Kenza eBookz

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 6

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 6

Ana barin halal original by anty nice Chapter 6: Ana barin halal original by anty nice Chapter 6. Ranan saturday da safe wurin 11:00am na fito da coolern…

4,116 words

Ranan saturday da safe wurin 11:00am na fito da coolern da ummie ta sakawa yayah Ahmad masan da tayi tun safe na kai mishi side ɗin su, a cikin kwando na haɗa komai na wuce side ɗin su, ina fitowa naga wata arnen mota ja a ƙofan su, a zuciyata nace ɗan gayun gidan mu ya chanja mota ne? Yaushe naji ummie na mishi faɗan yawan chanja mota da yakeyi, ina ƙara matsowa varander sai naga takalma kusan kala uku, a zuciya na nace tou hala ba motan shi bane, sallama nayi a bakin ƙofan, sau biyu nayi tukun aka amsa mun, yayah Ahmad ne ya amsa mun sannan ya bani izinin shigowa, buɗe ƙofan nayi na shigo ina ƙara wani sallaman, ban ƙarasa ƙarshe ba na yanke sallaman ya koma ciki, ido na ɗan zaro kaɗan...sai kuma nayi saurin maida nutsuwan jikina dai-dai, ganin ina shirin sake abun hannu na, "*AUNTY NICE* kin san suwa nagani a zaune?" kallonta nayi fuskana ɗauke da murmushi nace "a'a sai kin gaya mun hajjaju", Wani fari da ido tayi fuskan ta ɗauke da murmushi da wani yangan ta da take burgeni da shi, "Fararen nan nagani zaune a parlon".

Ina ajiye basket ɗin na sunkuya har ƙasa na gaishe su, bansan dalili ba sai na ji muryah na yana rawa, amsa mun gaisuwan sukayi amma ɗayan wanda naga kaman yafi tsayi kuma bai kai ɗaya jiki ba, lpy kawai yace ya maida kanshi kan wayan shi, ɗayan kuma wanda naga alaman yana ɗan jiki kuma yana da yawan fara'a, shi ya amsa mun fuskan shi kuma a sake, har ma ya tambaye ni suna, bayan na gaya mishi ya sake tambaya na s.s nawa nake? Nagaya mishi ina A.T.B.U zamu shiga level 2 next semester, zaro ido yayi cike da zolaya yace, "ashe mun kusa mu fara tara surukai, ni na ɗauka baki gama secondry school ba, wancan zuwan naga kaman ku biyu ne kan ku ɗaya ko"? Ɗaga kaina nayi alaman haka ne, "tou ina ɗayar? Don naji Ahmad na ƙiranku twins, hakane?" nan ma murmushi nayi na sake ɗaga kaina alaman haka ne, dariya yayi mai ɗan sauti yace, "inaga kema irin yayan kine, magana yana baku wahala", "kai kuma babu abu mai sauƙi a wurinka irin magana" naji ɗayan farin ya faɗa, da sauri na ɗago ido na kalle shi, abun mamaki ko kallon mu baiyi ba yayi maganan, daga gefe kuwa yayah Ahmad yana murmushi yace, " Ayshaa idan kin shiga kicewa ummi su A.G zasu shigo su gaisheta idan mun gama", miƙewa nayi da sauri ina amsawa yayah da tou, shi kuma ɗaya mai yawan fara'an naji yana faɗin "haba Barrister muna ɗan labari kuma ka sallameta? Bayan nasan dukkan ku yanzu kowa zai rungumi waya yayi ta faman danne-danne ku bar ni shiru", "tashi kije ciki ki isar da saƙon ki, ki rabu da yayanki mai yawan maganan nan," naji muryan ɗayan farin ya faɗa, da sauri na ɗago dara-daran ido na nadube shi, cikin sa'a kuma shima idon shi na kaina, rikicewa naso yi wanda bansan dalili ba, da sauri nayi hanyan waje.

Wajajen shaɗaya da rabi naji muryan su yayah da abokanshi a parlon ummie suna gaisheta, haka nakasa kunne nake sauraron gaisuwan su, inda naji yayah yana ambatan A.G da kuma M.G, ƙasa-ƙasa nake jin muryan ɗayan wanda bansan ko shine A.G ɗin ko M.G ɗin ba yana mata godiyan masan da aka kai musu, daga baya naji muryan ɗaya mai yawan fara'an shima yana godiya, zasu fita naji muryan shi yana tambayan hafsy ni, sokuwa naji tana cewa kaman bacci nakeyi, naji kaman na garzayo da gudu nace gani, amma sai na daure na gayara kwanciya na, a zuciya nace maganin mai baccin ƙarya, ɗazu ina ji hafsy na ƙirana nayi likimo, basu fi minti biyar da fita ba naji muryan Yayah Ahmed a parlon, da sauri na dirƙo a gadon nayi parlon, fuskana a murtaƙe na nemi wuri kusa da shi na zauna, idon shi akaina yace, "fatan kina lafiya dai ko"? Ɗaga kai nayi alaman eh, "yau kina azumin magana ne? Har kin sa M.G ɗazu yana cewa halin mu ɗaya, saboda shi Allah yayi shi mai son hira, baya so yaji an zauna shiru, da badan A.G ya sallameki ba haka zai ta cika mutane da surutu", ya ƙarasa faɗa yana dariya, nima murmushi nayi nace, "su ɗin ƴan gida ɗaya ne yayah"? "maƙota ne kawai, amma sun dawo ƴan'uwan juna, kuma sai akayi dace sunan iyayen su yazo ɗaya", Ummi tace "gashi ni har kama ma suke mun, yanzu dama maƙwafta ne ba ƴangida ɗaya ba? Kasan kullum da kake bani labarin su tun kafin na gansu na ɗauka ƴan gida ɗaya ne", murmushi yayi yana ɗaukan ruwan da hafsy ta ajiye musu yana buɗe bottle ɗin, "wallahi ummi nima farkon haɗuwa na dasu na ɗauka ƴangida ɗaya ne, irin kowa da maman shin nan, kinsan a school of low muka haɗu da shi A.G ɗin, ummi bamu mintuna kaɗan zakiji ƙiran M.G ɗin yana tambayan lafiyan A.G ɗin, kin san A.G ɗin yana da athsmah, kuma lokacin kaman ya ɗan matsa mishi, duk hankalin M.G ɗin a tashe, daga baya A.G ɗin ya gaya mishi ya haɗu da wani ɗan bauchi kuma yana taimaka mishi wato ni, haka M.G ya matsa ya karɓi wayana, ƙira akai akai yaji yyh A.G yake, na ɗauka nima yayan shi ne, ashe maƙwaftah ne suka taso tare, don kinga M.G a gidan su A.G ma yake zama ɗakin shi a gidan shima aka mishi saboda abotakan su ya dawo....." bai ƙarasa ba muakji sallaman yayah umar, haushi naji na ɗan harare shi saboda ya yanke labarin da yayah Ahmad yake bamu don so nakeyi naji ƙarshen labarin, kuma sanin halin yayah Ahmed dama maganan ba damun shi tayi ba, irin haka kawai kake ɗan jin maganan shi, hakan ma sai idan akwai ummie ko Abbah ko yayah mohd a wurin, da gudu hafsy tayi wurin shi ta rungume shi tana mishi oyoyooo, dama ta hannun daman shi ne, hararah na yayi dole na tashi naje mishi oyoyoooo amma ya matsa gefe yana gwale ni, "sai da kika dama tukun kika wani kwaso tsumman ƙafan ki ko"? Tou bana so koma chan da munanan idon ki a wurin da ƙaton kai" dariya mai ɗan sauti hafsy tayi saboda daɗin an kushe ni, tsayawa nayi kaman zan mishi kuka baki na a zunɓure, juyawa nayi na kalli yayah Ahmad nace "ka ganshi ko yayah" Rungume ni naji yayi yana dariya yana faɗin "wane ni na gwale ki wanda tafi kowa kusa dani a duniya, kin san fah da tare ummie zata haife mu ke kuma Allah yayi ki mai sanyin jiki, shiyasa na fole ki da ƙafa kikayi baya na iso duniyan, tsabar sakarci da son jiki sai da kika ɗauki tsawon shekaru kina jinya kafin kika zo duniyan", ya faɗa yana dariya, gaba ɗaya su ummie ma dariyan sukeyi, sannan ya ƙarasa wurin yayah Ahmad ya ɗan sunkuya ya rungume shi yana yayah na rabin jiki na, yayah Ahmad yana murmushi yace, "kun iso lpy corpers?" yayah umar yana dariya yace, "yaya munyi passing out mun dawo kenan", ya faɗa yana wucewa wurin Ummie itama sunkuyawa yayi ya kwanta akan cinyanta yana, "Ummie na my first love na dawo na sameki lafiya cikin kwanciyar hankali, raina yayi daɗi" ya faɗa kaman yana wani ƙara rungumeta, domin gaskiya yayah umar shi yana da maƙon iyaye da ƴan'uwa, don zan iya ce miki duk cikin mu yafi irin nuna damuwa da nashi, shidai barshi da masifa da zafin zuciyan shi, amma yana nuna ma kowa so. Hafsy ne ta shiga kitchen ta haɗo mishi masa da kunun gyaɗan da ummie tayi, dama ummie ita bata abinci kaɗan takanyi wanda ko baƙo akayi babu batun jin kunya, babu daɗewa mamah ta shigo daidai nan yayah mohd ma ya shigo, haba gaba ɗaya sai aka kachema da hira, kowa kaman zai cinye ɗan'uwan shi don so, irin waƴan nan lokacin idan muka haɗu sai dai kaga ummie fuskanta kaman gonan auduga, ta juya kan wannan ta juya kan wannan, "Allah sarki ummin mu, gaskiya *Aunty nice* Allah yayi mana kyauta mai daraja da ya bamu ummie a matsayin uwa, macece mai tsoron Allah, Allah sarki ummin mu".

Sun kuyar da kai Hajiya Ayshaa tayi ƙasa tana share hawayen da ya biyo kan kyakkyawar fuskanta,nidai sai naji duk jikina yayi sanyi, na tsura mata ido a zuciyana nace, Allah yasa dai ummin nata na da rai, don ni nasan zafin mutuwar iyaye, uwa ko uba duk wanda ka rasa sai kaji kaman baka da sauran komai a cikin duniya. Ɗagowa tayi ta dubeni tana share hawayen ta, amma fuskanta cike da murmushi, nima murmushi na mayar mata, bayan ta gama goge fuskan ta ta ɗago ta kalle ni sannan ta cigaba da bani labarin ta. A irin wannan lokacin mamah takan zauna a side ɗin ummie, abun da na lura daɗi takeji idan ta ganmu dukkan mu a hallare, kuma sai kiga kowa a cikin mu yana nan-nan da ita, domin babu laifi mamah tana da zuciya mai kyau, kuma idan za'a wuni itama ranan ko abinci bata ɗaurawa anan take zama, saidai idan itace da girki zata tashi zuwa wani lokacin, sallan azahar da akayi ma zuwa sukayi sukayi sallan sannan suka dawo nan parlor, basu suka bar gidan ba sai bayan la'asar lokacin kowa yaci abinci sannan suka watse, ana sallan ishaa sai ga yayah umar da yayah ishaq aminin shi sun shigo, bayan sun gaida ummie basu wani zauna ba suka wuce chan side ɗin aminiyar su hajiya ummah, nan kuma hafsy ta bisu, domin na hannun damanta yayah ishaq yazo.

Washegari haka nayita kasa kunne naji yayah Ahmad yayi maganan su A.G amma shiru, nayita zura ido ko zanga sunzo, amma shiru babu ko gilmawar motan su, haka da yammah na wuce gidan su maryam, ina shiga ta taso da ihu ta rungume ni, maryam duk duniya idan kika cire habiba tou babu wanda yasan sirri na kuma nake iya gaya mata komai a rayuwata sai ita, ita jamilah abun da na lura wani irin so na Allah ya saka mata a zuciyarta, don gaskiya sun zaune sit ɗaya ne da habiba, amma don ta ita bataƙi dani take tare ba, don ni komai nayi dai-dai ne a wurinta, don har tsokanan ta sukeyi wataran wai mayyar Ayshaa, kuma bata gajjiya da kallo na, idan na kamata tana kallo na sai tayi murmushi tace, "Ayshaa duk duniya babu mai irin kyaunki, don ni da madkhuri kike mun kama, kyaunki yana da kyau sosai", nidai murmushi kawai nakeyi idan ta faɗa, lokacin zakiga habiba da maryam sun hayayyaƙo mata, ita maryam abunda na lura ita kuma son da take mun bata so taga wani yana mun irin wannan son, don kullum cewa takeyi Ayshaa nata ne, ita kawai kishina takeyi don ko habiba ne ta cika shige mun haushi maryam takeji, ita ko tafiya akeyi tafi so ta tsaya ta gefe ne, gaskiya *Aunty nice* bana gane wacece tafi sona a cikin maryam da jamila, amma nidai har ga Allah nafi son maryam, mun taso tare kuma muma maƙwaftaka, gashi ni ganinta nakeyi kaman ƴar gidan mu ita, ɗakin maryam muka wuce muka zauna, hannu nasaka nayi tagumi na zura mata ido, dariya ta kwashe da shi tace, "duk wannan tagumin na rashin jin ƙarshen su farare ne?" tsaki naja nace, "matsalata da ke idan ana magana mai muhimmanci ke ba'a nan kike ba", dariya ta sheƙe da shi tace, "tou ke yanzu wannene naki?" Hararanta nayi nace "nawa kuma? Son su ma kenan nakeyi? Bakiji nace miki ni kawai kyau suka mun ba, amma yayah ma za'ayi ina mace na so su"? Dariya maryam ta kwashe da shi da shi tace, "sokuwa tou ni nace miki son su kikeyii? Kawai dole akwai wanda yafi burge ki a cikin su shine nufi nah", Ajiyan zuciya na sauƙe mai girman gaske nace "ni duk burgeni sukeyi, don dukkan su farare ne, kuma kyaunsu duka mai kyau ne, amma ɗaya baida magana ɗaya kuma yana da magana, kuma fara'ar fuskan shi tana burgeni", na faɗa idona akanta, shewa tayi tace tanaga mai fara'an ne zai zamu na hannun dama na, saboda ni shiru shi magana, abun zaifi, don idan na haɗu da mai shiru irina abun ba zaiyi armashi ba, "me kike nufi ne maryam? Kina ɗauka ni ina son su ne?" Kama baki tayi tace, "na isa nace ke kina son su? Ae babu so a wannan al'amarin kawai burgewa ne, nima har naji ina son ganin su, suna zuwa ki zabga mun ƙira", ta faɗa tana wani dariyar shaƙiyan ci, nidai tsaki nayi na miƙe don tafiya gida.

Kullum zuba ido nake naga farare sun zo gidan mu idan Yayah Ahmad yazo amma shiru kakeji, a haka aka kawo kayan auren habiba, domin Abba yace december tare da na yaya Ahmad za'ayi, saboda haka ita mamie tana ta shirye-shiryen ta da ƴan uwanta, don ta ɗaga hankali wa Abba dayace suje su sayi kayi kaya ita da mamah da ummin, amma fir taƙi yadda, shima ya dage bazataje ita ɗaya ba, sai da Aunty Rakiya ta saka baki tukun Abba ya bar mata, amma duk da haka komai na kayan ɗaki da parlor da su electronic Abba ya bawa Aunty Rakiya ta mishi, kayan kitchen da su kayan zaƙi kawai Abba ya bar wa mamie, koda yake Yayah mohd ne ya sayi set na gado duka biyun, da set na kujeru, yayah Ahmad Abba yace ya haƙura yayi hidiman haɗa kayan nashi auren, amma duk da haka sai da ya sayi deepfreazer, T.V da gascooker, Aunty Rakiya kuma ta sayi cottons na gidan gaba ɗaya, Abba dai kayan kitchen da tarkacen kayan zaƙi ya bayan don ko gara Aunty asma'u ne tace a bari zata aiko, bawai don ƙarfin Abba ya gaza bane, no kawai zumunci da ake da shi ne da kuma ƙoƙarin Abba wa kowa a zuriyan. *Aunty nice* zakiyi mamaki idan nace miki jammy taƙi yadda suyi magana da habiba? Duk yadda habiba taso irin su haɗa kai da jammy abun ya gagara, nima maryam ke bani labarin abun da yake faruwa, ashe haɗa kayan ma mummy ne ta haɗo shiyasa mukayi mamakin ganin kayan, don a matsayin gidan su ba haka mukayi zaton gani ba, sai bakin mamie ya rufu ruff, baka jin wannan rawan kan, sai dai gori da zagin wata bata da farin jini wato ni, wlh ko ajikina, nidai damuwa na yadda habiba taƙi yadda mu tsaran yadda bikin zai tafi, don na rutsata a side ɗin hajiya ummah duk yadda naso ta bani haɗin kai mu maida komai ba komai ba, amma taƙi, sai wani nonnoƙewa ta keyi, ganin bazata bani haɗin kai ba sai na rabu da ita, don ko magana na mata bazata amsa mun yadda ya kamata ba, sai dai tayi murmushi tayi shiru, zuwa wani lokaci kuma sai ta fara share hawaye, ganin haka sai na fara rabuwa da ita, sai dai ina jinta suna waya da ƴan'uwanta na wurin mamin ta, kuma ina jin yadda suke magana akan hidiman bikin, a lokacin naji wai har sun fitar da ashobe.

Washe gari aka kai kayan auren yaya Ahmad, maryam ta shigo gidan mu bayan mun dawo akaiwan, gidan su yarinyar gidan tantsan ƴan boko ne, domin itama ƴar bokon ne, babu ƙaryah ƴan gidansu sun haɗu, hira muka ɓarke ni da maryam, anan ta keta bani labarin yadda mummy take nuna bata son auren Aliyu da habiba, kuma ko a gaban kowa tana kushe auren, jamilah ma ko maganan auren bata son a mata hiran, "chan ta matse musu", na faɗa ina tura baki gaba, a nan na bata labarin yadda mukayi da habiba, zagina maryam ta fara kaman ita ta haifeni, wai bani da zuciya tun da anguje ni da abu na haƙura mana, tagumi nayi na ƙura mata ido har taga ma ban baminta sannan nace, "besty bazaki gane bane, idan na ƙi shiga cikin hidimanta za'ace ko ina kishi ne ko ina mata baƙin cikin samun miji don ni ban samu ba", Harara na maryam tayi sannan ta ɗaura da tambayan, "dama ita ta samo mijin ko ke kika sama mata, nike meyasa halinki na sokaye ne kam besty? Tou a hirr ɗinki na ganki cikin hidimanta, idan ita tayi niyyah ta nemeki fine, idan bata nemeki ba mu cigaba da hidiman na Yaya Ahmad", muna cikin hiran hafsy ta shigo tana wani ƙyalƙyala dariyan mugunta, har ƙasa ta tsugunawa tana tashi, kallo muka bita da shi, maryam na tambayanta meyake faruwa? Sai da tagama dariyan tukun ta bamu labarin dambatuwan da akeyi acikin gida yanxu, ashe mamie ne ta ɗagawa Abba hankali akan kayan yayah Ahmad, wai wannan kayan ba kuɗin yayah Ahmad bane ya haɗa kayan, dole Abbah ya dafa mishi, tunda hakane kuma dole ya bayar ta sake haɗawa habiba kaya, don na habiba basu da wani quality, shi kuma Abba yace mata bata isa ba, shidai yayi niyyan haɗa mata akwati ɗaya na kayan fitan biki yadda yayiwa Adda lokacin aurenta, daga nan ya ƙira Aunty Rakiya ya gaya mata yadda sukayi,shine fah Aunty Rakiya tazo ta sameta ta watseta, ke kam mamie sai kuka wai ana mata baƙin ciki don anga habiba ta samu miji ke baki samu ba, Aunty Rakiya ta zage ta tas tace wani mijin da sukayi ƙwace? Da ƙyar ummie taje ta kashe maganan, nidai banda dariya babu abinda nakeyi, Adda idan kukaga idon raliya dole kuyi dariya, hafsy ta sake tuntsurewa da dariya maryam na tayata, ni dai banji dariya ba sai wani abu daya tokare ni a zuciyata, wai ni nawa nake nema da mamie ke goranta mun rashin aure? Yaushe ma habiban tayi da za'a fara goranta mun?

Babu wuya wurin ubangiji, cikin satin nan aka fara hidiman auren su Yayah Ahmad da na habiba, gidan mu ya cika da dangin ummie da mamie, sannan kuma ga dangin Abban mu da suka zo, side ɗin su yayah Ahmad ma cike yake da friends ɗinsu, domin yayah umar ya kwashe nashi ya nashi sun koma gidan Aunty Rakiya shida yayah ishaq, sai suka mayar da gidan kaman majalisan angwaye, babu abun da kike gani sai shigan motoci da fitar su, gashi ummie tana wadata su da lafiyayyun abinci da kayan shaye-shaye kala da kala, hankali kwance suke hidiman su, yau ne gidan su amaryan suke liyafa thursday, habiba kuma kaman gobe friday naji hafsy tace za'ayi nata liyafan a farfajiyar gidan mu, wanda ita kuma zatayi ƙauyawa a gidan wan mamanta da yake gida dubu, kuma har lokacin bata ce mana komai ba, duk da ummie tace naje na shiga cikin ƙawayenta ko bazata kula ni ba, amma firr maman su maryam tace haka bazai faru ba, idan wani abu ya faru cewa za'ayi daga garemu ne, magani shi kawai kar a fara.

Wuraren 5:00pm mun gama shiryawan mu tsaf cikin wani arnen lace da yayah mohd ya ɗinka mana mu uku har da raliya, kowa da kalan nata amma zanen su ɗaya, nawa purple anyi mun gown mai lafiyan kyau, gaban an jera bakin lace ɗin tunda ga sama har ƙasa an kuma shiryashi da adon stones masu hasken gaske, dama tun wurin azahar muka dawo daga gidan lalle, dayake Allah ya mana baiwar hasken fata zokiga yadda lallen yayi mana kyaun gaske, ranan laraba yayah umar suka kaimu saloon aka mana gyaran kai har da maryam da ummitah sister ta, yau kuma suka kaimu gidan lalle, nidai mamakin yayah ishaq nakeyi yadda yake ta wani kaffah-kaffah da hafsy, lace ɗin hafsy Red ne, don ita mayyar red abu ne, ita kuma raliya green, amma ban san ko yau zata saka nata ba, don ita ma ɗauke mana wuta tayi, garama mutumiyarta hafsy idan sun haɗu sukan ɗan taɓa hali, kuma dai su basu daina kula juna ba, saidai suyi faɗan kuma suyi hiransu, don komai sai ta bawa hafsy labari, amma yanzu sai naga wani ƙawance na musamman ya shiga tsakanin hafsy da ummitah ƙanwar maryam, don da tsabar kowa danata halin masifan basu zama inuwa ɗaya, daga baya ma tun suna primary ummitah ta koma lagos hannun sister mamansu data girma a gidan, tana aure ta tafi da ummitah sai ta bar anguwan mu, yanzu kuma Auntyn su sun koma spain da mijinta sai maman su tace ummitah ta dawo saboda bata son girman ta achan, tou sai suka ƙulle da hafsy kuma abun ya mun daɗi, saboda ummitah ƴar gayun gaske ne, wanda na lura yanzu hafsy ma tafara koyi da ita, muna shiryawa nida fatiman Aunty Bintu da maryam a side ɗin hjy ummah fatima sai kwashewa da dariyan mu takeyi, nima dai dariyan na fara ina cewa, "wallahi fatima ni a sokanci na ae da binsu zanyi goɗai-goɗai, da badan Aunty Bintu ta tunatar da mu ba ae sokayen yayu za'ayi masu bin ƙanne da masoyan su", dariya dukkan mu uku muka kwashe da shi. "*Aunty nice* nifah ban lura akwai wata alaman ƙwollaliya ba tsakanin yayah ishaq da hafsy, yayah umar da ummitah ba, sai da Aunty Bintu tace idan mun shiryah sai mutafi wurin event ɗin tare, ta taho da motan ta, aiko nace mata dasu yayah umar zamu tafi, nan take zayyana mana abun da ta lura yake tsakanin su, tana dariya tace ko wasu irin yayun kawai ne zaku na bin yara goɗai- goɗai da masoyan su"? Dukkan mu dariya mukayi, wato sun raina mana hankali mune ƴan rakiya ko?

Mun fito haraban gidan mu uku muna jiran fitowan Aunty Bintu da ta tsaya suna magana da ummi, hannu na riƙe da Areefh wanda yayi wayo don ya kusa 4month koma ya cika yayi ɓul-ɓul, kaman nin shi da yayah mohd da yayah Ahmad dani ya fito sosai, wani ma idan bai san Baban shi ba zai ce nina haife shi, Allah sarki gashi har irin haƙurin mu ya ɗauko, muna tsaye jikin motan muna jiran Aunty Bintu sai ga su Yayah Ahmad da abokan shi sun fito a side ɗin shi suna wucewa wurin motocin su, muryan yayah Ahmad naji ya ƙirani, juyawan da zanyi kawai sai nayi ido biyu da fararen nan sun sha wani milk colour ɗin filtex, da sauri na ƙarasa wurin yaya Ahmad da yake tsaye yana ɗaura agogon shi, miƙo hannu yayi ya karɓi Areefh yana tambaya na dawa zamu je wurin event ɗin, yana tambayan idon shi yana kan Areefh, murya ƙasa-ƙasa kaman bana so wani yaji nace mishi, "da Aunty bintu zamu tafi" miƙo hannu yayi ya karɓi handbag ɗina, hannu yasaka a aljihun shi ya ciro kuɗi bunch guda ƴan 100 ya saka mun a ciki, idon shi akaina yace "wannan na liƙi ne, ina hafsy kuma"? Ya tamabaya yana duba cikin compound ɗin gida, a hankal nace "sun fita tare dasu yayah umar" sannan na mishi godiya sosai, kawai sai ganin M.G ya matso kusa da mu fuskan shi da murmushi ya miƙa hannu ya karɓi Areefh, idon shi akaina yace, "ƙanwar mu mai kyau wannan babyn kaman ki da shi yayi yawa, ba lallai ki haifi ɗa mai kama da shi ba gaskiya, ɗan wurin Yayan mohd ne"? Ya tambaya gaba ɗaya hankalinshi yana kan Areefh, gaishe shi nayi fuskana cike da murmushi, lokacin Aunty Bintu ta fito, ganin ta fito na ƙara yiwa yayah Ahmad na miƙa hannu zan karɓi Areefh yaro kawai ya wani juya yaƙi zuwa, kuma ban taɓa ganin yayi ƙiwuya ba, dariya M.G yayi yace, "kai yaron nan ya burgeni, kinga shima baya so ki tafi M.G ya daina ganin lallen ki mai kyau ɗin nan," kunya maganan shi ta sakani nayi saurin ɗan yin baya kaɗan ina ɓoye hannu ni fuskana ɗauke da murmushi, "don Allah kazo muje mana kana ɓata wa mutane lokaci fah", muryan A.G naji yana yiwa M.G magana, ɗago kai nayi da sauri na sauƙe akan shi, shima kuma alokacin gaba ɗaya idon shi yana kaina, saidai babu fara'a ko kaɗan akan fuskan shi, da sauri na juya fuskana na mayar kan M.G da yake miƙo mun Areefh murya ƙasa-ƙasa yace, "karɓi yaron kafin wannan masifaffen yayi yaga-yaga da ni", ina karɓan Areefh ya ɗaura mun wani bounch ɗin ƴan 100 ɗin akan Areefh ɗin, yana cewa "wannan ki ƙara na liƙin ko", Da sauri nace, "a'a don Allah ka bari yaya Ahmad ya bani". Cikin tsawa-tsawa kaɗan A.G ya sake cewa, "shi Ahmad ɗin ne yace miki mu ba yayunki bane? Ko kuma idan mun baki abu kada ki karɓa"? Murmushi M.G yayi ya juya suka tafi bai sake cewa komai ba, nima juyawa nayi wurin su Aunty Bintu don mu wuce.

Readers Also Read