Ana barin halal original by anty nice - Chapter 8
Ana barin halal original by anty nice Chapter 8: Ana barin halal original by anty nice Chapter 8. Ana sallan la'asar gidan mu ya cika maƙil da mutane, haka…
3,175 words
Ana sallan la'asar gidan mu ya cika maƙil da mutane, haka muka fito muka nemi sit muka zauna da su Aunty Bintu da dukkan wanda suke side ɗin ummin mu, dama kuma Aunty Rakiya ta sauƙe mun kyakkyawan warning akan zuwa inda ƙawaye suke, bata hana mu fita wurin ba tace saboda hakki na ƴan'uwan taka, amma tayi hani da shige musu, ko ita hafsy an ɗakatar da ita da zuwa wurin raliya, muna zaune aka fito da amaryah cikin shigan ta maroon, ƙawayenta na familyn su da ƴaƴan ƙawayen maminta ne suka rako ta, bayan ta zauna babu daɗewa dangin maminta suka rako mamin ta ita ma har wurin zamanta, wayaga uwar amaryah ansha leshi ɗan gaske kana ganinta kaga anaryar Alhaji Usman umar (U.U Ɓalewa) dama kafin fitowan ta mamah da ummi sun daɗe a fili kowa tana table ɗaya da ƙawayenta, ɗago da ido na ɗaɗɗaya ne zanyi ban tarar da idon habiba akaina ba, kuma duk haɗa idon da mukayi sai ta sakar mun murmushi, nima kuma sai na mayar mata, a haka naji tsakin hadiza, da wuri na juya sai naga harara ta ke ɓalla mun, sanin me take nufi ya sa ban kula ta ba na juyar da kaina ina kallon masu rawa.
Har sai dab da magrib dangin ango suka iso, abun mamaki basufi mutum biyar ba, bayan table mai ɗaukan mutum goma aka bar musu guda biyu, saiga mutum biyar sun shigo, haka aka rakasu suka zauna aka kawo musu abinci, ana fara ƙiran magrib suka je fili bayan an ƙirasu da amaryah suka mata liƙi marar ma'ana, daga nan sukayi sallama suka kama hanya, ni acikin su ma bansan fuskan kowa ba, banda ƙanwar mummy guda ɗaya, haka dai aka cigaba da chashewa da DJ, mudai ana fara ƙiran sallan magarib duk mukayi side ɗinmu domin sauƙe farali, basu suka tashi a wurin ba sai wurin 9:00pm, shima sai da Abba ya dawo yace a sallame su tukun suka watse, ni lokacin ma ina kitchen ina dafe tea wa yayah Ahmad, da yake girkin ummie nane sai na haɗa hadda na Abba na, flask ɗin Abba na cika sai na yayah Ahmad, sai na cika wani wa don naji Aunty Rakiya ma tace zata sha, ganin akwai time sai na gasa bread wa yayah Ahmad don yana so sosai, hafsy na roƙa ta kai mishi lokacin da naji shigowan motan shi.
Wuraren 10:00pm muka fito tafiya gidan Aunty Bintu, da yake yau babu ummitah da maryam motan zata ɗauke mu ba sai an nemo driver ba, muna isa babu wani ɓata lokaci muka fara shirin kwanciya, da yake kowa ya gajji yau, a parlor muka tarar da yayah mohd yana kallo, muna shiga ya miƙa hannu ya karɓi Areefh da yake bacci a hannun hafsy, dukkan mu gaishe shi mukayi sannan muka wuce, babu wani dogon hira a tsakanin mu dukkan mu mukayi bacci, cikin bacci naji vibration ɗin wayana, a razane na jawo wayan na duba mai ƙiran, sai naga number ne, da sauri na yanke wayan, sannan na kashe ta gaba ɗaya na koma na kwanta.
Ana sallan asuba babu wacce ta koma bacci, gyaran gidan mukayi tsaff aka turare shi da turaren wuta masu ƙamshin gaske, saboda idan mun fita baxa mu shigo ba sai lokacin kawo amaryah, abun breakfast muka haɗa, muna karyawa aka dinga shiga wanka, wuraren 9:00am muka shiga gidan mu, ana ta shirye - shiryen tafiya ɗaurin aure, da yake ƙarfe goma za'a ɗaura a masallacin gwallaga, daga na yayah Ahmad har na Habiba achan za'a ɗaura, parlon Abba dukkan mu muka shiga, achan muka haɗu da mamie da Aunty Rakiya tare da Abban mu suna magana, gaishe su mukayi muka fito.
Wuraren 11:30am gidan mu ya cika da ƴan'uwa da yayun mu, wanda sukaje ɗaurin aure daga dangin Ummie har na Abba duk sun hallaro gaisuwa da taya murna, gefe ɗaya kuma ga ƴan'uwan mamie da suke ta baza guɗa, nidai duk guɗan su yankar mun zuciyata takeyi, wato ya tabbata habiba ta auri Aliyu? Aliyun da ya soni, Aliyun daya gama cewa babu mace da yasani wanda ta kaini kyau, kuma yaji a duniya yana sonta sama dani, Aliyun da aka daɗe ana son aga macen da zaice yana so, wai yau ƴar'uwata da nakeyiwa so da ƙauna itace ta zama mallakin shi, itace zasuyi rayuwar aure ba ni ba? Tou Allah ya sanya alkhairi, Allah ya bani haƙuri da juriya.
Yau ma anko mukayi da hafsy, wata super da yayah Mohd yasaya mana, nawa ash nata yellow, gaba ɗaya munyu kyau babu ƙarya, ina lure da hafsy da ummitah jiki na rawa suke ta haɗa duk wani nau'in abinci da akayi a gidan wa yayah umar da yayah ishaq, yayah umar ne ke shigowa ya karɓa su tafi, nidai mamakin su yayah umar ɗin ma nakeyi, yabawa hafsy fah wurin 10yrs amma jibi yadda yake ta wani rawan jiki da kai wa ummitah, koda yake ni kaina bana gajjiya da kallon ummitah, domin duk gidan su tafi su kyau, ga wani diri da Allah yayi mata, ummitah ba fara bace, sai dai wani colour ta keshi mai hasken gaske, idan ka ganta sai kasake kallonta saboda wasu ido da takeda masu kyaun gaske, ga shagwaɓa kamar babu wata ɗiya a gidan sai ita, kullum kaga ganta cikin shagwaɓa take bansan yayah za'ayi da yayah umar ɗan zafi ba, hala fah sai ya biye mata a hakan, dariya nayi ni kaɗai na.
Ana sallan magrib babu daɗewa wannan number ta sake ƙirana, yanzu banƙi ba na ɗauka, murmushi nayi lokacin danayi karo da muryam M.G yana cemun, "mai kyau ina kika ɓuya ne yau? Gaba ɗaya ban ganki ba"? Murmushi nayi na fara gaishe shi batare da na amsa mishi tambayan shi ba, amsawa yayi ina jin sautin murmushin shi, "jiya kinyi bacci ae na ƙiraki, naso da safe na ƙira mu gaisa Allah bai nufa ba, yanzu ma ina so na sanar dake idan an tashi tafiya dinner ki jira zanzo na kaiko idan babu damuwa". Murmushi nayi na bashi amsan da "Allah ya kaimu yayah," Sallama mukayi yace sai yazo, yana zolaya na wai nayi ɗaurin da za'a san ƙanwar su 1 in town ne, dariya ne ya suɓuce mun na kashe wayan, ina murmushi a zuciyata nace, "nidai M.G yana burgeni, gaba ɗaya baida wani matsala kaman ɗan'uwan shi, shi baida wani sara sai hararan mutane da shegen son girma, ni mai yawan ɗaure fuska baya burgeni a duniya nan, ima son mutum mai faran-faran, gashi fari dogo ga fara'a", murmushi na sakeyi na miƙe nayi parlor wurin su hadiza.
Wuraren 9:00 M.G ya ƙira waya na yana tambayan mun shiryah,? Ido na yana kan zainab da take wani juyi a jiki mirrow tana kallon kyaun da tayi da aka mata make-up da aka mata, koni kallon kaina nake tayi ina ganin yadda na chanja kama, amma dai gaskiya yayiwa kowan mu kyau, domin ba'a wani tsauwala mana shi da yawa ba, muryan shi naji yana "tou ku fito na shigo gidan", amsa mishi nayi da "tou" sannan na kashe wayan, kallon su nayi nace su fito muje, dama Aunty Bintu tunda na gaya mata ɗazu tace yama fi mata sauƙi, don ita da yayah moha zasu tafi, hafsy da ummitah ma tare zasu tafi da su yayah umar, dama na gayawa ummie nah M.G yace zai kaimu, nasiha ta mun da mu tsare mutuncin mu kuma banda rawan kai, a haka muka fito, kowan mu tasha lace mai musulmin kyau, orange ne colour nawa, na hafsy black da golden, an mana wani fitted gown, ga gyalen mu shantily, munyi kyau dukkan mu kaman ka ɗauke mu ka ɓoye, *"MASHA ALLAH*" Naji muryan M.G yana faɗi lokacin da muka iso jikin motan, shima lokacin ya fito ya buɗe mun gaban motan yana wani sara mun, hakan da yayi sai duk ya saka mun dariya, naji kunyan abunda yamun har sai dana ɓoye fuskana a tafin hannu na, Ya Rabbi M.G yana da kyau da burgewa, nidai halayen shi da ɗabi'un shi sun fara burgeni, ina son yabawa, ina son kulawa sosai, haka na shiga gaban na zauna, maryam, fatima, hadiza, zainab suka shige baya, ina jin shi yana tambayan su basu matsu ba? Basu matsu ba suka bashi amsa dayake motan mai girma ce, amare tun yammah aka kaisu, habiba ma da yamma aka kaita gidan ta, amma dukkan mu babu wanda Aunty ma'u ta bari yaje rakiyanta, Aunty Bintu ma nan ta tsaya suka amshi amaryah, kuma ana magrib tana ciki. Wanda suka jagoranci amaryah zuwa gidanta, domin ummie tace a wuce da ita gidanta tayi shirin abun da yake gaban su, shiyasa gidan namu yayi shiru, domin duk an tafi kai amare.
Tunda muka isa M.G bai barmu mun shiga wurin programm ɗin ba, wanda aka shirya yi a *ZARANDA HOTEL* muna zazzaune a cikin motan yana ta jan mu da hira, inda hadiza da maryam suka fi mu zaƙewa wurin hiran, kuma daga dukkan alamu ko wacce a cikin mu taji daɗin yadda yake tafiyar da mu, ango da amaryah basu iso ba sai wuraren ƙarfe 10:00, wata irin jeep ce mai girma da kyaun gaske baƙa wuluk tana shaining ango da amaryah suka iso a ciki, gaba ɗaya kallo ya koma kan motan, inda wasu daga cikin angwaye da ƙawaye suka matso wurin motan suna jiran fitowan su, Ƙafan driver tana buɗewa naga A.G ya fito a ciki, fuskan nan kaman an mishi albishir da ranan mutuwan shi ko alaman ya taɓa dariya babu a fuskan, haka kawai naji yabani haushi, daga nan ango da amaryah aka buɗe musu suka fito. Kaiii yau wace rana Yayah Ahmad fuskan shi cike da fara'a? Sai wani dariya yakeyi kaman bashi ba, yana fitowa ya matso gefen amaryan shi ya riƙo hannun ta, bamu san me aka gaya mishi ba gaba ɗaya wurin suka ɗauki dariya, angwaye da amaren duka, shi kuma ya ɗan rungumo amaryan shi kusa da shi, dai-dai lokacin M.G yace muje wurin mu gaisa dasu sai mu shiga.
Muna isa wurin yayah Ahmad ya miƙo mun hannu na ƙarasa wurin shi ya rungumoni jikin shi yana sunkuyawa kunnen amaryan yana mata magana, inaji ta saka hannun ta tajawoni kusa da ita, dayake fuskanta rufe yake da mayafinta, gaisheta nayi zuciyana cike da ƙaunar ta, bayan mun gaisa abokan shi suka fara maganan a jera yadda za'a shiga DJ yana announcing shigowan su, jin haka mukayi niyyan shigewa cikin hall ɗin. Juyawan da zanyi naji an riƙo hannu na an jawoni, tunani na Yayah Ahmad ne, amma juyawan da zanyi sai naga hannun A.G ne riƙe da nawa, ina ji ya jawo ne baya kusa da ƙofan da ya fito na motan, gaba ɗaya idon M.G yana kanmu, Yayah kuma kallo ɗaya yayi mana ya sake maida kanshi kan abokin shi da yake maganan su gyara yadda za'a shige.
"ki maida hankalin ki nutsu a wurin nan, idan kikayi wani abu da bai mun ba zaki koma gida a ƙafa", A.G ya faɗa mun murya ƙasa-ƙasa wanda nima da ƙyar nake jin shi, ga wani yankewar zuciya da na samu kaina inayi akai - akai, bai ishe shi ba ya sake cemun, "wani irin kwalliya ne aka miki gaba ɗaya ya maida ki kaman dodo? Ga wani gyale kaman wani gidan sauro?" Zuciyata naji ya ɓaci na yanda ya wani kushe ni, turo baki nayi gaba kaman zanyi kuka, "zan buge mummunan bakin nan idan baki gyara shi ba", "kana bugewa zan buge naka, kabarta ƴan'uwan ta suna jiranta zasu shige ciki" M.G ya faɗa yana ƙarasowa inda muke, harara A.G ya mishi sannan ya sake hannuna, yana sake ni da sauri na ware nabi bayan su maryam jiki na yana rawa.
Tunda muka samu wurin zama muka zauna maryam da hadiza suke ɓaɓɓaka dariya, gaba ɗaya haushin su ya kamani, don na rasa me yake saka su dariyan, ɗaure fuska nayi naja tsaki nace, " amma dai za kusa a raina mu irin wannan dariyan ƙauyancin da kuke yi, tou meye ne ma kuke wa dariyan"? Na faɗa ina hararan su, kaman wani jira suke nayi magana sai suka sake kwashewa da wani dariyan, wanda har suka saka fatima ma ta ɗan dara, tana kallon su tace, "haba ku kuwa ku daina dariyan nan mana ae zaku saka ido ya dawo kanmu, gashi ma yanzu na hango Aunty b ta wani tsura mana ido," Sokaye ne ae na faɗa ina ƙara hararan su, dai-dai lokacin DJ ya isar da saƙon shigowan ango da amaryah, dole suka tsagaita da iskancin dariyan nasu muka maida hankalin mu kansu, ango da amaryah ne a gaba, bayan amaryah jerin friends ɗinta ne, bayan ango ma jerin friends ɗinshi ne, wato ko wani aboki yana jere da ango. Sulaiman da yusuf sune asalin abokan yayah Ahmad wanda suka taso tare tun primary, kuma an taso dasu anguwa ɗaya, da babu abunda yake rabasu dare da rana, yanzu ne kowa aiki ya banbanta musu garin zama, sai haɗuwan su ba irin da ba, sulaiman da yusuf duk sunyi aure kusan shekaru biyu baya, saboda auren su babu nisa a tsakani, kuma ko yanzu sune jagaba a hidiman, don bayan ango sulaiman ne, sai A.G, bayan A.G kuma yusuf ne, sai wani abokin shi nura babah, sai M.G sai wasu da bawani zuwa sosai sukeyi ba, ido na yana kansu har suka ƙarasa wurin zaman su, gaskiya matar yayah Ahmad mai kyau ce masha Allah na faɗa a zuciyana, high table ɗin ango ne kawai da amaryah a zaune, suna rakasu suka koma wurin zamansu suka zauna, gefe ɗaya amare ɗaya gefen angwaye.
Babu ɓata lokaci aka fara programm ɗin, inda aka ƙira babban yayah mohd ya buɗe taro da Addu'a, sannan aka ƙira babban abokin ango wato sulaiman ya bada tarihin ango, abun gwanin burgewa ya bada tarihin shi cike da burgewa da ilimi, yana gamawa wuri ya kaure da tafi, da yake saida ya gama yi mishi iya shege a ƙarshe wanda yasaka kowa a hall ɗin darawa, ina ganin yayah Ahmad bini-bini yana sunkuyawa kunnen amaryah yana mata magana, gaba ɗaya mamakin shi ya cika ni, dama yana sakewa haka? Sai wani murmushi yakeyi wanda yaƙi barin fuskan shi, bayan ƙawar amaryah ta bada tarihin ƙawarta sai aka fara abun da ya tara kowa, fili aka baje wa ango da amaryah domin rawa, fitowar su aka saka musu waƙan *ALI JITA* na amaryah da ango, haba zokiga abokan ango yadda suke baza naira kaman basu so, ina hango Nura Baba sai naji ɗan tausayin shi, domin yanuna yana son habiba har yayiwa yayah Ahmad magana lokacin zamu fara rubuta exams na SSCE, sai yayah yace yayi wuri yayi maganan ya bari sai ta shiga university, shima lokacin yana shirin tafi UK masters ɗin shi, har Yaya Ahmad ya ƙirani agaban Nura Baba ya tambayeni akwai wanda habiba take kulawa ne ko sukayi maganan aure da shi, a lokacin nace mishi bamu kula kowa dukkan mu, ya juya ya kalli Nura yace kaji abunda nagaya maka ko? Yaran nan basu fara zance ba, amma insha Allahu na maka alƙawari suna farawa zan maka magana, Nura ustaz ne shi ɗan sarauta ne me kuma sanin ya kamata, yana da kirki da zumunci sosai, kallo na yayi yace, "sister amana yana hannun ki, ki kula da ita kada kibarta ta kula kowa, ke kuma nasan gudumawanki na tsaro da zan baki," ya faɗa yana dariya ni da yayah Ahmad ma dariyan mukayi, sannan ya kwaɓe ni da kada nagaya mata, amsa mishi nayi akan bazan faɗa ba amma nasan bazan iya riƙewa ba, a wurin na tafi na barsu suna ta zanta maganan tafiyan Nuran, sai da mukazo kwanciya bana mantawa ina ta kallon habiba da take gyara mana wurin kwanciya ni kuma ina shiryah mana books ɗin da mukayi karatu ina ta murmushi, gajjiya tayi da kallon da nake mata tace, "sisto akwai wani jarida ne kam"? Dariya na kwashe da shi nace, " amanatul amana, azabatul axaba, dariya muka kwashe da shi don tare muka ƙarasa faɗa, yawanci idan ɗaya zatayi wa ɗaya gulman da aka kwaɓeta haka mukeyi, kamo hannu na tayi muka koma bakin gadon muka zauna, Bayani dallah -dallah na mata, ina gama gaya mata ta wani zaburo ta dafah ƙirji tace, "ustaz nura baba"? Ɗaga kai nayi alaman ehh, fuskana ɗauke da murmushi, rungume ni tayi tace , "Alhmdllh sisto, gaskiya naji daɗin wannan jaridan, kuma nutsuwar shi yana burgeni, matsalar ɗaya ne, ni guntuwa shi guntu, amma duk da haka babu matsala yaran zasuyi kyau masha Allah, kinsan ni bana son farin mutum, gashi nuru ba fari bane irin kalan mijin da nake so", hararan ta nayi cikin wasa nace , "yarinya baki da wayo, ae farin mutum duniya ne, yarinya miji ya tashi a bacci kiga farin jiki ae duniya ne, amma baƙin fata nayi juyi cikin dare nayi arba da baƙar cinya ae razana zanyi", na faɗa muna kwashewa da dariya, habiba ta kaimun duka a cinya.
Lokaci guda naji kewan habiba yazo mun, abun yana mun ciwo yanzu duk irin wannan ƙauna da shaƙuwan da yake tsakanin mu habiba ta yarda akan namiji muka rabu? Muryan maryan naji akaina tana cewa, "ke matar farare ana ƙiran familyn ango a fili, ke kuma kin tafi duniyan tunanin waye dai a ciki oho", ta ƙarasa faɗa tana dariya, hararan ta nayi na miƙe domin muje filin, don gaba ɗaya idon yayah umar yana kaina, ina cewa bazan fito ba zaizo inda nake, dama yayi mun warning agida, ko bazanyi rawa ba ya ganni a fili.
Muna fitowa aka sako mana waƙan Ali jita, haba zokiga su fatima da su hafsy, maryam ummitah, hadiza yadda suke chashewa, Aunty b sai chashewa takeyi yayah mohd yana dubanta fuska ɗauke da murmushi, liƙi yafara kaman ba gobe, dangin mu na gefen ummi da Abba duk sun fito, fili ya kachame da ruwan kuɗi, ballan tana da yayah umar da yayah ishaq suka kamo hannun ango suna liƙa mishi kuɗi suka shigo da shi fili, ae gaba ɗaya abun sai ya baɗa cittah da unga, Aunty Asma'u, Adda, Aunty b da mu duka muka fara mishi liƙi, yayah umar ya riƙe hannun shi yana rawa, abun mamaki dayawa kawai sai ga yayah Ahmad yana wani chashe rawa, ae dukkan mu muka hau ihu ana liƙa mishi kuɗi, Yayah mohd yana dariya ya jawu su dukkan su ya rungumesu, muma mukaje muka rungumesu nida hafsy, *AUNTY NICE* sai da naji hawaye yazo mun alokacin, domin yadda naga wani farin ciki da ƙaunan juna a fuskan mu duka, Aunty B sai video take mana ita dasu maryam da su ummitah, domin hattah hadiza da zainab yayah mohd ya rungumu su, Adda har wahaye ta fara lokacin da yayah Ahmad ya riƙo ta ita da Aunty ma'u yana rawa da su, kai zumunci akwai daɗi, Allah ka ƙara haɗa kanmu baki ɗaya, haka muka cinye lokacin mu kowa ta koma wurin zama, anan DJ ya sake gayyati familyn amarya, suma suka fita suka chashe nasu.