Ana barin halal original by anty nice - Chapter 21
Ana barin halal original by anty nice Chapter 21: Ana barin halal original by anty nice Chapter 21. Dariya ne ya kubce mun babu shiri, "ka dai chanja ne,…
4,426 words
Dariya ne ya kubce mun babu shiri, "ka dai chanja ne, ae ɗazu fushi kayi", shima dariyan yake yace, "ae danaga naki fushin yafi nawa tunin na daina, shi kuma M.G abun ya hanani tafiya wai sai yayi gaba irin na biyo shin nan, tou anƙi wayon, so yake mu kuma yaje yaga wannan mummunar budurwar wanshi, ni kuma yasaka nayita kallon bango".
Dariya sosai A.G ya sakani, wato idan ya samu wuri shima bakin shi buɗewa yakeyi ko? Wato har zolaya ya iya?
Ido ya zuba mun yana murmushi, gaba ɗaya yayi kyau sosai, har wani rausayar da kanshi gefe kaɗan yayi yana kallo na, a hankali na dakata da dariyan na kalle shi, "waya gaya maka Heedayah mummuna ce? ae da kai take kama fah, kuma ta fika ma kyau don ita mace ce", na faɗa ina kallon shi da murmushi a fuskana, kwaikwayon yadda nake tura baki yayi, "waya gaya miki mace tafi namiji kyau? Kema ae baki fini kyau ba ballantana heedayah, ku daina saka kwalli, da shafa powder da jan baki kuga idan ba ace munana bane ku, ke kinyi sa'a fah", ya faɗa yana shafa fuskan shi.
Hararan shi nayi cikin wasa nace, "yanzu kai kana ganin kafini kyau ne"? Ɗaga kai yayi yana kallon cikin idona, jijjiga kai nayi na kawar da ido na.
"kijira muyi aure, wanzami zan saka ya miki aski tal kwabo, ranan zaki banbance nida ke wayafi kyau, nima zanyi askin". Ya faɗa yana kashe mun idon shi.
Aeko bansan wani irin dariya bane yazo mun, amma na saka hannu na rufe bakina, dariyan yayi yace "kin yadda nafiki kyau?" Kai na girgiza alaman a'a, "tou sai mun haihu, me kama dani da me kama da ke, zakiji ance kai mai kama da Aminun yafi kyau" ya faɗa yana ɗaga mun dukkan giran shi.
Tura baki nayi dukka gaba nace, "ni duk masu kama dani zan haifa".
"Haba? Dayawa zaki haifa mun"? Ya faɗa yana sunkuyo da kanshi dab da fuskana, rufe fuskana nayi ban ce uffan ba, chan da na gajji da zolayan shi sai nace, "suɓutan baki ne fah", dariya ya fara yana miƙewa tsaye yace, "aeko ni A.G na dinga saka ki suɓutan baki, da ido a sai kin mun suɓutan zance, ƴan mata tashi kimun rakiya kada M.G ya zaune miki ni yau,"
A mota muka samu M.G ya kwantar da sit yana ta waya, harara yabi A.G da shi, shi kuma A.G ya wani ɗaure fuska kaman bashi bane yanzu yake ta ɓarin zance, ni dai murmushi kawai nakeyi ina kallon su, har sai da suka shige tukun A.G ya kallo ni, "gobe insha Allahu da yammah zan shigo, zanzo naga yarona ko"? "gara da kache kai, don gobe saloon zan kai Giwata, ba zanyi wani rakiya ba azo ana fito da ni waje da wayo", murmushi nayi nace, "tou yayah M.G a gaida giwar", sannan na juya da sauri nayi cikin gida.
Ina shiga na wuce direct ɗakin Ummie, anan na sameta ita kaɗai, tambayanta nayi hafsy, "tana ɗakin ku tana jaraban wayan kun nan", nidai murmushi nayi na zauna a gefen gado kusa da ita, zayyene mata yadda Aliyu yake damuna da ƙira nayi, da kuma yadda yau mukayi har ran A.G yaso ɓaci, ido ta ƙura mun tayi tagumi tana saurara na, har sai da nagama tukun ta sauƙe ajiyar zuciya, "kada ki ƙara ɗauka, insha Allahu da safe zamuyi magana da yayinki, abunda muka tsayar kuma zamu gayawa Abban ku, amma in banda neman fitina an ce musu da maganan aure akan ki, shi kuma zai dinga damunki da ƙira? Gaskiyan Aminun ne ae, yazo har gidan yaga ɗan na shi mana, ae Abban ku bai hana su ba, ko kuma ya ƙira mamin ta ku yaji yayah yake mana? Shirmen banza dama ya damu da abunda ke cikin ne ya wofintar da uwar yaron"? Muna maganan sai ga hafsy ta fito, zama tayi tana ta zabga masifah nidai ido na ƙura mata nayi tagumi ina kallon bakin masifan nan, sai da tayi iya yinta sannan ta dube ni tana wani murmushin shaƙiyanci, "Adda nace yayah A.G bai kawo mana wani tsaraba bane? Ina sauri ae naje muyi gaisuwa na musamman sai aka ƙirani a waya, dama turare nake sha'awa wallahi, idan bai sayo ba kuma sai ya ɗan zaga damu gari su ganmu muma mu gansu, don naga wata sabuwar mota sukazo da ita, nace harka taci uban tada kenan"? Hararanta ummie tayi tace, "wallahi naga kinje kin tambayi wani tsaraba kiga yadda zanyi gutsi-gutsi da naman bakinki, ke ni hafsy meyasa kunya ya miki ƙaranci ne kam"? Tana Dariyan ummie tace, "haba mumsy bawai kai tsaye za'a fito ba ae, kwane -kwane akeyi ae, bayan gaisuwa sai a sauƙe dabaru, kin san kuɗin nan fah kaman na banza suke da shi, ba wai daɗin shima suka sani ba", ta faɗa tana dariya. Dariyan nayi nace "kin ɗauka ranan bai fahimce manufanku bane keda ummie ko? Tou bayan kun fita dariyan ku yayi tayi, har ya ƙara mun haske akan halin ku". Baki hafsy tariƙe tana dariya, "kin fasan barristocin nan Allah ya musu ɗam banzan wayo, bakiga yayah Ahmad bane, duk shirun shi wayon tsiya yake da shi kina shirin cutar shi yake ganoki, kuma sai yabi diddigi kafin ya baki abu, shiko yayah muhammad bawan Allah yayanmu madadin ubanmu, kana faɗa zakaji tarararat a account ɗinka, baya ma bin ta kanka wallahi, tou inaga da M.G ne buris zaiyi damu yayi ta labta mana abun duniya, shi ko A.G nan daga ganin idon shi wayone da shi, idan bakiyi da gaske bama Adda sai yaci naki", ta faɗa tana wani ya mutsa fuska, ita dai ummie kallon bakin ta kawai take tana mamakin halin hafsy, nima dariyan ta nakeyi, "aiko zan gayawa Yayah Ahmad abunda kiƙa faɗa, tou na hannun damanki fah"? Na faɗa ina dariya, don nasan sharrin da zata zabgawa yayah umar. Aiko baki ta riƙe da hannunta, "dila kike ji, ae ba banza ba hajiya umma take ce mishi diƙa sarkin wayo, ae yayah umar sai da yaci naka, don ni har yanzu yana ƙwaƙile mun account ɗina, kullum alƙawari yake mun idan yayi kuɗi ni zan fi kowa morewa a gidan nan, a wayon shi wai ko ummie bazata ci kuɗin shi ba irina".
Aiko daga ni har ummi dariya muka kwashe da shi, ummie tace, "amma duk da kinsan wayo yake miki ae ko kullum ƙusƙus ɗinku tare ne," Dariya hafsy tayi tace, "tou ummie yayah na iya da saurayin kakata ummah? ni bana so mu rabu ne saboda duk gidan nan nafi jin taisayin shi, saboda baiyi dace da mace ba, don wallahi ummitah ɗan banzan wayone da ita ga son abun duniya, kedai kawai ummie godiyarki ga Allah da kika haifi su yayah Ahmad masu tausayinki, sai kuma da Allah ya baki ni, don ido na akan ummitah yake, tana samfe yayah umar zan samfe yayah ishaq, kema ki dongwali arzikin ƴaƴa, tou ina zan saka ido ana zuƙe miki ɗa acan side ɗin nima nakasa zuƙe na wasu ɗan", ta faɗa tana wani tura baki gaba. Dariya kaman zan faɗo a kan gado, ummie na kallon drammer hafsy tace, "nidai tashi kije kiyi alwala kizo kiyi shirin bacci, ae Allah yaga halin ku ɗaya ne ya haɗaku ƙawance, mazajen ma ya baku daidai da ku, halinku ɗaya da umaru a wayo, shiyasa kuke son junaku, kinga Ayshaa ae da yake halinsu ɗaya su uku sai naso yazo ɗaya, shiyasa ma mijinta bai da fitina irin halinta Allah ya bata".
"yanzu ummie kina nufin yayah ishaq baida halin ƙwarai kenan"? Hafsy ta faɗa tana wani zaro ido waje. "nikan ki rufa mun asiri hafsy, bance kije ki gayawa ishaq nace wani abuba, ae ishaq inda hali ake bi ae bazaku haɗuba, shima masha Allah, kedai tashi ayi shirin kwanciya", haka mukayi sallama cike da farin cike a zuciyar kowa, har bakin ƙofan parlor ummie ta rakani, tana tsaye har na ƙarasa ƙofan parlon hajiya ummah, hannu na ɗagawa ummie itama ta ɗaga mun, ina shiga na samu hajiya ummah zaune a parlor, harara take bina da shi, dariya nayi nace, "ke kuma matar umaru hararan na meye"? Tsaki tayi tace, "kin tattare kinje wurin mahaifiyarku, babu kunya ta zauna tana ta hira da ƴaƴan cikinta, ae da kuka gama hiran da A.G ɗin sai kizo muyi shawar -wari, amma bawai kawai ki wuce wurin uwarkiba, itaga ga mai ƴaƴa ta wani riƙe ki a chan", Dariya nayi nace, "ke idan Abba ko Aunty Rakiya sukazo kada ki kula su, ki dinga sharesu su zauna su gajji su tafi, ni kuma muna tare ne da hafsy bawai ummie ba", na faɗa ina ɗaukan ruwa nasha. "Wato ƴaƴan nawa kike so nabarwa duniya su? Tou baki isa ba, kinci uwar ƙarya kuwa, ita kuma hafsy take kowa? Munafuka baka ganin ƙafan ta anan sai isiyaku yazo tukun zata ishe ni da iyayi, ta dinga jele kenam kaman wutsiya", tana faɗa kuwa na kwashe da dariya. Waya nane ya fara ringing, ganin A.G ne ya saka na tashi nayi hanyar ɗaki ban kula ta kanta ba.
Kwanciya nayi saman gado tukun na ɗauki wayan, shiru dukkan mu mukayi babu wanda yace uffan, har kusan mintuna biyar, "hmmm yarinyar nan wato sai na sauƙe abunda yake mun yawo a kaina na tanka tukun ki amsa mun ko"? A.G ya faɗa bayan shirun da mukayi na wasu lokaci, murmushi nayi nace, "tou ae kai ke nema, kaga bansan me zaka ce ba kada na maka shishshigi", "kedai kika sani, yayah meye labari"? Duk yadda naso shareshi bai yadda ba, haka yayita jana da hira har zuwa wani lokaci tukun mukayi sallama, ya kuma sake jaddada mun kada na ɗauki wayan Aliyu, nidai da tou kawai na bishi, sallama mukayi nidai nayi shirin bacci.
Yadda yayi alƙawari kuwa da yamman yazo, parlon hajiya ummah na kaishi, bayan sun gaisa ta shige ciki ta bar mu nida shi, gaishe shi nayi sannan na tashi na fice domin ɗauko Sabeer.
Tunda na shigo rungume da Sabeer ya ƙura mana ido, da ƙyar naja ƙafa na zuwa gaban shi, hannu biyu ya saka ya karɓi Sabeer, shiru yayi mai ɗan tsawo yana kallon fuskan sabeer, kaman wanda yake ƙididdige abubuwan fuskan shi ya daɗe a haka, sai chan ya ɗago ya kalle ni, "masha Allah, Allah ya rayashi da imani, Allah ya jiƙan mahaifiyar shi yasa tayi shahadah", "Ameen ya rabbi", na faɗa ina duban shi yadda ya riƙe babyn.
Ɗago kai yayi ya kalle ni yamun murmushi, "girls nake so ki haifa mun masu kama da ke, two, or three, idan kina son boy tou mai kama dani amma ya tafi ana uku" dariya nayi mai ɗan sauti kaɗan, ina kallon shi yadda ya wani ci serious, "tou idan kuma duka boys ne fah"? Na faɗa ina mishi dariyan zaro idon da yayi waje, gaba ɗaya girman su sua bayyana, "a gidan M.G insha Allahu za'a haifa mishi boys, nikan girls nake so, boy ɗayan ma nafasa, sabeer ya wadatar, idan kin matsa kuma sai M.G ya bamu ɗaya a nasu muƙara", Fuska a ɗaure ya faɗa, daga gani kuma iya gaskiyan shi ne, murmushi nayi na girgiza kaina, "idan ya baka boy ɗaya zaka bashi naka girl ɗaya ne"? Harara na yayi "haba Eesha, yara ukun ne zamu bawa wani? Tsaya kiji iya maganan gaskiya, ni ko hutu ƴata baxata je ko ina ba ballantana nayi kyautan su". Kallon shi nayi cike da mamakin son kanshi, "amma kai kuma zaka ɗauki ɗan wasu? Tou idan ummie ko mummy sukace a basu ɗaɗɗaya fah"? "wayyo beauty ki rufa mun asiri kada ki haɗa abunda bazai yiwuba, yara biyu ko ukune kike zancen mu bayar da su? ko hutu baza suje musu ba ballantana kyauta, ni zan kula da ƴaƴana idan bazaki iya ba", dariya maganan shi ya bani, ga mamakin maganan da yakeyi, duk da dai shi maganan shi murya a ƙasa take amma dai yana iya mu hira, wanda duniya ta shaidah dagani sai M.G ake ganin yayi dogon hira da su, M.G kamma wataran baya amsa mishi, amma ni a rayuwar shi sai ya iya good 2hrs yana mun hira, some times nice ma ke nuna gajiyawa, kallo kuma a rayuwar shi har mamakin baya iya gajjiya da kallona nakeyi, "tou mu haifi 5, ɗaya mu bawa mummy, ɗaya wa ummie, sai mu rie 2girls 1boy, mu haɗa da Sabeer sun zama 4 mue dasu".
Harara na yayi yace, "ke Eesha nifa ko goma kika haifah bazamu bawa kowa ba, yauwa gari ki sani, ke ummie tayi kyautan kine ko ni mummy mai tsananin ƙulafucin ƴaƴa ta bayar da nine? Muma mu zamu riƙe namu, kuma 3 ne insha Allahu". Dariya nayi kawai na bar mishi zancen a haka, "wawan nan ya sake ƙiranki kuwa"? Naji muryan shi yana tambaya na, kai na girgiza mishi alaman a'a, "jiya nagayawa ummie yadda mukayi da shi, kuma tace zata samu yayah muhammad akan maganan, duk yadda sukayi zata gaya mun". Ajiyan zuciya ya sauƙe, "Allah ya sakawa ummie da alkhairi, gaskiya naji daɗin shawaran da ummie ta bayar, mungode Allah ya saka da alkhairi", Babu daɗewa yace na ƙira hafsy a waya, shigowan hafsy na ɗan harareta ƙasa-ƙasa ganin kallon da take mun tana ɗan iskan smilling, "yauwa hafsy zuki sha da yaro nan sai ki dawo," Miƙa mata sabeer yayi ya ɗaura mata 50k a kanshi, "kisaya mishi madara da pampers ko? Murmishi tayi ta fita da sabeer, kallon shi nayi bance komai ba, har hafsy ta dawo naga ya miƙe yace mata suje waje, gwalo ta mun da tazo fita.
Basu wani daɗe ba ya shigo, zama yayi ya ɗan ƙura mun ido, kunya naji nayi ƙasa da murya nace, "mungode Allah ya ƙara buɗi", shirun da naji yayi ne yasaka na ɗago ido na kalle shi, abun ko da nayi tunani ne ya faru, idon shi ne dai a zube a kaina, "idan uba yayiwa ɗan shi abu sai a mishi godiya"? Naji muryan shi yana faɗa, ɗago da kai na nayi ina duban shi kaina a ɗan langaɓe, "nidai nagode Yayah A.G, Allah ya ƙara buɗi", "bana son yayan nan, a bani wani sunan special, yayah ae Ahmad ne da M.G.
Bai wani daɗe ba ya mun sallama, rakashi waje nayi har jikin mota, bayan ya tafine na wuce wurin ummin mu, a ɗaki najiyo muryan su, har chan na samesu, ina shiga kuwa hafsy tayi charaff tace, "yauwa Adda gara da kika shigo, dama har haƙurina ya kusa ƙarewa, kaman zan leƙa waje nace ki dawo, ga tsaraban da nake ta ɗoki an kawo, buɗe mugani, ummie ta hanani buɗewa", ta faɗa tana wani washe baki, ummie na hararan ta "amma dai hafsy ke kam ko wa ke aka kawo kayan nan sai a hankali", murmushi hafsy tayi tana jawo babban jakan da yake kusa da ita, tana dariya tace, "ummie ae abun Adda na mu ne, yanzu hala ƙaramin jakan ma nawa tsaraban ne, bari mu fara na ma'in ɗin muga meye da meye a ciki"? Buɗewa tayi nidai ido kawai na ƙurawa bag ɗin, dogin riguna ne kusan kala biyar, masu kyaun gaske, sai jean skirt kusan kala uku da riguna masu kyau, sai holland guda biyu super guda biyu, lace guda biyu masu kyaun gaske, sai gayyan takalma designers masu kyau da wasu handbag masu kyau na yayi, sai turaruka da dai cusmetics sosai, idona na ƙura akan wani agogo mai kyaun gaske, ƙasan kayan kuma kaya ne kusan set 10 na Sabeer da takalmin babys guda uku masu kyau "tou ni khadijah, duk wannan tsaraba ne? Shi dayake da haɗa kayan aure a gaban shi ya kawo wani tsaraba mai yawa haka"? Ummie ta faɗa, na buɗe baki zanyi magana sai naji ƙaran shigan txt a wayana, Aliyu ne ya turo mun txt, tsaki nayi ko karantawa banyi ba na goge, ido na mayar kan ɗayan jakan da hafsy ta buɗe Leda na asama an rubuta ummie, ɗaukowa tayi ta buɗe, turmin zani ne holland guda ɗaya sai turare guda biyu, miƙawa ummie tayi tana dariya tace, "ummi gana ki tsaraban, sannan ta ɗauko leda na biyu, English ne a ciki sai wani flat takalmi mai ɗan laushi an rubuta Hajiya ummah ajiki, ajiye shi tayi a gefe ta ɗauko wani da aka saka shadda 10yrd fari da turare guda biyu a ciki, an saka Abba, dariya hafsy ta ƙyalƙyale da shi da ta ɗauko ledan gaba jiki na rawa ta buɗe saboda ganin sunanta akai, lace ne mai kyau a ciki, sai tarkacen, bags, shoe, cusmetics kala-kala a ciki, ga wani riga da skirt mai shegen kyau a ciki nata ma har da wani agogo mai kyau a ciki, rungume ledan tayi tana "Yaya A.G Allah ya baka Adda duniya da lahira, Allah yasa a aljannah a rabon kace", "Ameen ya rabbi" ummie ta faɗa tana kallonta da farin ciki, "hankalinki ya kwanta ko"? Ummie tace mata, tana wani jaririn dariya tace, "ae ummi bakiji yadda kayan nan suka sakani farin cikiba, gaskiya Yayah A.G duniya ne".
Harara ummie ta mata "tou maza rufe komai sai Abba ya gani tukunnah", ummie ta faɗa tana miƙewa zata fita, "ummie kada fa Abba yace no", hafsy ta faɗa, "bazai faɗa ba auta, amma abinda ya kamata kenan ayi", ummie na fita mutuniyata ta matso kusa dani, "Adda gaskiya kinyi dace da Ɗan gaske, don wallahi mutumin nan duniya ne, kiga wasu arnakun laces masu zafi? Wannan kam hala ma ya haɗa kayan shi achan, kuma ya tambayeki size ɗin takalman mune Addah"? Hafsy ta faɗa tana jin wani farin ciki domin ya nuna a fuskanta, nafi kowa sanin hafsy da son abun duniya, gashi dai akowani lokaci daga Abba har yayun mu cikin hidima suke mana, amma ita bata gajjiya da abun duniya, murmushi nayi na miƙe don jin an fara ƙiran sallan magrib, "nifa tun farkon tafiyan shi sister shi Heedayan nan ta tambaye ni size ɗin takalmi na dasu bra, ni na ɗauka ma mummyn su ce ta sakata, sai ana sauran kwanaki ya dawo ya mun wayo, don sai yanzu nagane, ya tambayeni nida ke wayafi tsayi nace kin ɗan fini kaɗan, shine yake ce mun kenan zaki fini tsayin ƙafa, ban fahimta ba nace mishi a'a size ɗaya mue sawa 39, kuma fah sai da yace kice hajiya ummah ma bazata wuce 39 ba nace mishi 38 take sakawa, ashe wayo yamun", dariya hafsy ta ƙyalƙyale da shi tace, "kai kaji ɗan bariki" harara na juyo na mata cikin wasa, "ae mijin nawa ne ɗan bariki? Ba laifin ki bane na bar shi ne har ya miki tsaraba", da sauri na shige toilet jin dariyan da hafsy ta sheƙe da shi, ima jiyota tana, "ashe fah kema Adda idan kin samu wuri duniya ce ke"? Ina toilet ni kaɗe ina smilling, wai nice ke ƙiran A.G da mijina ko kunya bana jin, haka nayi alwalan na fito na ɗaure fuska don kada ta kawo mun rashin mutunci, hannu ta saka ta rufe bakinta ta wuce toilet ɗin itama.
Abba bai wani yi faɗa sosai ba , kawai dai yace kayan sunyi yawa ne, ummie na taya shi, ƙiran wayan A.G yayi ya saka a speaker, ina jin muryan A.G na sunkuyar da kaina, godiya Abba ya mishi ya kuma mishi faɗan shi dayaje karatu kuma ga hidima a gaban shi ya kashe kuɗi haka? Shidai A.G godiya yake tayiwa Abba kaman wa shi akayiwa kyautar, daga jin voice ɗinshi risinawa yakeyi,haka ummi ma ta karɓa tayi godiya ta kuma ce ya gaida mummyn shi, itama godiya yayi ta mata, haka Abba ya sallame ni bayan ya tambayeni babu komai ko? Anan ne ummie ta ɗauko mishi maganan Aliyu da takurawan da yayi mana, ai kuwa Abba inda ya shiga bata nan yake fita ba, ɗaukan waya yayi ya ƙira yayah muhammad, ya umurce shi daya nemi Aliyu yaja kunnen shi, ya tabbatar mishi shifa bai manta riƙon da yayiwa habiba ba, sannan kuma ya gaya mishi ya tsayar wa ƴar shi da ranan aure, kada ya shiga hurumin da bana shi ba.
Ummi da kanta ta kaiwa hajiya ummah kayanta, ranan kuwa A.G yasha yabo a wurinta, har da cewa ba'a taɓa saya mata takalmi mai kyaun wannan ba tunda tazo duniya, ita dai ummie murmushi kawai bata tanka ba, sai da hajiya ummah ta gama murnan ta tukun tayi ƙasa da muryah tace, "tou kayan shi jaririn wa matsafiyar za'a kai ? Kada fah taje tayi wani surkullen ta ɓata maganan auren"? Murmushi ummie tayi tace, " babu abunda ta isa tayi akai hajiya, insha Allahu babu abunda zatayi yayi tasiri, za'a kaimata yau ɗinnan". Haɓa hajiya ta riƙe tana ya mutsa fuska tace, "tou duk yadda kuka gani, amma nidai da za'a bi shawara na da kada a kaimata, amma yanzu idan an kai babu bayanin matsayin shi, kawai abokin Ahmadu ne", "hajiya ae yanzu da maganan Aliyu ya taso tasan da maganar aure, amma dai bata san waye ba, don ko lokacin rasuwar habiba, yayansu ne ya haɗashi da ita awayan shi suka gaisa, inaga ae rasuwan nan ya rikitata bazata yi wani abun ba", ummie ta faɗa tana miƙewa, ya mutsa guska hajiya tayi tace, "a naki zucuyar imanin ba, don Hauwan da nasani ko mutuwa tayi ta dawo taga abun mugunta zata aikata, saidai Allah ya tsare".
********* 1month da dawowan A.G aka ska ranan auren mu, 3month mai zuwa, rana ɗaya dana M.G, zokiga rawan kai a wurin M.G, sai wani tsare-tsare yakeyi, sai da yagama A.G ya gwale shi, buɗan kai da reception kawai A.G ya amince zaiyi, haushi kaman zai kashe M.G, daga baya ne ma da A.G yaga ya tayar da hankalinshi ya yadda da maganan hawan da za'ayi, sai lokacin M.G ya ɗan sake, idan bani ba babu wanda ya isa ya ce ga ɗokin da A.G yakeyi, amma ni yakasa ɓoye mun farin cikin shi, photonan gidajen da zamu zauna bauchi da Abuja yake ta nuna mun, ya matsa wanne yafi mun kyau, babu yadda na iya dole na nuna mishi na bauchin yafi mun kyau, kallo na yayi yace, "Abuja yafi tsaruwa, kawai don baida girmane, shi 2bedroom ne, na bauchi kuma unguwa guda ne, side ɗin shi da ban nawa daban, 3bedroom ne nawa, ga parlor babbah, gidan yana kallon na M.G. Abuja kuma A haɗe suke Gate ɗaya. Kwanci tashi asaran mai rai, duk abunda aka saka mishi lokaci saurin zuwa ne da shi, yau saura 3weeks bikin mu, daga gefen mun har nasu A.G da M.G shiri akeyi sosai, abun mamaki ƴan'uwan M.G da suka haɗa mahaifi tare, wato ƴaƴan Alkali sai shirin biki sukeyi babu kunya, Aunty umatiti har ashobi ta fito musu da shi wai na familyn su, da yake ita da Aunty safiya sunayi da shi sosai, don karatun ƴaƴan umatiti duk yana kanshi, shidai alƙawari yayi ƙafan shi bazai leƙa cikin gidan da aka wulaƙanta shi ba, amma komai ya kama idan baifi ƙarfin shi ba zai musu, gashi yadda Allah ya bunƙasa mishi dukiyan shi abun har abun mamaki.
Gidan mu kuwa zuwa wannan lokacin mamie hali ya fara dawowa, don sabeer ma fir ta mun hali akan ɗaukan shi, wai yanata laulayin haƙori, sbd haka abar shi jikn babu lafiya, haka ba a son raina ba na haƙura, amma kullum sai naje na duba shi, gashi da ƙiwuya, amma idan ya gani ya dinga wangale baki kenan yana dariya, hanani ɗaukan shi da tayi sai danayi ɗan ƙaramin zazzaɓi, sai da hajiya ummah ta watse ni tukun na haƙura wa raina.
Gyara sosai ake mun a side ɗin ummie, akwai wata ƙawar ummi mai suna hajiyan basakkwata, itama ta na unguwar mu na G.R.A, ita take mun gyara mai sunan shi gƴara.
A week ɗin aka kawo kayan aure gidan mu, kaya ne da ya amsa sunan shi kaya, set biyu na akwatuna A.G ya haɗa, M.G ma komai iri ɗaya aka yi, colour ne kawai yake banbanta, wai ranan zokiga mita a wurin mamie akan ba a gaya mata za'a kawo kaya ba, an maida ita meye a cikin gidan? Haka ta ringa bala'inta babu wanda ya kulata.
******** Gidan su Aliyu kuma haka Mummy tayi ta fama da shi har ya sake amincewa da auren ƴar sister ta, shima jamy ne ta nunawa Mummy abun da sukayi bai dace ba, itafa bataga laifin Ayshaa da iyaƴenta ba, saboda son da akeyiwa jammy ya saka mummy ta fahimceta, har ta ƙira ummie ta bata haƙuri.
Shirye-shirye mukeyi sosai na liyafa a ta gefen ummie, don zainab ta tattaro tun ana saura 2weeks ta dawo gidan mu, haka hadiza ma ana saura 1week ta dawo, kowan su itama an saka mata rana, kuma satin auren su yayah umar zasiyi passing-out, gashi ya matsa sai ummie taje mishi, mudai dariyan drammer su muke tasha, domin ita ta kafe saidai Aunty Rakiya idan zata tafi mamah ta bita, shi kua fir yaƙi yace shima ummie yake son gani a ranan, koyaya za'ayi Allah masani.
Yayuna sun mun akwatin kayan fitan biki, babu ne kawai babu a kayan, don gaskiya sun mun kaya na kece raini, ga furnitures ƴan gaske da aa mun Abuja da bauchi, kuma ko ina an saka mun gadaje, Abuja duka ɗakuna biyun Abba ya saka mun gadaje, bauchi kuma sise ɗina ɗaki ɗaya ne ba'a saka ba, gado uku su yayah suka mun, ɗaya aka kai side ɗin A.G, ranan da akaje akayi jere shima an sha daga da mamie dn har da kukanta, akan ana mata rashin adalci, Abba dai kacha-kacha ya mata ya barta, dayake ana gobe passing-out ɗin su yayah su Aunty J Da Aunty B suka haɗu da Adda da Aunty ma'u da ta sauƙa Abujan sukayi, kuma ranan su ummie suka sauƙa Abujan, da yake mamah tana Abuja lokacin tare da Abba, tou duk tare sukaje wurin bikin fitan su Yayah, ga hafsy da ummitah ansha sabbin ɗinkuna taya masoyan su murna duk sunje, mu da su hadiza da Maryam da Goggonta aka bari a gida, sai mamie da take gefenta ita da raliya da tazo ranan da su ummie suka tafi, tayi wani kyau daga gani tana hutawa, sai dai bangan alaman taa da ciki ba, don naga daga Fatima har maryam suna da ciki, don maryam lokacin ma tana kwance cikin laulayi sosai, don sai da mukaje muka duba ta ana gobe su ummie zasu tafi, don a gidan suka ɗauki ummitah ma da zasu tafi, duk tayi wani iri abun tausayi.