Ana barin halal original by anty nice - Chapter 14
Ana barin halal original by anty nice Chapter 14: Ana barin halal original by anty nice Chapter 14. Lokacin da muka rabo da abokina sulaiman, sai nayita…
4,339 words
Lokacin da muka rabo da abokina sulaiman, sai nayita tunanin ina zan samu waya na ƙirashi? Babu ɓata lokaci na tuna da gidan Alƙali, banyi shawara da kowa ba na wuce direct gidan, don na taɓa jin yayah hassan da yayah hussain suna labarin wayan a tsakar gida yake, kuma ana barin mutane suna ƙira da shi, don sun taɓa raka wani abokin su yayi waya da yayanshi da yake Abuja, tuna haka ya sakani tafiya gidan kai tsaye, cikin sa'a kuma ina isa saiga ƴar'gidan mai suna Ummatiti, domin lokacin ita ɗin budurwa ce, ganin ita tana da sauƙin kai don bata da hayani da faɗa irin na yaran gidan, ba kamar ƙanwarta waleedah ba, da sauri naje inda take shirin shiga gidan na rusuna nace, "ina wuni Aunty ummatiti" da hanzari ta juyo ta kalle ni fuskanta ɗauke da murmushi tace, "ƙanina yau kaine da kanka kake gaishe ni? Yau ka kawo mana ziyara ne? Lallai girma ya fara zuwa", tana faɗa hannunta riƙe da ni, nidai ban kawo kalmar ƙanina da ta faɗa da wani muhimmanci ba, kawai dai na ɗauka don ta girme ni ne. Ina murmushi na nace, "nazo ki taimaka ki ƙira mun abokina mana Aunty", na faɗa ina miƙa mata takardar da yake ɗauƙe da number shi, murmushi tayi ta miƙa hannu ta karɓi takardar, tana riƙe dani muka fara shiga cikin gidan, "haba ƙanina kai da gidan ku sai ka nemi izini na? Kaima fah mai yiwa wani alfarma ne", nidai sai daɗi nakeji muka shige gidan, lokacin babu kowa a tsakar gidan mai cike da interlocks, tsakar gidan mai girman gaske, yana ɗauke da wani varender mai kyau, wanda zai sadaka da babban parlon iyalen gidan, ana a gefe akwai wani friedge dogo da aka ɗaura telephone ɗin akai, babu kowa sai masifaffiyar mai tuwon gidan sun nan, muna shiga ta fito daga kitchen fuskan ta ɗauke da fara'a tace, "lale maraba da uwar masu gida, uwar ɗakina kin dawo kenan"? Murmushi Aunty ummatiti tayi tana saƙo da wayan ƙasa, "eh Babah na dawo, gashi yau na haɗu da autan mu wai yazo zaiyi waya, shine fah ya tsaya a waje yana neman alfarma, bayan shima mai yiwa wasu aƙfarman ne", ta faɗa tana saka numbobin akan wayan, nidai daɗi kaman zan yi tsalle, ɗagowa tayi ta kalle ni tace, "ƙanina ina ga ana kan layi ne, amma zo kaga yadda ake yi, ni zan shiga na chanja kayane, idan baka gama da wuri ba zan fito mu sake gaisawa, sai na kaika ka gaida mamana," murmushi nayi domin wani daɗi nakeji idan tace mun ƙaninta nan, duk da bawai wani kyau take da shi ba, don baƙace sai dai doguwa ce kamar mahaifin mu, amma banga ta yi kyau kaman shi ba, sai dai akwai jininshi a tare da ita, so baza ace bata da kyau ba, don akwai ido da dogon hanci, sai dai baƙar fatan kawai. Tana juyawa ban wani ɗau lokaci mai tsawo ba na gwada saka numbobin yadda ta gwada mun, ae kuwa sai naji wani ƙuwwwwt, ƙuwwwwttt, alamar yafara ringin, banji ɗaukan wayan ba sai naji wani abu mai azaban zafi na ɗaukan hankali a gadon baya na, da ƙara abun da fita a hankali na duk alaokaci guda naji shi, kuma ban ƙara jin komai ba ko fahimtan komai ba sai zuwa wani lokaci da naganni kwance a ɗakin goggo na, goggo da innah ƴan'biyu da dukkan yayuna, banda yayah auwal da baya nan duk suna tsaye akaina, gefe ɗaya kuma ga Umar mai chemist a tsugune akaina yan gyara mun drip, kaman ma yana chanja wani ne, don maga kaman sabo ake ɗaurawa, tashi naso yi amma sai naji wani azaban zafi a bayana, bansan lokacin da nace, "wash Allah" Da sauri goggo ta riƙe ni idon ta na zuban hawaye tace, "mukhtari na sannu ko, ka tashi?.... Mekake so?" ta faɗa hawaye yana ƙara bin fuskanta, gefe ɗaya kuma Rabiu ne ya riƙoni jikin shi yana mun sannu. Mai da ido na nayi na rufe ina jin wani mummunan azaba a jiki na, ga wani nauyi da naji kaina yayi mun, ga hannu na ɗaya da naji kaman ba ajikina yake ba dom azaban azaba, a hankali na sake buɗe idona nace, "goggo na ciwo nakeji, me ya same ni ne"? Kuka Goggo ta fashe da shi gaba ɗaya ta rungume ni a jikinta, muryanta da jikinta gaba ɗaya suna rawa, "haba mukhtari na, meyasa ga cikin malam Garba, kaƙi ka fito a cikin wanda bai san daraja da girman ka ba? Wanda me aikin boyi - boyi ma agidan shi tafi daraja da girma? Wannan abu yana mun ciwo ni Fatima, wannan abun yana firgita ni, Allah ka raya mun mukhtari na, Allah ka ɗauka ka shi ɗaukakan da kake yiwa bayin ka nagari makusan tanka, Allah kayiwa mukhtari ni tanadi na alkahiri duniya da lahira, Allah ka ciyar da su a jikinka yadda basu ƙaunar ka Allah ka ƙaunace shi", ta ƙarasa tana fashewa da kuka, chan kuma naji muryan Bappan mu yana cewa, "ashha Alƙali basu kyauta ba, yau har an ƙure wannan baiwar Allah mai haƙuri, gaskiya basu kyauta ba Allah ya saka maka mukhtari, Allah ya fitar maka da hakkinka akan duk wanda yake da hannu aciki, don wannan kam ba halin Alƙali bane, yaran wasu ma ya riƙe, yaran nashi ma nawa ne? Amma duk gidan cike yake da yaran ƴan'uwa, ashsha abu bai yi daɗi ba", ya faɗa yana matsawa jikin ƙofa, inna dai sai kuka take tayi Allah kaɗai yasan me yake sakata kuka, nima sai lokacin na fara kuka don ganin ƴan'uwa na da goggo na suna ta kukan, wanda ni har lokacin ban san me ya faru da ni ba, don sai daga baya goggo ke hiran da yayah auwal da yazo tukun na sani, kin san waye ya mun haka"? Girgiza kai nayi alaman a'a, fuskana cike da tausayin shi har da goggon shi da ƴan'uwan shi, Murmushi yayi ya sunkuyar da kanshi ƙasa yayi shiru na wani lokaci.
Shifaɗo mai tuwon gidan mu, wata muguwar bafulatana ce garin su yana kusa da yankari, ni ban taɓa ganin muguwar mace ba irinta, ashe ganin yadda Aunty ummatiti tayi mun sai ranta ya ɓaci, windon ɗakin maman su ummatiti ta zaga ta kai mata gulman, ita kuma maman su Aunty da yake itama muguwar ce sai tace maza ta koreni, babu ɓata lokaci kuwa shifaɗo ta shigi ɗakin da ake zuba itace, ƙato ta ɗauko, shine ta zanga mun a baya na, gashi jikin shi akwai ƙwarzane na faskare, shine yayi mun wani yanka a bayana, Allah ne kawai ya kiyaye bata naƙasa ni ba, domin ba ƙaramin ciwo taji mun ba, amma abinda zai baki mamaki da haushi abu ɗaya ne, haka aka ɗauke ni ranga-ranga aka kaiwa goggo nah, ƴan gidan mu ne suka nemo wani ma'aikacin chemist yazo ya dubani, bayan yayi mun dressing ya ɗaura mun drip, shima a duk ƙoƙari na goggo ne, don da bappan su yayah auwal yaje ya samu Baba nah da maganan abunda ya faru, sai yace shi tou me zai iya cewa akai? Yaron ne ae mai laifi,, me ya kai shi gidan, shi ae yace kada a taɓa dosan shi da al'amurah na, jikin kowa sai da yayi sanyi a gidan mu, shine kukan da goggo na tayi kaman babu gobe, nidai an dake ni an daki banza, don ko gidan mu babu wanda ya biyo bayana banda Aunty umatiti, don ita har kuɗi tabawa goggo akaini asibiti, amma goggo taƙi amsa, ta mata godiyan shigowan da takeyi dai, anyi abun da ƴan watanni ne yayah auwalu yazo, a lokacin ne kuma naji goggo tana mishi bayanin abunda ya faro, anan kuma masan Alƙali shine mahaifina, lokacin dana fahimci haka nayi kuka baka ɗan ba, don wallahi ayshaa banyi farin ciki ba,", ya faɗa lokaci ɗaya dana taɓa ganin ranshi babu daɗi fuskan shi a wani irin yanayi. Ajiyan zuciya nayi na share hawayen da bansan lokacin da suka zubo a idanuna ba.
Muna haɗa ido yayi saurin kawar da nashi gefe, sannan ya cigaba da bani labarin, "Ayshaa nayi jinya sosai, don da ƙyar ciwon ya warke, amma lokacin dana warke sai naji ko ƙofan gidan Alƙali bana son gani, duk wani abu daya ƙunshi ƴan gidan kuma sai na kiyaye, Babbar jikar shi ƴar gidan safiya lokacin ake bikinta, Babanta wani babban mutum ne a cikin garin bauchi, don shahararren ɗan siyasa ne, ita kuma sa'o'i suke da umatiti, watarana na fito ta lungun da zai kawo ni gidan mu ɗauke da tallen masa na sai mukayi kicibus da ita tare da umatiti, tsayawa umatiti tayi hannunta riƙe da haɓan ta tace, "ɗan'uwa idonka kenan? Wato guduna ma kakeyi ko? Tou ko kaƙi Allah kai ƙanina ne, kuma favourite ƙanina", ta faɗa fuskanta cike da fara'a tana miƙa hannun ta ta sauƙo da tallen masa na, nidai murmushi kawai nakeyi don gaskiya ita bazan iya rabuwa da ita ba, kuma baxan iya ƙin kulata ba yadda aka ce kada na ƙara kula ƴan gidan alƙali, buɗe daron masan tayi taga saura guda ɗaya ne a ciki, tana kallona fuskanta da murmushi tace, "wayyo ƙanina yayi kwantai ɗin guda ɗaya, tou nawa ne a bani naci"? Murmushi nayi na ɗauko leda na saka masan a ciki, cike da kunya na miƙa mata nace, "Aunty gashi ba sai kin bada kuɗin ba, dama zan kaiwa mai baran gefen gidan mu ne", na faɗa ina cike da kunyanta, "wasa nake maka ƙanina", ta faɗa tana juyawa wurin ta gefentan tace, "wannan fah shine ƙanin mu wanda baba ya auri matan malam garba", Murmushi ɗayar tayi tace, "ae naga kaman shi sosai da kaka wallahi, ae ko yau zan gayawa mama naga autan su", itama umatiti dariyan tayi tace, "ɗan farin gidan mu ba," kallo na tayi tana nuna ta gefenta tace, "ƙanina wannna ƙatuwar da kake gani ƴar kace, domin mamanta ce babbar yar mu, auren ta za'a fara wannan satin, fatan dai zaka zo mana ko"?. Murmushi nayi idona akan amaryar mai suna ummulkhair, itama murmushin tayi tace, "zakazo ko kawu"? Faɗin kawun daa tayi yasaka na ƙyalƙyale da dariya, suma duk dariyan sukayi, ummul ɗin tace, "kana dariya ko? Sai kaga na turo mai auren nawa yazo gaishe da kawu mukhtar tukun zaka yadda kai kawu ne inaga", dariya na sake ƙyalƙyalewa da shi, kyautan kuɗi ta bani amma naƙi karɓa, da suka matsa mun nace , "za'a mun faɗa ne a gida idan anganni da kuɗin," basu ja ba suka mun sallama nima na musu na wuce ina ta waiwayan su, a ƙarahe zasu fita lungun suka ɗaga mun hannu, cike da farin cike na shigo gidan mu.
********** Rayuwa ta juya damu yadda ta so, mun sha wahala kaman abubuwa baza su wuce ba, sauƙin mu idan iyayen A.G sun mana aika mukan ɗan farfaɗo, ko kuma idan Alhaji inuwa ya waiwaye mu, sannan har zuwa wannan lokacin su suke biya mun kuɗin makaranta, amma duk da haka idan akace mace ita zata riƙe marayu, gaskiya akwai wahala, Allah sarki goggo, ta wahala da mu tayi hidima da ɗawainiya damu sosai, babu abinda zamuce sai dai Allah ya biyata, haka rayuwa tayi ta ja damu har yayah sanie ma ya gama karatu, a lokacin kuma yayah auwal ya samu scorlaship zuwa masters ɗin shi a spain, murna kaman zamuyi yaya da ranmu. Kafin tafiyan shi ya tattaro ya dawo bauchi, lokacin kuma yayau sanie ya tafi service a *KADUNA* bayan tafiyan shi da 1month yaya auwal ma ya tafi, ga yaya rabiu lokacin bai cika zama ba, suna yawan fita ball da club ɗinsu na wikki, munsha wahalan kewan su, a lokacin kuma na ƙara dagewa da ƙwazon tallen masa, don zuwa lokacin innah ƴanbiyu ta haƙura da sayar da komai, mune dai kawai muke iya ɗawainiya da ita, babu abunda ya dameni da mutane, har nazo aji biyar na secondry ina tallen masa na, lokacin su twins suna karatu a maiduguri.
******** Yayah sani ya kwana biyu bai samu aiki ba, don sai da ina ss 2 tukun ya samu aiki a CBN, daga lokacin abubuwa suka fara mana sauƙi na rayuwa, abun farin ciki kuma muna gama secondry school su A.G suka dawo ƙasan, lokacin dsddy yayi ƙerarren gidan shi a fadaman mada, lokacin da A.G suka dawo ƙasan idan kin ganshi kaman wani bature, gashi lokacin shirun shi ya ƙaru sosai, ranan tsabar murna kuka A.G ya fara da ya ganni, a gidan Alhaji Inuwa muka kwana babu wanda ya hanani, har gida mukaje da goggo tayi wa mummy barka da dawowa, idan kaga mummy baxaka ce ita ta haifi A.G ba, domin mummy irin mutane masu faran -faran da mutane ne, gashi tana da son hira, amma A.G ko yadda kika san kurma, sai dai kuma yana da bala'in fahintan mutane a rayuwar shi, zaman lokaci kaɗan zaiyi da kai ya fahimci kai waye, kuma zakaga kaman baya hankalce da kai, Ayshaa naji daɗin dawowar su A.G ba kaɗan ba, result yana fitowa babu ɓata lokaci muka samu admission a *ABU ZARIA* Law suka bawa A.G, ni kuma Mechanical engenearing, haka muka sake ƙullewa kaman bamu taɓa rabuwa ba, a wannan lokacin kuma farina ya samu dama da sararin sake dawowa, don komai daddyn su yake mana babu banbanci, hatta sutura babu banbanci a tsakanin mu, ballantana kuma mummy da tafi sakewa ma da ni akan A.G. Muna gama university Daddy ya sayawa kowan mu mota, nawa fari na A.G baƙi, amma duk iri ɗaya ne, a lokacin kuma yayau auwal yazo nigeria, yayi wani irin zama babban mutum gashi ya samu aiki acan bayan ya gama karatun shi, yazo da maganan auren shi da ƴar ubangidan shi da suka zauna a lagos, dama mutumin ɗan nan unguwar mune kobi, zama ne kawai ya kai shi lagos ɗin da iyaleshi.
Babu ɓata lokaci aka saka rana, kafin ya koma kuma akayi auren su, yanzu maganan da nake miki suna chan spain da familyn shi, yaran shi uku duka maza, yayah sanie kuma yana zaune a lagos da matar shi itama ƴar bauchi, yaran su huɗu, mata biyu maza biyu, sai yayah rabi'u da yake zaine a nan bauchi, amma yana da team a waje da yake zuwa bugawa, kuma yayi nisa a harkan ball sosai, yaran shi biyu duka maza, sai twins, yayah hassan yana auren ƴar ƙanin su innah, Ɗan su ɗaya, sai yayah hussain da yake auren sister A.G *HUDA* su kuma twins suka haifa duka mata, yanzu saura ni autan goggo" dariya duka muka ƙyalƙyale da shi. Bayan mun gama service sai A.G ya tafi law school, anan suka haɗu da Barrister Ahmad, anan kuma Allah ya haɗa jininsu sosai, nima dalilin A.G Allah ya haɗa jininmu, nasamu kuɗi a cikin shekara biyu na ban mamaki Ayshaa, Daddy shi yayi mun hanya ta hannun wani mutumin shi bayarabe a lagos, na samu contract bana wasa ba, sannan yaxo ya haɗani business da wani abokin shi balarabe, inda shima yayi mun hanyar haɗuwa da wasu a china, tou shine sanadin arzikina, wanda sanadi addu'an iyaye ne yake tafe dani, yanzu haka nayiwa goggo gida a bauchi, ɗuk wani abun jin daɗin rayuwa goggo ta samu, sai dai inna ƴanbiyu shekara biyu Allah yayi mata rasuwa, baki tambaye ni ina Baba nah ba"?
Murmushi nayi ina kallon shi cike da tausayin rayuwar shi nace, "ae nasan bazaka manta ba, idan an zo wurin zaka gaya mun".
Murmushi shima yayi yace, "gaskiya ne kam."
Baba nah ya aurar da yaranshi dukkan su, ummatiti tana auren wani ɗan bauchi, a lokacin banker ne, mamanta tana ta ɗaga kai wa mutane, don ya mata kaya na fitan hankali, auren su nada 5years yaran su biyu, alokacin banki suka mishi halinsu, bayan an sallame shi aiki sai abubuwa suka dagole musu, amma dai Baban mu bai barshi haka ba sai daya sama mishi aiki a ATAP, samun dai ba irin na da ba, ita dai ummatiti bata damu ba, saboda tana son mijinta, yanzu haka yaransu shida da shi, sai mai bi mata *WALEEDAH* ita wani ma'aikacin nefa ta aura, yanzu haka suna zaune a federal low-cost bauchi, ita ma yanzu haka tana da yara kusan shidah, duk da rayuwa ba yadda suka so ba, sai dai godiyar Allah, ita babbar yarmu yanzu mijinta girma ta cin mishi, gida de idan kin gani ginin gidajen manya ne, amma babu komai na kwabo a hannun shi, hakan yaran ta biyun su TJ duk babu wanda yayi dogon karatu a cikin su, kaman ƙaramin sune ma yayi diploma, duk dai nauyi ya hau kansu na iyalai, kuma Baban ne dai a tsaye akan kowa.
Lokacin da muke service Baba na ya kwanta jinya Kidney, duk wani kuɗi na Alƙali ya ƙare akan jinyan nan, India aka fita da shi aka cire kidney ɗin shi aka mishi dashe, dawowan su nigeria bai ɗau lokaci ba ya sake kwanciya jinya a Gombe, gashi su Tijjani basu bar shi ba da sata, komai nashi sai godiyan Allah, haka akai ta sayar da kadaran shi ana jinya, wata ranan Monday da bazan taɓa mantawa ba Aunty ummatiti ta ƙirani da safe a waya, da yake muna zumunci da ita, kuma ina zuwa gidan ta, sai dai gidan mahaifinane kawai ban taɓa shiga ba tunda abun nan ya faru, Yayah safiya ma ina zuwa gidan ta, domin ni da ummul ƴar ta muna zumunci, don duk shigowanta bauchi sai ta nemi ni, idan naje ne wurinta muka saba da yayah safiya, ita yayah safiya kana ganin mu kasan ƴaƴan mutum ɗaya ne, saboda yanayin zubin halittan mu iri ɗaya ne, hatta da bakin mu akance irin na Alƙali ne, banbancin ni fari ita baƙa, lokacin da ta ƙirane ta ke gaya mun Baban mu ne yasaka ta ƙirani a waya yana nema na, tsoro maganan ta ya bani, don ban taɓa tunani ko zaton Alƙali zai nemi ni ba, nidai ban bata cikakken amsan zan zo ko bazan zoba, zuwa yamma ta sake ƙirana, shiru nayi ban ce komai ba, sai da ta matsa mun tukun nace Goggo bazata bari ba shiyasa, shiru tayi zuwa wani lokaci, bata sake cewa komai ba sai sallama da ta mun, Na ɗauka ta bar maganan kenan, amma kawai ranan laraba sai ga yayah Rabiu ya shigo ana idar da sallan Magrib, bayan sun gaisa da Goggo ne sai ya ƙira number yayah auwalu, dogon bayani yayiwa goggo akan Alƙali ya neme shi a waya akan don Allah su taimaka mishi naje yana son ganina, da ƙyar yaya auwal ya lallaɓa goggo, don sun fi awa biyu ana abu ɗaya, ranan goggo taci kuka kaman yau komai suka faru, bayan sun gama ne yayah rabiu ya ƙirani na shigo, bayanin duk yadda baba nah da yayah auwal sukayi Yaya Rabi'u ya bani, sannan ya umurceni na shiryah gobe insha Allahu da sanyin safe zaizo mutafi Gombe asibiti na gaida babah nah,.
Faɗin baba nah ɗin da sukayi sai duk najini wani iri daban, ina kallon goggo yadda take ta kallo na cike da tausayawa, hakan duk sai yasa naji hankali na ya ƙara tashi, nidai tsakanina da Baba nah babu sabo, don zance a girmana na gaisa da shi kusan sau biyu, ɗaya lokacin auren yayah auwal ne, na fito daga ƙwallo shi kuma suna tsaye tare da limamin unguwar mu a ƙofar wani gida, daga gani kuma gidan abokin shine, don shima alƙali ne, kallon da liman ya bini da shi yasaka na tsaya na gaishe su, har na kure layin idon Alƙali yana kaina, sai wani haihuwan ummatiti na uku, ina zaune a parlon ta sai gashi ya shigo shida abokinshi da mijin Aunty umatiti, babu yadda na iya dole na gaishe su, lokacin farkon shiga na university, wannan ranan ma har na fita idon shi yana kaina, Saboda haka duk sai naji hankali na a tashe, zuwa dare kuma sai naji na samu kaina da tunanin tou yyh jikin nashi yake da har yake nema na? Tou idan naje me zaice mun? Haka dai na haƙura na kwanta.
********** Washe gari wuraren ƙarfe goma na safe muka shiga asibitin Gombe, muna shiga Aunty umatiti ta fito ta tarye mu har zuwa ɗakin da Alƙali yake, koda muka shiga mun samu yana bacci, a haraban asibitin illahirin matan shi ne da ƴaƴan shi zaune a kan darduma, gaishe su mukayi amma suka mana wani irin amsawa, mudai bamu tsaya bin takansu ba muka wuce ciki, a ciki muka tarar da Yayah safiya da mamanta, wato uwargidan Alƙali, sai kuma Tijjani, da fara'a matar ta amsa gaisuwan mu, wanda naji suna ce mata *HAJIYAH* sannan na risina na gaisa yayah safiya, itama da fara'a ta amsa mun, har tana tambaya na "yayah karatu", banzan kallo Tijjanin ya mana lokacin da muke gaishe shi, amma daga ni har yayah sanie bamu bi takan shi ba, saboda babu abunda ya fimu kuma muna cikin kyakkyawan kama da shiga. Shiru ɗakin yayi bakajin komai sai ƙara na'ura sai kuma nishin Alƙali kaɗan- kaɗan, alaman jinya taci jikin shi, gaba ɗaya ya rame yayi baƙi, sai naji tausayin shi da tausayin kaina ya kamani, yanzu wannan ɗin mahaifina ne a kwance? Wanda yayi silan zuwa na duniya? Sai naji wani rauni da ban taɓa samun kaina a ciki ba, tsakin da Tijjani yaja ne lokaci ɗaya ya maida hankalin mu kanshi, "tou wai tunda kun samu yana bacci kujira mana a waje sai ya tashi tukuna", yafaɗa kaman zai kai mana duka, murmushi hajiya tayi tana kallon shi, "wani irin magana ne haka Tijjani? Ae yadda Alhaji yake ta jiran isowar mukhtari kyaunta ae yana farkawa ya fara cin karo da shi, kai kafita ne da kake cewa wasu su fita? Ko ka manta duk matsayi ɗaya kuke taƙama da shi a wurin shi? Yadda kake ɗa na halak, haka fa kowa da ka gani agidan nan yake a wurin shi", hajiya ta faɗa still fuskan ta da murmushi, kyaɓe baki Yayah safiya tayi ta harari Tijjani ta mayar da kanta wurin Aunty umatiti suna magana ƙasa-ƙasa.
Tsaki ya sake ja yace, "hajiya me ya kawo wannan maganan ka nan? Idan dukkan mu ɗaya ne a wurinshi ae dai ni bai jefar da ni ya barwa duniya ni ba, kuma idan shi wannan da bani da tabbacin ɗan Alhaji nema na gaske ya shigo ya zauna, tou shi ɗayan fah? Gayyan meye nashi shi kuma?" Murmushi yayah Rabi'u yayi ya gyara tsayuwar shi yana facing ɗin Tijjanin, "gayyan autan shi na biyo, nazo da ɗan halal wanda mahaifinka ya nunawa duniya wannan ɗin ɗane kuma na halak, tunda kusan kwana nawa yake roƙan akawo shi su gana idan akwai rabon ganawan, kuma ina mai maka albishir cewa ɗan da aka barwa duniya, tou duniyar tayi mishi riƙo na gata da mutuntawa sama da wanda aka adana a gida ya ɓuge da tanɓelen rayuwa, rayuwar ma na hakkin wanda basuji ba basu gani ba, kuma wa kake da suna, tijjani ne kake ko wa? Tou kachi darajan jinin mahaifina da yake yawo cikin jinin naka mahaifin, kuma chi darajan jinin ƙanina da yake yawo cikin naka jinin, kuma kachi darajan marar lafiyan da yake kwance cikin bautar ubangiji, da wallahi idan na haɗa maka yawo da majina da haɗin jini a bakinka, da har abada ko shege ka gani bazaka sheganta shi ba ballantana ɗan halal, idan kuma kana jayayyah da hakan tou kaje wurin tsohuwar ka ta baka amsan *MUKHTAR ALƘALI ABDALLAH* ɗan waye? Waye sanadin rashin girman shi a gidan mahaifin shi? Tou amma......" Yayi shiru yana girgiza kai bai ƙarasa ba, sai ya juya kaina yace, "M.G zan ɗan shiga gari, duk yadda ake ciki ko Alhajin ya tashi ka ƙirani, sannan duk abinda ya faru kayi haƙuri darajan wannnan" ya nuna mun Baba nah da yake kwance, ɗaga kai nayi alaman naji, sanann yayi sallama wa hajiya ya juya ya fita. Tsaki Tijjani ya sakeyi ya juya ya fita a ɗakin, tsaki Aunty umatiti tayi ta nuna mun wurin zama sannan ta fita a ɗakin, bayanta yayah safiya tabi, aka barni daga ni sai hajiya a ɗakin, haƙuri hajiya tayi ta bani, ni dai bance komai ba sai murmushi, anan take bani labarin yadda Alhaji ya burkice tun suna India akan a nemo mishi ni nayafe shi, shi kam a nemo mishi Fatima da abunda ta haifa ɗan shi, haka dai akaita rarrashin shi ya haƙura, suna dawowa nigeria kuma sai abun ya mance mishi a kai, amma tun wancan satin ya ɗaga hankalin shi akai, tana kallo na tace, "kasan duk abunda ba na Allah da Annabi ba akwai ƙarshen shi, sai dai ba'ayi haƙuri ba, tou kaima ina ga tsakanimka da mahaifinka da aka shiga ne Allah ya kawo ƙarshen abun, duk da dai nasan ba haƙura za'ayi ba, sai dai Allah ya mana jagora kawai, amma akwai hakki kan, kaima sai ka dage da azkhar sosai," Ta faɗa idon ta akan Alhaji da yake ɗan mutsawa, nima da sauri na maida idona kanshi, wanda da hankalina yake kan hajiya cike da rashin fahimtar maganan ta, da rashin fahimtar inda maganan ya dosa, miƙewa nayi tsaye lokacin da naji muryan mahaifina yana, "ina mukhtar ɗin yake? Ku ƙira mun shi muyi bankwana, ku nemo fatima ta kawo shi na ganshi, ku bada kayan sallan shi akai mishi Yayah", abun da yake ta maimaitawa kenan hajiya tana riƙe da hannun shi, ido na zuba musu ina jin wani irin tausayin shi a raina, zabgegen mutum ƙarfaffah shine yau ya dawo ɗan ƙarami da shi, gaskiya jinya batayi ba, babu babban maƙiyi irin ciwo, kallo ni hajiya tayi tana mun alaman na matso. Ina tsaye inda nake idona akan su, duk jikina yayi sanyi, ƙura mun ido Alƙali yayi, bayan ya gama buɗe idonshi akai na, muryah ƙasa-ƙasa na mai jinya yace, "mukhtar" kallon shi nakeyi kawai bance komai ba, hannun shi ya ɗago mun yace, "taho gareni auta, zo kagaya mun ka yafe mun, ina Fatima?"