Kenza eBookz

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 15

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 15

Ana barin halal original by anty nice Chapter 15: Ana barin halal original by anty nice Chapter 15. A hankali naja ƙafafuna na ƙarasa har bakin gadon,…

4,494 words

A hankali naja ƙafafuna na ƙarasa har bakin gadon, banyi yunƙurin miƙa mishi hannu na ba yadda ya so, sai kawai naji hajiya ta jawo hannu na ta haɗa da na Alƙali, a hankali na ɗago idanuna na sauƙe akanshi, wanda naga fuskan shi cike da murmushi, numfashi yake ja cike da wahalan jinya yace, "mukhtar ina sonka ina son mahaifiyar ka, mukhtar ina son ka ina son yayunka su auwalu, amma haka kawai na wayi gari duk kun ƙaurace mun, Hajiya tagaya mun wai ni da kaina nace bana son Fatima da kai, wai na sallameku bayan na sake ta, ina ƴaƴana su Auwalu su Sanie? Banƙi ku ba, zuciyana tana sonku sosai, nakasa neman ka ne mukhtar, amma duk inda kake zuwa talle ko wasan ƙwallo ina bibiyanka, har makarantar ku nake zuwa na ganka, amma ina jin tsoron na maka magana," ajiyan zuciya ya sauƙe hawaye yana bin kuncin shi, "kayafe mu duk abunda ya faru a tsakanin mu, kayafe mun mukhtar, idan Allah ya bani lafiya zanje nabawa fatima baiwar Allah haƙuri, damo sarkin haƙuri, Allah ya mata albarka, Allah yayiwa zuriyarta Albarka, na yafe mata, ita ma kace ta yafe mun inda hali," hawaye ne naji suna bin kunci na ganin yadda fuskar shi take zubar da hawaye, zai sake buɗe bakin shi yayi magana nayi sauri na ɗaura hannu na na rufe bakin shi, kai na ke girgiza mishi, "Babah kayi haƙuri, ni baka mun komai ba, idan ma kamun na yafe maka duniya da lahira, nine ma nake son kayafe mun hakkin ka da yake kaina wanda bantaɓa sauƙewa ba, duk abunda ya faru mun yafe maka daga ni har Goggo, kullum tana ce mun na yafe maka kada na ƙullace ka a zuciyata har ranan da zaka neme ni, saboda akwai hakkin haihuwa na da kayi Baba, ni kamun komai a rayuwa da nazam ɗaya daga cikin ƴaƴanka, kai dattijo ne mai nagarta, kai adali ne kuma mafi girman alkhairin uba acikin duniya," hannu na hajiya ta riƙo kawai sai naji ta fashe da kuka, daga bayan mu ma kukan mukaji, wanda ba kowa bane sai Aunty umatiti da yayah safiya, sai mijinta da suka rako ya duba jikin Alƙali.

"Alhamdulillahi da tsatso nagari! Alhamdulillahi da uwa ta gari!! Wannan ya nuna mun kai halataccen ɗa ne daka fito ta tsatso mai kyau, ya nuna mun Fatima tayi namijin ƙoƙari wurin baka tarbiya, Allah ya saka mata da mafificin alkhairi, Allah ya saka ta cikin aljannatul firdausi" "Ameen" dukkan mu muka amsa da shi, duk wanda ya shigo a ranan gaishe da Alhaji sai yayi mamakin yadda gaba ɗaya ya rungume hannuna a nashi, don ko bacci yayi sai nayi dabara nake zare hannu na, lokacin da yayah Rabi'u ma ya dawo, Alƙali yayita neman gafar shi, ya kuma nemi da ya nema mishi gafaran ƴan'uwa na da mahaifiyata, Yayah Rabi'u ko agaban kowa ya ƙira goggo da dukkan yayu na ya saka wayan a handsfree duk suka gaishe shi, suka kuma jaddada mishi sun yafe mishi, da ma kuma shi ubane a garesu, mahaifi kuma ba ya laifi wa ƴaƴan shi idan yaran ƴan albarka ne kuwa, kuka yayi tayi lokacin da suka gaisa da Goggo, wanda har yasaka dayawan mu zubar da hawaye.

Yayah Rabiu bai yadda mun juya ba a ranan, ganin yadda hankalin Alƙali gaba ɗaya yake kaina, haka muka kwana a Gombe, nikan ma a asibitin na kwana, yayah ne ya nemi masuƙi.

********** Washe gari alhamis Alhajin mu ya tashi jikin kuwa da sauƙi sosai, don har aka zaunar da shi, wuraren ƙarfe 11:00 na safe muna shirin tafiya ya riƙo hannu na, murya chan ƙasa yace, "ayaba nake so ka saya mun naci", jin abunda yace na fita jikina yana rawa na ciro wallet ɗina naje na sayo ayaba masu kyau da girma, haka kurum naji na saya mishi ruwa, bayan naga ruwa masu yawa a ɗakin, lokacin da na dawo na samu an maida shi ya kwanta, bai samu yaci ayaban ba shi dai yana riƙe da hannu na har ya koma bacci, ganin haka sai Yayah Rabi'u yace na jira har sai ya tashi tukun mu kama hanya, Tijjani kuma shi da ƴan'uwan shi da mahaifiyar su tunda muka zo sai suka ƙi shiga ɗakin, asibitin ma ranan basu wani zauna sosai ba, ita kuma maman su umatiti darajan ƴaƴanta da take tsananin son so takan amsa gaisuwa na, kuma takan zauna a inda nake, sai dai fuska babu sakewa.

Baba bai farka ba sai wurin magrib, haka na bashi ayaban nan yaci, sannan na bashi ruwan da na sayo yasha sosai, yana gama sha ya dubi ƙanin shi yace, "malam bello kaga ikon Allah ko? Ni bam taɓa ciyar da mukhtar ba amma ni kuma yau ya ciyar da ni, kuma nayi imani da Allah da halal ɗin shi ya ciyar da ni,". Shiru ɗakin yayi babu wanda ya sake magana, sai chan ya ɗago kanshi ya sauƙe a kaina yace, "mukhtar na yafe maka nima ka yafe mun, Allah ya inganta rayuwarka duniya da lahira, jikina yana bani kaine tauraron da zai haska gidana bayan raina, ina neman alfarma ka kula da kowa da zuciya ɗaya, kayi saboda Allah kayi saboda jini na mahaifi da ya haɗa ku, insha Allahu duk mai cutanka bazai sake samun dama ba akanka har abada, Allah ya tsare gabanka ya tsare bayanka, nagode mukhtar, naso na saka maka suna Abubakar Garba, amma Allah baiyi ba, duk ranan da ka haifi ɗa ina so kasa sunan Malam Garba," yana faɗin haka ya maida kanshi kan kafaɗa na ya kwantar, bai sake cewa komai ba sai yayi shiru. Mudai ranan bamu tafi ba, saboda Babah yaƙi barin mu tafi, don yayah yana zuwa muna mishi sallama ya girgiza kanshi yace dare yayi, mu bari gobe sassafe idan Allah ya kaimu sai mu tafi, haka ko muka haƙura, jiki dai Alhmdllh yayi dama-dama, har bayan ishaa na sake bashi ayaban rabi yaci, sannan ya miƙo mun rabin naci, haka ya zauna ido biyu bai koma bacci ba, wuraren shaɗaya na dare su yayah suka tafi inda suka sauƙa, aka bar ni daga ni sai Tijjani sai hajiya da maman su umatiti, shabiyu da rabi kowa yayi bacci sai ni da Tijjani ne idon mu biyu, shima Alhajin lokacin yayi bacci, a haka dai nafara ɗan gyanggyaɗi Ƙafan Alhaji yana kan cinyana, wuraren ƙarfe ɗaya naji shi yana ta kakari kaman yana son amar da abu, da sauri na buɗe ido na, anan naga hajiya ta buɗe ƙofan ɗakin ta shigo, bayanta maman su umatiti na biye da ita, "lafiya" naji tana tambayan Tijjani da shi ma ya miƙe a lokacin, nurses muka ƙira muna musu bayanin amai yake son yi amma ya kasa, haka suka fara ƙoƙarin su don taimaka mishi, hajiya kuma ta koma jikin gadon tana ta mishi addu'a, nima ganin haka ya saka na fita a ɗakin naje nayi alwala na dawo, bayan sun gama abun da zasuyi sun fita na ƙarasa kan gadon na zauna inda kanshi yake, a hankali na maida kan shi kan cinya na ina mishi addu'a, a hankali ya buɗe ido kaman mai son kallo na, amma sai naga idon wani wuri yake kallo, ina mishi addu'a ina shafa mishi, hajiya ma da mama suna tayi, shidai Tijjani yana tsaye a bakin ƙofa ya ƙura mana ido, amma hankalim shi duk a tashe yake, muna haka har wuraren ƙarfe biyu da rabi, chan sai naji bacci yana ɗan ɗauka na, a haka dai har baccin yaci ƙarfina, kaman a mafarki naji muryan hajiya tana salati, mamah na taya ta, shi kuma Tijjani yana cewa, "hajiya wayace muku rasuwa yayi? Ku jira na ƙira ma'aikatan asibitin tukuna," jiki na rawa na tashi na gyara kan Babanah, na bi bayan Tijjani, sauri muka ƙira ma'aikatan suka shigo, duk wani wuri a jikina rawa yakeyi, waje suka saka muka fita, har tsawon wani lokaci su ka leƙo suka ƙiramu nida Tijjani, da sauri muka shige ɗakin, ido na mayar kan gadon da na bar Babanah akai, sai naga an lulluɓe shi har fuskan shi da bargon shi, zuciyata naji ya yi wani irin masifan yankewa, ido na ƙura mishi ban san me zanyi ba a haka naji muryan nurse ɗin yana cewa, " sai haƙuri bawan Allah yaya za'ayi kwana ya ƙare, Allah ya jiƙan Baba", da yayah Tijjani yake, shi kuma Tijjani yana kuka kaman zai yi yaya, a haka su hajiya suka faɗo ɗakin suna kuka suma tambayan Alhaji babu ko? Haƙuri ake ta basu nidai na rasa yanayin da nake ciki, ihuu zanyi? Kuka zanyi, addu'a zanyi? Komai ya tsaya mun chakkkk. Gaskiya rashin iyaye wani abu ne mai ciwo da babu kwatankwacin shi, duk da babu sabo ko shaƙuwa a tsakanina da Alƙali, amma tabbas rashin shi ya buge ni, bugu ma bana wasa ba, domin ɗan zaman da nayi da shi a halin rashin lafiya na kwana biyu, sai naji kaman tunda na fara rayuwata muke tare, naji ciwo naji ciwon rashin mahaifina, ina tsaye duk iyalen Baba Alƙali suka shigo asibitin, kowa ka gani kuka yake, Aunty umatiti ne ta rungumeni tana kuka, amma haka dai ina tsaye ban iya komai ba, gari ya fara haske sai ga yayah rabiu ya iso duk a firgice, wurina ya taho ya riƙoni jikin shi, sai lokacin naji nayi wani ajiyar zuciya, wanda ya ɗan lafar da turirin da zuciyana yakeyi, yayah rabiu ne ya taya ƴan'uwa na da maxajen su aka gama komai aka ɗauki gawan Alƙali sai bauchi.

Yayye na babu wanda bai ƙira wayana ba, amma nakasa iya ɗauka, nidai har zuwa wannan lokacin babu wani kalma da ya fito daga bakina, babu wani hawaye da ya zubo daga idona, ganin bana ɗaukan wayan ya saka yaya rabiu ya amshe wayata ya kashe, don ko ƙiran A.G ma kaɗai ya isa a kashe wayan, muna isa ƙofar gidan naga mutane maƙil a ƙofar gidan, haka dai muka sauƙo iyaye mata da yayye na suka shige cikin gidan, mu kuma muka fara ƙoƙarin fito da gawan, ana fito da shi ƴaƴan shi da ƙannen shi suka shige da shi cikin gida, amma ni sai na tsaya a waje tare da yayah rabiu da su yayah hassan da hussain, muna tsaya anan waje muna ta gaisawa da jama'a, duk da dai ni kan kaina a sunkuye yake a ƙasa sai su yayah ne ke amsa gaisuwan, muna haka chan wani ƙanin mahaifinmu ya fito daga cikin gida wurin da ake yiwa Baba Alƙali wanka, har inda muke tsaye yazo ya tsaya, "mukhtar ka shigo kayiwa mahaifinka addu'a", kallon shi nayi zuciyata tana wani irin tafasa, wai na shigo nayiwa mahaifina addu'a? Yana raye basu yi sanadin na shigo ba sai da ya bar duniya? Aiko bazan shiga ba, girgiza kai nayi alaman a'a, duk kallo na suka tsaya sunayi, daga nan naga yayah hassan ya wuce zuwa gidan mu, haka mutane suka taro a kaina suna magiyan na shiga, amma tunda na sauƙe kaina ƙasa ban sake ɗagowa ba, ballantana wani yayi tunanin zan ji kunyar shi nayi abunda suke so, bawai ban yafewa Alƙali bane ko banji nasihar shi ba, a'a gidan ne kawai da sukayi sanadin rashin shiga na tun yana da rai nake jin bazan shiga ba, ae baya raye, abunda suke ƙulafucin an bar musu, kafaɗa na naji an dafa, ko ban juyo ba nasan hannun goggo ne, lokaci ɗaya na sauƙe ajiyan zuciya, batace mun uffan ba ta saka hannunta ta riƙoni har zuwa cikin gidan inda aka keɓe ta varender baya na side ɗin Alƙali, binta nayi babu musu har inda gawan yake, bayan mu kuma yayu na suke biye da mu, ko wanne a cikin su ka kalli fuskan shi kuka yakeyi amma banda ni.

Har gaban gawan mahaifina goggo ta mun rakiya, dukkan ahalin shi suna wurin, matayen shi, ƴaƴayen shi maza da matan su, yayunshi da ƙannen shi, jikokin shi da aminan shi duk suna wurin, da yake wurine mai gurman gaske, hatta surakunen shi suna tsattsaye a wurin, tsugunar dani goggo tayi a gefen yayuna maza wanda suke durƙushe a daidai kanshi suna mishi addu'a. Addu'a sosai goggo ta mishi, ta ƙira sunan shi ta tabbatar mishi da duk wani abu daya faru ta yafe mishi, hajiya da wasu daga jama'an wurin sai da sukayi kuka lokacin da ta ɗago hannuna ta ɗaura a kanshi, tace, "Abdullahi rahmar Allah ta isar maka har kabarinka, halayen ka nagari, da jinƙan ka da kyautatwa talakawa dana ƙasa da kai Allah ya kai rahmar kabarinka , Allah ya haɗaka da mala'ikun rahma, Allah ya baka ikon amsa tambayoyin kabari, ga ɗanka Mukhtar ya yafe maka, Allah ya yafe mana gaba ɗaya, sai lokacin naji kukan gaske mai ƙarfin gaske yazo mun, abunda ya tokare ni a ƙirjina naji ya wuce kaman na haɗiye abu, ina kuka ina mishi addu'a, gaba ɗaya iyalen shi sai suka fashe da kuka, lokacin da nace na yafe mishi Allah ya jiƙanshi, sai naji yayah safiya ta runguma ni tana Alhamdulillahi, Allah ya maka albarka mukhtari, wannan lokacin dai nima dawowa nayi layin ƴan'uwa na mata, don da ƙyar su yayah hassan suka ɓanɓareni daga jikin gawan Baba nah lokacin da za'a fitar da shi, nayi kuka kaman numfashi na zai ɗauke.

Muna futowa aka saka shi a motan ɗaukan gawa, haka dukkan mu ƴaƴan shi da ƙannen shi muka shige wannan motan, ina zaune dai-dai ƙafafunshi, sai hawaye nake sharewa, mu muka sakashi a kabarin shi, muka kuma zuba mishi ƙasa, lokacin da aka kammala komai aka fara shirin juyowa sai naji hankalina yayi masifaffen tashi, tunani na yanzu fa za'a zo fara mishi tambaya, kuma tsakanin bawa da ubangiji shi kaɗai yabarwa kanshi sani, tsakanin bawa da bawa shine abun tsoro, Baba nah ya samu yabo a wurin jama'a, tou tsakanina da shi fah sai Allah ya iya kama shi fah? Duk da naji a zuciyata ni na yafe mishi, kuma dama ban tashi da wannan ciwon azuciyata ba saboda uwa ta gari danayi dace da ita, amma sai naji tsoro ya kamani, bansan lokacin da nasake furta, "Baba nah nayafe maka, na yafeka Babana har abadan", da sauri naji wani ƙanin shi ya rungumo ni yana kuka, sai yayah rabiu ma ya kamoni yana kuka muka fara tafiya, muna zuwa wurin shiga mota Alhaji Inuwa ya riƙo ni muka shi motan shi, nayi kuka a motan kaman zan shiɗe, bai bani haƙuri ba bai kuma hanani ba, sai baya na dayake ɗan bubbugawa kaɗan kaɗan har muka isa gida.

Nidai ban sake jin sha'awan na shiga gidan ba, don ko gaisuwa da ake shiga ayi acikin gidan wa iyalenshi ni ban shiga ba, inda Alhaji Inuwa ya zauna nan muka zauna nida ƴan'uwa na da suke taya ni jimamin rashin da aka mun, nidai ko kallon mutane bana yi, na sunkuyar da kaina ƙasa ina yiwa mahaifina addu'a.

Wuraren bayan sallan la'asaar sai ga A.G nawa ya iso tare da barr Ahmad, wanda ranan shine rana ta farko da muka fara haɗuwa da shi, kawai dai munyi sabo ta waya ne, tun isowar A.G naji wani sabon kuka ya taho mun, shima zuwa yayi ya riƙe hannu na, da ƙyar bakin shi ya furta, "sorry" daga nan bai sake iya yace komai ba, sai hawaye da yake ta sharewa. Bayan anyi sallan ishaa muka shige cikin gidan mu wurin Goggo na, lokacin da mukaje na kalleta sai naji wani sabon tausayinta ya kamani, Allah sarki Goggo dukkan ƴaƴanta yau sun zama marayu babu iyaye maza, goggo na taga rayuwa a cikin rayuwarta, gaba ɗaya sai naga ta zabge wanda har girmanta ya bayyana kanshi sosai, kanta a ƙasa ta amsa gaisuwan mu, ina hankalce da ita yadda duk bayan wasu mintuna sai ta goge hawaye a idon ta, gefen ta na koma na zauna, a hankali na saka hannu na riƙo nata da ta ɗaga zata share hawayenta, kasa ɗagowa tayi ta kalle ni tayi, sai kawai ta kwantar da kanta a kafaɗa na tana kuka, "sannu mukhtar, sannu da rashin da aka yi mana yau, na tausaya maka na tausayawa kaina auta nah, zuciyata tana mun ciwo auta na, baka san daɗin mahaifi ba, baka raɓe shi ba har ya bar duniya, wannan wacce irin rayuwa ne muke ciki? Allah ya jiƙan Alƙali, Allah ya gafartawa malam Garba, Allah ya kai hasken kabarin su gabaki ɗaya", rungumeta nayi ina kuka a hankali, shiru parlon yayi banda sheshsheƙan kukan mu dukkan mu baka jin komai, a hankali A.G yazo ya rarrashi goggo tayi shiru, sannan ya riƙo hannuna muka fice a parlon muka wuce gidan su, nidai ranan sai bacci ɓarawo ne ya ɗauke ni.

******** Bayan anyi bakwai kowa ya watse, a washe garin rasuwar kuma yayah sanie ya iso, da yake raunin shi mai yawa ne, kuka ya dinga yi kaman mace, kada ki manta Ayshaa kinsan ko ba matsayin mahaifina Alƙali yake ba dama ɗan'uwan Baban su ne, saboda haka sun haɗa abu dayawa da Alƙali wanda dole suji mutuwar shi, don ko irin yadda aka tarwatsa rayuwar mu aka raba tsakanin mu yaci ka tausaya mun wannan rashin, ballantana kuma suma Bappan su ne kuma mijin mahaifiyar su, kuma mahaifina, Ayshaa ranan da Alƙali ya rasu sai Allah ya haɗa idanuna da wannan mai tuwon gidan alƙali wanda ta kwaɗa mun itace a baya, ganina a cikin gidan duk sai ta ruɗe, ranan uku tazo zata shiga gidan har ƙasa ta kai tana gaishe mu, nidai amsa mata kawai nayi na juyar da kaina, gashi ta manyanta lokacin, don ta kai goggo a shekaru, dama lokacin mijinta ya rasu ne tafara aiki a gidan mu, tun bayan anyi auren Alƙali da maman su umatiti kaɗan tazo gidan, shiyasa nasu ya zamo ɗaya, domin kowa gwana ce a munafurci, wajen zuwa tsubbu kuma nasu yazo ɗaya da mahaifiyar su Tijjani, don a wurin tane muka samu ƙabarin yadda akayi aka shiga tsakanin Alƙali da goggo, da ni kaina,, zanin Goggo da tayi shanya suka yanka, akwai wani malami ko bokan su zance a garin Dass, shi ya musu aikin da aka shiga tsakanin Baba Alƙali da Goggo na har abada, alokacin har abun cikin sai da akayi aikin rabasu, wato ni, kuma ta zaga ta gayawa maman su umatiti, ita dai tace neran ta bazaiyi kuka a wurin neman asiri ba, amma tunda sun fara ita zata taimaka musu da bakinta, kuma haka akayi ga asiri ga munafurci da akai ta haɗawa Goggo har sukayi nasara ba don Allah ya fi son su ba, sai don jarabawa na dana Goggo a haka yazo, su kuma Allah yana musu talala.

Bayan anyi arba'in ɗin Baba na suka ɗago maganan rabon gadon shi, haka suka tsaya tsawon sati guda suna harhaɗa abun da ya bari, nidai babu irin neman da basuyi mun ba amma naƙi zuwa, lokacin da Yayah safiya ta matsa mun da ƙira sai nace na wakilta mijinta a nawa, don ko dasuka nemi goggo itama baya na ta bi, yayah auwal nema da ya ƙirani bayan arba'in nake gaya mishi yadda mukayi da su, shiru yayi kaman baxai ce komai ba, sai chan daga baya yace, "auta kodai baka yafewa Baba bane"? "Subhanallahi, yayah ae ni ban taɓa riƙe shi da zafi a zuciyata ba, kullum goggo kyawawan halayen shi take sanar mun har na girma, bata taɓa aibanta shi ba yayah, ko ita tace mun ta yafe mishi ballantana ni da yayi sanadin zuwa na duniya? Wallahi ba haka bane, kawai dai naga saboda gado dama suka raba ni da shi, tou ni narayu da wuya da daɗi, gado kuma suje ni sadaka ma zanyi wanda zai isarwa Alƙali har kabarin shi". Ajiyan zuciya yayah ya sauƙe, sannan yamun fatan alkhairi sosai, ya kuma mun nasiha, wanda kullum tsakanin mu sai ya mana.

Lokacin da aka gama rabon gadon shi kowa ya tashi da abunda Allah ya hukunta iya rabin shi ne, Alƙali jinya ta cinye kuɗin shi, sannan kadarorin shi su Tijjani sun sayar, abun da yayi saura gidan shi ne, sai wasu filayen shi da suke chan bayan gari, sai motocin shi guda biyu, sai wani gidan hayan shi ɗaya da yake dutsin tanshi, haka aka raba gado kowa ya karɓi rabon shi, lokacin da mijin yayah safiya ya ƙirani, tare mukaje da yayah Rabi'u, bayanin komai ya mun, ya kuma gaya mun abunda yake nawa rabon, acikin gidan mu side ɗin Baba na shine ya tashi a rabo na, sai kuɗin da aka sayar da wannan gidan da motocin Baba da filayen shi aka raba mana, kuɗin na barsu hannun mijin yayah safiya nace ina son a nemi inda babu ruwa a yi, ko da a masallaci ne ko kuma ƙauyen da suke buƙatan ruwa, ina so yazama sadakatul jariwa wa Baba nah, shi kuma gidan na barwa yayah umatiti, saboda nasan basu da ƙarfi ita da mijinta, yanzu haka ma baya komai, side ɗin Baba kuma parlor ne babba da bedroom da toilet, sannan kuma parlon ma akwai wani toilet a ciki da kuma ƙaton store, sai sama kuma ɗakuna biyu ne da ƙaton kitchen da store shima a wurin, kuma akwai fili a wurin, duk nace na bar mata, ɗago kai yayah safiya tayi tace, "mukhtari fushi kake da Baba ne wanda har baka son gadon shi"? Jujjuya kaina nayi alaman a'a, "fushi kuma yayah? Na isa nayi fushi da mahaifina nayi kuma tunanin gamawa da duniya lafiya? Waneni yayah, nidai kawai a zuciyata naji ina so na sadaukar mishi da dukiyan, gidan kuma ummatiti ta fini buƙata, ina tausayinta da yadda rayuwa ta juya mata, gashi bata aiki sai ɗan sana'an da take taɓawa, kuma gidan haya suke har yanzu, wannan wurin kuma zasu iya fitar da ƙofar su daban basai sun shiga ta gidan ba, nima kuma Allah zai buɗa mun wani lokacin", ina gama faɗin haka ta fashe da kuka tace, "tabbas Alƙali yayi gaskiya, gashi ba'aje ko ina ba komai ya fara nuna kanshi, Mukhtar Allah ya saka maka da alkahiri, tabbas ka taimaki umatiti, domin duk gidan mu ita da Tijjani suka fi kowa shan wahala, shi yaƙi tsayawa yayi karatu ko yayi wani sana'a, duk kuɗin Baba ya tsole mishi ido, gashi kuma yadda rayuwa ta mai da shi".

Haka muka gama rubuta duk yar jejeniyan da zamuyi, aka tsayar da magana kuma za'a samu lawyer da alƙalin da ya mana rabon gadon.

********* lokacin da saƙo ya isarwa umatiti, kawai sai gata a gidan mu ita da mijinta da ƴar'uwar ta, sun yi kuka sunyi godiya wa goggo, don son samu bana nan, naje wurin A.G baida lafiya, tou na tafi duba jikin shi, a wurin suka ƙira mahaifiyar su, wanda lokacin suna takaba, duk da sun fita arba'in, amma ba kowa bane yake sakewa ya fito, kuka maman su tai tayi tana neman gafarar goggo, daga nan kuma tayi ta godiya tana saka mun albarka. Daga gefe na koma umatiti ce ta ƙirani tana kuka tana mun godiya, mijinta ma karɓa yayi yai godiya, sannan mamanta ma ta karɓi number wayana tayi ta neman gafara na tana kuma bani haƙuri, kafin kice me magana ya zagaye gidan Alƙali, ƙannen mahaifina duk sai da sukaje sukayi wa goggo godiya, sannan suka karɓi number na sukayi ta mun godiya, har hajiya sai da ta kirani tayi ta saka mun albarka, nidai har nafara jin kunyar ɗaukan baƙon number, a haka dai naga wata baƙuwar number ta shigo mun, ina ɗauka kuwa ashe Tijjani ne, kin san meya ce mun"? Girgiza kawai nayi alaman a'a ina share hawayena, murmushi yayi yacigaba

Yana ɗauka kawai naji yace "mukhtar kai kuma yayah akayi ka kyautar da wurinka wa mace? Ina laifin cikin mu ko ni ko shehu ae sai ka bayar wa ɗaya daga ciki, yanzu fah kaman wa mijinta ma kabayar domin gaba ƴaƴanta ne zasu gaje wurin kaga ya koma na mijinta, kawai kace mata ka fasa, idan yaso sai ka bani ko kabawa shehu". "a'a yayah baza ayi haka ba, kaga fah ita umatiti ƴar'uwar muce, kuma itama tana cikin rashin wurin zama, kawai ayi haƙuri da hakan idan muna tare kowa ma zai mallaki nashi, fatan dai Allah ya jiƙan Babah da rahma", ina jin da ƙyar ya amsa Ameen ɗin, don ba haka yaso ba, kuma babu yadda ya iya dani, tunda gida dai nawa ne, koda goggo taji yadda mukayi da ƴan'uwa na daɗi taji, don ko ita abunda tace kenan, sun raba tsakanina da mahaifina akan gado ne, tou suje gado baya gaban mu, fatan mu kowa Allah ya bashi nashi.

*********** Haka rayuwa tayi taja damu har suka fita Takaba, bayan nan kaɗan umatiti suka fitar da ƙofan da zai shigar da su gidan, kuma wurin yayi kyau, suka tare a ciki, iyaye mata kowa side ɗinta ya fito a gadonta, sannan duka cikin gidan da wani babban fili inda ɗakunan masu aiki da kitchen na waje yake, da wurin packing mota duk gadon su tijjani ne, suma anware wa kowa nashi, babu wuya wurin ubangiji komai namu yayi ta tafiya yadda Allah ya so har muka zo kowa ya samu abunyi, shi A.G barrister ne, yana aikin shi anan Abuja office ɗinsu ɗaya da Ahmad, sannan akwai wani chamber da suke zuwa chan tare, ni dai Contractor ne, kuma ina ɗan taɓa ƙananun business na fita da abu waje, kaman china, sai kuma na shigo da nasu, Abuja kuma mun sayi gida a wuri ɗaya nida A.G, domin plan ɗinmu kenan, yanzu haka kowa jiran abokiyar zama yakeyi, duk da dai shi A.G ya samu, nine dai nake laluɓe", ya ƙarasa maganan murmushi ɗauke da fuskan shi, sannan idon shi kuma zube a kaina, ganin haka sai na maida kallona ƙasa, "kinji taƙaitaccen labarin *MUKHTAR GARBA* Da ɗan'uwan shi *ALIYU GARBA INUWA* Kinji irin abotan da yake tsakanin mu, da amintan da yake tsakanin mu ko, kinji irin rayuwar dana sha a rayuwata mai daɗi da marar daɗi, kinji irin hidima da kyautatawan da A.G da iyayen shi har da kakanun shi sukayi a rayuwata dana ƴan'uwa na har dana yayye na,? Dalilin baki tarihina da labarin rayuwar mu abu ɗaya ne, a tunaninki akwai wani abu wanda bai kaucewa addini na da shari'a ba da A.G zai so naƙi mishi? A tunani na da ana kyautan rayuwa A.G ya chanchanci na mishi, A.G sun inganta rayuwa ta batare da sun goranta mun ko a wasa ba, A.G ya mayar da iyayen shi nawa, ƴan'uwan shi nawa, mahaifiyar shi ta haɗa ƴar ta aure da yayah na ba tare da shi ya nema ba saboda ta ƙullah dangantaka mai ƙarfi a tsakanin mu, akwai abunda bazan iya yiwa A.G ba don ya samu farin ciki a rayuwan nan ba"?

Girgiza kai kawai nakeyi ina kallon shi cike da tausayawa, a haka na sake tsinkayo muryan shi ya cigaba da cewa, "shawaran da nake so muyi da ke, kina ga yakamata na nemi auren ƴar'uwar shi *HEEDAYAH*"?

Readers Also Read