Kenza eBookz

Arman maleek book 1 complete - Chapter 13

Arman maleek book 1 complete - Chapter 13

Arman maleek book 1 complete Chapter 13: Arman maleek book 1 complete Chapter 13. Bugatti Veyran suka shiga tare da hakincewa a gidan baya, cikin natsuwa…

4,486 words

Bugatti Veyran suka shiga tare da hakincewa a gidan baya, cikin natsuwa driver dinsu ya fara tafiya, ita kuwa jinginar da kanta tayi a jikin ƙafadarshi ta fara zuba mishi surutu wanda shi bama ya biyata ita daya take.

cikin 15 minutes suka ƙaraso cikin Asibitin, bude musu moto aka yi suka fito a tare, shiga cikin Asibitin suka yi, Yan matan ranar ne Jere rairas suna fira, suna ganinshi suka miƙe jikinsu har yana wani irin rawa , suka fara gaisar da su, Sadiyyerh ce kawai ta ƙarɓa musu Amna gogan gaba yy abun shi, dan bai ma nuna Alamun cewar har an yi wata halitta a gurin ba.

Suna shiga cikin room din da sauri Sadiyyerh ta nufi gurin Sawwa da take kwance idanunta biyu sai kallom sama take tana dan wuntsila hannu, irin na Yara masu rangwamen lafiya, da sauri ta zauna kusa da Yarinyar tana murmushi , dagota gaba daya tayi ta daurata kan cinyarta tana shafa kanta da yake lunkif da gashi duk da wanda aka aske mata nata.

kamar wata Baƙuwar Halitta haka Sawwa take kallon Sadiyyerh, irin kallon nan na ƙurulla kallon da ake tantance kalar Abu, ita kuwa da sun haɗe ido sai ta sakar mata murmushi, saɓanin Yaah Shehi da suna haɗa ido zai lumshe idanunshi , cikin kula Sadiyyerh ta haɗa mata madarar da ake bata ta shiga bata tana sha tana kallonta har ta gama shanyewa tas.

kamar wata babba tana gama shanyewa tayi wani luuuuu da lulu eyes dinta ta rufe, hannunta ta daura kan sumar girarta wadda ta yanka sakamakon karfen da ya yanketa a gurin, ya raba sai dai har ma ya warke, a hankali ta shiga shafawa, kamar yadda taga Yaah Shehi nayi ko yaushe in ya zo ganinta, "kalli!", Sadiyerh ta fada taba kallon Yaah Shehi.

kyawawan idanunshi ya bude tare da watsasu kan fuskar Sawwa wadda take jikin Sadiyyerh, ga mamakinshi , yaga abun da take, a ranshi ya ayyana "Uhmm ko mai irin nawa ?", ya fada yana din taune lips , "tashi mu tafi ", ya fada yana yin hanyar waje, da sauri Sadiyyerh ta sanya Showel ta goye Sawwa a bayanta, roon din Abie ta samu Yaah Shehu, Sallana ta tarar yana mishi, itama yi mishi tayi kafin su fito tare [4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: BARKANMU DA SHAN RUWA YAN UWA! . FATAN KOWA YANA LPY ?, YA IBADA ?, TOM UBANGIJI ALLAH YA ƘARƁI IBADUNMU, ALLAH YA SANYAMU CIKIN BAYINSA WANDA ZAI ƳANTA A CIKIN WANNAN WATAN MAI ALBARKA.

*P. 28*

"Bayan wannan cutar tana da wasu daban-daban ya kamata a bata kula fiye da komai, gashi kuma naga Asthma dinta ta kara yin worse dole zata fara Amfani da Inhaler sa boda gudun matsala", ya fada yana rubutu akan wata farar takarda, numfashi Yaa Shehi ya sauke yana mai tsotsar Lips dinshi na ƙasa tare da zare Eyes Glasses din da yake idanunshi, bayan gama dan dogon rubutu da Dr yay ya miƙa mishi paper din, hannu Yaah Shehi ya sa ya ƙarɓi Takardar , musabaha suka yi da Dr din tare da mishi godiya ya fice.

in da aka kaita nan ya wuce, yana zuwa ya tarar da su Zayn a waje su ukku suna magana, Sauran kuma suna ciki, dan kallonsu yy, tare da miƙa musu paper din Magungunan kallon Zayn yy kafin chan ƙasan maƙoshi kamar wanda akai wa dolen magana yace "A siyo yanzu", yana faɗa ya shiga ciki, su ukkunsu suka fita domin siyowa, A zaune ya samesu duk sun yi jigum suna mamakin wannan abu da ya faru, daga gurin ƙofa ya tsaya,hannayenshi naɗe a kan kirjinshi yana kallon kowa da yake cikin ɗakin, a hankali ya sauke ganinshi kan Sawwa da take kwance,hannunta daure da drip, lokaci daya ta wani rame, jikinta yy fari sosai, dauke ganinshi yy a kanta kafin ya fice Abun shi, kai tsaye ya yi gida.

*BAYAN SATI DAYA*

Satin ta daya currr aka basu takardar Sallamarsu izuwa gida, in da Sadiyyerh ta ci gaba da kulawa da ita sosai, bata barinta ta taɓa ruwa sai da dalili, kullum tana cikin kayan sanyi lunkuf, har wani ƙiba tayi ta ƙara girma kasantuwarta na mai girman jiki, komai yi mata ake, shaƙuwa mai mugun tsanani ta ƙara shiga tsakaninsu.

A hankali take tafiya, cikin kayan sanyi masu masifar kauri pink ƙafarta da safa har da takalmi kanta ma sanye da hular sanyi pink , a hankali take tafiya sa boda bata son a ji ƙarar takun takalminta, palon Yaah Shehi ta shiga, jin palon tsittt bb ƙarar komai ko motsi yasa ƙara tabbacin baya gidan,cike da murna da kuma sauri ta yi gurin Fridge dinshi, da sauri ta bude Robar FanIce Vanilla ta fito da ita, da cokalinshi.

kan kujerar Yaah Shehi ta zauna ta lankwashe ƙafafunta, buɗe robar tayi a hankali, lumshe ido tayi tare da sakin tattausan murmushi abin da bata fiye yi ba, yatsarta ta fara sanyawa cikin ice cream din ta lakuta tare da sanyawa a bakinta, kaɗa kanta tayi, kafin ta sanya Cokalin ta fara sha a hankali cike da natsuwa.

Idon mutum taji yana yawo a kanta, bata ɗago ba dan tasan babu mai shigowa Ɗakim daga Yaah Shehi sai Ammynta , ita kuma barci take, Yaah Shehi kuma baya nan, hakan yasa ta ci gaba da hidimarta , jin dai idon ya yi yawa, yasa ta ɗago da idanunta a hankali, tare da haske direction din da ake kallonta da idanunta, mutuwar zaune tayi ta kasa ko da miƙewa daga in da take zaune, sai kawai ta zauna ta kame jikinta, fuskarta babu alamun fara'a gaba daya ta ɗinke, A hankali ta dauki murfin Ice Cream din ta rufe tare da ajiyewa akan stool din da yake gabanta, ƙara kallonshi tayi, ganin fuskarshi ta taka nata a haɗewa da ɗinkewa tasa ta miƙe a hankali, hanyar fita ta fara nema , duk yana tsaye yana kallonta, sai da ta kusa waje kafin ta tsinkayo muryarshi , "zo!", kawai ta ji ya ce,daskarewa tayi a inda take tsaye, idanunta ta lumshe. zuciyarta tana mata dukan tara-tara , ga wani tsimkewa da taji tana yi, ta kai 3 minutes a gurin kafin ta juyo a hankali ta faratakawa zuwa gareshi , sai da tazo gurin da yake kafin ta zube a ƙasa, a hankali kanta na ƙasa, yatsarta daya na kan lips dinta na ƙasa wanda ta tura cikin bakinta, take tsotsa a hankali, Azahiri Sam idanunta babu Alamar tsoro a cikinsu a baɗini kuwa mugun tsoro ya cika mata zuciya.

sai da ya mulu ya mulmule ya gama shan iskarshi kafin yace "me kika yi ?", shiru tayi ta kasa magana, dan bata ma san mai zata ce mishi ba, a hankali ta shiga wasa da hannayenta, maimaita abun da yace mata yay, still bata ce komai ba sai ta ci gaba da wasa da hannunta, "Sawwama!", ya faɗa rashin a dan ɓace, dan ya mugun tsanar yana magana ayi shiru a kyaleshi.

da sauri ta ɗago dara-daran idanunta farare ta zubasu cikin nashi, suna haɗa ido dashi ta sauke nata ƙasa. A hankali bakinta na dan rawa tace "Ayya SorryChubado(Zaɓaɓɓe) ", fa fada idanunta na yi narai-narai, lumshr idonshi yay, yarda ta kira sunsn zaka rantse cewar yarenta ne Fulatanci , Alhalin a Sama ta sameshi .

Shiru yay bai ce mata komai ba, kusan 3minutes kafinya yunƙura kunnenta ya riƙe da hannunshi, tare da dan riƙewa da sauri ta rumtse idanunta,kafin tace "Baaa fi! baa fi Chubado!", ta fada tana daura hannunta akan nashi, cikin cool voice ya furta "ba na hana ki ba ?", cuno bakinta tayi kamar za tayi kuka tace "Uhmmm Baa fi!", ta faɗa tana manna gefen fuskarta da hannunshi, a hankali ta zame kunnenta daga hannunshi, ta kifa kanta kan cinyarshi tana goga fuskarta , wadda zufa ya wanke tsabar zafin kama kunnenta da Shehi yay.

Mayar da idanunshi yy ya lumshe a hankali ya sanya hannunshi kan gemunshi ya dan shafa a hankali, bai fi 10 minutes ba aka turo ƙofar palon, Sadiyyerh ce ta shigo hannunta riƙe da wani babban tray wanda yake shirye da Wormans masu kyau da daukar ido, ga wani Jug mai kyau duk kala daya da Wormans din.

Murmushi ne ya kwace mata kafin ta shiga ciki da Sallama, chan ciki ya ƙarɓa mata Sallamar ba tare da ya bude idanunshi ba, sai da ta ajiye tray din hannunta kafin tace "like Father like Daughter! barci ake ?", ta faɗa tana ƙoƙarin zamo Sawwa da take jikinshu, wadda barci ya dade da yin gaba da ita, dauketa tayi ta mayar da ita chan wata kujera da take dan kusa da wadda Yaah Shehi yake zaune a kai, Hijab din jikinta ta cire, wanda gaba daya kayan jikinta wanda suka fitar da surar jikinta, wanda ta ƙara fitowa sosai, jibgegen Hips dinta wanda ya ƙara wani faɗi da tudu sosai ya bayyana, Na shanun nan kamar za su faso rigar da take jikinta su fito sosai.

ta gaban Shehi ta zo wucewa , hannunta ya kama tare da jawota, gaba daya tai baya , da sauri ta samawa kanta gurin zama kan cinyarshi daya, tare da harɗe ƙafarta, a hankali tace "na ji tsoro fa", ta faɗa tana cuno baki, bai ce mata komai ba haka itama bata ƙara cewa komai ba, sai da suka share tsawon mintuna , "Abin cin zai huce", ta fada tana yawo da hannunta akan fuskarsa, a hankali ya riƙe hannun nata da yake yawo a kan fuskarsa, kan lips dinshi ya daura hannun ya ɗan ciza, da sauri ta zame hannun tana yarfewa , ido cikin ido suka kalli juna, idanunta da sukayi narai-narai kamar za tayi kuka ta zuba mishi kafin tace "baa fi fa!'', lumshe idanunshi yy kafin ya ƙara waresu kan fuskarta.

Matsawa yy gurin carpet din da yake shimfiɗe tsakiyar palon in da nan ta ajiye tray din, zama yy tare da harɗe ƙafafunshi ya zubawa Hips dinta idanu, wanda take tafiya a hankali , suna wani motsawa kamar mai kaɗawa da gangan, lumshe idanunshi yy lokacin da ta rankwafo gabansa , kamshin turarenta mai dadi da sanyi tare da kwantar da hankali ya bugi hancinshi, har ta gama haɗa mishi Abin cin idanunshi a lumshe yana shaƙar kamshin.

bai bude idanunshi ba sai ji da yy tace "Haaa!"a hankali ya fara ware idanunshi, saitin lips dinshi ya ga ta matso da spoon, kallonta yy ya kuma kalli Spoon din da ta ciko da Dambun Shinkafa.

"Chubado!", ta furta tana mai nun Mishi spoon din da idanu, "Bissimillahi!", ya furta yana mai bude bakinshi, cikin natsuwa ta shiga bashi yana ci, yy loma biyu a ta ukku ya shaqe,a hankali ya fara dan tari, idanunshi suka yi jaaa,cikin ruɗewa,ta zuba Lumon Mangwaro da yy wani irin sanyi har raɓa yake jikinshi, matsawa tayi jikinshi tare da kafa mishi cup din a bakinshi, tana shafa mishi kirjinshi sai faman sannu take jera mishi, ƙwarewa ya ƙara yi da Lemun , ga ƙwarewq ga shaƙewa, ai tuni ya fita Hayyacinshi, cikin sauri ya zame Cup din da ta kafa mishi a bakinshi, ya shiga tarin sosai.

Jawota yy ya ƙanƙameta ya shiga tarin sosai, kamar wanda ranshi yake shirin barin gangar jikinshi, tarin da yake ne kuma yy sanadiyar farkawar Sawwa daga barcin da ya dauke a firgice , juyin da zata yi, ta faɗo daga kan kujera, tare da buga kanta a jikin ƙafar kujera, kuka ta fashe da shi a gigice, wanda yasa Shehi saurin ware idanunshi da suke jaajir har lokacin kuma bau dai na tarin da yake ba.

da sauri Sadiyyerh ta ɗagota tare da sanyata a jikinta, tana jijjigata ganin tarin Shehi ya dan yi sauƙi ba kamar da ba. hawaye ne a idanunta, kamar yarda Sawwa take kuka itama haka take yi.

duk ya dabarbarce , baya sob kukan mace a rayuwarsa, domin in yana jinsa yakan rasa natsuwarsa gaba daya, yana tadar mishi da hankali, ya rasa tunaninshi ma gaba daya, hakan na tuna mishi da shuɗaɗɗan tarihi na shekara da shekaru wanda in ya tunasa, yakan shiga wani hali, zuciyarsa dama kwakwalwasa tana dakatawa da aiki na wasu mintuna.

Numfashin Sawwa ne ya fara fusga sakamakon yarda take kukan da iyakacin karfinta da natsuwarta, ganin yarda numfashita yake wani shaƙa , yasa tayi saurin ɗagotw daga jikinta, tana kallonta jijjigata ta fara yi , tama busa mata iskar bakinta.

Jikin Shehi ta faɗa, tana miƙa mishi ita, da sauri ya tallafa hannayenshi duka biyun ta sanya mishi ita a hannayenta, ganin yarda take yasa hankalinshi ya dan tashi, da sauri yace "Inhaler! inhaler !! Inhaler!!! Sauri kan Bedside Drawer na ki dauko", ya fada yana jijjigata ganin yarda ta yi kamar wadda zata samu, da sauri tayi bedroom dinshi.

jijjigata ya shiga yi, ganin idan ya barta a halin da take kafin a kawo inhaler din zata iya suma, da sauri ya daura lips dinshi kan bakinta da ya bude ya fata busa mata iskar bakinshi a hankaki tana shiga cikin cikinta, kusan 2 minutes yana mata haka, numfashinta ta dam jaaa ciki, a hankali ya ware kyawawan idanunshi farare wanda golden ya zagaye blue din da yake ciki, sai ya zamana idon kamar yana ciwo.

ware idonshi yy akan fuskarta yana mata kallon da bai taɓa mata irinshi ba, tun daga kan goshinta da gashi ya kwanta luf-luf baƙi siɗik har izuwa, gashin girarta mai yawan gaske da ya kasance baƙi wanda har ya kusa haɗewa da juna gave din da yake tsakaninsu ba wani babba bane, har kan zara -zaran Eyes Lashes dinta baƙaƙe suma wanda suka kwanta , siririn karan hancinta wanda ya tafi da tsarin gaba daya hancinta ya fitar dashi yay kyau, zame fuskarshi yy daga tata, yana mai kallon lips dinta dama Sajen fuskarta da ya kwanta sosai .

dai-dai nan Sadiyyerh ta dawo riƙe da inhaler din, miƙa mishi tayi , ɗago Sawwa yy, tana mai dan marin kumatunta , cikim numfashinta da ba sosai yake fita ba ta ɓude idonta tare da kallonshi, inhaler Inhaler din ya sanya mata a baki, da sauri ya matsa mata, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke , a hankali suma duk suka saki sanyayyar Ajiyar zuciya.

"Alhamdulillah!", Sadiyyerh ta furta tana mai dan lumshe ido, Yaa Shehi kuwa bai ce komai ba, sai jingina da yy da kujerar bayanshi sai yanzu ya tuna da wata ƙwarewa da yay "Ana ta kai wa yake ta kaya!" ya furta a ranshi, sanyayyar Ajiyar zuciya ya saki, yana mai shafa tulin sumar kansa, da ta wani ƙara yawa ta kwanta mishi luf har gaban goshi ta wani zubo ,baƙa da ita gwanin kyau.

A hankali yake saukowa daga Upstairs Waya ce Maƙale a kunnansa, wanda rabin hankalinshi yana gurin wayar da yake, sanye yake da wani tattausan Yadin Voile Fari mai kyan gaske, tsabar taushinshi har ya bi jikinshi yy luf Voile din na da zanan Gold a jiki, wanda hakan ne ya bashi damar Sanya Milk Alƙyabba da ratsin gold a jikinta, ta wani yi kyau sai daukar ido take ga Rawaninshi da Hiraminshi tare da maka wuya, da ya sanya ƙafarsa tana cikin White Felipe milano Leather Slippers , sai wani irib daukar ido yake, tsintsiyar hannunshi na sanye da Agogob Rolex mai kyan gaske, sai baza kamshin turarensa na Huge Boss yake.

tun da ya fara saukowa daga kan Stairs Sadiyyerh ta waji zuba mishi idanunta masu kaifi sosai tana kallonsji, har ya ƙaraso gurinta, a hankali ta furta "Maa sha Allah, Fa tabaraqallahu Ahssanun Qaliqin!, Allah yay halitta a gurin nan, Yaah Shehi ka gode Allah!. dukkan wani abu da Bawa yake nema a gurin Allah!, Allah ya baka, kana da kyau, cikar zati, haiba, kamala da kwarjini, kana da kuɗi, ilimi both side Arabi da boko, Sarauta , da babban Ahli masu kaunarka." ta ƙarasa faɗa idanunta na tara kwalla.

Wayar da take kunnenshi ya cire dai-dai da ya zo gurinta, iskar bakinsa ya fesar, idanunshi a kanta yace,"Ooh See you! . ke mai kika rasa ? " ya fada cike da kamewa, "gaskiya na faɗa , Allah y baka Ahli babba mai Asali da tushe ga kaunar Yan uwanka da baka rasa ba , ka gode Allah", taɓe baki yay kafin yace "ke fa ?,kina da Mahaifiya!, miji! , Ƴa da soyayyarsu gaba daya,mai kika rasa kuma ?", ya fada yana kallonta.

"Uhmmm", ta faɗa ba tare da ta ƙara cewa komai ba, shima tsuke bakinshi yay ba tare da ya ƙara cewa da ita Uffan ba.

Sawwa da take zaune kan kujera hannunta riƙe da Chocolate da kuma cup cake , duk a hannunta ya kalla, tana sanye da wasu kalar kayan sanyi manya-manya masu bargo mai jikin mage, lingif suke, pink colour da su, sun yi kyau sosai kuma sun hau da jikinta, kamar Ƴar Turawa, hularta ta dan jaa baya sakamakon kusa rufe mata idon da tayi.

Sai safar ƙafa da take sanye da ita da wani fashion shoes , masu kyau da tudu. A hankali yace "kina koyawa Yarinyar nan shan zaƙi da yawa", cuno baku tayi gaba kafin tace "aa fa kwara daya ne!", ta fada tana ƙoƙarin gyara mishi zaren Alƙyabbarsa.

tabe baki yay kafin yace "Uhmmm"hannunsa ya daura kan waist nata, tare da yin dan sama da ita, yarda tsawonta zai yi dai-dai da nasa, kasantuwar ya fita tsawo sosai , dan ba zata wuce kafadarsa ba.

"Yarinya ki ringa cin taliya ko kya samu ki ƙara tsawo", ya fada yana jaaan dogon hancinta, dan murmushi yay, ita kuwa taɓe bski tayi kafin tace "Arɗo!" shiru yay mata bai Amsa ba, "Shehi!", shima yay shiru, "Chubado!!!!!!!", ta fada cikin sigar shagwaɓa , tana kwaɓe fuska.

lumshe idonshi yat kafin yace "mene!", kallon kasan ido ta mishi kafin tace "kana jina dama ..!", taɓe bakinshi yay, kafin yace "barci nake . baki ga Alama ba ?", karkata kai tayi kafin tace "Uhmmmm!".

kai tsaye waje yay bayan ta gama gyara mishi zaren Alƙyabbar."come on Bongel am , kar Chubado yat jiranmu", ta faɗa tana miƙa mata hannu, sai da ta kalleta na tsawon minutes kafin ta miƙe zuwa gareta, kama hannunta tayi suka yi waje,kafin su fita Yaah Shehi har ya kame cikin mota, idanunshi sanye da wani siririn farin glasses mai kyau sa ya ƙara fitar da sahihin kyanshi.

Sawwa ta faea zama kusa da shi kafin Sadiyyerh ta shiga, zaune yake da laptop akan cinyarsa yana latsawa. phone din Sadiyyerh ta fita, ta fara lallatsawa , ita kuwa Sadiyyerh titi ta zubawa ido, har suka bar cikin gidan kai tsaye titin Gombe suka hau. tafiya suke cikin nishaɗi da jin dadi duk da ba wani fira suke ba, kowa da abun da yake , Shehi na lura da yarda Sawwa take shige da fice cikin wayar ta Sadiyyerh,mamakibya mugun kamashi, in da ya ga tana shiga shi kanshi bai san gurin ba, amma sai shige shige take.

Garin Gombe!.

gari mai tarin Albarkarai , da ni'imomi kama daga kan Noma .Kiwo kasuwanci da sauransu. suna da Qabilu , sai dai Qabilar Fulanu sun fi yawa, daga su sai Hausawa, kafin kuma duk sauran Qabilu su ka biyo baya, ba wani babbsn gari bane sai Abubuwan Albarka na ban mamaki.

kusan yinu suka yi zungur dan tun 9am suka fito sune sai guraren 4pm suka shiga cikin garin Gombe, har Sallah a hanya suka yi, don Yaa Shehi baya kaunar jinkirta Allah saboda halin rayuwa.

Lokacin sa suka shiga cikin Masarautar. gaba daya garin Yay wani irin duhu aai iska ce take kaɗawa da ƙarfi , Alamar gab ake da tsugewa da ruwan sama sosai............ [4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 27*

Hannunta na cikin nashi tana goye da Sawwa suka fito daga cikin Hospital din, Motarsu suka shiga, Driver ya jaasu, Direct wani haɗaɗɗan guri mai masifar ƙayatarwa, wanda ya fi kama da gurin hutawa , sai dai gurin a mugun tsaro yake, sojoji Yan sanda, ko wane kalar Kaki na Ƙasar an zubasu a gurin,ga kuma wasu Yan Ubansun Motoci kala-kala wanda suka fi na Yaah Shehi Haɗuwa ma da wanda basu kai su ba.

A tare aka bude musu Mota suka fito, yana gaba ita tama baya , a hankali suke tafiya, itama kanta a ƙasa, wannan ƙaron har da Niƙaf dinta wanda ya ɓoye mata gaba daya fuskarta har idanunta, sai dai wani dan shararan guri take gani, hannunta ƙafarta jikinta, gaba daya yana lulluɓe dan Alƙyabbarta ma tayi bala'in mata yawa har jaan ƙasa take mata, ɗazun da suka je Asibiti sai dai dan ɗagata sama tayi, yanzu kuwa babu dama.

tun daga nesa , muka rinƙa jiyo wata zazzaƙa ɗaɗɗadar murya mai masifar dadi da sanyi tare da garɗi tana raira karatun Al-qur'ani mai girma,a cikin suratul Nisa'i , a hankali Sadiyyerh ta shiga lumshe ido karatun na ratsa mata gaba daya sassan jikinta, wani mugun shauƙi take ji, har suka ƙarasa gurin bata ɗago da kanta ba.

Cikin natsuwa da Kamala suka shiga keta taron mutanan da suke gurin suna shiga ciki, ba mutane bane sosai, bai fi mutum 50 ma maza da mata,sai dai da Alama gaba daya gurin Mata da Miji ne, bb Saurayi ko Budurwa, babu yawan Yara sai wanda suke shaan Maama , hakan yasa gurin bb hayaniya,domin duk wanda yake gurin ya mallaki hankalin kanshi, kuma sub san mai suke sun san Azabar wanda ake karatun Al-qur'ani yana magana, shu yasa gurin yg wani mugun silent bb mgn ko kaɗan ko tari bb, hakan yasa gaba daya karatun yale Amsa kuwwa a kafatanin gurin.

Gaba suka zauna, in da suna Zama Aka miƙawa Sadiyyerh Lund speaker, shiru ta ɗan yi, tana kallon gefe, tana kuma kallon Yaah Shehi da Ƙasan ido, ganin shima ya zuba mata idanunshi yasa ta ƙarɓa, da Bissimillah ta fara, kafin ta fara ƙaratunta cikin Suratul Ankhabut gaba daya gyara zamansu suka yi, suna ƙara jaddadda godiyarsu ga Allah, bb ma kamar Yaah Shehi da yaji karatun nata na Yau ya fi na ko yaushe dadi, ta sakin jikinta tana fidda dukkan wasu haƙoƙƙin haruffa da kalmomi,cikin taushin murya take karatun har ta idar, daga nan kuma Haleesa Aliyu Haydar Aliyu ce ta daura akan nata karatun.

bayan gamawa, aka daura da walima mai kayatarwa wadda Sarkin garin Makkah ne da kansa, ya shirya Walimar,bayan an gama ya bawa Yaah Shehi babbar kyauta, haka suka tattara guraren 5pm suka wuce gida.

A mugun gajiye suka shigo gidan, bb kowa a palo, hakan yasa suka yi sama, kowa ɗakinshi ya wuce cike da ɗinbin gajiya,bama kamar Sadiyyerh da take ta rugumniya da Sawwa da take ta barcinta abinta, zare Alƙyabbar jikinta tayi, tana mai fiffita da hannu sa boda zafin da take ji ga kuma zufa da take.

Gefe ta ajiye Alƙyabbar, tare da ƙoƙarin kwance goyon da yake bayanta,cikin gajiyawa ta sauketa, tana kallonta, ajiyeta tayi kan bed, tare da yunƙurawa zata miƙe , tarrr Sawwa ta bude idanunta wanda suka kasance manya-manya , har wani madara-madara cikin idon yake sa boda tsabar fari, fa kwanciyar wani mai-mai, kwayar idanunta ta kasance golden colour , wanda wani dan blue yy mishi da'ira, ya zagaye gaba daya Golden colour din.

hannu Sadiyyerh ta kai a wuyanta, tare da yin magana a hankali, kofar bedroom din ta sanyawa key kafin ta wuce ta shiga bathroom in da ta bar Sawwa ita ƙadai a zaune, bata jima ba sosai ta fito tana daure da towel jikinta sai ɗigar da ruwa yake, Sawwa da take in da ta ajiyeta ta kalla.

bata ko matsa daga in da ta ajiyeta ba, tana zaune ta haɗa hannayenta, sai bin ɗakin da kallo take, sai kace mai nazarin wani abu, Wuce wa gaban Mirror Sadiyyerh tayi ta shiga mulke gaba daya fatar jikinta da mayuka masu taushi da kamshi, sai da ta gama, ta sanya wasu Ɗamammun riga da wando wandon irin crazy din nan ya ɗameta sosai rigar ma top ce sun bala'in mata kyau, wata blue black din hula mai dan gashi gashi ta sanya, sai ta sanya fashion na ƴan kunnaye blue suma, sai ta dan murza white lips a bakinta.

daukar Sawwa tayi ta nufi Bathroom da ita, bata jima ba suka dawo hannunta riƙe da na Sawwa da take tafiya kamar tana tsoron taka ƙasa, tana daure da Dan towel ƙarami pink, jikinta nata turiri da kamshi shower gel , kan Stool din Mirror ta ajiyeta, ta dan shafa mata mai da turare kaɗan, ta mata sample kwalliya a fuskarta, sai dai Yarinyar tayi wani Ɗan jarababbiyar kyau da har sai da ta firgita, duk kyan da ake cewa tana dashi yarinyar ta takata kyau, bada ban kar tayi ƙarya ba da zata iya cewa ta ma fi Yaah Shehi kyau, sa boda kasancewarta na Ƴa mace, ga kwalliya da sauransu, ɗirarrar Yarinya ce da tun tana ƙarama kana kallon tsarin zubin Halittar da Allah yy mata, sai ka kara jadadda godiya gareshi, kana kallonta zaka san ta girma ba ƙaramin rush za'ayi a kanta ba.

komai nata jif-jif, kama daga kan yana yin tsarin halittarta, ita ba doguwa ba ba kuma gajera ba, fara tarr da ita, fari irin na Larabawa , mai sirki da na Turawa, tana da lallausan Baƙin gashin kai, mai yawan gaske da har bayanta ya sauko, tana da matsakaiciyar fuska, mai dauke da gashin gira mai yawan gaske, dara-daran idanu, zara-zaran eyes lashes , siririn hanci wanda ya kasance har baka, dan ƙarakin baki mai dauke da pink lips dai-dai sai dan kaurin da suke da shi ƙadan.

Cikin kaya irin nata sak ta shiryata, har takalmi iri daya haka ta sanya mata, Hijab ta zura mata ta dauki wayarta suka fito daga bedroom din.

Bedroom din Yaah Shehi suka fara shiga, suna shiga suka sameshi zaune yana aiki a laptop, da sauri Sadiyyerh ta cire hijab dinta ta ajiye a kan kujerar da take gefenshi, shigewa jikinshi tayi ta kwantar da kanta kan kirjinshi.

Miƙawa Sawwa hannu tayi kafin tace "Come My Dolly", ta fada tana ware mata hannu, a hankali ta fada jikinta, tare da kwantar da kanta itama kamar yarda ta kwanta kan jikin Yaah Shehi.

Firar Gurin taron Ɗazun Sadiyyerh ta shiga yiwa Yaah Shehi da son dauke hankalinshi daga aikin da yake, sai dai baya wani biye mata dan Amsa ma a gajarce yake bata ita.

gajiya yy da surutunta, kallonta yy kafin yace "Sadeey!", kallonshi tayi, "tashi ku koma palon ƙasa",tura baki tayi kafin tace "korar mu kake ?", kai tsaye ya gyaɗa mata kanshi, fushi tayi ta kams hannun Sawwa suka fice Abin su, sauke ajiyar zuciya yy kafin yace, "hakan shine ya fi min", ya fada yana mayar da kanshi kan aikinshi.

Duk a zaune suka tarar da su, su Amah na ganin Sawwa suka nufeta, cike da murna, kama hannunta suka yi izuwa gurin wasansu, bin su kawai take komai sai dai ta kalla suna yi, amma ita bata iya ba,ko magana bata iya ba sai dai gwaranci.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull