Ana barin halal original by anty nice - Chapter 2
Ana barin halal original by anty nice Chapter 2: Ana barin halal original by anty nice Chapter 2. Yayah mohd da Yayah Ahmed basu da hayaniya, amma na Yayah…
4,370 words
Yayah mohd da Yayah Ahmed basu da hayaniya, amma na Yayah Ahmed har ya ɓaci, sbd shi komai kukeyi baya tankawa, maganar ma da ƙyar yake iya buɗe baki yakeyi, don kullum ina jin Ummie tana cewa yayah yake iya magana a kotu? Wucewar Abba kaɗan raliya ta juyo ta zabga mana harara, sannan taja tsaki tace, "wallahi duk iya munafurcin ku kwakwan nan namu ne mu duka, tare za'ayi kwakumetin, ko kuma kunayi na faɗawa Ummie ta ƙwace ta raba mana dai-dai wa dai-dai, kunga ku da shan wahala mu kuma da morewa"' ta faɗa tana murguɗa mana baki kaman sa'o'inta.
Mari hafsy ta kai mata a bakinta tana, "mumafuka mai zubin shaiɗanu, shiyasa kikayi baƙi ke kaɗai a gidan nan sbd baƙin zuciyar ki" aiko raliya ta juyo zasu kama dambe da masifar su, Yayah Umar ya daka musu tsawa wanda lokacin fitowar shi kenan daga side ɗinsu, marasa kunyan banza da gudu sukayi cikin gida, amma bakin Raliya bai rufa ba tana cewa, "wallahi sai na haɗaki da ummie, kince a wurinta na ɗauko baƙi da baƙin hali", mudai kallon mamaki kawai muke musu nida habibah.
Kama hannu mukayi muka wucce side ɗin hajiya ummah, dai dai lokacin kuma yayah umar suna gaisawa da yaya Ahmed, hannun su riƙe da na juna, sbd gaskiya yayuna ukun nan akwai ƙauna mai girma a tsakanin su, idan ka gansu kaman abokaina, muma wucewa mukayi side ɗin Hajiya Ummah inda muka haɗu da Abban mu yana shirin fitowa.
Bayan anyi sallan ishaa an haɗu a dinning wurin cin abinci, ido na nida Habiba zuru-zuru muna jiran ko mamie zatayi wani magana akan faɗan ɗazu amma shiru bata ce komai ba, sai dai hararan mu da takeyi a kaikace nida Habiba.
Ana gama cin abinci Yayah Umar ya dubi Abban mu da ke shirin tashi ya wuce cikin parlon yace, "Abba ina son magana da kai" da ɗaurarren fuskan shi kaman shine maigidan ba yaron gida ba, da sauri Mamie ta ɗago tana duban shi, ita kuwa Ummi baki ta buɗe tana, "Ubanah bana son dogon magana fah" babu ɓata lokaci Abba ya ɗaga mata hannu, da nufin ta mishi shiru, yana bada hankalin shi gaba ɗaya kan Yayah Umar.
Girgiza kai Mamah tayi irin alaman Abba ya mata dai-dai, tana hararan Ummie.
"Abba dama alfarma nake nema a wurinka, ina so kayiwa mamie magana akan duk wani abu a gidan nan da ya faro ko akan yara ko na cikin gidan nan, kada ta sake zuwa kan ummie da faɗa, idan ba haka ba wlh Abba wataran labarin da za'aji bazaiyi daɗi ba, don gsky ni haƙurina yana gazawa," ya faɗa yana hararan Raliya ƙasa-ƙasa.
Kaman Abbah bazaice komai ba, har zuwa wani lokaci idon shi yana kan Yayah Umar, zuwa wani lokaci kuma ya maida kan ita mamin, gyaran muryah yayi sannan yace, "Baba nah kafin kagaya mun kai Ummah ta gaya mun, kuma insha Allahu zamu zauna da iyayenkan, kuma zanyi maganin komai, zan kuma kawo ƙarshen komai insha Allahu, kaima ina son ka dinga haƙuri da wani abun, kana kuma kawar da kanka akan su", da sauri mamah ta buɗe baki cikin ɓacin rai tace, " sai an kai uwarshi ƙasa tukun zaiyi magana? Wannan ae ba shari'a bane, shiyasa kullum Hauwa takeji a ranta abun da takeyi dai-dai ne, don ba tsawatar mata akeyi ba" ta faɗa tana miƙewa tsaye da niyyan barin wurin, Abba ya dakatar da ita, "Zainab bawai bana lura da abinda yake faruwa bane ko bazan ɗauki wani mataki akai bane, nan ae ku da yaranku ne zaune, kuma naji ƙorafin Baba na, insha Allahu zan zauna daku muyi magana, ba lallai sai a gaban su ba", ya faɗa yana mai da kallon shi kan mamie da ta wani tura baki gaba kaman zata zunduma ashar, sai dai babu dama, don daga Mamah har Yayah umar tana shakkan su, haka kowa ya tashi yayi side ɗin shi, amma Yayah mohd, yayah Ahmad, Yayah Umar, Hafsy duk miƙewa sukayi suka wuce side ɗin Ummin mu, mu kuma ganin Abba zai tashi da wurin mukayi hanyar Hajiya Ummah, don gaskiya yau babu mafaka a wurin Habiba sai chan, munafukar kuma Raliya muna shirin fita tana hararan mu, mudai bamuyi takanta ba muka wuce.
Hajiya Ummah tana ganinmu ta harare mu, cikin hararan mu tace, "nice rumfah sha shirginku ko? Idan ana zaman Allah da annabi ne ina binku kuzo mu kwana sai kuƙi, ku masu iyaye sai ku gudu chan, idan sun gallabe ku kuma sai ku kwaso mun ƙazamin jikinku kuzo ku takurani ni da gidan ɗana," ta faɗa tana maida kanta da hankalinta kan T.V, dariya muke mata Habiba ta faɗa jikinta tana dariya, ni kuma na zauna wurin ƙafanta ina nawa dariyan, Habiba tana neman tsokano mana ita tace, " hajiyar mu maganin kukanmu, idan bamu zo wurinki ba wurin wa zamuje? Kinyi na Abban mu kina namu, ae kin muri duniya da abunda yake cikin duniyan, ƴaƴanki su miki jikoki su miki", nima ina dariya na chabke da "gashi muna haihuwa ƴaƴanmu na fari masu sunanta zamu saka".
Buɗe baki tayi tana kallon mu cikin mamaki tace, "amma Allah yayi manyan maƙaryata a nan, ae idan na samu kuka cigaba da zumunci dani ma ae nayi sa'a, da shegen bakin ƙaryanku ae kuna haihuwa kowa wa uwarta zatayi wa mai suna, babu ma ya waƴennan gardawan Umar da Ishaq, duk sun lotsa mun gado da kujeru na, amma nasan sunayin na kansu bazasu taimakeni ba, ballantana mai suna, sai gatan kashe mun kujeru da yawan zamansu" ta faɗa fuskanta a murtuƙe, dukkan mu dariya muka kwashe da shi, habiba tana ƙara ingiza magana da cewa tun ba ma Yayah Umar ba, don naga ya sakoki a gaba da labcecen jikin shi, juyawan da zanyi kawai sai na ganshi a tsaye a bakin ƙofan parlon, ae banbi takan Habiba ba na rantama ɗakin Hajiya ummah da gudu na murɗa key, ina jin dariyar Hajiya Ummah don babu abinda takeso irin taga yayah umar yana labtan mu, ina jingine da ƙofan ina dariyar Habiba ko ita ina tayi, don naji ihun ta da gudun ta. Muna shiga SS 1, first term ɗin mu aka fara shirin biki Yaya mohd, wanda bai wuce 2weeks ba ayi, Wani farin ciki nakeji sbd bikin da za'ayi a gidanmu, gashi Yayah Ahmad ya mana ɗinkuna kusan kala biyar-biyar mu da su Raliya, abun daɗin ma har da Maryam friend ɗinmu, mudai shagali babu kama hannun yaro, gashi dodon mu baya nan, don sai ana satin ɗaurin auren naji ance zaizo, kuma fah Yaya Umar duk zafin shinnan yana mana so na ban mamaki, shidai daga mamie tayi wani rashin hankali ne zaki ga ya wargaza hankalin kowa a gidan, don ni gaskiya bansan wani irin so yakeyi wa Ummie ba.
Biki ya kankama Aunty Asma'u tazo haka ma Adda ta iso, abun farin cikin ma nida Habiba an bar mu zuwa maiduguri wurin event ɗin amaryah, wanda tafiyan mu da Aunty Asma'u ne.
Aunty Asma'u , Adda, da goggo ƙanwar ummin mu duk zasuje, sai kuma wata ƴar ƙawar ummin mu, sai ni da Habiba za'ayi tafiyan, mota biyu zai ɗauke mu, Yayah ishaq zai ja motan Aunty Asmau, Yayah Umar zaija motan Adda, sai kuma gayyan motan abokan ango da zasu ɗauko amare, Yayah Ahmad dai da Abba zasu haɗa hanya, su kuma ana gobe ɗaurin aure zasuje da tawagar Abba.
Maiduguri munga karamci munga kara, an mana karɓa na ban girma, munga shagulgula na har kan arziki da mutunci, a mutunce akayi komai aka gama, ranan ɗaurin aure muka kama hanyar Bauchi cike da farin ciki, ga kyakkyawar amaryar mu Aunty Bintu.
Mun iso bauchi wuraren ƙarfe uku na yamma, haka kuma a gurguje aka shiryah domin buɗan kai da za'ayi a gidan mu.
Aunty Rakiya ne ƙirjin biki, sai kai kawo takeyi a filin gidan mu, inda ake decorating wurin saboda buɗan kai, ana sallan la'asar wurin ƙarfe biyar aka fito wurin buɗan kai, ranan naga washe baki a wurin Yayah Mohd, ashe yana fara'a haka? Mudai muyi nan muyi nan, gaba ɗaya farin ciki cike da zuciyar mu, anyi taro lpy an gama lpy, inda amaryah da ango sunga karamci, su kansu ƴan maidugurin sun yaba da karɓan da aka musu.
Bayan sallan ishaa akayi rakiyar amarya gidan ta dake *TAMBARI ESTATE* Gida ne mai ɗauke da flat guda uku, ko wanne yana ɗauke da three bedroom da parlor 2, Abba ne ya gina musu su uku ƴan samarin shi, wanda ansha artabu da mamie lokacin da Abbah ya ɗauke su sukaje ganin gidan, don ko gaya musu yana ginin baiyi ba, sai da aka saura 1month bikin ya kaisu, ya kuma shaida musu halak malak ya damƙa su, amma na yayah mohd ne kawai akayi penti, sauran biyun yace kowa ya tashi auren shi ya fente.
Mamie kasa daurewa tayi a lokacin, zuciyar ta kaman zai fashe tana huci tacewa Abba, "amma dai Abban su duk wani dukiyarka anan ka ƙarar ko? haba jama'a idan mutum yace ba'a mishi adalci ace ba haka ba, yanzu namu yaran idan sun tashi aure sai ace komai ya ƙare, kuma ana magana ace kishi ne", ta faɗa kaman zata fashe da kuka.
Tana rufe bakinta, mamah tayi charaf tace," wa na zaice kishi? Sai da ace hassada da jahilci, idan bake kanki baya saiti ba mutum da ƴaƴan shi har kina da bakin cewa wani abu idan ya musu har kan arziki? Wannan hassada naki akanki zai ƙare, naki yara matan cewa akayi ya basu wurin zama idan zasuyi aure ko me?"
Harara mamie tayiwa Mamah ƙasa-ƙasa don tana shakkanta kuma tana tsoronta, Abba ne duk ya dakatar da su idon shi akan mamie yace, "matsala ta da ke baki da wayo, baki da dabara, huruminane ko kuma dole nane akan ƴaƴana mata? Kinga anyi auren su sun wofinta ne? Don Allah Halima bana son rashin hankalin ki, shiyasa abu dayawa bana son sanar dake sbd ƙorafinki da nuna kishinki akai". Ya faɗa yana barin wurin ya wuce wurin motan shi.
Ummin mu batace komai ba sai murmushi dake sauƙe akan kyakkyawar fuskanta, haka zalika daga Yaya mohd, Ahmad, umar, ni da sauran ƴan'uwa na mata babu wanda tace wani abu, sai duk muka juya mukabi wurin mototi guda biyu da mukazo a ciki, Raliya ce kawai cikin mu take ta wani harare hararenta na banza da wofi, mudai cike da farin ciki.
Bayan ankai amaryah gidan ta, ana ta saka albarka, a gidan da musu fatan zama lpy, kaii Aunty nice gidan yayi kyau, ranan na ƙara tabbatar da ƴan maiduguri ƙarshe ne a wurin ƙyale, gidan nan kaman kada mu tafi ga wani ƙamshi kaman babu gobe, inda muke tsaye nida Habiba da maryam wata yar Aunty Bintu ce tsaye, suna ce mata yah falmata, nidai matsawa da hanci nakeyi ina shinshina laffayanta Aunty nice, tafaɗa fuskanta ɗauke da dariya, nima ina dariyan nake ƙara maida hankalina kanta, sannan nace mata ae Hajjajo ƙamshi rahma ne, tana dariya tace rahma ɗaya ko biyu, ae nidai tun ranan naji babu abinda nake so irin ƙamshi, muna ji muna gani Yayah umar ya tiso ƙeyar mu muka dawo gida, wanda har ga Allah bamu so ba, a wautar mu bamu ƙi kwana a chan ba.
Da safe kuwa bayan sun karya sun shiryah suka biyo gidan mu domin yin sallah ma da mutanen gidan mu, saboda ranan duk zasu juya maiduguri, wurin 11:00am duk sun kama hanya cike da karamci irin namu na ƴan bauchi da iyayen mu suka shiryah musu.
Bayan biki da sati biyu yayah mohd ya kawo Aunty Bintu gidan mu ta gaishe da iyayenmu, murna kaman babu gobe, don muna dawowa gida daga school muka ganta a parlon Ummin mu tana zaune, a gefe ɗaya kuma ummin ce zaune suna ɗan taɓa hira kaɗan kaɗan, tunda dama akwai sabo a tsakanin su, da gudu naje na mata oyoyo baki na kaman zai tsage don murna, itama fuskan ta cike da farin ciki tace, "ae nayi fushi daku Aysha, daga ke har habiba babu wanda ya leƙoni"? Ina dariya nace zamuzo Aunty Bintu, mun koma school ne ga kuma Haddan mu an matsa mana zamuyi sauƙa this year.
"Masha Allah" Aunty Bintu tace, sannan na miƙe nayi ɗakin mu domin na chanja kaya.
Har sao wurin nine na dare tukun yayah mohd ya ɗauke ta suka tafi, nida hafsy da habiba har wurin mota muka rakata, muna mata alƙawarin ɗin zuwa mata ranan friday.
Motan su bai gama fita ba motan yayah Ahmad ya shigo gidan ,muma fasa wucewa mukayi cikin gida domin mun jiran ƙarasowan shi, don yamana alƙawari bai cika ba, gara kafin ya bar garin a san nayi.
Bayan sun gaisa da yayah mohd ya ƙaraso ciki da motan shi, yana buɗewa muka ganshi bashi kaɗai bane ashe, tare da wasu abokanshi muka gansu.
"kaiiii" naji muryan Habiba tana faɗin, sisto juyo kiga wasu farare tare da yayah Ahmad kaman wasu halfcast, da sauri na juyo ina duban su, nace "hala twins ne, ina Yayah Ahmad ya samo fararen mutane haka? Har sun fishi fari" muka haɗa ido nida Habiba, sbd kowani magana ɗaya tayi tou ɗaya tasan ina maganar ɗayan ya dosa, riƙo hannu na habiba tayi muka ƙarasa wurin Yayah Ahmad, hafsy na binmu abaya tana cewa, "inaga fah inyamure ne, don farin su yayi yawa, ko kyau basu mun ba sbd farin su yayi bauu, amma kukuma nasan sun burgeku, mayun farare kaman ku ba fararen bane", babu wacce ta kula ta muka ƙarasa wurin yaya Ahmad.
Hannu ya miƙo mana yana "ƴan biyu Abba yyh kuke? Fuskan mu ciki da farin ciki muka miƙa mishi hannun mu mukayi musabaha, ranƙwashi ya kaiwa hafsy yana cewa, "jerry ina tom"? Baki ta turo tana "Allah sarki yayah Ahmad niƙan a gidan nan kaman kowa bai damu dani ba wlh, kowa Sai ƴan biyun Abbah"? Ta faɗa tana hararan mu nida habiba, mudai dariya mukeyi muda Yayah Ahmad, juyawa yayi yana duban abokanshi cikin shiru-shirun shi da rashin son sakewa da dogon magana yace, M.G, da A.G ga sisters ɗina, yana nuna mu yace waƴan nan sune favourite sister ɗina, suɗin kaman twins suke ga hankali, wannan kuma yana nuna hafsy yace autar mu kenan, ita kuma twin sister nata halin su ɗaya basuji, yadda kasan tom and jerry haka suke, basujin magana basu son zaman lpy", ya faɗa yana riƙo hannun hafsy data turo baki tana hararan mu.
Wanda naji yayan mu ya ƙira da M.G da AG ɗin muka juya muna gaishe su, suma cike da murmushi a fuskansu suka amsa mana, inda ɗayan bayan gaisuwan bai sake cewa komai ba, saidai fuskanshi ɗauke da murmushi yana duban mu, shima ɗayan fuskanshi cike da murmushi yake ƙara mana tambaya akan ajin mu nawa? Habiba ce ta gaya mishi ajin mu da sunan mu, bayan ya sake tambayanta, sannan ya dubi hafsy yace ke kuma kece tom ɗin ko jerryn?
Dukkan mu dariya muka kwashe da shi, banda ita da tasake turo baki gaba tana cewa, "wallahi sunana hafsy ne" Kawai dai kowa a gidan yafi son sune shiyasa ba'a ganin laifin su, amma wlh manyan ƴan tawayen gidan mu kenan, kuma basu ji ga iya haɗa munafurci," ta faɗa tana ture hannu na da nakawo kusa da ita, yana dariya yace, "tou nidai banga alama ba, nima ina ga sune favourite sisters ɗina, ke kuma inaga friend ɗina zaki zama" still dai fuskan shi cike da fara'a, daga gani shi yana da ɗan surutu, amma ɗayan tunda ya amsa gaisuwan mu bai sake cewa komai ba, saidai yana bin dukkan mu da kallo, shima kuma fuskan shi cike da murmushin, amma dai bai sake tankawa ba.
Wucewa side ɗin su Yayah Ahmad sukayi, bayan muma mun juya side ɗin Hajiya Ummah, hafsy ko hararan mu tayi ta wuce cikin gida, kaman wasu munafukai, muna shiga parlon hajiya umma muka zauna a kujeranta two sitter muka haɗa kanmu wuri ɗaya domin tattaunawa, kallo ta bimu baki a buɗe tace, "wannan munafurcin da baya sakin ku kuma fah" kudai yaran nan kullum aka ganku cikin nuƙu-nuƙu na gulmah kuke, nidai duk wacce tayi gulma na nabarta da Allah, domin duk abun mutum da gulmanshi nan gidan ɗanane, iko nane, idan ma hassada kukeyi ya kawo ni nan sai kuyi tayi" ta ƙara faɗa tana hararan mu.
Mu dai dariya muka kwashe da shi muna kallonta, habiba ce ta bata amsa da, "in banda ke hajiya ummah gorin na menene? Muma idan muna raye zamu haifi yaran da zasu mana gida gidan sama ma mu wataya, bake da aka miki ɗan akurki ba," ta faɗa tana taɓa ƙafa na, don mun san yau zamusha gori iri-da kala, don hajiya ummah ji takeyi mu kishiyoyinta ne a wurin Abban mu, don ko shigowa mukayi tare da shi ta dinga hararan mu ƙasa-ƙasa, watar tace amma dai kai kan jakin ƴaƴa nane, baka kama gabanka suma su kama gaban su? Amma kullum kana naniƙe da su, su hanaka yin abun kanka?
Aiko kaman habiba ta jefa mata ƙarfe a tsakarka ta zabura tana nuna mu da yatsa, "ahir ɗinku wlh, don babu wacce zata haifi ɗa irin wanda na haifah, don ni ɗana ɗaya ne tamkar da dubu,don ko gwabna bai kai shi kuɗi ba, gwamne me a kusa da a kusa da usmanu nah? Ae inaga idan gwamnaty ta kasa biyan albashi usmanuna zai iya bawa gwamna bashi yayi albashi na wata ɗaya kam, kuma arzikin shi bai taɓu ba, don kaf Tafawa ɓalewa ba'a taɓa haihuwa irin nawa ba, kawai dai ya haɗu da jarabawan tara mata marasa abinyi ne sai abun da ya musu", ta faɗa tana mana kallon banza.
Dariya muka kwashe dashi, habiba tana cewa, "a tafawa mahaifiyar Ɗangoten bauchi" bakuyi gatse ba marasa kunya ni nan da kuke gani nafi uwar ɗangote farin cikin haihuwar ɗa mai albarka,
Hajiya Aysha tana duba na cike da dariya tace, "Aunty nice kinsan kakarmu irin mutane ne masu son nasu, kuma har cikin zuciyarta ji take duk ƙasan nan babu wanda yakai Abban mu sukuni, shiyasa muke manna mata hauka akan Abban mu yafi gwamna kuɗi, kuma ta hau ta zauna," Dariya nayi ina ƙara maida hankalina wurin Hajiya Aysha, ina kuma ƙara jinjina irin baiwar kyau da Allah ya mata, domin murmushi fuskanta ba ƙaramin kyau yake ƙara mata ba
Tun ranan da mukaga abokan Yaya Ahmad bamu sake ganin su ba, kasancewar shima ba a gari yake zama ba, amma rana ɗaɗɗaya ne bamu hiran su nida Habiba, wanda har ta kai mun bawa Maryam labarin su da irin farin su, cikin zolaya maryam ta kalle ni tana dariya, "amma dai Ayshaa ke kike koyawa habiba ganin kyaun farin mutum? Kuma daga dukkan alamu kin ƙyasa? Inaga gara a sanar da yayah Ahmad"'
Hararan ta nayi nace, "ban dake maryam yaushe ma na girma da har zanga wani nace ina so? Soyayyan ma ae bamu kai ba, kuma bani da class ne zan ce ina son su? Kawai ni fararen mutanene bana gajjiya da ganin su, kin san bana son baƙin fata", dukan da habiba ta kai mun ne na hankalta da kwafsin da nayi, don mantawa nakeyi mamie baƙace, haɗa ido mukayi muka kwashe da dariya dukkan mu.
Babu wasa rayuwar tana wani irin gudu, a haka yau muke kammala waec ɗin mu, kowa a cikin mu cike da farin ciki da burika kala-kala a zuciyar mu, ranan dukkan mu huɗun, ni, habiba, maryam, jamilah muna zaune kafin driver yazo ya ɗauke mu, a yanayin mu bamu da hayaniyah dukkanmu, sai dai nida habiba da maryam idan mun haɗu mukan taɓa surutu sosai a tsakanin mu, amma idan wanda bai sani bane bazai taɓa yadda muna da surutu ba, amma ita jamila da wuya kaji maganan ta, sai dai kawai ta biku da ido, jamilah bata da matsala ko kaɗan, shirunta yayi yawa, amma akwai azaban kai, domin kanta yana mugun ja sosai.
Maryam ce ta dubi jamilah tace, "yanzu besty da gaske auren za'a miki? Tou karatun naki fah"? Ta faɗa fuskanta cike da jimami, domin duk munyi shawaran karatu zamuyi a wuri ɗaya, wato ATBU, don ko jamb ɗin mu shine first choice ɗin ko wacce a cikin mu.
"Besty tou an yanke muyi auren saboda na bishi chan na fara karatuna, nima kuma gaskiya hakan yafi mun, don ina tsoron yana tafiyan nan wata ta mun wuff da shi", dukkan mu dariya muka kwashe da shi, ni kuma na zabga tagumi ina duban Jamilah cike da mamakin wai zatayi aure, cousin ɗinta ne, kaman wasu zamu shiga SS 3 yace yana sonta, kuma cikin hukuncin ubangiji yagama masters ɗin shi a London kawai ya samu aiki achan, shine iyayen su suka yanke kawai ayi auren su tafi tare, idan yaso karatun sai tayi achan.
"ikon Allah" kawai na furta ina kallon ta, sannan nace, "jamilah kuma zaki iya rayuwar auren da ɗan ƙaramin shekarunki?" kallo na tayi tana murmushi tace "me zai ban tsoro, yayah nane fah, kuma zai ɗaga mun ƙafa sai na ƙara girma yace mun".
Dariya dukkanmu muka kwashe da shi, habiba ta dubeni tana ɗaga kai cikin salon mu idan zamu zolayi mutum tace, "dogon magana" kwashewa muka sakeyi da dariya, maryam da jamilah na taya mu.
Maryam ce ta dube mu tace tou yanzu me zamuyi na event? Kun san muma yanzu bebs ne, don mun girma ta faɗa tana wani juya idanunta, shiru mukayi na zuwa wani lokaci, sai jamila ta gyara zama tace, "mummy na zasuyi liyafa ne kawai, nima bana son wani event sosai, tunda angon yace shi babu wani event da zaiyi bayan recieption da zasuyi, saboda haka ya kamata mu gwangwaje adon mu a liyafar nan.
Da yake nima bana son wani damuwa sosai sai kawai na bada ƙarfin ayi hakan, babu yadda habiba da maryam suka iya kowa sai ta amince, a haka drivern su yazo ya ɗauke ta, muma babu daɗewa aka zo aka ɗauke mu.
Bikin jamila ya gabato sai shirye-shiryen ashobi mukeyi, inda muka haɗu da wasu friends ɗinta guda 6, sai cousins ɗinta guda 2, muka zama mu 11, muke ta shiri da tsare-tsaren mu, ranan da mukaje sallon a *SHAGARI SHOOPING COMPLEX* Yayanta Aliyu ne yazo ɗaukan mu, shima yadda kika ga jamila da kyau da shiru tou shima haka yake, sai dai ba fari bane, kuma baza'a ƙirashi baƙi ba, saboda yana da haske wanda wasu zasu iya kwatanta shi da fari, amma a wurin wanda basu ganin fari sosai, lecturer ne a Federal polytechnic bauchi, yana Computer depertment, ɗan gayu ne na nuwa, kuma daga ganin shi mai tsafta ne, don motan shi wani irin azaban ƙamsh yakeyi, ga kuma sanyin A.C
Gidan mu aka fara wucewa ya sauƙe mu, sannan suka wuce tare da jamila da wata cousin ɗinta Ummitah, daga kaduna suka zo, kuma sun shaƙu sosai da jamilah, saboda kullum hiranta Ummitah ne.
Muna shigowa gate ɗin gidan mu Habiba ta juyo tana kallona, fuskan ta cike da gulmah tace mun, "sisto naga daga dukkan alamu Yayan jamilan nan hankalin shi yana kanki, duk wani nutsuwar shi ina hankalce da shi, sai kallonki yakeyi, ita kuma ummitan nan inaga sai wani rawan kai take mishi, har da wucewa gaban mota ta wani zauna, bayan duk hankalin shi baya tare da ita,"
Hararanta nayi nace, "ke kuma cutar gulmar ki ta motsa duk kin kafe shi da ido, saidai in kece ya miki har ya birge ki, don ni wnn ba layi na bane, fari nake jira", ina faɗan haka na juyo ina kallon habiba na kama haɓa na, "habiba niko ina dai labarin fararen abokanan yayah Ahmad ɗinnan? Kullum yazo ina hankalce ko zan sake ganin su amma shiru, ko dai aljanune?" na faɗa ina ɗan zare ido.
Dariya ta kwashe da shi tana cewa, "inaga wannan karon idan yayah Ahmad yazo dole ayi cikiyar su, kada naje sun kama kurwar ƙanwata," hararanta nayi nace, "me kike nufi? Kina tunanin sun shiga raina ne? Kuma waye ƙanwarkin?" Allah sarki habiba na, wato Aunty nice kullum kika ga faɗan mu tou akan shekaru ne, kowa bata so ace itace ƙarama, a haka ma habiba da tasan ta ɗan fini da kaɗan wataran ta kance ta bar mun girman, ta ƙara mun shekara uku ma bayan wata ukun, ni kuma na dinga tsokananta ae tunda na fita tsayi tou na rigata zuwa duniya, a haka muke kullum cikin soyayyar junan mu, donni son da nake yiwa habiba ko hafsy da muke ciki ɗaya bana mata.
Washe gari tun safe muka tafi gidan su jamila, saboda wacce zata mana make-up da wuri zata zo.
*EVENT CENTRE* a wurin aka shirya yin liyafan, masha Allah amaryah tayi musulmin kyau ita da ƙawayenta, sai wani jin falli mukeyi irin muma mun girman nan, har mun fara aure, da yake shine biki na farko da muka farayi na ƙawayen mu sai abun ya ƙayatar da mu sosai, sai wanni basarwa mukeyi muna wani rangwaɗa irin ƙawayen nan, Aysha ta faɗa fuskar ta kaman alokacin ake hidiman, ga kuma wani rangwaɗa kanta da takeyi, kaii ni Aunty nice ina ga mata mai yanga kam, don ƙuri na mata ina kallon yatsun hannunta yadda take watsa su kaman wata ɗawisu, ga magana ɗaya tana juya idon nan kaman ka sace ta ka gudu, gaskiya macen da bata da yauƙi ta rako mata duniya ne, na faɗa a cikin zuciyata.
Aunty nice ina baki labari, maganan habiba kuma sai ya tabbata, domin Aliyu yayan jamilah gaba ɗaya ya takura ni, duk inda nayi idon shi yana kaina, tun lokacin da muka fito za'a tafi wurin liyafan yakasa ya tsare dole sai na shiga motan shi, haka ya aiko Fatie ƙanwar su mai bin jamilah ta ƙirani, gashi ba mai son magana ba, ina fitowa yace na shiga motar shi, ido na zuba mishi ina ɗan kame-kame da riƙe gyalen jikina, a haka na daure nace mishi zan bi motan amaryah ne, ya kallo ya bini da shi cikin nutsuwa da kwantar da kai yace, "amaryah ma da angon ta zasu tafi, kema kibi naki angon kawai ku wuce tare", ya faɗa bada wani damuwa ba kaman dama muna tare.