Ana barin halal original by anty nice - Chapter 26
Ana barin halal original by anty nice Chapter 26: Ana barin halal original by anty nice Chapter 26. Muna shiga parlon na hango M.G zaune Shi da Daddy, T.V…
3,902 words
Muna shiga parlon na hango M.G zaune Shi da Daddy, T.V kunne yana aiki, su kuma Suna hira, lokacin kuma mummy ta fito daga hanyar kitchen heedaya na biyota a baya hannun ta ɗauke da filet da soyayyen ƙwai sai cup da tea a ciki, direct dinning muka wuce muka ajiye kayan da yake hannun mu, ɗan ihu kaɗan heedayah tayi tana mun oyoyoyo, hararanta da A.G yayi ne taɗan nutsu, amma idon ta nakaina tana murmushi, nima murmushin nayi idona yana kanta, "har kun iso kenan"? Na tambaye ta bayan na ajiye abunda yake hannu na na juyo hannu na riƙe da handbag ɗina, "ai ina ga da ƙyar idan ba a ƙofan gidan nan 8:00am ta musu ba, gashi ni tunda tazo bata barni na huta ba", mummy ta faɗa tana dungure kan heedayah, Murmushi nakeyi na ƙarasa har parlon inda mummy suka ƙarasa da A.G suka zauna, har ƙasa na je na tsuguna na gayar da Daddy, amsawa yayi cike da jin daɗi, haka itama mummy na gaisheta tana amsa cike da jin daɗi, M.G na gayar, murmushi ɗauke a fuskan shi ya amsa da, "yauwa matar babban yayah, kun samu iso ko"? Nidai murmushi nayi bance uffan ba, hararan shi A.G yayi ya kawar da kai, bayan heedaya ta gaishe da A.G ne ta mun alaman mu wuce ɗakinta, ban wani ja ba nabi bayanta muka wuce, "Aunty naje na soya miki egg ɗin ne ko zamu ci wannan na zubo miki tea"? Murmushi nayi nace, "ga abun breakfast na taho mana da shi, kada ki wani wahalar da kanko, ci kawai ke kaɗai", dariya tayi tace, "aiko naga kuloli kawai ban isa nayi wani rawan kai akai bane tunda tare kuka zo da yayah, amma ae dana biɗe na fara ci, yanzu sai sun gama hirarrakin su tukun ace mu fito" ta faɗa tana hararan tea ɗin hannun ta, nidai murmushi nayi bance mata uffan ba, aiko baifi wasu mintuna ba mummy ta ƙwala mana ƙira, da sauri muka fita zuwa parlon.
A dinning muka same su dukkansu suna zaune, fuskanta cike da farin ciki ga murmushi a kai tace, doug ashe hidima sosai kika mana haka? Gaskiya abu yayi kyau Daddyn kuma sai yabawa yake tayi", ta faɗa tana zubawa daddy a filet, shima Daddy godiya yayi har yasa naji kunya a lokacin, kallon mu tayo bayan ta zubawa mijinta da kanta yadda zai musu, ta cika musu cups da kunun gyaɗan tace, "tou kowa tazo tayi saving kanta da mijinta, kuna na kuma kada a zuba dayawa, a saka dai-dai a bar wa mijina sauran," ta faɗa kowa yana mata dariya, da sauri heedayah ta matso zata zuba, hararanta A.G yayi yace, "ke matsa a wurin don Allah, ki bari wanda ta hanakanta bacci tayi ta fara zubawa, ke ae haka kika bar kanki da mijinki don lalaci da shirme kika taho", aiko baya taja ta tsaya, daga Daddy har Mummy dariya sukeyi, shi ko M.G hararan A.G yakeyi baice mishi komai ba, mayar da kallon shi yayi kan matar shi yace, "dawo nan kafin ya kai miki naushi a kyakkyawan fuskanki, su gama zubawa mu ko sauran nasu ne bamu da matsala zamu ci," ya faɗa ya na maida ita gefen shi ta tsaya, ni dai cike da kunya na zubawa A.G na, gaban shi na ja filet ɗin da cup na ajiye, sannan na zuba ƙwaya biyi anawa filet ɗin, ban zuba kunu ba nace, " heedayah ki haɗa mun tea mana" mummy ne rayi charaf tace, "a'a doug bazaki sha kunun bane? Ko kinfi son tea ɗinne"? Ina murmushi na amsa mata da ehh, dama nayi saboda sune kunun, ni nabar nawa a gida ae, tea ɗin heedayah taje ta haɗo mun, sannan tazo taa zubawa M.G na shi a filet ɗin, kunu ta zuba mishi ta miƙa misho, ta ɗauko cup zata zuba A.G ya dakatar da ita, "kema ki zuba tea ɗin yadda kika ga ita ma tayi karan barwa Daddy, idan kunun kike so idan kin kuma gidanki ki dama", dariya sosai mummy da daddy sukayi, inda Daddy yace "godiya nake ranka ya daɗe, ita bata kawo ba zata shanye mun kununa mai daɗi" ya faɗa yana kurɓan kunun, mummy kuma cewa tayi, "ni banga ta inda wani abu zai shiga cikinta bama idan ba fitina ba, shigowan ku fa ta gama soya egg ta haɗa da tea, shiyasa daga ita har mijinta suke labta uban ƙiba, tsabar cinsu yayi yawa, sun bar mun kai da matar ka baku ƙara ko taki ɗaya ba, sai ma ramewa da kuka sakeyi", kunyar maganan mummy naji har na ɗaga kai na kalle shi, shima kallo na yayi ya mun alaman ae duk nine na jawo. "Daɗin abun ma ae an bawa mijinta, kuma bazai shanye duka ba zai bar mata ko Giwata? Kuma muna zuwa gida zan zo na karɓe na matar ka data ajiye a raba musu", ya faɗa yana duban A.G yana dariya, harara A.G ya zabga mishi sannan yace "ke jata kuje ɗakinki zata fi sakewa ta ci sosai, saura kuma ki cinye naki kici nata", ya faɗa yana ƙara mun sinasir biyu akan wanda na zuba, ita dai heedayah ta tura baki gaba, parlon kuma duk dariyanta sukeyi, haka muka wice ɗakinta wanda hakan kuma wallahi ya fi mun daɗi.
Muna shiga kuwa tace, "kaii Allah ya baki fitinannen miji wallahi Aunty, kuma akwai sauran kunun ne a gida kika bari"? Nidai murmushi nayi na zauna akan lazy chair da yake garkame a ɗakin nata ƙwaya ɗaya, "akwai amma baifi cup 2 ba, wa mijina na ajiye dama ba wa kaima ba, saidai ku raba ke da shi idan mun koma", na faɗa ina fara kai sinasir ɗina baki, "chaɓɓ sai dai kawai na lallaɓa daddy anjuma idan babu kowa ya sanmun, amma cup biyu kam bazai bani ba, kinsan yadda yake shan kunu kuwa shi da Daddy? Ae yafi son kuni ma akan tea, Giwa ne kawai yake son tea, amma mijinki kam dama kunu ya sameki, nima ina so, idan na dama baya kyau ne kawai yasa banayi," ta faɗa tana zama a bakin gadon.
Bayan su daddy sun gama sun kuma parlor ne na fita na samu mummy zata tattare, hanata nayi na kwashe nakai kitchen, ina jin A.G ya ƙwalawa heedaya ƙira ta fito da sauri, nuna mata hanyar kitchen yayi ya juya, shigowa tayi muka wanke komai muka gyara, tambayanta nayi mai zamu ɗaura na rana? Ya mutsa fuska tayi tace, "don Allah Aunty fito mu tafi, akwai fa mai ƴiwa mummy girki, breakfast ne kawai ta keyi da kanta, don Allah fito bacci nakeji, yanzu ina fita mijinki zai koroni", Dariya nayi nace, "gaskiya yai mu zamiyi abinci, nemi wuri kawai ki zauna, idan zaki iya ki fakaici idon shi ki wuce, haka ko akayi ficewa tayi ta gudu, dariya ma ta bani sosai.
Friedge na buɗe na ɗauki mama na wanke na ɗaura akan gas, sannan naga akwai markaɗaɗɗen kayan miya shima na fito da shi, ina haka sai ga mummy ta shigo, "doug kaii jeki huta akwai wacce zata zo ta ɗaura" ta faɗa tana ƙarasa shigowa, "mummy yai kam ta huta, babu komai zan yiwa Daddy abinci da hannu na yasaka albarka", na faɗa ina ajiye kayan miyan, "doug wanda kika kawo mana for breakfast ma ae ya saka albarka, Allah ya muku albarka gaba ɗaya, Allah ya zaunar daku lafiya a gidajenku," haka dai na ribace ta tabari na ɗaura, muna zaune ta ɗauko shuwaka ta gyara, ina ganin haka nagane tuwo takeso ayi kenan, haka na zage na tuƙa tuwon shinkafa mai kyaun gaske, muna hira da mummy da taja kujera ta zauna, duk abinda na nema sai ta nuna mun, haka na haɗa miya ne wanda yaki cyryfish da egusi da stockfish ga nama sosai, muna ciki A.G ya shigo, "ina wannan malalaciyar ita kuma take"? Mummy na murmushi tace, "don Allah amata haƙuri ta kwanta bacci ne" "mummy ita ba mace bace da ku zaku fito kuna aiki ita kuma taje ta kwanta don son jiki? " Mummy tana murmushi tace, "kasan kowa da yadda abu yake zuwa mishi, ita na lura ciki ta samu na gaggawa, kuma yazo mata da bacci da yawan ci, wata macen ranan da aka kaita ranan take samun ciki idan an dace, tou inaga ƴar'uwaka haka nake tunani, saboda haka kayi haƙuri kaima naku da irin na shi salon zaizo" kunya naji ya kamani, don kuwa yace mun ita fah Mummy bata jin kunyar watso zance, saboda haka idan kinje kiyi haƙuri ki saba da haka, sunkuyar da kaina nayo, amma kawai sai naji A.G da wani zance, "mummy ita wannan ae ban san meye matsalanta ba, tunda aka kaita fah har yau period ɗinta bai tsaya ba, ke da yake tsohuwar ma'aikaciyar jinya ce may be zaki san meye matsalan"?
Shiru nayi tsabar kunya naji kaman zan nitse a ƙasa, murmushi mummy tayi tace "shikenan son babu komai, insha Allahu zamu yi magana da ita, zanje koma menene," "yauwa mummy idan kuma tsoro ne ta saka a ranta please ki hanata ni wallahi......" sai kuma yayi shiru yana kallon mummy yakasa cewa komai. Dariya tayi tace, "babu komai son zamuyi magana da ita, bari ta gama abincin mu shiga ciki, idan akwai matsala ma zan sani idan babu ma duk zan sani, ka gajji kuma tou kayi haƙuri, kasan mata da matsala iri-iri", murmushi yayi ya juya ya fice, nidai ji nayi bazan ma iya juyowa na kalli mummy ba wallahi, kai amma A.G bai san meye kunya ba naga alaman shi wallahi, har wa mummy yake iya irin wannan bayanin? Gashi yana magana kaman zai mata kukan nan na shi na jaraba, naga alaman shima idan a kusa da ita yake shagwaɓaɓɓene.
Yana fita kuwa ta sauƙe ajiyan zuciya mai ɗan ƙarfi, nidai kawai kasa sakewa nayi da ita, ita dai sai ɗan jana da hira takeyi nakasa sakewa, ana ƙiran sallah kuwa ta wuce ɗakinta, amma sai da tagaya mun, ina tuƙa tuwa kuwa ya shigo kitchen ɗin, ɗan hararan shi nayi na juyi na cigaba da tuƙawa, haɓan shi ya ɗaura a kafaɗa na bayan ya saka dukka hannayen shi akan kunkumi na, "beauty zanje nayi sallah", dakatawa nayi da tuƙin nace, "A.G nah ya kamata ka iya gayawa mummy wannan zance? Tou yanzu idan ta tambayeni mai zan iya cewa"? Dariya yayi mai ɗan sauti kaɗan, "ki ƙirani zan mata bayani, don ni kam a hargitse nake, ina buƙatar matata", dakatawa nayi da abunda nakeyi cike da mamakin shi nace, "don Allah ka wuce masallacin kada mummy ta shigo", "alwalan ne baby ya lalace" aiko ji nayi kaman na nutse a wurin, gaskiya ashe A.G bai da ta ido, Allah ya taimakeni sai naji muryan Daddy yana neman shi, da sauri ya fice a kitchen ɗin, ajiyan zuciya na sauƙe, na furta "Allah ka taimakeni har mu bar gidan nan kada A.G ya sake kunyata ni, ni dama ashe haka yake ne"? Na faɗa wa kaina da kaina, ina gamawa na wuce ɗakin Heedayah lokacin mummy ta tashe ta tayi sallah, tana yamutsa fuska irin an tashe ta tawuce toilet tayi alwala, bayan tayi sallah ne tace mun zataci abinci sai muje gidan su goggo, haka ko akayi suna gama cin abincin muka wuce gidan Goggo, na ɗauka mummy zata mun magana sai naga bata ce komai ba, gidan Dadda mukaje aka gaisa, mun kai good 1hr a gidan muna hira, godiya sosai Alhaji da Dadda suka mana da zamu tafi, suka mana addu'a sosai, gidan Goggo muka shiga da chan, mun samu goggon kwance babu lafiya, mura da zazzaɓi ne ke damunta, haka muka zauna a parlonta, godiyan sinasir ita ma tayi mun sosai, daga baya ta mana nasiha na zaman lafiya sosai, anan take gayawa M.G mai aikin gidan Alƙali zuwan ta biyu tana so taje gidan shi taga matar shi ta mishi murna, dariya yayi yake gayawa Goggon ya sayi wani ƙaramin gida nan kusa da su na wasu magada ɗaki biyu ne a ciki sai ɗakin girki da ƙaramin store, zai bata ta koma ciki insha Allahu, albarka sosai goggo ta saka mishi, "Aunty nice idan baki manta matar ba, itace wacce ta zabgawa M.G itace a bayan shi Lokacin da yaje gidan alƙali yin waya yana yaro", jijjiga kai nayi alaman na tuna labarin matan, ana sallan la'asaar A.G ya ɗauke ni muka wuce gidan mu, har parlorn ummie ya shiga suka gaisa, ya daɗe zaune a parlon tunda Abba baya nan, hajiya ummah bata nan sunje gaisuwan rasuwa itada Aunty Rakiya da Mamah chan garin su Abba, bayan ya tafi ne nida hafsy muka je na duba jikin sabeer a chan side ɗin mamie, tunda muka shiga take wani bina da kallo daga sama har ƙasa, gaisheta mukayi na duba jikin sabeer da yake bacci, Allah sarki duk ya zabge har abun tausayi, ganin irin kallon da take bina da shi yasa hafsy tace, "Adda muje ko", hararanta mamie tayi ƙasa-ƙasa, muna dab da zamu fice najiyo muryanta tana, " Ayshaa auren sati biyun ne ya wani zabgar da ke haka? Ko baya baki irin abinda ake baki a gida? Ko yafi ƙarfin kine a auratayyah duk ya figar da ke haka"? Nidai murmushi nayi bance mata komai ba, ganin bazanyi magana ba yasaka ta ja tsaki tace, "tou Allah ya rufa asiri, hala a jininku ne keda habiba rashin dace da aure", "ajinin habiba dai, Adda kam ae banga wanda yakaita dace da miji ba a gidan nan, sai dai muce Allah yasaka a madadin su, miji ya ganka yana sonka kam ae duniya ne, idan har ba tura mishi kai akayi ba kam ae kayi dace babba" habiba ta faɗa tana riƙo hannu na muka fita, ina jin mamie na aika mata da zagi, amma ko ajikinta har muka fita ina mamakin halin hafsy na rashin barin sai ta kwana.
Ɗakin ummie dukan mu muka ƙule, daɗi nakeji kaman zanyi yayah, sai ina ganin gidan ya dawo mun sabo, sai shiri ummie take mun na kayan marmari kaman ba kwanan nan tagama na auren ba, har kilishi ta saka aka mana, ga dambun kaji da ta saka aka sake mana, daga ni har su yayah ta haɗa mana kaya rigijib, hira sosai mukeyi har aka ƙira sallan magrib, anan hafsy tace na shiga nayi alwala, "bana sallah hafsy" kallo ta bini da shi cike da mamaki, chan tace "wani irin baki sallah Adda? Yaushe naje gidan ki nasamu bakiyi? Sau uku kikeyi wannan watan kenan"? Girgiza kai nayi ba tare da nufin komai a raina ba nace, "tun wancan bai ɗauke ba, kusan 2weeks fah? Har tsoro nakeji kada jinina ya ƙare", na faɗa ina maida kaina kan ummie da ta shigo lokacin, "ummie kiji wai Adda mensis ɗinta 2weeks bai tsaya ba amma take zaune bata ce wa Yayah A.G suje asibiti ba, sai jininta ya ƙare mu shiga uku", ta faɗa tana wani harara na kamar nice ƙanwar ita kuma yayar.
Kallona ummie takeyi cike da mamaki, "tun yaushe kika fara sokancin ɓoye mun abu irin haka eyyeh ayshaa"? Ummie ta tambaye ni, "ummie wallahi na ɗauka zau ɗauke danaga ya rage zuwa, amma kullum sai naga akwai yananan, ni ummie tsoron aje asibiti ace wani allura za'a mun nakeji", kallona ta tsaya tanayi, chan kuma sai tace "hafsy tashi kije kiyi sallan", tashi hafsy tayi ta fice, sannan ummie kuma ta mayar da duban ta kaina, "yanzu shi A.Gn bai ce miki komai ba? Tun angama bikin ku da kwana nawa ya dawo miki"? Ummie ta faɗa, tura baki nayi gaba saboda nasan yanzu za'ace asibiti, "ummie ni baice komai ba, amma yau da mukaje gidan su naji yana gayawa mummy, inaga tunda tsohuwar ma'aikaciyar asibiti ce zata san yadda za'ayi", ummie ni tun ranan da aka kaini yazo mun, yau kusan 15dys ko 16 ne ma" na faɗa ina duban ummin. Shiru ummie tayi tana kallona, sallaya riƙe a hannunta, "Ayshaa ni wallahi ban san ina zaki kai rashim wayo ba, ae komai kiga baki gane ba sai ki ƙira ki gaya mun, Allah ya rufa asiri, bari muji me ita mummyn zatace tukun, idan abun bai yiwuba sai ki daure kuje asibiti kicire tsoron nan", kaman an taɓo mun abunda yake damuna, "ummie ni tsoron gidan ma nakeji, kinsan abubuwan da nake gani kuwa a gidan"? Ƙawai nasamu bakina da gayawa ummie duk abubuwan da suke faruwa, ido ta zare tana kallona, chan tace, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, shine kuma da ga ke har A.Gn baku gayawa kowa ba? Tou ae wannan kam akwai matsala babba a gidan, hala ma wani matattaran shaiɗanu akaje akayi ginin shine suke damun ku? Gaskiya wannan ba abun da za'ayi shiru bane, bari nayi sallah na ƙira mummyn shin, ae sai suje su sauƙar miki da jininma suce kunzo musu gidan su, gara ayi sauƙan qur'ani kafin abun yayi yawa", tana gama maganan ta fara sallah.
Shiru nayi ina tunanin abubuwan daya faffaru a gidan, ko dai aljanu ne a gidan na faɗa a zuciyata, sai naji zuciyata ya yanke lokaci ɗaya, kada fa sune suka shiga jikina har nake jin abunda nakeji akan A.G? Hankali na nane naji duk ya tashi, a haka hafsy ta shigo ta sameni, "Adda kinyi azkhar ne? Naga kinyi shiru kina tunani"? Lokaci ɗaya sai naji hankali na ya ƙara tashi, tunda naje gida na kuwa nayi azkhar ko karatun qur'ani? Hala ko addu'a idan zan kwanta ma na manta ranan da nayi, ko alwala idan zan kwanta kuwa inayi? Sai naji ƙwaƙwalwata ta kasa tuna inayi kp banayi, sai kawai nabar tunanin na fara azkhar ɗin da hafsy ta tuna mun, ima idar wa na karanta surutul mulk.
Ummie tana idar wa ta juyo kaina, "aysha kima addu'a kuwa"? Shiru nayi kaman zanyi kuka na ƙura mata ido, "hmm Allah ya kyauta, hala daga ke har A.G ɗin kunje kuma wasa da addu'a", nidai bance mata komai ba, wayanta ta ɗauka ta ƙira mummy, ina jin su suka fara magana akan matsalan da nagayawa ummie, nan itama mummy take mata bayanin ae tun ɗazu da A.G ya mata maganan period ɗin ta samu sister ta sukayi magana, suma dama sunyi tunanin ko jinnu ne, don bayan A.G ya kawo ni daya koma ta ajiye shi sunyi magana sosai, inda duk abunda yake faruwa sai da ya gaya mata, nan Mummy tace tou zata samu Daddy ta gaya mishi A.G ya wuce aikin shi chan Abuja shi kaɗai, ni ka abarni a bauchi a gwada magani agani, itama Ummie tace yanzu kuwa zata gayawa Abba, duk yadda ake ciki zuwa safiya zataji ta, bayan sunyi sallama ne ummie ta titsiyeni da wasu abubuwan da mummy ta gaya mata, kawai sai naji kuka yazomun, kuka na ringayi ummie na mamakina, chan dai ta rabu dani ta ƙira Abba ta gaya mishi, amma Abba sai yace wai babu matsala idan anyi hakan, amma ba shi ko ummie bane suke da hurumin nema mun magani, saboda gudun zargi ta barni a gida na ko wurin surukuwata suyi mana magani, don shi Abba cewa yayi ƴat'shi lafiyanta qalau sai dai matsalan daga A.G ne, amma kafin ayi komai shi yafi so muje asibiti akan issue ɗin jinin, haka dai ummie ta rabu da shi don tasan halinshi, ba lallai bane dama ya yadda da maganan wasu iskokai, sai wurin 9:00pm A.G yazo ɗaukana, aikuwa ummie ta haɗamu ta mana kacha-kacha akan addu'a, da kuma zama da alwala, kanshi kuwa ya sunkuyar yana ta bada haƙuri, domin ta nuna mishi dole amatsayin shi ma namiji kuma babba ya dinga hankaltar da ni, har mota hafsy ta rakamu, naso maje naga sabeer, amma ummie ta nuna mun hanyar waje, haka na wuce hafsy tana dariya don ita ta kitsa komai.
A mota babu wanda yace komai daga no har A.G duk munyi shiru, a haka muka tsaya ya sayi Bread da nama sai yougouth muka shige gida, a parlor ya zauna ya ƙura mun ido, "Eeshan A.G kin san ni duk mummy ta razanani da gidan nan? Kinsan nifa mutum baya bani tsoro, don ko ɓarawo ne sai muyi gaba da gaba da shi banji tsoro ba, amma aljani? Gaskiya ina tsoro," ya faɗa yana nuna mun ledan naman wai na ɗauko filet da cups muci, kallon shi nayi baki a buɗe nace, "ni kaɗai zanje kitchen ɗin? Gaskiya ni tsoro nakeji, kawai kazo muje tare", ido ya ƙwalo mun yace, "me zai sameki? Ga wuta ga komai, jeki nima ae dare nake tsoro ba wai yanzu ido naganin ido ba," zama nayi ina kallon shi, ganin da gaske yake bazai rakani ba, "A.G na bazaka raka Eeshan kaba"? Na faɗa ina rausayar da kaina, miƙewa yayi yace, "wuce muje kin cika tsoro," bayan mun ɗauko na zuba mana tare babu yadda na iya, don ni wallahi kunyar cin abincin tare da shi nakeyi, amma yadda ya takura ni haka nake daurewa nake ci, "ina ga gobe tafiyan nan ba zai yiwu damu ba beauty. Washe gari da safe mummy ta ƙira A.G, bayan sun gama wayan ne yake cemun mummy tace yau na maida ki gidan ta, ni kuma mu wuce tare dasu M.G, kinaga babu matsala komawanki wurin mummy"? Hararan wasa na mishi nace, "akan mummyn batawa bace kenan da zai zama matsala don na zauna a wurinta"? Murmishi yayi ya girgiza kan shi , "mummyn muce, ni na ɗauka zasuce kije wurin ummie don zaki fi sakewa". "Mummyn ma zan sake, ae mama nane itama, kuma a haka ne ma zamu saba idan mun zauna wurina ɗaya, ummie ae ta ɗanani tunda ga haihuwa, yanzu kuma turn ɗin mummy ne" na faɗa fuskana ɗauke da murmishi, jawoni yayi jikin shi ya rungume, daidai saitin kunne na yace, "ni kuma yaushe nene turn ɗina"? "forever" na faɗa murya chan ƙasa, shiru mukayi har zuwa wani lokaci, kiss ya mun akan lips ɗina, sannan ya ɗago fuska na muka haɗa ido, murmushi mukayi wa junan mu, murya ƙasa-ƙasa yace " muje na tayaki haɗa kayan ki, ki ɗauki duk abunda kike so", hannuna ya kama muka wuce ɗakina, jaka ɗaya na zuba duk abunda nake buƙata, tunda a gari nake idan basu isa ba zan iya shigowa na ɗauka, haka muka lalace a parlor muna ririta junanmu kaman zai bar ƙasan ne ba garin ba, kuma abun mamaki duk rungume ni dayake yi abun da nakeji shiru, shima taya shi haɗa kayan da zai tafi da shi nayi, danbun da aka mun nayi mishi packaging ɗin shi, haka dai na dinga jin kewan shi tun bai tafi ba. A gidan mummy mukayi lunch, har aka yi sallan la'asaar muna tare dukkan mu a parlorn ta ana hira tare, bayan sun dawo daga mosque ne M.G shi kaɗai ya shigo, idon shi a kaina yace, "matar babban yayah kije yana miki magana, yana side ɗinmu na da", ido na mayar kan mummy, amma sai naga hankalinta baya kanmu, kallon Heedayah nayi na mata alaman ta nuna mun ɗakin, dariya tayi ta miƙe ta riƙo hannuna, har ƙofan parlon ta rakani, fuskanta ɗauke da murmushi tayi ƙasa da muryanta irin na gulman nan tace, "ki fa bar shi ya fito akan lokaci matar yayah", murmushi nayi nayi nocking ƙofan, sannan na buɗe a hankali na shige batare da na bata amsan maganan ta ba, itama tana dariya ta juya da sauri ta koma cikin gida.