Ana barin halal original by anty nice - Chapter 11
Ana barin halal original by anty nice Chapter 11: Ana barin halal original by anty nice Chapter 11. Hannu na riƙe dana yayah rabiu muka tsaya muma abakin…
4,486 words
Hannu na riƙe dana yayah rabiu muka tsaya muma abakin titi muna kallon yaran alƙali, akwai wani ɗan shi masifaffe, babu abunda na mishi kawai naji ya zabga mun ranƙwashi ƙwaff akaina, "shege da ido kaman na tsohon maye, ka wani zurawa mutum su", ya faɗa yana ƙara shambe ni da ƙafan shi, ihu nasaka da ƙarfi ina rungume yayah rabi'u, hannu na yayah rabiu yaja muka fara tafiya yana tacewa saurayin "Allah ya isa da ka doka mun ƙani, kuma wuta balbal a kabarin ka", juyowa ɗan gidan Alƙalin yayi zai daki yayah Rabi'u sai abokanshi suka riƙe shi, ɗayan yana cewa "haba mana Tijjani yaron nan kam ba ƙanin ku bane? Kuma naga bai maka komai ba ka dake shi, ba girman ka bane, wuce mu tafi", ƙwafa Tijjanin yayi sannan ya juya suka tafi mu kuma muka dawo gida ina ta kuka, yayah hassan da yayah hussain suna ta lallashi na. Muna shiga gida muka samu yayah sanie zaune a gefen goggo yana cin abinci, cikin sanyin shi da sanyin maganan shi ya tambaye su meya sameni? Nan kuwa hussain ya zayyano mishi duk abinda ya faru kaman zaiyi kuka, hannu yayah sanie ya miƙo mun, gefen shi na zauna yana ta lallashina, sai da yace mun zai saya mun chinchin ɗin shagon tela tukun nayi shiru, abinci goggo ta zuba mana nida su yayah hussain tace na zo muci, bana wasa da abinci a rayuwa na Ayshaa, shiyasa naji na huce daga ranƙwashi mai zafin da yayah T.J yayi, ballantana na hango nama akan shinkafar da goggo ta dafa mana, dariya nayi ina kallon M.G cike da tausayin shi, shima dariyan yakeyi domin naga alaman ya tuna wannan lokacin ne sosai. "Ayshaa wato na taso ina son abinci especially idan naga namomi akai, amma alokacin Allah bai bamu ba, idan naje gidan su A.G abinci ne cike fal da nama, gashi kakan shi Alhaji Inuwa mutumin kirkine shida kakar A.G, haka zasuyi ta fama dani naci amma ina nasha kwaɓa da training ɗin yayah auwalu, bana iya ci, sai dai nayita haɗiyan yawo, idan kinga naci tou A.G ya biyoni gidan mu da abincin shi wai muci tare, mu kuma abincin mu yawanci kwaɗon garin kwaki ne, ko ƙanzon da goggo ke tarawa na matan dake cikin gidan mu ƴan'uwa, idan kinga sakekken abinci tou tuwo ne ko kuma gwaten tsaki, sai ɗanwaken dawada alabo da ake mana, amma Ayshaa komai mukayi A.G yana ci, idan ya kawo abinci hankalin goggo ya tashi ta rasa yadda zatayi da shi yaci shi kaɗai, amma fir sai yaƙi yace shi da aboki zai ci, saboda A.G shi yasaka mun sunan aboki tun bamu fi 3yrs ba, idan zasu tafi yayi ta ihun da aboki zai zauna, har nima nafara ƙiran shi da aboki, yanzu kuma yakance M.G aboki, ko M.G friend, ni kuma nace mishi A.G friend ko A.G aboki. Sai da innah wata rana tayi goggo maganan tayi haƙuri ta barmu muci abincin mu tare, rabo nane ya tsaga ana su shiyasa Allah ya haɗa kanmu, nan inna take cewa goggo, ae shi Mukhtar abun tausayi ne, bai taso ya samu kulawan da yara suke samu daga iyaye na daɗi ba, yayun shi malam Garba yayi iya ƙoƙarin shi, saboda haa ta barmu kada a tauye ni dayawa, sannan goggo ta haƙura, idan yazo sai a fara cin nawa, nan kuwa A.G zaici sosai yana jin daɗi, ballan tama idan goggo taɗan yaryaɗa mana mangyaɗa ta ƙara yaji akai, idan munzo cin nashi wataran nama kusan shida, takwas ake zubawa akai, haka zakiga yayah hassan da yayah hussain suna fakaitan idon goggo suna ɗan miƙa mana hannu, na dinga musu dariya ina ɓincina musu nama kaɗan, amma sai kiga A.G ya basu ɗaɗɗaya wataran har yayah rabi'u, ni kuma na cinye nawa, A.G ya soni, iyayen shi sun soni da kakanun shi, babu abunda bazan iya yiwa A.G ba arayuwa idan bai saɓawa addini ba, a wannan shekaran Daddyn A.G ya dawo ƙasan, kuma a wannan lokacin Allah ya karɓi ran innah, munyi baƙin ciki da kewan innah, goggo tayi kuka har sai da ta kwanta jinya, sannan rayuwa ya sake yiwa goggo ƙunci, bayan anyi sadakan bakwai kuma wani mummunan labari yazo mana na tashin su A.G zuwa London inda daddy yayi karatu ya samu aiki, duk da ƙanƙancin shekaruna naji zafi da ciwon tafiyan su A.G, ranan da zasu tafi sai da nayi kuka, shima A.G ihu ya dinga yi yana abarshi a wurin aboki, rarrashi akayi ta mishi sannan suka tafi, wannan ranan dole a gidan Alhaji inuwa na kwana, domin nayi kuka har saida nayi zazzaɓi, haka kakar A.G tayita lallashi na, da taji jikina akwai zazzaɓi sai tace wasu yayah Rabi'u sucewa goggo zamuje asibiti, da muka dawo ma ta barni na kwana a wurinta, da safe da kanta ta mun wanka ta saka mun kayan A.G da mummy ta bar mun su dayawa, har da su school bag ɗinshi.
Rayuwa tayi mun babu daɗi, babu innah babu A.G, duk wani abun dsɗi da innah ta samu sai ta ɓoye mun, ko jikokinta bata bayarwa saboda tausayina take ji, sannan akwai balbalin ɗan wan mijinta da yake da ɗan dama-dama a cikin gidan, shima ba wani sosai badai, amma yafi mutane dayawa a cikin gidan, tunda shi akwai T.V a gidan shi kuma suna ɗan kunna generator, yakan sakawa inna abinci rana da dare, kuma shi sukanyi shinkafa sukanyi taliya da su doya, saboda matar shi ma malamar makaranta ce, babu laifi sukan ci abinci har da salak, tou Inna bata cinyewa, sukanci da inna ƴanbiyu, sannan takan ɗiba mun nida su hassan da hussain, sai dai ni takan ƙara mun, idan kuma an saka nama ko kifi tou wannan nawa ne, ko ita bataci. Ayshaa innah ta mun so da gata da bazan taɓa mantawa ba, burina da fatana na saka sunanta cikin ƴaƴana, sannan na saka yayah auwal nasaka A.G, ya faɗa yana kallo na, murmushi nayi nace Goggo fah? Shima murmushin yayi ya kama haɓa yace, "Inna, Goggo, mummy, sune sunan yara na mata, A.G, yayah auwal, yayah sanie, rabiu, hassan da hussain, Abdullahi (baba nah) Abubakar (baban mu) duk insha Allahu sai nayi" ya faɗa yana dariya, nima dariyan nayi nace, "kace mata huɗu zakayi kenan"? Girgiza kai yayi yace "mata ɗaya shine burina, sai dai idan banyi dace ba na ƙara wata, ballantana ma insha Allahu zan dace, yaran babu yawa fah Ayshaa, mata uku, maza 7, yara goma ne fah" zaro ido nayi nace sunyi yawa ae yayah M.G wa mace ɗaya, sai dai biyu kowa tayi biyar - biyar". Murmushi yayi ya ƙura mun ido, "tou a shawaranki da zaki bani mata 2 kenan zanyi? Hakan ya miki?" Hararan shi nayi cikin wasa nace " nidai babu ruwa na bance ba, kalan matar kan taji haushina idan kace ni na baka shawaran kayi mata biyu", Kallo na yayi yana murmushin shi mai kyaun nan, "a misali idan kece zaki iya haifah mun yara goman babu ƙorafi da ragwanta"? Ɗago kai nayi da nufin magana amma kallon da yake mun ya saka na maida kaina ƙasa da wuri ina riƙe wayana da ɗan ƙarfi, baki na turo gaba nace, "ni kuma yayah? Ni ae bazan iya haifan yara da zasu wuce uku ba, kuma ni ae kaiyayah nane", murmushi yayi mai sauti yace, "tou ae yayah yana iya auren ƙanwa, kenan misali idan ke zan aura dole mata uku kenan zanyi?" kallon shi nayi da sauri nace "uku kuma?" Girgiza kai yayi yana murmushi yace, "uku mana sisto, ke kiyi uku, ta biyu tayi huɗu, ta uku tayi uku, ko kuma suyi biyar biyar saboda suma su saka sunan nasu iyayen", "Nidai bana son kishiya, kuma wallahi yaran sun maka yawa", na faɗa ina juyar da kaina gefe saboda haushi ya bani da yace mata uku zaiyi, dariya yayi sosai yana kallo na, " wato Aysha baki son kishiya ko? Lallai ko idan nine mijinki sai kin daure kin haifi dozin, nawa goma naki biyu, sai dai idan cin girma zanyi na barwa ƙanina A.G, don shima irin ki ne mai raki, yarah uku zuwa huɗu yace mun yake so, don baya son hayaniya, kinga tsarinku zaizo iri ɗaya kenan". "Haba yayah M.G idan zaka mun fatan aure ae baxaka mun fatan wannan abokin kan ba, wannan ae kullum sai ya daki mace ae daga alaman shi, kuma mutum baya fara'a bai magana, wacece zata iya zama da shi"? Dariya ya kwashe da shi yace, "tou ae kema baki yawan magana, kinga ae kunyi daidai kenan, gidan zaiyi daɗin zama kuma", ya faɗa yana dariya. Tura baki gaba nayi nace, "ni yayah duk da bana yawan magana ae ina son hira, kuma ni ina murmushi, amma shi fa? Ni dai ka daina kwatan tani ma dashi, don tsoro ma yake bani, wannan ae sai...." sai kuma nayi shiru ganin shi yana tahowa inda muke, dukkan mu shiru mukayi, M.G ya ƙura mishi ido ni kuma na sunkuyar da kaina ƙasa, "Friend ya kamata mutafi numfashi na yana mun wani iri, " Ɗago kai nayi da sauri na dube shi cike da tausayi, amma sai ya hani manna mun hararah, gashi kuma numfashin shi yana jan shi da kyar, da sauri M.G ya miƙe tsaye yana riƙo hannun A.G ɗin, "aboki ina inhelar ka"? Ko akwai ƙura ne a wurin"? Murtuƙe fuskan shi kawai yayi baice komai ba, duk sun maida kallon su inda yayah Ahmad yake tahowa, bayan ya iso yake sannu wa A.G, sannan yace ya gama clearing bilƙ ɗin su taho mutafi, ae magrib ya gabato shi yasa ma numfashin yake haka, ga sanyi yana sauƙa, nima miƙewa nayi jiki na a sanyaye, ga labarin da M.G ke bani ga kuma yanayin A.G dana gani, gaba M.G yayi yana danna wayan shi alaman doctor yake nema, shima yayah Ahmad juyawa yayi ya nufi inda su Aunty jeedah suka miƙe ana shirin tafiya, Tafiya nafarayi sai naji muryanshi yace, "idan kin koma ki dafa mun lipton mai kayan yaji", juyowa nayi na dube shi, sai naga ko kallo na baiyiba wayan shi yake dannawa, sai bance komai ba kawai na wuce gaba zuwa wurin su Aunty.
Koda muka isa gida kowa haraman sallah ya fara, muna idar wa fatima ta juyo tana kallo na, batace komai ba sai ido da ta zuba mun, gajjiya nayi da kallon nace, "wannan irin kallon fah teemah"? Murmushi tayi ta ce, "naga alaman M.G yagama tsaraki kin tsaru yau, don naga sai wani annuri ne ke fita a fuskar ki," Nima murmushin nayi na girgiza kai na, "wallahi babu wani tsari teemah, kawai labarin rayuwa mukeyi, amma ba abun da kike tunani bane ya faru", ina gama faɗan haka na miƙe tsaye ina naɗe hijab ɗina, bana son mucigaba da zancen don banyi niyyan sanar da kowa yadda mukayi da M.G ba, don wannan sirrin shi ne kuma bai gama gaya mun ba, sannan bansan maƙasudin zaman namu ba ballantana har na fara isarwa wani, sai na chanja topic ɗin maganan da, "teemah kunyi waya da maryam ne yau da muka fita?" "eh ta ƙirani wai wayanki akashe, sannan hadiza ma ta ƙira" muna cikin maganan hafsy ta shigo, wani kallo ta ke mun na alaman gulma na muntsininta, bana so ta sake jawo wani magana sai na yi hanyan fita na bar ɗakin, parlor naje gefen Aunty na zauna kusa da ita, kallo na tayi tana murmushi tace, "ƴan matan ummie yyh akayi?" murmushi nayi na kalleta nace wai wannan abokin yayah Ahmad ɗinnan ne wai na dafa mishi tea, ni kuma wallahi maganan su teemah da hafsy ne bana so, don Allah Aunty kice wa ke zan dafa". Dariya ta ɗanyi kaɗan tace, "babu komai bestyn husby na, bari su fito sai nace ki dafa mun tea ki kuma zubawa jeeddah a flask, kinga sai ki ɗauka kaman zaki kai mata sai ki kai mishi, amma yyh ake ciki akwai wani update ne"? Murmushi nayi na girgiza kaina nace, "Aunty babu komai fah wallahi, ni bamu cika wani shiri bama da shi, kinsan baida lafiya yana da asthma, inaga shiyasa yake son shan tea ɗin", ina rufe baki su teemah suna fitowa, basu wuce minti biyar ba Aunty ta umurceni da na dafa mata tea, idan nagama kuma na zubawa Aunty J, yadda dai muka tsara, haka na tashi naje na haɗa na dafa shi tsaf sai ƙamshin kayan haɗin su na ƴan maiduguri yakeyi, sannan na haɗa sandwich, M.G kaman yasan nagama abunda nakeyi sai ga call ɗinshi, ina ɗauka yace gasu nan a parlon yayah Ahmaɗ shi da A.G.
Ajiye musu basket ɗin tea ɗin nayi akan center table ɗin da yake gaban M.G, Kallo na yayah Ahmad yayi yace ki zubuwa A.G shine zai sha, fatan dai kin saka kayan yaji ko? Ɗaga kai kawai nayi batare da na buɗe baki na amsa ba, har gaban A.G ɗin naje na durƙusa na ɗauki cup na zuba mishi sannan nasaka sandwich ɗin a kan wani plet, na miƙa mishi, kallo na yayi fuskan shi ta nuna alaman yana shan wahala, don har wani ja tayi ta kan hancin shi, murya ƙasa-ƙasa naji yace, "ki ƙara mun sugar" kallo na sake binshi da shi "na saka sugar fah sosai, taɓa kaji", eyyh kallon yau babu masifa da harara a ciki, sai mai da kanshi yayi ya kwantar ya lumshe ido, nidai ina kallon shi da cup a riƙe a hannu na, sai naga kaman numfashin yana jan shi a hankali a ƙasan ƙirjin shi, duk sai naji ya bani tausayi, murya ƙasa - ƙasa wanda babu wanda zaiji sai shi nace, Yayah A.G sannu, ka tashi kasha tea ɗin kada yayi sanyi", Buɗe ido yayi a hankali ya ƙura mun sannan yace, "nace ki ƙara mun sugar kinƙi, bazan iya sha babu sugar sosai ba", da sauri na ajiye cup ɗin na ƙara zuba spoon ɗaya, bayan na gauraya shi na miƙa mishi, hannu ya saka ya karɓa, ina kallon shi daya kurɓa ya ɗan runtse idon shi, a hankali yake shan tea ɗin, cike da tausayi na miƙa mishi bread ɗin, babu musu ya saka hannu ya karɓa, shima a hankali ya ke gutsura, abun mamaki naga yaci har biyu, sannan ya shanye tea ɗin, rufe ido shi ya sakeyi yayi shiru, naga shirun yayi yawa gasu yayah Ahmad suna zaune akan dinning shi da M.G suna cin abinci suna ɗan taɓa hiran su, sai na miƙe zan tafi chan side ɗin yayah muhammad kawai sai naji muryan shi yace, "ki ɓalla mun maganin nan nasha plz", juyowa nayi na kalle shi, amma har lokacin idon shi a lumshe yake, tsayawa nayi shiru kaman bazan ce komai ba, sai kuma na ƙarasa inda yake na sake durƙusawa daidai inda gwaiwan shi suke na miƙa hannu na karɓi satchet ɗin maganin da yake miƙo mun, dubawa nayi naga guda ɗaya zan ɓalla na bashi, cike da mamakin shi wato ɓalla maganin ma bayajin iyawa, ko kuma samun wuri ne oho, haka dai na ɓalle mishi na buɗe baki nace "gashi", ɗagowa yayi idon shi duk sunyi kalan tausayi, hannu ya saka ya karɓi maganin, idon shi na kaina yace "ruwan ma sai nayi tambaya"? Juyawa nayi na ɗauko goran ruwan da nasan Aunty j ne ta kawo musu da drinks ɗin, zuba mishi nayi a cup na miƙa mishi, idon shi yana kaina ya saka hannu ya karɓa, bayan ya shanye ya sake yin shiru, ni kuma ganin yayi shiru ya saka na sake niyyan miƙewa don na tafi, "ban sallameki ba tukun madam" ya faɗa yana ƙura mun idon shi. Turo baki nayi gaba alaman na gajji, "gobe insha Allah by 9:00pm tafiya na school, akwai wani abu da kike so?" Da sauri na ɗago kaina na dube shi, bansan yayah akayi ba naji bakina yana furta, " gobe kuma? Wani irin school kuma? Tafiya zakayi kabar Yayah M.G shi kaɗai?". Ido ya ɗan ƙura mun kaman mai nazarin wani abu, chan kuma sai ya ɗaga kai ya dubi M.G na wani lokaci sai ya dawo da kallon shi kaina, duk yanayin shi sai naga ya canja, wannan ɗaurewa da masifan sai naga kaman babu su a yau, "M.G ne kawai damuwan ki? Baki tunanin ni yayah zan kasance? M.G kawai kike tsoron ya shiga wani yanayi bani ba ko?" ƙasa yayi da fuskan shi har dab da fuskana, a hankali naji ya furta, "ke baki da damuwa da tafiyan da zanyi ko? Zan daɗe fah, amma duk bai dameki ba sai M.G ne damuwanki ko"?. Yana gama faɗin hakan ya miƙe tsaye bai sake duba na ba ya wuce direct hanyan waje, da sauri naga su yaya Ahmad sun miƙe suna tambayan shi jikin ne? Girgiza kai yayi alaman a'a ya fice a parlon, sallama M.G ya mun ya bi bayan shi, shima yayah Ahmad yabi bayan su, ajiyan zuciya nayi jikina duk yayi sanyi, tou ni mai nace mishi wanda baiyi dai-dai ba? Duk sai naji hankali na yayi mummunan tashi, ga wani yankewa da naji zuciyana yayi, haka na daure naja ƙafana na koma wurin su Aunty B.
Lokacin da na shimfiɗa kafaɗa na a gado sai na neme bacci na rasa, ina jin fatima da hafsy suka gama wayoyinsu suka kwanta, amma ni nakasa bacci, kuma ba komai bane ya hanani bacci sai yanayin da A.G ya fita a ɗazu, narasa tausayin shi nakeji ko me? Ko ganin baida lafiya amma kuma zaiyi tafiyan a haka makeji oho, ko kuma barin M.G da damuwan da M.G zai samu kanshi ne nake ji oho, nidai ranan ban samu nayi bacci ba har wurin sallan Asubah, saboda haka muna idar da sallah nace musu kaina yana ciwo, haka suka rabu dani na koma nayi bacci, ban tashi ba sai wuraren ƙarfe shabiyu na rana, ina tashi wanka na shiga sannan na fito parlor na gaida Aunty B, nan na samu suna ta kiciniyan haɗa girki domin 2:00 yayah muhammad zai iso, sai wani shirye-shirye Aunty B takeyi kaman wani tafiyan shekara guda yayi, duk an share gidan an baɗa mana ƙamshin su na borno, hattah Areefh yasha gayu, a lokacin hafsy ta matsu kusa dani tace , "Adda yau fa zuwan su yaya M.G biyu gidan nan neman ki, ya ƙira wayan ki akashe," kallon ta nayi nace, "shine baki tashe ni ba hafsy? Shi kaɗai ko su biyu"? "su biyu suka zo Adda, ae yace na tashe ki a zuwan su na biyu, sai kuma ɗayan ɗan'uwan shin yace a barki tunda nace kanki ne yake ciwo, amma yace ki ƙira shi idan kin tashi", tana gama gaya mun yadda sukayi na juya na koma ɗaki domin kunna wayana, haka kawai naji ina so nasan yayah suke, kuma lafiya suka zo har sau biyu nema na?.
Ina kunnawa wayan maryam na shigowa, raina a ɗan jagule na ɗauki wayan, "besty meye haka ne, tun jiya nake ƙiranki wayan ki akashe, sannan nace ki ƙirani shima shiru, monday fah zamu koma school kunje kun rashe, baza ku dawo bane kam?" ta faɗa ba tare da jiran mun gaisa ba, ajiyan zuciya na sauƙe domin ganin wayan M.G da yake shigo mun, "besty yi haƙuri bari na ɗauki waya don Allah", katse wayanta nayi na ɗauki wayan M.G. "Ayshaa wa kika samu haka?" gaishe shi nafara ba tare da na bashi amsan tambayan shi ba, shima bai bi takan tambayan da yayi mun ba, kawai ya shiga tambaya na yayah jikina? "da sauƙi" na bashi amsa, "Ayshaa munzo sau biyu kina bacci, dama A.G zai miki sallama ne, kin san da tafiyan shi a nan abuja ne, sai ga shi kuma ya koma ta lagos, kuma flith ɗin shi 1:00 ne, so yanzu ma muna hanyan airpot," "ina yayah A.Gn"? Kawai nasamu kaina da tambayan shi, bai jira me zance ba kawai ya miƙawa A.G wayan, baice mun uffan ba da ya karɓi wayan, amma dai nasan ya karɓi phone ɗin, saboda yadda nake jin fitan numfashin shi wanda bai daidai tu ba har yanzu, nima shirun nayi bance uffan ba, har zuwa wani lokaci sai naji yace, "yayah akayi"? Ajiyan zuciya na sauƙe da ƙarfi sannan nace, "yayah numfashinka", shiru na sakeyi, shima yayi shirun na ɗan wani lokaci, kafin chan yace, "shine damuwan ki?" "a'a ni bashi bane", "meye tou"? Sai da naja lokaci mai ɗan yawa kafin nace, "Allah ya kiyaye hanya, ka kula don Allah", "Hmmm" kawai yace sannan ya miƙawa M.G wayan, sallama M.G yamun akan sun iso zasu shiga ciki, idan ya dawo zai neme ni, mukayi sallama na kashe wayan, tagumi nayi da dukkan hannu na biyu, ban ankara ba sai naji dariyan hafsy, juyowa nayi da sauri na kalle ta, ashe tana zaune akan gado ta ƙura mun ido, tambayanta nayi yaushe ta shigo, tana dariya tace mun tun lokacin da nake soyayyah ta shigo, lokacin idona a rufe ban sani ba, hararanta nayi na fice a ɗakin.
Washe gari muka koma bauchi cike da tsaraban mu da su Aunty j da Aunty B suka bamu, gefe ɗaya ga wani shooping na ban mamaki da M.G ya kawo mun, su fatima ma nasu daban,. Muna komawa da 1week muka koma sch, kuma a wannan lokacin maryam tayi sabon saurayi likita ne mai suna Dr Abdoul, yana aiki a T.H, sunje da mamanta ne bata da lafiya Allah ya haɗa su, haɗuwan su da Dr ya fara kwancewa maryam lissafi da soyayyah, gashi lokacin ma zainab ma ta haɗu da wani ma'aikacin banki mai suna Abdoulmaleek, ɗan gayu ne shima sosai, hadiza tana nan da suraj ɗin ta, haka fatima ma tana nan tare da kabir ɗan maiduguri, da yake duk munyi addn ɗinsu a cikin group ɗin mu, sai ya kasance 9:00 na dare sai mun haɗe a group ɗin ana zuba chafter, yanzu dai ya kasance nice ƙwalli ɗaya banida ma shinshini, don yau mun haɗe an saka zainab a gaba da tsokana, duk da rashin maganan ta da baƙin halinta yau sai da tanka har da dariyan ta, domin sunan da mukaje tana gayawa Abdoul ɗinta wai handsome, duk tsiya muka fara mata anata voice note ana shan dariya, da taga abun ya mata yawa sai ta mayar da chaftern ta kaina, "tou ke ayshaa har yanzu baki samo mana naki gwanin bane? Ko rawan ido irin na yaran GRA kikeyi ne"? Jammy ce ta bata amsa dacewa, "wan irin rawan ido kuma? ae kinsan da badan wani dalili ba da yanzu besty na gidan auren ta, gwaninta special ne zai zo, duk da teemah ta ɗan tsegunta mun wani lafiyayyen soyayyah da akeyi a ɓoye", ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya, sticker na zaro ido teemah ta turo, irin yyh akayi jammy ta tona mata asiri, nan kuwa zainab tafara tambayan waye?, haka mukai ta sharhin mu har 10:00 tayi, daga nan maryam tace zatayi waya da luv, hadiza kam dama bata daɗe ba ta mana sallaman cwit yayi ƙira, haka dai ta ɗaɗɗaya aka watse, sai ni da jammy ne ƙarshen sauƙa, bayan munyi sallama na koma na kwanta nayi shiru ina tunanin habiba, yanzu wasa gaske duk wani alaƙa da muka taso a ciki da ita ya rushe? Duk irin wannan yanayin idan ya faru ita nake tunani, gashi duk wata alaƙa dake tsakanin mu mamie ta bunne shi, ganin tunanin zai mun yawa sai na tashi na fito parlor nayiwa ummie nah sallama na wuce side ɗin hajiya ummah, ina shiga parlor na samu yayah ishaq da ummitah zaune a parlon suna hira, hjy ummah kuma tana fitowa da ga ɗakinta kenan, gani kuwa ta wani kalloni tana ya mutsa fuska, "jirgin danƙaro an ƙaraso ne"? Ko kulata banyi ba na wuce kan dinning ɗinta ina haɗa tea, "tou baiwar Allah idan kinji haushi yau naji ance ga wani yazo wurinki hira mana, kuma da baki so na faɗa kin wani haɗa fuska kinje kina ɗiba mun kayan shayin da ɗana ya saya mun don gadara ko? Tou daɗinta na nan gidan ɗana ne halak malak ba na wani ba, ballantana anuna mun iko", ta na gama faɗa kuwa hafsy ta juya kanta tana cewa, "kaji mun mata wai gidan ɗanta? Tou ae munfi iko da gadara akan gidan da komai na gidan, mufa nan gidan mahaifin mune", Hararanta hajiya ummah tayi, baki agaba tace, "kaji marar hankali, tou ke idan an barki sai ki ɗauka ke wata abarce a wurin shi? Tou ae shi usman daba don farin cikina ba don ƙaniyar ku da duk ya maida ku zaman tafawa ɓalewa, duk kuje ku saje da su hadiza", dariya dukkan mu mukayi, yayah ishaq ya miƙe yana dariya yace, "ni wallahi surutunki ma ya ishe ni, duk kin takura ni kin hanani ƙarasa I Luv u na, bari na tafi ma na bar miki gidan, gidan da ba malam umaru bane yayi amma ake damun mutane da gadara", kafin ya ƙarasa hanyan fita hajiya ummah ta jefe shi da kofin hannunta, "ɗan banza mai wargajejen baki kaman na ubanshi, ae abunda malam yayi har ka mutu bazaka iya ba, har wani gida ne Usman yayi na nunawa a duniya wanda malam bai yi shi ba? Ja'iri ni irin gatan da malam ya nuna mun ni da ƴaƴana ae ƙaryan Usman yayi shi, har kuna wani ɗagawa gaku ƴaƴan wani ko"? Dariya muke mata gaba ɗayan mu, don dama ƙarshen faɗan kullum haka yake komawa, ana taɓo mijinta zata koma kare shi, dariya yayah ishaq yayi ya fice yana ƙara mata ɓacin rai da, "wargajejen bakina fah na mamana na ɗauko, don baba na yafi kyau", da gudu ya ƙara sa fita saboda ya ƙara ƙular da ita, tsayuwa tayi ta rasa abun da yake mata daɗi, nida hafsy kuma sai dariya muke, bata kula mu ba ta wuce ta kashe T.V ta, sannan ta kalli hafsy ido a ɗaure tace, " maza tashi ki tafi inda kike kwana sokuwa mai nacewa soyayyan ɗa namiji, bakida zuciyar karatu irin na ƴar'uwar ki sai zuciyar son ƙaton banza mai babban baki, tashi ki fita marasa kunya", ta faɗa tana nunawa hafsy hanyar waje, dariya hafsy tayi ta gyara zama tace, "anan min zan kwana, babu mai fitar dani a duk inda yayi mun a gidan nan, idan mutum ya matsa kuma na ƙira Abba yanzu yaji irin sakayyar soyayyan da yayiwa mahaifiyar shi take mishi nata, bata son ƴaƴan shi, bata son su raɓeta", "amma dai Allah wadaran munafuki mai haddasa fitina tsakanin ɗa da uwa, ni yaushe naƙi ƴaƴan usmanu? Yoo ko gadona ƴaƴan usman sukace na sauƙa su kwanta ae sai na sauƙa, ballantana ɗan banza cikin wani ɗaki na daban? Tou a hirr ɗinki kika ƙirashi kika tayar mishi da hankali", tana faɗa ta juya zuwa ɗakin kwanciyar ta tana ta mita, mudai dariya mukeyi nida hafsy, don babu abunda yake rufe bakinta irin ace za'a gayawa Abba bata son mu, Allah sarki hajiya Ummah.