Kenza eBookz

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 27

Ana barin halal original by anty nice - Chapter 27

Ana barin halal original by anty nice Chapter 27: Ana barin halal original by anty nice Chapter 27. Pralon babu kowa sai ƙaran t.v da A.C kawai, ƙofan dana…

4,467 words

Pralon babu kowa sai ƙaran t.v da A.C kawai, ƙofan dana gani a buɗe na nufa, don ƙofa uku ne a parlon, ɗaya yana kallon ɗaya a gefen dama idan kashi go, ɗaya kuma yana yamma da parlon, alama wannan ƙofan kitchen ne, waƴan nan kuma ɗaya na A.G ɗaya na M.G, shiga nayi kai tsaye, a kwance na ganshi akan gadon yayi ruf da ciki, tsayawa nayi a bakin ƙofan ban ƙarasa shiga, ba don ganin daga shi sai gajeren wando, bai ɗago ya dubeni ba naji yace "shigo ki rufo mun ƙofan", banja ba na shige na rufe mishi ƙofan, har bakin gadon naje na zauna a ta gefen shi, shiru yayi na wani lokacin kafin ya mirgina ya tashi zaune, hannu ya saka ya matso dani jikin shi, idon shi a lumshe kaman baya kallona, amma nasan kallona yakeyi, murmishi nayi jin ya jawoni gaba ɗaya jikinshi, ajiyan zuciya dukkan mu muka sauƙe, "Eesha Allah yasa idan kunje asibiti ace komai lafiya qalau tsoro ne kawai, idan sunce maganin islamic ɗin ma za'ayi Allah yasa komai lafiya ne Eesha nah". Ajiyan zuciya na sauƙe a zuciyana nace "Ameen" A fili kuma nayi murmushi na saka dukka hannayena na rungumeshi, "A.G nah banji daɗin irin matsalolin da nake tare da su ba, nasan har....." sai kuma na kasa ƙarasa wa nayi shiru, murmishi yayi ya rungumeni gam ajikin shi yace, "kin san har na ƙosa ko? Eeshaa na lafiyan ki da kwanciyar hankalinki yafi mun wani kwanciyar aure muhimmanci, yes ina so naga mun zamu abu ɗaya kodan naga mun Haihu tare, amma nafi son lafiyanki da kwanciyar hankalinki, kawai dai zanyi kewanki ne idan na tafi wlh, gaba ɗaya bana jin marmarin tafiyan ne da zanyi babu ke, nasan M.G ɓata mun rai zai tayi da gangan", dariya ne naji ya kufce mun, shima dariyan yayi ya sake matse ni ajikin shi, munfi mintuna goma a haka sannan ya raba jikin mu ya tashi ya shige toilet, wanka yayi ya zo ya kintsa ya maida wasu kayan, yayi kyau sosai, ya ɗauko agogon shi zai ɗaura nayi sauri na miƙe na ƙarasa inda yake, hannu na saka na riƙe ina tayashi ɗaurawa, ido ya ƙura mun har nagama ɗaura mishi, "Beautyn A.G zakiyi missing ɗin A.Gn ki"? Murmushi nayi na juya kaman zan fuce a ɗakin, rungumoni yayi yana murmushi yace, "haba ƴar fullo a gaya mun mana naji daɗi", ina murmishi nace, "A.G na zaku makara fa, ya kamata muje", "hmmm beauty kenan", iya abun da yace kawai ya kamo hannuna muka fice, parlon muka koma muka samu M.G a tsaye yana magana da mummy, shigowan mu kenan ya kalle mu yace, "yanzu nake shirin ƙiranka na tuna maka flight ɗinmu fah 5:00 ne ya kamata by now mun fita daga gida", ɗan ya mutsa fuska kawai A.G yayi ya harare shi, ƙarasawa yayi har gaban mummy ya ƙarasa, hugging ɗinta yayi yana wani shagwaɓe fuska, "mummy nah" murmushi tayi ta ɗaura hannun ta akanshi tace, "yarona Allah ya tsare ka a duk inda kake, Allah yayiwa rayuwaeku albarka, Allah ya baka lafiya, Allah ya kaiku lafiya, duk inda ka shiga alkhairin Allah ya isar maka" ɗagowa yayi hannun shi yana riƙe da nata aka fita har haraban gidan, heedayah sai ya mutsa fuska takeyi tana kallon mummy, dariya mummy tayi tace, "auta yayah ne ne kam"? Juya ido tayi ta ɗan kalli A.G sai kuma ta tura baki gaba hawaye yana taho mata, kamo hannunta mummy tayi tana "haba auta kukan kuma na meye? Zanzo har Abujan insha Allahu na rako doug, kuma ke kam ma ga A.G ga M.G ae kaman kina gida ne, zasu kula mun da ke nasani" kwanciya tayi a kafaɗan mummy tana hawaye, hannunta A.G ya kamo yana rarrashinta, driver ne ya matso da motan har inda muke, kallona A.G yayi sai naji kaman zan rasa shine, kaman zai tafi wani nisan duniya ne, sai naji hawaye ya cika idona, amma na daure na mayar da shi, lumshe idon shi yayi ya buɗe gaban motan ya shige, M.G kuma da heedayah suka shige baya tana ta kukan shagwaɓa, gaba ɗaya M.G ya birkice ko kunyan idon mummy baya ji yake ta jawota jikin shi yana rarrashinta, tunda A.G ya shige motan bai ɗago ya kalleni ba, ƙure inda yake zaune nayi da idona, amma yaƙi kallona, haka nayi haƙuri na maida idona ƙasa, har suka fice a gate ɗin gidan tukun mummy ta riƙo hannu muka shige cikin gidan, duk yadda tayi ta jana da hira kasa sakewa nayi, sai yaƙe kawai nakeyi.

Lokacin da suka isa sun ƙira mummy sun gaya mata, fatan alkhairi ta musu suka wuce zuwa gida, yadda nakeji suna faɗa Yayah Ahmad ne da Aunty J, sukaje ɗaukan su.

Bamuyi magana da shi ba sai wuraren 9:00 na dare lokacin na fito a wanka, ɗakin mummy ta sauƙe ni, lokacin tama parlor tana waya da Daddy, saboda shima ranan da safe ya wuce lagos, shagwaɓa yayita mun a waya wai shi kaɗai ne a gidan babu daɗi, M.G yaƙi zuwa suyi hira ya wuce gidan shi, nidai dariya nakeji amma naƙi yi, hak nayita rarrashi har da ƙyar ya haƙura, sallama mukayi yace bari ya barni na kwanta tunda da wuri zamuje asibiti gobe.

********** Da wuri washe gari na tashi, gyaran ɗaki da wanke toilet na fara yi, sannan nayi wanka, saboda na leƙo naga an share parlon ana morping, kitchen na shige na ferw doya na soya mana, ganin akwai markaɗaɗɗen gyaɗa sai na dama mana kunun gyaɗa da peppesoup ɗin kifi dana gani a freazer, 9:00 na gama komai, bayan munyi breakfast da mummy muka wuce asibitin *NI'IMA CLINIC* wani gueiny Dr muka gani a asibitin mai suma Dr Robbin son, ƙwararrene a fannin matsalolin mata, test kusan kala uku ya bamu, sannan ya mun wasu tambayoyi, duk na amsa mishi yadda ya kamata sannan ya mun scarning, shima scarning ɗin bai nuna akwai matsala ba.

Bayan 3dys muka koma lokacin dukka test ɗin sun kammalu, shima bayani ya mana akan babu matsalan komai, sannan ya rubuta mana wasu magunguna akan mu saya, bayan 2weeks sai mu dawo, mun dawowa Mummy ta ƙira daddy ta mishi bayanin komai, sai cewa yayi babu komai a jira 2weeks ɗin su cika a koma, idan baiyi daidai ba sai a fara na gidan, haka ko akayi, bayan 2weeks ɗin mukakoma asibitin, dama tayiwa Ummie da A.G bayanin yadda akayi da Daddy da kuma asibitin, suma basu ƙi ta Daddyn ba, nan ma ya sake chanja mana magunguna kuma, bayan wasu gwaje -gwaje da akayi again, nayi 1week ina sha A.G yazo, lokacin yayi 3weeks da tafiya, ɗaukana yayi babu kunya yayiwa mummy sallama muka wuce gidan mu, shi ya tayani muka gyara gidan tsab, har sai da akayi la'asaar tukun muka gama gyara ko'ina, sannan na ɗaura mana abinci, gudun kurna na mana wanda na ɓararraka kaza guda a ciki, sai daya dawo a sallah mukaci, daga nan na gyara wurin sauran na saka a container na saka a friedge, ɗauka na yayi mukaje gidan Goggo gaisheta, don har lokacin bataji daɗin jikin ba, anan muka haɗu da ɗanta Rabiu yayan M.G, mutum mai kirki da fara'a kaman M.G, hira sosai akan ball sukayi da A.G, ni kuma muna hira da matar shi, anan muka barsu muƙa wuce gidan Daddah, sun man alƙawarin zuwa gidan mu. Dadda sai hida take tayi dani, ga shi ƙafa ya sakota a gaba amma bata zama, daga parlon mijinta zuwa nata ma bata ganin wuyanshi, bayan mun gaisa da Alhaji inuwa na dawo parlon Daddah muƙa zauna da ita, shi kuma yana tare da kakan shi a chan, har sai da akayi Magrib tukun muƙa fito, ina ganin shi yayi bauchi club da mu, bayan fitan shi bai daɗe ba ya dawo motan ya zauna ya ƙura mun ido, ganina kallon yayi yawa yasaka na mayar da kaina gefe ina kallon waje ta glass ɗin motan, hannum shi yasak ya riƙo nawa, ina jim shi duk da haka ban juyo ba, sautin murmishin shi kawai naji, nima murmushin nayi yadda yake matsa mun hannu na a cikin nashi, muna haka aka miƙo mana ledan naman, tada motan yayi mukayi gaba, na ɗauka gidan mu zamu wuce sai naga yayi hanyar gidanmu, daɗi naji yau zanje naga ummie, a bakin gate ya tsaya, na juya zan buɗe motan da sauri na, kawai sai naji mota a kulle, juyowa nayi ina kallonshi, sai naga yana danna wayan shi, chann babu daɗewa aka ɗauka, "ki fito mun bakin Gate" iya abunda ya faɗa ya mayar ya kashe wayan, ido na ƙura mishi cike da mamakin shi, meyake nufi bazan shiga gidan mu ba?.

Isowar hafsy wurin ya sakani ƙara shiga mamakin shi, bayan ta gaishe shi ta glass ɗim window shi da ya sauƙe mata, tana dariya ta kalle ni tace "manyan mu barka da dare", harara na mata na mayar da kaina kan A.G, miƙa mata leda biyu yayi yace, "leda ɗaya na hajiya ummah, ɗaya kuma naki ne", ƴa faɗa bayan yace ta gaida kowa da kowa, hannu ta ɗaga mun alaman bye - bye, bayan ta mun gwaliyo, bansan lokacin dana fashe da kuka ba ganin yana shirin tayar da motan shi, kallo na yayi baki buɗe, "lafiya kuwa Eeshaa"? aikuwa kukan na fashe mishi da shi gaba ɗaya, ido na zube akanshi, dariya yayi yana kama haɓa, "lafiyar ki qalau kuwa"? Turo bakina gaba nayi nace, "zanje naga ummie ne", dariya yayi yana kallona cike da mamaki yace, "nono zaki sha ne"? Hararan na mishi ina ƙara sautin kuka na, yana dariyan yaga ina ta ƙoƙarin buɗe motan, buɗe mun yayi yana kallo na yace, "jeki gaisheta ki fito da wuri, ina jiranki", ganin ya buɗe yana dariya yasa na buɗe na fice da sauri, direct side ɗin ummie na shige, a parlor na same su da hafsy, ganina hafsy ta kwashe da dariya, Ko bin ta kanta banyi ba, wurin ummie na kawai na ƙarasa ban bi ta kanta ba, ido cike da mamaki ummie take duba nah, "lafiya na ganki"? Rungumeta nayi nace , "ummie ganinki nake sonyi", murmushi tayi tace, "tou kin ganni wuce ku tafi nasan bai yi niyyan ku tsaya ba, tunda ya ƙira mai kwaɗayin nan taje ta amso saƙo", ya mutsa fuska nayi nace, "ummie kin daina sonane kam"? Jawo hannuna tayi na zauna sosai a gefenta, bayan mun gaisa tace tou na tashi mu tafi, ina shirin miƙewa muksji sallaman shi, hafsy ce ta amsa mishi, ummie kuma ta gyara mayafin ta, bayan ya shigo har ƙasa ya sunkuya ya gaida Ummie, ɗan hira kaɗan sukayi ya tashi ya fice, alama ummie ta mun na tashi nabi bayan shi mutafi, parlon hajiya mukaje muka gaisheta, daga nan dole nabi bayan shi muka wuce gidan mu.

Sabon salo, bayan munci namu naman mun haɗa da tea, sai na wuce ɗakina domin nayi wanka, shima nashi ɗakin ya wuce, na fito a wanka nagan shi zaune akan gadona yana danne danne a wayan shi, ganin haka na daure naje mafara shirin kwanciya, ina gamawa jiki a sanyaye na juyo inda yake akan gado, abun mamaki sai naga A.G a tuntsire yana ta sharara bacci, abun mamaki ya bani, ganin irin kwanciyar da yayi kaman wanda yasha wani maganin mai ƙarfin gaske, ganin haka yasa na gyara ta ɗayan gefen na kwanta bakina alekum.

Bamu muka farka ba sai da hasken rana ya hasko idon mu, a firgice A.G ya farka, salati naji yanayi na buɗe idona da wuri, "Eeshaa wani irin bacci kenan mukayi haka? Har gari fa ya waye rana ya fito,", ƙarasa faɗa yayi yana shigewa toilet ɗin ɗakina, tashi nayi zaune cike da mamakin irin baccin da mukayi, nifa daga cewa bari na ɗan kwanta kaɗan kafin ya tashi shikenan sai da gari ya waye tangararan tukun muka farka?.

Yana fitowa na shige da sauri nayi wanka da brush, bayan na fito ne naga baya ɗakin, amma ga sallaya a shimfiɗe alaman anan yayi sallan, shiryawa nayi na fice zuwa kitchen, ina cikin aiki ya shigo, rungumo ni yayi ta baya, fuskan shi ya ɗaura a kafaɗa na, har ina jin hucin numfashin shi, murya chan ƙasa yace, "Beauty jiya kawai sai nayi bacci, wani bacci mai shegen daɗi, nayi mamakin baccin danayi baby", murmushi nayi ban ba shi amsa ba, haka dai na ƙara aikin nan yana manne da ni, bayan munyi breakfast ne ya sake tambayana naga wani chanji danake shan maganin? Girgiza kai nayi alaman babu wani chanji, "inaga dai kawai a nemi maganin gargajiyan aga ko zai tsaya, ni wallahi tsoro nakeji kada jininki ya ƙare", ya faɗa duk fuskan shi cike da damuwa, nima dai abun yana damuna, amma na ƙarfafa mishi guiwa akan insha Allahu za'a samu sauƙi, wunin ranan dai haka muka ƙare shi rungume da juna, ana sallan magrib Alhaji Inuwa kakanshi ya ƙira shi akan ya taho tare da ni yana neman mu, hijab na saka muka wuce gidan.

Muna isa gidan muka samu mummy agidan suna tare da Dadda a parlon Daddan,, gaishe su mukayi dukkan mu, nidai ina zaune a ƙasan carpet na lanƙwasa ƙafafuna duka, hiran jinya na naji sunayi da A.G da mummy wa Daddah, ita ashe sai yau taji da mummy ta ƙira da safe ta gaya musu, akan ko za'a sama mana mai maganin gargajiya ko na islamic, shine Alhaji Inuwa ya ringa faɗan meyasa ba'a sanar musu da wuri ba? An bar yara suna ta fama da damuwa, yanzu mai maganin ne yazo shine aka ƙiramu, nidai tunda naji sunce mai maganin yazo naji hankalina ya tashi, wani tsoro ma duk sai ya rufe ni, kadafa aje ina da wani matsala ne tuntuntuni.

A parlon A.G ya barmu ya wuce wurin Alhaji, nidai kaina yana sunkuye a ƙasa ina wasa da yatsuna, sukuma suna ta hiran su kaman uwa da ƴar'ta, duk sun ban sha'awa kaman ba surukune ba.

Alhaji inuwa ne ya ƙira wayan Dadda yace muzo parlon shi dukkanmu, da ƙyar na miƙe ƙafana na bi bayan su, duk inda ƙofa yake ajikina zufa yana fitowa, cike da tsoro da wani fargaba da ban san daga ina yake ba suka runtumo mun, a haka dai na cigaba da jan ƙafana har parlon Alhaji, da sallama a bakina na shiga parlon, su huɗu muka same su a zaune a parlon, Alhaji, A.G, sai wani dattijon mutum kan shi da rawani sai jikin shi da Alkyabbah, sai gefen shi kuma wani matashin dattijo ne, wanda a ƙallah zai iya kai shekaru hamsin, nan ma ƙasa na nema ta gefen mummy na zauna, itama mummyn a ƙasa kan carpet take zaune, A.G na a ƙasan naga ya zauna, Daddah ce kawai ta zauna akan kujera kusa da Alhaji, gashe da Alhaji nayi ya amsa mun fuskan shi cike da murmushi, ga annurin dattaku a fuskan shi, mayar da kaina nayi kan wannan Dattijo mai rawani aka nayi, sai naga shima gaba ɗaya fuskan shi a kaina, gaba nane yayi mummunan faɗuwa, saboda haka nayi saurin sauƙe idona ƙasa, murmushi yayi ya maida kanshi kan Alhaji yace, "naji dukkan bayanan ka Ahaji, amma kuma ko ma aljanine ya ke sakata haka tou aljanine na ture, domin daga shigowan ta naga inuwan shi yana mara mata baya, amma insha Allahu komai zai daidaitu", ɗago kaina nayi da sauri na dubi A.G da mukaji muryan shi yace, "Aljani kuma Ranka ya daɗe"? A firgice yayi maganan, daga dukkan alamu abun ya bashi tsoro, murmushi dattijon yayi bai bashi amsa ba, Alhaji kuma sai ɗaga kai yakeyi kawai, daga nan alaramman mutumin ya ƙira sunana "AYSHAA", ɗago kaina nayi ban iya amsawa ba, sai idona danaji suna cikowa da hawaye, alama ya mun dana taso naje gaban shi, ban tashi ba sai idona dana mayar kan A.G, shima kallona yake duk hankalin shi a tashe, Alhaji ne ya sake ƙirana da nazo gaban wannan dattijon, babu yadda na iya ne kawai ya sakani ƙarasawa gaban mutumin, kuma kada kiyi tunanin da ƙafana naje gaban shin, a'a samun kaina nayi da ja da gindi har na ƙarasa gaban shi, miƙawa matashin dattijon hannu yayi akan ya miƙo mishi jakan da yake gefen shi,

Tambaya ya fara mun game da ire-iren mafarkan da nakeyi, da kuma yadda jinin yake zuwa, akan da yawa ne ko kaɗan,? Buɗe baki nayi zan mishi bayani amma naji kaman an naɗe harce na, juyawa nayi da sauri na dubi A.G ko shi zaiyi mishi bayani, amma shima sai naga alaman jira yake yaji mai zance, juyowa nayi zan dubi mutumin kawai naji ya saka mun wani roban faro da yake ɗauki da wani ruwan abu kaman ruwan nono, fari mai ɗan kauri, amma azaban abun a hancina kaman an fasa mun bom a tsakar kaina, haka naji zafi da ƙarfin abun acikin kaina, nidai abunda zan iya tunawa shine naji na yi ihuu iya ƙarfina, sannan na miƙe zan tashi naji muryan mutumin yana umurtan A.G daya riƙeni, daga nan ban san meya faru ba, sai wuraren ƙarfe tara na dare na farka na ganni rungume a jikin A.G, mummy na riƙe da hannayena, Dadda kuma tana zaune a gefen mummy hankali duk a tashe, gefe ɗaya kuma Alhaji ne zaune da waƴannan mutanen, farkawa na ne naji mutumin na hamdalah, sannan ya miƙe tsaye shida abokin tafiyan shi, sallama yakeyiwa Alhaji akan gobe idan Allah ya kaimu da safe ɗayan zaizo, ka duk yadda ake ciki su neme shi, haka Alhaji ya miƙe domin ya musu rakiya, A.G daga inda yake zaune rungume dani ya ke yiwa mutanen sallama, godiya sosai naji su mummy da Dadda suna musu, a haka suka fice tare da Alhaji, tambaya na mummy tayi zan iya tashi mu wuce ɗaki? Juya kaina nayi gefe, da ƙyar na iya buɗe bakina nace, "mummy bana jin ƙafana a jikina", ido ta mayar kan ƙafana a ɗan tsorace tace, "doug ga ƙafan ki, ko kina jin suma miki ciwo ne"? Lumshe ido nayi ban sake magana ba, daga nan naji A.G ya saɓeni kawai yayi hanyar ɗakin Hajiya daddah da ni, lumshe idonayi saboda wani irin ƙunci da nakeji a cikin zuciyata, a haka yaje ya kwantar da ni a ɗakin kan gadon Daddah, zama yayi a gefe na yana tambayan abun da nake so? Nidai a cikin zuciyata bana jin ina son tankawa kowa magana, haka yayi ya gajji ya barni, Dadda ce tazo ta zauna a gefena ta ƙira sunana, ɗago kaina nayi na kalleta, ganin ina kallonta yasa ta tambayeni me nake son ci takawo mun? Ƙura mata ido nayi ban ce uffan ba, saboda wani iri nakeji a cikin jikina da kaina, dukkansu ukun babu yadda basuyi dani ba amma ban tanka suba, haka suka gajji kowa ya koma gefe ya zabga uban tagumi.

Washe gari da safe mutumin nan yazo, wuraren ƙarfe 11:00am yazo, Hajiya ummah kuma da Aunty rakiya tun wuraren ƙarfe 10:00am suka iso, saboda duk yadda akayi mummy ta ƙira ummie ta sanar mata, shiyasa sukayi smmakon zuwa dubani, suma babu yadda basuyi dani na amsa musu magana ba amma fir naƙi, domin wani mummunan ƙunci nakeji a zuciyata, ji nake idan na buɗe baki nayi magana zuciyata zata fashe, Wanka Aunty Rakiya ta sakani na tashi mukaje tare da ita ta tsaya nayi, sannan ta bani wani roba da akasaka ruwan magani kuma naga an zuba wani turare mai ƙamshi a ciki wai nayi wankan da shi bayan nagama normal wanka na, haka dai badon rai yaso ba na karɓa nayi wankan, zani aka bani na ɗaura muka fito, kaskon wuta naga Dadda ta miƙo wa Aunty rakiya, sannan suka koma parlor suka barmu, wani garin magani ta zuba akan kaskon sannan ta sakani na tsuguna akai, bayan na gama ta saka na tashi ta bani pant data manna mishi pad a jiki na saka, nayi tunanin maina zan shafa, amma sai naga labarin ya chana, wani maganine daga gani mayukan islamic ne aka haɗa ta miƙo mun, hattah gashin kaina sai da na shafa mish, ina gamawa ta bani wata doguwar riga mai haɗe da gyalanta nasaka, duk yadda naso shafa turarena ta hanani,

lokacin da mutumin nan ne yazo jikina ya sake burkicewa, don maganin daya shigo da shi akan dole sai na shanye a lokacin ne ya tayar mun da hankali, wanda har sai da na ringa zabga mishi ihuu ina kuka yadda naso, A.G dai sai lallaɓani yake har saida nasha maganin, da ƙyar nasha, sannan ya bada wani magani akan na shafa ajikina sai nayi hayaƙi, aiko da daru da komai sai da nayi, bayan ya tafi ne naji yadda jiya aka ƙare da ni, lokacin mummy keyiwa su Hajiya ummah da Aunty rakiya bayani, hajiya ummah sai zabga salati kawai takeyi, "jiya kam ai munga tashin hankali, ae mutumin yana shaƙa mata maganin ta miƙe a firgece zata gudu, shine ya saka mijinta ya riƙota, nan kuwa suka fara bayani a jikin ta, wai su biyansu akayi da jinin baƙin taure, baƙin agwagwa, baƙin kaza, baƙin yadi, baƙin zare, da tsiren gidan mashaya, kuma wai a hakan ma bai samu daman ƙarasawa jikinta ba, raɓanta yayi," mummy na musu bayani hajiya ummah ta sake zabga wani dogon salati tana kama haɓa, Aunty Rakiya ƙurawa mummy ido tayi, chan ta tambayi mummy "tou basu faɗi waya sayo su ba"? Mummy tayi ajiyan zuciya tace, "cewa sukayi wai wata mata ce baƙa mai ɗan jiki guntuwa, amma sunƙi faɗin sunanta, sun daice wai ta daɗe tana jefawa Ayshann sharruka basu kamata ne, wannan ma sunce tayi wasa da ibadunta ne da zama babu alwala yasa suka sameta," "ehhh babu shakkah zatona ya zama gaskiya, tabbas babu baƙa gajeruwa mummuna kaf a wanda na sansu sai Hauwa, kuma zatayi abunda yafi haka indai zuciyar da yake tare da Hauwa yana nan a ƙirjinta Usamanu bai taimaka an kaita ƙasar indiya a cire ba, don tabbas idan ba'a cire ba Hauwa zata kashe mutum idan ta samu sarari," hajiya ummah ta faɗa tana fashewa da kuka, ido Dadda ta ƙura mata na wani lokaci, kafin daga baya tace, "hajiya wacece hauwa? Akwai wacce kuke tunani zatayi wa Ayshaa irin wannan muguntan ne"? Ajiyan zuciya Aunty rakiya ta sauƙe sannan ta dubi Dadda tace, "matar babanta ce," sannan ta ɗaura da basu labarin abunda ya faru lokacin auren habiba, da wasu halaye na rayuwar mamie tunda aka aurota, ita dai hajiya ummah kukanta sosai tasha, haƙuri suka ringa bata, chan bayan tayi shiru sai ta maida kallonta kaina tace, "ni tsoron da nakeji ɗaya ne, dubi yadda baiwar Allah yarinya ƙarama take fama da sharrin kishiyar uwa ba nata kishiyar ba, dubi yadda Ayshaa tayi jigum taƙi tankawa kowa, tsoro na kada shegen aljanin ya taɓa mata saitin kanta, miji yaje ya gaji yace ya fasa aure, ha yaro sam barka da shi," sai kuma ta sake fashewa da kuka tana tsinewa mamie da zuriyarta kaff, haƙuri sukai ta bata, nidai ban san tafiyan su ba saboda baccin daya ɗauke ni, lokacin dana farka sai na samu sun tafi, A.G ma baya nan ya fita, daga ni sai Daddah, domin mummy ma wai ta tafi chan nata gidan, amma wai zata dawo jimawa.

Ranan monday jirgin safe A.G yabi ya koma Abuja, amma kafin ya tafi mun ɗan taɓa hira da shi sosai, don na ɗanji sauƙin ƙuncin da nakeji, lokacin da Alhaji ya kawo shawaran a dinga kunna mun karatun Al'kur'ani ina saurara.

Na kai 2weeks a gidan Dadda ana mun magani, kuma alhamdllh an fara gani sauyi sosai, domin kwanana tara ina wannan hayaƙin jinin ya ɗauke, yanzu abun da yake ɗan damuna shine rashin ƙarfi a jikina, wasu mafarke da bana iya tunasu idan na tashi, sai kuma rashin son dogon magana, a haka muka cika sati uku cif, sai A.G ya dazo, wannan zuwan tare da M.G suka zo, amma Heedayah an barta a chan, gaba ɗaya A.G yayi wani iri da shi, daga ka ganshi kaga baya cikin kwanciyar hankali, duk sai tausayin shi, da son shi suka cika zuciyata, suk inda yayi idona da hankalina suna kanshi, bayan na idaar da sallan ishaa ne naji Dadda tace na haɗa kayana nabi mijina idan ya dawo daga masallaci, ban ɓata lokaci ba kuwa na haɗa kayan wuri ɗaya, saida suka shigi shida Alhaji tukun muka musu sallama muka tafi, bayan Alhaji yayi mana dogon nasiha da shawarwari akan riƙo da ibadah, sannan aka ja kunnena akan shan magunguna na.

Muna shiga gidanmu nagan shi fes yana tashin ƙamshi, kallon A.G nayi da aman tambaya a fuskana, murmushi yayi yana dubana da kyawawan lumsassun idunan shi yace, "gaggawa da ɗoki irin na sabon ango yasaka nazo da wuri na gyara gidan, hafsy naje na ɗauko ta gyara miki ɗakunan da toilets ɗinki," murmushi nayi kawai na wuce hanyar nawa ɗakin, ina jin shi a baya yana biye da ni, tsaf kuwa nasamu ɗakin da toilet ɗin, kallo na yayi yace, "Eeshaa bari naje nayi wanka na dawo, kafin nan ma kema kinyi wankan, sai nazo musha maganin ko"? Murmushi na mishi kawai bance komai ba, bayan ya fice a ɗakin ne n shige toilet nayi wanka, shiryawa na farayi sai gashi ya shigo, magunguna na ya ɗauko mun dukka nasha, sannan na shafa na shafawa, magic charcol ya kunna nayi hayaƙi na, ina ganin shi yana ta hatishawa saboda asthman shi da baya son hayaƙi, bayan a gama na zauna warin hayaƙin ya ɗan bar jikina kaɗan, chan na ɗauƙo humrah zan shafa naji ya riƙe hannuna, "beauty yyh kuma da ɗauko turare"? Kallon shi nayi jiki a sanyaye nace, "zan sakane kada warin hayaƙin ya dameka", lumshe ido yayi ya ɗan buɗesu kaɗan yace, "hakan bazai yiwuba baby, idan Allah ya bamu lafiya zamuyi karaƙin shafa duk turare da muke so,amma yanzu kam ni *AMINULLAHI GARBA INUWA* na yafe, a haka nake son Eeshaa ta, kuma ni ƙamshin ki nake ji a haka.

Jiki a sanyaye na ajiye kwalban turaren a inda na ɗauko shi kan mirrow, rigan bacci na kawai na ɗauko nasaka, duk abinda nakeyi idon shi na biye da ni, ina gamawa ya miƙo mun hijab ɗin da nake sallah da shi, jiki na a sanyaye na saka, sannan ya miƙo mun socks ɗina na saka.

Sallah ya jamu raka'a biyu, bayan mun idar ya mana dogon addu'a na zaman lafiya, nidai Ameen nake bishi da shi, daga nan ya ɗauko mana cooler da wani cocounut juice mai cike da ƙamshin flavour da madara, duk yadda naso ƙin cin naman kazan da akayi shi kaman danderu, amma bai barni ba sai da naci, a baki ya dinga bani har na ƙoshi, daga nan na shige toilet na wanko bakina sosai, bayan na fito na samu ya kwashe kayan zuwa kitchen.

Readers Also Read