Kenza eBookz

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 13

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 13

Ana barin halal original by anty nice Chapter 13: Ana barin halal original by anty nice Chapter 13. Ina shiga kuwa na haɗu da Areefh yana buga ball a…

4,426 words

Ina shiga kuwa na haɗu da Areefh yana buga ball a parlon su, gefe ɗaya kuma yayah muhammad ne ke ta aiki a laptop ɗinshi, six month banga Areefh ba, amma da yake muna yawan video call bai manta ni ba, sake ball ɗin yayi da gudu yayo kaina, shima yayah muhammad ajiye aikim da yakeyi yayi ya ƙura mana ido yana murmushi, bayan na ajiye kayan hannu na da sauri na tare Areefh na rungume shi muna ƙyalƙyala dariya, yana rungume a jikina na wuce wurin yayah muhammad, rungumeshi nayi ina dariya, shima dariyan yake ya rungumo ni tare da areefh yana oyyoyoooo bestyn yayah, muna haka Aunty B ta fito daga kitchen tana, "maraba da maman areefh, bestyn Baby na, dukkan mu dariya mukayi saboda Aunty B idan taso ta iya barkwanci, ajiye areefh nayi na ƙarasa wurin ta nayi hugging ɗinta, dukkan mu cike da farin ciki muka taho parlon muka zauna, gaishe su nayi suma suna tambaya na su ummie da su mamah, yayah muhammad yana tambayan ina hajiya ummah daro? Dariya mukayi saboda tuna last month da yayah yaje dagewa tayi sai ta biyo shi taga su Aunty B, wai ae mugunta ne tunda ya mayar da su Abuja yaƙi kawo su, ita zata saka a maida shi lagos ɗinshi su kuma su dawo nan kusa ya fi mata, da ƙyar aka lallaɓa ta akan zasu zo hutu ae kwanan nan, dariya mukayi sosai, Aunty ta miƙe zata koma kitchen nima sai na miƙe, juyowa tayi ta harare ni, "koma ki zauna ki huta ke da yayanki ku ƙara gaisawa, nima na kusa gamawa, jeeddah ce wai ke son cin miyar ɗanyar kuɓewa shi yasa kika ganni iwar haka a kitchen," murmushi nayi na koma na zauna muka cigaba da hira da yayah na, a haka kuma yaya Ahmad ya shigo suka gaisa, shima wuri ya samu ya zauna yana rungume da Areefh, hira suka fara na yadda maganan neman auren raliya ya taso suke yi, inda yayah muhammad ya juyo yana tambaya na ko akwai wanda muke tare ne? Girgiza kai nayi alaman a'a, "babu komai kar kisaka wani damuwa a ranki kinji besty, shi aure lokaci ne, kuma duk surutun mamie kada ki bari ya dame ki, insha Allahu mijinki special yana nan tafe, ki dage kiyi karatun ki kawai, daga ke har hafsy insha Allahu zakuyi aure na mutunci," yayah muhammad ya faɗa, yayah Ahmad yana jijjiga kai alaman haka ne, nan ma yayah Ahmad ke cewa, "nawa ma suke ne, yanzu ne fa zata je level 3, hafsy ko yanzu ne ma suka gama ss 3 ɗin, just 17yrs ne fa, Aysha suna 20yrs, gaggawa ne kawai irin na mamie har take waƴannan surutan, ni dai nacewa ummie kada ta ɗaga hankalinta, komai zaizo a lokacin da Allah ya hukunta, " "Hakane Ahmad, ae tun jiya da Abba ya gaya mun abun da ke faruwa na ƙira ummin har nace mata idan taga hankalinta zai tashi ta biyo Abba ta taho Abuja ta kwana biyu, amma taƙi wai kula da hajiya umma, ga umar ya gama service yana gida", cewar yayah muhammad, hira suke tayi nidai ina sauraran su rabin hankali na kuma yana tare da Areefh, a haka har aka ƙira magrib suka fita sallah, idan kin gansu kaman wasu ƴan biyu, don su ina ga ko abokai da baka ganin su tare sai junan su, ban taɓa ganin wa da ƙani da suke so close irin su ba, ko abun da ya shafi office gidajen su tou da junan su suke hiran, don da ku zuwa hira yayah muhammad zai tafi maiduguri tare suke zuwa kaman wasu aboka ne, kodan halin su yazo kusan iri ɗaya ne oho, amma banda nida hafsy, ayi shiri ayi tsiya, don ma mi bana kula tane, amma yanzu naga abun yafara mata sauƙi, tana yawan bibiyata muyi hira, ko tsakaninta da yayah ishaq ni take zuwa tayi shawara da, tom ɗinta an samu ɗan matsala ko sai daga baya? Side ɗin yayah Ahmad na tafi ɗauke da Areefh a hannu na, ina shiga na haɗu da Aunty jeeddah tana fitowa daga ɗakin yayah Ahmad, da murmushi ta tarye ni, ni kuma naje da sauri na rungumeta, bayan mun gaisa ta tambaye ni su ummie sai na wuce ɗakin ta nayi sallah, na idarr ina askhar sai gata ta shigo hannun ta ɗauke da kilishin da ummie ta saya mun, stool ɗin dressing mirrow taja ta zauna, ina ganinta har wani lumshe ido takeyi tsaban daɗin kilishin da takeji, sallaman Aunty B ne ya sakani fasa tsokanan da nake da niyyan mata, ita ma Aunty B ɗin bakin ta ɗauke da murmushi tace, " kai jeeddah anya tuwo na zai samu wurin shiga kuwa? Naga alaman kwantai zaiyi yau tunda an samu kilishin bauchi," murmushi Aunty j tayi, "Aunty wallahi yanzu na na shigo na tura ayshaa karɓo mana tuwon ne, sai naga tana askhar". Dariya Aunty B tayi tace, "tou ku fito parlon na shigo da abincin, chan su Abu areefh suna cin nasu kada mu damesu, naga hira yau sukeji da shi, ko sunyi sabon kamu ne suke irin wannan ƙus-ƙus ɗin yau? Don naga suna ganina suke chanja topic". Zaro ido waje Aunty j tayi, "haba Aunty ae ko ke bakici a miki kishiya ba ballantana ni da cin amarcin ban fara ba, kawai dai wani hiran su ne na daban da basu gamawa suke yi", dariya Aunty B ta kwashe da shi ina tayata, don ganin yadda Aunty j ta wani lanƙwashe kai kamar zatayi kuka, "waya gaya miki muma mum fara cin amarcin mu? Me ma akayi? Hala ma har ku gama na ku akawo amaryah ni bamu gama ba", Aunty b ta faɗa tana juyawa zuwa parlor, bakin ta ɗauke da dariya, da sauri Aunty J ta rufa mata baya tana, "haba Aunty ki dena irin wannan wasan, nifa ko hiran za a ƙara aure bana so ballantana aje ga batun za'a mun kishiya, Allah dai ya tsare mu da ita,", ta faɗa tana jan kujeran dinning ɗinta tana zama, muma zaman mukayi muna dariyan Aunty J, a haka muka gama cin abincin na tattare nayi side ɗin Aunty B na barsu zaune a parlor suna wani hiran daban, tattare wanda su yayah suka gama ci nayi na wuce kitchen duk na wanke su, mopping na sakeyi na fito parlon, ɗago kai yayah muhammad yayi yana kallona fuskan shi cike da murmushi, "hajjaju makkatun, ƴar Abba da ummie jikar ummah, ƙanwar Muhammadu da Ahmadu Adda da ummaru da habiba, yayar raliya da hafsy ikon Allah" dariya muka kwashe ni da yayah Ahmad, gefen shi nazo na jingina ina dariya, shima dariyan yayi yace, "baxaki mun liƙi bane sisto"? Dariya yayah Ahmad yayi yace ae kuwa kachi liƙi, da dollers ma kuwa zan maka", yana rufe baki wayana ya fara ƙara, da sauri na duba screen ɗin sai naga yayah M.G ne.

Murmushi nayi na maida wayan a silent, ɗago kai nayi sai muka haɗa ido da yayah muhammad, ganin irin kallon tuhuman dayake mun, bansan lokacin dana fara dariya ba ina rantse mishi ba fa wani bane daban Yayah M.G ne fah na faɗa ina yi hanyar barin parlon, dariya suka kwashe da shi su biyu, ina jin muryan shi yana cewa yayah Ahmad kaji mun yarinya da tsarguwa, tou idan tayi wari zamuji ae, nidai ban ƙarasa jin sauran abun da suke cewa ba nayi gaba, sai dai ima jin dariyan yayah Ahmad, ina shiga parlon ban saurari su Aunty J ba na wuce ɗaki, rufo ƙofan nayi na nemi wuri na zauna, kaman jira yake call ɗinshi ya sake shigo mun, cikin nutsuwa na ɗauka ina mishi sallama, "sisto nayi fushi, nayi fushi da ke, munyi waya da ke fa jiya, amma ko kice mun zaki shigo Abujah, adalci kenan?" Rufe fuskana nayi kaman yana kallo na ina dariya nace, "nifa na ɗauka yayah Ahmad ya gaya maka"? "sauƙe tou don dai kam bai gaya mun ba, kuma bashi ne ya kamata ya gaya mun ba, kece ya kamata naji daga wurinki, yanzu sai da A.G yagaya ya tukun na san kinzo, hala har muyita waya baza kice mun kinzo ba, don kada ɗan marayan Allah yazo ya ganki". Cike da mamaki nace, "shi kuma yayah A.G ɗin yayah akayi yasan nazo"? Dariya ya kwashe da shi yace "wurin yayanki yaji kin san shi da bin dindigi yasan komai da yake faruwa a ƙasan, yakan riga sanin wani abun ma misali kaman wannan", ya ƙarasa faɗi yana murmushi, ajiyan zuciya na sauƙe, ni dai mamakin abun kawai nakeyi, "tou shi ina ruwan shi da sanin me nake ciki? Na ɗauka ma ya manta dani ae zuwa yanzu"? "kina ƙanwar aminin shi ne zakice ina ruwan shi da sanin me kike ciki? Tou ae yanzu ko shi barrister ba lallai bane yabi ƙwaƙwafin rayuwar ki irin A.G, kinsan shi fa yana da mugun kiyayewa akan abunda yasa a gaba, yanzu hala ma result ɗinki ma ya riga ki sani" ya faɗa yana dariya na. Nidai share maganan nayi na cigaba da gaishe shi, "sai kin koma sch tukun zaki bar Abuja ko"? Najiyo muryan shi yana mun tamabaya, "ehh insha Allahu" na bashi amsa. Kafin ki tafi insha Allahu zan shigo, domin yanzu akwai wani aiki dana tafi yi a Benin, kafin komawanki insha Allahu zan dawo", daga nan muka ci gaba da hiran mu yadda kullum muka saba, har muka gama hiran bamu sake sako sunan A.G a ciki ba, bayan mun gama wayan ne na fito zuwa parlor, anan na samu yayah Ahmad ya shigo, ashe ita kuma Aunty B har ma ta tafi gidan ta, ban wani ja lokaci ba nayi musu sallama na koma ɗaki, domin ummie tana yawan tunatar damu, idan munje gidan yayun mu muna rage zama a wuri idan suna tare da matan su, idan an taɓa hira kaɗan mu basu waje.

Kullum idan na tashi da asuba, ima idar da sallah nayi azkhar zan gyara gidan gaba ɗaya, kuma har side ɗin Aunty B nake zuwa na gyara, domin ummie ta horar da mu aiki, duk da sanyi na zakiyi mamakin yadda nake aiki, amma idan an haɗa ni da hafsy ne tou babu mai ganin saurin nawa, sai dai banbancin ƙyalƙyale wuri, gidajen nasu babu wani datti, sharewa nakeyi nayi mopping sai na kunna turaren wuta a kowanni sashi, domim tun dare nake wanke-wanke, kuma tunda naje bamu ɗaura abinci a side ɗin yayah Ahmad, wannan Aunty B ta ɗauke, sai dai idan tayi ta saka na kowanne side, ina gama gyara ko ina nake zuwa na kwanta tare da Areefh a side ɗinsu, sai Aunty b ta gama haɗa breakfast nake fitowa na mishi wanka nima nayi, don gaskiya bana tayata aikin breakfast, saboda ko dankali zata soya tun dare nake fere mata, ranan da zatayi masa ma ni na kwaɓa mata shi da wuraren ƙarfe huɗu na asuba, so bayan na musu ayyukan su sai na ɗan kwanta na huta, amma abincin rana tare mukeyi, don gaskiya ba kasafai nake barinta da aiki ba, na dare ma tare mukeyi, don ma bamu cika yin abinci da rana ba, saboda su yayah basu nan, magrib suke dawowa sai kawai ayi abinci ɗaya, zaman mu gwanin ban sha'awa, kullum muna tare da juna, gashi akwai ƙauna mai girman gaske tsakanin mu da matan yayun mu, don gaskiya ummie a tsaye ta ke da Addu'an haɗin kan iyalanta, kuma Alhmdllh Allah ya amsa mata.

********* Rayuwa kullum ciki take burirrika, amma kwanakin mu kuma kullum ƙarewa suke, a haka hutun mu ya ƙare, dama 3weeks aka bamu, a haka har na shiga sati na huɗu, wanda lokacin nafara shirin komawa gida, zo kiga yadda hankalin Aunty j gaba ɗaya ya tashi, nidai har wani tausayi take bani, haka yayah Ahmad yayi ta rarrashinta akan idan ya maida ni zai taho da hafsy, insha Allahu ita ma zataji dadin zama da ita, babu yadda ta iya saboda ni karatu nake.

Ana saura kwana 2 na koma sai ga M.G ya dawo daga tafiyan da yayi, tun ana gobe zai dawo ya gaya mun na mishi special girki, saboda haka ranan Aunty B ta tayani muka mishi abinci kala biyu, sannan mukayi snacks kala wurin uku, muna gamawa na kwashe su zuwa side ɗin yayah Ahmad na jera akan dinning, sannan na wuce naje nayi wanka na shiryah cikin wata baƙar abayata mai kyau, Aunty Asma'u ce ta kawo mun ita bana da taje aikin hajji.

Wuraren ƙarfe uku suka shigo gidan shida yayah Ahmad, leƙowa nayi muka gaisa hannu na riƙe da na Areefh, ɗaga dukkan giran shi yayi yana kallona cike da mamaki, " barrister yayah naga kaman Ayshaa ta ƙara girma da tsawo? Anƴa zamu barta tagama school bamu aurar da ita ba"? Ya ƙarasa faɗi yana dariya, juyawa nayi da sauri na koma cikin ɗaki nima ina dariyan, gaskiya na daɗe banga yayah M.G ba, sai naga ya wani ƙara haske da kyau, gashi komai yayi kyau yake mishi, yanzu ɗaga giran da yayi sai yayi mun bala'in kyau a fuska, ina jin su suna ta hira da yayah Ahmad suna cin abinci, suna kan dinning ɗin har aka ƙira sallan la'asaar, daga nan suka wuce zuwa masallaci, bayan sun dawo ma suka cigaba da hiran su har zuwa wani lokacin, sai chan daga baya yayah ya ƙirani maje parlon, ima shigowa kuwa ya sake ƙura mun ido, fuskan shi ɗauke da murmishin shi mai kyaun nan, "ki zo ku gaisa da M.G, bari mu ɗan fita da yayah muhammad, bazamu daɗe ba zamu dawo", hannu na riƙe da gefen gyalen abayata ina kallon yayah har ya fita, bayan sunyi sallama M.G sai ya ƙura mun ido, har ajikina nake jin kallon da yake jifah da shi yayi mun yawa, saboda haka sai naja kujera na zauna, ƙasa-ƙasa na sake gaishe shi, kuma ban yadda dana sake yadda mun haɗa ido ba, shiru wurin ya ɗanyi na wani lokaci, kaman bazai ce komai ba, har na sake ɗago kaina amma sai charaf idon mu suka sake haɗu, da sauri na mayar da kaina ƙasa ina wani zazzare ido irin na rashin gaskiya. Murmushi yayi sannan yace "ƴan mata ina labari"? Ɗagowa nayi na kalle shi, domin kalmar da ya jefe ni da shi wai *ƳAN MATA* ya taɓoni, kasancewar bai taɓa ƙirana da hakan ba, giran shi ya sake ɗaga mun fuskan shi ɗauke da murmushi, kafin ya samu zarran sake jefo mun wani maganan, sai ga wayar shi tana kawu wuta, alamar tana neman agaji, ina kallon shi fuska cike da murmushi ya ɗauka, "mummy barka da yau yyh bauchi"? Sannan jimawa kaɗan na sake ji yace, "insha Allahu zan shigo very soon mummy nah," Bayan yayi shiru na wani lokaci yana sauraran me wayan sai kuma naji yace "ganin nan ma wurin ayshaan mummy" babu daɗewa ya miƙo mun wayan ƙasa -ƙasa yana cemun. "mummyn muce na wurin A.G. Cike da jin kunya na amshi wayan na shiga gaisheta, "Doughter nah yayah kike? Hope dai babu wata damuwa ko? Kuna gaisawa da A.G dai ko?" cike da jin kunyar ta na amsa mata gaisuwan, sauran kuma naji nakasa sakewa nace komai, sai murmushi kawai nake tayi kaman ina gaban ta, fatan alkhairi ta mun sosai da addu'a, sannan na miƙawa yayah M.G wayan cike da jin kunyar matar, sallama sukayi ya kashe wayan, ƙura mun ido yayi fuskan shi ɗauke da murmushi, "itace mummyn mu ƙwalli ɗaya da muke ji da ita nida A.G, itace mahaifiyar A.G dana fara baki labari wato Aunty Rashida, macece mai ilimin gaske da kirki, akwai shaƙuwa sosai tsakanina da ita, tana sona sosai kaman ita ta haifeni, abun mamaki kuma hiran da zamuyi da ita bazaki taɓa ganin A.G sunayi ba, wani lokacin idan tayi magana taga bai ce komai ba sai ta hau shi da faɗa, "ni dai idan baxaka ringa amsa mun magana ba a daina zama kusa dani, haba mutum yana naniƙe da kai amma kuma bazai yi magana da kai ba yadda ranka zaiyi daɗi", sai dai ni kiga muna hira da ita sosai, amma kuma idan kinga irin son da take mishi zakiyi mamaki, don idan ciwon shi ya tashi ta dinga kuka kenan, tana masifar son shi sosai". Murmushi nayi ina sauraron shi, "kin san duk abun da ya shafi A G tana so, ballantana da taga ya damu da ke bakiga yadda take mugun sonki ba,", ɗago kaina nayi cike da mamaki nace "ya damu dani ko kuma dai ya damu da jin haushi na, har labari na yake bawa mummyn? Dama ya riƙe sunana ne?" Dariya yayi yace, "ae duk abunda ko ni ko barrister ya damu da shi tou A.G ma ya damu da shi hala ma har yafi damuwa da shi, kin san tsakanin shi da barrister akwai wata ƙauna mai ƙarfin gaske, don tunda ga kaina bai sake sakewa da ƙaunar wani ba sai barr." Murmushi nayi ina jijjiga kai alamar ina tare da shi, wayan shi a karo na biyu ta fara kukan neman agajin a ɗauke ta, murmushin fuskan shi ne ya wadata lokaci ɗaya, sannan kuma ya ɗauki wayan yana ƙara wadata murmushin, "A.G friend, kaman kasan yanzu hiran ka nakeyi", shiru yayi yana sauraran wayan, nidai ido na yana kanshi, can sai naga ya kwashe da dariya yana, "wallahi nida Ayshaa, yanzu ma na haɗa su suka gaisa da mummy", Kallo ni yayi sai naga ya miƙo mun wayan, kasa karɓa nayi kaman yadda ɗazu na karɓi na mummy, "karɓa mana A.G ne a layin", babu yadda na iya haka na saka hannu na karɓa, da ƙyar na kai wayan kunne na, shiru dukkan mu mukayi, ina ganin M.G kuwa ya wani ƙura mun ido yana smilling.

Nima smilling ɗin nayi nace bari na haƙura da typing ɗin nan, sai kuma gobe idan mai kowa mai komai ya kaimu.

Numfashin shi naji alaman ba daidai ba, daga dukkan alamu abun yana kusa ne, sai naji hankalina kuma ya tashi, har bansan lokacin da bakina ya furta, "yayah baka da lafiya ne"? "kin damu ne da kisan lafiya na"? A.G ya mayar mata da amsa, runtse ido na nayi saboda yadda zuciyana naji ya yanke, daga jin yadda muryan shi yake fita babu lafiya, "sorry yayah A.Gn mu ka daina faɗa da fushi kaga baka da lafiya, kuma ni.....kuma shikenan dai yaya jikin"? Na tambaye shi, "kin taɓa ganin nayi fushi da ke? Na tafi banida lafiya anma bakiyi tunanin ƙiran kiji yaya nake ba, hakan kuma bai saka nayi fushi ba, ki tsoraci ganin fushina kawai, sannan meye kuma....kuman da kike son faɗi"? Ya ƙarasa yana ɗan tari da jan numfashin shi a hankali, " babu kawai zance tou kadawo mana tunda baka da lafiya, kuma ae kaima baka ƙirani ba", "idan na dawo me zan miki? Akwai wani dalili ne da zai saka na ƙiraki? Ko ance miki kowa nake ƙirane"? Tura baki nayi gaba kaman yana kallo na, murya chan ƙasa -ƙasa nace, "tou nima kowa ne nake magana da shi"? "me kikace? Wato kin raina ni ko? Nine kowan ko"? Buɗe ido nayi ina zaro su don banyi tsammanin zaiji abinda nace ba, amma sai nayi diris nakasa bada amsa saboda yadda naga idon M.G ya koma, kaman wani marar lafiya, amma ganin na buɗe ido sai ya jefe ni da wani murmushi wanda bai wuce lips ɗin shi ba, da sauri na miƙa mishi wayan, yana ƙara murmushin fuskan shi ya karɓi wayan yakai kunnen shi yace, "Friend yaya ƙarfin jikin? Amma yau kam ina ganin zasu sallameka ae ko? Don naji daddy yace zuwa friday zai dawo". Hankali na ne naji ya sake tashi, wato a kwance a asibiti ma kenan yake? Wayyo Allah dama ban miƙa wayan ba, hannu bibbiyu na saka nayi tagumi ina kallon M.G da suke ta magana, zuwa chan naji yayi masa sallama ya ajiye wayan, kaman a sama na jiyo muryan shi yace.

"Tafiyan A.G wani abu ne da ya daɗe yana muƙurƙusa na, idan kinga na shiga gidan kakanun shi wato gidan Alhaji Inuwa tou sai ranan jumma'a, shima ba ko yaushe ba, domin yadda rayuwa ya ƙara juyawa goggon mu, Aysha goggo tasha wahalan rayuwa na kula da mu, kuma bazaki taɓa ganin gazawanta akan komai ba, goggo kitso ya janye a wurinta, yanzu ƙarfin sana'anta surfe ne da dakan hannu sai kuma masan da takeyi da safe, kuma babu lalaci ko kunya zamu fitar da tallen masan nida Hassan da hussain, da kuma kananzir ɗin inna ƴan'biyu, wanda yanzu itace zaune a ɗakin innan mu.

********** Shekara na takwas yayah auwal ya gama school ɗin, wanda baya zuwa hutu sai ƙarshen shekara, domin yayah auwal ana hutu yake tsayawa da wani mutum ɗan bauchi mazaunin chan lagos, yana taimaka miki shi da zaman shagon shi, a haka yayah yake ɗan tara abun buƙatun shi na karatu, wanda kuma bayan wasu ƴan watanni ya kan turowa goggo da wani abu, lokacin da ya dawo gida yayi wani fari tass da shi, idan ka ganshi sai ka ɗauka balarabe ne ko wani bature tsabar farin shi, yayah sanie kuma yana level 2 a A.T.B.U, yayah Rabi'u this year ya rubuta weac da neco, amma shi hankalin shi gaba ɗaya akan ball ne, don ma yayah auwal ya gaya mishi dole fah sai yayi karatu, twins kuma suna S.S 1, ni kuma ina aji huɗu na primary, haka mukai ta murnan dawowan yayah auwal, babban abun farin cikin kuma yau shinkafa da miya goggo ta dafa mana, gashi har nama aka saka, nidai murna nan shinkafan yafi mun murnan dawowan yayan mu ma," A.G yana zuwa nan sai da muka kalli juna mukayi dariya, domin wani nishaɗi yake ji idan yana maganan shinkafan nan, nima kuma abun daɗi da dariya yake sakani, domin idan ka dube shi a yanzu yadda Allah ya dafa mishi baxaka taɓa tunanin ya shiga wani mawuyacin rayuwa ba.

********** "Rayuwa ta cigaba da tafiya har nagama primary, baki tambayeni wa yake biyan kuɗin makarantar su yayah ba? Don ni dai har zuwa lokacin Aunty Rashida (mummy) ke biyan nawa, kuma idan an ɗauki lokaci tana mana aika, daga baya ma Daddy ya haɗa har da twins yana biya mana, karatun yayah auwal goggo ce ta sayar da wani gonan ta na gado, kuma yayah bai tsaya a neman kuɗi ba, son sai daga baya yake gayawa goggo har wanki da guga yayi a lagos kuma ya samu, so shi ya cigaba da biyan kuɗin shi, sai abun da yafi ƙarfin shi wannan ɗan'unguwan mu da yazama mishi uban ɗaki ya taimaka, yana gama service ɗinshi kuma ya tattara ya koma chan lagos ɗin, domin ya tsaya mishi ya samu koyarwa a wata private school, yayah sanie kuma da yayah rabi'u wannan bappan namu ne ya taimaka musu, sai kuma abunda goggo ta kalata, yayah rabi'u result ɗin shi baiyi wani kyau ba, saboda bai maida hankali ba, ba kuma babu kan bane, tsantsan ƙwallo kawai da yasaka a ranshi, saboda haka *BACAS* ya je yayi diploma ɗin shi a *PUBLIC ADMIN* yana gamawa kuma ya samu ɗaurin gindin fara buga wasan ƙwallo a team na wikki, kuma Alhamdulillah ya shiga a sa'a, don babu daɗewa sunan shi Rabi'u ya ɓace, sai dai kiji ana cewa *JOHN ZAKI* kuma babu laifi duk gidan mu babu sama da shi a son walwala, duk wani abun da yasa mo goggo ne, sai kuma ni ɗan lelen shi, don a lokacin asiri na yafara rufuwa da kayan gwanjon da yake tsinto mun, ga takalma har kala uku nake da su alokacin masu kyau, ina son ƙwallon a raina amma fir Goggo ta fige mun, kullum john zaki ya shigo na ringa tsalle ina mishi waƙan ƴan ball kenan, tou anan zakiga fushin goggo, rarumo abu takeyi ta jefeni, "ae wallahi yadda Rabiu ya ƙeƙashe yaje ƙwallo kai kam ƙaryar ka, don da wuri zan taroka", shidai dariya kawai zaiyi kiji yana, "sai goggon mu" hararan shi takeyi ta shareshi, idan su twins suna nan su kama dariya suna cewa, "ana yafito mata na goro kuma zakaji tace, "tou Allah yayi albarka Rabiu", dariya kowa yakeyi har goggon, don yadda suka iya kwaikwayon muryan mutane.

Bana mantawa lokacin da zamu gama primary, wani abokina da muke zaune sit ɗaya da shi Sulaiman, zasu koma kaduna da zama, dama baban shi banker ne, ya rubuta mun number wayan su, da yake landline ne lokacin, akan idan sun tafi zamuyi waya, shirme irin na yarinta, nasan fah unguwar mu gaba ɗaya gida biyu ne kawai masu wayan, daga gidan *Alƙali Abdullahi* sai gidan *Alhaji inuwa* gidan Alh inuwa kuma sun tafi umarah lokacin, kuma naji ance daga chan zasu wuce England su duba A.G da baiji daɗi ba, don ni naraka Goggo yiwa kakar A.G sallama, anan take gayawa goggo A.G asthman shi yana yawan damun shi, don lokacin wai har oxcygen aka saka mishi, duk da yarinta na damuna amma sai na shiga halin damuwa, gashi mun daɗe bamu gaisa ba, don an hana mu gaisawa, A.G duk ranan da ya gaisa dani iyayen shi sunce ya kan ɗauki tsawon lokaci yana fushi da kowa, makarantar ma ƙin zuwa yakeyi, idan an matsa kuma yayi ta kuka kenan, gaba ɗaya sukan kasa gane kanshi, gashi dai Allah ya ƙara basu haihuwan yara biyu amma duka mata ne, sun koma da 1year aka haifi *HUDA* wato A.G ya bata shekara shida kenan, sai bayan three years kuma aka haifi *HEEDAYAH* amma duk da haka son A.G daban ne a zuciyar iyayen shi, gashi kuma shi kaɗai ne mai ciwon asthmah ɗin, sai *HUDA* da ita tana da yawan mura amma ita bata da shi, sai dai ana kiyayewa sosai, bayan mun dawo ne nima nasamu kaina a damuwa da tunanin rashin lafiyan A.G, saboda haka na ɗauki paper da biro naje ɗakin yayah sanie, zama nayi a gefen shi nace "zan rubuta letter wa friend, idan nayi mistake ka gyara mun kaji yayah", murmushi yayi ya dafa kaina yace, "babu mistake ɗin ma da xakayi ae kai nasan gwani me mai brain", daɗi naji sosai na hau rubutu, gaisuwa na mishi da tambayan yayah jikin shi? Sannan na bashi labarin abokina sulaiman, na kuma tambaye shi yaushe zasu dawo ƙasan"? Gyara kaɗan yayah ya mun, da farin ciki na wuce gidan su A.G na kai letter na akan akai mishi, itama kakarshi da farin ciki ta karɓa, ta kuma mun alƙawarin zata kai mishi insha Allahu, daɗi naji na dawo gida.

Readers Also Read