Kenza eBookz

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 3

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 3

Ana barin halal original by anty nice Chapter 3: Ana barin halal original by anty nice Chapter 3. A razane na kalle shi nace, "ni kuma? Ni ae banida aure,…

4,446 words

A razane na kalle shi nace, "ni kuma? Ni ae banida aure, yana duba na ido cikin ido yace, "ehh kema ae zakiyi tunda ba tabbata xakiyi ba, babu yadda na iya da shi, dole naje na jawo habiba da maryam akan mutafi tare, kafin kuma kiyi haka ummitah ta fito tayi jikin motan Aliyun tana wani rangwaɗa, gata kaman zata ɓalle don rama, "Bro bari nazo mutafi, tun da kaima chan kanufa. Dubanta yayi kai tsaye yace, " bana son takura ki wuce ki nemi wani motan, akwai wanda zan tafi dasu", kuma bai wani ɓata lokaci ba ya buɗe mun gaban motan fuska a ɗaure ya mun alaman da na shige, sannan ya dubi habiba da maryam ya musu alaman su shige bayan motan, ko takan ummitah da ta buɗe baki tana kallon mu bai bi ba.

Ummin mu da maman maryam da mamie duk sunzo wurin liyafan, mamah kawai aka bari a gids, duk inda mukayi idon ummi yana kanmu.

Bayan an buɗe fili da addu'a an fara programm babu daɗewa ango ya iso da rakiyar abokan shi guda uku, bayan sun zauna babu daɗewa D.J ya basu umurnin fitowa filin, aka saka musu waƙan aure, haba zokiga iyayen zamani, ba uwar amaryah ba bana ango ba, duk ɓarin kuɗi sukeyi, damu abu duk ɗaya, kai ranan naga matan manyan bauchi, kowa ɓarin naira kawai takeyi don ace ita ce tafi burgewa, bayan fili ya ɗan lafah amaryah sun koma sun zauna, sai D.J ya sake bada daman ƙawayen amaryah su fito fili.

Da ƙyar maryam ta riƙo hannu na muka fito, domin ita da habiba suna da son rawa a rayuwar su, ni dai haka na fito na tsaya na ɗan riƙe handbag ɗina ina kallon su, batare da nayi rawan ba, sai dai ina ɗan juya jikina kaɗan, wanda wani zaiyi tunanin nice amaryah, a haka Aliyu ya fito yana mun liƙi kaman bai san daɗin kuɗin ba, ganin haka duk inda na kauce yana biye dani sai mummyn su ta fito tare da wata ƙawarta suka shiga liƙa mun kuɗi daga ni har Aliyun, fuskan mummyn sun cike da fara'a, wanda alamu ya nuna mata Aliyunta yayi kamu, wanda ta daɗe tana fata da kuma burin ganin wannan lokacin.

Daga gefen su ummin mu kuma mamie ta wani matse fuska tana bin mu da harara, a haka bakin ta ya suɓuce taja wani dogon tsaki, babu kunya tace, "shishigi a wurin yaran nan yayi yawa, abu gaba ɗaya babu armashi? Sai wani shishshige musu Aysha ta keyi, ae idan yaro mai rawan kaine idan zaije wuri sai a ja mishi kunnen kamun kai, bawai yaje wuri yana nuna halin rashin kamun kai ba", daga maman maryam har ummin mu babu wacce ta bi ta kanta, a haka aka cigaba da progrmm har magrib tayi, sannan aka fara haraman tashi.

Ummi ana ƙiran sallah sukayiwa mummy sallama suka tafi, sannan ta riƙo hannuna tace ana idar da sallan ishaa Umar zaizo ya ɗauke, sbd haka akula da kai ko". Insha Allahu na amsa mata, ina son umminah Aunty nice, sbd matace mai zuciya mai kyau, bawai yabon kai ba, ban taɓa ganin mai irin zuciyar ummi na ba, tafaɗa tana saka hannun ta tana ɗaukan bottle na ruwa, ni kuma na ƙara gyara zamana ina kallon ta da sauraranta da dukkan hankali na, zuciyata tana son jin yayah labarin fararen abokan yayan ta ya nufa, amma bana so na mata gaggawa.

Bayan gama bikin Jamila da 1week suka bar ƙasan da mijinta zuwa london, Allah sarki har gidanmu tazo ta mana sallama da yammah ita da mijinta, lokacin da muka fito rakata wurin motan ta riƙo hannu na muka ɗan tsaya tana dubana, "Ɓesty kim san yayah Aliyu ya birkece akan ki kuwa? Duk tsare gidan shi amma sai da ya sake ya sameni da maganan, yana ta tambaya na akwai wanda yake neman kine ko yayah ake ciki? Ni dai nace mishi for now babu kowa sai burin fara karatu da kikeyi, nagaya miki mummy sai farin ciki ta ke tayi, yanzu haka ma ya koma lagos kin san achan yake aiki, ya tambayeni number wayanki nace har yanzu de baku fara riƙewa ba", ta sake damƙe hannu na fuskanta cike da jimami tace, "Besty gashi zan tafi na bar ƙasan ban san yayah zanyi da ke ba, nasan hala idan baki ganin ido na kiƙi amsa yayah na, don nafi kowa sanin baki son baƙi, Besty yayah na fa bawai baƙin har chan bane, gashi mai ilimi da class", ta faɗa kaman zata mun kuka.

Juya ido nayi ina kallon ta, "Besty nifa bawai baƙine bana so ba, nifa ban kai aure ba, karatu nake son yi, kuma.... Sai nakasa ƙarasa faɗin abun da zan faɗa na ƙura mata ido. "kada ki damu besty insha Allahu komai zai tafi daidai indai har muna tare" maryam ta faɗa tana dafa kafaɗan jamila, ni dai ido na bisu ban sake cewa komai akan maganan yayan ta ba, bayan sun tafi muka wuce raka maryam gidan su. Maryam sai bayani takeyi akan haɗuwan Aliyun, amma ita tsoronta jujuna, nidai ko kulata banyi ba.

Wannan dawowan Abban mu daga Abuja ya taho mana da waya masu shegen kyau da tsada, murna nida habiba kaman babu gobe, a lokacin hafsy take turo baki gaba tana, "Abba mu fah? Muma fah muna son wayan Abba", Abba yace, "Yayanku Ahmad ne ya bayar aka wo musu, dama ya musu alƙawarin idan sun gama school result ɗinsu yayi kyau zai saya musu waya, kuma Alhamdulillahi abu yayi kyau, kuma ku dage ku maida hankali akan karatunku, idan kun gama za'a saya muku".

Mudai sai murna mukeyi muka miƙawa su ummi domin su saka mana albarka, murmushi ummi tayi tace angode wa yayan su Allah ya bar zumunci, sannan ta mana nasiha akan riƙe waya da muka jin tsoron Allah, mamah ma nasihan ta mana, sannan ta mana murnan wayan, sannan ta maida hankalinta kan su Raliya tana musu faɗa akan komai aka mana sai sunyi mita, mu sa'o'in su ne? Mamie cikin ɓata rai tace "tou ae suma su Raliyan sun kai su riƙe wayan, ae da sai suma a saya musu".

"Babu wanda zai saya musu waya sai sun gama makarantan suma, kuma sai anga result ɗinsu yayi kyau irin nasu Ayshaa, yaran da SS 1 zasu shiga gaggawan me akeyi"? Yayah Umar daya ke shigowa parlon shi da yayah ishaq ya faɗa, ganin haka mamie bata sake tankawa ba, sai tsaki da taja ƙasa-ƙasa.

Gaishe da kowa sukayi sannan suka nemi wuri suka zauna, Yayah ishaq yana duban hafsy data ɗano baki sama kaman zatayi kuka yace, "jerry kada ki damu, nine nan zan saya muku haɗaɗɗe keda tom, amma da sharaɗin babu sim, don kada ki addabe ni da flashing," yana zolayanta ya faɗa, don babu hali taga wayan ummi sai tayi flashing ɗinshi ya ƙira, idan ummi tayi magana tace shine fa kawai ya ƙira, dama tun tana ƙarama Aunty Rakiya da Aunty Asma'u suke zolayanta haɗin gidan shi, gashi babu dama taga yana wasa da Raliya zata zunɓura baki gaba, kowa saidai yayi dariya don yadda ko mu mukayi wasa da shi sai tayi fushi.

Mamah tace tou Allah ya nuna mana lokacin ishaq, amma flashin kam zaka sha shi a wurin wannan ƴar fitinan.

Babu wuya wurin ubangiji yadda lokaci yake ta tafiya har abun tsoro, a haka admission ɗinmu ya fito, ATBU ta bamu gurbin karatu, ranan da mukaje registration sai da muka tuna jamila, Allah sarki jammy besty, tayi burin shiga ATBU amma Allah yayi achan zatayi karatunta.

Course ɗaya muka samu nida jamilah wato *BUSINESS ADMIN* ita kuma habiba *COMPUTER SCIENCE* dama ita da jammy shi suka zaɓa tun lokacin jamb ɗin mu, sai Allah yayi ita bada ita za'ayi ba, kuma zuwa wannan lokacin Yayah Aliyu ya samu number nah ta wurin jammy waya mukeyi har lokacin ban bashi daman zuwa gida ba, don gaskiya ni tsoro nakeji, a haka kuma habiba tayi wani saurayi yana da wurin sai da mota, tana kula shi amma banga alaman zuciyar ta na kanshi ba, sbd da na mata magana sai tace mun yana da rawan kai da yawan surutu, ita bata son mai irin ɗabi'an shi, dama irin Aliyu ne tou bata da damuwa. Tana faɗan haka na dube ta nace, "sisto tou ko na haɗaku da Aliyun ne? Don ni kinga gaskiya bai mun ba, fari nake so", Hmmm, "sisto kenan ina kika taɓa ganin anyi haka? Shima ae bazai yadda ba, tunda ae ya ganni amma bai ce ni yake so ba sai ke, kawai dai akwai lokaci sisto,yanzu ne fah muke cika 17yrs, me ma mukayi?" ta faɗa tana maida hankalinta kan wayanta, nidai tsura mata ido nayi ina kallon ta, chan na sake cewa "amma dai sisto idan an mana aure sumul zamu zauna, kuma har mu haihu, kinga ae jamilah har ciki fah take dashi, kuma gashi maryam ma ta samu saurayi ɗan abokin Baban ta, kuma ita ma muna shiga level 2 kinji aure zatayi, kawai na haɗaku nima sai na jira nawa rabon, kinga december this year auren Yayah Ahmed, mu kuma kawai irin next december sai a miƙa mu", na faɗa ina dariya, itama dariyan tayi tana "wayaga Aysha da habiba a ɗakin aure", gaba ɗaya muka kwashe da dariya, " sisto kin san me yake burgeni da aure"? Tana kallo na ta jijjiga kanta alaman a'a, na rausayar da kaina ina fari da ido nace, "na tashi da safe nayi breakfast wa miji na da ƴaƴana, shi zai tafi office su kuma school, ni kuma ina busy a kitchen", dariys muka sake kwashewa, habiba ta riƙo hannu na tace, "sisto ni kuma na ganni da ciki ina irin laulayin nan, nayi amai na dawo yana ta mun sorry wife, ni kuma ina ta shagwaɓa ina ni abu kaza zanci", dariya muka sake tun tsirewa da shi, cikin dariya nace, "Allah yasa muyi aure rana ɗaya sisto" Ameen mukaji hajiya ummah ta amsa, tana ƙara shigowa cikin ɗakin. Zaro ido nayi ina kallonta cike da mamaki, wato tsohuwar nan laɓe ta fara mana ko mai?

"yakamata nayi zama da ɗana, domin na shaidah masa inda yaran da yake yabo suka dosa, don alama ya fara nuna kun ƙosa, kun ƙosa mana tunda har lissafin ciki ku ka fara, Allah ya nufa ma baku kai da lissafin kwanciya ba, kafin aje a haka gara ya samu labari" ta faɗa tana ɗirkawa habiba dundo a baya tana, "babu ma yake, domin na lura jaraba irin na uwarki duk kin haddace, sai dai Allah ya rufa asiri.

Tana cikin sababinta Yayah mohd ya turo ƙofan ɗakin ya shigo, yana "kefa tsohuwar nan fitina ne da ke, mutum yana ta sallama ke kuma kina ta sababi ba bazaki saurara ba, kuma kizo kina cewa ba'a miki sallama ba, Ina zan saurareka yai nakama yaran nan da ake musu kallon sallah -sallah amma ashe ko alwala basu iya ba, dama ina cike dasu yadda ɗana kullum bakin shi yabon shi akan sune, don koni da nayi namijin ƙoƙari wurin haihuwar shi baya gani ballantana kaji ya yabeni, sai waƴannan masu kai kaman na zabuwa", Dariya yayah mohd yayi yana miƙo mana hannu yana faɗin , "kuzo muje parlor kumun bayanin yayah karatun ATBU yake"?

Hararan mu hajiya ummah tayi, tana ya mutsa fuska tace, "ae ni shirme ma nayi da na gaya maka me sukayi, don babu wani mataki da zaka iya ɗauka, dama Ummaru ne, na sanshi aiki ne da cikawa", mudai babu wanda ya kulata don sanin halinta yanzu zata zageka, idan wani kuma ya taɓa ka sai inda ƙarfin ta kuma ya ƙare.

A haka watan azumi ya shigo, kowa ka ganshi sai shirin shiga watan Ramadan akeyi, ko ina sai sayayyah ake, haka ƴan'uwa na Yayah mohd da yayah Ahmad suka haɗo kayan azumi wa Abba, don yanzu komai sun tsaya akai, basu wani jiran Abba yayi, yayah umar kuma suna shirin tafiya service, shi Kaduna a ka cillashi, yayah ishaq kuma Benin, haka suka shirya suka tafi, azumi nada kwana uku mummyn jamila tazo gidan mu, abin mamaki boot ɗin mutanta shaƙe da kayan Azumi, doya ne dankali ne fruit ne, wai duk toshi ta kawo, sai farin ciki kawai zaka gani a saman fuskanta, ummi da mamah ne suka karɓeta cikin mutunci, suna tambayanta labarin jamilah a chan inda ta ke, nidai bayan nagaishe ta guduwa side ɗin hjy ummah nayi, rai na duk a ɓace, bayan nagayawa Aliyu kada ya fara saka mama tazo, donni tsoro nakeji a sani a gida, amma nayi imani yau kowa sai ya sani, raina a ɓace haabiba ta isoni, kallo ne takeyi cike da damuwa tace, "Sisto tou meye laifin Aliyun nan ne? Nifa banga makusa fah a tare da shi, kawai ki amince, inaga auren farin mutum wani abu ne?" hararanta nayi nace mata ni bani da ra'ayi akan shi, kawai ya rabu dani, tana kallo na tace tou ki gaya mishi mana kafin komai yayi nisa.

Zuwa dare ummi ta ƙirani, tambaya na tayi game da alaƙan dake tsakanin mu da Aliyu wanda ban taɓa gaya mata ba, rai na a jagule na dubeta nace, " ummi nifa bana son shi, nace mishi ma fah ya nemi habiba saboda ita ya mata, amma shine yakama ya gayawa mummy, nidai ummi bana son shi".

Kallo kawai ta bini da shi, sannan tace, "a wani gari kika taɓa ganin anyi haka? Ina ke yagani yake so? Meya kawo maganan habiba kuma, ko yace miki yama sonta ne?"

"Nidai kawai ummi bana son shi, ita kuma ya mata gara kawai ya nemeta," "Allah ya kyauta, Allah ya muku zaɓi na alkhairi inji ummi.

Ganin yadda nayi ummi sai ta ɓoye bata gayawa Abba zuwan mummy ba, kuma ta kwaɓi mamah mah, A haka satin sallah ya shigo, gaba ɗayan mu ranan mun karɓo ɗin kunan mu, sai murna muketayi gaskiya *JAMILAH HANCO* ta chanchara mana ɗinkuna masu kyau , da safe bayan mun dawo daga tafseer sai ga driver gidan su jamilah ya kawo kaya kusan kala biyar a ɗinke, da wani abayah mai masifan kyau da tsadan gaske, ɗaya ledan kuma jaka ne da kalmi set 2, haka mummy ta haɗo aka kawo wai duk kayan sallah nane, ummi ta ƙirah mama akan suyi shawarah, haka mamah ta bata shawaran kawai ta sanar da Abba kada abu yayi nisa, nidai ko kaɗan kayan basu mun ba, don bana son mai kayan ballantana kayan, kawai kunyar jamilah ne yasa nake raga mishi, amma sai ya ƙirani sama da goma ban ɗauki wayan shi sau biyu ba, yawanci habiba ce ma ke ɗauka suyita hira akan course ɗinta, nidai nawa ido, a haka yace mun ran sallah zai turo a nema mishi ison zuwa muna gaisawa nidai ƙin amince mishi nayi sai habiba ne tace mishi babu damuwa hakan ma yayi.

Washe garin sallah iyayen Aliyu suka zo wurin Abbah na neman ison Aliyu ya gani yana so, kuma da neman iznin ya fara zuwa zance, cikin mutunci Abba ya karɓe su, kuma ya bada daman yazo, amma da sharaɗin baya son dogon nema, idan mun sasanta kanmu baya so abu ya ɗauki lokaci, kuma baya son yawan zuwa zance, haka taron ya watse kowa fuskan shi cike da farin ciki, amma ni kuma takaici kaman zai kashe ni, baya ma da naga habiba ta saka hannu biyu tayi tagumi, duk sai naji abun bai mun ba, muna shigowa parlor nida habiba muka haɗu da mamie, fuskan ta cike da fushi ta kalle ni, babu kara tace, "sannu madam Aysha, wato an baki suratul yusuf an haɗa miki da surkulle sai murna kike kin samu mai so ko? Tou ayi dai mugani, amma insha Allahu bazaki riga habiba auruwa ba kam a gidan nan, kai hattah Raliya ma sai kin rakata, don ba rako mata duniya nayi ba ballantana na zura ido"....... "lallai ko zai tabbata kin rako mata duniya mushirikiya kawai, ke kam ban san ranan da zakiji tsoron Allah a zuciyar ki ba, gani kike duk surkullen da kikeyi wani ma haka yakeyi"? Cewar Aunty Rakiya da shigowan ta kenan gidan, tsaki mamie tayi ta wuce ta bar wurin batare da ta tanka wa Aunty Rakiya ba.

Ita ko Aunty Rakiya haka takama masifah har ta wuce ɗakin ummin mu, rai a ɓace takama masifa akan shirun ummi yayi yawa, sannan ta ƙara addu'a fah, don zuciyar mamie babu Allah a ciki, murmushi ummi tayi tace, "banda abunki Rakiya mamin su ta isa ta hana abun da Allah yayi nufi? Kuma ni kullum addu'a na akansu yake, babu dare babu rana, kuma insha Allahu khairan, ni damuwa na ma da ita Ayshan kaman yaron bai mata ba, gashi kuma mahaifiyar tana son abun, ni har kunya nakeji wlh".

Wuri Aunty Rakiya ta nema ta zauna, "tou idan Aysha bata so ae baza a mata dole ba, kawai addu'a zamu dage, idan babu alkhairi Allah ya kawo mata wanda yafi alkhairi, amma babu dole babu kuma kunya", amma dai abun bahaka naso ba, don ni banga aibin yaron ba, cewar ummi, Ita ko yarinya taga aibu, kuma babu mai takura mata sai abun da taso" Aunty Rakiya ta faɗa, ita dai ummi murmushi tayi ta sake zancen ta koma wani chafter daban.

Ranan sallah na uku Yayah Aliyu yazo gidan mu, parlor Hjy ummah habiba ta kaishi, bayan sun gaisa ta kai mishi abun sha da cake ɗin da mukayi na sallah da cincin sai naje, hiran dai dani kam babu armashi, amma shi ds habiba kaman sun shekara da sanin juna, nidai ban da ehh da a'a babu abinda yake ji daga gareni, ganin haka sai ya maida hankalin shi kan habiba yana ta bata shawara akan karatun ta, tunda shima computer science yake koyarwa, nidai gaba ɗaya hiran ba wani ɗaɗani da ƙasa yayi ba, saboda nakasa jin wani abu akanshi, sai dai ban wani nuna mishi sosai a fuska ba, babu daɗewa sai ga Raliya ta shigo, ko gaishe shi batayi ba kanta tsaye ta kalli habiba tace, "kizo mamie na nemanki" daga nan ta juya ta fita a parlon, dukkan mu kallo muka bita da shi cike da jin kunyan abinda tayi, shikuma da yake ba mai damuwa bane idon shi kawai ya mayar kan habiba yace, "tou Aunty habiba godiya nake, amma a ƙara riƙe mun wuta fah" ya faɗa cike da zolaya, itama dariyan tayi tace, "baka da matsalah sai dai ka nemi wani abun kuma daban" daga haka ta fita, shi kuma ya maido da hankalin shi na, "ina muka tsaya ne princess?"

Ɗago kai nayi na dube shi, muryah cike da rauni nace "babu komai", Zura mun ido yayi har sai da naji nauyin idon shi akaina ya mun yawa, sai dube -dube nake tayi akan wayana, ba tare da nasan me nake ganiba, duk a takure nake, ganin haka yace, "tou princess nidai zan wuce sai munyi waya, fatan babu wani abu ko"? Cikin gaggawa na amsa mishi da babu komai na gode," ina miƙewa kaman an ɗana mun abu, murmushi yayi yace, "tou a mun rakiya mana".

Zaro ido nayi ina kallun shi nace, "Rakiya kuma? ae za'a ganni, nidai kawai.... " sai kuma nayi shiru ina maida kaina ƙasa saboda irin kallon daya ƙureni da shi, bai wani ja ba ya juya ya fita yana cewa, "baki da saƙo wurin mummy"? Da sauri nace a gaisheta.

Bayan ya fita hjy ummah ta fito tana ya mutsa fuska tace, "ashe ke sokuwa ce ban sani ba? Wannan wani irin zance ne babu armashi? Sai dai ƴar'uwarki ce bakin ki? Tou a kul kada nasake ji ko ganin wannan ƙauyancin, don ko mutanen da iya kachi".

Tura baki nayi gaba ban bata amsa ba na fiche a parlon.

Wasa-wasa shaƙuwa tsakanin Aliyu da habiba sai yafi ƙarfi, wani lokacin ma idan ya ƙira waya na sai dai hiran ya koma da habiba, zuwa ɗari kuma hiran da ita yafi armashi, nidai nawa ido da binsu da kallo, a haka mukayi wata uku tare da shi, lokacin kuma mahajjata sun dawo makkah, da yake mummy taje, sai ga kaya na fitan tunani an kawo mun tsara ba, ranan ina wuta mamie ta jefah ni a ciki, haka tayi ta banbami tana cewa ummi ta rufe taurarin farin jinin ƴarta, don shigan habiba side ɗin mu tasan ba ƙaramin illah akeyi wa ƴarta ba, amma a zuba da ita insha Allahu sai ummin tayi kuka, kuma daga yau ta shiga tsakanin habiba da ni, idan ba mugunta ba ummi ma taja kunne na da ƴarta, ko kula ta kanta ummi batayi ba, sai mamah ne ta fito ta watse ta iya son ranta ta kuma ce ta jira dawowan Abba da hukuncin da za'a ɗauka, don wannan mummunan fatan da takeyi idan ita ummi bata ɗauka ba ita mamah zata ɗauka, duk abunda akeyi Raliya tana tsaye sai bina da kallon banza ta keyi, ƙasa-ƙasa tana zuga mamie, haka dai akaita rikici. Bayan dawowan Abba mamah ta tasu da maganan agaban kowa, kuma ta rantse idan Abba bai dakatar da matan shi ba ita zata dakatar, cike da banbami take magana, ita kuma mamie ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya tana wani jijjigawa, a ƙarshe dai Abba yayi gyaran muryah yace, "don Allah ku saurara mun, yanzu ko a tunanin ku akwai asiri? Kun ma yadda da akwai kenan? Tou ni ban yadda akwai ba, amma duk da haka zan tsawatar da irin wannnan muggan fatan da akeyi wa ƴaƴa na", ya juya yana duban mamie, "don Allah mamin su bana son tashin hankali, shin Aysha ke ba ƴarki bace? Tou me yasa zakina jifanta da munanan kalamai? Don Allah ku zama ɗaya kowa yabar maganan nan bana son ya fita ma, kuma da yau bana son a dinga shiga tsakanin ƴaƴa nah, a barsu suyi zumuncin su bana son a raba mun kan ƴaƴa a damuwan ku na banza da wofi", sannan ya maida kanshi kan ummi yace, "ummin su don Allah bana son abubuwa na chanfi a gida na, wannan maganan ya fito ne saboda mamin su bata da haƙuri ko kaɗan shiyasa idan ranta ya ɓaci sai tayita magana babu kan gado, amma bawai nufin ta ta cutar da wani bane, fatan kowa ya gane kuma maganan zata tsaya a haka"?

Murmushi ummi nah tayi ta kau da kanta gefe tace, " dama ni ka taɓa ganin na taɓa zargin wani a rayuwata? Nayi imani fah da ƙaddara mai kyau ko marar kyau, kuma ban saka zuciyata akan wani ya isa ya cutar dani ko yarah na ba, don na dogara da Allah, kuma nasan zai isar mun akan komai".

Baki a buɗe mamah take bin Abba da ummi da kallo, chan tace "tou haka zancen yake kenan ko? Kai a irin adalcin ka kenan iya abun da zaka ce kenan? Tou Allah ya mana jagora", sannan ta maida kanta kan ummi tace, "ke kuma baiwar Allah ya isar miki yadda kika ce, kuma Allah ya tsare ki da yaranki daga sharrin mai sharri, amma mukan mun sha tabara mun sha lahaula, duk sharrin mai sharri haka zai barmu," ta faɗa taa barin wurin tana faɗin ita ta gajji da ganin kayan ɓacin rai.

Bayan kwana biyu da mamie ta hana habiba shigowa side ɗin mu, sai zaman mu ya koma chan wurin hajiya ummah, amma kuma abinda na lura sai Raliya ma ta maida zamanta chan, amma duk da zamanta a wajen baya wani lasting sbd abu kaɗan zasu kanchale da Hafsy sai kuma hjy ummah ta fatattake su, nida habiba kuma ganin an koresu sai muyita dariyan su, a ranan kuma habiba ke gaya mun raliya ae ƴar aike ne, gulma take kaiwa mamie, nidai dariya nayi nace, "zata shiryu ae, yarinta ne yake damunta".

Gaba ɗaya sai zaman mu da kwanan mu ya koma chan, saboda mai aikin hjy umma da tayi tafiya, gashi zazzaɓi ya sako hjyr a gaba, sai Abba yace mu koma chan gaba ɗaya muna ɗebe mata kewa, mamie babu yadda ta iya sbd lokacin data so ta dakatar da habiba har cikin gida hajiya ummah ta shiga ta watse ta kuma ta kafa mata kyakkyawan worning.

A hankali na lura Aliyu ya janye ƙirana a waya, sai dai naji shi suna hira da habiba, duk da dai ba hiran soyayyah bane sukeyi, amma duk sai naji jikina yayi sanyi, sai dai bance komai ba, don ni idan ka cire ummi na duk duniya babu abinda nake so irin habiba.

Habiba ta matsa mana ranan friday muje gidan yayah mohd mu wuni wa Aunty Bintu, ban ƙi mata ba muka shiryah mukaje, gashi lokacin da mukaje fatima sister Aunty Bintu tazo mata hutu saboda Aunty Bintu cikinta yayi girma, haihuwa yau ko gobe, sbd ma ta daɗe bata samu haihuwan ba, murna wurin Fatima kaman yayah sbd ita dai son mu takeyi.

Zuwa la'asar sai naga habiba tana amsa wayan Aliyu, bayan sun gama sai ta juyo cike da farin cike tana duban mu tace, "sisto Yayah Aliyu yazo, mu shigo da shi parlor ko"? Ido na zuba mata kaman bazan ce komai ba, sai chan kuma nayi wani tunani, fuska na cike da murmushi nace "sisto tunda yazo ku gaisa ne kije kawai waje ki same shi mana". Babu ɓata lokaci da magana na ta ja gyalen ta tayi hanyar waje tana faɗin "sisto ki fito tou ku gaisa, bari naje, yace zai kawo mun wani mini computer ne da yayi order shi ya iso, shine zai kawo mun nawa", daga nan tayi hanyar waje cike da sauri.

Zuciya nane ya yanke a lokacin *Aunty nice*, saboda sai na rasa dalilin da naji hankali na ya tashi, kuma kaman alaman kaman naji kishin yayah akayi tsakanin su yakai haka da ƴar'uwata? Amma banja ba sai na ture abun a raina, na maida hankali na kan Aunty Bintu da take mun tambayan bawai saurayina Aliyu bane yazo? Tou meyasa ni ban fita ba sai habiba? Ban iya nace mata komai ba, sai murmushi da na bita da shi, amma *Aunty nice* haka kawai naji zuciyana yana wani irin ɓaci, sai dai dana tuna habiba sister nane sai ture abun a raina.

Daga nan naga Aysha ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wani murmushi marar armashi, har zuwa wani lokaci kaman bazata sake cewa komai ba, sai kuma ta ɗago ta dube ni fuskanta cike da murmushi tace, "*Aunty nice* ina son habiba komai na mallaka zan iya sadaukar mata, amma shaiɗan sai ya fara rinjayar zuciyata naji kaman Aliyu fah ya dace da ni, kuma ina jin wani iri a zuciyata kaman fargaban kada na rasa shi.

Readers Also Read