Ana barin halal original by anty nice - Chapter 31
Ana barin halal original by anty nice Chapter 31: Ana barin halal original by anty nice Chapter 31. Ajiyan zuciya na sauƙe, "tou ummien yayah ta ke? Fatan…
4,264 words
Ajiyan zuciya na sauƙe, "tou ummien yayah ta ke? Fatan dai bata wani ɗaga hankalinta da surutun banzan matar nan ba ko"? Na tambayi hafsy. "eh tou ba sosai ba, da hankalinta ya tashi amma dai Su Yayah sun ƙirata sun lallaɓeta sun bata baki, sunce ta ƙara ƙarfin addu'an ta akanmu, insha Allahu babu abinda ta isa tayi wanda Allah bai nufa xai faru ba, ni wallahi Adda Ayshaa narasa meye ummie tayiwa matar nan da ta sakata a gaba? Naga dai ita tazo ta aure mata miji, ta sameta a gidan, kuma ga mamah kaman tafi ƙin ummie da mu". Murmushi nayi idona yana kan A.G daya shigo ya kwanta shida ƴar shi da ta fara bacci a gefe na, ido na yana kan shi yadda naga yana ɗan jan numfashin shi a hankali, daga dukkan alamu yana jin jiki. "Tou ke banda abunki Hafsy dole ae ummie ta tsole ata ido, zaratan sojoji har uku ta dire a gidan, ga kyawawan folawowi guda biyu da ta dire a gidan, ba dole tayi kishi da ummie ba, kuma duk da yarintar ta miji hankalin shi yana kan ladan noman shi, kedai kawai addu'a shi zai raba mu da kowa, da sharrin kowa, amma insha Allahu babu abunda zai sake faruwa damu,munfi ƙarfinta taji da damuwarta kawai".
Dariya hafsy tayi sannan ta tambayeni "ina A.Gn ki da Nasreen Ɗiyata"? Murmishi nayi na saka hannu ina shafa fuskan A.G nace, "ga A.G na kwance agefe na, ga Ƴarki Nasreen kwance a gefe na ta hanani sakat da mijina, da tayi six month ma turo miki ita zanyi na huta tare da mijina", dariya ta kwashe da shi tana kashe wayan don jin nace ga A.G na kwance a gefe nah, shi kuma harara na yayi yace, "kada ki fara cire mun ƴa a nono beauty, ki bar wannan mafarin, mumcy nah sai tasha ta ƙoshi a cireta".
Dariya nayi na kwanta a jikin shi, ina shafa fuskan shi nace, "ae Jarumina kun makara da shan nono har wai kusha ko ƙoshi, ae sai dai kuga wasu suna sha amma banda ku, tunda kun cika gaggawa sai kuyi haƙuri idan kunyi 10month" na faɗa ina jan kunnen shi, tayi yayi zaune ya ɗago ni sosai muna fuskantar juna.
"Eesha kada ki cire mun mamana a nono na roƙi alfarmanki, tasha nono har sai kin haihu tukun a cireta, idan bazaki damu bama su sha a tare, shima likitoci sun yadda da hakan, amma idan kinga zaki takura tou sai ita ki cireta idan kin haihu, don Allah beauty abi yadda nace", ya faɗa da wani kalan tausayi, wanda har sai da naji kaman hawaye zai taho mun, rungumeshi nayi sosai a jikina, "baby duk yadda kace haka za'ayi, insha Allah mumcy zata sha nono har ranan da ƴar'uwarta ko ɗan'uwanta zai zo duniya, na maka wannan alƙawarin indai ina raye".
Rungumeni yayi sosai a jikin shi yace, "insha Allahu ma kina raye, don jikina yana bani zaki rayu da ƴaƴana, zaki musu tarbiya irin wanda ni nake fata da burin ganin su da shi, don kema ƴar gidan tarbiyane mai tarbiya, sbd haka bani da damuwa da hakan, sai fatan Allah ya ƙara miki haƙuri da juriya akan tarbiyansu, don iyaye mata dayawa rashin haƙuri da juriya ne yake saka su kasa bada tarbiya wa ƴaƴansu, amma ke kam bani da haufi akanki, shiyasa kullum nake ƙara godewa Allah daya mun ni'ima da samun salihar mace irinki, roƙo na da fata na Allah yasa mu kasance har aljannah a tare, Allah ya bani ke har a aljannah", ya faɗa yana ƙara matseni a jikin shi, "Eesha ina sonki wani irin son da inaga ko uwa batayiwa abunda ta haifah, wani irin sone da Allah ne kaɗai yasan irin shi, don ko ni ban isa nace ga irinshi ba, ki kula dani ki kula da ƴaƴana, kiyi haƙuri ki basu kulawa wanda zasu zama abun sha'awa a ko'ina, ina so su rayu tare da mu, bana fatan su tashi a hannun wani ba hanun mu ba ni da ke, ina roƙon Allah ya musi albarka, ya baki juriya beauty nah".
Shiru mukayi daga ni har shi muna rungume gam da juna babu wanda ya sake magana, sai numfashin shi da yake mishi babu daɗi, sai kuma ɗan yari kaɗan da yake yi lokaci-lokaci. Muna haka har aka ƙira sallan la'asaar, tashi yayi ya fice masallaci ya barni, nima sallan nayi daga nan na ƙara gyara ɗakin ma fice parlor ina ɗauke da Nasreen ɗayan hannun kuma ina manne da wayana muna waya da ummie nah, muna ta labarin hali irin na mamie da raliya, wai don ɗazu Raliya ta ƙira hafsy sunyi kacha-kacha wa junan su, inda itama hafsyn bata barta ba don dama kar ne tasan kar, sunyi wa junan su fatafata yau, don sai da Abba ya ƙira raliyan ya mata babu daɗi, nidai haƙuri nayita bawa ummie, inda nake kuma sanar mata A.G nah baijin daɗi, "subhanallahi asthman shinne ya tashi? Idan ya shigo ki haɗa ni da shi, Allah ya bashi lafiya, ina kuma nasara take"? Cewar ummie dariya nayi don jin yadda ummie ke jan jikar nata, don kirarin da take mata kenan, Nasreen nasaran mata, bayan munyi sallama ne kaɗan sai ga heedayah ta shigo ɗauke da basket mai ɗan girma, kan dinning ta wuce bayan ta goye da Affan wanda ya kusa cika 1yr, idon shi biyu yana ta mun dariya, nia dariyan nake mishi har ta ƙarasa kan dinning ɗin ta ajiye ta juyo, hannu na miƙa mishi, ai kuwa ƙoƙarin ɓalle goyon yake yi, dole ta sunce shi ta miƙo mun shi, ina karɓan shi ita kuma ta ɗauki nasreen, ɗan ya mutsa fuska tayi ta juyo tana kallona, "Aunty yayah kamar ƴata tana ɗan zazzaɓi"? Lumshe ido nayi na buɗe akan Affan daya ke tsallen sun sauƙa ƙasa daga cinya na yana wasan shi, "wallahi kuwa heedayah, harda mura ma", na faɗa ina kallon idon Nasreen ɗin, "an bata magani ne? Inaga kaman haƙori ne, don ga bakinta yana ƙarni", cewar heedayah, "da wuri zata fara laulayin haƙori kenan ", na tambayi heedayah, zama tayi gefe na rungume da Nasreen a hannunta, ido na ƙura musu sai naga kaman ita ta haifeta tsabar kamanin da sukayi, sannan na maida kaina kan Affan daya ke ta zaga parlon da, tafiyan shi wanda baigama ƙwari ba yanayi yana faɗuwa, sai dariya yakeyi don jin daɗin su na yarah, dawo da kaina nayi kan heedayah nace, "nabata maganin mura da zazzaɓi, ni na ɗauka shi yake damuta ae, ni duk asthman Abbeenta ne yake damuna wallahi, idan naji sautin numfashin shi hankalina tashi yakeyi da yadda yake fita, bana jin nutsuwa wallahi", na faɗa ina miƙawa Affan hannu daya zo kusa dani yana mun gwalantun yarah.
"Allah sarki yayah A.G wallahi asthman nan yana matsa mishi sosai, kuma idan ya tashi fah sai ya bawa mutane tsoro, amma ae da sauƙi tunda ya fita mosque nagani," cewar heedayah, haka dai mukaita hira, nan take gaya mun ta haɗu mana da alale, jin akwai alale yasa na miƙe naje dinning ɗin, alalen na zuba da peppesoup ɗin, sai kunun gyaɗa mai zafi shima na zuba a cup, wuri na gyara na fara ci, ina kallonta jefi-jefi tana wasa da su Affan, Nasreen na lafe a jikinta.
Sai da akayi salan magrin A.G suka shigo tare da Yayah Ahmad da M.G, ɗaukan Affan yayi suka zauna a kan kujera, Yayah kuma ya ɗauki Nasreen, dayake bata ƙiwuya sai ta karɓe shi ta wani ƙura mishi ido kaman ta san waye, har sai da yayi dariya yace, "Ayshaa ƴar nan zatayi wayo sosai kamam hafsy", dariya dukkan mu mukayi, heedayah kamar muna fika ta musu sallama ta wuce gida, anan ta bar Affan, nima ɗaki na wuce ɗauke da Nasreen domin sun wuce dinning don cin abincin, sai da aka ƙira ishaa A.G ya mun magana nazo yaya zai tafi, sallama mukayi yace ya haɗa Ummie da A.G sun gaisa, godiya sosai na mishi, har waje na rakasu, bayan ya wuce ne na dawo na barsu tsaye shida M.G, kowa yana rungume da nashi ɗan, inda naji M.G na zolaya na wai A.G yace ya haɗa auren Nasreen da Affan, saboda haka gobe zasu musu baiko, dariya nayi na wuce ciki na barsu.
Dinning ɗin naje na tattare, duk sun cinye alalen, kunun kaɗai suka rage kaɗan sai peppesoup ɗin ma kaɗan, gyara parlon nayi naje kitchen nayi wanke-wanke, indomie na dafa da wani kifina da yake friedge, parlon na dawo naci, har nagama naje na wanke basu rabu ba, daga baya ne ma ya ƙirani na karɓi nasreen akan na bata magani tana so tayi rikici, ciki muka shiga, goge mata jiki kawai nayi da towel, nasaka mata kaya masu ɗan kauri,na bata magani sannan na saka mata nono tana sha, ido duka zube akanta inaga tsantsan kamanta da A.G, wani wurin kuma sai naga kaman Mummy, inaga da mummy take kama farinne na A.G, domin mummy kam baƙa ce, murmushi nayi na ƙura mata ido ina jin daɗin yau gani ina shayar da ƴar A.G, Allah sarki ashe fararen nan miji nane? Shiyasa tun ranan da na fara ganin su suka tsaya mun a raina, ashe dogon ciki wanda bai kai ɗayan haske ba rabo nane, dariya nayi ni kaɗai, sannan na cire mata nonon a baki ganin tayi bacci, kwantar da ita nayi na ɗan lulluɓata.
Toilet na shige nayi wanka na, ina fitowa nayi ɗan gyare gyare na, nasaka rigan bacci milk colour wani gajeren wando da riga armless, silk ne kayan A.G yasha gaya mun yana son wannan kayan baccin, shafa humrah nayi sosai a jikina, bayan na gama shiryawa ne na ɗauki wayana, Data na buɗe na shiga group ɗinmu, ai kuwa hira na samu sunayi gashi full house dama ni ake jira, hira sosai mukeyi ana shan chafter, Fatima tace ta sama mana wani haɗin daka mai gigita mai gida, hadiza sai wani zaƙewa takeyi don Allah a aiko mana, nima dai cewa nayi Fati kada amanta da Eashann A.G please, muna cikin haka ne naga ya buɗe ƙofa bakin shi ɗauke da sallama ya shigo, yayi wanka ya saka wata farar jallabiys yayi kyau yayi wani haske sosai, amma kuma ciwon kwana ɗaya ko biyu har ya ramar da shi, ido na zuba mishi a zuciyata nace, "akwai matar da tayi dace da haɗaɗɗen miji irin nawa kuwa? Gsky A.G na Duniya ne".
Lumshe ido yayi ya ɗan kanne munsu, murmushi nayo na cigaba da yaba kyaunshi azuciyata, ɗaukan nasreen yayi ya gyara mata kwanciya bayan ya matsar da ita, hannu yasaka ya jawo ni yana kwantar da ni a jikin shi, kashe wutan ɗakin yayi yana cewa, "zoki gaya mun murmushin me kikeyi dana shigo ɗakin,"? sautin murmushi nane ya sake fitowa, rungumeshi nayi sosai a jikina nace, "Baby nayi dace da miji, babu wata mace a faɗin duniya da tayi dace da miji irina, daɗi nakeji idan naga wai A.G na miji nane". Murmushi yayo yana ƙara rungumeni jikin shi sosai yace, "a hakan ma mijinki ke kaɗai insha Allahu duniya da lahira".
Rungumeshi nayi ina dariya nace "Allahu yasa ni kaɗai ce matarka A.G nah, don ranan da zaka Ƙara auren wata mutuwa zanyi nasani", "insha Allahu ma A Gn naki ne ke kaɗai, Allah ma kada ya nuna mun ranan da zan haɗaki da wata ƴa mace a duniya, don wuta xan tafi direct, bazan iya adalci a tsakanin ku ba, Allah na roƙeka kasa Eeshaa ce kawai rabona a mata", rungumeshi nayi ina jin son shi kaman zai zautar dani, murya a ɗage nace, "Ameen! Ameen!! Ameen!!! A.G nah, nagode Allah ya bar mu tare."
Ɗago ni yayi ya kunna hasken wayan shi yana kallona fuskan shi ɗauke da wani murmushi da ya mun kyaun gaske, "akwai wano namiji da zako so a duniya na bayan ni"? Ya mutsa fuska nayi ina hararan shi nace, "ae musulunci ma ya haramta mun wani ɗa namiji ballantana har ta kai dana so shi", na faɗa ina murguɗa mishi baki.
Lumshe ido yayi yana murmushi, "misali idan bana raye zaki so wani sama da yadda kika soni"?
Wani irin mummunan faɗuwar gaba naji, har sai da naji wani ɗumi a tafin hannuna dana ƙafana kamanmai zazzaɓi, fuska a ɗaure nace, "bana son sake jin irin wannan furucin jarumina, bana son irin wannan tunanin da kakeyi, nida kai insha Allahu har sai mun tsufah tare, zamu rayu da ƴaƴanmu mu aurar da su muyi jikoki yadda su mummy suka ga jikokin su insha Allahu".
Lumshe ido yayi yana jawoni jikin shi, wani irin sex yayi dani a wannan rana da wannan lokacin wanda zance bai taɓa yin irin shi ba, don wuraren ƙarfe ɗaya kuka mai ƙarfin gaske ya saka mun, "Eeshaa kin gajji ni ka bansan me yake faruwa ba nakasa gajjiya Eesha ta, ina sonki Eesha, ina sonki Beauty nah", rungumeni yayi sosai yana kuka, "Eesha ki kula mun da yaranah, baby yarah nah, mummy nah", rungume shi nayi ina rarrashin shi, don ji nake kaman gabana xai buɗe cikin ya zubo, dauriya kawai nakeyi har nasamu yayi shiru.
Wankana tashi na shiga, bayan na fito na same shi rungume da nasreen a jikin shi ya fara bacci, tashin shi nayi a hankali nace yaje yayi wanka, Buɗe ido yayi da ƙyar yana kallona, chan kaman zai koma baccin sai kuma ya miƙe, kiss ya yiwa nasreen a goshinta sannan ya wuce toilet, baifi mintuna kaɗan ba naga ya fito, bakin gaɗon yazo ya zauna ni kuma ina kan dressing Mirrow ina busar da gashi na, tari yakeyi sosai yana jan numfashi da ƙyar, ajiye dryer nayi na zo wuron shi zama nayi a gefen shi ina shafa kanshi ina mishi sannu, "ru...wa..a," ya faɗa aɗan fusge, da sauri na koma jikin mirrow na ɗauko bottle na ruwa na kawo mishi, kaɗan yasha ya miƙo mun, sannan ya mun alama na bashi jallabiya, ɗauko wannan jalabiyan nayi na miƙa mishi, taimaka mishi nayi yasaka, ae kuwa kaman jira yakeyi agama sakawa sai numfashi yafara gardama, ga tari mai zafin gaske, nidai jikina duk rawa yakeyi na rungumeshi ina kuka.
Wayan shi ya nuna mun nayi sauri na ɗauko na miƙa mishi, murya a fusge yace, "mu..m..my" zaro ido nayi ina nuna moshi time, wurin ƙarfe biyu saura ne fah, amma sai ya ɗaga mun kai alaman na ƙira mishi ita, banyi nawa ba na danna mata ƙira nasaka a handsfree, ae kuwa kaman wanda take zaman jira kuwa naji charaf ta ɗauka, "A.G nah jikin ne? Nakasa bacci wallahi inata tunanin jikinka", naji muryan mummy, nine nayi saurin amsa mata da "mummy wallahi jikin ne, shine yace na ƙira ki", na faɗa ina kuka, "subhanallahi A.G nah kajina" muryan Daddy ne naji, bayan najiyo muryan mummy tana kuka a gefe. Lumshe idon shi yayi ya buɗe yana ɗaga kai alaman yanaji, da ƙyar kuma yasake cewa, "mu..mmy ki..zo, mat......aa nah, ƴa.....ata, mummy ki...zo". Muryan Daddy naji yana cewa, "Ayshaa kashe wayan ki ƙira M.G ku wuce asibiti", jiki na rawa na kashe wayan, ƙiran M.G na fara amma sai naji shi number busy, ashe ina kashe wayan Daddy kuma sai ya hau ƙiran shi, ae watsi nayi da wayan na fice a ɗakin da gudu, buɗe ƙofan parlon nayi kawai na kama hanyar side ɗin su M.G ina kuka ina tafiya gudu-gudu, ban ƙarasa ba naga ya buɗe ƙofan parlon su yana fitowa hannun shi riƙe da jallabiya yana sakawa, bayan shi kuma heedayah ce riƙe da key ɗin motan shi, ganin suna tahowa sai kuma na juya gidan mu da gudu.
Har ɗakina suka shigo dukkan su inda A.G yake yashe a ƙasa yana ta kokuwa da numfashi, duk fuskan shin nan yayi wani ja sosai, kuka na sake fashewa da shi na durƙusa ina ƙoƙarin riƙo shi, gefe ɗaya kuma nasreen ta fashe da kuka, ɗaukan ta heedayah tayi tana rarrashi, M.G kuma na taimaka mishi muka ɗaga A.G, rungume shi yayi mukayi mota da shi, daga chan heedayah ta fito mun da dogon hijabi nasaka don na manta ma wannan kayan baccin ne kawai a jikina, baya na shige na rungume kan A.G a jikina ina kuka, heedayah M.G yace ta rufe gidan mu ta wuce da Nasreen gidan su, taso bin mu amma ya hana, haka mukaja muka tafi da gudu zuwa asibitin.
Muna shiga suka wuce emergency da A.G nah, nidai kuka kawai nake ta zabgawa, muna shiga wayan daddy ya sake shigowa wayan M.G, ɗauka yayi sukayi magana da Daddy, daga nan ya miƙo mun wayan yace na riƙe, bayan wani lokaci aka maida shi wani ɗaki, sakawa A.G oxygen aka yi, da ƙyar numfashina yake tafiya daidai, ganin yadda A.G yake shan wahala, sai naƙara tsorita da ciwon asthma, ido na yana kanshi har zuwa ƙarfe huɗu saura, lokacin sai na fara jin ƙaran sautin Oxygen ɗin yana fita da ban, da sauri wasu nurses guda biyu suka zo kanshi, M.G kuma yayi waje ya ƙira Dr, tare suka shigo yana mishi magana suna tahowa tare, nidai sanyi naji yana rufe ni sai na fita a ɗakin, na neme kujera na zauna. Huɗu yana cika dai-dai kaman wanda aka tsabureni na miƙe tsaye n shige ɗakin da aka kwantar da A.G, ina shiga naga nurses ɗin nan suna rirriƙe M.G dayake shirin faɗawa kan A.G, zuciyana ne naji ya tsinke, ɗago da kaina nayi na ƙurawa A.G ido danaga an cire mishi oxygen yana bacci, azuciyata nayi hamdala nace ya samu bacci, sannanna maida kallona kan M.G dayake wani irin kukan fitan hankali, muryana yana ɗan rawa nace, "Yasamu bacci ne? Numfashin ya ɗan lafa ko"? Na tambayi Dr da yake tsaye akan A.G, ɗaga mun kai yayi alaman hakane, sannan na maida kaina kan M.G nace, "Yayah M.G kayi shiru mana tunda kaga ae da sauƙi tunda har ya samu bacci", na faɗa ina shigowa ɗakin, amma lokaci ɗaya naja na tsaya bakina a buɗe jin abinda M.G yake faɗa muryan shi a sama kaman muryan shi zai cika ɗakin ya fasa, "Ayshaa Ɗan'uwana yayi baccin da babu farkawa ne, A.G nah ya tafi ya barni da ƙalubalen duniya, A.G na ya rasu ya barni alaokacin danake tsananin buƙatanshi".
Ido na mayar an A.G domin na gasganta abunda M.G yake faɗa, amma sai banga alaman ya rasu ba, domin ni dai naga kaman numfashi yake a nutse, sai kuma wayan shi da yake ringing a hannu na na kallah, DADDYna gani akan screen ɗin, ban wani ja ba na ɗaga wayan, har lokacin kukan Mummy nakeji, muryan Daddy cike da damuwa yace, "M.G yyh jikin A.G ɗin, an samu numfashin ya lafa? Ga mamanku ta ɗaga mun hankali akan mu taho a daren nan, amma yanzu inaga zamu taho kawai", yana gama faɗin haka na ji bakina ya buɗe da ƙarfi nace, "Daddy A.G nah ya rasu inji M.G, mijina wai ya rasu inji M.G," kaman kuma an zabure ni sai na kashe wayan bayan naji sautin salatin Daddy da ihunn mummy, ido na yana kullewa don azaban zafi haka nasaka number yayah Ahmad nayi dialing, yana ɗauka naji yace, "M.G yyh dai, meya faru"? "Yayah mijinane wai ya rasu inji M.G, A.G nane a kwance wai ya rasu inji M.G", shima salatin daya sakane na yi sauri na kashe wayan ina zare ido kaman kuncacciya, layin ummie na kawai nasaka, amma har ya gama ringing ba'a ɗauka ba, chan sai nasaka na hafsy na ƙira, yana farawa kuwa ta ɗauka, sallama a bakinta amma ban barta ta gama ba, "ummie na A.G ya rasu inji M.G, ummie kizo mijina ya rasu inji M.G" salati hafsy ta saka tana ƙwalawa ummie ƙira da take toilet, kashe wayan nayi kaman sukuwa, lokacin kuma ƙiran Daddy da yake shigowa ya sake shiga, Miƙawa M.G wayan nayi ina nufan kan Gawan Mijina, "wai da gaske ne mijina ya rasu"? Iya ƙarfina nayi wannan tambayan Aunty nice, wani tambaya mai ciwo wanda amsan shi yafi komai ciwo a zuciyata da rayuwata. A lokacin hajiya Ayshaa tsayawa tayi da bani labarin,domin wani irin ciwon rashin A.G daya zo mata alokacin, wanda muka haɗu mukayi kukan da muke yawan yi idan mun tuna mazajen mu da rasuwar su, wanda shine ƙarfin tarayyah da ita, nayi kuka a ranan na tuna nawa mijin.
Wannan shafin na sadaukar wa duk wacce ta rasa mijinta ko ɗanta daya rasu da ciwon asthma, na sadaukar wa duk matar da ta rasa mijinta a shekarunsu kaɗan na rayuwar aure 😭😭😭😭😭😭Irin wannan mutuwa yana da ciwo yana da taɓa zuciya, tabbas naji mutuwar A.G kwatankwacin yadda naji mutuwar nawa mijin 😭😭😭
*Allah ka haskaka kabarin A.G, ka haskaka kabarin Nuhu, karaya mana abunda suka bari cikin amincinka* 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻😭😭😭😭
Allah kajiƙan ƴan'uwana da suka rasu ɗauke da ciwon asthma *Ƙassim Jama'are* *Musa yawale* 😭😭🙏🏻
*NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* (Bappah) *KHADIJA AMINU GARBA* (MAMAH) ALLAH YA MUKU ALBARKA
Tabbas wannan rana munyi kuka, munyi kukan rashin Gwarzayen mazajen mu, mazajen da suka nuna mana ƙauna sama da kansu, nayi kukan tausayin kaina, nayi kukan tausayin Ayshaa,.....shin da gaske akwai wata mace a duniya data saura kamar ni da Ayshaa da kewar mijinta? Idan akwaita please ta nemi ni ta wannan number 08036181881, a zuciyata da tunani na kaman babu sai ni, amma dana haɗu da ayshaa sai naji akwai dai ɗaya kam bayan ni, Allah ya jiƙan mazajen mu Allah ya musu rahma,.... Da ƙyar muka rarrashi kanmu da kanmu, sannan na nemi ayshaa da mu bar wannan hiran a wannan ranan, amma sai tayi murmushi tace, "Aunty nice yanzu ma zamu fara kuma mu gama, kinfi kowa sanin duk yadda muka haɗu mukayi hira akan su sai mun koka, ballantana na yau akwai banbanci", hawayen ta ya sake biyo kan kuncinta, ganin haka ya saka na sunkuyar da kaina na bar kallon ta, shiru kaman babu mai sake tankawa a tsakanin mu, chan kuma sai na tsinkayi muryanta da yake rawa wanda yake ƙara raunana mun nawa zuciyar ta cigaba da bani labarin.
"Jikin gadon da gawan A.G na yake na ƙarasa, ido na ƙura a cikin shi don ganin ko yana numfashi, amma sai naga shiru, hannun shi da yake ɗaura akan cikin shi na ɗaga sama, sai kuma na mayar na ajiye, still dai A.G na bai motsa ba, murmushin da bai kai ciki ba nayi wanda har yau ban san dalilin hakan ba ko yin hakan, ido na mayar kan kyakkyawar fuskar shi da tayi wani fari sol, skin ɗin shi kaman idan an zuba ruwa bazai zauna ba tsabar santsi da sheƙin da naga yanayi, dab da fuskar shi nakai nawa fuskan, a hankali kaman wanda nakejin tsoron wani yaji ni nace, "A.G nah" naji shiru bai amsa ba, "mijina ka buɗe idonka kacewa kowa kana da rai, bacci ne kawai kakeyi," sai na kai hannu na kan cikina nace, "wannan babyn tana ciki, idan tazo duniya zatayi kuka batagan ka ba, zatayi kuka baka ɗauke ta ba, bazan iya bata haƙuri ba" sai na juyar da kaina gefe kaman ina neman wani abu, "Nasreen zatayi kuka baka ɗauke ta ba, waye mummy zata gani idan baka nan? Gidan mu kake so na koma na zauna A.G? No bazan koma gida ba, gidan ka zan zauna, zan maka komai, zan ƙara addu'a Allah ya baka lafiya ka daina asthman nan bana son shi," sannan na kai hannu na kan fuskan shi ina shafawa, dai dai lokacin naji an dafa kafaɗa na, da sauri na ɗago kaina na kalli yayah da hawaye yake bin fuskan shi gefe ɗaya kuma yayah muhammad ne ya sunkuyar da kan shi ƙasa, nuna musu gawan A.G nayi nace, "mijina" juyawa yayah muhammad yayi ya bar ɗakin, matsowa dab dani yayah Ahmad yayi ya riƙo ni jikin shi, amma sai na turje na sake nuna mishi gawan A.G nace, "mijina yayi bacci, amma M.G ya rikice yace wai ya rasu, matso ka duba fuskan shi kataɓa ganin wanda ya rasu mai kyau? Yayah mijina bai rasu ba bacci yakeyi, ina son mijina, ina son ya tashi yanzu ku gani, kada a yadda da maganan M.G aje a bunne shi na shiga uku", kuka sosai Yayah Ahmad yake a lokacin, amma ni ko tarfin hawaye babu a ido na.
"innalillahi wa'innah ilaihir raji'un, dana san zanji ciwo da tashin hankali da ban rubuta book ɗinnan ba, wannan page yana bani wuyan rubutawa 😭😭😭😭😭 Ina jin ciwo sosai a zuciyata, how i wish kun san ciwo da zafin da nakeji a yanzu da nake rubuta wannan page ɗin? Nasani ba kowa bane yasani, kuma nayi imani da Allah ba kowacce mace bace da mijinta ya rasu tasan zafin irin yadda nakeji, don kowa da irin rayuwar shi, kowa da irin ƙaunar da aka mishi, kowa da irin ƙalubalen rayuwar da ya shiga bayan mutuwar mijinshi 😭😭😭😭😭 Kana kuka ne sbd ciwon mutuwar, da kuma rayuwar bayan mutuwan 😭😭😭
Riƙo hannu na Yayah Ahmad yayi yana rarrashina da mu fita waje Dr zasu sake dubawa suga ko yana raye, don ba lallai bane ma ya rasun, kaɗa kaina nayi alaman hakan ne, sai na maida kaina kan Dr da yake tsaye ya ƙura mun ido, gefen shi wani Dr ne daban da ban san lokacin da ya shigo ba, sai nurses guda biyu da suke tsaye, "Dr kuzo ku duba mun mijina, hala ma dogon suma yayi, don nasan yana sona, bazai rasu ba yanzu bayan ban haihu ba", ina faɗa suna ɗaga mun kai alaman zasu zo su duba shi, haka na fita nabi bayan yayah Ahmad muka bar ɗakin.