Kenza eBookz

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 20

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 20

Ana barin halal original by anty nice Chapter 20: Ana barin halal original by anty nice Chapter 20. Washe gari kuwa su mummyn A.G suka zo, macece ƴar gayun…

4,440 words

Washe gari kuwa su mummyn A.G suka zo, macece ƴar gayun gaske, duk da ta fara nanyanta amma bazaki taɓa cewa ta haifi A.G ba, Abaya ce a jikinta baƙa marar kwalliya, sai glass fari a manne a idonta, daga gani na ƙara ƙarfin kallo ne, gefe ɗaya kuma Goggo ce, farar bafulatana, ita ta zama dattijuwa, duk da girma ya kama goggo amma akwai farin fatan nan da kyaun fuska, daga ganin ta macece da lokacin ƙuruciya tayi jiki da tsayi, masha Allah, yau kam naga inda M.G ya samo kyaun shin nan, don babu ƙarya Matar akwai kyau, ga fara'a, mummy ko ina ganin idon ta sai da na runtse nawa idon, da sauri na sunkuyar da kaina ƙasa, domin sai naga kaman idon ,A.G na kallah, duk da Mummy baƙace, amma kyakkyawar mace ce, ga ido kaman wanda ta cire nata ta mannawa A.G, hattah lumshewan da yake dashi irin nata ne, sai dai hala farin fatan shi na mahaifin shine, doguwace kuma bata da wani jiki sosai, gefe ɗaya kuma Heedayah ce, itama kyakkyawa ce amma dai bata kama ƙafan A.G ba, duk da dai suna kama da A.G, amma ita bata kai shi fari sosai ba, amma sunyi kama, don hattah idonta irin na Mummy ne, irin na shi, haka kawai naji haushinta a zuciyata, wato akan wannan M.G ya share ni ko waya baya mun, sai naji bana son kallon fuskanta.

Bayan mun gaisa da sune dukkan mu a parlon ummie, sai mummy take miƙo mun wayanta, "Ga A.G ko dougter", a kunya ce na karɓi wayan, "Eesha sannu ko, sorry beauty, sannu da rashin da aka mana, wayan ki akashe tun ranan bana samunki, M.G kuma yace mun yazo kina ta kuka shiyasa ya kasa haɗamu, kiyi haƙuri Eesha, addu'a take buƙata, Allah ya jiƙanta ya raya abunda aka bari,", ina jin muryan shi sai naji rauni na ya ƙaru, hawaye kuma suka soma mun sintiri, ban san lokacin da bakina ya ambaci sunan shi ba, amma murya chan ƙasa wanda nayi imanin ko maryam da ta ke gefe na bata iya jiyo maganana, "A.G na rasa habiba, ta tafi ta barni da amanan babynta, bansan yaya zanyi na bashi kula ba, bansan yayah zanyi da ciwon rashinta ba, kadawo please", na faɗa sautin kuka na yana fita, a hankali naji hannun mummy shi ta rungumo ni jikinta, shi kuma daga wayan naji yana magana, haƙuri yake ta bani kaman zai mun kuka, a haka na miƙawa mummy wayan ina ƙara fashewa da kuka, rungumeni tayi sosai tana rarrashina, gefe ɗaya kuma su hafsy suna ta share hawayen su.

Ranan uku su Aliyu suka shigo bayan anyi addu'a tare da Yayah Ahmad da su M.G, ashe kullum da su ake zama bansani ba, sai lokacin naji su Aunty B suna faɗa, akan yadda Aliyu yayi laushi sai kuka yakeyi, hattah mummyn su jammy rasuwar ta bugata, gashi ƙannen mamie naji fir sunƙi basu yaron su gani, ganin kada abu yazama abun magana Mummyn ta share bata tanka musu ba, hatta Aliyun sun hanashi har sai da Abba ya musu jan ido tukun aka miƙa mishi ya mishi huɗuba ya mishi addu'a, tunda na ɗaga ido muka haɗa ido da su ban ƙara ɗaga kaina ba, don ko gaishe mu da sukayi idona yana ƙasa, kuma a washe gari M.G ya tafi, don naji Yayah Ahmad yana gayawa Ummie M.G zai koma gobe insha Allahu.

Nidai banje naga babyn ba sai ranan da akayi bakwai, wato ranan da aka raɗa mishi suna, kuma yaro yaci sunan Abba wato *USMAN* nan ma sai bayan magrib na shiga side ɗin mamie, wanda tun ranan da akayi rasuwan ban ƙara marmarin shiga ba, haka na daure muka shiga tare da su Aunty B, domin zasu mata sallama gobe zasu wuce idan Allah ya kaimu, zama nayi a ƙasan carpet da muka shiga parlon mamie, don dukkansu suna zaune a parlon, yaron yana hannun raliya tana bashi madara, kallo ɗaya na mishi na kawar da kaina, nayi-nayi na iya buɗe baki na gaida mamie amma na kasa, har sai da ita don kanta ta miƙo mun hannu, kuka naji yazo mun, wanda itama kukan ta fara, sannan raliya ta miƙo mun babyn tana cewa, "Adda gashi ki mishi addu'a ki zaɓa mishi sunan da za'a ƙira shi da shi," ta faɗa hawaye yana bin fuskanta, "wato Aunty nice idan kikaga mamie da raliya a lokacin zakiyi zaton har abada duk wani gaba yaƙare a tsakanin mu, amma ina kibar zuciyar da babu Allah a cikinta, " hannu na saka na amshi babyn da ya buɗe idon shi tar yana kallo, babu abun da yabari na kamanni da mahaifin shi, hatta baƙin fatan na Aliyu ne, don duk da jariri ne bai yi wani fari ba, ido na zuba ina ƙare mishi kallo, gefe ɗaya wani ƙaunar shi da tausayin shi na cika zuciyata, "SABEER" na ambace shi da shi muryana yana ɗan rawa, kuka mamie ta sake fashewa da shi tana furta, "Allah yasa ƙazamo mai haƙurin irin mahaifiyarka, Allah yasa ka amsa wannan sunan ɗan albarka", miƙewa nayi da shi a hannuna har gaban mamie, ƙasa na durƙusa na furta, "Mamie ki amince na tafi da shi don cika umirnin sisto", bata bani amsa ba sai sunkuyar da kanta da tayi ƙasa tana share hawaye, yayarta ce ta bani amsa da, "Aysha kiyi haƙuri ya ɗan ƙara tasawa, sai ki karɓe shi, yanzu idan ya tashi kuka da dare yayah zakiyi?" ido na ƙura mata bance komai ba, amma abun mamaki sai naji muryan mamie tace, "ta tafi da shi tunda ae ba nono za'a bashi ba, kuma nayi imamo da Allah ummie zata taimaka mata", tana rufe baki mahaifiyarta ta amsa da "a'a bazaiyiwu ace yarinya ƙarama ta riƙe ba, kawai ta dinga zuwa da safe tana amsan shi, amma bamda a tattara shi a miƙa mata, ke mai zaki gani zuciyarki tayi sanyi bayan shi"? Ta faɗa tana kawar da kanta gefe, babu musu na miƙa shi hannun sister mamie muka musi sallama muka fice a parlon.

Kullum safe kuwa sai na shiga side ɗin mamie na ɗauko ɗana, gashi mai haƙuri baida rikici, wuni mukeyi tare da shi, har su raliya suka koma kaduna, idan zanje makaranta ne kawai na kan bar shi hannun mamie, wataran ma mamah ce ko ummie suke riƙe shi, ita dai mamie har zuwa lokacin a sanyaye take.

Habiba tayi arba'in aka raba gadon abun da ta bari, sannan a ranan Aliyu da iyayen shi suka sake zuwa gidan mu gaishe da su Abba, a wannan ranan kam an bar su sun ɗauki sabeer, don har video call sukayi da jammy, duk da munsha video call tana ganin shi, Aunty nice zaki sha mamaki idan nace miki sanadin yaron nan har video call munayi da A.G? Murmushi nayi ina kallonta cike da mamaki, itama murmushin tayi ta cigaba da bani labari.

Ranan farko da muka fara, na dawo daga sch yana ta kuka, an rasa me ya same shi, sai na ɗauke shi inata jijjiga shi, lokacin wayan A.G ya shigo, a rikice na ɗauka, jin kukan da sabeer yakeyi yasa yace bari ya ƙirani video call ya rarrashe shi, hummm abun mamaki indai akan ɗa nane zan iya komai, ae babu shiri na ɗauki wayan da ya sake ƙirana video call, duk nayi sukuku doni, matso mishi da fuskam sabeer nayi, shi kuma yanata rarrashi, ranan naga ikon Allah kawai sai yaro yayi shiru yanata sauƙe ajiyan zuciya, murmushi A.G yayi yace, "yarona yana missing ɗinane, ko kuma Ammin shi bata iya bashi kulawa ba, yafi son na Abbin shi", tura baki nayi cike da shagwaɓa, sanan ya umurce ni na saka mishi yatsa a baki , ina saka mishi kuwa ya riƙe yana tsotsa idon shi a kaina, a haka har yayi bacci, ajiyan zuciya na sauƙe na maida kallona kan A.G, ido ya kashe mun yana murmushi, "yakamata na dawo na baku kulawa sosai ke da ɗanmu, don naga wannan rikicin uwa da ɗan duk A.G ne zai iya shanyewa," Murmushi na mishi lokacin, sannan nace, "saura kwana nawa kadawo"? Idon shi cikin nawa yace, "saura 2weeks oum sabeer", daɗi nake ji idan ya ƙirani da wannan sunan, amma sai na wani harare shi, dariya ya ɗanyi. Lokacin da su Aliyu suka zo da mummyn shi takeyiwa Ummie maganan ya kamata su turo manya akan maganan Aliyu, ita dai Ummie bata ce komai ba sai murmushi da tayi, bata kuma gayawa kowa yadda akayi ba har bayan sati biyu da maganan, ana saura 2dys A.G ya dawo, iyayen Aliyu suka zo wurin Abba da maganan Aliyu ya dawo da maganana, a haka ma basu san da wasiyan Habiba, kawai da so da ƙauna da Aliyu yake mun da iyayen shi ne, anyi dace kuma ranan da sukazo Yayah Muhammad yana nan, don yazo weƙend.

Bayan Abba ya gama sauraron su sai yayi murmushi ya gyara zama, "ALHAMDULILLAHI Naji daɗin wannan batu na ku, don duk inda akace ƴar'uwa ta rasu tou daɗin zama ya kansa a sake neman auren ƴar'uwarta, duk da ansamu saɓani a tsakanin su har ta kai ga batun saki, tou naji daɗin zuwan ku, don alama ya nuna Habiba ɗiyata bata zalunci ɗanku Aliyu ba a zaman takewar su, don nayi imani da Allah da ace ta zalunce shi ko ta cutar da ku, babu wanda zanga ƙafan shi a ƙofar gidana don neman auren ɗaya daga cikin ƴaƴana," gƴaɗa kai kawai iyayen Aliyu sukeyi, Abba ya cigaba bayan yabi kowan su da kallo, "Habiba, Ayshaa duk abu ɗaya ne yayi su sannan ƴaƴa nane mafi soyuwa a zuciyana, sanadin halayen su Allah ya saka mun ƙaunar su a zuciyata, yara ne dattawa, masu haƙuri, yarah ne masu albarka, Allah ya jiƙan habiba", Abba ya faɗa da wani yanayi a fuskan shi na jimami, "Kunzo da maganar neman auren ƴar'iwarta, wanda da ko ba ayi zaman lafiya ba Albarkacin wannan jariri zan iya amincewa da buƙatanku, tou amma gaskiya banji daɗin riƙon da Aliyu da ku iyayen shi kukayi wa habiba, tabbas banji daɗi ba, amma komai ya wuce zamuyi zumunci a tsakanin mu ko dan albarkacin wannan jariri, amma maganan aure da Ayshaa abune ba mai yiwuba, don a yanzu akwai maganan aurenta da wani yarona, har an saka rana, kunga kuwa duk dattijon arziki baya magana biyu", Abba yana kaiwa nan ya miƙa musu hannu suka sake gaisawa, sannan yace su gayawa Aliyu duk lokacin da yaji yazo ko shi ko iyayen shi da ƴan'uwanshi ganin yaro ƙofa a buɗe take, amma maganan bashi ɗa kuma kada ya saka a ranshi, don ya wufantar mun da ƴa da abinda ke cikinta, bai san lafiyan su da komai da suke ciki ba har sai da Allah yayi ikon shi tukun na gan shi gidan nan, bawai na riƙe shi bane a zuciyata, a'a kawai zanyi abun da nake ga shine dai-dai, nagode da zuwanku neman sake haɗa iri dani a karo na biyu".

A kunyace ɗaya daga cikin ƙanin baban su Aliyu ya ɗan risina yana yiwa Abba godiya, sannan dukkansu suka sake bawa Abba haƙurin abunda ya faru, don gaskiya ne sun san basu kyauta ba, lokacin da Aliyu yayi saki babu wanda ya biyo bayan habiba, haka dai suka fita duk jiki a sanyaye, Gida suka wuce wurin mummy, bayani dalla -dallah suka mata, gaba ɗaya ran mummy ya ɓaci, a fusace tace, "tou ae dama tun farko Aliyu baice yana son habiba ba, kuma bamuce habiba tana da aibu ba, kawai naƙita saboda halin mahaifiyar ta ne, don Aliyu ba'a hayyacin shi ya furta ya amince da auren ta ba, kuma lokacin da ya dawo hayyacin shi ya nuna baya sonta, amma ae dana san habiba tana raya baza'a taɓa barin ya auri ayshaa ba ae ban nuna komai ba, amma da habiba ta rasu sai naga akwai dama da Aliyu zai maye gurbin habiba da ƴar'uwarta, wanda dama tun farko itace zaɓin mu da shi baki ɗaya", cikin ɓacin rai ta ƙarasa maganan, su dai haƙuri suka bata suka tashi suka fice, cike da ɓacen rai ta ƙira Aliyu ta zayyane mish komai, dama yayi tafiya baya gari, "mummy wani maganan aure aka tsayarwa Ayshaa da shi? Kawai munafurcin uwar habiba ne ta hana komai, ki ƙira ita ummie kiji komai daga gareta", sallama sukayi mummy ta ƙira ummie a lokacin, nan dai ummie tayi namijin ƙoƙarin sanarwa mummy akwai maganan aure akaina, wanda zan aura ma cikin satin nan zai gama ya dawo, "duk da haka dai ummin su a duba al'amarin Aliyu, yana son Ayshaa sosai fah, kuma ashirye yake daya haƙura da wancan maganan auren idan Ayshaa zata amince," Murmushi ummie tayi tace, "gaskiya koda zai auri ayshaa bazan so a fasa maganan auren shi da yarinyar da ta ke matsayin ƴa a wurinki ba, ga magana kuma yayi nisa, kawai dai mu ƙara addu'a, Allah ya zaɓa abunda yafi alkhairi a tsakani", badon mummy taso ba tayi sallama da ummie akan idan Aliyu ya dawo zaizo ya samu ayshaa suyi magana a tsakanin su.

Zuwa dare Abba ya ƙiramu nida ummie zuwa parlon hajiya ummah, achan muka same su harda yayah muhammad, nan Abba ya gaya mana yadda sukayi da iyayen Aliyu, kuma ya sake jaddada bai hana Aliyu yazo ya ga ɗanshi ba, amma su yayah muhammad su zama shaidah har abada bazai bashi riƙon yaron habiba ba, dom sakamakon izayan da suka yiwa habiba kenan, nan hajiya ummah ta tafka salati hannu riƙe da bakinta tace, "amma dai Aliyu da iyayen shi anyi sokayen banza, yoo sokaye mana, ku wahar da habiban don babu kunya a idonku kuzo kuma neman auren ƴar'uwarta? Da shegen baƙar fuska kaman na boss ɗin indian film ya kwaso ƙafa yana zabgegen bazawari yace Ayshaa budurwa wanda zata auri saurayi yake so? Tou haram wannan shirmen ba'a gidan Usmanu na ba, don ko Gwamnah ne mahaifin shi bai isa yaja da kai ba usmanu, nera yafi ka ko suna a gari"? Dariya ne ya kubcewa yayah muhammad yace, "ballantana ma besty kam bata son wani Ali black, A.G ɗinta kawai tace sai shi, bawai don farin fuska bako besty"? Ya faɗa yana duba na da murmushi a fuskan shi, sunkuyar da fuskana nayi ina duban fuskan Sabeer da yake rungume akan cinyata yana bacci, ido na ƙura mishi ina jin wani irin son shi alokacin kaman zai fasa mun ƙirji na, ummie ce cikin murmushi take zayyana musu yadda sukayi da mummyn Aliyu, nan ma hajiya sake rabka salati tayi tace, "amma kuwa sun tabbata manyan sokaye, daga uwar har ɗan", ta maida kallonta kan Abba tace, "ae wannan satin ne dawowan Aminun ko?" Abba ya ɗaga mata alaman haka ne, "tou kayi aniya sati na sama a sambaɗa auren nan", tayi ƙasa da murya har tana sunkuyowa kaɗan tace, "gama zafin uwar shinnan da yadda tafi ƙarfin Hauwa da zuriyarta da suka shahara a yawon bin malamai, tou itama bazata gaza bin bokaye ba, tou bokaye mana, don itama ae Hauwan su tabi ta jawo hankalin Aliyun ya bar Ayshaa ya dawo kan nata ƴar, amma da yake na uwar Aliyun sun fi shahara ae kaga abun baiyi lestin ba, tunin yayi espiya", ta faɗa tana watsa hannu.

Ɗago kai Abba yayi da sauri ya maida kallon shi kan ummie, "dama bada amincewar ayshaa ya fara neman habiba ba ne"? Ita dai ummie bata ce komai ba, sai kallo na da ta ɗanyi ta kawar da kanta gefe, "dama baka da labari ne? Lallai khadijah kin cika cikakkiyar bafulatana, kawaicinki yakai duk inda ba'a zato, tou Ayshaa ya fara gani a bikin ƴar'uwarshi Ƙawarsu, ya kware yana sonta, ita kuma marigayiya ban san ya akayi ba, don bana ce taci amanar ƴar'uwarta ba tunda ƙasa ya rufe idanunta, kuma da kunya ga idon ɗanta na faɗi wani mummuna akanta, tou haka dai muka samu zance ya juye ya koma kan habiba, amma dai ba wai da yardar Ayshaa ba yadda suka tsara maka, juya kanshi akayi ya bar kan Ayshaa, daga wannan rana kuma uwar habiba ta raba tsakanin ayshaa da habiba, Allah dai masani amma shu'umancin uwarta na shige da fice wurin bokayen da baka son afaɗa ne ya tabbatah, shi kuma Aliyu bayan aure Allah ya kuɓutar da shi uwarshi ta tashi tsaye ta lalata ɗan ƙaramin shirkan Hauwa, don daga ganin idon uwar Aliyu gwaska ce, tou komai dai ya karye Aliyu ya dawo hayyacin shi yace baiji ba bai gani ba baya son habiba, don ba ita yace yana so ba, ita kuma marar kunyar ƙanwar tatah Raliya ta tsayar mishi rashin kunya ya labga musu uban na jaki, kaga asalin ƙiyayyan shi da ita marigayiya kenan, sharrin rashin da ce da uwa ta gari".

Abba ido ya zuba mun kaman bazai sake furta komai ba, chan kuma sai yace, "Aysha ki yafewa ƴar'uwarki, nayi imani ko da laifin habiba tou babbar mai laifin uwartace, don Allah ina roƙon arzikin ki kiyafe mata, taci darajana"! Hawaye na saka hannu na share, "Abba ni ban taɓa rike habiba da zuciya ba ɗaya ba, kuma ni tun farko ban so Aliyu ba, shiyasa ma ni banja ba, amma ni ban riketa da komai ba tun farko, Allah ya jiƙanta da rahma", na ƙarasa ina share hawayen da bansan ranan daina shi ba.

Addu'a sosi Abba ya mana na alkhari gaba ɗaya ƴaƴan shi , sannan ya umurce ni da na je na cigaba da kula da yaro na, tashi nayi ima rungume da Sabeer na fice, ina ganin hajiya ummah da ummie suna ta share hawayen su.

Ranan friday da 6:00am jirgin su A.G ya sauƙesu a garin lagos, 9:00am kuma suka tashi zuwa Abujah, amma A.G bai shiga bauchi ba sai ranan saturday da yamma, don basu samu flight me zuwa bauchi ba, dole suka bugu mota sai bauchi, ya iso ya samu gidan a cike, ga Hudah ga Heedayah da suke ta girke-girke don isowan big broh, twins ɗin ta suna ta shawagi a tsakani, hatta Daddah ranan a gidan ta wuni tare da goggo, suna dakon isowan A.G, suna isowa kuwa su hudah sukaje suka rungume shi suna murnan dawowan shi, ranan dai ya ɗan sake musu har yana zolayan heedayah washi take girkin nan ko dai wa M.G ne? Rufe ido tayi takasa bashi amsa sai dariya da takeyi, haka dai suka kasance cikin farinciki, mummy kaman ta goya ɗanta, gashi wannan dawowan yayi kyai sosai yayi fari ya ƙara jiki, don har M.G na tsokanan shi ya samu kan Ayshaa ne yasaka ya nutsu bakaman farkon tafiyan shi ba, shidai murmushi kawai yakeyi baice komai ba, anyi sallan ishaa duk suka koma parlor suka zauna, bayan M.G ya mayar da su Goggo da Daddah, ido ya zubawa M.G dayaga ya wani share shi yaƙi kallon shi, ganin bazai kalle shiba ya sa ya aiki heedayah ta bar Parlon, harara M.G ya jefe shi da shi yana gyaɗa kai, alaman zamu haɗu, share shi A.G yayi, sai ya tura mishi text, "wai me kake nufi ne da bazaka rakani wurin beauty ba"? Dariya M.G yayi yaƙi maida mishi reply, chan sai A.G ya dubi mummy yace, "mummy key ɗin motan ki please"? Ido ta zaro waje tace, "haba son yau ɗaya kam doug ta mana haƙurinka mana, muna marmarin ganinka ae", kunya ne yaji ya rufe shi, tun bama da M.G ya kwashe da dariya ba, "mummy ba wurinta zanje ba fah, phermacy nake son zuwa na duba wani magani", ya faɗa yana zaro ido, M.G yayi wuf yace, "Indo pharmacy ba", dariya dukkan su Parlon suka saka, Shima dariya ƙaryan da yayi ya bashi, haka dai ya daure ya zauna da su har zuwa 9:30pm, a maraice ya dubi mummy yace, "zanje na huta mummy", murmishi tayi tace, "hakan na da kyau son, jeka huta akwai gajjiyan karatu ae", bai jira shaƙiyancin da M.G yake mishi ba ya wuce side ɗinsu, da sauri ya rarumo wayan shi ya zabga wa Beautyn shi ƙira.

Tun ɗazu da Aliyu ya ƙira wayana, wai yaji lafiyan sabeer nakejin zuciyata babu daɗi, ni ban san ma na tsane shi ba sai yanzu, da baya burgeni ne kawai, yanzu kuma daya wahalar da habiba sai naji haushin shi nakeji, gashi yau ana magrib mamie ta aiko mai mata aikin side ɗinta ta karɓi Sabeer, sai naji haushin sun mun yawa, don na lura kwana biyu idan naje ɗaukan shi ta ringa mun wasu kwane -kwane, ko tace ya tashi da mura ko tace yana bacci, ni dai naƙi yin zuciya saboda ina ji a raina ɗana ne habiba ta haifa mun, anzo an ɗauke shi babu daɗewa Aliyu kuma ya ƙirani, gaya mishi nayi ya ƙira mamie Sabeer yana chan, haka dai ya ɗan taɓa kame -kamen shi ya barni, don ina jin shi har da cewa tsaraban me nake so idan zai dawo, darajan jammy yaci da na kashe wayana a lokacin, amma na daure mukayi sallama. Ɗaukan ƙiran A.G nayi duk babu wani walwala a tare da ni, jin muryana wani iri sai yayi ƙasa da muryan shi yana tambayana, "waya taɓa beauty ne"?

Turo baki nayi kaman yana gani na nace, "mijin habiba ne ya ɓata mun rai", "lallai ya maida hankalin shi, don darajan habiba ne da yaron mu zai saka na ɗaga mishi ƙafa, sbd haka kada ya sake", dariya maganan shin ya bani, haka dai baya son yawan maganan amma yaja ni da hira, har 11:00 muka kai muna hira, yawanci ma nike bashi labarin, rayuwar mu na ƙuruciya da habiba yawanci nake bashi, wani yayi dariya wani ya tayani alhinin mutuwan Ayshaa, da ƙyar dai yayi sallama dani, don sai da yaji na fara jera hammah tukun ya barni.

Washe gari kuwa ana idar da sallan ishaa suka zo tare da M.G, bayan sun gaida ummie parlon hajiya ummah suka wuce, nima achan naje na same su, gaba ɗaya sai na samu kaina da jin kunyan A.G, gashi tun da na shigo idon shi suke zube akaina, ko kunyan M.G da keta zolayan shi baya ji, nidai sai sunne kai nakeyi kamar wata munafuka, abun mamaki M.G kaman bai taɓa sona ba haka yayi ta acting, irin dai kawai ni wanda amininshi ɗan'uwan shi zai aura ne, nima ganin yadda yayi kawai sai fuske, muna zaune kuwa sai ga wayan Aliyu ya shigo, ido na zubawa wayan har ta gama ringing ina kallo ban ɗaga ba, a karo ta biyu da ta sake shigowa sai A.G ya ƙura mun ido, ganin haka sai M.G yace, "ki ɗauki wayan mana, ko ba important call bane"? Ɗaga kai nayi alaman hakan ne, shidai A.G ido kawai ya ƙura mun, jin kusan 5mnt ba a sake ƙira ba sai hankali na ya kwanta, amma da yake Aliyu jarababbe ne sai ya sake ƙira, haɗa ido mukayi da A.G, bai buɗe baki ba yayi mun alaman na ɗaga wayan, ganin fuskanshi ya ɗan chanja sai na ɗaga wayan, sallama mukayi daga nan muka gaisa, tambaya na yayi Sabeer, gaba ɗaya naji haushi yakamani, har ban san lokacin da nace, "bayan magrib nae maida shi wurin mamie, ka dinga ƙiranta kana jin yayah yake mana", murmushi yayi yace, "haba ayshaa ae tunda ba nono yake sha ba kidinga barinshi a wurinki mana, ae inaga kwana ma zai iya a wurinki, ni ina so ya buɗi ido baisan kowa ba a matsayin uwa sai ke",..... ban jira ya ƙarasa shirmen shi ba nace, "sai da safe ina tare da baƙi", kashe wayan nayi na ajiye, ina ajiyewa muka haɗa ido da A.G, ƙura mun ido yayi kawai, duk sai naji babu daɗi, a ɗan ruɗe nace, "mijin habiba ne, yana so yaji yayah sabeer yake"? "ok shirmemen mutumin da Barrister ya bani labari wai don shirme ya turo mamyan shi wai a bashi ke madadin habiba ko? Tou ya manta irin uƙuban da ya bawa habiba ne? Baida hankali ae".

Da sauri A.G ya maida kallon shi kan M.G, har muryan shi na ɗan shaƙewa yace, "yaushe haka ya faru"? Tsaki M.G yayi yace, "ae inaga maganan nan bai wuce 2weeks ba, yafa saki habiba kafin ta haihu, amma don rashin hankali wai a bashi Aysha, sai da Abba ya fito musu a mutum tukun suka haƙura", M.G yace. Idon shi ya dawo dashi kaina, batare da ya kalli M.G ba yace, "bai haƙura ba", Kallon shi M.G yayi sannan yace, "kaman yayah? Kaji sun sake dawowa ne"? Fuskan shi a matuƙar murtuke yace, "dama ae wancan ɗinma daga kai har ita babu wanda ya sanar dani, ballanyana har naji a wani wurin, salo ya chanja, meyasa zai ƙira wayanta? Yaron ya isa magana ne"? Ajiyan zuciya na sauƙe na maida kallona kanshi, harara ya aiko mun da shi, hakan ya saka na buɗe bakina da sauri nace, "tou ae Abba ya dakatar dasu", "duk da haka kin gaya mun"? Naji A.G yana faɗa, ganin haka yasa M.G ya miƙe tsaye yace, "bari na ɗan miƙe ƙafana kafin ka fito", shima A.G miƙewa yayi tsaye yace, "muje kawai, nima zan leƙa gidan Daddah", murmishi M.G yayi mun sannan yayi sallama ya fita, nidai ban tashi ba kuma kaina yana sunkuye, ɗaure fuskana nayi naƙi kallon inda yake, ganin haka yasaka ya kasa fita, dukka hannayen shi ya zuba cikin aljihun wandon shi, ido ya ƙura mun har na zuwa wani Lokaci, ko ya fahimci raina a ɓace ne yasaka ya ƙaraso gaba na ya tsaya, shiru naji yayi hakan ya saka na ɗan ɗago kaina na dube shi, ganin kallona yake yasa na murguɗa bakina na maida kaina ƙasa.

Tsugunawa yayi dai-dai saitin fuskana, sannan naji yace, "tou meye ne kuma Eeshaa"? Murguɗa baki na sakeyi na ƙara hararan shi, kawar da kaina gefe kaɗan nayi, wani ƙamshine mai nutsuwa yake tashi daga jikin shi, hakan ya saka naji na sake kallon shi, kallo shi kuma na sakeyi, ya wani marairece fuska kaman zaiyi ihu, "tou ni meyasa zan gaya maka maganan da baida wani muhimmaci a gare mu, kana Exams fah lokacin", na faɗa ina maida ido na cikin nashi, idon nan a lumshe an zuba mun su kaman zai lashe ni, "bana son ƙiran da yakeyi Eeshaa, please ki daina ɗauka, idan yana so yazo gidan yaga ɗanshi, shima bake zaki kai ba, yaje wurin kakar yaron please".

Ɗaga mishi kai nayi alaman naji, "tou ki sake fuskan ki bar fushin", ya faɗa still yana tsugune a gabana, kallon shi nayi nace, "tou meyasa zaka tafi yanzu"? Tashi yayi ya zauna a kujeran da yake gefe na yace, "an ma fasa tafiyan nan, dama M.G nake yiwa wayo ya fita".

Readers Also Read