Ana barin halal original by anty nice - Chapter 29
Ana barin halal original by anty nice Chapter 29: Ana barin halal original by anty nice Chapter 29. Bayan kwana 2 da faruwan haka kuwa sai ga su ummie da…
4,248 words
Bayan kwana 2 da faruwan haka kuwa sai ga su ummie da mummy, hajiya ummah da Aunty Rakiya sun zo, naji daɗin ganin du ainun, da suka shigo na rasa wurin wa zanje kawai sai na rufe fuskana da hannu na ina dariyan daɗi, don babu wanda yace mun zasu zo, mummy naje na fara hugging tana dariya na ita ma ta rungumo ni, hajiya umma ta turo baki gaba tana , "don Allah ja jiki da munfurcinki yarina, nidai ku bani wuri na zauna kada kayan takaici ya kaini bango, nasan da ba don ganin idon surukuwar ki ba nuna mana zakiyi bamu taɓa haihuwa ba, uwarki zaki runguma, kaman mu bamu da yara Allah na gode mishi ma da ya bani usmanu, ɗaya tamkar da dubu" riƙo hannunta yayah Ahmad yayi yana zaunar da ita akan kujera, cikin muryan shi marar hayaniya yace, zaunawar ki lafiya uwar usmanu", dole ita ma tayi dariyan, bayan duk sun zauna na koma daf da Aunty rakiya na zauna akan cusion da yake ƙasa a wurin, gaishe su nayi ɗaya bayan ɗaya, sannan suma suka mun yayah jiki, duk ido na ya na kan ummie nah, itama muna haɗa ido take sakar mun da murmushi.
Shigowar heedayah ne ya mayar da hankalina kanta, tana tura ciki gaba ta rungume mummy tana dariya, ita daga alama bata san da zuwan su ba sai yanzu, abun karyawa Aunty B ta fito musu da shi, saboda isowan ƙarfe 9 sukayi, dayake flight ne, saboda kada uwar usmanu ta gajji a mota, ɗakina ta wucewa su mummy da ummie, Aunty Rakiya dai tace a barta tare da ummanta, A.G sun fita tare da yayah, ɗaki heedayah ta bisu, nidai ina xaune tare da su, nima tare da su mukayi break ɗin.
Naji daɗin zuwan su, duk da ummie na bata kwana gida na ba, chan gidan su yayah suka tafi tare da Aunty Rakiya, hajiya ne ta kwana mun duka biyun da sukayi, mummy ma kwana ɗaya tayi taje gidan M.G, duk da A.G yaso yi mata gardama amma tace ae chan ma gidan ɗanta ne, kuma ranan M.G ɗin ya dawo, babu yadda ya iya haka taje.
Ranan Laraba Suka koma, haka kuma bayan nayi 2weeks Aunty B ta tafi, naso na kara jin karfin jikina ba tare dana komawa A.G ba, amma kaman yana jiran tafiyan Aunty B ne ya ƙiya mun, dayake jinin baifi kwanki kaɗan ba ma ya tsaya, tou Allah ya so Aunty ta ɗan mun gyara ba mai tsananin yawa ba, dahuwar kaza na nonon raƙumi, da gumba sai wasu da zansha da nono ta saka wata mata ƴar sudan ta mun, ga kuma dahuwar wani kazan kaman gasa shi akayi da maganin ajiki, kaman dai irin anyi tukunyan nan da shi, haka kuwa nasha gumurzo a hannun jarumin mijina.
Babu wuya wurin ubangiji, ranan 10/08/2022 heedayah ta haifi ɗanta kyakkyawa mai kama da M.G, lafiyayyen yaro mai kyawawan ido irin nasu heedayah da jarumina, don idan ka kalli yaron zakace sak M.G, idan ka matsa kuwa sai kace gidan su maman shi ya biyo, amma a zahiri farin shi da siffanshi, da kamanin hancin shi da komai irin na M.G ne, amma ƙwayyar idon shi sak nasu A.G da su heedayah ne, yama fi kama dana A.G, ranan farin ciki kaman zai huda zuciyar mu, A.G yaje bauchi akayi haihuwar, saboda haka ranan gaba ɗaya tarewa nayi a gidan bayan an dawo daga asibiti, kuma gaskiya daga Aunty B har Aunty J sunyi kara sosai wa A.G da M.G, don abunda zasuyi idan ni na haihu tou haka sukayi wa Heedayah, sun yi komai a mutumce, muna dawowa gida Aunty B ta ƙira wata ƴar'uwarta babbar matace da take zaune a suleja tazo har gida ta wanki yaro tsaf, fararen kayan sanyi aka sake saka mishi, sai naga ya ƙara wani haske da aka mishi wankan, nono aka saka heedayah ta bashi, da ƙyar ta yarda tasaka mishi nonon, don sai da Aunty j tayi da gaske da ita, yana kamawa kuwa ta fara kuka, nidai banda dariya babu abunda nakeyi, harara na Heedayah tayi tana jijjiga kai, "wallahi Aunty na lura tun kafin na haihu kike mun dariya, Allah kaɗai yasan ke me zaki aikata, gara ni ma halah", ta faɗa tana ƙara matse idonta don yadda babyn ya kama kamam ya shekara a duniya da ƙwarewa, nidai dariyan na sakeyi ina kallonta nace, "nifa kin san me yake sakani dariya ne? Tou matar da take cikin labour me ya kaita salati da kuma waƙa a lokaci ɗaya, ni shiya ɗaure mun kai, dama ana haka ne"? Na faɗa ina dariya, dukkan su dariyaɓ suka ƙyalƙyale da shi, hattah ita kanta mai haihuwar dariyan abunda tayi takeyi, "Allah ya nuna mana naki yarinya, hala ma pareri zakiyi" Aunty J tafaɗa tana zama bakin gadon, nidai karɓan babyn nayi na ƙura mishi ido ina murmushi, "ni wallahi kada ace nayi son kai, nidai yaron nan kyaun miji na ya ɗauko wallahi, jibi da ya buɗe idon nan kaman na Jarumi na, kai Masha Allah", na faɗa ina yiwa babyn kiss a fuskan shi.
"Chabb kaji wani zance, kina ga yaro ya ɗauko kyaun baban shi zaki wani haɗa shi da mijinki mai ɗaurarren fuska? Nidai ɗana kyaun Giwa na ya ɗauko", heedayah ta faɗa tana wani fari da ido, bakina a buɗe ina kallon ta, dariya su Aunty suke mana, wato kowa nata gwanin ne kyakkyawa.
(Na manta ko na gaya muku Aunty J ta haihu itama? Tana da yaro namiji, yanzu kuma dukkansu suna ɗauke da ciki ita da Aunty B, ita Aunty J lokacin da Ayshaa tayi ɓari cikinta ya kai 3month, so yanzu cikinta 5month, ita kuma Aunty B yanzu ne take cikin na, 3month, ita kuma ayshaa na maƙale da ɗan 2month, wanda daga ita har A.G alokacin basu da labarin shi, don tunda tayi miscarrige bata sake ganin period ba, so batayi tunanin ciki bane a lokacin, don bai nuna alaman komai ba da za'a gane).
Bayan 2dys A.G ya dawo, kuma ya dawo tare da wata umman mummy ce, wanda zata zauna da heedayah,matsayin kaka take a wurin du A.G, mace cr mai kirki, ga tsabta, ga ta da kazarkazar kaman mummy da heedayah, tunda tazo wancan matar da Aunty B ta kawo ta koma, Aunty j kusan kullun sai tazo duba heedayah, kuma takanzo da abinci, Aunty B dai cikinta da laulayi, so bata zuwa, bata ma sake zuwa ba sai ranan suna, shima sai yammah sosai tazo.
Ranan suna yaro yaci sunan *MUHAMMAD AUWAL* sunan babban yayan su M.G inda naji M.G yace yayan shi ne kuma Baban shine, a wannan ranan naga kara da zumunci na ƴan'uwanta ka, domin matar Yayah Auwalu ne kawai da basu ƙasan ba suzo ba, amma naga matar yayah sanie, rabiu, hassan da hussain, duk da dama Huda kam tamuce, babu wacce bata zoba daga inda ta ke, kuma ranan naga Yayah Auwal, domin ya ƙira video call don yaga takwaran shi, bawai ba'a taɓa mishi takwara bane, a'a yaji daɗin na wurin M.G sosai akace, domin shima gani yake yiwa M.G ɗane a wurin shi, babyn yana hannu na lokacin da M.G ya shigo da wayan, bayan sun gaisa da heedayah ne, M.G ya miƙo mun wayan yana cewa "Yayah ga matar A.G da takwaranka", kai so masha Allah, inaga duk ƴaƴan Goggo masu kyaune da farin fata, don ko yana xaune turai ne, duk da girma ya fara kama shi amma naga duk yafi su fari da kyaun, fuskan shi ɗauke da murmushi yana kallon fuskan babyn yace, "barka da ƙanwata, yyh Aminu yayah takwara na? Fatan yana cikin lafiya ko"? Sai da nasake ɗaga ido na dube shi, wai nan hausa yake yi, amma kaman turancin ne a bakin shi, ashe bayan M.G dana sani da mugun iya turanci ashe akwai wanda ya fishi a gidan su? Ko da yake duka ƴaƴan Goggo masu ilimine, don Yayah Sani yanzu professor ne, shima kuma yayah auwal ɗin hakane, twins kuma dukan su P.H.D suke da, Drs ne su duka, Yayah Rabiu ne kawai iya kaciɓ dhi degree ya kama ball, duk da nace kuma wai Yayah auwal ɗinne kawai ya fishi ƙwaƙwalwa, kawai dai nashi abincin a ƙwallo ne ba a boko ba, murmushi nayi na amsa mishi da komai lafiya.
Suna yayi kyau mun chakare abunmu, amma tun ranan sunan kuma zaman ƙafiya tsakani na da abinci ya ƙare, don tun da naji warin alale hankali na ya tashi, sai duk lokacin da zanci abinci sai naji warin a hanci ne, sai naji bazan iya ba, dole rayuwata ta koma daga tea, sai idan ka matsa nace zan sha garin kwaki.
Watarana naje gaida su Aunty B, don jikinta daya ɗan matsa, duk sai nakasa cin komai, da yayah muhammad ya matsa sai nace ni garin kwaki kawai nake so, jikin shi na rawa ya fita nemo mun, daya dawo kuma ya taho mun da gyaɗa da ƙarago wai ya tuna yadda suke sha da a school, hakan kuma ya mun daɗi, sai naji na daka ƙaragon na kwaɗa kawai, aiko na kwaɗa na zuba albasa da attarugu, daga ni har duka Aunties ɗina muka dinga ci, muna cine naji Aunty B tace, "Besty cikin ki how many months kenan"? Tsayawa nayi da cin nace, "ciki kuma Aunty? Ni ae Aunty banida ciki, tunda nayi miscarrige ae har yau ban sake period ba". Dariya suka kwashe ita da Aunty j, "tazarce kenan kikayi"? Aunty j tace, nidai tsayawa nayi ina binsu da ido, a zuciyata kuma ina mamakin wai ina da ciki, tou wani irin cikine kuma babu ciwo babu komai? Shigowan yayah muhammad yaga suna ta mun dariya ni kuma ina zare ido ya tambaye su da lafiya kuwa?
Nan Aunty B ta mishi bayani, shi dai murmushi yayo kawai yace , "ae sai suje asibiti ayi test ko?inaga hakan zaifi kwanciyar hankali", nidai shiri nayi ina tunanin in da gaske cikine wani irin farin ciki Jarumina zaiyi? Sai naji gaba ɗaya asibitin kawai nake so muje mu tabbatar, basu ankara da ni ba na ɗauki waya na tura mishi message.
Aikuwa ko ƙwaƙƙwaran awa uku bai cika ba ya baro abunda yakeyi ya taho gidan, mudai kawai ganin shi mukayi yazo, kuma yace na taso muje asibitin, dariya sosai Aunty B ta mana ta kuma mana fatan alkhairi, garin kwaki na ta ɗauko mun, karɓa nayi muka wuce.
Scarning Dr ya mun, inda ya juyo yana duban A.G.
"Congratulation barr, madan na ɗauke da ciki na kusan 8weeks", fuskan Dr cike da murmushi, ɗaga hannu sama A.G yayi yana hamdalah wa ubangiji, nidai na sunkuyar da kaina ƙasa ina wasa da yatsu na,a hankali ya saka nashi hannun ya riƙo nawa, ido na ɗago na zuba mishi, idan banyi ƙaryah ba hawaye ne cike a idon shi, baiyi magana ba amma alama ya nuna mun da ido, na tashi muje, miƙewa nayi hannu na cikin na shi, sallama sukayi da Dr bayan ya bu wani paper da zamu sayi magani.
Har muka je pharmacy muka saya muka kama hanyar gidan mu baiyi magana ba, daga baya kuma dainaga ya juyo ya dube ni, "ko akwai wani abu da kike so kici"? Lumshe ido nayi na buɗe ina duban shi, "ina son cin kwakwa da soyayyan kifi", mirmushi yayi ya juya hanyar winti market, aiko leda guda aka ciko da kwakwa, kifi ma lodi guda aka sayo, kusan kala huɗu, sit ɗin baya ya ajiye ya dawo Sit ɗinshi ya zauna, "sai kuma me beauty na? Me unborn ke so? Me cwit heart ɗina take so?" yana faɗa hannun shi akan lafaffen cikina yana shafawa, turo baki nayi gaba nace, "boy ɗina dai, wacce irin takeso kuma, ni baby boy ne aciki? Buɗe idon shi yayi duka a kaina yana murmushi, "beauty insha Allahu girl ce, kin san yadda nake son yara mata kuwa? Duka girls zaki bani insha Allahu, ke ko ɗaya sai nayi ƙoƙarin baki tunda kina so", tada motan yayi muka kama hanyam gida, still hannun shi ɗaya yana riƙe da ni.
A parlon shi mukayi masauƙi, shi ya ɗauko ledojin, direct kitchen yaje ya jubge mun so, bai fito ba sai da ya ɓare mun kwakwa guda, ruwan ya juye mun a wani ƙaramin cup, kifin kuma ko wanne a ciki sai daya saka mun akan filet, inda nake yazo ya ajiye mun, idona akan shi ina jin wani azababben son shi yana ratsani, murmushi ya mun ya ajiye komai akan stool ya matsu mun da shi a gabana, kifin kuwa na dirawa, ko wanne sai dana ɗauki ɗaya aciki na taɓa, a ƙarshe na tsaya akan wani buɗaɗɗe kaman banƙararren kaza, shi sai danaci har biyu, bayan wanda naci a farko, tissue ya miƙo mun ma goge hannu na da baki na, sannan na ɗauki ruwan kwakwan nasha, hannu na ɗauka na ɗauko kwakwan, ina sakawa bakina na wani runtse ido tsabar daɗin da ya ratsa ƙwaƙwalwa na, murmushi yayi yana bina da kallo, "Eeshaa na baza a ɗan samma A.Gn Eesha bane"?
Kallon shi nake ina murmushi, "Jarumina ae kaine baka nemi zaman lafiya ba", na faɗa ina murguɗa bakina, murmushin shi ya faɗaɗa, "beauty me nayi kuma"?
"Kace baby girl ne, ni kuma boy nakeso don mu saka sunan M.G" na faɗa ina kallon shi ido cikin ido.
Dariya yayi ya tashi daga tsugunen da yake a gabana, gefen inda nake zaune ya zauna " beauty ina fatan Allah ya raya abinda ke cikin ki, idan tazo duniya sunanta *KHADIJAH* sunan ummie zan saka saboda ta bani farin cikin rayuwata, ita ta haifa mun beauty nah, ita ta bani kyauta mai girma da daraja a rayuwa na, ina so na faranta mata yadda ta faranta mun, ina son na girmamata sama da wanda ta haifi mai mun, Na biyu kuma zan daka Heedayah, ina son ta sosai, ina ƙaunar ta, gashi kuma tana riƙe mun da farin cikin rayuwata, M.G, tunda aka haifi heedayah nake jinta kaman zuciyata, amma in kin cire M.G da mummy kowa gani yake Hudah ce tawa, ita nutsuwanta yake samu zama inuwa ɗaya Heedayah kuma hattah sunanta ni ma zaɓa mata shi,ni nayi kusan rabin rainonta, shi yasa naji daɗin aurenta da M.G. Na ukun sai ki haifi naki boy ɗin, na huɗu kuma girl nake so, ita kuma RASHIDAT, (mummy) ce, auta ta da zan mata kauna na daban, ƙaunar da babu wani mahaifi daya taɓa yiwa ɗiyar shi irin shi, zan so ta sama da irin son da mummy tayi mun, xan so yarah na sosai beauty", ya faɗa yana kwantar da kanshi a kafaɗa na, ajiyan xuciya na sauƙe, "kaɗa fah ka so su sama dani", na faɗa ina kai mishi kwakwan bakin shi, murmushi yayi ya gutsuri kwakwan sannan yace, "hmmm beauty kenan, ni ae babu wani abu da zai zo yafi mun ke a rayuwan nan, bana fatan ganin hakan ma, amma dai kada fah ki fara kishi da su axo ana ƙin basu nono su sha, don zamu samu matsalah akansu fah ƴan mata na", dakata wa nayi da cin kwakwan na ɗaga anshi na ƙura mishi ido, "bangane magananka ba jarumi nah? Kana nufin akan su zanga ɓacin ranka? Kenan ma ka zaɓe su sama dani"? Na faɗa bakina a ture a gaba.
Rungumeni yayi yana dariya, sanann ya chanja topic ɗin, "Beauty next week zanje lagos, kuma inaga zamuyi 1week nida barrister, zamuje ko"? Tashi nayi nayi hanyan ɗakina don nayi wanka, kallon shi nayi ban ce uffan ba, shidai dariya kawai yake mun,don yasan na shaƙa ne game da maganan zaiso yaran shi da yawa, kaman ma sama da ni.
Cikina yana six month lokacin Aunty j ta haihu, wannan karon ma ɗa namiji, ta haifah, gashi kowani yaro kama yake da gidan mu, yaran nan babu abunda suka baro na yayah Ahmad, a lokacin kuma aka saka Date ɗin auren mutane na, Yayah umar da ummitah, yayah ishaq da hafsyn shi, gashi garin zaman su ya banbanta, shi yayah umar kaduna yake, yayah ishaq kuma Maiduguri, (october 2023) bikinsu, ni kuma zai kama na haihu da kusan 6month kenan,an saka date ɗin da nisa saboda zasu tafi wani training ne na six month, shi yasa aka kai shi wannan lokacin.
A cikin wannan watan da zamu shiga ne bikin hadiza, saboda haka nayi shiri sosai na zuwa bauchi, bamu samu zuwa a lokacin da muka so ba, sai ranan friday ɗin bikin muka tafi, don ma flight ɗinmu na safene, tafi da gidanka mukayi, don gaskiya duk yayuna sunyi kara, mun iso wuraren 10:00am, gida naso wucewa amma fir A.G yaƙi amincewa, amma ganin Heedayah ma gidanta zata sauƙa sai abun ya ɗan mun sauƙi, gidan su muka wuce nida shi da M.G da kuma heedayah, inda su Aunty B ma da mazajen su da yaran su gidan mu suka shige, achan mukayi break, bayan munyi na matsawa A.G akan zanbi su Aunty B zuwa garinmu, inda achan zatayi event ɗinta.
Saida mukaje gidanmu ya ɗan gwangwaje ni yadda yaso tukun muka ƙarisa sir kashim, ina shiga kuwa nayi karo da ummie na ta fito daga ɗakinta xatayi kitchen, aiko banji nauyin cikina ba, banji kunyan su yayah da dukkansu suna parlon ba naje na rungumeta, murmushi cike a fuskanta tana kallon na cike da tausayawa irin na uwa idan taga ƴarta ɗauke da ciki, gashi kowa yayi mamakin bajewan dana ɗanyi, babu wanda yayi tunanin zanyi jiki haka, duk da dai ƙarfin cikin a cinyoyina ne, amma kuma shima ya ɗan tasa kaɗan. Muna rungume da juna Su Aunty suna mun dariya, hafsy ka sai mita takeyi wai zan kayar mata da mahaifiya na fallashe ta, nidai ban bar jikin ummie ba ina ta murmushi ido na cike da ƙwallan daɗin ganina tare da ita, a haka A.G ya shigo parlon, ganin shine ma yasa ummien ɗan matsar dani a jikinta, dawowa tayi cikin parlon sosai ta zauna tana amsa gaisuwan shi, hira akan ɗanyi a parlon kaɗan, sannan yayah muhammad yace mutashi mu tafi kafin a fara shirin jumma'a , haka ko akayi, mota ɗaya aka ce zamu yi tafiyan da ita.
hajiya ummah ance tayi sati achan, tafiyan da mamah zamuyi, sai Aunty B, Aunty J, ni sai Hafsy kuma, mamie da ummie ance gobe zasu taho da su yayah ƴan ɗaurin aure, fitowan mu dukkan mu muka wuce side ɗin mamie don a gaisheta, nidai ina ta bayan yayah muhammad, kuda muka shiga muka samu Raliya da mamie zaune a parlor suna cin abinci suna hiran su ƙasa-ƙasa, ban fito fili yadda zata ganni sosai ba, gaisheta mukayi tana wani bin mu da kallo kaman taga kashi a zube a wurin, yayah Ahmad ne ke tambayan Raliya dama tazo ne?
Kafin ta bashi amsa mamie tayi charaf tace, "taxo tun ranan laraba, ina xaku sani kun watsar da ita kaman ita ba ɗaya take da su Ayshaa ba a wurinku, tou ina zaku sani tunda ita ta dawo bare a cikinku, Ta faɗa tana wani banzan kallo wasu Aunty B da suke miƙewa domin barin parlon, shi ma A.G miƙewa yayi yabi bayan su, nidai ina manne sosai ta bayan yayah muhammad, don ni ko cikin bana so ta gani, don ma ummie ne tace na biyu su mu shigo tare amma da banyi niyyan zuwa ba.
Murmushi yayah muhammad yayi sannan yace, "mamie kenan Allah ya rufa asiri, amma ita inaga ko number ɗaya daga cikin mu bata da shi, ba'a taɓa mana haihuwa ta ƙira wani tayi barka ba ballantana taje suna, ina kaduna ina Abujah"?
Sunkuyar da kai ƙasa Raliya tayi alaman ta ɗan ji kunya, don yaushe ma su yayah muhammad suke magana ballantana har du nuna maka abunda kayi ya ɓata musu rai ko baiyi daɗi ba a wurin su?
"Tou ae ganu tayi baku damu da ita bane, waye a cikin ku ya taɓa bin inda take? Don kunga ita Allah bai bata haihuwa ba ko? Don ma yanzunaga alaman sun zama biyu, don ga ita Ayshann ma abokiyar auren ta har ta haihu amma ita shiru, anyi biyu kenan a gidan magadan mamah, Allah dai yasa ba maman suka gado ba".
Miƙewa mukayi dukkan mu, yayah Ahmad ne ya bata amsa da, "insha Allahu suma zasu haifi nasu, fatan da muke musu kenan", ni dai fit nayi na fice a parlon, gaban motan na shige na xauna, inda mamah da Aunty B suka zauna a tsakiya, chan baya kuma Aunty J da hafsy suka zauna, yara kuma dama Aunty j ta ajiye su a gidan su, daga Areefh har Ameer ɗinta, babynta Ammar kuma yana riƙe a hannun Yayah Ahmad, sai da ta shiga tukun ya miƙa mata shi, addu'a sosai suka mana, A.G dai babu ko kunya yana tsaye a ƙofan da nake zaune, sai da driver zai tashi ya ɗan sunkuyo kaɗan yace, "ki kula mun da baby nah plz beauty", murmushi nayi na mishi alaman ummie fah naganin mu, itama ummin kaman tasan magananta nakeyi sai ta juya ciki, lumshe mun ido yayi bayan ya kashe ido mun ido ɗaya, murmushi nayi na ɗagawa su yayah hannu, da fatan sai sun shigo goben idan Allah ya kaimu.
Hadiza taji daɗin zuwan mu sosai, achan muka samu zainab da maryam besty nah, aiko munsha chaftah ranan, suna ta zolayana da cikin A.G, maryam har da cewa, "yanzu yadda A.G yake wani ciccin magani yana basarwa haka ya juye wa ƴar mutane ciki babu kunya"? Dariya da kan mu mukayi, bakina baiyi shiru ba nace, "yadda Dr Abduol babu kunya ya juye miki nashi haka shima Jarumi na ya juye mun nashi", na faɗa ina juya ido ina rausayarwa, dariya duka mukayi Anan kuma aka ƙira fatima itama aka zolayeta, sannan aka ƙira jammy aka sha dariya da ita don video call akayi da su dukkan su, haka kuma sukayita zolayana, Allah sarki ƙarshe sai da nafara kukan tunawa da sisto na habiba, kai rayuwa ina jin mutuwan habiba kaman zai fasa mun zuciya idan na tuna, habiba tana son taji ana labarin rayuwar aure tsakanin mata da miji, ana farawa zakaga ta matso tana munafukin dariya, gashi yau babu ita a duniyan, kukan da nafara ne ya kawo ƙarshen rahan mu, dayake a side ɗin matar yayanmu babban wan su hadiza muka zauna, ɗakuna biyu ne sai muka kama ɗaya, haka duk jikin kowa yayi sanyi,ita dai zainab tashi tayi ta fice dama tun wuri, ita zainab bikinta da Abdoulmaleek sai April, watan haihuwa na kenan, yanzu kuma january muke.
Waliman kuwa yayi kyau amaryah ma tasha kyau sosai Bayan mun dawo ne da daddare mukaje duk muka gaida Bappanun mu nida hafsy da su Aunty B da suka sauƙa a ɗaya side ɗin da Abba ya gina, kusan ɗakuna 6 ne a wannan gidan, ɗakin ummie suka buɗe a ciki suka sauƙa,mamah ma a nata ɗakin ta sauƙa tare da hafsy, hajiya ummah kuma nata ɗakin tare da Aunty Rakiya da Aunty ma'u.
********* Washe gari tun ƙarfe 9:00am bata cika ba su Abba da dukka yayuna da ummie,mamie, raliya suka iso, mota Biyu sukayi suma, yayah Muhammad ke jan su Abba da su mamie da ummie, Abba ke zaune gaba tare da yayah da yake ja, baya kuma umie ne da mamie sai raliya, ɗayan motan kuma Yayah Ahmad ne tare Da A.G a gaba, baya kuma M.G ne da heedayah sai babyn su Affan.
Babban parlon side ɗin Abbah suka sauƙa, kuma nan aka kai abin breakfast, duka ƴan'uwan Abba sunzi sun gaisa, maza da mata da ƴaƴayensu, nidai parlon ummie muka zauna tare da A.G, daga bayane da suka shigo muka fice domin a basu wuri suyi break, parlon mamah duk muka koma, kuma har lokacin bamu haɗu da mamie ba.
Ƙarfr 11:00am aka ɗaura auren hadiza da suraj, kuma aranan zaayi wuni, kuma akaita family house ɗinsu suraj inda yayi ginin shi, washe gari da sassafe za'a wuce da ita kaduna inda gidan ta yake.
Anyi wuni mai daɗi cike da jin daɗin ganin ƴan'uwa Abba da ƴan'uwanshi kaman bazasu rabu ba suke ji, ƙarfe biyar da kusan rabu Abba yace duk su ummie da suka zo tare yau su fito a wuce gida, har waje muka rako su, inda Abba yace ita Raliya ta zauna ta biyo mu gobe, amma fir mamie taƙi, inda take cewa gobe wai da wuri zasu fita da surkuwarta, jin haka ne yasa Abba rabuwa da su, muna tsaye a waje ga mutane dayawa ana jiran fitowan Abba, kawai saiga mamie da raliya biye a bayan Abba suma sun fito, nidai ina tsaƴe gefen headayah rungume da Affan, gefe na kuma xainab ce a tsaye.
Wani irin Salati da mamie ta zabga ne ya bani tsoro, wanda ya jawo hankalin kowa kan ta, "me nake gani tare da ayshaa kaman ciki? Yayah akayi kuma naga ciki"? Kalmar da ta fito da ƙarfi kenan a bakinta, hakan kuma ya jawo hankalin kowa zuwa gareni, nidai duk sai naji tsoro da kunya ya kamani, "ikon Allah kuwa, wanda yake bayarwa a duk lokacin da yaji ya mishi, wanda yake hanawa a duk lokacin da yaji ya mishi, shi ya bata ya kuma tsare mata shi har ya kai haka, ba dabaranta babu ikonta, sai ƙarfin mulki irin na rabbil- izzati" Aunty Rakiya ta faɗa tana karɓan Affan da yake hannuna, ko lura da irin tsoritan da nayi tayi, hala shiyasa ta karɓe yaron ko kuma mamie ta samu daman ganin abunda ke cikin ne ohoo.