Ana barin halal original by anty nice - Chapter 5
Ana barin halal original by anty nice Chapter 5: Ana barin halal original by anty nice Chapter 5. "Abbah" habiba ta ƙira sunan shi, sai kuma tayi shiru kan…
4,313 words
"Abbah" habiba ta ƙira sunan shi, sai kuma tayi shiru kan ta a ƙasa, "ina jinki ƴan biyu nah" da sauri ɗaga kai na dubi habiba, wanda ita ma ni ta ɗago tana kallo, gaba ɗaya sai naji wani tausayinta saboda yadda duk na ganta a wani firgice, ga idon ta ya ciko da ƙwallah, da sauri ta mayar da kanta ƙasa, "Abba watarana muna zaune a side ɗin ummah nida ayshaa, sai tace ta nema na mata alfarma, ita dai bata son Aliyu kuma tayi-tayi taji tana son shi amma ta kasa, gashi tana jin nauyin ƙawar mu jamilah da kuma mummyn su, don Allah na taimaka mata na amshe shi ya zama nice zai aura, don sun gama magana da shi kuma ya fahimce ta, nidai naƙi amince mata har tayi fushi da ni ta daina kula ni, danaga abun zai kawo mana saɓani sai na sake neman ta mukayi zama, nan ta sake mun bayanin sun gama magana da Aliyun kawai amincewa na take jira, tou Abbah ganin bana so saɓani ya sake shiga tsakanin mu sai na amince, nan kuma tace mun bata son kowa ya sani ko mamie ce, har sai ranan da za'a zo gaisuwan wato yau, shiyasa mukayi shiru, itama mamien na ɓoye mata sai yau taji, don ce mata nayi wani ne ɗan katagum, kuma baya zama anan yana saudi, wannan shine gaskiyan maganan Abbah", ta ƙarasa faɗa idon ta yana zubar da hawaye, nidai tunda ta fara magana na shiga al'ajabi, don a duk zamana da habiba ban santa da ƙaryah ba, kuma daga ji wannan magana tsara mata akayi, kuma nayi imani da Allah ba asiri mamie ta mata ta burkita tunanin ta ba, don tun farko habiba ran ta yaso Aliyu, saboda haka ƙofa kaɗan za'a buɗe mata ta zurma, kawai *Aunty nice* naji tsoron ɗan adam a ranan ta bakin hajiya ummah, kuma nayi mamakin ashe duk ƙaunar mu da habiba namiji zai iya shiga tsakanin ƙaunar mu? Don ni ina jin ko yayah namiji yake bazai ɗauke hankali na ba, har na haɗa so da ƴar'uwata, ae *ANA BARIN HALAL*... don kunya, ko da naji son wani wanda ƙawata take jin so ko ƴar'uwata inaga zan iya yakice shi a raina, ya kicewa kuma na har abada, amma meyasa ƴar'uwata da nakeyi wa wani irin so ta mun haka, meyasa habiba ta yanke yadda da amincin da yake tsakanin mu na tundaga tashin mu? Kallo na Abba yayi, sannan yace "haka akayi Ayshaa ta"?
Ɗago kai nayi na dubi habiba, wanda har zuwa lokacin jikinta rawa yakeyi, maida kaina ƙasa nayi na saka hannun cikin na ummie nah na riƙe, ina ji itama ta damƙe a hannu na tana sauƙe ajiyan zuciya, muryah ƙasa - ƙasa na amsawa Abba da, "hakane Abbah, duk abinda ta faɗa haka ne ya faru" da rawar muryah na ƙarasa maganan, dai dai nan kuma Bappan mu ya amsa da, "Allah ya muku albarka, kema ayshaa Allah ya baki miji nagari, don baza ace kinyi wauta ba, amma gaskiyar batu kam akwai wautan a al'amarin, don dai komai ya wuce ne ae, ina laifin kiyi shawara da mahaifiyar ki kafin ki zartar da komai? Don dai duk ɗaya ne kawai, Allah ya kyauta", ajiyan zuciya Abbah ya sauƙe ya maida hankalin shi kan mu gaba ɗaya,bayan yayi mana dogon addu'a ya sallame mu, amma muna miƙewa mamah ma ta miƙe da sauri tabi bayan mu, tana ita bazata iya wannan zaman kayan takaicin ba, don idan ta cigaba da zama rai zai ɓaci, ina kallon yayah mohd ya bini da kallo, yayah Ahmad kuma ya dawo kusa da ummi ya zauna.
Muna fitowa habiba ta riƙo hannu na muryah ƙasa- ƙasa tace, "sisto nagode da kika rufa mun asiri, wlh duk wannan abun ya faru ne bada son zuciyata ba, amma insha Allahu zan miki bayanin da zaki fahimta, yanzu dai nagode"' , tana gama faɗa ta sake hannu na ta wuce side ɗinsu da sauri saboda hango raliya da ta fito daga babban kitchen ɗin dayake wurin, nidai bin ta da kallo kawai nayi ban iya nace mata komai ba, Mtssss, tsakin raliya naji dabdani, da sauri na bar kallon inda habiba ta wuce nayi, na maida kallo na inda raliya take nayi, itan ma bance mata komai ba sai ido dana zuba mata, matsowa kusa dani tayi tana wani murguɗa baki, "mutum dai yaji kunya duk kyaun da yake gadara amma ya zama mai baƙin jini, baƙin jini kuma yanzu mutum ya fara, sai dai yaga ni wal ta gaban sh" tana rufe baki hafsy na kai mata mari a bakinta, "bakinki ya sari shegen guntun kashinki, insha Allah aniyar ku ta biku, ae kune masu abun kunyar da har babu kunya babu tsoron Allah kuka iya cin amana ƴar'uwarku, ae kuwa kune masu abin kunya, sannan da kike maganan baƙin jini, shin akwai wanda ya kaiku baƙin jini? Kun kasa raminku sai dai ku ƙwace na wasu? Abun kunya ae ya tabbata akanku zuriyar matsafah".. tana rufe baki kuwa suka kancame da dambe, kowa duka take kaiwa ƴar'uwarta, nidai jan hafsy nake ina roƙon su dasu bar wannan shirmen, da sauri yayah mohd ya fito shi da yayah Ahmad, tsawa ya daka musu daga bakin ƙofan da yake tsaye, da sauri suka saki junan su suna huci kaman wasu zakaru, "ku wuce kubawa mutane wuri sokayen banza da wofi, ku gaba ɗaya rayuwar ku baku da hankali, kullum sai faɗa baku son zaman lafiya"? Nidai ganin yayah mohd ya fara faɗa wanda ba kasafai zaka ganshi yana yi ba, nayi wuff na wuce ɗakin mu, ina shiga na wuce chan ɗakin ummie na, kwanciya nayi na faɗa tunanin yadda al'amura suka juye, yanzu abun da habiba ta mun akwai adalci kuwa? Shin zan iya yafe mata har mu sake komawa kaman da? Shin idan tayi auren zan iya zuwa gidanta? Duk irin waƴan nan habiba batayi tunanin faruwar su ba, kawai hankalinta kwance taji ta so abun da yake sona? Tashi nayi na zauna, wayata na jawo nayi blocking number Aliyu na kuma goge number, bayan na share duk wasu massege ɗin shi, sannan na tafi whatsapp na sake blocking ɗin shi na kuma goge massege ɗin shi, don dama a yawancin lokuta bani ke reply ba habiba ce, shiru nayi ina tunanin yadda rayuwa zata miƙe tsakanina da habiba kawai nakeyi, a haka naji shigowan ummie nah, hannunta riƙe da na hafsy da taketa huci, bayan ta kuma yayah mohd da yayah Ahmad ne.
Wuri suka samu dukkan su suka zauna, ummi zama tayi akan gadon tana riƙo hannu na, yayah mohd ma a gefenta ya zauna yana riƙo hannun hafsy, shi kuma yayah Ahmad kujeran dake ɗakin 3sitter ya zauna akai shima idon shi akaina, wani abu naji da ban taɓa ji ba na rauni a lokacin da yayah mohd yace mun, "Ayshaa akwai gaskiya a maganan da kuka faɗa ke da habiba a wurin Abbah? Don gaskiya ni nakasa gasgata maganan, don nasan babu yadda za'ayi ku iya tunanin shiryah haka a tsakanin ku ba tare da kinyi shawara da ummie ba, don kwanaki B<ntu ta fara mun wani zancen da bangane ba sai na da katar da ita, amma yanzu ina son sanin gaskiyan maganan"? Faɗawa jikin ummie na kawai nayi ina jin duk dauriya na ya ƙare, ina jin babu abinda nake so irin nayi kuka, kukan ne nake tunanin zai saka na samu sauƙi, domin ni dai bawai shaƙuwa nayi da Aliyu ba ballantana nace ina son shi da hankali na zai tashi ba, amma abunda habiba ta mun shiyake bani tsoro da sakani cikin damuwa, yanzu da ace ina son shi haka zata rufe ido babu kunya babu tsoro ta so shi? Kenan habiba zata iya son mijin da nake aure ma idan yayi mata tayi, kuka nakeyi sosai ummie tana rarrashina.
"kiyi haƙuri ayshaan ummie, komai insha Allahu zai wuce, kuma mijinki special zai zo", cewar yaya Ahmad, wanda tashi yayi zai fita don shi wani iri ne da baya son ganin abun da zai tayar mana da hankali, bayi da dauriyan yayah mohd, kuma shi sanyin shi da haƙurin shi dama yafi na kowa, yana miƙewa yace, "ummie don Allah ku kwantar mata da hankali, ni zanje gidan Aunty Rakiya mu gaisa, zan koma leƙa wurin su M.G ɗa A.G, don munyi waya suna gari," zuciyata ce naji lokaci ɗaya ta yanke saboda jin sunan fararen abokan shi masu kama da larabawan nan daya ambata, bansan lokacin dana ɗago da ido na ina kallon shi ba, matsowa yayi kusa dani yace, "ko akwai abinda kike so ne na sayo miki"?
Hannu na miƙa mishi ya riƙe, muryah na yana rawa nace, "yayah ni waya nake so ka chanja mun", murmushi yayi yace "angama my sister, zaki ga waya mai kyau insha Allahu", ya faɗa yana mun murmushi, a haka na sake mishi hannu ya juya ya fita, "wariyar launin fata, gaskiya kowa yafi son Addah Ayshaa akaina a gidan nan, yanzu fah kuka akasamu inayi amma babu wanda ya damu dani, amma ita kowa hankalinshi yana kanta, yaushe ma aka saya musu wayan amma don nuna so da sakalci har wani za'a sake mata wani, nidai bana son natan da za'a chanja mata nima sabo za'a saya mun ba kunce ba", hafsy ta faɗa tana turo baki gaba tana harara na, "tashi ki fita uwar rashin kunya, dama akwai wanda yace miki za'a saya miki waya ne yanzu? Fita kije ki ɗaura mun abinci" ummie ta faɗa tana nuna mata hanyar waje, haka ta miƙe tana Addah idan nagama don Allah ki bani akwalar wayar ki nayi game, nidai miƙa mata wayan nayi ban dube ta ba, ta juyo ummi ta wafce wayan tana, "rabu da ita sai ta gama aikin, idan kin bata wayan Game zata tsaya yi har abincin ya ƙone ko kuma tayi dare, Bayan fitan tane yayah mohd ya dawo da duban shi kaina, ganin haka na bashi amsa da "wallahi yayah ni bansan duk abunda tace ba, kawai dai na bita a hakane don kar hankali Abbah ya tashi, kuma naga babu amfani tunda yaƙini ya koma mata na ƙaryata, don ni dai bazan sake kula shi ba tunda ya koma mata, akan ayi biyu babu gara itan suyi", na ƙarasa hawaye yana bin fuskana, riƙe hannu ummie tayi ta jawoni jikinta tana, "kiyi haƙuri insha Allahu zakiga alkhairin haƙurin da kikayi, ki barta da shi Allah zai kawo miki naki rabon, amma don Allah yanzu bana son wannan sakewa ki bar saurayi da ƙawa ko ƴar'uwa, duba da yadda rayuwar yanzun ya koma, amana yayi ƙaranci, ni dama tun lokacin da kika nuna mun bai kwanta miki ba sai na ƙara dagewa da addu'an neman alkhairi akai, kuma ko a yanzu ina ji a raina babu alkhairi a ciki shiyasa duk hakan ya faru", ummi tana rufe bakinta naji wani kuka yazo mun, Allah sarki uwa, gaskiya duk wanda ya rasa uwa dole ya koka *Aunty nice* domin ita wani abu ne na daban, nifa babu wani addu'a da nakeyi akan al'amarin amma kiji ita kuma tana mun, Allah sarki ummie nah, riƙo ta nayi sosai nace, "ummie amma duk da haka sai habiba ta so mutumin da yake sona? Kenan zata iya son mijin da nake aure ma kenan? Ummi ciwon ɗa nakeji a zuciyata bawai na rabuwa da shi bane, ina jin ciwon abun da ƴar'uwata da nafi so ta mun ne, yanzu dole danganta kar mu yaja baya" na faɗa ina share hawayen ido na, "babu komai sis insha Allahu tsakanin ku zai dai-dai ta, ke ae zuciyar ki mai kyau ce, kuma nasan zaki yafewa ƴar uwaki ki mata uzuri, insha Allah komai zai wuce" yayah mohd ya faɗa, sannan ya chanja topic ɗin, suka koma maganan haihuwar Aunty Bintu, inda yake gayawa ummie wai maiduguri take son zuwa haihuwa, amma shi gaskiya baya son hakan, itama ummie ta goyi bayan maganan shi akan gara ta haihu a ɗakin ta don babu abunda zai gagara.
Tunda ga ranan da abun ya faru mamie ta samu abun habaici, babu garin Allah da zai fito ya faɗi bakaji ta tana surutun masu rashin farin jini ba, a haka Aunty Rakiya watarana ta shigo ta samu hakan na faruwa, ae ko ta sille mamie tass, harta habiba bata bari ba, don hajiya ummah ta gaya mata yanzu an hana habiba zuwa side ɗinta, ni kaɗai nake zuwa kwana a chan, aeko aka bar mamie da kame-kame tana bata haƙuri, tass ta zage habiba tana gaya mata indai cin amana da halin uwarta take so ta ɗauko wlh zata sha wahala, kuka habiba ta dinga yi, bayan mamah da Aunty Rakiya sun haɗu sun watse su, zuwa dare ina kwance a ɗakin mu na side ɗin ummah sai ga habiba ta shigo, yadda bata yi sallama ba ta shigo nima sai ban ɗaga kaina na dube ta ba, nidai ina riƙe da wayana muna chatting da jammy, haƙuri kullum take bani akan dukkan su basuji daɗin abinda ya faru ba, don mummy tayi rantsuwa ita dai babu yawun ta acikin maganan auren, don tun ranan tace babu jituwa tsakanin shi da mummy, shima Aliyun tace duk jikin shi yanzu a sanyaye yake, nidai ban tofah komai ba akai, don ummie nah taja mun kunne sosai akan al'amarin, saboda haka sai na chanja topic, na tambayeta yaushe zata fara karatunta? Tace sai bayan ta haihu,, so tanaga zai kai next year, haka mukayi sallama, ina kallon habiba ta gefen idon na tagama duk abinda zatayi na shirin kwanciya bata kulani ba, nima ganin hakan sai na rabu da ita, nayi shirin kwanciya na nima na kwanta.
Washe gari bayan mun idar da sallah na juya na kalleta nace, "sisto an tashi lpy"? A razane ta juyo ta kalle ni, amma abun mamaki sai bata iya ta amsa mun ba, kawai dai naga idon ta ya wani ciko da hawaye, ganin haka sai na koma kan gado na kwanta, na juya mata baya, ban farka ba sai wurin ƙarfe 8:00 shima hafsy ne ta shigo ta tashe ni, akan naje ummie tana nema na, dubawa gefen habiba nayi naga babu ita babu alaman ta, maida kallo na nayi kan hafsy nace, "da kika shigo kinga sisto ne?" tsaki tayi ta fita a ɗakin tana faɗin " ke kika san wata sisto, ni dai naga habiba ta wuce side ɗinsu tun wurin 6:30am, idan zaki yiwa kanki faɗan ta nutsu gara ma kiyi", ta wuce tayi hanyar waje.
Lokacin da na shiga ɗakin ummie na nasamu tana waya ne, a hankali na fahimci da mummyn su Aliyu take wayan, zuciya nane naji ya yanke, kasa kunnena nayi ina sauraran abun da suke faɗa, haƙuri kawai ummie ke ta bawa mummy akan ta kwantar da hankalinta komai nufine na Allah, Allah yayi babu aure tsakanin shi da Ayshaa, rabon da habiba ne, da yake ya wanci ummie idan zata amsa wayanta handsfree ta ke bari, sai idan na sirri ne sosai ba zata saka ba, tsaki mummy ta ja mai ɗan tsayi sannan tace, "wallahi ummin su rai na baya son haɗa iri da matar nan, don babu Allah a zuciyarta, amma bbu komai abunda ta keso bazata samu ba, don insha Allahu bazan bar ɗana a mallake ba, a farko kan sunyi nasaran chafko shi amma gaba kan tayi kuka da kanta", murmushi kawai ummie tayi sannan ta chanja zancen da wani chan daban, a haka kuma basu daɗe ba suka yi sallama. Daga nan ummie ta juyo tana kallona fuskanta ɗauke da murmushi, ni kuma da sauri na ƙarasa wurin ta, gaisheta nayi, ita kuma ta tambayeni fatan babu wani matsala ko? Murmushi nayi na kwanta a kafaɗan ta, bance mata komai ba nayi shiru kawai ina kwance ido na a rufe, nasiha da kwantar da hankali na ummi tayi ta mun, tunin naji zuciyata tayi sanyi, muna a haka wayan ta ya fara neman a gajin a ɗauke shi, hannu ta saka ta ɗauka sannan ta saka shi a handsfree, muryan yayah mohd naji yana gaisheta, ni kuma na ƙara gyara kwanciyata a jikinta, kawai sai naji yayah na gaya mata Aunty bintu ta haihu, da sauri na miƙe zaune ina fara'a idona akan ummie nah da duk fuskan ta ya gauraye da murmushi, "ta samu boy, daga ita har babyn duk suna lafiya, muna asibitin", ya faɗa ummie kuwa sai fara'a ta ketayi, "insha Allahu mamanku suna zuwa yanzu, Allah ya raya baby da imani, ita kuma Allah ya bata lafiya da lafiyan shayarwa, suna ajiye wayan na rungume ummie ina "ummie munyi ɗa, wayyo ummi nayi ɗa," da sauri na miƙe nace "ummie bari na shiga wanka na bi mamah muje muga baby", ko jiran me zatace banyi ba na wuce toilet da gudu na.
Kafin kace me duk gidan mu ya kachame da murnan haihuwan barin ma hafsy da ta ringa tsalle kamar ƴar 6yrs, haka muka shiryah sai *NI'IMA HOSPITAL* mukaje mukaga yaro fari kyakkyawa, kana ganinshi kaga jinin gidan mu, sak Yaya mohd kaman wanda yayi kaki, haka muka ringa murna muna ta ɗaukan babyn, bayan 1hr aka sallame su, lokacin Aunty Rakiya ta iso ita da hajiya umma, mu kuma dama da mamah mukazo da hafsy sai driver, abun mamaki har muka gama murnan haihuwan nan babu mamie babu ƴaƴanta ko ɗaya, kuma duk suna gida, ganin zuwan su ummah nayi tunanin ita mamin zata biyosu amma shiru, haka muka ɗunguma gidan zuwa gidan yayan mu. Muna zuwa muka samu Fatima ta gama gyaran gidan ko ina sai ƙamshin turaren wuta yakeyi, dama ana haihuwan yayah mohd yace ta koma gida ta gyara, amma bata ɗaura abinci ba daga gida ummin mu ta sa akayi, ana zuwa mamah ta saka ruwa ta wanke baby tsaff, Aunty Bintu kuma Aunty Rakiya ta shiga ta gasa mata jiki ta fito ta barta ta ƙarasa wanka.
Bayan kwana 2 sai ga yar maman Aunty Bintu ta taho daga maiduguri, dama mamah tun ran haihuwar muke gidan tare, sai ranan ta tafi, amma ni ina nan tare da fatima, ummie tace na zauna na taimakawa fatima.
Ranan suna yaro yaci sunan Abban mu wato *USMAN* amma sun mishi laƙani da *AREEFH* sai wajen dab da magrin sai ga mamie da su habiba driver ya kawo su, muna zaune a parlor nida su maryam da fatima, da wata ƴar'uwar su da suka zo suna mai suna Ayshe itama, muna zaune suka shigo, muna haɗa ido da mamie ta zabga mun hararah, ganin haka na ɗauke kaina a kan su, ganin akwai su maryam a wurin habiba ta tsaya, ita kuma raliya suka shige ciki ita da mamie, banyi niyyan kulata ba duba da ganin bata kula ni, duk da dai ni yau sati na guda da barin gida, ita kuma ba zuwa barka ma sukayi ba, kawai kaman daga sama naji muryan ta tana faɗin "sisto sabon waya kikayi ne"? Ɗago kai nayi ina duban ta fuska na ɗauke da murmushi na amsa mata da "ae yayi 2weeks ae, ranan da aka kawo ina gaya miki naga kin wuce kitchen da sauri, so nayi tunanin idan kin fito zaki zo ki gani ae", da sauri ta saka hannu ta karɓa tana juya shi, cike da mamaki tace, "kin san irin shi ne a hannun Baby", ta sake juya wayan a hannunta tace " Gaskiya wayan ta tafi da ni don tun ranan dana gani a hannun shi wayar ta mun, shi kuma yana cewa ta fi ƙarfi na, gashi kuwa a hannun sisto, aeko zan ce mishi batafi ƙarfi na ba, tunda sisto na ma shi ta ke riƙewa", "chaɓ aiko tafi ƙarfinki, amma ta wani wuri kuma bata fi ƙarfin kiba, tunda naga alama ke duk abunda siston naki tayi sai kin nemi ƙwace shi zuwa gareki, kin ƙwace saurayi yanzu kuma kina shirin na waya, wai ke habiba baki ƙoƙarin yin abun kanki ne sai na wani? Inaga Babyn ma wanda kikayi ƙwacen ne kika mayar da shi Babyn ko?" cewar Fatima wanda ita dama kullum dare zamu kwanta ta dinga mitan wannan al"amarin, zuwan Ayshe ma jiya-jiya sai da ta bata labari, da yake dukkan su ƴan zafin kaine ita da ayshen sai abun su ya ɗauki zafi, ni dai da sauri na juya ina duban fatima da tayi maganan tana wani chin magani kaman zata kai duka, tana wani hararan habiba, miƙo mun wayan habiba tayi fuskan ta ɗauke da murmushi tana kallo na, bata tanka abun da fatima ta faɗa ba, sai ce mun tayi bari taje taga babyn sai ta dawo, hannu na miƙa na karɓi wayan da ta miƙo mun, tana barin wajen maryam taja wani dogon tsaki mtssssss, "yarinyar nan kullum na ganta kashe ni ta keyi da mamaki, kana ganinta kaman ta gari ashe zuciyar ta babu kyau ko kaɗan? Amma ba laifinta bane wlh, duk laifinki ne besty", maryam ta faɗa tana maida hararanta kaina, "good kin faɗi abun da yake zuciyata tun jiya, wlh tun jiya da fatima ta bani labari na kalli Ayshaa naga kaman bata wani damu ba sai kare ƴar'uwarta ta keyi, nace gaskiya Ayshaa itace mai laifin, don sai bango ya tsage kadangare yake samun ƙofa, idan ba sakacin Ayshaa yayi yawa ba ta yayah ƴar'uwata zata mun ƙwace a ƙaramin lokaci, haba jama'a wannan ma ae raini ne da chin fuska, sannan kuma babu daɗewa nazo ina buɗe miki baki ina miki dariya har ina miƙa miki waya na"? Aysha ta faɗa haushina cike da zuciyar ta, nidai bance komai ba banda mirmushin da nakeyi kaina a sunkuye ina kallon waya na kaman zan ga wani abu a ciki, amma zuciyata cike ta ke da damuwan maganan da habiba tayi, wato Aliyun ne ake ce mishi Baby? bayan haka ma yaushe yake zuwa gidan mu hiran da har taga wayan shi? Ikon Allah yanzu ya tabbata da gaske habiba tana son wanda ya so ni har yaso aure na? Muryan Fatima ne ya dawo da ni kan tunani na danaji tana cewa, wai ko yanzu habiba ta kuskura ta dawo sai ta ƙara watseta, jin haka nayi saurin ɗago kaina nace mata "a'a fatima idan ummie taji raina zai ɓaci, don taja kunne na sosai akan maganan kuma tace bata son wani magana daga gare ni ya fito, don Allah ku bar maganan don ni yanzu ma duk kunsa naji babu daɗi, don gani zatayi kaman na damu ne yasa na gaya muku, don Allah kubari". "dole ae kowa ya bari, tunda me abun bata so, mu ƴan abi yarima a sha kiɗa kuma mai ya talo mana? Allah ya bada sa'a", cewar maryam. Babu daɗewa aka fara ƙiran sallan magrib, daidai nan habiba tazo inda muke, still fuskanta ɗauke da murmushi, gefe na ta zauna tana sake karɓan wayan hannu na, ban ja ba na miƙa mata, ƙasa-ƙasa take tambaya na waya saya mum? Murmushi nayi ina kallon inda ta buɗe, gallery nane wanda babu pic kowa sai na hafsy, sai kuma wannan babyn da aka haifa, sai kuma dukkan mu har da yayah mohd da babyn da maman babyn da mukayi yau da safe, bance mata waya saya mun ba sai murmushin da nayi, dai-dai wani photon da nayi riƙe da babyn a hannu na, lokacin na karkato da fuskan shi ya fito sosai, ƙurawa yaron tayi ido tana murmushi, chan ta ce, "sisto yaron nan kaman ke kika haife shi, kunyi kama sosai, Allah ya baki miji fari ku haifi irin wannan" ta faɗa tana ƙara zooming pic ɗin, nidai ban bata amsa ba sai murmushin kawai da na faɗaɗa shi, idon hafsy kaman zai faɗo ƙasa tsabar hararan da ta ke jefo mun, bai isheta ba ta ƙaraso inda muke ta miƙa hannu ta karɓi wayan a hannun habiba tana cewa, " Adda zamuyi photo da ƙawata" ko jiran amsa na batayi ba ta juya da wayan tayi ɗakin Aunty Bintu, nidai duk sai naji kunyan habiba, gashi su maryam sun wani nuna kaman ma basu san da ita a wurin ba, bai ishe su ba Ayshee tace su tashi suje suyi sallah suyi addu'a Allah ya rabasu da zuciyar cin amana, fatima kuma tana ƙarawa da kuma zuciyar son zuciya da ƙyashi da hassada, ita dai habiba bata ko kalle su ba idon ta kawai yana kan waya na, har sai da hafsy ma tazo tayi nata iskancin tukun ta ɗago idon ta danaga alaman kaman da hawaye, amma fuskan ta cike da murmushi ta dube ni, lokacin kuma mamie da raliya suka fito daga ɗakin mai jego, idon mamie akan mu amma kasan cewar Aunty bintu na bayan ta bata iya cewa komai ba sai harara da ta watsa mun, ƙasa-ƙasa tana hararan habiba, "tashi mutafi Addah, ko kuma sai an ɗaga ki amaryar Ali"? Raliya ta faɗa babu ko kunya a idon ta, tashi mukayi dukkan mu nida habiba muka tsaya, wani kallo mamie ta bini da shi na ƙasƙanci, a gadaran ce tace "ke kuma kin yafe school ne kika tattaro nan kika zauna? Ko aure za'a cire ki a miki tunda karatun yana takuraki?" ta faɗa tana mun wani banzan kallo, "mamie ae sai da white blood ake auren ko? Ae kawai kiyi shiru mamie mu wuce" raliya ta faɗa tana wani dariyan iya shege, daga ni har habiban kallo muka bita da shi, ganin haka Aunty Bintu ta dubeni tace, "Ayshaa maza jeki ɗakin yayan ku ki feshe shi da shelktox, ki rufe duka windows ɗin plz" ganin na samu sauƙin cin zarafin su akaina nayi sauri na amsa da tou na wuce ciki, bayan na amsa da tou, sannan nayiwa su mamie sallama, wanda ina gani bata amsa ba sai bina da harara da tayi
Washe gari na shiryah tun da safe na musu sallama na wuce gida sbd monday zan koma sch, duk da an koma tun last week.