummie babu mai karɓa na, yau kam jikina zaiyi yakuwa", tana gama faɗa muka sake kwashewa da dariya, nima cikin zare ido na sunkuya dai-dai fuskar ta, don nafita tsayi sosai, Habiba guntuwa ce kaman Mamanta, ni kuma daga Abba har Ummie dogaye ne, sai yazama gaba ɗaya ɗakin mu muna da tsayi, kuma dukkanmu farare ne sol, su kuma kasancewar maman su guntuwa ne sai Habibah ta ɗauko guntancin maman ta, amma farin Abba ta ɗauko, sbd haka banbancin mu babu yawa a haske, don ita har taso ta fini, don ni na sirka da ɗan jaja haka, amma Raliya baƙa ce, ta ɗauko kalan fatar Mamie da kamannin mamie, sai dai ita doguwa ce, don tsayin su ɗaya da hafsy, "Sis kawai mu gudu wurin hajiya ummah, har sai Abba yadawo munga abun da hali yayi, idan ba haka ba ina tsorata miki na jaki da zaki sha yau", na faɗa ina kama hannun ta mukayi wurin kakarmu.

Ana daf za'ayi sallan magrib Abba ya dawo daga tafiyan da yayi zuwa Abuja, ta window muka leƙo nida Habibah muna ganin masu aiki dasu hafsy da suke masa sannu da dawowa, inda ya rungume hafsy da Raliya a jikin shi, Abba yana son mu, wani irin son da ko iyayen mu mata basa nuna mana, da gudu muka fito mukayi wurin shi, fuskar shi cike da fara'a yana, "oyoyo ƴan biyu na," mukaje ya rungume mu, muma muna mishi oyoyo Abba, Yayan Ahmed ne ya fito a motan shima fuskar shi cike da farin ciki yana kallon mu, hannun shi riƙe da hannun hafsy da raliya, don tare suka dawo da Abba, farin ciki kaman zanyi yaya ganin an fito da kwakwa daga boot ɗin Abba, ina kallon Habiba nace, "sis gobe akwai kwakumeti a gidan nan", Abba ma yana dariya yace, "ae saboda ku na ce dole a sayo kwakwa a gidan nan, ƴan biyu na zasu mun kwakumeti naci,"

"Abba mu kuma fah"? Cewar raliya da ta zunɓuru baki gaba, tana sake hannun yayah Ahmed ta taho wurin Abba, "ku kan ae baku da tsaraba sbd yawan masifar ku da faɗan ku, shiyasa ma ku bana ganin ku kaman ƴan biyu," Abba ya faɗa yana wuce side ɗin Hajiya Ummah, sannan yacewa Yayah Ahmed yayi alwala bari yagaida jatumar sa sai su wuce masallaci.

Readers Also Read