Ana barin halal original by anty nice - Chapter 28
Ana barin halal original by anty nice Chapter 28: Ana barin halal original by anty nice Chapter 28. Gado na hau na ja duvet na rufu, ko minti biyar ban…
4,351 words
Gado na hau na ja duvet na rufu, ko minti biyar ban cika ba ya shigo, ina jin shi yana tambayan yaya na rufe har kaina,? Nidai shiru ban amsa mishi ba, kashe wutan ɗakin yayi ya kunna bedside lamp, a haka ya hawo gadon yana jawo ni jikinshi, "Eeshan A.G shine baki jirani ba"?
Nidai bance komai, wayan shi aka ƙira ina ji yaja tsaki ya katse wayan, murya chan ƙasa yana mitan, "kaji mun munafukin yaro, kagama angwancewa tun shaiɗan yana saurayi, ni yanzu da nake niyyah zaka wani dameni da ƙiran tsakar dare", ya faɗa yana jan tsaki, nidai dariya ne naji yazo mun, ban shiryah ba ya kubce mun, shima ina jin shi yayi dariyan kaɗan ya kwanto a jikina.
Fuskanta cike da murmushi tana wani lumshe ido ta dubeni, "Aunty nice a wannan daren ne alama ya nuna nasamu lafiya, domin kuwa a wannan rana mai cike da tarihi, aminci, ƙauna, amana, da kuma soyayyah, A.G ya karɓi darajana da ƙima na, wanda wannan wata rana ce da bazan taɓa mantawa da shi ba a tarihin rayuwata, Dare ne daya ƙullah abubuwa masu girman gaske a rayuwata da A.g, dare ne mai haske wanda ya haska duniyar mu da A.G, a wannan daren nagama zama A.G shima yazama Eeshaa", kallona tayi fuskan ta cike da farin ciki, sannan ta cigaba, "Allah sarki A.G wato ranan naga rawan jiki da ƙauna, don a wannan daren ya mun alƙawarin mota, kuma haka akayi, washegari kuwa ko idon shine ya rufe, yana idar da sallah ya ƙira mummy a waya, wato nidai naga takaina a wannan rana, don tana ɗauka kuwa yace, "mummy wallahi beauty ta warke, inaga gobe tare ma zamu tafi Abujah da ita", duk sai naji kunya ta lulluɓe ni, ballantana da tace mishi tana zuwa idan gari ya ƙarasa washewa.
Nidai dawowa nayi kaman wata sarauniya, don komai shiya mun, yadda kika san babu wata mace a duniya bayan ni, wato Aunty nice naga so, ƙauna, kulawa a rayuwar A.G, haka yayi komai ya gyara ni ya gyara ɗaki, wuraren ƙarfe 10:00am kuwa sai ga mummy, kayan breakfast ta haɗu mana rinkicicif, ga peppesoup Ɗin kaza daya sha kayan ƙamshi na gargajiya, haka dai itama ta lalace a tarairaya na, ga tonun sili da suka mun, don wallahi sai da ta ƙira ummie ta zayyane mana lafiya ya samu, ita dai ummie murmushi ne nata da hamdala, mummy day sai da akayi sallan magrib ta bar gidan, bayan ta zayyana mishi Dadda tace babu inda zanje sai na ƙarasa magani na, kuma haka babu yadda ya iya, dole da zai tafi ya mayar dani, da zai tafi ƙin sake fuska yayi, ya haɗe kaman A.Gn da dana sani, don ko ni banga fuska ba ranan, ko da ya isa yaƙi ƙiran kowa, sai nice ma ya turo mun msg ya sauƙa lafiya, nima reply na mishi da Alhamdulillah na barshi.
Humm ranan friday sai ga Gwani A.G kam ya dawo bauchi, baki mummy ta riƙe tana kallon shi cike da mamaki, sharewa yayi kaman bai san me yake faruwa ba, daga nan kuwa ya shige ɗakin mummy inda nake kwance ina waya da Hadiza, ganin shi tsaye a bakin ƙofa ya ƙura mun ido yasaka na tashi zaune ina sallama da hadiza.
Ido na ƙura mishi ina kallon shi, shima idon ya zuba mun yana kallo na, "ki shiryah idan kin gama kallona ɗin mu wuce gida" ya faɗa yana wani harara na, dariya ma yabani , "nikan don Allah ka barni anan, bansan me zan iya gayawa mummy ba, ae zataga kaman bamu da kunya", na faɗa ina maida kallona ƙasa, don ganin irin yadda ya ƙura mun ido, hmmm naji yace, sannan ya matso ciki har bakin gadon ya tsaya, "anan kenan kike ga yakamata mu kwana ko"? Ɗaga kafaɗa yayi alaman babu komai hakan, "shikenan bari na sauƙe kayana sai mummy ta bamu wuri mu kwana anan".
Jin abunda yace yasaka na wani zaburo nace, "yayah kuma mu kwana tare da kai a ɗakin mummy? ae ko gidan nan bai kamata mu kwana tare ba ballantana kuma a ɗakin mummy", na faɗa ina sauƙowa da ƙafufuwana ƙasa.
"Tunda kinga hakan bai dace ba sai ki tashi baki alaikum mu wuce inda ya dace da mu, don wallahi yau babu wanda ya isa hanani kwana ɗaki ɗaya gado ɗaya da ke"........ Bai gama ba kuwa mukaji muryan mummy tace, "babu kam Barrister, ke kuma Ayshaa ɗauki kayanki ku wuce, kafin ya nuna mun shi baijin kunyan kowa, kedai ki kula da magungunan ki kinji ko", ta faɗa tana juyawa ta bar ɗakin, kunya naji ya rufe ni, duban shi nayi kaman zanyi kuka nace, "haba mana A.G", hararana yayi yace, "kin tashi ko sai na ɗale gadon"?
Tashi nayi ina ƙunƙuni ƙasa-ƙasa na zuba magunguna na a wani leda, banda shi ban ɗauki komai ba sai handbag, ko sallama banyiwa mummy ba, don ta wuce parlon daddy duk da baya nan, shi kaɗai yaje yayi mata sallama, a tsaye a bakin mota ya sameni, kashe mun ido yayi bayan ya ɗaga mun giran shi duka biyu, nidai kunya ya bani na juyar da kaina kawai na shige motan.
A gidan mu nida shi muka gyara gidan, naso ɗaura a binci amma fir yaƙi barina, dole mukaje *MCDOWALS* muka sayo snacks, sai kaza gashin injin da yogouth, haka ranan ma muka lalace da nunawa juna ƙauna, wannan daren ma darene mai girma a wurin A.G, mun nunawa juna so da ƙauna, kulawa da A.G ya nuna mun har sai da naji kaman babu yani a duniya, ranan monday ya sake juyawa ya koma Abuja, ni kuma na koma gida wurin mummy.
********** Bayan 2month jiki yayi sauƙi sosai, sai lokacin mukayi shirin tafiya tare da A.G, satin da yazo ummie ta ƙirani inda hali na tambayi A.G nazo na duba jikin sabeer, domin yau sai da aka ɗaura mishi drip, hankalina a tashe da yazo na gaya mishi, kuma ana sallan magrib muka wuce gidan mu, muna shiga kuwa muka haɗu da su suna shirin wucewa asibiti da shi, duk sabeer ɗina ya fige yayi baƙi, hankali atashe muka bi bayansu akaje asibitin, *ALWADATA* wani private hospital na yara da yake Fadaman mada mukaje, muna asibitin har 10:00 na dare ana abu ɗaya, sai da mukaga an bsu ɗaki har an saka mishi drip yana bacci tukun muka tafi, duk zuciyata babu daɗi muka dawo gida.
Ƙarfe shida bayan mun gama azkhar munyi karatun qur'an, sai ga wayan ummie ta ƙirani, wani irin faɗuwan gaba sosai naji ya kamani, amma na daure na ɗauka, bakina yana rawa na gaida ummie, "Ayshaa" naji ummie ta ƙirani a hankali, da ƙyar na amsa mata, tambayana yyh A.G yake tayi, shima amsa mata nayi da yana lafiya, sannan cikin lumana da nasiha take gaya mun Allahn da yafi mu son sabeer ya karɓi abunshi, idan A.G ya amince nazo kafin a kaishi, kuka sosai na fashewa ummie da shi, wanda tayi sauri ta kashe wayan, da sauri A.G ya matso jikina ya rungumeni, bai tambayeni komai ba don volume ɗin wayana daya ke bayyane ya kai mishi komai, rarrashi na yakeyi har zuwa wasu mintuna, sannan yace na tashi na sake wanka muje, shima ɗakin shi ya wuce yayi wanka, bayan nayi wanka na saka dogon rigan atamfah ta soso, sannan na ɗauko hijab green kalan atamfar na saka, sai ga A.G ya shigo da cup ɗin tea a hannun shi, babu yadda na iya haka ya takura ni sai dana sha half na tea ɗin tukun muka tafi gidan mu, duk illahirin ƴan gidan s]na parlon mamie, gaban ummie naje na zauna n kwantar da kaina a kan cinyanta ina kuka, tabbas naji mutuwar Ɗana sabeer, amma babban damuwa na na rabu da wani abu daya danganci habiba, don mutuwar habiba ne najishi ya dawo mun, kaman yau akayi rasuwan nakeji.
Ko kunya mutane mamie bataji ba lokacin da Aliyu da maman shi suka zo da ƴan'uwan shi, haka ta dinga fade -faɗen magana ana hana ta amma batayi shiru ba, har Allah ya isa saida ta musu, amma da yake mummyn Aliyu tafita bariki ko bin ta kanta batayi ba, ɗaukan gawan jikanta tayi ta mishi addu'a, shima Aliyu addu'a yayi mishi sosai yana share hawaywn shi, gefe ɗaya kuma amaryar shi tana zaune cikin ƴan'uwan shi, har ita mamie bata bari ba ta zage ta tsaf, lokacin da suka gama kuwa suka ɗauki gawan yaronsu suka gita domin ayi mishi sallah, lokacin kuwa Aunty Rakiya ne ta mata jan ido ta nuna mata bata isa ba sue da ƙarfi akai, gashi gida babu Abba babu mazajen gidan, mudai munga fitina da tashin hankali ranan, don ƙarshe sai da sukayi uwar watsiya da Aunty Rakiya da Mamah, don da abun yafara tsamari wai Abba yace tunda A.G yana gidan ya tsaya akan komai kafin su iso, ai kuwa inda ta shiga bata nan take fita ba, shine su mamah suka taso mata, don tana farawa ummie ta jani muka fice, hajiya ummah sai da ta kusan tsine mata albarka ranan, nidai ban sake komawa ba sai da zamu tafe A.G yajani muka shiga, nan ma sai da ta gaya mana abunda banji daɗi ba, ina ankare da A.G duk sai mamakinta yake tayi, jiki na a sanyaye uka wuce
Washe gari kuwa Abba da yayah muhammad suka zo, kacha -kacha Abba yayi mata ka yace kowa ma ya watse a zaman, kuma ya ƙira Raliya da itama ranan tazo yayi mata kacha-kacha yace kuma ta juya ta tafi, nima ya mana sallama da A.G yace mu wuce Abuja baice mu zauna ba haka ya isa, abarta da halinta, Allah yaga yaron jinin habiba ne, baida hakkin girban ayyukanta shiyasa Allah ya ɗauke shi batare da ya girma ya girbi baƙin ciki ba.
Hafsy da Huda ce suka mana rakiya zuwa Abujah, mun isa lafiya muka samu Aunty B da Aunty J sunzo, tare suka sake gyara mun gidana da Heedayah, mun samu an mana abinci, ga drinks kala-kala da suka mana, heedayah ce tazo ta rungume ni, ga cikinta da bai wuce 5month ba ya fito ɗas da shi, bayan ta sake ni ne taje ta rungume Hudah, hararanta A.G yayi sannan ya wuce ciki, gaskiya gidan yayi kyau kuma ya tsaru sosai, ga wasu kaya da aka saka mun a gidan kaman ma sunfi na bauchi kyau, da yake jirgi muka biyo sai babu gajjiya a jikin mu, abinci muka haɗu mukaci da su, M.G suna tare da A.G a parlor, hira sosai mukayi da su Aunty, daga baya suka ce zasu tafi, sun so su tafi tare da hafsy amma A.G fir yaƙi, daga Hudah har hafsy yace a gidan zasu kwana, don heedayah taso su tafi gidanta da Hudah, kallo ɗaya A.G ya mata ta risina, ita dai Hudah murmishi kawai tayi tace wa Heedayah ta bari kafin ta taɗi zata zo mata, "dayake mijin ta ne ya kawoki ko"? Ya faɗa yana hararan Heedayah, ita dai miƙewa da sauri tayi tana girgiza mishi kai alaman a'a, shi kuma M.G dariya kawai yake don yasan darun A.G.
Da wuri su Aunty B suka mana sallama suka tafi, dukkan mu uku muna zaune a parlor bayan tafiyan su M.G ma, amma shi kuma A.G ya wuce ɗakin shi, abun gwanin burgewa gidan, gashi dai 2bedrooms ne, amma a mugun sake gidan, don ɗakun A.G yana parlor, shima bawai ƙofan cikin parlor kai tsaye bane, zaki bi wani ɗan corrido ne daga parlon sai ki samu ɗakin shi, tou duk abunda ake a parlor bazai dame shi ba, haka shi bazai takura na parlor ba, imda dinning section yake nan ƙofan shiga kitchen yake, akwai store mai ɗan girma a kitchen ɗin, daga nan zaka fice ƙofan baya, wanda tanan ma zai sadaka da gidan Heedayah shima ta nata kitchen ɗin, amma tsakiyan su akwai wani ɗan boysquater mai ɗauke da ƙaramin parlor da ɗaki ɗaya da store, a parlor zaki bi wani ɗan dogon corridor zuwa ɗakina, ɗakine babban gaske, ga toilet ga kuma wani ɗan ƙaramin ɗaki a cikin ɗakin, kaman wurin da zaki ajiye wasu kaya haka akayi wurin, idan baki son shirgi a ɗakinki, may be ma wata zata iya mayar da shi ɗakin yara ma, don zai ɗauku madaidaicin gado da sauran tarkacen gado.
Fitowan A.G ne ya nuna mana an ƙira sallan magrib, ido ya ƙura mun yna maida links ɗin rigan shi, miƙewa nayi ina faɗin, "bari mu tashi muyi alwala, ashe an ƙira sallah"? Lumshe ido yayi ya sake buɗesu akaina, batare da yace mun uffan ba ya maida kallon shi kan Hudah, "babu buƙatan wani abu ko"? Sannan ya ƙure hafsy ma da kallo, jiran ko da mai buƙata a cikin su, murmushi hafsy tayi ta juya kanta alaman babu komai, sannan ta miƙe hanyar nawa ɗakin tana faɗin, "sai ka dawo Yayah", amsawa yayi sannan ya ƙure Hudah da ido, itama murmushi tayi tace, "Yayah babu komai, komai da muke buƙata naga sun kawo, sai ka dawo Allah ya tsare", ta faɗa tana juyawa hanyar ɗakina.
Giran shi ya ɗaga mun duka biyu, alaman nifah? Murmushi nayi nace, "babu komai Jarumina, fatan kadawo mun lafiya kawai damuwa na", na faɗa ina kallonshi ina ɗan rakuɓewa gefe kaman munafuka.
"Jarumi ko"? Sannan ya lumshe ido ya buɗe, "Jarumin ki ko? Lallai da magana, bari na dawo kimun bayanin jarumtar A.Gn ki yarinya".
Baki na ɗan rufe kaɗan da hannu na ina dariya, "nifa bana nufin komai ranka ya daɗe kawai dai...... Kawai dai fatan ka dawo lafiya ne nima nayi maka", na faɗa ina dariyan shi, shima dariyan yayi mai kama da murmushi ya wuce waje, domin ƙiran shi da naga M.G yayi ta waya, bai ɗauka ba kawai ya duba ya mayar da wayan cikin aljihun shi.
Ɗakina su Hudah suke shirin bacci, ni kuma na gajji da mitan Hudah akan na tafi wurin ɗan'uwanta na bar shi shikaɗai, ita dai hafsy tana kwance rub da ciki tana ta wayanta da yayah ishaq, kaman munafuka ko muryanta baka tsinta, haka na shige toilet nayi wanka da ruwa mai zafi, bayan nagama na fito na shiryawa cikin wani rigan bacci red colour, rigan dogone ya ɗan wuce gwiwa na kaɗan, amma kuma hannun shimi ke gareshi, gaban rigan gaba ɗaya net ne, gashi yana da alaman gidan bra, magani na nasha wanda hudah ta sake jaddada mun, nasha nayi hayaƙi, na kuma shafa na shafawa, daga baya nasaka rikan bayan na jira ƙaurin jikina ya ɗan rage, hijab ɗina na ɗauka har ƙasa na saka, sai da safe nayiwa Hudah, hafsy kuma mari na ɗaka mata a cinyoyinta na fice.
Ido ya ɗago ya ƙura mun tunda na shigo parlon, nima idon na ƙura mishi bayan naja wuri guda na tsaya, ganin haka ya saka ya buɗe dukka hannayen shi, "ki matsar da wannan abun jikin kin kafin ki ƙaraso nan baby girl", zare hijabin nayi idona yana kanshi, akan kujeran da yake gefene na ajiye, sannan na sauƙe ajiyan zuciya mai ɗan ƙara kaɗan ganin yadda A.G ya wani lumshe idanun shi kaman ba zai iya ganin mutum ba ya ƙura mun, hannun shi ya ƙara buɗewa yana mun alaman na ƙarasa wurin shi, nidai cike da tsarguwan warin hayaƙin da jikina yakeyi na ƙarasa, kan cinyar shi ya zaunar dani, dama ya cire rigan shi sai wani white singilet ne ajikin shi, sai dogon wandon shi, zama nayi sosai akan cinyan shi, shi kuma yasaka hancin shi yana shinshina wuya na, abun har mamaki yake bani, ni da nake warin hayaƙi shi kuma yana wani shinshina ni, da ƙyar na samu ya iya tashi muka wuce room ɗin shi, muna shiga ya kwantar dani ya wuce toilet ɗinshi, ya daɗe sosai sannan ya fito yana ta zabga ƙamshin shwer gel ɗin dayayi wanka da shi, shiryawa yayi gaba ɗaya hankalinshi ya tafi kaina, hmmmm Aunty nice A.G nah nace miki duniya ne, babu wata ƴa mace inaga a doron duniya da tayi dace da miji mai tsananin sonta ba irina, gaskiya A.G ƙarshe ne a nuna so, ashe dam haka sirrin auren shiru -shirun namiji yake? Wato Aunty nice babu dare ko rana da A.G zai kasance dani bakiji yana kuka ba, kuka kuma da hawayen shi, wani sa'in har tsoro nakeji naga kaman suma zai mun idan yana kwance dani, kuma hakan sai na lura nima wani shauƙi sosai ya ke sakani, ji nake babu wata mace da ta fini dacewa da miji a duniya".
nidai murmushi nayi ina ƙara maida kaina da nutsuwana kan Hajiya Aysha mayar A.G uwar Nana khadijah (Mamah) A zuciyata kuma nace naki kika sani nima haka nakeji nawa Gwarzon yafi naki iya nuna mun so da kulawa, don kawai ....... Kawai dai shikenan, na faɗa a zuciyata, a fuskana kuma na bita da murmushi, ina ƙura mata ido, idan kuma nayi ƙarya ku tambayi , *sahibata ummie yawale* nima tasan irin son da nawa mijin ya mun, wane wani A.G 😡.
Hudah da hafsy sun mana 2weeks, da ƙyar A.G yabar Huda taje gidan M.G tayi 2dys, Shima sai da yaga ran M.G ya ɗan ɓaci ne, don yace idan yana ganin gidan heedayah gidan ƙanwarta ne, wato shi ba yayan huda bane shi bare ne ko? Shi bai wani ɗauka ta wurin yayan shi mijinta ba, shima ae ɗan daddy da mummy ne, amma idan A.G ya cire shi babu komai Huda basai tazo gidan shi ba, ganin yau ɗaya M.G ya nuna ɓacin ranshi yasaka yace taje tayi 2dys, hafsy kam dama 5dys tayi a gida na ta ɓalle chan gidan su yayah, wai a cewar ta da zaran A.G ya shigo tou bata wani ƙara ganina, wai bana bata kulawa, kaji sharri irin na autar ummie, naji daɗin zama dasu wallahi, da zasu tafi duk sai naji kewar su ya ishe ni, amma babu yadda na iya haka suka tafi, tare da M.G da kuma yayah Ahmad suka tafi, mota suka bi a komawar su, A.G nah yana fita office kuwa heedayah take shigowa, biyar nayi take guduwa nata gidan, gashi cikinta mai ƙin yin girkine, Allah yasota M.G baida fitinan sai tayi kaza tayi kaza, bata ma yin girki banda breakfast, Ni nake mana taci ta tafi da na M.G, gashi bai ma yawan zama a Abujah yanzu sosai, kullum yana hanyar lagos, yakanyi 2weeks a chan kafin yazo yayi 5dys haka a Abuja.
Bamufi 2month da dawowa ba nafara laulayin mai zafin gaske, gashi ya sakani wani irin shiru da rashin son cin abinci, A.G yayi fama dani akan abinci amma fir naƙi, saidai zan wuni ina shan ruwan tea, shima black tea, a haka har na shiga 3month, lokacin heedayah tana 8month, wata rana A.G ya fita da wuri shida Yayah Ahmad, kasa tashi nayi na mishi ko ɓreakfast, shima bai wani takurani ba, fita sukayi bayan ya jaddada mun nine nayi na tashi nayi wankan magani nasha tea, da ƙyar na amsa mishi ya fice, daga nan kuma Heedayah ya tattaro yace ta dawo parlor na ta zauna, idan nine yayi ta tasheni nayi wanka nayi break, haka doe tazo ta kwanta a parlor tana kallon dole, don ba gwanar kallo bace ita sai yawan son karatun hausa novel, inda muka ƙara ƙullewa da ita ma kenan, duk da A.G baya son karatun haka ya barni.
Bacci na nakeyi cike da wasu birkitattun mafarki, a haka nayi mafarki wai gani nan a garin bauchi ina kwance a ɗakin hajiya ummah, kuma alama ya nuna kaman ina gida lokacin banyi aure ba, amma ka ina kwance da ciki a jikina rusheshe, ina so na tashi amma kuma na kasa, chan sai naga ƙofa ya buɗe wata mata mai fuska a rufe da wani abu ta shigo, hannunta ɗauke da wani jaririn yaro fari sol an mishi kwalliya, kyaun yaron sai ya mun kaman fuskan A.G, duk sai naji hankalina da ƙauna na ya koma kan yaron, yana ta wasa da hannayen shi da ƙafafun shi, chan sai naga matar ta yaye abunda ya rufe fuskan ta, kawai sai naga fuskan mamie tana mun wani dariya har da hawayenta, tana kuma nuna mun fuskan kyakkyawan yaron daya ƙura mun ido yana kallona kaman ba baby ba, gashi fuskan sak na A.G, amma kuma yana so yayi kuka alaman wurina yake son zuwa, "kina son ki karɓi yaron ne"? Naji muryan ta tana tambaya na, daga bayanta kuma sisto na habiba ce take mun alaman a'a da kanta, ita kuma tana riƙe da ƙofa tana kokiwan shigowa amma sai naga an figo ta ta koma baya, chan saiga Raliya da surkuwarta sun shigo suma suma dariya, hannu na miƙa don na karɓi jaririn da yake ƙoƙarin miƙo mun hannunshi, kawai sai naga sun haɗu su uu sun koma mutum ɗaya amma da fuskan mutum uku, wato mamie, raliya, surkuwata, jeho mun babyn sukayi ya faɗo jikina, abun mamaki duk kyaun da nagani da fari a tare da yaron sai ya juya mun baƙiƙirin da suka jeho mun shi kan cikina, kuma hannayen shi duk sun watsu a jikina kusan guda goma ko fi, don ko ta ina sun manne a jikana, gashi ya wani ƙamƙameni yana ƙyalƙyalah dariya irin yadda suma sukeyi, aiko banbi takan nayi addu'a ba kawai sai na zabga wani rin ihuu mai ƙarfin gaske, daidai lokacin kuma naji na farka da wani uban ƙara a bakina, ga zufa daya gama wanke mun jiki kaman wanda nayi tsere, ina tashi zaune kuma saiga Heedayah ta faɗo ɗakin da saurinta, jikinta duk rawa yake tazo ta rungumeni a jikinta.
Jinta a jikina nima nayi saurin rungumeta ina kuka, gashi gaba ɗaya illahirin jikina rawa yakeyi, inda mamie suka tsaya na ƙurawa ido, amma sam babu kowa ballantana komai, "meya faru Aunty kike ihu"? Heedayah da duk hankalinta yake tashe ta tambayeni, jikina da muryah nah gaba ɗaya rawa sukeyi, da ƙyar na buɗe baki nace, "zuwa sukayi suka bani tsoro da jariri", ina gaya mata abunda ya faru duk ta wani firgice, da sauri ta ɗauki waya ta ƙira A.G nah, sun riga da sun fita a gari shida yayah Ahmad, suleja sukaje Domin zasu gana da wani mutum daya nemi su, umurni ya bata da na tashi ta taimaka mun nayi wankan maganina, kuma ta tabbatar nasha tea da bread, kuma kada ta yadda su kunna kallo idan ba karatun qur'ani ba a gidan, haka akayi wanka ta riƙe ni akan na tashi naje nayi, ai kuwa kaman jira ake naje daidai ƙofan toilet ɗin sai naji wani iein mummunan murɗawan ciki mai azaban gaske, hannun ta na riƙo da ɗan ƙarfi na runtse ido na, chan sai naji abu shaaaa ya zubu mun ta ƙasa na kaman wani ruwan naƙuda idan mace zata haihu, dagani har uta muka ƙurawa ruwan da yake zuba kaman wani fitsarin sati guda na riƙe.
Sai da ya gama zuba tukun naji na fara jin wani azababben ciwo a marana, amma haka muka ƙuƙuta muka shiga toilet ɗin, da ƙyar na samu na tsaya, ai kuwa tana fita naji marana yayi wani mummunan ƙullewa, sunanta na ƙwala ƙira da ƙarfi, da shigowanta da ɓalluwan jini a jikina duk lokaci ɗayane, daga nan sai naga toilet ɗin yana mun duhu, ɗif kuma sai naji komai ya tsaya mun.
Lokacin dana dawo hayyaci na sai na samu kaina kwance a gadon asibiti, gefe na A.G ne zaune ya yi tagumi, yayah Ahmad kuma tsaye ya rungume hannayen shi a ƙirji, heedayah kuma zaune ta buga ubantagumi, da sauri A.G ya matso kusa dani, daidai kuma Aunty B na fitowa daga toilet ɗin ɗakin, "beauty sannu", naji muryan shi kaman wanda zaiyi kuka ya furta, matsowa yayah Ahmad yayi kusa damu, shima sannun ya mun, nidai ido kawai na bisu da shi, chan kuma na lumshe ido na nayi shiru, inajin yayah Ahmad nagayawa Aunty J a waya na farka, wanda daga dukkan alamu ita tana gida ne, gefe na Aunty B tazo ta zauna, hannun ta tasaka ta riƙe hannu na tace, "bestyn besty kin tashi? Sannu ko besty".
A.G Dr ya ƙira a waya ya gaya mishi, babu daɗewa nurse ta shigo ɗauke da tray ɗin sun nan, ita da Aunty B suka taimaka mun na tashi muka shiga toilet, wato daga dukkan alamu nasamu misscarrige, mummunan tashin hankali naji ya sameni, amma na ɓoye don kada su fahimta nai kunya, haka suka tayani nayi wanka, gyara jikina nayi da pad, muna fitowa Aunty B ta bani tea mai kauri wanda na samu heedayah na gaurayawa, hannu na saka na karɓa, ina zaune a bakin gaɗon ƙafana suna ɗaure akan kujeran da A.G da ya zauna,shi kuma yana zaune a gefe nah ya doka uban tagumi.
Allura nurse ɗin ta mun da wani magani , bayan ta gama ta fice a ɗakin.
2hrs na ƙara aka sallame mu, bayan mun shiga Dr yayi mun scarning, inda naji Dr yana yiwa su yayah da A.G bayanin cikin gaba ɗaya ya fice ba sai anyi wankin ciki ba, jiki a sanyaye A.G ya amsa mishi, sannan ya bamu takaddan maganin da zamu saya.
Gida na muka taho tare dasu, bamu daɗe ba Aunty J tazo tare da Areefh ta kawo abinci, suna nan a gidan dukkan su har 10:00pm, munyi waya da su ummie, Aunty Rakiya, mummy, hajiya ummah, hattah Abbana da Daddy sun ƙirani, a gidan Aunty B ta kwana da ni, kuma inaji hajiya ummah tace kada ta barni nasha ruwan sanyi kuma nayi wanka ko na sati biyu ne zuwa uku.
Washe gari kuwa Abba na ya shigo ya duba ni, inda yace daga lagos yake, kuma gobe zai wuce bch, idan yaje ummie zasu zo su dubani, nidai ranan farin cikin zuwan Abba na kaman zanyi yayah, da zai tafi kaman zanyi kuka yana riƙe da hannu na har jikin motan shi muka raka shi, a kunne ya sunkuya ya gaya mun "insha Allahu sisto zan dinga zuwa dubaki idan kinyi murmushi", ae kuwa dariya na ƙyalƙyale da shi, hakan kuma ya saka shi shima yin dariyan su yayah suna taya mu.