Kenza eBookz

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 9

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 9

Ana barin halal original by anty nice Chapter 9: Ana barin halal original by anty nice Chapter 9. Bayan ƙawaye da amaryah sun fito sun chashe, mun musu…

4,450 words

Bayan ƙawaye da amaryah sun fito sun chashe, mun musu liƙi sosai, sai aka ce amaryah ta tsaya a fili ita kaɗai, sannan ango yazo ya nuna mata irin ƙaunar da yake mata, wurin yayi tsitt, fitowan ango yazo ya tsaya gaban amaryah ya ƙura mata ido yana wani binta da kallo fuskan shi ɗauke da murmushi ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa, sautin waƙan *ALI JITA* kawai yake tashi a hankali, inda yake raira waƙan 🎸🎸🎺Gimbiyata sai ke, soyayyar mu har abada, ko rana da wata sun daina haske, Gimbiyata sai ke, soyayyar mu har abada, i luv u baby, sarauniya baby soyayyarmu har abada🎸🎸🎤 waƙan mai ratsa zuciya, yana zuwa wurin ya rungumeta a jikin shi, gaba ɗaya hall ɗin aka ɗauki tafi da shewa, ya saka hannun shi ya ciro zube ya saka mata, ya riƙe hannun suna rawa a hankali kaman wasu turawa, sai ganin yayah mohd nayi a fili yana musu ruwan kuɗi sai liƙa musu kuɗi yakeyi, haka muka sake tasowa muka liƙa musu, a haka abokan ango suka fito suna ta liƙa musu kuɗi, ɗago idon da zanyi charaff sai a cikin na A.G, muna haɗa ido ya mun alaman na fita, ban wani ja ba kowa na juya na fara barin wurin, a lokacin kuma sulaiman ya fara mana liƙi nida hafsy da su yayah umar, yanayi yana tsokan hafsy da "jerry ina tom ne kan ban ganta ba"? Dukkan mu muna dariyan hafsy da ta turo baki gaba, hakan ne ya saka na dakata da fita a filin, inda M.G ma ya shigo ya fara mun liƙi, don kaɗan yayiwa ango da amaryah ya dawo kaina, lokacin fatima ta riƙe hannuna a dole sai nayi rawa, M.G yana murmushi yace, " yauwa fatima gara ki saka ta tayi rawa, auren yayah barrister guda baza tayi rawa ba? Ae bai yi dai-dai ba", ya cigaba da liƙa mun shida sulaiman da nura baba da wasu a cikin friends ɗin su da suma hankalin su ya dawo kaina, mantawa nayi da kashedin A.G na tsaya hannu na riƙe da ɗan ƙaramin purse ɗina, na rungumeshi ina ɗan juyawa, ni ba rawa ba ni ba tsayuwa ba, a haka DJ ya sallame muka koma. Zuwa 11:00pm aka tashi a dinner ɗin, fitowa mukayi inda motan su Aunty b yake, yayah umar da yayah ishaq suka ɗauki ummitah, hafsy, zainab a motan su, yayah mohd kuma shida Aunty b a gaba, baya kuma ni, fatima, hadiza, maryam, a haka muka wuce gidan yayah mohd, muna shiga motocin angwaye na suna ta shigowa, sun dawo da ƙawayen amaryah, dare yayi bai dace a mayar da kowacce ƙawa gida ba, cewar yayah mohd daya gayawa angwaye, saboda haka dole a gidan amaryah zasu kwana, idan yaso gobe sai ango ya dawo gidan shi, haka kuma akayi, muna jin shiga da fitan motocin angwaye gidan, har kusan 12 sai ga ƙiran M.G, ina ɗauka ya tambaye ni don Allah idan babu damuwa na kawu ruwa mai ɗan zafi a cup A.G zai sha magani, idan na fito suna wurin motan shi, tashi nayi na ɗauki ƙaramin flask mai ruwan zafi a ciki da cup, kallon hadiza nayi nace ta raka ni don Allah, muna fitowa na tsaya ina duba inda motan M.G yake, sai naga an kunna wutan mota an kashe, alaman naga inda suke, ƙarasawa mukayi, dai-dai nan M.G ya buɗe gaban motan ya miƙo hannu ya karɓi flask ɗin, duk hankalin shi a tashe, gefen mai zaman banza kuma yayah Ahmad ne zaune ya juya baya yana kallon A.G yana ta mishi sannu, a hankali na maida kaina ina kallon A.G dake zaune a bayan motan, sai hakki yakeyi yana ta maida numfashi daƙyar- daƙyar, hannun shi riƙe da inhela yana fesawa, gaba ɗaya fuskan shi tayi zufah, Allah sarki sai naji gaba ɗaya ya bani tausayi, kaman bashi bane ɗazu yake ta wani faɗi a wurin dinner, amma dube shi yanzu yana ta kanshi cike da azaban fusgan numfashi da yakeyi. Fifita ruwan M.G yakeyi da cup ɗin da marfin flask ɗin, ganin haka yasaka na karɓa ina yi mishi, shi kuma ya ɗauko magani a gaban motan ya ɓalli guda ɗaya ya miƙawa A.G, ina ganin shi ya karɓa gaba ɗaya jikinshi yana rawa, sai wani hawa da sauƙa ƙirjin shi yakeyi a laman numfashin yana mishi wahalar jawowa, duk jiki na sai naji yayi sanyi, barin ma yadda naga hankalin M.G ya tashi sai naji duk nima na rasa nutsuwa lokaci ɗaya, miƙa hannu A.G yakeyi alaman a bashi ruwan, ganin haka yasa na buɗe ɗayan gefen inda yake zaunen na miƙa mishi a hankali nace, "sannu ga ruwan", ɗago kai yayi ya kalle ni kaman bazai karɓa ba, sai kuma ya sake jan wani numfashin da ƙyar ya saka hannu ya karɓa, a hankali ya shanye maganin da ruwan ɗumin, duk ido muka ƙura mishi kaman zamu karɓa mishi, yayah Ahmad sai sannu kawai yake mishi, M.G ko kaman shine ciwon yake jikin shi, a hankali naji muryan shi yace, muje ka kaini gida M.G, ango nagode sannu", ya faɗa wani tari na zuwa mishi, haka ya tsaya da maganan yayita tarin suna mishi sannu, nidai bansan lokacin da na buɗe bayan motan na shiga na zauna a gefen shi ba, don gani nayi kaman numfashi zai ɗauke, ga wani hakki da yakeyi har kana jin sautin numfashin yana sarƙewa, zama nayi ina duban shi ina ta jera mishi sannu, sannan na dubi yayah Ahmad muryan na yana rawa kaman zanyi kuka nace ,Yayah ko asibiti zaku kaishi? Da ƙyar fa yake numfashi", na faɗa ina maida kallona kanshi, Ajiyan zuciya M.G ya sauƙe yace, "taurin kaine da A.G, nace mu wuce asibiti yana wani cewa idan yasha ruwan ɗumi da maganin zai sauƙa, gashi kuma numfashin har yanzu bai dai-dai ta ba, ni ban san meyasa baya son asibiti ba wlh, gashi ciwon shi na asibiti ne", "yayah tou ku kaishi basai kun jira shi ya yarda ba", na faɗa ina ƙara matsawa kusa da shi, ɗago kai yayi ya harare ni murya a shaƙe yace "ke ina wasa da ke ne? Bana son manyance fah, ce miki akayi bazai faɗa bane kina wani shirin yin kuka"? Ya faɗa yana ƙara maida inhelan bakin shi ya zuƙa sannan ya maida kanshi kan sit ɗin motan ta baya ya kwantar, dukkan mu shiru mukayi muka zuba mishi ido, baka jin ƙaran komai sai na heater da yake kunne, ita dai hadiza tana tsaye ta side ɗin yayah Ahmad ta ƙura mana ido, niko shigewa ne jikin A.G kawai banyi ba, saboda ni bansan ma lokacin da na sake matsawa kusa dashi daf ba, ina jin ya sake fara tarin na matsa kusa da shi nace, "plz yayah kuje asibitin mana dare nayi kuma kana shan wahala", na faɗa idona yana wani cikowa da hawaye, Ɗago kanshi yayi ya ƙura mun ido, abun tausayi duk idon ya maida su ciki ciki ya lumshe su kaman baya iya kallon mutum, yana kallo na yana jan numfashin shi da ƙyar, a hankali yace, "M.G muje asibitin" har ya faɗa idon shi yana kaina, ni ma kuma ban ɗauke ido na ba akanshi, ina ji kaman na fashe da kuka, ajiyan zuciya M.G yayi ya gyara zaman shi, ya dubi yayah Ahmad yace, "kai ka koma masauƙi kai da sauran abokan mun, ni zan wuce da shi duk abun da ake ciki zakaji ni insha Allahu", hararan shi yayah Ahmad yayi yace, "idan na tafi ma baccin ba iya yin shi zanyi ba, zan gayawa Nura baba ya tsaya akan komai tunda yusufsun wuce gidajen su, ni sai muje kawai", ya ƙarasa faɗa ya na ciro wayan shi a aljihun shi domin ya ƙira nura baba da suke chan cikin parlor da ƙawayen amaryah. "Nima yayah M.G zan biku asibintin", na faɗa ba tare da na san maganan ya fito bakina ba, harara na A.G yayi, shi kuma M.G ya juyo ya kalle ni fuskan shi ɗauke da murmushin dole, "ki koma gida dare yayi, insha Allahu komai zai zo da sauƙi, akwai alluran da suna mishi zaiji sauƙi, har ma yafi ki yin bacci," ya faɗa yana maida kanshi kan Yayah Ahmad. Hannun A.G naji ya riƙo hannuna ya riƙe da ɗan ƙarfi kaɗan, da sauri na ɗaga kaina ina kallon shi, shima kallona yakeyi, sai dai wannan kallon yau ɗin babu harara a ciki, idan ban yi ƙarya ba sai naga kaman kallo ne na rarrashi, ganin haka sai naji jikina yayi sanyi har wani hawaye naji yana so ya zubo mun, girgiza kanshi yayi alaman no, kada na fara kukan ya mun, ajiyan zuciyan M.G na sake ji shi yasa na maida kaina kanshi sai naha idon shi gaba ɗaya a kanmu, kunya naji kuma naji na ɗan ruɗe kaɗan, ganin haka sai yayi murmushi yace, "kije hadiza na jiranki ku wucce gida zan ƙiraki kiji yayah ake ciki, yana gama faɗa na zare hannu na a hankali a na A.G, bai wani ja ba ya sake mun hannun na juya na fita a motan, a hankali nace "Allah ya sauwaƙa yayah A.G" ina faɗa na yi sauri nayi hanyan cikin gida, hadiza na bina a baya har muka shiga ciki na rufo ƙofan muka wuce ɗaki, muna shiga hadiza ta nemi wuri ta zauna ta zabga wani uban tagumi, ni kuma bakin gado na wuce na zauna ina jina kaman akwai abun da na rasa na farin ciki a zuciyata, kallon mu fatima tayi tace "lafiya dai malamai kuka shigo kaman masu mummunan labari"? "Hmmm, akwai ja a gaban mu, ehh nace akwai charkwakiya a gaba, nidai dije sai zuru, naga abunda ba'a gani ba, ehh naga abun al'ajab," hadiza ta faɗa tana ƙara wani tagumin kaman tsohuwa mai shekara 100, hararanta maryam tayi tace, "ke wallahi dije jan rai ne da ke, meye ne kam? Ango ne ya haiƙewa amaryah a gaban idon ku"? Gaba ɗayan mu dariya muka kwashe da shi, don hattah zainab da baƙin halinta na share mutane sai da ta kwashe da dariya, nima duk damuwan da nake ciki sai da na dara, ita ma kanta mai maganan dariya abunda ta faɗan ƴa dawo yana bata, tana dariya tace, "wallahi al'amarin yayah Ahmad tsoro ya koma yana bani, kunga wani rawan kai da yakeyi kuwa? Kaiii maxa sai a hankali duk yadda kake ganin su barsu kawai a yadda suke, tou na sani ko kunje kunƙi barin wurin, shi kuma haƙurin shiya ƙare ya zaburar mata? Don ina razane da shi a wurin dinner nan kada ya bamu kunya,Allah ya rufa asiri dai aka gama taro lafiya", dariya muka sake kwashewa da shi, don wallahi abunda ta faɗa gaskiya ne, koni nayi ta mamakin shi. Duk yadda suka so jin gulmar hadiza taki tofawa, wanda ni ban ma gane akan me take maganan ba a lokacin, haka muka ɗan taɓa abubuwan dariyan mu, a hankali fatima tace "ko yayah habiba yanzu? Tunda ance surkuwarta ta hana dinner da komai, nasan yanzu ɗaki daga ita sai Ali sai abunda suka ƙullah" dariya dukkan suka sheƙe da shi, amma ni kuma sai naji wani mummunan gaɗuwan gaba,wanda har ya kaini da duba agogon hannu na, ganin ƙarfe 2 saura sai naji wani abu ya chaki zuciyata, runtse ido naji lokacin da naji muryan maryam tana cewa zuwa yanzu kam ko an kashe big boss ko ana kashe busawa masu tsaron gidan, habiba kuma hankali ya kwanta, yadda taci burin dogon miji ya kuma an haɗe da su zulaihatu", ta ƙarasa faɗa suna ƙyalƙyalewa da dariya, don duk wanda yasan habiba yasan ta da wannan language ɗin na zulaihatu, kowa yasan ma'anar da ta ɗaura kalman zulaihatu akai, ga habiba da masifan son aure da ma, ni ko a sch idan naji ana hiran aure da abunda ya ƙunsa kunya nakeji, kuma bazak ji baki na ba, amma habiba duk shirun ta tanajin an fara hiran aure zakaji ta akan gaba, yanzu kaji ta tana, "kai auren baƙi dogon mutum duniya ne, don yanzu zakayi kiciɓus da hajiya zulaihatu mai lafiyar zuciya", ya faɗin haka kowa zai kwashe da dariya, don an san me take nufi, tana farawa nake janta mu bar wurin, na ringa ranƙwashin kanta kenan tana dariya, ana cikin dariyan naji sauti wayana, da sauri na ɗauka, su kuma duk sukayi shiru suka ƙura mun ido, muryan M.G naji yana ce mun "bakiyi bacci ba har yanzu?" murmushi nayi nace, "yanzu muke shirin kwanciya" "Tou ki kwanta ki huta shima yayi bacci, an mishi allauran Alhamdulillahi ya sauƙa har ya kwanta", ya faɗa yana mun sallama. Ajiyan zuciya nayi, sannan na maida kaina na kwanta. Washe gari tunda asuba Aunty B ta tashe mu, haɗuwa mukayi dukkan mu a kitchen muna haɗa breakfast na amaryah da friends ɗinta, ga kuma na yayah Ahmad da friends ɗinshi, don duk yau zasu koma, so kafin 8:00 mun gama komai, na amare aka kai side ɗinsu, na angwaye kuma yayah ne da yusuf suka zo suka ɗauka, nidai lokacin da suka zo ma na shiga wanka, 10:30 mun gama komai mun shiryah, nan mukayi wa Aunty B sallama zamu wuce gida, domin driver yana waje ummie ta turo yazo ɗaukan mu, haka muka fito gudu - gudu mukaje side ɗin amaryah muka gaisheta, tayi kyau tana sanye cikin wani lace black mai ratsin golden, fitted gown ne ya yi matuƙar amsan jikin ta, Gsky Aunty jeeddah tayi babu ƙarya ƴar gayu ce na nuwa, da fara'a sosai a fuskanta ta amshe mu, bayan mun gaisheta muka mata sallama zamu tafi, da sauri ta miƙe tana tmbyn meyasa bazamu zauna ba sai anjima? Da murmushi a fuskan mu nace mata ummie tace mudawo zamuyi aiki a gida, amma insha Allahu zamu zo, har bakin ƙofah ta rakamu hannunta na riƙe da hannuna, ina kallon hafsy sai harara na takeyi, ai kuwa muna shiga mota ta juyo tana harara na, " Adda wannan karon kan inaga sai Abba ys shiga lamarin mu, don babu yadda za'ayi ki ƙwace Aunty B, yanzu ma ki ƙwace Aunty jeeddah ba, duk iyayin ki sai kin bar mun ɗaya", ta faɗa tana wani tsuke baki da fuska, dariya muka kwashe da shi, ina riƙo ta jikina dama a gefe na take zaune, "haba hafsy masoyiya tah, ni dukkan su ma na bar miki, har mai zuwa a gaba ma, nidai fatana Allah ya bar mun ke, shine babban buri na," kwanciya tayi a kafaɗa na tana ƙyalƙyala dariya kaman ba ita bace take harara na yanzu, "Adda ae mai zuwa na gaban kai ae dama tawa ce, sai yadda nace", ta faɗa tana zungurin ummitah, mudai dariya muka musu.

Muna sauƙa a motan muka wuce side ɗin hjy ummah mu gaisheta, a parlor muka sameta dasu Aunty ma'u, Aunty Rakiya dasu yayah umar, gaishe su mukayi sannan na shige ɗaki na ajiye kayana.

Angama biki da 1week Yayah Mohd da yayah Ahmad suka fara shirin komawa Abuja, domin wannan karon yayah mohd zai tafi da Aunty B, sun kama gida wuri ɗaya da yayah Ahmad, gidan offstair ne ɗaya yana sama ɗaya yana ƙasa, ko wanne yana ɗauke 1 parlor 2 bedrooms, ana saura 2dys su tafi Abujan, Aunty b da Aunty jeeddah suka zo gida dukkan su suka wuni, ranan wani farin ciki na musamman nake gani a fuskan ummie, don lokacin ɗaura lunch tare muka shiga kitchen da su Aunty b, ummie dai tana zaune parlor da su yayah, don dukkan su ranan a parlon ta suka wani, akai - akai zakiga mamah ta shigo, abinci kala 2 akayi, domin ko wacce abinda mijinta yake so ta girka, suna ta raha a tsakanin su, nidai sai kallon su nakeyi ina jin daɗi a raina, nida hafsy da fatima aka barmu da haɗa drinks, mukayi zoɓo mukayi kunun aya, sannan hafsy ta sake haɗa tarmarrin juice, wai tasan shi yayah umar yake so, nidai kallon ta kawai nakeyi don nasan ƙarya ne, yayah umar kunun aya yake so shida yayah Ahmad, yayah mohd ne mai son zuɓo, yayah isgaq ne mai so, duk da ban ganshi a parlon ba amma nasan babu daɗewa zai zo, don inaga wataran a gidan nan ma yake wanka idan banyi ƙarya ba, haka muka je muka jera komai a ƙasan parlorn bayan mun shimfiɗa babban ledan cin abinci, domin ummi tace kada a ɗaura akan dinning Suna dawowa a sallan azahar dukkansu suka shigo parlorn, murmushi nayi ganin harda yayah Ishaq, babu wani kunya ko takura na wani surkunta, ita ummie ta gaya musu su ɗauke ta uwa, itama ƴaƴa ta ɗauke su, ita dai bata son raini, amma duk abunda suke buƙata wanda uwace keyi tou bata ɗauke musu ba su tunkareta, kuma ko wani matsalah ne idan baifi ƙarfinta ba su sameta, bata son su nemi iyayen su sai sunga gazawanta, zuwan su sama sai da ta zaunar dasu da mazajen su ta musu nasiha sosai, sannan ta nemi haɗin kansu dasu zauna da junan su lafiya, kallon Aunty jeeddah tayi tace, "Hauwa maijeeddah, yanzu ne kika shigo cikin mu ke, domin ita Bintu ta riga da ta daɗe da shigowa, mun santa ta sanmu, domin ta zauna dani ɗaki ɗaya na tsawon shekara guda, yanzu kece kika shigo kuma bana so ki ɗauki kanki kaman baƙuwa, kema ki saka a ranki tuntuni kina tare a cikin mu, yanzu kece ƙarama kafin auta na ya kawo ta shi, abunda nake so dake kiyiwa Bintu biyayyah kamar kina tare da babbar yarki, ku haɗa kanku kada ku bada ƙofan da za'a shiga tsakanin ku, domin haɗin kanku shine ƙarin haɗin kan ƴaƴa na, ni kuma shine burina da nutsuwata, mu haɗa kai dukkan mu mu zama abu ɗaya, shine fata na da buri na, kuma dukkan ku irin so ɗaya nake muku, babu wacce tafi wata a wurina sai wacce tafi kyautata mun, kuma tafi zaman amana da mu, ni wacce umar na zai aura tun bata zo ba iri ɗaya nake jinku a zuciyata, yadda dukkansu ƴaƴan iri ɗaya nake jin su a raina, saidai wanda yafi kyautata mun" nasiha sosai ummie ta musu, kuma tayi wasu yayah ma, bayan fitan matan su ma ta ƙara yi musu, domin yadda muka taso da son junan mu tana so abun ya miƙe har kan ƴaƴa da jikoki, inda ta nuna musu haɗin kan matan su shine nasu haɗin kan, domin idan matan su babu haɗin kai zai shafi zumuncin su, don kowa nashi ya sani, haka dai aka zauna cin abincin kowa cike da farin ciki, filet ɗaya Aunty B ta zuba musu da Aunty jeeddah, nima da hafsy da fatima filet ɗaya muka zuba yadda muka saba ci da hafsy tare, yaya umar da yayah ishaq na nasu tare, yayah mohd da yayah Ahmad da ummie filet ɗaya suka zuba, domin yawan cin lokuta tare suke cin abinci, da ƙyar kiga ummie nacin abinci dani ko hafsy, amma yayah Ahmad da yayah mohd yawanci tana cin abinci tare da su, tun bama yayah mohd ba, shi yawan ci duk irin abunda ummie keso na abinci shima yana so, don ko zuwa yayi duk inɗa ta zauna yana gefenta, idan ta koma ɗaki zakiga baya wani daɗewa zai bita, idan tayi kitchen ma zaki ganshi ya bita, toilet ne kawai da bayida iko baya binta, kuma har yanzu idan ya zauna zakiga ya jingina da ita, narasa wani irin ƙulafucin uwa yake da shi a zuciyan shi, Areefh dai yana gefen yayah umar, don tunda suka zo yake wurin shi domin son shaƙu sosai. Gaba ɗaya parlon ya ɗauki shiru, banda ƙaran spoons sai Areefh da yake ta gulaniyan shi, a haka mukaga an ɗago labulen parlon da sallama, Abba ne ya shigo, hannu ya saka ya riƙe haɓan shi yana duban mu ɗaya bayan ɗaya, idon shi ya tsayar akan ummie yace, "baiwar Allah irin wannan wariyar launin fata haka? Haba baiwar Allah ae sai aɗan taimakawa marayan Allah ɗan ɓoto a gayyace shi yazo shima ayi wannan ciye-ciyen da shi, kayan daɗi iya kayan daɗi amma sai a ware ni gefe guda"? Ya faɗa yana neman wurin zama a gefen yayah umar da yayah ishaq, mudai parlon gaba ɗaya dariya muke mishi, sannan kowa yana mishi sannu da shigowa, hararan su yayah mohd yayi yana cewa, "ni ae tunda naga muhammadu an fito a sallah bai wani tsaya munyi hiraba ya wani kamo hannun ɗan'uwan shi Ahmadu sukayi gaba har suna tuntuɓe na xargi wani abu, ubana ne kawai da ishaq suka ɗan tsaya da mummunan ɗansu muka ɗan zanta, a lokacin nace tou anya babu wani abu da ake ɓoye mun?". Dariya ummie tayi tace, "wallahi kana raina, duk loma ɗaya idan nayi naji daɗin girkin da ƴaƴana suka shirya mun sai na tuno ka, kawai dai babu yadda zanyi ne na share, don nasan amaryah ta shiyah maka table da danasha", ta faɗa tana kallon shi da dariya, dukkan mu dariya mukayi ganin yadda Abba ya wani kama haɓa yana hararan ummie, kallon sa ya maida kan su Aunty b yace, "yanzu yarana hadda ku anuna mun wariya ko"? Sun kuyar da kai Aunty B tayi tana dariya, a hankali tace, "Abba nima fah kana raina shiyasa na zuba maka naka a flask, yana kitchen dama jira nakeyi muna gama na bawa hafsy ta kai maka", ta ƙarasa tana dariya. Spoon yayah umar ya miƙawa Abba yana cewa, "rabu da kowa Abba muci abinci tare, kaga nima ware ni sukayi, dama kullum haka ake mun, shiyasa kaga sau ɗari wurinka ko wurin hajjaju makkatu nake zuwa ci, don yayah mohd yana shigowa yake cinye abincin gidan nan shida ummin shi," ya faɗa yana kai loman abinci bakin shi, dariya mukayi ummie tana cewa, "wallahi yaron nan kaji tsoron Allah, nafi yawan cin abinci da kai fah, yanzu ka fito da tsirfah kala -kala kace baka cin wannan baka cin wannan" haka dai akayi ta raha ana cin abincin, wanda Abba sai da yaci duka girki kala biyun yana ta santi, ana gama ci muka tattare komai, sannan Abba yaja ƴan mazan suka tafi side ɗin shi, mu kuma dukkan mu muka wuce wurin hajiya ummah, ummie kawai muka bari.

Wuraren ƙarfe 9:00 na dare suka yi shirin tafiya, lokacin yayah Mohd yake gayawa ummie Abba yace umar, ishaq, hafsy, raliya da ni zamu musu rakiya, da yake flight zamu bi sai yace zamuyi 1week mu taya su shiga sabon gida sai mudawo, gaba ɗaya muka ɗauki murna nida hafsy, ita ma fatima sai taji daɗi, domin dama har ta fara mitan ita kaɗai zataje ta dawo, don itama ta fara ATBU damu, tou anyi idan lokacin school ne zata zauna damu, idan anyi hutu sai ta wuce Abujan, haka muka rakasu wurin motocin su muna ta murna.

Washegari hafsy mukaji muryan mamie tana ta zabga masifa, da ta kwana biyu batayi ba, don tunda aka gama bikin nan batayi wani abun azo a gani ba, sai da hafsy ta fita ta jiyo don tsegumi, tazo tana gaya mana wai akan maganan komawan su yayah Abujah ne, wai Abba ya sake ƙarar da kuɗin shi wurin saya musu gida, ita bata yadda ba su ƴaƴa matan ba ƴaƴa bane? Nan Abba ya watse ta yace mata gida ba saya akayi ba, rent suka kama kuma kowa da kuɗin shi ya kama, amma haka ta dinga rantsuwa akan Abba ne yasaya, idan ma kamawan ne shi ya kama, kuma bazata yadda ba, shi kuma yace kada ta yadda ta kaishi ƙara koton ƙulin duniya, sannan tace kuma babu inda raliya zataje, kala taje a cutar mata da ƴa, yadda aka so cutar da habiba a mallake mata ƴa, a nan ne Abba yace mata ita taso shi ya gajji da fitinan ta, shi dai yayi ƙoƙarin haɗa kan ƴaƴan shi, amma tunda ita ta raba ita taso, itace da baƙin ciki gaba ba shi ba, nan mamie ta sake maimaita "raliya fah bazata je ba, kalan idan sun dawo kace suje gidan habiba? Wanda bansan wani sharrin za'a shiga mata da shi ba? Kowa yanzu ya tsaya kan nashi, don baza je a wargaza mun zaman lafiyan ƴa ba, ita kuma wannan da tauraron ta ke haskawa baza'a je a wargaza mata nata, domin an haɗa kai da mutanen borno ae babu abun da bazasu tsayawa mutum ba, anan ne mamah ta fito ta mata jan ido tukun ta koma ɗakin ta. Murmushi ummie tayi tace ita dama bata saka aranta raliya za'a bar ta taje ba, saboda haka ita ta sani fitina kawai maganan zai jawo, Allah ya kyauta kawai ummi tace, mudai babu abinda ya dame mu shirin kayan mu kawai muka cigaba dayi, muna ciki shirin naga ƙiran M.G na shigowa wayana, kallon waya na tsaya yi ban ɗauka ba, don tun ranan da suka isa Abuja bai sake ƙirana ba, ban san kuma dalili ba.

Har wayan ta yanke ban ɗauka ba, ƙira na biyu ya sake shigowa shima har ya yanke ban ɗauka ba, daga nan bai sake ƙira ba, kallo na hafsy ta tsaya yi, chan dai ta kasa haƙuri tace, "Adda kaman ƙiranki naga Yayah M.G nayi?" kallon wayan nayi ba tare da nuna mata wani alama da zata fahimci komai ba nace, "kinsan shi da son labari yanzu sai ya hanani abun da nakeyi, ni kuma abunda mamie tayi yau na duk ya ɗaga mun hankali bana jin son magana, shi kuma yanzu zai fara tambayan yyh nake me yake faruwa?" na faɗa ina ɗaukan wayar don na maida ita silent. "Allah sarki Adda ae mai sonka ne yake damuwa da damuwanka, ni kuma wallahi bakiji yadda nake son ki da yayah M.G ɗin nan ba, don ranan ma sai da mukayi ta gulman ki nida yayah ishaq", ta ƙarasa tana dariya, na ɗago kai ina kallon ta cike da mamakinta, "gulma na kuma name kukayi ke da yayah ishaq ɗin"? Dariya ta cugaba dayi sannan ta dawo kusa dani ta zauna, hannun ta tasaka ta dafa kafaɗa na tana magana cike da dariya a fuskanta, "kina rawa yayah M.G yana miki liƙi kukayi bala'in yin kyau, shine yayah ishaq yake tambaya nah saurayinki ne? Nace mishi a'a kawai kuna shiri ne, sai yace Allah yasa shirin ya koma soyayyah don kun dace da shi sosai, kuma wallahi Adda kun dace sosai ga shi kyakkyawa da shi, don ni yafi mun wancan ɗan'uwan shi mai ɗaurarren fuskan", ta faɗa tana wani ya mutsa fuska. Nidai murmushi kawai nayi bance mata komai ba, don ko ni M.G yana burgeni kuma kyaun shi yana mun kyau, fara'ar shi tana sakani nishaɗi, da fatan nasu zai zama gaskiya da nayi farin ciki sosai, amma dai iya zuciyata na bar abun.

Readers Also Read