Ana barin halal original by anty nice - Chapter 32
Ana barin halal original by anty nice Chapter 32: Ana barin halal original by anty nice Chapter 32. Muna fita muka samu su Yayah muhammaɗ suna zazzaune,…
3,146 words
Muna fita muka samu su Yayah muhammaɗ suna zazzaune, M.G kanshi ɗaure akan kafaɗan wani abokin su ɗan bauchi yana ta rarrashin shi, gefe ɗaya kuma Yayah muhammad ne rungume da Aunty B da taketa kuka yana rarrashinta, Aunty J kuma ta kife kanta akan kujera tana tsugune a ƙasa tana kuka, hannun ta ɗaya rungume da babyn ta, matsuwa nayi kusa da su ina cewa, "bai rasu ba dai, yanzu Dr yazo da wani Dr zasu sake duba shi, haba A.G nah ne zai rasu, suma yayi, yanzu zasu farkar da shi mu tafi gida, yana tashi ma ni bauchi zamu tafi tsoron Abujan ma nakeyi, zan gayawa su Daddy zamu gudu bauchi mu ɓuya, Abujah kam mutuwa akeyi", ganin surutu na ɗin ya fara yawa sai Yayah muhammad ya sake Aunty B yazo ya rungumeni, "Ayshaa tou muje gida ki shiryah kayanki kawai mu wuce Bauchi da zaran A.G ya farka, inaga hakan yafi kamata" murmushi nayi na riƙo hannun shi nace, "mutafi kam bana son ganin asibiti ma, kawai mutafi" sannan na juya na dubi Yayah Ahmad da ya kasa daurewa ya kifa kanshi a jikin bangon wurin yana kuka kaman ran shi zai fita, murmushi nayi nace, "yayah barrister kadaina kuka zafa mu gudu mu bar Abujan nan, kuma ku tattaro kayanku kubar garin, kajira Drs ɗin su gama duba shi mu kam zamu wuce gida," ae kuwa kaman na tsokano M.G sai yafara wani irin kuka kaman zai sandare a wurin har yasa naji jikina yayi sanyi, amma sai yayah Muhammad ya riƙoni su Aunty suka bimu a baya muka fita, gaban mota na shiga su kuma suna baya, daga shi har su hawaye sukeyi amma ni kam ko gezau, sai zare ido kawai nake ina kallon hanya, muna dab da zamu shiga unguwar mu sai ga ƙiran ummie na ya shigo wayan yayah muhammad, akan idona ƙiran ya shigo, saboda haka ganin bazai ɗaga ba yasaka na ɗauki wayan na ɗaga, kuka naji tana yi tana tambayan yayah, wai yayah nake fatan dai babu abunda ya sameni? Murya na da yake asama na kasa daidaita shi nace, "ummie ae ba rasuwa yayi ba, yanzu ma zamu gudu mu bar Abujan ne kada ace kuma ya rasu, kinga idan mun gudo bauchi ae zaku ɓoye mu keda mummy ko? A.G nah yana kwance shiru baya motsi, shine M.G daya rikice yace wai ya rasu ne, ae na ƙiraki nagaya miki yace ya rasu sai hafsy ta ɗauka, ae bai rasu ba, yayah ma yagani ae", ina faɗa na juya ina kallon yayah da yake tuƙi hawaye yana zuba mishi, "yayah ae kaga mijina bai rasu ba ko?" ɗaga kai yayi alaman hakane, dariya nayi na cigaba, "ummie yayah ma ae yace bai rasuba, bakiga yadda yayi kyau ba, kinsan mijina mai kyau ne fari, ina ae bai rasu ba".......kuka sosai ummie ta fashe da shi, sai kuma naji muryan mamah a gefe tanata salati, Abba ne ya karɓi wayan daga baya yace, "Ayshaa tah" jin muryan shi yasa naji wani hawaye mai ɗan ɗumi ya taho mun a kan kunci na, "Abba mijina bai rasu ba, kawai M.G ne ya gigice da ciwon yace wai ya rasu"..... Hawayen ne suka ƙara zubo mun, a hankali Abba ya sake ƙiran sunana yace, "Aysha ki ringa faɗin Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un" ɗaga kai nayi kaman yana gani na, amma bance komai ba, ganin mun shiga gate ɗin gidan mu yasaka na miƙawa yayah wayan shi, saboda hango heedayah da nayi ta fito hannun ta ɗauke da nasreen da taketa kuka, da ƙyar na jira yayah ya buɗe ƙofan na fita, wurinta naje ina kallon yadda duk ta wani fige ta birkice, "Aunty yayah jikin Yayah A.G"? Murmushi nayi nace, "yayi bacci ae, shine mijinki ya burkice yana ta ihu yana kuka wai mijina ya rasu, ta yayah ma zai rasu kowa mijinta yana nan"? Miƙa hannu nayi na karɓi nasreen muƙa shige parlour mu, har ɗakina muka shige da su Aunty muka bar yayah a parlour yana waya da su Abbah.
Bakin gado na zauna ina bawa nasreen nono, da ƙyar ta kama tana ta sauƙe ajiyan zuciya, kallon su nayi suna haɗa mana kaya suna kuka, heedayah kuma sai tambayan su takeyi wai meya faru ne? Meyasa suke haɗa mana kaya? Da taga bazasu bata amsan da takeso ba ne yasa ta dawo kusa da ni, "Aunty ina zakuje da kaya mai yawa haka? Yyh jikin yayah na yake"? Murmushi nayi nace, "kema kije ki haɗa kayan ki bauchi zamu koma Abujan nan gaba ɗaya babu alkhairi a zaman shi, yanzu Drs ɗin zasu farfaɗo da shi sai a wuce, kowa ma ya amince", na faɗa ina kallon su Aunty da suka gama haɗa kayan.
Kuka heedayah takeyi sosai ta fara ƙiran wayan Mummy, daga nan ta biyoni parlour inda muka samu yayah zaune yana ta kuka, dafa ƙirji heedayah tayi tace, "yayah meya faru ne kam kowa bai ce mun komai ba, M.G kuma yaƙi ƙirana", kallonta yayi sannan yayi dauriyan ce mata itqma ta haɗa kaya bauchi za'a mayar da A.G, idan ya samu sauƙi sai a dawo, hankalin Mummy zaifi kwanciya, ɗaga kai tayi alaman hakane, sannan ta wuce side ɗinta ta haɗa kayan M.G da nata da kuma na Affan.
Duk yadda naso su bari na haɗa kayan A.G sai yayah yace na bari akwai kaya a bauchi ae, haka na haƙura muka zauna a parlour, shi kuma ya fice waje yana ta amsa waya.
A wannan baƙin daren ne kafin six na asuba Abba da Daddy har Alhaji Inuwa sunyi arranging tahowar mu bauchi ta jirgi, an tsayar 8:00am zam shigo bauchi, zuwa 10:00am za'a kai A.G nah gidan shi na gaskiya, ni kuma gefe ɗaya burkitan kai yakasa sawa na gane hakan sai surutai nakeyi, gashi babu wani babba a wurin da zai sakani nutsuwa, suma su Auntyn duk ba sanin abunda ya kamata suyi mun ba sukeyi, duk suma sun burkice iya irin nasu, yayau na kuma tsantsan tausaya mun yasaka suka kasa taɓuka komai.
Duk yadda aka so bamu shiga bauchi ba sai 9:00am, kuma babu wanda ya nuna alaman da na fahimci gawan A.G yana jirgin, muna isa kuma mu aka fara gaba damu kafin fitar da gawan, direct gidan su A.G da yake fadaman mada muka wuce, jama'a kaman an haɗa garin bauchi ne a ƙofar gidan ya saka na fara jin yankewar zuciya, ido nafara zarewa ina kallon mutan.
Gate ɗin gidan a buɗe haka muka shiga cikin gidan har inda ake packing motocin gida muka tsaya, jikinane naji ya ɗauki rawa lokaci ɗaya, juyawa nayi na kalli Aunty B da ta rufe idonta da hijabin ta tana kuka, dawo da kaina nayi gefen Aunty J na ƙura mata ido, ita ma kwantar da kanta tayi jikin murfin ƙofan tana kuka, chan naji muryan heedaya a rikice tana tambayan driver, "Malam Ali waye ya rasu a gidan mu mukazo? Alhaji ne ya rasu"? Hankali na yana kan driver naji me zaice amma sai kawai ya kifar da kanshi kan stearing motan ya fashe da kuka, ae buɗe motan tayi da gudu-gudu ta fice, a wurin ma ta ajiye Affan tana ƙwala ƙiran sunan Mummy tayi cikin gidan.
Buɗewa mukayi dukkan mu muka fito, hannu Aunty J tasaka ta karɓi nasreen a hannu na, ban ƙiba na bata ta haɗa da nata muka shige ciki, bin mutane kawai nakeyi da kallo suna ta kuka, barin ma da suka ganmu mum shigo, nidai banyi kuka ba har lokacin sai zare ido ina kallon mutane, parlour mummy muka shige dukkan mu, inda daga wurin nake jiwo muryan Heedayah tana kuka tana tambayan waye ne ya rasu a gaya mata, ban bi takanta ba na ƙurawa ummie da ke rungume da hafsy, kuka hafsy takeyi gefe ɗaya kuma ga ƴan gidan mu, gasu Gogho ƙanwar ummie maman zainab, ga zainab, sai kuma maryam a gefenta, hajiya ummah, mamah, mamie, ga kuma dangin Abba dana ummie cike a parlour, cinyar ummie Aunty B da Aunty J suka saka kansu suna kuka, Goggo kuma ta amshi nasreen daga hannun Aunty J, nidai kasa ɗaga ƙafa na nayi daga inda nake, dukkan illahirin jikina rawa yakeyi.
A shigowar mu na hango Daddy a waje, tou mummy ce data ji jikin A.G ta rasu? Sai kuma tunani na ya tsaya daidai lokacin da mummy ta fito daga bedroom ɗin ta Huda na biye da ita a baya, kasa rufe bakina nayi wanda nake shirin tambayan waye ya rasu?
Rungumeni naji tayi ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya, "Ayshaa an mana mutuwa ni da ke, tabbas rasuwar A.G ni da ke akayiwa, innalillahi wa'innah ilaihir raji'un", naji ta faɗa tana ƙara rungume ni, Huda ma ta rungume mu tana kuka, ɗaga kaina nayi na dubi ummie na da ta ƙura mun ido tana share hawayenta, wani ƙararrawa mai ƙaran gaske naji yana kaɗawa a ƙwaƙwalwata, wani abu mai zafi da ƙarfi kuma ya taho tun daga tsakar kaina har ɗan yatsan ƙafa na, ido na namayar kan yatsan ƙafa na ɗin don ganin menene, amma banga komai ba, maida kaina nayi kan mummy nasaka duka hannaye na na ɗago ta, "A.G nane ya rasu"? Na tambayeta, kuka ta fashe bata ce komai ba, ido na mayar kan Hida na sake tambayanta, "mijinane ya rasu muna hanƴa"? Nan ma kuka takeyi ta ƙara rungume ni.
Juyawa nayi na kalli ummie, daga inda nake na biɗe bakina da ƙarfi nace, "Ummie!!!" na ƙirata da ƙarfi, sannan nace, "ke kaɗai zaki iya gayamun hankalina da tunani na su fahimta", ido na ƙura mata.
Tashi tayi daga inda take tazo har gabana, hannunta ta saka ta riƙo hannu na, inda take zaune ta kaini da nufin na zauna, girgiza kai nayi sannan nace, "bazan iya zama ba ummie," Kujera aka nuna mata kusa da hajiya ummah akan na zauna, har wurin ta kaini na zauna ita kuma ta zauna a gefena hannun kujeran, dafani tayi a hankali tace, "ki ringa furta innalillahi wa'innah ilaihir raji'un", kallonta nayi alaman ita nake jira, hawayenta ta share tacigaba, "kiyi haƙuri Aysha nah, Allah daya fimu son Aminu shi ya karɓi abun shi tun daren jiya, bawai kuna hanya bane ya rasu tun jiya Aminu ya amsa ƙiran ubangiji, kiyi haƙuri ki rungumi irin naki ƙaddaran, kiyi haƙuri da juriya irin yadda addinin mu ya koyar da mu, ki dubi Mummy wacce ta haife shima ta karɓi ƙaddaran ta, kiyi haƙuri Aminu yanzu addu'ar ku ita yake buƙata". Kallon ummie nayi na tsawon lokaci mai tsawon gaske, daba don ita ta haifeni ba, kuma nasan dattijan takarta da gaskiyarta, yau dana ce ko dai ummie ta samu rauni ne a ƙwaƙwalwarta, amma sanin dattakunta da girmanta gareni nasan bazata mun ƙaryah ba, kenan dai tabbas A.G na ya barni, A.G na ya barni bari na har abada, A.G na bazan ƙara ganin shi ba, bazan ƙara taɓa jikin shi ba, baxan ƙara jin muryan shi ba, mutuwar na dai da akeyi itace yau A.G na yayi, da sauri na ɗaga kai na kalli jama'ar da suke parlour suna kuka, bance komai ba banyi kukan ba, ido kawai na ƙurawa nasreen da take rungume a hannun Mamah da ta karɓa a hannun Goggo, na daɗe ina kallonta ban san tunanin me nakeyi ba, chan na mayar da kallona kan hafsy da take rungume jikin su Aunty B suna kuka, maida kaina nayi kan Mummy da gaba ɗaya ta firgice, Huda ma kuka takeyi tana rungume da Mummy.
Kallon kyakkyawar fuskar ummie na nayi na tsawon lokaci, babu abunda na iya cewa, sai kallon su kawai nakeyi suna kuka, idan na kalli wannan sai na kalli wannan, ina ma zan iya jin kukan yazo mun, amma abu ya gagara.
Tsawon lokaci muka fara jin hayani a waje alamar an taho da gawar A.G gidan kenan, kuka ne ya sake tashi a parlour, Mummy ta miƙe da sauri zata fice, amma wata yakombonta ta bada umurnin a riƙeta tukun, kuka sosai sukeyi amma banda ni.
Daga baya Hassan mijin Huda ne ya shigo, yace mummy wai tazo inji Alhaji, Goggo ce da sai a lokacin na ganta ta kamo hannun mummy suka fice, daga baya akazo akace muzo parlour Abba dasu Huda da Heedayah, Ummie a lokacin ta riƙo hannu na ta miƙawa mamah akan muje tare, haka na bi bayan Mamah muka fice zalam zalam ina binta, babu uhm babu ah'ah, A gefen dinning ɗin Daddy na hango gawan A.G na kwance akan tabarma, an mishi wanka an saka mishi kayan gado, Gefen shi Alhaji ne sai Dadda, ga Daddy da Mummy duk a wurin, alama dai addu'a suke mishi, wurin ƙafafuwan shi kuma M.G ne yashe a wurin ya kifa kanshi daidai ƙafan A.G, juyawa nayi gefe sai naga Abba na dasu yaya a zaune a cikin parlour, kasa yin gaba nayi na ƙurawa Abba na ido, a hankali naga ya taso ya taho har inda nake tsaye, hannun shi duka ya riƙo ni ya wuce dani har inda gawan A.G yake kwance, yayah muhammad yana mara mana baya, gefe ɗaya kuma yayah Ahmad ya kwantar da kanshi yana kuka anata bashi haƙuri.
Tsugunawa nayi a gaban gawan mijina, Abba yana riƙe da hannu nah, ɗago ido Daddy yayi muka haɗa ido, idon shi duk sun kumbura yayi kuka kaman ba namiji ba, "sannu baiwar Allah, sannu Ayshaa, matso kiyiwa mijinki addu'ar ban kwana", muryan Alhaji inuwa naji yana mun magana, kallon shi nayi na sake maida kallona kan A.G, buɗe fuskan shi sukayi bayan an yaye mayafin da yake rufe da shi.
Kuka Mummy tafara tana jera mishi addu'o'i, "nayafeka Aminu nah, nayafe maka duniya da lahira, dama ni baka taɓa mun komai ba Muhammad Aminullah, idan ka mun ma na yafe maka, Allah ya karɓi baƙuncinka Aminu na, Allah yasa kayi ƙarshe mai kyau, Allah yasa ƙarshen wahalar kane Aminu nah, nikan na yafe maka, Allah ya kula da bayanka, Allah ya raya abunda ka tafi ka bari cikin aminci, Aminu na maka alƙawarin kula da abunda Allah ya bar maka har ƙarshen numfashi na, zan sota tamkar yadda na soka ɗana, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" mummy ta furta da ƙarfi tana kwanciya a jikin shi, duk dauriya irin na Alhaji inuwa sai da ya share hawaye, rungumeta Daddy yayi, Huda da heedaya ma addu'a suka mishi, amma dai huda ce ƙarfin yin, heedayah kam kukanta kawai takeyi.
Hannu na na ɗaura akan fuskan A.G, na ƙura mishi ido ina jin wasu daga kalaman shi suna dawo mun cikin kaina, bakina nake son buɗewa amma sai naji wani abu yana tokare mun bakin, muryan Daddy na ji yana cewa "ki mishi addu'a Ayshaa za'a fita da shi ne."
Ɗago kai nayi da sauri nace, "mijina ɗin za'a tafi da shi?" sun kuyar da kai Daddy yayi yana share hawaye, sai Abba ne ya mun magana a hankali yace "addu'a zaki mishi magana Ayshaa ta" Dawo da kaina nayi kan fuskar Abba, sannan naji wani nutsuwa yazo mun lokacin da Abba ya ɗaga mun kai alaman nayi addu'an.
Bakina ne ya buɗe maji na furta, "Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un, Allahummah inna (Muhammad Aminu) fee thimmatika, wa habli jiwaarika, faqihi min fitnatil - qabei, wa 'athaabin - naari, wa 'anta 'ahlul - wafaa'i wal haqqi - ghafoorur - raheem. Allahummaghfur lahu warhamhu, wa 'aafihi, wa'fu 'anhu wa'akrim nuzulahu, wa wassi mudkhalahu, waghsilhi bil maa'i waththalji walbaradi, wa naqqihi minal-khataayaa kamaa naqqaytath-thawbal -abyadha minal - danasi, wa'abdihu, daaran khayran min daarihi, wa ahlan khayran min 'ahlihi, wazawjan khairan min zawjihi, wa'adkhilhul jannataa, wa 'a'ithhu min 'athaabil qabri wa athabin -naar. Allah ya baka ikon amsa tambayar kabari. Allah ya haɗaka da mala'ikun rahma mijina, Allah yasa ka huta", kafin nagama mishi addu'a hawayena sun cika gaban riga na, zuba sukeyi kaman ruwan pampo, rungume ni mummy tayi kawai dukkan mu muka fashe da kuka, lokacin kuma ake riƙe M.G don a ɗaga shi za'a ɗauki gawan A.G
Mutuwa rigar kowa, wannan book bawai soyayyah bace ta ja hankalina ga rubuta shi, gaskiya babu wani abu sai darasin ciki, book ne daya taɓa zuciyana kuma nayi imanin ya taɓa zuciyar mutane da dama, misali irin mugunta da asirin da akayi wa Goggo wurin rayuwar aurenta a gidan su M.G, anshiga hakkin uba da ɗa, an rabaƘaunar su an hana su zama tare, kuma duk macece sila, Rayuwar gidan su Ayshaa shima ƙalu bale ne akan mu mata, mamie ta cutar da Ayshaa tun farkon labarin, ta rabata da wanda ya sota ta haɗa auren da ƴarta, abun ɗubawan bawai rashin auren Aliyu bane damuwa, a'a raba tsakinin habiba da ayshaa shine muguntar da tayi, wanda habiba ba mai tsawon rayuwa bace, na uku muguntar da tayi a tsakanin rayuwar auren A.G da Ayshaa, ta cutar da su ta hana musu jin daɗin zaman su, wanda a ƙarshe tana shirin jifan su da mummunan abu, sai kuma Allah yayi ikon shi ya ɗauki rayuwar A.G, duk fah sharrin na mace ne, mata me muke nema a duniya da babu wani buri a zuciyar mu illah mugunta. Mu raba mata da miji Mu raba ɗa da mahaifi Mu raba ɗan'uwa da ɗan 'uwa Mu raba uwa da ɗa Mu nemi da ƙusar da rayuwar ɗan'uwan mu wai duk a matsayin kishi, tou ƙaryah ne ba kishi bane mugunta ne da kuma hassada, da kuma rashin tsorom Allah Ya Allah ina roƙonka kasaka wannan littafi yaje har wurin mamie ko ƴarta Raliya. Ya Allah kasa ɗaya daga cikin su ta karanta, ko wata nasu ta karanta, yadda tabbas zata san duniya ta san me take ciki, Allah yasa ka mu fi ƙarfin zukatan mu, inda muke kuskure Allah ka shiryar damu 🙏🏻😭😭
*ALLAH KA KAI HASKE DA RAHMA KABARIN MIJINA DA MIJIN AYSHAA, ALLAH KAYI WA RAYUWAR YARANMU ALBARKA, ALLAH YADDA KA NUNAWA AYSHAA AUREN ƳARTA CIKIN LUMANA NIMA KABAWA TAWA ƳAR AURE NA MUTUNCI NA ALKHAIRI, ALLAH KABAWA NUHU NA LAFIYA DA DUKKAN MAI CUTAR SICKLER DA ASTHMA, ALLAH KABAWA KO WACCE MACE DA TA RASA MIJINTA HAƘURI DA JURIYA* 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻😭😭😭😭 ******** INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY, IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA, TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI, BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY, DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA, MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN. DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR 08064586559 ******* Masu Buƙatar Siyan Atamfa ɗaiɗai ko sari a farashi na rangwame, da masu order na anko kama daga dangin atamfa zuwa laces da Adire, ku garzaya zuwa ga shafin Halima.hz Collection (gidan Atamfa) a instgram ko ku tuntuɓe su direct ta whatsapp 07018098175.