Kenza eBookz

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 10

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 10

Ana barin halal original by anty nice Chapter 10: Ana barin halal original by anty nice Chapter 10. Washe gari muka lula birnin tarayyah mu da ƴan'uwan mu…

4,240 words

Washe gari muka lula birnin tarayyah mu da ƴan'uwan mu da matayen su, koda mukaje gidan mai gadi ne ya buɗe mana gate, babu laifi compound ɗin zai iya ɗaukan motoci guda uku, ga flowers masu kyau da ƙamshi a shuke, gidan sama da ƙasa ne, ƙasa shine na Yaya mohd sama kuma yayah Ahmad, da shike kafin biki Aunty B da yayah sun zo sun saka komai a gidan su, amaryah ma anzo an mata mata jeren, kawai ɗan sharewa da gogewa kawai mukayi, sannan aka shimfiɗa bedsheets, a side ɗin yayah mohd muka sauƙa nida fatima da hafsy, su yayah umar kuma hotel aka kama musu, amma munyi hira tare dasu, kuma babu abinda muka girka, order kawai aka mana, washe gari da yammah muna zaune a parlorn Aunty B mukaji buɗe gate da shigowan mota, ba'a wani ɗau lokaci ba yayah Ahmad ya ƙirani a waya yace nazo sama na same shi, ɗaukan ɗan ƙaramin gyalen abayan jiki na nayi na fita. Ina shiga parlorn shi bakina ɗauke da sallama nashiga, Yayah Ahmad da su M.G nagani zaune a parlorn gaban su cike da kayan snacks da drinks da Aunty J takawo musu, hannun kujeran da yayah Ahmad ke zaune naje na zauna, na ɗaura hannu na a kafaɗan shi na sunkuyo kaɗan setin kunnen shi ina gaishe shi, dariya yayi yana amsa mun, ganin M.G yana kallon mu fuskan shi ɗauke da murmushi, shi kuma A.G ko ɗago kanshi ya kalle ni ma baiyi ba, niko don yau ɗaya na bashi haushi sai na kalli M.G fuskana cike da fara'a nace yayah M.G mun same ku lpy? Shima cike da fara'a ya amsa mun da munzo lafiya? Bayan mun gaisa na juya kan yayah Ahmad ina ce mishi gani. "Dama M.G ne yace a ƙiraki ku gaisa, shine daman ƙiran, yyh hafsy fa babu wani damuwa ko?" ya faɗa yana riƙe da hannu na da yake kafaɗan shi, murmushi M.G yayi yana kallon mu cike da sha'awa yace, "barrister kuna burgeni kai da ƴan gidanku, kuna ƙaunar junan ku sosai, har sai naji dama ina da ƙani ko ƙanwa mana, da na nuna mata ƙauna kwatankwacin irin naku, amma insha Allahu zan so mata na irin haka da ƴaƴa na", da sauri na ɗago kai na kalle shi, shi kuma ya wani ɗaga mu giran shi duka biyu yana murmushi, sai kawai na samu kaina da maida mishi murmushin. Baby sis baki gaida A.G ba shine fah ya taso ni akan muzu mu muku sannu da hanya, tun jiya ya matsa muzu naƙi" ya ƙarasa faɗa yana ƙunshe dariyan fuskan shi, "amma wallahi kayi girman banza tunda baka daina ƙarya da ƙazafi ba, munzo dai duba amaryah da ango ba yaran nan marasa kunya ba, bana son jan raini M.G", A.G ya faɗa muryan shi a ɗan cike da ɓacin rai yana hararan M.G, shikuma babu abinda yakeyi sai dariya, yayah Ahmad na tayashi, ni kuma jin abunda A.G ya faɗa sai na maida kallona kanshi fuskana ɗauke da jin haushin yarfen daya mun, harara ya zabga mun, nima ban wani ɓata lokaci ba na zabga mishi harara na murguɗa baki ina guna-guni ƙasa -ƙasa don yaji haushi, ae kuwa nan take ya ƙule, miƙewa yayi da sauri ya tsaya yana duban M.G yace, "tou ƙaton banza maƙaryaci sai ka tashi mu tafi tunda ba'a abun arziki da kai, yanzu sai kaja yarah su raina mutum", ya ƙarasa faɗa yana zungurin ƙafan M.G. "wani raini kuma? Daga faɗan gaskiya? Tou shikenan muje kada na sake suɓutan baki", ya faɗa yana miƙewa, hannu ya miƙawa Yayah Ahmad yana dariya shima yayah Ahmad ɗin dariyan yakeyi, hararan su A.G yayi ya juya kaina yana kallo na fuska a murtaƙe, kaman baxai ce komai ba sai kuma yace, "ke baki iya suturce jikinki ba ko?" Ban samu daman bashi amsa ba ya wuce ya fita da sauri, nidai kallon kaina kawai nayi naga shigana baiyi muni ba sannan na maida kaina kan su M.G da yayah, suma kallona suke fuskan su cike da dariya, M.G ne yace "kada ki damu baby sis, yau ɗan'uwa na acike da zafin kanshi yake, tunda aka taso da maganan tafiyan mu karatu hankalin shi baya jikin shi, sai faɗa kawai yakeyi," dariya suka sake kwashewa shida yayah, "ae kasan A.G baya wani son tafiyan nan, shi damuwan shi yayi aure, kuma wai ae nigeria ma ana karatu, shi wajen ne baya son zuwa", yayah yafaɗa yana ƙara dariyan fuskan shi, M.G ma dariyan mugunta kawai yakeyi yace, "ae barrister duk inda ya biyo ya rushe maganan tafiyan nan yayi amma Daddyn shi yaƙi sauraron shi, ƙarshe ma ya ɓuge da wai asthman shi yana yawan tashi idan ya fita waje, nan ma Daddyn yace sai yaje dai, haka babu yadda ya iya ya dawo yace shi tou sai yayi aure tukun ya tafi, Daddy ya tmby shi waye yake nema aje ayi magana nan kuma yayi shiru yana muzurai," dariya suka kwashe da shi suna tafawa, M.G ya kalle ni yace, "baby sis ku shiryah gobe in the evening zamu ɗan zagaya da ku kusha iska" godiya na mishi na juya na fita, ina sauƙowa na samu su fatima na gaya musu gobe idan Allah ya kaimu su M.G zasu fita damu shan iska.

****** Wuraren ƙarfe 5:00pm yayah Ahmad ya ƙiramu a waya mu fito, saboda mun saka fita a zuciyan mu tun muna idar da sallan la'asaar muka shiryah, dukkan mu shigan abayah mukayi, Hafsy onion colour, fatima ash, ni kuma blue black nasaka, ko wanmu tayi kyau masha Allah, motan yayah Ahmad shi da Aunty jeeddah ne da Aunty B sai Areefh da yake riƙe a hannunta, sao motan yayah mohd kuma dama yau ya tafi lagos zaiyi 2dys ya dawo, yayah umar da yayah ishaq sai hafsy ne a ciki, motan M.G kuma A.G nagaba sai ni da Fatima abaya, a tsaye a gaban motan muka samu M.G, tou anan muka gaishe shi fuskan shi cike da fara'an shi, yana ta zolayan mu wai munyi kyau kaman zamuje fadan shugaban ƙasa, mudai murmushi dukkan mu mukayi, muna shiga motan wani fitinannen ƙamshi ne yake tashi mai daɗin gaske, fatima ce tafara gaishe da A.G, juyowa yayi kaɗan gefen da take, wato bayan sit ɗin driver ya amsa mata mata, nima a hankali na gaishe shi, amma sai yayi kaman bai jini ba, murguɗa baki nayi na masa gwalo ta bayan shi, don nasan yaji tsaf gaisuwan danayi, narasa dalilin daya sa mutumin nan yake jin haushi na, kome na mishi ohoo, mintsini na fatima tayi a cinya tana harara na, kallon tanayi ina tura baki gaba alaman naji zafin mintsinin, alama ta mun da na gaishe shi, hararanta nayi na sake murguɗa baki a ƙeyan shi na ɗaga kafaɗa alaman naƙi, a haka M.G ya shigo, "*JABI SHOPRITE* zamuje kun taɓa zuwa wurin Aysha"? Ya faɗa yana tayar da motan bayan ya ɗan juyo ya kalle ni, murmushi nayi nace mishi, "ehh muna zuwa, yayah mohd yana kai mu ko yayah Ahmad idan munzo hutu", juyowa kaɗan yayi ya sake kallo na yace, "ok kuna zuwa wa Abbah hutu ne? Na ɗauka su ummie ne kawai suke zuwa", "muna zuwa yawanci a ramadan ko idan mun samu dogon hutu", na bashi amsa, kafin yace wani abu A.G yace, "don Allah malam ka maida hankali a toƙin da kakeyi kada ka chika mun kunne da yawan magana", Murmushi A.G yayi ya maida hankalin shi kan driving da yakeyi bai tanka mishi ba, a zuciyana nace ganshi kaman wani Boss, na ɗan murguɗa baki na cike da jin haushin shi.

Muna gama yin parking kowa ya fito aka jera ciki, bamu shiga wurin shopping ɗin ba muka wuce wurin shan iska, muna isa muka zauna nida fatima da M.G, ina kallon A.G suka zauna suna magana da Yayah Ahmad, gefe ɗaya kuma yayah ishaq ne da hafsy, Aunties kuma suna tare, bamu daɗe da zama ba M.G ya yafito yaya umar, yana zuwa yace "ga amanan fatima ka tayata hira, bari muyi gefe zan yi magana da Ayshaa please", ya faɗa yana miƙewa tsaye, kallon fatima yayi yace "please teemah a bani aron baby sis zamuyi wani shawara ne da ita," murmushi tayi ta ɗan kalli yayah umar da yake zama tace, "babu komai Allah yasa muji shawara mai kyau", murmushi yayi ya wuce ina biye da shi a baya, Ɗan gefe dasu kaɗan muka zauna, muna zama na ɗago kaina na dubi inda su A.G suke zaune, abun mamaki sai naga ya bimu da kallo, ɗago kan danayi na kallesu yasa shi harara na, nima ban ɓata lokaci ba na murguɗa mishi baki, dariya yaso bani ganin zaro ido da yayi yana ɗaga mun duka giran shi biyu, alaman na raina shi ko, juyar da kaina nayi kan M.G shiru yayi yana kallo na, kaman baxai ce komai ba, chan sai naji ya sauƙe ajiyan zuciya mai ƙarfen gaske wanda har sai da na ɗago kaina na dube shi. "shawara zamuyi ni dake baby sis, amma kafin nan ina son ki san waye M.G" kallon shi nakeyi bance komai ba, amma dai na maida hankali na gaba ɗaya kanshi, don na daɗe da wannan burin a zuciyata. *MUKTAR GARBA (M.G)*

Shine cikakken suna na, gidan mahaifina yana unguwar kobi da ke cikin garin bauchi, mahaifiyata Fatima wacce muke ƙiranta da suna Goggo mu bakwai ta haife mu, yaranta guda shida manyan uwa ɗaya uba ɗaya suke,nine autan su wanda kuma mahaifina daban da su, gaba ɗaya yaranta maza ne, bata taɓa haifan ƴa mace ba, Malam Garba shine sunan mahaifin yayuna wanda nima da sunan nake amfani da shi, malam Garba malamin makaranta ne a *KOBI PRIMARY SCHOOL* unguwa ɗaya suke da mahaifiyata, auren soyayyah sukayi da Goggo, Goggo nah faran macece bafulatana ƴar *KAFIN MADAKI* amma girman garin bauchi, sunyi zaman lpy da mijinta malam Garba da ƴan uwan mijinta sosai, kuma babu laifi suna rayuwar su cike da rufin asiri, Babban wanmu sunan shi Auwal, sai Sani, Salisu, Rabi'u, sai twins da tayi na ƙarshe wato Hassan da Hussain, gaba ɗaya tsakanin su shekara bibbiyu ne, ƴan biyun suna da shekara biyu mahaifinsu Allah ya mishi rasuwa, lokacin yayah auwalu yana da shekara goma, yayah sani takwas, salisu shida, yayah rabi'u huɗu, yayah hassan da hussain kuma suna shekara biyu, domin an yaye su suna tafiya ko ina da ƙafan su, dukkan su kuma farare ne sol kaman mahaifiyar mu, gashi kowa a cikin su yana hanci tamkar na goggo, sai dai kamanin su ɗaya da mahaifin su, Yayah Hassan da hussain ne kawai suka ɗauko fuskan Goggo sak, mijin goggo ya rasu ne sakama kon ciwon wuni ɗaya tak, a yanda ake bani labarin mutuwan ya bugi jama'an da suke cikin gidan, domin gidane mai girman gaske a kobi, shashi- shashi ne a gidan, gidane daya ƙunshi family dayawa, gashi malam Garba mutum ne na kowa, gashi baida tashin hankali yana zaune lafiya da kowa, bayan rasuwan shi da kwana goma mahajjata suka dawo lafiya cikin ƙasashen su, wanda yayi daidai da dawowan ɗan'uwan shi da suke ƴaƴan bappanu, kuma sun tashi sa'o'i juna, akwai shaƙuwa mai yawan gaske a tsakanin su, wato *ALHAJI ALKALI ABDULLAHI* haka ya samu jagorancin ƴan'uwa da abokan zumunci har zuwa sa shin mahaifiyar malam Garba, hannun shi riƙe da na yayah salisu da yayah rabi'u, bayan shi kuma su yaya auwal da yayah sani ne ke biye da shi da sauran ƴan rakiya, kuka sosai yayi a ɗakin Inna, domin itama ganin shi sai duk hankalin ta ya tashi tayi ta kuka ana bata haƙuri, alkhairi sosai ya ajiye mata ya koma jaddada mata insha Allahu babu komai zai kula da su, daga nan ya taho ɗakin goggon mu, nan ma ansha kuka ba kaɗan ba, domin tsakanin Alkali Abdullahi da Malam Garba akwai shaƙuwa sosai, duk da yayi kuɗi baida makusanci irin malam Abdullahi, duk da matan shi basu so, domin gani suke ajin mijin su ya wuce na tarayyah da malam Garba, amma furr ya nuna musu basu isa ba, sudai suna zumumcin su, amma matayen su basa zumumci, gara ma uwargidan wani lokaci ta kan leƙo goggo, irin ko anyi rasuwa ko ta haihu ta shigo tayi barka, itama ko suna bata shigowa, amma takan dai ɗan leƙo, ita ƴa ɗaya ta haifah wanda a lokacin ta kai shekara shabiyar, domin Alƙali ya riga malam garba aure, kuma tun da ta haifi ƴarta mai suna safiya ta samu matsala a mahaifanta bata sake haihuwa ba, safiya na da shekara uku Alƙali ya ƙara aure na biyu, ita amaryar tana isa da izzah domin ita ƴar cikin fada ce, tana ji da sarauta ita ko ɗaga kai ta kalli mutane da mutunci batayi, Tana da shekara ɗaya ta haihu ɗa namiji, bayan shekara ta ƙara ɗa namiji, wanda tare aka haife su da yayah auwal, na uku sa'an yayah sani ne shima namiji, lokacin alƙali ya ƙaro wata ƴar wani Ambasoda tana karatu a Bacas, itama tunda tazo ta haifi nata yara mata guda biyu alokacin, a wannan lokacin ne malam garba Allah yayi mishi rasuwa. Alƙali yayi kuka sosai ana bashi haƙuri, daga nan ya tafi, bayan tafiyan shi aka shigo da kayan abinci sosai gidan, inna tazo har gefen Goggo ta raba abincin biyu ta ɗauki ɗaya ta barwa goggo ɗaya, daga wannan lokacin Alƙali ya an bawa yaya auwal kuɗi idan an kwana biyu a shigowa goggo da shi, tana arba'in ma ya sake haɗo kayan abinci aka kawo,. Haka dai rayuwa tayi ta ja har goggo ta ƙarashe takaba, Alƙali bai gajji da hidima da su ba, makarantan da Malam Garba wanda ake ƙiran shi da Baba suka cigaba da ɗaukan ɗawainiyar karatun su yayah na, bayan shekara aka saka su yayah hussain a makaranta, sannan a wannan lokacin Alƙali ya bijiro da maganan auren Goggo, innah kuwa tayi ruwa tayi tsaki ta dage akan sai anyi, domin maganan gaskiya ta hanga ta hango babu wani tsayayye da zai iya cigaba da kula da su irin shi, kuma idan goggo tayi aure duk watsar mata da yara zatayi, don babu mai iya riƙeta da yaran nan, matan Alƙali kaman zasuyi ƙaramin hauka da sukaji maganan auren nan, domin maganan gaskiya Goggo irin kyawawan matan nan ne, wanda kyaun su yake firgita mutum, amma babu yadda suka iya Allah ya nufa akwai rabon haihuwata a gidan dole sai Goggo taje, ya ɗago kai ya kalle ni bayan ya faɗi hakan, nima ɗagowa nayi na kalle shi, amma lokaci ɗaya sai naji jikina yayi sanyi saboda ban taɓa ganin rashin murmushi a fuskar shi ba sai yau, fuskan shi na kallah sai naga kaman shi da A.G yau, kamane bawai kaman hanci ko ido ko wani abu ba, kama ne dai kaman na yanayi, juyar ds kai na nayi na kalli gefen da su yayah suke zaune, abun mamaki karaf idon mu ya haɗe da na A.G, ya ɗan kwantar da kanshi saman kujeran da yake yana kallon mu, yayah Ahmad kuwa suna ta hira da Aunty J, kawar da kaina nayi da ɗan sauri ganin ƙura min ido da yayi, kallon na yar kan M.G, ajiyan zuciya ya sauƙe bayan ya ajiye ruwan da ya ɗauka ya sha. Ranan jumma'a aka ɗaura auren su a babban masallacin jumma'a da yake ƙofar fadan bauchi, kuma a ranan Goggo ta tare gidan ta, Baba nah yaso goggo ta tare da dukkan yaran nata, amma inna ta hana kan, cewa tayi daga baya za'a kawo ƴan biyu da Rabi'u, sauran kuma zasu zauna anan, tunda gida biyu ne tsakanin gidan Baba na da gidan mu. Tunda ga ranan da Goggo ta shiga gidan auren ta bata samu nutsuwa da kwanciyar hankali ba, dukkansu matan gidan da yaran gida haɗe mata kai sukayi suka hanata sakat a cikin gidan, hattah da masu aikin gidan basu ganinta da mutumci ko girma, don ko aikin gidan Uwargida (hajiya hauwa) bata amince a ringa yi mata ba, sannan yaranta rabiu da ƴan biyu sun sha wahala da dukan gaske a hannun ƴan gidan, har ta kai zaman su yafi ƙarfi a chan wurin Inna, yawanci sai kwanciya ke dawo da su gidan, ranan girkin Goggo kam ma achan gidan mu suke kwana a ɗakin Inna cikin kulawan Yayah Auwalu, Baba na duk yadda yaso ya bada kulawa wa goggo na da ƴan'uwa na abu ya gagara, Goggo tasha wahala a hannun kishiyoyinta har tsawon shekara uku Allah ya nufa ta samu cikina, laulayin da Goggo tayi ya wuce tunanin mai tunani, don ko ruwa bata isa tasha ba sai ta dawo da shi, abun da yake iya zama a cikinta shine ruwan sirki wanda Inna ke aiko yaya Auwalu ya kawo, domin shi kaɗai ne yake shigowa gidan basu hantare shi ba, don shi babu fuskan rainia tare da shi, cikina yana wata uku bai cika huɗu ba Baba na ya saki Goggo, babu wanda ya isa yace ga dalilin shikan, shi dai kawai shigowa yayi ya miƙa mata takaddar saki ya kuma ce yabata wunin yau kaɗai ta tattare kayan ta tabar gidan, a lokacin yayah auwalu yana tare da ita, shiru yayi yana sauraron kukan goggo wanda gaba ɗaya ta rame ta fita a hayyacinta, sai ɗan dogon hanci a fuskanta, fita yayi yaje ya gayawa inna, babu ɓata lokaci Inna ta turo ƙanwar ta inna ƴanbiyu, haka aka tattare kayan goggo aka dawo da shi ɗakinta na gidan Malam Garba, dama akwai sauran kayan ta a ciki har da katifan ta na da, dayake ɗakin ciki biyu ne da parlor a tsakiya, su yaya suna ɗayan ɗakin goggo ta dawo nata ɗakin,abun tausayi tunda goggo ta dawo lafiya ya gagara, laulayi na yau daban na gobe da ban, haka inna ƴanbiyu ta dawo ta zauna da ita, saboda inna tana fama da ciwon ƙafa sosai, cikin goggo na wata bakwai amma bata taɓa zuwa awon ciki ba, domin tun da ta fito Alƙali bai taɓa waiwayan ta ba, lokacin da yayan Baban mu ya tare shi da maganan zuwanta asibiti cewa yayi ba zai iya ba, cikin ma taje ya bar mata shi duniya da lahira, shi sauran yaran da yake da shi ma sun ishe shi rayuwar duniya. Gidan Alhaji inuwa mai Gwal shine gidan da yake maƙwabtaka da mu ta gefen dama, gida ne da zance duk kobi babu gidan da aka tara ƴan gayu masu tafiya da zamani a gidan, Babban ɗan shi Garba inuwa ma'aikaci ne a banki, lokacin yana ji da tashen samartaka da kuɗi, domin ɗan gata ne a wajen mahaifin shi, don kuwa shi kaɗai ya haifa ɗa namiji kuma babba, sai ƙannen shi mata guda biyu, bai daɗe dayin aure ba yana xaune a fadaman mada, amma duk weeƙand yana gida da amaryar shi wacce ake ƙiranta Aunty Rashidah, ma'aikaciyar asibiti ce mai bala'in tsabta, gata da sauƙin kai da son mutane, gata ƴar masu kuɗi don lokacin idan akace miki gidan mutane a GRA ne tou shi na musamman ne, Goggo na ta iya kitso sosai, lokacin sai surkuwar ta matar Alhaji Inuwa mai suna Dadda tasaka ƙannen Garba suka rakota kitso wurin Goggo, shigowanta wurin goggo taji a zuciyarta Goggo ta mata domin yanayi tsabtar Goggo da haƙurin ta ya taɓa zuciyar Aunty Rashidah, shigowan ta na biyu ta samu Goggo tana jiƙa shinkafan masan ta na gobe, domin Goggo da taji sauƙi sai ta riƙe sana'ar Inna na suyan masa domin su rufawa kansu asiri, ita kuma goggo ƴanbiyu da yake bata taɓa haihuwa ba tana nan tare da su domin kula da inna.

Sun zauna yin kitso Aunty Rashida ta tambayi Goggo a wani asibiti take awo? Murmushi kawai Goggo tayi ta gyara ta fara tsaga kanta domin kitse mata shi, har suka gama yaryara kitson goggo bata ce mata komai game da maganan awon cikin ba, har sai da zata fita tacewa Goggo gobe idan anyi masan zata turo driver ya karɓa musu da yake sunday ne, sannan ta miƙawa goggo kuɗi mai ɗan kauri tace ta shiryah taje asibiti domin fara awo, cike murna goggo tayitq godiya, wanda har inna da inna ƴanbiyu suka fito suna tayata, idon inna cike da hawaye take duban goggo da take ta share hawayen da yaƙi tsaya mata a idon ta.

********** Ai kuwa ranan monday goggo batayi aikin masa ba tabarwa su inna ta wucce asibiti, haka ma'aikatan sukayi ta mata masifan rashin zuwa da wuri, ita dai bakin ta shiru sai ido da take bin su da shi, bayan angama komai ta fito zata dawo gida suka haɗu da Aunty Rashida da ta fito gaisuwa cikin asibitin specialist ɗin, ganin goggo na ta sauri zata tari abun hawa domin tafiya ta tsayar da ita, Goggo fuskanta ɗauke da murmushi ta tsaya suna gaisawa, murmushi daya kasance nida ƴan biyu mu muka ɗauke shi, domin ni ba sosai ake gane abun da yaɓata mun rai ba kamar Goggo na, don fudkan mu kullum ɗauke yake da mirmushi, wannan kuma ba wani abu bane na daban halittah ne da Allah ya kanyi mutum da shi, bawai rashin aji bane ko kamun kai, kawai halittah ne na ubangiji, ya faɗa yana duba na alokacin fuskan shi ɗauke da murmushin, nima murmushin nayi ina sunkuyar da kaina ƙasa, don samun kaina nayi da jin kunyan shi mai girman gaske *Aunty nice* ga shi murmushin shi wani irin kyau yake ƙara mishi, gaskiya *Aunty nice* M.G mai kyau ne, kyaun da idan kina kallon shi zakiji zuciyar ki tana samun nutsuwa na musamman, gashi M.G mutum ne mai zuciya mai kyau. Murmushi nayi ina kallon fuskan hajiya ayshaa da take wani lumshe ido tana buɗewa cike da yanga, daga alama kuma zuciyar ta ba ƙaramin so takeyi wa M.G ba, domin sunan shi kawai idan ta ambata sai naga fara'a a kan fuskarta.

Kallon shi nayi ina ƙara jinjina labarin a zuciyana, Ayshaa muna unguwa ɗaya da mahaifina amma ban taɓa sanin shi ɗin mahaifina bane, ni har nakai 11yrs ban san shi mahaifina bane, kuma baa taɓa barina na shiga gidan ba, domin yayuna sun razana ni da shiga gidan, yaran gidan ma basu shiga gidan mu, abun da nasani dai akwai wata mata mai aikin su masifaffiya da take shigowa gidan mu, domin bayan tafiyan yayah auwal sai abubuwa sukayi yawa wa goggo da innah, gashi kitson ya ɗan ja baya a hannun goggo saboda ta fara girma, an fi zuwa wurin yarah, ita sai ɗaiɗaiku ne suke shigowa irin su Aunty Rashida, dole goggo ta fara karɓan surfen gero na kunu, idan tayi tana dakan hannu na garin kunun, wannan yana kawo customers dayawa, amma goggo tana shan wahala sosai, dole ta haƙura da masa yayah sani da yayah Rabi'u suke hidiman innah ƴan biyu na taimaka musu, alokacin kuma su hassan sukan fitar dashi da safe su sayar, ni kuma ina riƙe da ƙaramin ruban kananzir ɗin inna, Allah yayi mu da hanzari, muna sayarwa zamuyi gudu- gudu muyi shirin makaranta, tanayi, abun haushin kuma Baba na yana son kunun tsamiya na dakan hannu, tou wannan mai aikin ita ke shigowa da shi takawo goggo ta daka su bata kuɗin, kuma goggo bata taɓa nuna baxata yi ba saboda tana samun kuɗinta chass idan tayi, (wannan labarin true life story ne, kada kuji haushina akan abunda goggo takeyi na ƙasƙantar da kanta na aikin gidan tsohon mijinta, hakan ya faru ne, wasu abun ma zafin su yasaka na cire su a labarin,). Ana shirin kama azumi gidan Baba na aka aiko wake buhu guda da geron da goggo zata gyara musu, haka ta haɗa kan yayah sani, yayah rabiu da ita kanta sukai ta aikin surfe wake suna gyarawa, tsaf ta gyare shi ta zuba a wasu boketai da aka bayar ta zuba, sannan tayi aikin geron shima tsaf ta haɗa garin kunun kafin afara azumin, wannan masifaffiyar mai girkin gidan Baba na ita tazo da wasu samari biyu suka ɗauki kayan, sannan wannan azumin babu gidan da Baba na bai aika kayan azumi ba sai gidan mu, haka sallah yazo yayi hidima wa maƙwafta da ƴan'uwa da abokan arziki amma banda mu, bana mantawa wannan kuɗin da goggo ta haɗa da shi ta mana kayan sallah, wani yadi wai shi Bambalasta shi tasaya mana, ruwan ƙwai, ranan sallah mukayi wanka mukayi tsaf da mu, nidai sai murna nakeyi bakina a buɗe ranan ina dariyan daɗi, domin idan naga yadda yadin yake wani walai-walai sai na ƙara jin farin ciki, haka mukaje ɗakin inna wanda tun tsakiyar azumi bata ji daɗin jikinta ba, muka gaisheta mukayi mata sallaman zamu wuce masallaci, hannu ta miƙo mun, gaban ta naje na tsuguna, a hankali ta dafa kaina tace "ubana Allah yayiwa rayuwar ku albarka, ayi haƙuri da rayuwa da yadda tazo, duk cikin yaran nan kai nake tausayi babana, idan anje masallaci ayi addu'a", Murmushi nayi ina duban ta nace, "zan miki addu'a ki samu sauƙi innah" itan ma murmushin tayi ta ɗan juyar da kanta inda yayah sanie yake tsaye tace, "Auwalu idan yayi waya a gaishe shi ku mishi biyayyah banda raini, auwalu ubane", haka muka fita zuwa masallaci, Bayan an sauƙo an dawo gida duk unguwan mu labarin kayan da yaran Alƙali Abdullahi suka saka kawai akeyi, don har wani kallon su aka tsaya anayi, saboda wancan lokacin ba kowa bane yake sayawa yaran shi kaya masu tsada, amma su baban mu komai yi musu mai kyau yakeyi.

Readers Also Read