Ana barin halal original by anty nice - Chapter 30
Ana barin halal original by anty nice Chapter 30: Ana barin halal original by anty nice Chapter 30. "Tou ae ban taɓa zato ko tunanin ayshaa zata haihu ba,…
4,426 words
"Tou ae ban taɓa zato ko tunanin ayshaa zata haihu ba, na ɗauka ita da raliya sun gado mamah ne, abun ne yaban mamaki don ba haka aka gaya mun ba" mamie ta sake faɗa cike da suɓutar baki, dariya mai sautimamah tayi sannan tace, "abu na Allah kuwa, ae shi baya shawara yake abun shi, gado kuma ae raluya ce kaɗai a gidan nan ta gado ni, nima Allah yasan dalilin daya sa bai bani ba, bawai shirkah ko tsafin mutane bane ya hanani, duk cikin rahamar shi yasa bai bani ba, kuma bana baƙin ciki, tunda yabawa mijina kuma Alhmdllh inaji kaman ni na haifah, bani da damuwa ko baƙin cikin komai, Ayshaa kuma Allah ya bata sai fatan Allah ya inganta shi ya sauƙe ta lafiya, Allah kuma ya kare mata daga sharrin ma sharranta". Tsawa Abba ya daka musu ganin zasu fara baza hali a wurin, ga surakunen shi ga ƴan'uwa da ƴan unguwa, ga kuma ya hango hajiya ummah ta fito, mota ya nuna wa mamie akan ta shige su tafi, aiko hajiya ummah ta iso wurin hafsy a bayanta, daga gani ita ta ƙirata, mitsi - mitsi tayi da ido tana kallin Abba tana maida kallonta kan mamie kuma, "amma dai hauwa anyi mutuniyar banza anan, har yanzu usmanu bai ɗauki shawarana ya kai ki ƙasar india anmiki sabon ɗashen zuciyar ba ko? Tou aniyar ki ta biki, insha Allah khairan a gidan ayshaa babu sharran, sharran ya ƙare akanki da munafukar ƴarki da tayi saura, rashin haihuwa ba Allah yaƙi mutum bane sakarya abokiyar tafiyan shaiɗan, gaskiya kin cuci usmanu da yahaɗa zuriya da ke, tou ta Allah ba taki ba wuce da mummunar fuskar ki aniyarki ta biki ku tafi," sannan ta maida kallonta kan A.G tace, "kai kuma ja matar ka ku tafi, ka kaita chan wurin dattijuwar kakarka kace inji ni a rubuce mata Tabara da yaseen, a ƙara da lahaula saboda sharrin bakun maƙiya, ni nan ina wurin bikin jikata ce, bazan samu zama da ita na saka a rubuce shi tsaff ba, inda hali qur'ani ma izzu sittin a rubucr mata, din sharrin matar usmanu yawa ne da shi". Abba ne ya ƙurawa Aunty Rakiya ido ita kuma ta gane mai yake nufi, kamo hannun hajiya ummah da ta fashe da kuka tana tsinewa sharrin mamie tayi, haƙuri take bata akan su juya suje ciki, sannan tacewa A.G yayi haƙuri insha Allahu babu komai, zasu kula dani gobe da wurin za'a dawo.
Ajiyan zuciya yayi yana bina da kallo, hannu na za<nab ta riƙo muka koma gida , jama'a dai sai mamakin halin mamie kawai akeyi, haka suka tafi mu kuma muka dawo gida.
Aiko suna isa bauchi a tsorace heedayah ta labartawa mummy, jiki na rawa mummy ta sanar da Daddah da Daddy, shi kanshi Daddyn ya umurci A.G ya koma ya ɗaukoni, babu inda xan kwana sai nan, haka ko akayi muna idar da sallan ishaa sai ga call ɗinshi, waje na futa cike da mamaki, ai kuwa ganin shi nayi a mota zaune shida M.G, Buɗe mun sit ɗin baya yayi na shiga, sannan ya ɗaga waya ya ƙira hafsy,nidai bai wani sake fuska ba shiyasa ban iya mishi magana ba, sakata yayi ta tattaru mishi duka kayana yace ta kawo mota muna jiranta.
Dariya kawai Aunty Rakiya tayi lokacin da hafsy ta gaya mata xamu tafi, ita kuma Hajiya ummah da mamah daɗi abun ya musu, sai addu'a isa lafiya kawai suke mana.
Banso ba don banyi sallama da kowa ba, hattah hadiza bamu haɗu ba, akan zamu zo gidan ta idan mun gama, don banje kai amaryah ba akan daga baya sai muje.
Haka yaja motan shiru baya kula owa, A.G dai nada dana sani ya koma mun, sai M.G ne kawai yake ɗan hira dani jifa-jifah, shima ganin nakasa nutsuwa ya saka ya rabu dani.
Fadaman mada Mukaje Gidan su A.G, har waje mummy da heedayah suka fito taryan mu, ina ankare da mummy yadda hankalinta yake tashe, fitowa tayi ta riƙo hannun na muka shige parlor, ita kuma heedayah ta karɓi kayana da yake hannun A.G.
Ɗakinta taja ni muka shige, A.G kuma suka zauna a parlor shida M.G, heedayah ta wuce kitchen kawo musu drinks.
Har bakin gado Mummy ta karasa riƙe da hannu na, zama mukayi still hannun ta rike da nawa, cike da damuwa tace, "Doug babu wani matsalah da kike ji ko? Idan akwai wani abu ki faɗa mun muje asibiti, sannan kuma a haƙura da haɗuwa da wannan ƙatuwar azzalumar, duk da dai matar mahaifinki ne amma a kiyayeta don Allah doug, don duk abunda tayi sanadi ya samu cikin nan sai nayi shari'a da ita, kuma zata gane shayi ruwa ne", ajiyan zuciya na sauƙe mai ɗan karfi kaɗan, "akwai wani abu da kike son ci ne"? ta sake tambayana a cike da tashin hankali, idona na ɗaga na kalli A.G daya shigo ya ƙura mun ido, mirmushi nayi don hankalin su dukka ya kwanta, "mummy babu komai da nakeji, kawai zanyi wanka ne sai nasha tea".
Ina gama rufe bakina naga ya juya ya fice a ɗakin, dawo da kallo na nayi kan mummy ina mai cike da kunyarta nace, "Allah da gaske mummy babu komai, kuma bana in komai", murmushi itama tayi kaɗan wanda bai ƙarasa har ciki ba, daga gani iya kan leɓe ne, tashi tayi tsaye tana tambayana, "zaki iya wankan ko kuma A.G yazo ya taimaka miki? Bana son ki ɓoye mun idan kina jin wani abu, fatana ma Allah yasa babu komai ɗin, don gsky zan ciwa matar nan mutunci yadda bata zato, Allah ya sauƙe lafiya", ta faɗa tana karasawa jikin mirrow.
Tashi nayi ina ƙoƙarin shiga toilet sai ga A.G nawa ya shigo hannun shi ɗauke da cup ɗin tea, ɗaya hannun kuma ɗauke da snacks a filet, ido na ƙura mishi, ganin har lokacin fuskan shi a ɗaure, kuma na rasa meye dalilin fushin, ajiye mun cup ɗin yayi da filet ɗin, sannan ya bani umurnin na zauna nasha tukun nayi wankan.
Mummy ficewa tayi a ɗakin ta barmu, ganin babu fuska yasa ban wani ja musu ba na zauna na ɗauki cup ɗin, idan na ɗago zan ajiye tea ɗin sai naga irin kallon da yake mun, dole yake sakani ci gaba da sha, ban ankara ba na shanye tea ɗin dukka, nine da sha amma shine kuma da ajiyan zuciya, runtse ido nayi ina jin yadda ɗumin tea ɗin yake zaga dukkan illahirin jikina, "zaki iya shiga toilet ɗin ne ko na taimaka miki"? Sautin muryan shi naji dab dani, buɗe ido nayi na zuba mishi dukka kaifin idonuna akan shi, sannan na maida kaina kalan tausayi, don fushin na shi ya dame ni, harara na yayi na wasa yace, "baki son kiyaye abu ko? Bakinki bazai buɗe kice zaki biyo mu ba ko? Idan wani abu ya sameki fah"? Ya faɗa kaman zaiyi kuka, zuwa nayi gaban shi kawai na rungumeshi, "Jarumina afuwan".
Shiru yayi bai ce uffan ba, daga baya kuma ya saka hannun shi ya rungumeni sosai, mun daɗe a haka babu wanda yayi magana, sai numfashi kawai da kowan mu yake sauƙewa, "Eeshaa na don Allah ki kula mun da kanki, ni matar nan tsoro take bani, babu imani a zuciyarta," ƙara rungumeshi nayi amma sai nai ya ɗan sassauta, ɗago fuskana yayi ya ƙura mun ido, "beauty ina jin babyn mu na motsi, ko mun matse ta ne"? Murmushi nayi na cika shi nayi hanyar toilet, nasan zai iya biyoni don ba kunyar mummy yake ba, shiyasa ina shiga nasaka key a ƙofan, har bakin ƙofan yazo yana mun faɗa, "beauty ki buɗe ƙofan mana, baki san hatsari bane ki shiga ki rufe ƙofa"? Shiru na mishi ban kula shi ba, wanka na nayi na fito, hararana yayi dana fito sannan ya juya ya fice.
Murmushi nayi kawai na wuce nasaka kaya, ina gamawa mummy ta shigo ɗakin tare da heedayah, sallama heedayah ta mun, nidai daga zaune na mata sallama ban wani tashi rakiya ba, don yanzu muna haɗuwa da A.G zaice bana kiyayewa, daga nan ma kwanciyata nayi ina ɗan chatt dasu jammy dasu Fatima, a haka har bacci ya fara ƙoƙarin ɗauka na, tashi nayi nayi addu'a, kashe wutan nayi na kwanta a buna.
Da Asuba alerm ya tashe ni, nayi mamakin irin baccin da nayi, don tunda na kwanta ban farka ba sai da na tashi sallan asuba, gani nayi an lulluɓeni an saka mun hula akaina, nasan kuma ko A.G ne ko Mummy.
Addu'a sosai Alhaji Inuwa ya bani a rubuce a wani takadda, duk addu'a ne na neman tsari, haka muka juya Abujah lafiya bayan ƴan biki sun dawo.
Haihuwar Aunty B lokacin cikina ya shiga 8month, itama boy ɗin ta haifah, mudai wato gidan mu babu jika ƴa mace sai masu ƙaton kai, haka jiki na rawa don ɗauki mukaje gida ganin baby, don haihuwar yazo mata da sauƙi babu wani jinkiri, saboda haka a gida mukaje muka same su, shima wannan yaron kaman areef damu yake kama, nayita wa Aunty Dariyan bai ɗauko ta ba, don tasha alwashin ita zai biyu, shima wannan yaron farine kyakkyawa da shi, amma yafi ɗauko yayah umar da hafsy, A gidan na wuni har bayan ishaa A.G nah yazo muka tafi,.
Ranan suna yaro yaci sunan Yayah Ahmad, aka mishi laƙabi da *DEEDAT* yasha gata kam kaman babu gobe, nidai wani ƙaunar yaron nakeji a zuciyata kaman me, duk da son da zanyi wa kowani yaro bazai kai irin son da nayiwa Areef ba, amma kowanne ina son shi na Areef ne daban, Deedat kuma ko don sunan yayah Ahmad ne, sai nakejin daban a zuciyata, muna tare da Fatima da su hafsy, a gida na Fatima da hafsy suka sauƙa, saboda haka da zamu tafi tare A.G yazo ɗaukan mu.
********** 04/04/2023 na haihu, ansha gumurzu amma an sauƙa lafiya, labour room A.G na kan gaba kaman shi zai fitar da babyn, Yayah Ahmad, Yayah Muhammad, M.G da matansu duk suna tare da mu a asibitin, mai gayyah mai komai kuma yana ɗakin na haihu, yana rungume da kaina yana mun addu'a, dukka hannayena suna riƙe da shi, kukan babyn ne yasaka ya runtse ido yana furta, "ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! sai da yayi baki uku tukun ya buɗe idon shi ya manna mun kiss a fuskana da ya jiƙe da zufa, ɗago da babyn akayi aka nuna mun suna tambayana me na haifah? Murmushi nayi na runtse ido na ina hamdalah a zuciyata, naji daɗi don ko babu komai nasan na farantawa A.G dayaci burin haihuwar ƴa mace, tashi yayi da sauri ya amshi babyn yana ta furta hamdalah, Gyarani sosai akayi sannan aka gyara babyn aka miƙa mishi, suka fice a ɗakin, addu'a sosai ya yiwa babyn, sannan ya dawo da kallon shi kaina, saboda jin ƙiran sunan shi da nayi a hankali " Jarumina, ina neman alfarma don Allah", na faɗa murya chan kasa a gajjiye, "beauty me kike son na miki"? Murmushi nayi na mishi alaman ya matsu, dab dani kuwa ya matso, ƙurawa babyn mukayi ni da shi muna kallonta ganin yadda taketa motsa baki kaman wanda za'a bata abinci ta karɓa, murmushi mukayi dukkan mu Idon mu akanta, wani irin ƙaunarta kaman zai fasa zuciyar mu, "jarumina sunan Mummy nake so a saka wa babyn mu mai kama da Abbinta, next year insha Allahu zamu kawo ummie, saboda jarumina Gwarzo ne", na faɗa ina kashe mishi ido, murmushi yayi ya sumbace ni, kafin yace wani abu akayi nocking ƙofan ɗakin, su yayah ne da matan su sai M.G da heedayah suka shigo, kowa ɗaukan babyn yayi ana ta santin kyaunta da girmanta, babu abunda ta bari na kama da A.G, har irin manyan idon shi ta ɗauko, lura yayi da yadda jikin heedayah yake rawan son ɗaukan babyn, sai ya karɓi yaron hannunta Affan ya bata hanya, kaman bata taɓa ganin jaririya ba sai ranan, bakinta yaƙi rufuwa don farin ciki, rungume babyn tayi tsam a jikinta tana ta smilling, da ƙyar dai ta miƙawa su Aunty J, ɗauka akai tayi 1 by 1, kowa kuma sai yayi addu'a idan ya ɗauka, M.G ne ɗaukan ƙarshe, babu tunanin komai kuwa ko shawara yayi wa jaririyar Huɗuba da sunan Mummy, Wato *RASHIDA* kaman wanda yasan abunda yake zuciyar mu kenan, ɗago da kai yayi ya ƙurawa A.G ido, chan kuma yayi murmushi yace, "sunan ƴar mu RASHIDAT wato mummy, sai anema mata nickname don sakaye sunan", lumshe ido A.G yayi ya buɗe su akaina, murmushi nayi na maida kallona kan M.G da yake miƙawa heedayah ƴar, su yayah dukkansu suka fice a ɗakin sukayi waje, sunaye kala -kala heedayah take ta ambatawa don zaɓawa ƴar ta, nidai murmushi nakeyi kawai ina kallonsu.
Babu daɗewa mummy suka ƙira waya ita dasu Hudah da su Goggo, hattah Daddah ma sai data ƙira, ummie da su hafsy duk sun ƙira, hafsy tana ta roƙon Aunty J da heedayah su mata video baby su turo mata, sai ja mata rai sukeyi.
Ana sallaman mu muka wuce gida, wanka sosai aka mun akayi wa babyn ma, inda aka saka mata pink kaya tayi kyau sosai, hattah farinta ya wani fito kamar ƴar turawa, nima kaina sha'awan ƴar naji ya cikani.
Har dare tukun heedayah ta tafi gidan ta, don su Aunty B ana magrib suka tafi, amma matar da take wurinta ta zauna mun, don gobe mai zuwa mun biƙi zata taho daga bauchi ini yayah muhammad.
Anyi haihuwar yau washegari sai ga Abba, naji daɗin ganin shi, don shima yaji daɗin ganina lpy babyn ma lpy, a wurin yayi ta tsokanan su ummie daya ƙira su awaya, yana ce musu shi yanzu ya tare a wurin sabuwar amaryan shi, dariya sosai mukayi, bayan ya tafi ne A.G ya shigo har ɗakin ya zauna bakin gadon, ɗaukan babyn yayi ya ƙura mata ido, "beauty ashe fah na fiki kyau", kallon shi nayi baki buɗe, "ta ina kafini kyau jarumina"? na tambaye shi cike da mamaki, dariya yayi yana kallon babyn yace, "dubi ƴata yadda tayi kyau saboda ta ɗauko kyauna, kinga fa ta fiki kyau sosai yarinyar nan", ya faɗa yana manna mata kiss a goshi.
Ya mutsa fuska nayi nace, "kyauna ta ɗauko, kasan sbd ta haɗa jini dani ne yasa kyaun nata bayyana sosai, da watace ta haifeta kyaun baxai kai haka ba", na faɗa ina jan zip ɗin rigana da yake zuge. Murmushi yayi yace, "wani suna zamu ƙira mummy da shi"? Kallon shi nayi da ƴar a hannun shi nace, *NASREEN* murmushi yayi ya sumbaci babyn yace, "Allah ya raya mun mumsy nah, Allah ya mata albarka flower gidan aljannah, Allah ya haskaka rayuwarta", da Ameen na amsa mishi, muryan shigowan heedayah da mukaji ne ya saka shi ajiyeta ya fice.
Ƴan bauchi sunzo sosai, daga gefe na da gefe A.G duk an zo, ranan suna kuwa babyn tacu sunan *RASHIDAT AMINU GARBA, (NASREEN)*
Munsha gata sosai nida baby na, daga mahaifinta har ƴan'uwana da kakanun ta sun mata gata, anyi suna da 2dys ummie da mummy suka zo ganin Nasreen, ranan naga ƙauna na zahiri a wurin mummy, don gaba ɗaya ƙaunar A.G da takeyi duk ya koma kan Nasreen.
Nasreen watan ta uku wani tsautsayi ya hau kaina, don zazzaɓi sosai nayi, ga wani ulcer daya sakoni gaba, muna zuwa asibiti kawai sai ga ciki, nayi kuka kaman zuciyata zatayi bindiga, na birkicewa A.G akan sai na zubar da cikin, munyi rikici sosai da shi sosai a lokacin, amma daga baya yafi ƙarfina na haƙura, domin fita hidimana yayi gaba ɗaya, baya kulani baya cin abinci na, idan na gaishe shi baxai amsa ba, sai dai kawai ya shigo ya ɗauki Nasreen yayi mata wasa, idan ya dawo ma ya ɗauke ta ya wuce ɗakin shi da ita, baya fito da ita har sai idan tayi kuka, wani lokacin har suyi bacci tare.
Abun ya taɓa zuciyata sosai, ballantana wani rana da yayi tafiya bai sanar mun ba, ya shigo da safe ina toilet, ina jin shi yayi ta mata wasa, fitowa na kuma ya tafi, tashin fitan motan shi kawai naji, sai da yammah da heedayah ta shigo ne naji wai yaje jos kuma asthman shi ya tashi, Daddy ya tura driver ya ɗauke shi, mummy duk hankalinta ya tashi, sbd ko awa guda baiyi da shiga jos ɗin ba ya tashi, cikinane naji yayi wani sauti kaman ana buga ganka, sai dai naƙi nuna mata ban san da tafiyan ba, sai dai na nuna ban san ciwon ba, har ima vewa ko shiyasana ƙira bai ɗauka ba, nan dai tace tou kada na faɗa ita ta gaya mun, domin yayah zaici ubanta, gaskiya na shiga tashin hankali, kuma alokacin nayi wa kaina faɗa,bazan zubar da cikin ba, zan kuma neme sulhu.
Da dare na ƙira wayan shi lokacin yana tare da mummy, bai ɗauka ba mummyn ce ta ɗauka tace mun, "doug yayah kuke"? Amsa mata nayi da muna lafiya, bayan mun gaisa take cemun gashinan bacci yakeyi, amma gobe insha Allahu zai biyo jirgi ya dawo Abujah,idan ya tashi zai ƙira, godiya na mata daga baya take tambayana mai sunanta.
Wurin 9:00am M.G ya ɗauko shi daga airpot, gida suka taho tare, sun dawo ina kitchen, jin sautin muryan M.G ne ya fito dani ina kallon A.G daya wuce bedroom ɗin shi, bayan mun gaisa da M.G ne ya mun sallama ya wuce ya fita, barin abinda nakeyi nayi na wuce side ɗinshi Nasreen goye a bayana tana ta bin ko ina da kallo, ga ajiyar zuciyar da ta ke tayi, domin yau rikici ta tashi da shi tun asuba, taƙi kwanciya ita kaɗai sai dana goyata tukun tayi shiru.
Ina shiga naji shi a toilet ɗinshi, zama nayi bakin gadon ina kunce nasreen da take shirin cika 4month, don kwanaki ne ya saura ta cika, ɗago ido nayi na ƙura mishi ganin ya fito, kallo ɗaya ya mun ya ma yar da kallon shi kan nasreen, wuce mu yayi ya zauna a bakin gadon shi, ganin irin shareni da yayi ya saka na kwantar da nasreen akan gadon.
Tashi nayi naje har gaban shi na tsuguna a gaban shi ina kallon fuskar shi daya matsar da shi ya bar kallona, hannu na nasaka na riƙo nashi hannun duka biyu, ina ganin alaman zai ƙwace hannun shi nayi sauri na rungume shi na fashe da kuka, shiru yayi yabar ƙoƙarin tureni a jikin shin, kuka sosai nake mishi ina ƙara rungumeshi ajikina, kaman nasreen ta san fushi Abbinta yakeyi dani sai ita ma ta fashe da kuka, da sauri ya ɗagoni ya matsa ya ɗauko ta ya rungume yana rarrashi, ganin ya miƙe da ita tsaye yana jijjigata nima na miƙe naje na rungumesu shi da ita ina mishi nawa kukan itama tanayi, "Jarumina na kawo ƙaran kaina wurinka, don Allah ka mun hukunci da bulala bada kanka ba, ina buƙatan ka sosai nida ummie nah dake manne a cikina, baby nah ina kewan ka sosai don Allah ka yafe mun, ko kuma ka hukunta ni da dorina amma bada ƙaurace mun ba Gwarzo na, na gajji bazan iya ba", na faɗa ina ƙara sautin kuka na, ita ma nasreen sai ƙara nata kukan takeyi, ganin duk mun rikita shi sai ya kamo hannu na muka zauna a bakin gadon, ɗaura mun ita yayi akan cinya na yace, "ki rarrasheta sai naji da ke tukun", kallon fuskan shi nayi cike da tausayawa, ganin har lokacin yana fusgan numfashin ne da ƙyar, nono na saka matata ɗan fara sha kaɗan yana shafah mata kanta a hankali, tayi shiru tana sha tana kallon fuskana, idona mayar kan shi, shima kallona yakeyi cike da alaman jin jiki.
Bacci ta koma bayan tasha nonon, ganin ta sake nonon ya sa ya karɓeta ya ɗaura ta a kafaɗan shi, chan bayan tayi gyatsa ya maida ta kan gadon ya kwantar, sannan ya miƙo mun hannun shi, da sauri na ƙarasa jikin shi ya rungume ni. "Beauty bana son rikici kinji, idan kin zubar mun da ciki ae baki sonane kuma baki godewa Allah daya baki ba ko?" Jijjiga kai nayi bance komai ba sai kukan daya zo mun na ba shiri, murmushi mai sauti yayi, "kayi fushi dani jarumina, gaba ɗaya bana jin farin ciki, bazan ƙara ba, ko yanzu ma ka ƙara wani cikin akan wannan ina so".
Wannan karon sautin dariyan shi ne ya fito, "Beautyn A.G wannan ma dana baki ajiya kinyi mun tawaye inaga na ƙara wani akai kuma fah? ae sai ki gudu ki barni, ki saka nayi ƙaramin hauka", ya faɗa yana sunsuna wuyana yana dariyan kukan da na sake baki ina yi.
Ganin kukan yaƙi ƙare ya saka shi rarrashi na dole, ni ma na bashi haƙuri sosai na nemi gafaran rikicin dana mishi, "beauty tun ranan na yafe miki, ban taɓa kwana dake a zuciyata batare dana yafe miki ba, nidai fatah na da buri na ki riƙe mun ƴaƴana da amana, ki kula dasu da tarbiyan su, ki sani bayan Mummuy duk duniya babu abunds nake so irinki da ƴaƴana," ya juyar da kanshi ya dubi nasreen da take bacci, sannan ya dawo da kanshi kaina, "Eeshan A.G" ya faɗa idon shi na kaina, "Beautyn A.G" ya sake faɗa yana lumshe ido yana kallo na, "Babyn nah ki kula mun da Nasreen duk duniya bani da sama da ita, ki kula mun da abunda yake cikin ki ina mata wani so na musamman, kaman ina mata son da duk wani mahaifi ba zai taɓa yiwa ƴar shi haka ba," kallon shi yadda yake shafa cikin, "idan kuma namijine fah"? Naji bakina ya tambaye shi, murmushi yayi ya sumbuce ni. "*NANAH KHADIJAH CE* insha Allahu, amma idan Allah yayi ikon shi yazama namiji ne tou masoyinane ". "Daddy" na tambaye shi, murmushi ya kuma yi yace, "Daddy mahaifinane, M.G masoyina ne, ina son shi, ke kaɗai ne a duniya kika ture wannan gwamnatin shi a zuciyana, har nafi jin daɗin zama da ke akan shi", ya faɗa yana wani turo bakin shi gaba irin na sakalcin nan da yakeyi idan yana tare da Mummy, buge bakin nayi da wasa nace, "Babyn mummy kawai", dariya yayi ya rungumeni a jikin shi gam, yana kuma jan numfashi babu daɗi.
"A.G na ko za'aje asibiti ne?" na tambaye shi, ƙara rungumeni yayi yace, "kawai ki gaisa da GITANDRA muna gaisawa zan ware," murmushi nayi nace bari na kawo maka tea mai ɗan zafi kasha tukun, rungumeni ya sakeyi yana ƙara maida kanshi wuyana. Wani abu daya bani mamaki a wannan ranan guda biyu ne, shine irin baccin da Nasreen tayi har zuwa azahar bata tashi ba, da kuma A.G daya kasa barina har zuwa azahar abu ɗaya yakeyi,A.G baida yawan takuri, idan yaga bakida buƙata yana ɗaga ƙafa, amma yau na gajji har sai da nayi kuka lokacin da ya dawo mun ana uku wurin azahar, ina fara kuka shima yafara mun kuka, "Eesha kada ki guje ni, Eeshaa ina sonki! Eesha kina mun daɗi! Eesha Allah ya kare mun ke da ƴaƴana", jin surutan shi yasa na haƙura da ƙyar, ana fara ƙiran azahar na zame jikina ana shi, toilet na shige na sakarwa kaina ruwan zafi a chan, lokacin kuma Nasreen sai ta tashi, wurinta ya koma yana rarrashi. Dana fito a toilet kitchen na wuce na bar shi tare da Nasreen, bansan yyh yayi da ita ba tayi shiru, don nidai abinci na ɗaura, achan kitchen ɗin ya tarar dani yana rungume da nasreen da har lokacin ƙananun rikici takeyi, "Eesha sai ina ji kaman yarinyar nan bata da lafiya ne, ga rikicin ta yaƙi ƙarewa ga kuma yanzu naji jikin da ɗan ɗumi, sai mura kuma". Juyowa nayi na dube shi yadda naji yana ɗan jan numfashin shi yasa na ajiye abunda nakeyi na ƙarasa dab da shi, "A.G da ruwan sanyi kayi wankan ne? Naji kaman numfashin yana maka wuyan ja"? Hannu na miƙa na karɓi nasreen, amma sai ta maida kanta kafaɗan shi ta kwanta, wuyanta na taɓa naji da ɗumi, maida kallona nayi kanshi yadda yayi mun kyau sosai cikin white three quater da white armless da ya saka, sai ƙamshi mai ɗan sanyin daɗi yake yi, "A.G na kaida doug ka gaba ɗaya baku jin daɗi, ko na ƙira M.G ne kuje asibiti? Bana jin daɗin ganin haka", na faɗa ina ƙoƙarin ɗaukan wayana, amma sai naji ya saka hannun shi ya karɓe wayan, gefe ya aiye ya matso ya haɗani da nasreen ɗin duk ya rungume mu. "Eesha ki bar maganan asibitin nan, yanzu sai hankalin mummy ya tashi, babu wani abu ae na shaƙi inhela yanzu kafin na fito, kawai kiji damu nida ƴata", ya faɗa yana ƙara manna ni sosai a jikin shi, "tou bari na mana ɗan abinda zamu ci sharp-sharp", girgiza kai yayi alaman a'a na bari. "Baby tou me zamu ci"? Lumshe ido yayi yana ƙara mannuwa da jikina yace, "ki ƙira heedayah kice tayi abinci dake, nidai kizo ki kula damu, bamu da lafiya", ajiyan zuciya na sauƙe mai ɗan ƙarfi, "kai bazak ci abincin bane"? Ɗago kai yayi ya kalleni, "kice ta mun peppesoup kawai ya isa", riƙo hannun shi nayi muka fito daga kitchen ɗin, bayan mun zauna aparlon ne na ƙira Heedayah nace tayi mun peppesoup ta soya mun irish, muna gama wayan na sake miƙa hannu zan karɓi nasreen amma taƙi ta sake lafewa a jikin Abbeen ta, ido na ɗan ya mutsa na tura baki gaba, da ido ya mun alaman tambaya, "ta takurani ta hanani kwanciya a ƙirjin mijina, ni ka ajiyeta na kwanta a jikinka", murmushi yayi ya miƙa mun hannu, jawoni yayi jikin shi, dai-dai kunne na yace, "mumcy baby ce amata uzuri plz, yau ɗaya taji ɗumin jikin Abbeen ta kaɗan". Marairaice fuska nayi ina kallon yadda ta manne sosai a jikinshi, ina kalon su wayan hafsy ya shigo wayana, bayan na ɗauka mun gaisa ne take bani labarin yau Abbah yayiwa mamie kacha -kacha akan rashin kunyar da tazo har ɗaki tayiwa Ummie, kuma ya mata kyakkyawan warning akan cewa da tayi wai ta shiryah taryan baƙin ciki akan rayuwar aure na dana hafsy da ba a riga da anyi ba, yace duk abunda ya samu yaranshi itace, ina jin maganan ya fara tsayi na miƙe na wuce bedroom ɗina, sannan kuma yayah umar ya mata rantsuwa wallahi ta sake kai ƙafanta koda parlon ummie ne bada zaman lafiya ba sai ya harbeta, sai dai Abba ya sallama shi, yanzu haka ta fita tun safe a gidan ita da sister ta da tazo bayan abun ya faru.