Ana barin halal original by anty nice - Chapter 19
Ana barin halal original by anty nice Chapter 19: Ana barin halal original by anty nice Chapter 19. Ajiyan zuciya ya sauƙe mai ɗan sauti, shiru mukayi…
4,458 words
Ajiyan zuciya ya sauƙe mai ɗan sauti, shiru mukayi dukkan mu babu wanda yayi magana, amma kowa yana sauraran sautin bugun zuciyar ɗan'uwan shi, mun ɗauki sama da mintuna goma babu wanda yayi koda tari ne, har nayi niyyan kashe wayan, amma kuma kaman wanda yake duba sai naji muryan shi a ɗan shaƙe yayi magana, "beauty na dawo gida, mummy ta ɗan tsayar da ni muna hira", ajiyan zuciya na ɗan sauƙe a hankali, sannan nace, "bakayi wayan ba kenan"? Shiru yayi kaman mai tunani, don shi gaskiya a gefen shi ya manta da maganan wata da yayi bayan Eeahan shi, chan kuma abun ya faɗo mishi a rai yace, "ni na isa na ƙira wata bayan na miki alƙawarin ke zan ƙira? Heedayah ma tana gaishe ni nayi kaman ban san tana wurin ba, ganin haka itama tayi ta kanta". Dariya ne ya suɓuce mun, "ni fa bance maka har da sisters ɗinka kada ka kula ba", na faɗa ina riƙe dariya na, don yanayin yadda yayi maganan ya sakani dariya, "ok tou nagane, banda su heedayah, tou ƙirgamun wanda baki son na dinga kula su beautyn A.G". Gyara kwanciya na nayi nace, "wannan yarinyar da friend ɗinta", ina jin shi yace, "one", Murmushi nayi nace ko wacce mace idan ba ƴan gidanku ba ko kuma tsufaffi, har ƴan office ɗinku", ina gama faɗa na saka hannu na toshe bakina, "insha Allahu zan kiyaye beauty, sai dai ina neman alfarma guda ɗaya a wurinki", ya faɗa da mugun nutsuwa a muryan shi, ban amsa mishi ba naji yafara mun bayani, "Eesha ni mai tsare kaina ne sosai, kuma zan ƙara fiye da yadda nake a baya, ni lawyer ne dole wasu matan zasu neme ni akan damuwan su, insha Allahu na miki alƙawari daga abunda ya haɗani da su babu wani abu da zai biyu baya, sannan Ina da family both side, mummy da daddy nah, kuma akwai mata, insha Allahu zan tsaya dai dai da yadda shari'a ya umurce mu dayi, wata mace insha Allahu bazata ga dariya na ko murmushi naba idan bake ba, sai dai a bisa kuskure, zan tsare miki kaina yadda bakiyi zato ba, amma kema bana son ki kula ko wanni saurayi please." Wani irin nutsuwa ne yazo mun a zuciyata, wanda bansan meye dalili ba, "ni ae bana kula samari, ni basu ma burgeni," na faɗa ƙasa-ƙasa da murya, "amma dai ni ina burge ki ko"? Naji muryan shi yana tambaya na, runtse ido na nayi, sannan nace, "ni tausayinka kawai nakeji". "Alhamdulillah" naji ya faɗa, sannan kuma naji yace, "Eesha kin gama mun komai a rayuwata, duk macen da take tausayinka tou ba ƙaramin so zata maka ba, Allah na gode maka", ya faɗa da ɗan ɗaga muryah. Zaro ido nayi ina rufe bakina da hannu ɗaya, "nifa ciwon kanne yake sani tausayi bawai sonka.....", sai kuma nakasa ƙarasawa, saboda yau ɗaya kawai naji ina jin kunyan nace bana son shi, haka dai mukayi ta hira wanda bansan ma 12:00 am yayi ba, sai da naji yace nayi haƙuri ya jani muna hira har 12, sallama mukayi kowa ya kashe wayan shi.
******** Washe gari yazo amma a parlon hajiya ummah muka zauna, sallama ya mun akan gobe zai wuce Abuja, don tanan zai tashi, yau banji yana jana da hira ba kawai shiru yayi ya ƙura mun ido, har narasa yadda zanyi da kallonshi, duk ɗago kaima kuma sai ya ɗaga mun giran shi sama, haka dai har 9:00 tayi sai yace nayiwa hajiya umma magana suyi sallama zai tafi gida, tashi nayi naje ɗakin na mata magana, sallama sukayi tana ta saka mishi albarka, da alƙawarurruka Kaman itace mai auren shi, bunch na 500 ya ajiye mata ya fice, tana ta zabga mishi addu'a, nidai nabi bayan shi, muna fita yace muje yayiwa ummie sallama, haka naja tsummukaran ƙafana jiki a sanyayae na raka shi har parlonta, suna tare da hafsy da yayah Ahmad, hannu ya miƙawa yayah suka gaisa, sannan ya gaishe da ummie, nidai gefen hafsy naje na zauna kaina a ƙasa, hira suka ɗan taɓa kaɗan, sannan yayiwa ummie sallama akan gobe zasu wuce tare da yayah Ahmad, flight na ƙarfe 9:00am zasu bi, hafsy ya ƙira sukayi waje, chan sai gata ta dawo, hannunta riƙe da envelop an saka 100k wa ummie, sannan tace mun naje yana jirana a waje, ni dai tashi nayi na fice, ina jin ummie nayiwa hafsy faɗan meyasa ta karɓo, ita kuma tana cewa, ko da wa ita yabayar karɓewa zatayi wallahi, tana faɗa tana dariya abunta, haka dai na wuce nayi waje.
A jikin motan na tsaya hannu na riƙe da murfin motan, shi kuma yana zaune a driver sit, ƙafan shi ɗaya a waje ɗaya a ciki, hannun shi akan stearing motan, dukka ida nun she a zube a kaina, munyi shiru babu wanda ya tanka a cikin mu, chan dai nayi ƙarfin hali nace, "kana ta hidima dasu ummie da hajiya ummah, an gode Allah ya ƙara buɗi", baice uffan ba sai ido dai da yaci gaba da zuba mun su, ɗago kaina nayi muka haɗa ido da shi, "Beauty zakiyi mssn ɗina"? kawai naji ya faɗa ido a lumlumshe, Girgiza kai nayi alaman a'a, da sauri ya daga kanshi yace, "shiyasa nakeso nayiwa yarinyar nan tambayan gaskiya, idan ta amsa mun kawai zanyi haƙuri na amsheta". "tambayan me zaka mata"? Na tambaye shi, "ko da gaske tana sona, idan har da gaske ne zan bawa kaina haƙuri kawai ayi da ita", ya faɗa yana wani ya mutsa fuska, sama na ɗaga kaina kawai ia kallon taurari, batare da na sauƙe kaina ba nace, "idan ta amsa maka kuma zaka sota? Bayan kache mun bazaka sake kula wata mace ba"? Kallona na mayar kanshi jin yace, "tou ae kene beauty, ni so nake kawai a soni, ke kuma kin nuƙe kin ƙi ki soni", ya faɗa idon shi na kaina, idona cikin nashi ina jin yadda zuciyata take wani irin mugun harbawa, a hankali na ɗauke kaina saboda yadda nake jin wani irin yanayi idan muna kallon juna, baki na tura gaba nace, "tou ni dai bama son kayi magana da ita, bana son ma ka koma school ɗin", "tou please Eeshaa ki soni", ya faɗa kanshi tsaye, shiru nayi ina tunani, chan kuma sai nace, "shine zai saka bazaka so wata ba" ido na akan shi, lumshe ido yayi ya ɗan ɗaga mun kai alaman ehh, "tou zanyi tunani, amma..... Sai kuma nayi shiru ganin Yayah Ahmad ya fito, ƙurawa Yayah Ahmad ido nayi, _Sai da ya Kusa isowa inda muke sai nayiwa A.G sallama na wuce, anan suka ɗan tsaya kaɗan, sai kuma naji tashin motan kowan su.
Washe gari suka wuce Abuja, zuwa dare kuma jirgin su A.G ya ɗaga, kafin ya wuce ya ƙirani munyi waya, washe garin ranan tafiyan shi kuma ya ƙirani wuraren ƙarfe shida na asuba akan sun isa lpy, daga wannan ranan kullum sau biyu a rana sai munyi waya da shi, wataran ma sau uku zuwa huɗu, amma bamu wani dogon hira da shi, M.G kuma shiru banji ko sau ɗaya ya ƙirano a waya ba, nima haka sai na share shi.
********* Kwanci tashi asaran mai rai haka dai rayuwa ta lula damu har december, har satin bikin raliya, wanda har zuwa lokacin mamie bata san da maganan aure na ba, ana sauran 2weeks auren raliya kuma Aunty j ta haihu, itama ɗa namiji aka samu, wanda yaci sunan Yayah Auwal, wato *MUHAMMAD AUWAL* amma suna ƙiran shi da Affan, a zuwan mu sunane nasan M.G yana ƙasan yana Abuja abun shi, domin ranan sunan ma hafsy tace mun sun haɗu da shi, yace ta gaishe ni suna saurine zasu fita da yayah, nidai naji haushi, saboda meyasa M.G ya wani ƙaurace mun, babu waya babu ziyara, gaskiya Alƙawari baice haka ba, haka dai nima na share batun shi, mun dawo kuma bikin raliya.
Mudai babu ruwan mu da wani rawan kan bikin, yayun mi dai duk sunzo daga Abuja, kuma har da Aunty B da Areef, maijego kawai aka bari da wata ƴar'uwar ta, Adda ma tazo, Auntƴ ma'u ma tazo, gida dai ya cika da dangi sosai, ranan da za'ayi walima, da safe hadiza suka zo da ƴan'uwa na chan, zuwan tane ma ta jani muka shiga side ɗin mamie, anan naga habiba, tayi wani irin ƙiba, ga cikin ya fito sosai, tana zaune a ƙasa tana shan kankana, gaisawa sukayi da hadiza, ni kuma ta kalleni fuskan ta ɗauke da fara'a, murmushi na mata, itama ta maida mun da gaggawa, sannan naga ta kalli gefen da mamin ta take zaune, ganin bata ganinta sai ta mum alaman nazo nasha kankanan, murmushi nayi na mata alamamn na gode tasha kawai, haka dai tayita ƙureni da idon ta, har muka gama muka fita fatar bakin mu bai furtawa juna komai ba, tausayin ta cike da zuciyata. A haraban gidan mu akayi haɗaɗɗen walima, wanda yafi na habiba ƙayatuwa, amaryah tasha kyau sosai, tayi shiganta mai kyau, sit ɗaya muka zauna da ni da hadiza da maryam, domin tazo mana, hafsy da ummita suna chan cikin friends, don raliya bata tsoron mamie irin habiba, ita da taga bikinta ya matso kusa sai ta jawo hafsy ajiki suka cigaba da sha'anin su, duk ɗaga kna da zanyi sai mun haɗa ido da habiba, kuma sai ta mun murmushi, nia sai na mayar mata, har magrib tukun aka watse, washe gari aka ɗaura aure, akayi wuni, bayan la'asaar aka kai amaryah ɗakinta, naji ance bayan 1week zasu koma kaduna da mijin, don achan yake da zama, mudai washe gari muka bi Adda da Aunty ma'u muka ga gidan amaryah, gida yayi kyau sosai, don da muka fito naji Adda da Aunty ma'u suma hiran wannan karon mamie ta samu yadda ta keso, don Abba ya sakar mata kuɗi sosai bakaman na habiba, shiyasa tayi bushashanta son ranta.
Rayuwa tana ta jan mu da gudu har muƙa shiga watan Febuary, wanda yana daidai da saura 2month A.G ya gama ya dawo, alokacin idan kin kalli habiba sai ta baki tausayi, duk haskenta ya ƙaru tayi bauu ga kumburi da ƙafafunta da jikinta gaba ɗaya sukayi, wata ranan laraba ta tashi da wani azababben naƙuda, mamie har side ɗin ummie ta shigo ranan a ruɗe ta gaya mata, haka aka ɗunguma akayi asibiti da ita, *RIMI CLINIC* Mamie da iyalenta suke zuwa, saboda haka chan suka nufa, bayan ummie ta umurce mu da mu ɗaura abinci nida hafsy, babu nutsuwa a tare dani muka shiga kitchen ɗaura abincin, chan wayan A.G ya shigo, a tsatstsaye na ɗauka na mishi bayanin aiki nakeyi, a cikin muryana ya fahimci akwai matsalah, tambaya nayi me yake faruwa, nan na gaya mishi habiba ce zata haihu, kuma tana shan wahala, rarrashi na yayi da kalamai masu daɗi, inda har yake ce mun saura mu, nida shi, yasan shikan duk ranan da zan haihu sai an mishi Alluran bacci, dariya nayi na mishi sallama. Wuraren 12:00 mun gama haɗa komai, hattah flask da akace mu sake cika guda biyu mun cika, driver ne ya ɗauke mu tare da mahma muka bi bayan su, isan mu kuma babu wuya akace Abba ma ya taso daga Abuja yana hanya shi da yayah Auwal, har ɗakin da take muka shiga muka duba ta, nidai sai da nayi hawaye irin wahalan da naga tana sha, mahma da ummie suna riƙe da ita akan tasha ruwan ɗumi, ita kuma mamie tana tsaye daga bakin ƙofa, idan anjima kaɗan kuma ta fita tayi kiran waya, abu dai har wurin magrib babu haihuwa, ana haka Abba suka iso, bayan ya dubata ne suka shige office ɗin Dr don suji ko yayah ake ciki, nan Dr yace idan ta cika zuwa 8:00 bata haihu ba zasu mata C.S, haka su Abba suka wuce mosque sukayi sallah, har sai da sukayi ishaa tukun suka shigo, mu dai muna tsaye cirko -cirko a bakon ɗakin, shigan Abba bai daɗe ba naga mamah ta leƙo ta Ƙirani, jikina yana rawa nabi bayanta.
Muna shiga na kalli habiba rungume ajikin Abba tana kuka duk ta galabaita, "Abba na roƙeka ka umurci mamie ta bani izinin magana da ƴar'uwata kafin na bar duniya, Abba ina son magana da Ayshaa kafin na mutu, Abba mutuwa zanyi", ta faɗa tana ƙara kukan da takeyi, Abba ne ya dube ni sannan yace, "Ni nabaki daman kiyi magana da ƴar'uwarki, ae da nasan duk tsawon lokacin nan ta hanaki zumunci da ƴar'uwarki wallahi da na ɗauki mataki, kuma yanzu ma bai ɓaci ba zan ɗauka akan kowa, da wanda ta hana da wanda sun san an hana basu gaya mun ba, Allah dai ya sauƙe lafiya habiba nah".
Kallon mamie tayi cike da rauni tace, "mamie ki gafarce ni na mata magana"? Ɗaga mata kai tayi tana share hawayen ta, hannu habiba ta miƙo mun, ni kuwa ban ɓata lokaci ba na ƙarasa jikinta, rungumeta nayi hawaye na zuba a ido na, "sisto na kiyafe mun duk abunda ya faro, wallahi ɓa'a son raina nake ƙin kula ki ba umurni nake bi don na rabauta, amma kullu kina raina, ki yafebmun aure miki Aliyu da nayi sisto", hannu na nasaka na rufe bakinta hawaye na yana zuba babu kakkautawa, itama hannu ta saka ta riƙe nawa dana Abba tace, "Abba kazama shaidah duk abunda na haifa na bawa sisto duniya da lahira, idan mace ce a saka sunan sisto, idan kuma namiji ne sunan ka nake so Abba, ina kwaɗayin su yi rayuwa da halaye irin na ko, duk duniya babu abun da nake so irin kai da sisto na", sannan ta dawo da kanta kaina tace, "kicewa Aliyu na yafe mishi duk abunda ya mun duniya da lahira, kuma ku haɗu ku riƙe mun abunda zan haifa idan mai rai ne", azaban ciwo ne yasaka ta ɗan yunƙura kaman zata sauƙo, nan kuma likita ya shiga yace mu ɗan fita daga waje zai dubata.
Muna waje ina rungume ajikin Abba inata kuka yana rarrashina, gefe ɗaya kuma mamie ce ta sunkuya tana ta share hawaye ummi na bata baki, ita dai hafsy sunyi tagumi ita da mama da yayah auwal da hajiya ummu suna zaune a ɗan gefe kaɗan.
Muna nan har wurin 1hr likita bai fito ba, chan kuwa muka jiyo kukan jariri, wani zabura nayi zanyi ciki Abba ya riƙoni, ita ma mamie tashi tayi tsaye, sai Ummie ta hana ta shiga, duk jikima rawa yakeyi narasa murna nakeji ko kuma me nake ji, muna haka har bayan mintuna kusan ashirin sai ga nurse ɗaya ta fito hannun ta riƙe dababy a farin showel, da sauri na nufeta hannu na miƙa ita ma sai ta saka mun babyn fuskanta da fara'a, da sauri na buɗe ina kallon fuskan babyn mai tsananin kama da su jamilah, sai dai farine sosai kaman ƴan gidan mu, murmushi da fitan hawaye ne a fuskana, ina jin nurse ɗin tace an samu ɗa namiji, godiya wa ubangiji duk aka fara, Abba yana tambayan mai haihuwan fah, nan naji tace Dr yana duba ta, na daɗe ina kallon fuskan yaron ina jin wani irin ƙaunar shi a zuciyata, hannu Abba ya saka ya karɓi yaron, babu yadda na iya na miƙa mishi, addu'a ya mishi sosai, sannan ya miƙawa yayah Auwal yana zolayan su da nikan bazaku bani ƴar budurwa bane kam na cika ta huɗu? Kowa sai ya sulluɓu ƙaton saurayi munana, dariya su mamah sukayi suna mu ae haka yafi mana, ayita haiho mana mazaje, ita dai mamie dariyan yaƙe ne a fuskanta, amma duk hankalinta yana ga ɗakin da habiba take, yaron yana rie a hannun ummie Dr ya buɗe ɗakin da habiba take ya fito, Abba ya miƙa mishi hanni suka sake gaisuwa, Abba yana tambayan shi yaya jikin ita mai haihuwan? Share zufan goshin shi yayi sannan yace wa Abba, "Munyi iya ƙoƙarin mu mubata kariya ta haihu lpy, amma tana haihuwa wanda yafi mu sonta ya amshi abunshi, sai dai nace kuyi haƙuri wanda yafi mu son habiba ya amshi abun shi", nidai abu biyu kawai naji bayan magana shi, shine naji muryan mamie da ƙarfi tace, "Ƙarya kakeyi likita, habiba bana bata mutu ba", sannan naji muryan hajiya umma tana "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wannan wani irin mummunan labari ne"? Daga nan ban san me ake ciki ba, sai farkawa nayi na ganni a ɗakin ummi na akwance, gefe ɗaya kuma yayah Auwal ne yayi tagumi hafsy na gefen shi tana ta share hawaye, da hanzari na miƙe zaune nace, "Yayah mummunan mafarki nayi, ina ummie nah"? Riƙo ni yayi da yaga ina ƙoƙarin zurawa waje a guje, Yace "ina xakije Ayshaa"? Da sauri nace "zanje parlor ne ummie ta rakani na duba yayah habiba take, mafarkinta nayi wai ta haihu......", sai kuma naji tsoron Ƙarasa faɗin sauran, hafsy ne naji ta fashe da kuka ta taso ta rungume ni, "Adda ba mafarki bane da gaske kin rasa ƴar'uwar ki yau", kallonta nayi baki a buɗe nace, "kuma kinga ta haihu? Yaron namiji mai kama da su jamilah"? Ɗaga mun kai tayi tace, "Adda ae har kin ɗauki yaron ma kafin a faɗa mana rasuwan". Juyawa nayi na kalli yayah auwal, muryana yana rawa nace, "yayah rakani na ganta", hannu na ya riƙo muka fita har side ɗin mamie, muna shiga a parlor na hango mamah da sai hajiya umma a zaune a saman kujera, sai wasu daga cikin ƴan uwan Mamie a parlon, ga mahaifiyar mijin raliya da wasu daga maƙotan mu, daga ɗaki kuma ina jin sautin kukan mamie da ake ta bata haƙuri, ido na na mayar wurin dinn<ng ɗin mamie da aka matsar da kujerun aka kwantar da habiba a ƙasa, ga wasu ƴan'uwan mamie da suke zaune a gefen gawantan, juyawa nayi na kalli yayah Auwal bakina yana rawa ina nuna gawan habiba nace, "Habiba ce wannan yayah"? Ɗaga kai yayi alaman itace, "bakaga ana sanyi ba ne yayah aka kwantar da ita a ƙasa"? Hawaye na bin fuskana, bai amsa mun ba sai ya juya ya fice a parlon, ɗakin mamie na shige na tsaya a bakin ƙofan ina bin su da kallo, idon ummi yana kaina ni kuma ina raba ido na, chan na hango babyn a kwance akan gado, kallon mamie nayi da take ta kuka naji na ƙira sunan ta da ƙarfin da bansan murya na yana da shi ba, "mamie kinga abunda kikayi ko? Ashe ƴar'uwata bazata daɗe ba, bazamu goyi yaran mu tare ba? Kin raba mu, bayan tace mun duk ranan da ɗaya ya haihu zamu kwana muna kallon babyn mu saka suna mai daɗi, muyi wa junan mu takwara, mu so ƴaƴan, zata so nawa kaman nata, zan so nata kaman nawa, amma kin raba mu, ashe ma Allah a kusa zai raba tsakanin mu, kukan me kikeyi? Nice nan kuka ya same ni", na faɗa ina buga kƙirjina, da gudu mamie ta taso ta rungume ni tace, "dukkanmu kuka ya same mu Aysha", runtse ido nayi saboda kukan da naji babyn yana yi, juyawa nayi na fita zuwa parlor, direct wurin gawan habiba na nufa.
A gaban gawan ƴar'uwata habiba na durƙusa, hannuna toshe da bakina, saboda bana son yi mata kuka akan gawanta, hannu nasaka na yaye mayafin da aka rufe fuskanta da shi, kyakkyawar fuskanta mai kama da na Abban mu shinfiɗe da annuri, ga wani fari da tayi na alaman babu jini a jikinta, fuskanta a ɗan kumbure kaɗan, wani abu ne naji ya bugi zuciyana, sai na dinga tunata a yadda muke da kafin komai ya lalace a tsakanin mu, wai yau habiba ce shimfiɗe a gabana tazama gawa? Duk sai naji nakasa riƙe kaina, ina kuka ina mata addu'a, har wani lokaci aka zo aka mata wanka aka shiryata, duk dai ina wurin, addu'a Abba ya shigo yayi mata, ranan dai kwana mukayi a zaune babu wanda ya samu daman runtsawa. Washe gari dukkan yayun mu sun iso, yayah umar ne kawai ba'a bar shi yazo ba, zuwa lokacin duk nayi laushi bana iya komai sai dai hawayen da yake zuba mun, ina ganin mama tayi wanka a babyn habiba, ta bashi madaran da tun jiya ummie ta aika aka sayo da su glucose, ana bashi madaran hafsy ta goya shi a bayanta, ita dai mamie babu abun da take iya taɓukawa, wuraren tara na safe raliya suka iso, inaga daga ita har su yayan mu ko da asuba suka kamo hanya oho, shigowan ta ne ya sake hargitsa mu, domin rungume gawan tayi tana kua kaman ranta zai fita da ƙyar yayah muhammad yajata zuwa ɗakin mamie, ganin su ya saka mamin sake fashewa da kuka, shima yayah muhammad kukan ya fashe da shi yana zama a bakin gadonta. Ana shirin fita da ita ƙarfe goma saura, sai ga Abba sun shigo tare da Aliyu, har gaban gawan Abba ya rakashi, ina kallon shi cike da jin haushin shi, yana ta share hawaye hannun shi riƙe da hanky, addu'a sosai ya mata, sannan naji yana cewa "habiba na yafe miki, Allah ya miki rahma, ya raya abunda kika bari, haƙurin ki da halayenki nagari, ya miki jagora har cikin aljannatul firdausi" daga nan ya fashe da kuka, har sai da Abba ya umurci yayah Ahmad ya fita da shi, gefe ɗaya kuma Mummyn shi ce zaune da wasu daga cikin ƴan'uwan shi mata, Addu'a sosai Abba yayiwa habiba shi da wani abokin shi da yayan mamie, Abba ya ƙurawa gawan ido na wani lokaci sannan yace, "haƙiƙah mutuwa xafin ta nada ciwo, mutuwa irin na ƙuruciya, habiba Allah ya gafarta miki, Allah ya baki ikon amsa tambayoyi, Allah yasa kinyi shahada, ni Usman mahaifinki na yafe miki duniya da lahira, ballantana ma baki mun komai ba, haƙuri da son zumunci duk naki ne habiba, Allah yasa kin huta," juyowa yayi idon shi akaina yace, "Aysha Allah ya ƙara miki haƙuri, tabbas kinyi rashin masoyiya, kinyi rashin twin sister ki", ta shi nayi da gudu na rungume Abba ina kuka, shima Abban kukan yakeyi, da ƙyar aka riƙeni lokacin da naga ana ɗaukan gawanta, yayuna ne da Aliyu da wasu daga dangin mu suka ɗauke ta, nidai farkawa nayi na sake ganina a ɗakin hajiya ummah, wato suna na sakeyi da aka fita da habiba.
Hawaye nima na share, ganin yadda Aysha take kuka kaman a yanzu ne aka mata wannan rashin, jikina duk a sanyaye na miƙa mata ruwa, karɓa tayi tasha sosai, sannan ta dube ni da idonta da suka chanja kala, tsabar rinewa da sukayi saboda kuka, "Aunty nice rasuwar habiba yana daga cikin mutuwa masu ciwo da aka mun a rayuwata, naji ciwon rashin ƴar'uwata, naji ciwon rashin masoyiyata, har gobe ina kokawa wannan mutuwan", ajiyan zuciya nayi na kalleta, "hajjaju ae mutuwace mai ciwo, rashin ɗan'uwa ae babban rashine, ballantana ke zafin har da raba tsakanin ku da akayi, Allah ya mata rahma", na faɗa, "Ameen ya rabbi, nagode Aunty nice, naji an fara ƙiran sallah, bari mu tashi muyi sallah, sai mu cigaba kafin nan ma zuciyata ta ɗan yi sanyi", miƙewa nayi na mata jagora har bedroom ɗina, tana shiga toilet na shimfiɗa mata sallaya na fice.
Bayan ta idar da sallah ne na kawo mata abinci, fuskan ta ɗauke da murmushi tace, "Aunty nice abincin nan zai samu shiga kuwa"? Nima murmishin nayi nace, "ae ko idan bakici ba bazan ji daɗi ba, gara ko kaɗan ne ki taɓa nasan dai kinci", Rausayar da kanta tayi sannan ta jawo coolern abincin ta zuba kaɗan, nidai bance mata uffan ba, don halin da take cike Allah ne kawai ya bar wa kanshi sani, fuskanta da murmushi ta dubeni, "tare zamuci ko"? Murmushi nayi na gyara zama mukaci taren, bawai don ina jin yunwa ba, kawai dai ta samu sukunin ci, muna gamawa na tattare komai, wannan lokacin a ɗaki muka zauna, tana duba na da murmushi a fuskanta ta cigaba.
Bayan na tashi zaune na muka haɗa ido da Aunty Rakiya, Zama tayi a gefe na , "sannu Ayshaa, sannu ko", naji tana ta jero mun, ido na sun mun wani nauyi na riƙo hannunta, "Aunty an binne habiba ko"? Na faɗa idona suna zubar da hawaye masu zafin gaske, hawayen ta share itama, bata ce mun uffun ba ta jawoni kawai ta rungume, munyi kuka ba kaɗan ba, har zuwa wani lokaci tukun ta tashi ta haɗa mun ruwa mai zafi tace na shiga nayi wanka, bayan nayi wanka nayi brush, na ɗauro alwala na fito, tea mai zafi ta miƙa mun, kaɗa kai nayi alaman bazan sha ba, harara na tayi ta ɗaure fuskanta tace, "maza karɓa ki shanye ki bani cup ɗin," ganin fuskanta ya saka na karɓa ina hawaye na shanye, ina sha kuwa cikina naji yana wani uban kuka, haka dai na miƙa mata cup ɗin, sannan na wuce na saka kaya, chan ta dawo tace mu fita parlor. Duk familyn su Abban mu suna zaune a parlor tare da hajiya ummah da taci kuka kaman yayah, sai cewa take, "usmanu na an mishi mutuwa, usmanu yayi rashi", haka dai duk muka gaisa dasu ina ta daurewa, amma kukan da hajiya ummah ta fashe da shine ya sakani sake fashewa da kukan, da ƙyar aka rarrashe mu, sannan na wuce parlon ummie na, achan na samu so zainab, hadiza, hafsy, ummtah da maryam da tun safe tazo, gefe ɗaya kuma Aunty B ne zaune tare da su Aunty j, gaisuwa mukayi sannan na wuce wurin ummie na, akan gadon ta na zauna gefenta, ɗago kai nayi don na gaisheta amma muna haɗa ido kawao sai na kasa, rungumeta nayi ina kuka, kuka mai ciwo da zafi nakeyi, bata hanani ba sai buga baya na da takeyi a hankali, da ƙyar nan ma Goggo maman zainab ta rarrashe ni, ban fita parlon ba sai na naɗe a jikin ummie kawai na kwanta, a hankali ina share hawayen da suka kasa tsayuwa.
Muna idar da sallan magarib muna zaune dukkan mu a parlon ummie, sai ga Yayah Ahmad da M.G sun shigo tare, nidai kallo ɗaya na musu na maida kaina ƙasa na cigaba da jan chasbi na, ummie aka ƙira suka gaisa, sannan ya matso har inda nake ya ambaci sunana, ban iya na amsa mishi ba sai kukan da naji kawai yazo mun, wanda ban san meyasa ba ko sunana aka ƙira sai dai naji kuka yazo mun, wai habiba dai, habiba tawa ce babu yau a duniya? Wayyo Allah mutuwa, ashe haka ciwon ta yake? Haƙuri sosai ya dinga bani, bayan ya mun gaisuwa, sannan yace mun Goggo tana mun gaisuwa insha Allahu gobe zasu shigo tare da Mummyn A.G, kai kawai na ɗaga mishi alaman amsawa, amma ban ɗago Kaina na dube shi ba, ya daɗe a wurin kafin ya miƙe ya fice.