Ana barin halal original by anty nice - Chapter 7
Ana barin halal original by anty nice Chapter 7: Ana barin halal original by anty nice Chapter 7. Haɗuwa iya haɗuwa wurin programm ɗin Aunty Jeedah yayi…
4,350 words
Haɗuwa iya haɗuwa wurin programm ɗin Aunty Jeedah yayi kyau, don komai akace da ƴan boko babu bakin magana, hidima iya hidima anyi shi, gayu iya gayu mun ganshi, Aunty jeedah ƴar'gayu ce mai amsa sunan gayu na na'am, kuma ita ma babu laifi kyakkyawace ajin farko, amma dai bata kai Aunty Bintu ba, sai dai ta nunawa Aunty bintu gayu, duk da Aunty bintu babu wasa, sai dai ita Aunty jeeddah irin first class ƴan gayun nan ne, nidai farin ciki nakeji ganin matan yayu na duk babu na zubarwa, a zuciyana addu'a nake Allah yasa itama ta zama mai kirki irin Aunty bintu, domin Aunty bintu irin matan nan ne da samun su a cikin al'ummah sai an sha wahala, zuciyarta mai kyau ne, gashi suna zaune lpy da yayah mohd. Muryan DJ ne ya karaɗe wurin da neman dangin ango, haka muka taso da ƴan'uwan ummie, Abbah da mu ƴan gidan mu muka shiga filli, Aunty bintu Aunty Rakiya, Adda, Aunty asma'u, da wata ƴar ƙanwar maman mu Aunty halima suka taso a manya suka fara mana liƙin kuɗi na gasken gaske, kowa ka gani kwance bounch kawai takeyi tana liƙi, ganin hafsy nayi tana liƙi da ƴan 100 ɗinta, sai lokacin na tuna danawa, haka muka shiga liƙawa juna cike da farin ciki, daga nan kowa taje ta zauna. Bayan ƙawayen amarya sun chashe sai DJ ya sake fito da amaryah tsakiyan fili, gayyatan ƴan'uwan ango yayi fili ds muzu mu fanshi amaryan mu, nan ma amaryah taga ruwan liƙi da muka fito muka mata, nidai ban ankara ba sai dana ƙarar da kuɗin jakana, kuma da na barshi hadda na wurin dinner na ajiye, saboda naji Ali jita zaizo, duk ɗaga idon da zanyi sai mun haɗa ido da amaryan mu, muna haɗa ido take aiko mun da murmushi, nima sai na mayar mata, Aunty Bintu na riƙe da hannunta suna rawa, Aunty Rakiya sai liƙa musu kuɗi sukeyi, gaskiya luyafan ya mun daɗi, sai bayan ishaa muka bar wurin, mun dawo gida bamu daɗe ba Aunty bintu ta kwashe mu duka har dasu ummitah da maryam mukayi gidan ta, dole sai driver ne ya ɗauko wasu, saboda akwai ƴan mata biyu da suka ƙaru ɗaya ƴar gidan Goggo ce ƙanwar ummi wato zainab, sai kuma hadiza ƴar ƙanin baban mu ne daga tafawa ɓalewa tazo, hadiza tana B.U.K tana karanta Accounting, itama ƴar gayu ne sosai, ga rawan kai, amma kuma tana da kirki da son zumunci, idan munje garinmu a ɗakin mamanta muke sauƙa, zainab kuma ƴar Goggo tana kashere, chan Gombe state, zainab bata cika son mutane ba kuma bata cika yawan magana ba, so ita zaiyi wuya ma ka ganta cikin mutane saidai irin haka ya faru kaman lokacin biki, gara ma yayarta Nanah mai sunan ummin mu, ita tana da son mutane sosai, yanzu ma bata da lafiya ne da nasan komai da ita za'ayi.
Gidan Yayah mohd flat uku ne dama a ciki yanzu an gyara na yayah Ahmad inda za'a saka amaryar shi, duk da Abujah zasu zauna amma nan za'a kawota, kai mutanen nan sun wuce reni, nan gidan ma sun jere mata shi, haka gidan dayake Abujan ma an jere shi, gidan dayake farkon shigowa shine aka barwa Yayah umar, na tsakiya kuma yayah mohd, wanda yake ƙarshe shine na yayah Ahmad, mun shigo bamu daɗe ba yayah Ahmad da yayah mohd suka shigo gidan, a parlor suka zauna suna hira, Aunty bintu macece mai himman gaske, gata da iya kula da miji, abun ya ban mamaki da naga ashe sai da tayi abinci tukun ta fita, haka ta haɗa abincin ta saka hafsy da ummita suka wuce da shi dinning wasu yayah, gidan kana shiga parlorn yayah ne da dinning section sai ɗakin shi toilet a ciki, sai kuma guest room a parlon shima haɗe da toilet, sai kabi wani ɗan corido da zai shigar da kai wani ɗan madaidaicin parlor mai ɗauke da ɗakuna biyu, shima ko wanne da toilet a ciki, shine side ɗin Aunty bintu, kuma ko wani side haka yake, gidan babu laifi yayi kyau sosai,ballantana da tasamu kayan kece raini. Parlon muka shigo dukkan mu muka gaishe su, Yayah mohd na zolayan hadiza akan sunyi waya da bappanmu wai yayi mata cikiyan miji a birni ta bar ƙauye, da yake bakinta baya shiru haka ta dinga maida mishi amsan da ae shi tazaɓa, saboda haka ya bawa bappah amsan ta samu wuri, idan kuma bashi iyawa ga yayah Ahmad, shidai yayah Ahmad murmushi kawai yakeyi, haka tayi ta zolayan su shida yayah Ahmad, amma yayah mohd kaɗai ke maida mata amsa Aunty bintu na taya shi, yayah Ahmad dai sai murmushi yake yi baya iya cewa komai, ko ta tsokano shi sai dai yace ta jira Jeeddah shi tafi ƙarfin shi, zainab dai sai kallo ta ke binsu da shi kaman ba abokan wasanta ba, bayan sun gama chakalan junan su sai suka koma ciki, Aunty bintu kawai aka bari a wurin sai ni da naje kusa da yayah mohd na zauna, hannun shi na riƙo ina dariya, shima dariyan ya fara yana, "akwai abunda bestyn yayah moh takeda buƙata kenan, dariya na sakeyi ina ƙara riƙo hannun shi, "yayah duk duniya kaida ummie kuna saurin ganoni, narasa sanin dalili", na faɗa ina dariya, Aunty bintu ne ta bani amsa itama tana dariyan mu, "saboda duk duniya sun fi kowa sonki, shiyasa kowani language naki suke ganewa", ɗago ido yayah Ahmaɗ yayi yana dubanta, kaman baxai buɗe baki ba, amma sai naga kaman bashi ba yace, "banda son kai matar yayah, nasu ne ya bayyana, amma ni son da nakeyiwa Ayshaa sai inaga kaman yafi son da uwa takeyiwa ɗanta, saboda ko jeeddah ta gane, idan nayi fushi tou hiran Ayshaa take mun na sauƙo, duk abunda yake saka ni farin ciki kawai na ganta tana annashuwa", ya faɗa yana maida kallon shi kaina, da sauri na sake hannun yayah mohd na koma jikin yayah Ahmad na kwantar da kaina a kafaɗan shi, a hankali nace yayah Ahmad baka taɓa gaya mun ba, sai dai abunda kullum nake tunani a raina shin acikin ku ni waya fi nuna mun so da kulawa ne? Sai na ga kowa yana sona, kaga yayah mohd na shaƙu da shi kuma bana iya ɓoye mishi komai na, kuma sai inaga shine yake bani solution na kowani abu da ya sha mun kai, kuma yana son farin cikina, kai kuma Yayah Ahmad kasan me nakeji akanka?" girgiza kai yayi alaman bai sani ba, riƙo hannun shi nayi nace, "duka rauni na yana kanka, haka kawai zuciyata take jin tausayinka ko shiru kayi sai na dinga jin babu daɗi, kuma duk ranan da kazo sai naji tou gidan ya cika, duk abun da yayi giɓi a gidan ya cika," "ni kuma duk wanda naga zai tayar miki hankali ko zai taɓaki sai na rushe duniyar shi gaba ɗaya, duk wanda ya taɓa mun ke zan tada ƙaramar yaƙin ƙare dangin shi duka", yayah umar ya faɗa yana shigowa cikin parlon shida hussainin shi yayah ishaq, dariya dukkan mu parlon muka kwashe da shi, da gudu naje na rungume shi ina dariya, "yayah umar nasan kana sona, ni ma ina sonka, amma kai kana mun tsawa wataran har sai nace kodai ba yayah umar ɗina bane" dariya yayi yana riƙe dani muka zauna, " bazaki gane bane Ayshaata, ina miki faɗa wataran don wancan autar ummi marar jin maganan, laifinta ne yawanci yake shafanta, amma daga Abba, Ummi, yayah mohd, yayah Ahmad, fitinanniyar ɗakin mu, duk babu wanda yakaini sonki", ya faɗa yana duban yayah ishaq da yake binshi da harara, shi kuma yayah umar yana mishi dariyar mugunta. Shigowar hafsy da zunɓurarren baki a gaba ya sake bawa kowa dake parlon dariya, gefen Aunty bintu taje ta rakuɓe tana turo baki gaba tace, "Adda duk wannan son da suke faɗa miki suna miki duk abakine, ni nawa bazai faɗuba, ni nawa da nake miki baxai misaltu ba, har abada har gaban abadah baxan so abu kwatankwacin irin kiba a duniya, ni ko ummi da Abba bana jin ina da kusanci dasu sama da ke, ko ƴaƴan da zan haifa suyi haƙuri su biyo bayanki Adda, ballantana kuma miji, sorry ɗinshi" ta ƙarasa tana hararan yayah ishaq, murmushi yayi ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana danne-danne a jikin wayan shi. Gaba ɗaya hira muka kachame da shi, kaman ba jiran yayah Ahmad abokanshi sukeyi ba, sai da yaga wayan su yayi yawa tukun ya mana sallama ya tashi zaifita, lokacinne yayah mohd yake tambaya na meye nake so? "kuɗin liƙi yayah zaka ƙara mun, nawa duk na ƙarar a wurin event ɗin yau, gashi akwai dinner". Ɗan dawowa da baya yayah Ahmad yayi yace, "ki bar yayah moha, goben kituna mun na baki ko", godiya nafara mishi bai saurare ni ba yayi waje, harara na hafsy tayi," wallahi Adda duk kuɗin da aka baki sai mun raba, wannan ae wayo ne, sai ki lallaɓa kowa komai sai ke, tou ni ɗin da babu mai sona sai an bani", dariyar ta kowa yakeyi, Aunty bintu tace kada kiji komai ke baga ishaq ba ae kece favourite sister shi, kema kina da wanda ya damu dake over, kuma gani nan nima ke nafi so", Turo baki hafsy ra sakeyi tace, "haba Aunty bintu nafasan gaskiya, Adda kema kika fi so, ina jinki fa ranan kikace Adda duk tafi mu kyau saboda tana kama da mijinki, wai har baki gajjiya da kallonta, wato nice mummunar wanda ake gajjiya da kallona? Daɗinta ma da Abba da Aunty Rakiya nake kama, kuma ina isar musu da saƙo za'a samu matsala da kowa, ni yanzu bandamu da ku soni ba bari na jira zuwan matar yayah Ahmad, naga ko ni zata kama? Idan kuma takama mai ƙwala-ƙwalan idon nan sai najira ta yayah umar da haƙuri, don ita kam nasan nice overoll" ta faɗa tana kallon yayah umar tana dariyan shaƙiyanci, dariya dukkan mu mukeyi, shidai yayah ishaq hararanta yake tayi, wanda narasa na menene, " Haka mukai ta hira har saida yayah mohd ya bar parlon, yana tafiya Aunty bintu ta wuce kitchen, kallo na yayah ishaq yayi yace, "tou ae sai ki tashi ki koma ciki mai masoya da yawa, amma nidai ki sani favourite ɗina hafsy ce, duk da ma yanzu ta gama yaɓa mini baƙaƙen magana, wai nine na ƙarshe acikin wanda zata so, hala har da wannan ƙaton banzan yayantan", ya faɗa yana kai naushi wa yayah umar, nidai banbi takansu ba saboda nagane inda zance ya dosa, kawai miƙewa nayi nayi hanyan ɗakin Aunty bintu, ina kusa da shiga naji yayah umar yana ƴar'uwa ki turo mun ummitah plz, mirmushi kawai nayi na wuce ciki, babu daɗewa kowa ummitah ta fito parlon, kafin nan kuma yayah umar ya koma kan dinning yana jiranta, ina shiga ɗakin na kalli su maryam nace, "gara fah muma muyi takanmu mu samu abokanan rayuwa, don idan muka zauna ta boko tou zamu raka ummitah da hafsy ɗakin aure". Wani fari da ido hadiza tayi tana wani juya jiki tace, "ke kenan da kika zauna zaman jira, ni dai akwai wani ɗan unguwan mu suraj, yana aiki yanzu da NNPC, shima yace mun yasan Yayah mohd suna tare a lagos amma yayah seniour shine, tou nidai zanyi wuff da shi, don insha Allah shekaran nan da zamu shiga zasu zo suyi gaisuwa", ta faɗa tana wani jujjuya jiki tana saka kayan baccin ta, kallonta kawai nayi ina dariya, na juya kan zainab nace ƴar'uwa kefa? Harara ta mun tace, "sai kin samo na karɓa irin na habiba," dariya muka kwashe da shi, na juyawa wurin fatima nace,"kefa sis", Itama dariyan tayi tace, "ni yanzu akwai wanda ya mun magana, amma baya ƙasan yana masters a London, yayan ƙawata ce, sunan shi kabir ɗan maiduguri ne shuwa ne shima, sai kumun addu'a Allah ya dawo da shi lpy," tafi dukkan mukayi muna mata guɗa, kallon maryam nayi nace "besty yyh ke kuma ina muka dosa"? Murmushi tayi tace nidai besty gamu nan muna addu'a, ina ga wannan lokacin sai mundage kada yaran nan su bamu kunya, don naga har ƴan aika muka zama musu, ni ae bansan yayah umar me yake tafiya ba, jiya fah aikana yayi na ƙirata", dariya muka kwashe da shi nace nima baka shi yanzu ya aiko ni ba, kawai besty muma mu dage mu samu wanda zamuyi wuff da shi. Muna gamawa muka fara tsara yadda zamu kwanta, nan ɗakin Aunty bintu akwai wani lazychair a ciki, kai na hau na kwanta, gadon kuma hadiza, maryam da zainab zasu kwanta, ɗayan ɗakin da yake gefe inda fatima suke sauƙa tace zasu kwanta ita da hafsy da ummitah, haka mukayi sallama kowa ta kama wurin kwanciyarta, ina rufe ido sai tunanin fararen nan ya faɗo mun a zuciyata, da sauri na buɗe ido na, ganin an kashe wuta sai na mayar da idon na rufe.
Washegari muna tashi muka raba kan mu, wasu sukahau gyaran gidan, wasu suka fara haɗa abun karyawa, muna gamawa kowa ta shiga wanka, wajajen ƙarfe 12:00pm muna shirin fita zuwa chan gida, a haraban gidan muna tsaye muna jiran fitowan Aunty bintu sai ga motan yayah Ahmad ta kunno kai, yana fitowa lokacin Aunty bintu ma tafito daga nata gidan, "yauwa Alhmdllh ga ango ma ya shigo sai ya rage wasu tunda har yanzu drivern bai zo ba", Aunty bintu ta faɗa tana gyara yafan gyalenta, yana fitowa ɗayan side ɗin ma aka buɗe sai ga M.G ya fito shima, yana rufe motan kowa ya ƙaraso inda muke, gaida Aunty bintu yayi tana tsokanan shi da ango kasha ƙamshi, shidai murmushi kawai yake bai bata amsa ba, sai hannu da ya miƙa ya amshi Areefh da yake hannun hafsy, wasa ya mishi yana ta ɓangala mishi dariya, sannan ya miƙawa hafsy yaron, mu kuma muka shiga gaishesu shida M.G, gaba ɗaya idon M.G yana kaina fuskan shi ɗauke da murmushi, Aunty bintu ta tambayi yayah Ahmad akan daga nan gida zai wuce? Ya amsa mata da ehh, yanzu ma yazo duba ac da aka chanja na ɗakin shine, yana so yaga ko sunyi yadda yake so, "tou shikenan bari mu baka mutum uku, dama driver muke jira, naga kuma ya ɓata mana lokaci tun ɗazu yake cewa zai fito ya kai aika ne," riƙo hannu na yayi muka fara tafiya chan side ɗinshin, yana amsawa Aunty Bintu da babu komai sai a bar mutum uku, bari ya duba ya fito, Aunty b tace "tou maryam da hadiza kujira Aysha sai ku taho ku uku, fatima, zainab, hafsy, ummitah ku kuma ku shiga mutafi, uku a baya ɗaya a gaba," Ɗaga muryah hafsy tayi da ƙarfi tana "wlh yaya duk abunda ka bata nima sai an bani, don na lura da wayon da ake mun, kai da yayah mohd kowa ya samo sai ya yafito ta, yayah umar ne kawai mai tunawa da ni", tana gama faɗa ta wuce gaban motan da sauri don taga zainab tayi gaban zata shiga, anan ma sai da suka yi ɗan hali da zainab, tace dole hafsy ta koma baya ae itace babbah, amma firr hafsy taƙi fita, tana cewa ae ita tana riƙe da yaro a hannunta, ganin Aunty B bazatace komai ba yasa zainab shiga gaban ta wani ɗaure fuska kaman....., ita dai fatima dariya takeyi ƙasa-ƙasa, gefe ɗaya maryam da hadiza suka koma suna jiran mu fito.
Muna shiga side ɗin yayah Ahmad na wangale baki, domin suna gama jeren babu wanda yazo a cikin mu, Aunty ma'u ne ma naji suna hiran haɗuwa da tsaruwan gidan, haka yayah Ahmad ya zaga dani ko ina na cikin gida, "kai gidan nan yayi kya yayah, gashi kuma ba'a nan zaku zauna ba, ae da Abujan aka kai kayan nan", na faɗa hannu na riƙe cikin nashi muna fitowa daga kitchen ɗin, dariya yayi mai ɗan sauti yace, "shatu na ae kayan da suka saka a abujan yafi wannan tsari da haɗuwa, nan kawai sunfi zuba kaya mai yawa ne, chan kuma 2bed room ne 1 parlor, amma chan ae yafi kyau, komai white aka saka achan, ɗayan ɗakin ne ma suka saka Brown bed, amma parlor da nawa room ɗin komai white ne," yayah nikan gidan nan ya mun kyau irin sosai ɗinnan, kuma ya dace da kai yayah nah", na faɗa ina kallon fuskan shi, murmushi yayi kawai, M.G ne ya bani amsa da , "sister naga alaman irin wannan kayan zamu saka miki ko? Tou kiyi gaggawan kawo mana suruki idan kina soa miki irin wannan kayan", ya faɗa yana bina da kallo fuskan shi ɗauke da murmushi, saida naji faɗuwar gaba mai ƙarfin gaske lokacin da muka haɗa ido da shi, domin wani irin kyau yake da shi kaman wani india, gashi fara'a da murmushin fuskan shi yana ƙara mishi kyau na sosai sosai ɗinnan, don na lura kaman yasan fara'an na ƙara mishi kyau shiyasa yake yawan yi, gashi da wani dogon hanci da wasu manya - manyan idon shi masu masifar haske, abunda na lura yafi A.G manyan ido da dogon hanci, shi kuma A.G idon shi basu da girma sosai kuma basu da ƙanƙanci, sai dai sukuma round ne su masu yawan gashi ido da gashin gira, gashi na lura hancin bamai tsayi bane irin na M.G, sai dai suna da masifan kyau, kuma shi bai cika buɗe idon shi waral ba, yana ɗan lumshe su kaman yana tsoron wani abu ya faɗa mishi, sannan yafi tsayi kaɗan kuma bai kai M.G jiki ba, dukkan su dogaye ne, amma A.G yafi tsayi kuma yafi haske, M.G yafi kyau amma ba lokaci ɗaya zaka fahimci hakan ba, saboda farinsu da tsayin su yasa har ake ganin kaman suna kama, amma ni ranan ƙasa - ƙasa na ƙare musu kallo har na fahimci abunda mutane da yawa basu fahimta ba, yana faɗin haka na rufe ido na a jikin yayah Ahmad, dukkan su dariya sukayi, yayah Ahmad yace, "ayshaa tana kula samari ne ma, ae inaga bata ma kula su, amma duk ranan da ta kawo mun miji insha Allahu kayan da zamu saka mata sai yafi wannan burgewa da kyau", murmushi nayi ina kallon yayah Ahmad ina jin wani farin ciki a zuciyata da Allah ya bani yayun da suke sona, buɗe baki M.G yayi cike da neman zolaya yace, "waya gaya maka mai kyau bata da samari? ae Allah kaɗai yasan yawan su, ta ɓoye maka ne, amma ni zamuyi labule nasan duk zata lissafo min su, ni kuma sai na tantance na zaɓa mata guda ɗaya gwani", ya faɗa still idon shi yana kaina, nidai juyawa nayi nabar parlon ina jin dariyan su. Shigan mu gidan muka tarar da A.G tsaye da wasu abokan su guda uku a ƙofan side ɗin su yayah Ahmad, shi dai yana gefe yana waya, amma tunda mukayi parking muka fito ya maida kanshi kanmu, ƙura mana ido yayi kaman ranan yafara ganin mu, ganin yana wuya sai niyyan wucewa batare dana gaishe shi ba, amma na gaida sauran abokan yayan, don wasu ma sun ƙara fitowa, na juya naji muryan shi ƙasa - ƙasa yace, " Zonan" kaman zan nuna banji ba sai naji ya sake cewa, "ba ƙiranki nakeyi ba"? Da sauri na ƙaraso inda yake, bai cire wayan a kunnen shi ba naga ya wuce wurin motan shi bayan ya mun alaman na biyo shi, haka na juya na bi bayan shi jiki a sanyaye, boot ɗinshi naga ya buɗe yasaka hannu cikin wani jaka bayan ya zuge ziff ɗin jakan ya ɗauko wani envelope, miƙo mun yayi batare da ya cire wayan a kunnen shi ba, hannu biyu na saka na karɓa ina bin shi da kallon neman ƙarin bayani, "na dinner kiyi amfani da shi" yana faɗa bai sake bi ta kaina ba ya wuce inda su yayah suke, ko godiya ban samu daman yiba ya wuce, na juya sai naga idon M.G akan mu, ganin haka sai na fasa zuwa nayi godiyan kawai nayi cikin gida.
Ina shiga ɗakin ummie nah na wuce, tun a parlor na fara gaida mutane, a nan naga su Aunty b da su Aunty asma'u zaune, ummitah da maryam kuma sun fito zasuyi gidan su, nan maryam tace mun sai anjuma zasu shigo, ɗaga mata kai nayi don nasan ƙarya takeyi don tace bazata zo gayyan soɗiba, don habiba har yau bata ce mata komai ba, ko a group da jammy tayi magana bikin habiba bata ce komai ba, daga baya ma sai mukaga tayi left a group ɗin, nan kuwa jammy tafara masifa da kyar na danne ta, murmushi nayi kawai na matsa mata ta wuce, daga nan nayi ɗakin ummie na, dayake safiya ne su huɗu ne kawai a ɗakin daga ummi da goggo sai ƙawayen ummie guda biyu, gefen goggo kuma zainab ce ke zaune suna magana ƙasa-ƙasa, bayan na gaishe su na wuce wurin ummie, zama nayi a gefenta na gaishe ta, na miƙa mata envelope ɗin hannu na,ƙasa-ƙasa nake mata bayanin abokin yayah Ahmed ne ya bani wai na liƙi a wurin dinner, karɓa tayi ta buɗe, da sauri ta ɗago ta dubeni tace, "Ayshaa nasan bazaki roƙe shi ba amma meyasa zai baki kuɗi masu yawa haka, 100k ne fah ƴan 500, bounch 2, yayi yawa ae, kuma haka kawai ya baki"? Ta faɗa tana jawo wayanta, ni dai bance komai jin tana ƙiran yayah Ahmad yazo ya sameta a ɗakin mu, daga nan babu ɓata lokaci ta miƙe tace na biyota, muna shiga kowa sai ga yayah Ahmad ɗin ya shigo, dama muna shiga ta sallami su hafsy waje, ummie nuna mishi kuɗin tayi tana mishi bayanin wai abokin shine ya bani, murmushi yayi yace, "ummie A.G ne, zai bada abunda yafi haka ma, nima inayiwa ƙannen shi, wannan kuma ba wani abu bane a wurin shi, inaga jiya ne dana basu kuɗin liƙi sai M.G ya ƙara mata, shi a lokacin babu mint a jikin shi sai da muka bar wurin ya mun maganan na tuna mishi idan ya shigo ya bata nashi, nasan kuma shi nashi bugun girmane, ummie inaga babu komai rabonta ne", "Tou kayi musu godiya dukkan su, kuma gaskiya kuɗin sunyi yawa tayi liƙi da su, ta ɗauki 20k kawai a ajiye sauran", murmushi yayah Ahmad yayi yace, "haba ummie shi da yabata 100k ae yana so yaga ƙanwar shi tayi fitan manya ne, idan bazaki bata duka ba tou a bata 50k, sai ki ajiye mata sauran, don naga hafsy umar da ishaq ke mata komai ko suma kamun ƙafa ne Allah ya sani" ya ƙarasa yana miƙewa, yana fita ummie ta dube ni, "saura ki bawa ƙawayenki da ƴan'uwanki labari, gama ke kanki baya saiti, ko hafsy kada naji labarin kin gaya mata, don magana ne da ita yanzu zata isar da shi", ummi nagama faɗa ta miƙe riƙe da envelope ɗin ta fita a ɗakin, nidai ajiyan zuciya na sauƙe na nemi wuri na zauna, ban daɗe ba saiga su fatima da hadiza sun shigo, hawa gadon kusa dani sukayi, hadiza ta miƙe kwance fatima kuma ta zauna a gefe na, "wurin habiba fah muka fito, tana ta tambayanki, mukace kina ciki, duk tayi wani iri da ita," inji hadiza, daga gefe kuma fatima tace, "duk haushinta da nakeji sai kuma ta bani tausayi, duk ta damu sai tambayanki takeyi, chan kuma sai hawaye yazo mata gashi ana mata make-up, da ƙyar ta tsayar da hawayen, shima sai da wannan ƴar yayar mamien sun tace zata haɗata da mamie tukun tayi shiru, ganin banzan kallon da ƴan'uwan da ƙawayenta kemana ne yasa muka fito", duk sai naji babu daɗi a zuciyata, tunani na komai yake damunta? Duk sai naji babu daɗi, tagumi nayi ina kallon su, sai ga hafsy ta shigo tana tambayana ina waya na? Yayah Ahmad yana ƙirana, da sauri na buɗe handbag ɗina na ciro wayan da na saka shi a silent, ina fitowa da shi ƙiranshi yana sake shigowa,, da wuri na ɗauka "Ayshaa kizo M.G nason ganinki, kiyi sauri fita zamuyi", Ina gama jin abunda ya faɗa nayi sauri na miƙe don naje ƙiran.
Ina fitowa nagan su dukkan su a waje, wasu sun shiga motocin su wasu suna tsatstsaye suna magana, hango M.G nayi tsaye a jikin motan su, wanda bansan wannene nashi ba wannene na A.G, wataran nakan gansu a Red, wataran a Black, so bansan nawaye a ciki ba, ƙarasawa nayi wurin shi bakina ɗauke da sallama, ɗago kansa yayi daga danna wayan da yakeyi ya sauƙe mun idon shi a kaina, abun mamaki yau babu wannan fara'an da yake fuskan shi, "meye schedules ɗinki na yau"? ya tambaye ni idon yana kaina, ɗan juya idona nayi sannan nabashi amsa da, "yanzu dai babu komai, sai zuwa anjima muna da liyafa da za'ayi acikin gidan nan," ina faɗa ido na yana kan masu decorating wurin, shima maida idon shi yayi wurin, muryan shi chan ƙasa yace, " barrister yace mun tare aka haife ku da amaryar, itace wannan twin sister ki da muka taɓa ganinku tare ko"? Murmishi nayi ina ɗaga mishi kai alaman hakan ne, ƙura mun ido yayi har sai da naji kunyan shi na sunkuyar da kaina ƙasa ina wasa da gyale na, kaman bazai sake magana ba sai kuma chan yace, "saura ke kenan, fatan dai bazai ɗauki wani lokaci ba zamuji kyakkkyawan labari"? Ɗan juyar da kaina nayi gefe ina murmushi, bance komai ba haka shima bai sake ce komai, amma idon shi yana kaina, chan na hango Yayah Ahmad da A.G suna tahowa wurin mu, a hankali na juyar da kaina ina kallon M.G nace, " yayah yace nazo kana ƙirana", wayan shi ya miƙo mun yace, "saka mun number ki zamuyi magana daga baya" Hannu na saka na karɓi wayan nasaka mishi number na, ina miƙa mishi su Yayah Ahmad suna ƙarasowa wurin, wani kallo mai kama da harara naga A.G yayi mun sannan ya kawar da kanshi ya shige motan ta side ɗin mai zaman banza, sallama na musu bayan yayah Ahmad yace zuwa dare idan an watse na dafa mishi ruwan tea.