Kenza eBookz

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 12

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 12

Ana barin halal original by anty nice Chapter 12: Ana barin halal original by anty nice Chapter 12. ********** Kwanci tashi babu wuya a wurin ubangiji, yau…

3,543 words

********** Kwanci tashi babu wuya a wurin ubangiji, yau wata shida da aure su habiba da yayah Ahmad, sannan yau ranan laraba 06/06/ 0000 muka tashi da labarin habiba ba lafiya wai tayi misscarrige, haka mamien ta da raliya sukayi ta sintirin zuwa asibiti, da yake Abba yana gari babu yadda muka iya, ana sallan magrib yace duk mu shiryah muje asibiti mu dubata, da yake a Ni'imah clinic take, ana sallah muka fito, da ummie, mamah da hafsy driver yaja mu sai asibitin, muna isa kowa saiga Aliyu zai shiga, bayan sun gaisa da su ummie muma muka gaishe shi, duk idon shi yana kaina ya amsa mana gaisuwan, bin bayan shi mukayi har ɗakin da habiba take kwance, muna shiga muka sameta a zaune maminta na bata tea tana sha, ganin ma tare sai mamie ta wani haɗa rai kaman taga mai ɗaukan ranta, ko kunyan idon Aliyu bataji ba ta wani kawar da kanta ta cigaba da bawa habiba tea ɗin, har gaban gadon mukaje dukkan mu muka gaisheta, ko ganin idon su ummie ne sai ta ɗago ta amsa mana fuskanta ɗauke da murmushi, amma kana ganinta kasan ta sha jinya, tayi baƙi ta rame, ni har raman ta ma da baƙin ya ban tsoro, kaman ba habiba ƴar gayu ba duk tazama kaman wata ƴar ƙauye, gefe ɗaya kuma kan carpet hajiya umma ne zaune tare da raliya, wanda kallo ɗaya ta mana ta cigaba da danna wayan ta, gefe ɗaya muka koma muka tsaya nida hafsy, domin mun gaida mamie ko kallon mu batayi ba, gara ma su ummie ta amsa gaisuwan su fuska a ɗaure, chan kuwa najiyo hajiya ummah tana tambayan Aliyu ina mummyn shi, "nikan Aliyu ita mahaifiyar taka kam bata gari ne? Naga har yanzu banga idon ta ba ko wani daga gidan ku? Ko dai baka gaya musu bane kana jin kunya irin na ƴan fari? Tou ae yanzu anci gaba ko haihuwa ne ae za'a faɗa ballantana ɓari, ɓari ma irin wannan da Allah ya kiyaye ba'a rasa rai ba", murmushi Aliyu yayi baice komai ba, sai mamie ce tayi magana ranta a ɓace, "hajiya ae ta ƙira taji yayah jikin, kuma tace tana tafe wani abune yasha kanta, amma kuma ae bai kamata ayita magana ba, naga wanda ya zama mishi dolen ae yana tsaye akan komai", ta faɗa tana ƙara ɗaure fuskan shi, mitsi-mitsi da ido hajiya ummah tayi tana kallon mamie, "ni kikan Hauwa neyasa bakijin kunyan shera ƙarya ne? Ina nan ɗazu da la'asaar muke jajanta rashin zuwan ta da rashin ƙiran wayan da batayi ba? Shima Aliyun wani sintiri ya tsaya yakeyi akai? Ina tunda yazo ya ajiye ta yace zaije office bai dawo ba sai wurin ƙarfe biyar, hidiman komai inace Abbanta ne a tsaye akai shida ɗanshi Umaru? Ga Aliyun nan ae a tsaye shi kam bazai zabga uban ƙaryan nan ba, tun da yazo a tsatsatsayen sai yanzu ya dawo, ko coolern abinci ɗaya banga ya shigo da shi ba, kuma hakkin sune bana Usmanu ba, dubi habiba inda ta lalace tafita hayyacin ta, haka aka basu ita? Kawai ƙatuwar mata baki son a faɗi gaskiya". Hajiya ummah ta faɗa tana miƙewa tsaye, shidai Aliyu shiru yayi yana wani murmushi chan ƙasa-ƙasa, idon shi akan habiba da taketa sharan hawaye, babu daɗewa yayi waje abinshi, "sai a haƙuri dai za'a dinga yi, yanzu ta lafiyan ta kawai za'ayi ummah ba wai ta abinda sukayi ba, idan basu zo bama ae mu munzo, kuma Alhmdllh tunda mahaifinta na tsaye akai ae yafi akan ace babu kowa", ummi ta faɗa tana matsa jikin gadon domin rarrashin habiba da ta fara ƙara sautin kukanta, tsaki hajiya ummah tayi tana kallon mamah tace, "baiwar Allah ku tashi mu tafi, ae gaisuwan ya isa haka, na Allah da annabi kam ae munyi shi, kinga ae da yasan basu da gaskiya daga shi har iyayen shi da ƴan'uwan shi ae kinga fita yayi, yoo ba dole ya fita ba, yaga na banza ya samu, an tula mishi uban dukiya ankai gidan shi ya dawo yana cin uban ta la'ada waje, gashi ya lafta mata uban cikin da bai shiga mahaifah ba yabar mahaifinta da ɗawainiya, shi ko a kwalar rigan shi, ina zai damu daman yadda ake so, tunda junin mutane chushen mata ce ae kaɗan kuka fara gani, dama matan chushe ina take daraja".

Kuka mamie ta fashe da shi, cikin ɓacen rai take magana, " hajiya naga dai da habiba da ayshaa duk ɗaya suke a wurinki, amma kullum sai ki nuna ayshaa sune ƴaƴa nawa kuma ba ƴaƴa bane, idan mijinta da ƴan'uwanta basu zo ba ae bai kamata ki tallata ta a duniya ba, ae sai ki rufa mata asiri, tunda kowa yasan kowani aure da irin jarabawan shi, ae gara dai wanda tayi akan wadda batayi ba, ayshaan ko mashin shini tana da shine? Ae itace abun magana ba habiba da mijinta yake tsaye akanta ba, ina ruwana da uwar shi idan bata so? Shina ae kowa yasan ba banza bane an shiga an fita an raba tsakanine kawai, amma ni ae nagode Allah da naga nawa ƴar a ɗakin aure, ga ƙaramar ma tana shirin tafiya, wasu fah? Saidai suga a nayi". "A hir ɗinki hauwa, wallahi a hir ɗinki da jinin usmanu, insha Allahu Aysha da hafsy sai kin ɗauki ƴaƴan su da jikokin su, kuma insha Allahu auren sai ya rufa miki asiri, ki rubuta ki ajiye koda bayan rai na ne, kuma na ƙara jin bakin ki ima magana kina yi wallahi zakiga matakin da zan ɗauka, don ko shi wanda ya ajiyeki sai na juya mishi baya kiga idan auren naki zai yiwau, shashasha marar tarbiya, duk kinbi kin ɓata tarbiyan yaranki, nan rumi-rumi yara sun taso tare amma mugun halinki da banzan nonoki sai da kika ɓata tsakanin su, kikasa ƴarki tayi ƙwacen mijin auren ƴar'uwarta, da yaki Allah ba azzalumin bawan shi bane sai Allah ya baku nasara domin ya kare Ayshaa don tasha nono mai kyau da tsafta, zuciyarta bata gurɓace ba irin na ƴarki da tasha mummunan zuciya nata ya gurɓace, insha Allah miji ɗangaske ayshaa zata samu ba mai dukan mace ba, inba tozarci da wulaƙanta kai ba ina duka ya mata har aka samu cikin ya bar mahaifan, ko dama bai shiga ba, tsabar babu Allah a zuciyar ki kuma kina mummunan fata a wasu? Kijira kiga yayah naki zasu ƙare tukun", hajiya tana ƙarasa faɗi tayi hanyan fita waje, hafsy da ke bin raliya da harara ban san me ya haɗu suba tom & jerry naga tabi bayan ummah, ita ma raliyan na binsu da harara, ita dai mamie kuka ta cigaba da yi tana guna-guni ƙasa -ƙasa, tsaki mamah tayi ta dubi habiba tace, "Allah ya baki lafiya, idan kinga dama ki gyara halayenki tun baki makaro ba, idan kuma baki gajji da wahala ba ki cigaba da biyewa uwarki, ita kuma ta cigaba da ɗoraki a hanyar da bata dace ba, inace yau wata shida da yin auren ki? Amma duk lokacin da kika shigo gidan kin fi ƙarfin ki shiga ɗakin kowa ki gaishe shi saidai idan kin haɗu damu a waje ki gaisa damu, kuma nayi imani da Allah su yayunki da sukayi hidima dake a auren ki baki taɓa zuwa gidan kowa ko ƙirasu ki gaishe su ba, tou wallahi kikabi ta haikar uwarki abun bazai miki daɗi ba gaba, domin mu duk nan mutuwa zamuyi mu barku tare, yayunki sune iyayenki, shi kuma aure haƙuri akeyi, kiyi biyayyah wa mijinki da iyayen shi, idan kika bi ta uwarki zaki sha wahala", tana gama faɗi ta juyo ta kalli mamie da ke kallonta da harara, itama hararan mamin tayi tace, "idan ke mai shirya ce Allah ya shirye ki, kuma magana da kika maidawa ummah ki tabbatar Alhaji yaji, idan kin dawo sai kiyi mishi bayanin wani dama kika samu da tana magana kinayi, mahaukaciya futsararriya". "Tou uwar gami karki bari ƙuda ya riga ki, ni dai insha Allahu nafi ƙarfin mace, tsakanina da Alhaji kuma sai Allah, duk munafurcin mutum kuma ae ko dan haihuwa Alhaji zai zauna dani", juyowa mamah tayi ta dubeta tana murmushi, "ae da haihuwa irin taki gara da Allah ya bar ni ba haihuwan, don idan bazan iya tarbiyantar da ƴaƴan ba gara na xauna haka, kuma wani kalma na rashin ɗa'a ya sake fitowa a bakinki zuwa gare ni, tou wallahi zan manta a asibiti muke na nuna miki ni ɗin *ZAINABU* ce kinsan bana ɗaukan wargi, kuka habiba ta fashe da shi tana, "wayyo Allah nikan na shiga uku, don Allah mama kuyi haƙuri, mamie don Allah ki daina jawowa ana rashin zaman lafiya, da wanne zanji ne kam"? Ta faɗa tana ƙara ɓarkewa da kuka, lokaci guda naji hawaye ya zomun, don wallahi ni shaida ce habiba bata so taga ana wannan tashin hankalin, kuma gashi ni tunda naji dukanta Aliyu yayi sai naji hankali na yayi mugun tashi, gaba ɗaya tausayinta ya rufe ni, juyawa nayi na fita a ɗakin duk jikina a sanyaye, gashi nasan maganan da habiba tayi dole ne sai mamie taci ubanta idan mun tafi, duk da dai nasan yanzu bazata doketa ba, muna fita mukaga Aliyu tsaye a jikin motan shi yana waya, ganin fitowan mu ya kashe wayan ya taho har inda motan yake, ƙofan gaba inda hajiya ummah ta shiga ya riƙe murfin motan, fuskan shi ɗauke da murmushi yake mana sallama, tsaki hajiya ummah taja lokacin da motan ta fara tafiya, cike da ɓacin rai tace, "ni wallahi na raina wayon Aliyu nan, idan akace maka zai iya saka hannu ya daki mace, macen ma irin habiba sokuwa ae sai abun ya baka mamaki, ta wani gefen ne kawai bazan yi mamaki ba, idan na tuna nonon uwarta da yake yawo a jikinta, amma abun takaicin ɗaya ne ace jinina kuma jinin usman ta zama boran miji da uwar miji?" "hajiya ae ba jininki abun ya bi ba, jinin uwarta ne yake yawo a jikinta, itama uwar da badon ta Allah ya taimaketa ba darajan ƴaƴa ae da boran ce a gidan namu"..... ae bata gama rufe baki ba ummah tace "ae boran ce kuwa a gidan usman, tou wa tafi daraja a cikin ku? Idan ba duban yarah ba da tsoron Allah irin nawa ae da tunin usman ya sallameta, tou tsoron riƙon ƴaƴan fitina kawai nake jiye muku, don jifa kam har dana dodon ningawa za'a na muku, idan ba masifa ba irin na hauwa saurayin ƴar uwarta kisaka ta janye shi? Don wannan al'amari kam a yawon asirinta ta samu sa'a, amma taga ranan asiri ae, don Alhaji yace mun tana ta masifah ɗazu, wai ashe tunda akayi auren babu wani ɗan'uwan shi da yaje gidan ta, ita ma ko taje gidan iyayen na shi surkuwar ta mata tsakani da ɗakinta, idan taga dama ta fito su gaisa idan bata so ba kuma har su bar gidan bata fitowa, shima Aliyun kullum gorin ta cuce shi ba ita yake so ba amma mashiryiciyan uwarta ta asirce suka juya mishi hankali zuwa kanta yakeyi, rayuwar fah Alhaji yace mun babu daɗi, don ko kuɗin makaranta uban ne ya cigaba da biya, don uwar yaron tace yaronta bazai wahala a banza ba, yanzu ma wai auren ƴar ƙanwarta ake nema mishi, shine maka sudin dokan, sunje jiya gidan maman nashi, itama yarinyar ashe tazo, suna zaune suna hira da Aliyun a parlon maman shi sai marar kunyar ƙanwar tata ta gansu, kin san ba tarbiya take da shi ba, ashe da zasu tafi taje har ɗakin da yarinyar take ta zazzageta, ita kuma yarinya mai tarbiya ce bata tanka ta ba, sai da suka tafi ta gayawa maman Aliyun, ita kuwa uwa ta ƙira tace yaja kunnen ƙanwar matar shi, kuma kada ya sake shigo mata dasu gidanta, ae kuwa inda ya shiga bata nan yake fita ba, yace dole raliyan ta bar gidan a daren, ina ga ita kuma ƴar uwar ku taƙi ne, shi ko zuciya ya ɗebe shi yayi ta bugunta har abun yazo da tsautsayi," Dariya mamah tayi babu wani shakkah a ranta tace, "hakki ne kawai hajiya, ae kaɗan ta gani, ae idaɓ junin mutum hassada ne ya ringa ganin abun da baya so, duk wanda yace ruwan wani bazai tafasa ba tou insha Allahu nashi ko ɗumi bazai yi ba, ta cigaba dai kada ta daina".

Ita dai ummie bata ce komai ba sai jinjina magana da take tayi, nima duk sai naji hankali na ya tashi, a haka muka iso gida gaba ɗaya kowa ranshi babu daɗi, muna isa kuwa ummi da mamah da hajiya ummah suka wuce parlon Abba, ni da hafsy dai side ɗin ummin mu muka wuce, muna shiga hafsy ta wani zabga mun harara, "ke wai Adda tausayin su kike jine? Wallahi gara ma ki daina don bakiji me banzan raliyan nan ta faɗa bane akanki", "bance ki gaya mun ba tunda banji ba, kuma ke hafsy ko babu zuciyar imani ajikin ki ae zaki tausayawa habiba, ae ba raliya da mamie zaki duba ba, ita zaki duba", na faɗa ina neman wurin zama a parlon, tsaki tayi itama ta nemi wurin zama ta zauna, "nikan Adda bana tausayinta, don banga abun tausayi ba, lokacin da taci amanar ki ita ta tuna da tausayin kene? Ina wani falli ma takeyi ta ƙwace miki miji? Ni wallahi ya mun daidai, dama mai siffana sheɗanun nan ya laftawa dukan da sai bakinta ya kumbura yayi, amma itama ana tafe, nata laftan yana zuwa", ta karasa faɗa tana kwashewa da dariya, nidai ido kawai na zuba mata, tana dariya tace , " bari manyan mu ya shigo musha dariya" yayah umar take nufi, nidai ko maida mata amsa banyi ba, don haushi ta bani kawai na ɗauki remote ina kunna T.V.

Kaman jira yake ta ambaci sunan kuma sai ga shi sun shigo tare da ummin mu, fuskan ummie a ɗaure ta nemi wuri ta zauna, gefe ɗaya kuma yayah umar ma ya zauna a gefen ummin mu, "ummie tou ke ina ruwanki da wani shiga abun da bai shafe ki ba? Ki barsu kawai Abba ya ɗauki duk matakin da yaga zaiyi dai-dai". Ajiyan zuciya ummie tayi cikin rashin jin daɗi tace, "ita hauwa hankali ne bata da shi, amma yaran ae abun tausayi ne, yanzu yaushe akayi auren da har duka zai fara shiga? Ni wallahi habiba tausayi ta ke bani, kuma zan nemi ita mummyn Aliyun muyi magana, meye laifin ita habiban da zata bari haka yana faruwa"? Da sauri yayah umar ya riƙo hannun ta da ta ke shirin ɗaukan wayanta yace, "haba ummie na don Allah kada ki fara yadda Abba yace, wallahi duk abinda ya biyo baya kanki mamie zata mayar, ki fita sha'aninta da ƴaƴanta, ae dai kinji mai Abba yace, tou babu ruwanki naki ido ne kawai". Shiru ummie tayi tana kallon mu ɗaya bayan ɗaya, chan kuma tace , "Allah ya kyauta", sannan ta miƙe tayi hanyar ɗakinta, tana shigewa hafsy ta ƙyalƙyale da dariya, ƙasa-ƙasa ta shiga korowa yayah umar labarin abubuwan da ya faru, dariya sukayi tayi har suka ban haushi, ganin zasu ƙara ɓata mun rai kawai sai na fita na wuce side ɗin ummah, ina fita suka sake kwashewa da dariya da ƙarfi don naji.

Ranan da aka sallami habiba mamie tayi niyyan wuto wa da ita gida, amma fir Abba yaƙi amincewa, bada son ranta ba aka wuce da habiba gidan ta, Abba kuma ya hana raliya zuwa, ita mamin yace bazata zauna ba, idan har ta damu da aje a kula da ƴar tou ta nemo wata ƴar'uwarta ta aika, haka kuma dole tayi, Umman ta ƙanwar mamanta ta ɗauko ta, tunda ta dawo gida ta fara sauƙe mana habaici iya son ranta, ganin abun zaiyi yawa mamah ta fito ta taka mata uban warning, babu yadda ta iya tayi shiru, ganin tana cikin damuwa ta shirya ta tafi Abuja wurin Abba, raliya kuma ta haɗa kaya ta wuce gidan ƙanwar mamin, dama duk wacce taga zataje Abuja wurin Abba baya hanawa, yawanci ma ita da mamah ne suke yawan zuwa, ita ummien mu sai ta ɗauro ko zataga likita tukun take zuwa, haka dai muka samu gidan yayi shiru na tsawon sati biyu kafin suka dawo tare da Abba.

******** Muna ta shirin fara rubuta exams yayah Ahmad ya ƙira ummi yace idan anyi hutu zaizo ya ɗauke ni, ummi ƙin amince mishi tayi, amma da taji Aunty jeeddah ce babu lafiya sai ta amince, M.G kuma rana ɗaɗɗaya ne bamu waya da shi, gashi munyi wani kyakkyawan sabo da shi, dana tambaye shi ya cigaba da bani labarin daya fara bani sai ya ƙi, yace sai ranan da yazo bauchi tukun, sannan tun ranan bamu sake hiran A.G ba da shi, gashi ina son tambayan shi yayah jikin A.G amma na kasa. Ranan laraba muka gama rubuta Exams ɗin mu, Alhamis kuma su hafsy suka gama rubuta neco, sai wani falli suke ji da shi, mu kuma mun gama level 2 sai shirin shiga 3, sannan a wannan lokacin ne aka saka ranan auren fatima, itama hadiza ana shirin zuwa neman auren ta, murna kaman zamuyi yayah muke ji. Friday yayah Ahmad yazo bauchi tare da Abba, zuwan sune mukaji labarin wai za'a zo gaisuwan auren raliya da wani ɗan ƙawar mamin ta, abun ni mamaki ma ya bani, haka kuwa akayi ranan saturday suka zo, kuma a son ransu sunso a saka musu rana , amma Abba yaƙi amincewa da buƙatan su, yace gaskiya sai ta shiga university za ayi, babu yadda suka iya haka suka yadda. Washe gari sunday muka kama hanyan Abuja, da yake da mota yayah Ahmad suka zo da Abba, don ba kasafai Abba yake bin jirgi ba, yafi tafiyan mota ko dan yayi saye-sayen tsaraba, parlon Abba muka shiga yi mishi sallam nida yayah Ahmad, a can muka tarar da mamah da mamie a zaune, daga gani kuma wani abunne ya haɗasu Abba ya nemi su, don muna shiga na tsinci muryan mamah na cewa Abba yaja kunnen matar shi, banji me yace ba muka shigo, kuma sai duk suka dakata da maganan suka dawo da kallon su kanmu, gefen Abba naje na ɗan tsuguna ina ƙara gaishe shi, hannu ya saka ya dafa kaina, "sisto na har an fito za'a yi himmah ko"? ɗaga kai nayi alaman eh, fuskana ɗauke da murmushi, domin Abba ne ya fara saka mun sisto, kafin habiba ma takama, da yake sunan sister shi naci, "Allah ya tsare hanya Ayshaa kuma don Allah idan anje ko ina kada a chanja hali da tarbiyan da muka baku, a ko'ina kuke ku nuna ko jinin Usman ne, kuma don Allah a zauna lafiya da matan yayun ki, kinga dai yadda mahaifiyar ta ke zaune da mutane? So plz kuma duk inda kuke haka nake so, Allah yayi albarka ya kawo mazaje na gari", ya idasa faɗa yana ciro kuɗi a aljihun shi masu yawa yana miƙo mun, itama mahma nasihar ta mun, sannan ta dubi yayah Ahmad tace, "duk zaman lpyn da zai biyo baya daga gidan ka kaine, idan ka mutunta matar ka ƴan'uwanka su mutunta ta, idan ka wulaƙanta ta su wulaƙantata, idan ka nunawa matarka ƴan'uwanka suna da daraja ta mutunta su, saboda haka kai zan jawa kunne don munga iya gudun ludayin muhammadu naka ne bamu gani ba, kaga dai yadda yarinyar nan Bintu take naknak da ku, tou daga muhammadu ne, shima kuma bai bari anci mutuncin matar shi ba, kaima sai ka kiyaye," godiya yayah Ahmad ya mata sannan muka musu sallama gaba ɗaya muka miƙe, tsaki mamie taja tana faɗin "halan miji zakije nema mata a Abujan ko? Tou nema mata miji mana tunda kaf bauchi an rasa me tayawa". "Wuce ku tafi malam Ahmadu Allah ya tsare hanya, Ayshaa idan rabon yana Abuja Allah ya kawo mana babban rabo wanda zai kai ƴan baƙin ciki masu ciwon hassada makka", mamah ta faɗa tana bin mu da murmushi kaman bata faɗi wani abu zuwaga mamie ba, nima murmushin nayi na juya muka fita, ina kallon yadda Abba ya zubawa mamie uban harara kuma daga gani jira yake mu fita ya dirarmata, Sai wuraren ƙarfe biyar muka isa, yayah ne ya tayani ɗaukan kayan muka shiga side ɗin shi, bamu samu Aunty j a parlor ba, ɗakinta na wuce yadda yayah ya umurceni, ina shiga kuwa na ganta dunƙule akan sallayan da tayi sallah tana bacci, ganin haka na ajiye troley nah a gefe, sannan na fito a hankali na tattara ledodin da ummie ta haɗa musu tsaraban bauchi na shige da su kitchen, ina fitowa kuma na haɗu da yayah Ahmad shima ya fito daga room ɗinshi zai shiga na Aunty j, cikin sanyin muryar shi yace, "ɗauki na gida yayah muhammad ki shigar musu da shi," da sauri kuwa na ɗauka nayi gaba, tsaban ɗokin naje naga Aunty da Areefh, don nasan fatima bata iso ba don munyi chatt tace mun sun gama Exans, amma sai ta ɗan huta zata zo, har na zolayeta kodai kabir zai shigo ƙasan ne ya sa bata taho ba, dariya tayi tace ae idan kinga kabir ƙasan nan tou ki fara shirin miƙa ni, dariya mukayi tayi ina zolayanta.

Readers Also Read