Kenza eBookz

Arman maleek book 1 complete - Chapter 14

Arman maleek book 1 complete - Chapter 14

Arman maleek book 1 complete Chapter 14: Arman maleek book 1 complete Chapter 14. duk da zamanta cikin Yara da yarda suke jaanta, amma bata ko dariya ,sai…

4,439 words

duk da zamanta cikin Yara da yarda suke jaanta, amma bata ko dariya ,sai in ta ƙure tayi murmushi.

Zama Sadiyyerh tayi kusa da Anty Rayhana da take shan Damammiyar Jalal Alawa da Madarar Peck tayi, "Anty Dan bani nasha Wallahi yunwa nake ji, yau yini nayi ban ci Abin ci ba", " baki ci Abin ci ba kuma ?, to ni dai sanin da nayi taron da kuka je Akwai Abin ci sai dai in kece baki ci ba", taɓe bakinta tayi kafin tace ", Ayya abubuwansu basu min ba".

"kin dai bawa Ƴar Abin ci ko?", dafe kai ta yi kafin tace "na manta itama bata ci ba", ta fada tana miƙewa da sauri, dariya Anty Rayhana tayi kafin tace "kun ji aikin hankali, Yanzu Ƴar taki ki manta da baki bata Abin ci ba ??, Lallai Sadiyyerh akwai gyara", ta fada tana kallon Yaran da suke wasa.

sai da ta haɗa mata komai akan tray ƙara mi, kafin ta fara kiran sunanta "Sawwa! Sawwa!! Sawwa!!! Sawwama!!!", ta fada tana zuba Drinks a cup.

cikin natsuwa ta ɗago luɗu Eyes dinta ta zuba in da take jin ana kiran sunan, dan izuwa yanzu ta san sunan ko na waye, "Came!", ta fada tana yafi tota.

gurinta ta nufa a hankali, tana tafiya tana lumshe ido,har ta ƙarasa gurinta, daukarta tayi ta daurata kan kujera tare da cewa "Say Bissimillahir rahmanur rahim!",ta fada tana kallonta, shiru tayi, sai da Sadiyyerh ta ƙalleta ta kara mai-maitaww kafin a hankali kuma a rarraɓe magana mai kama da ta mai in-ina tace "Bis..bi...Bissimillahi!", abun da taxe kenan ta tsuke bakinta, a hankali ta fara ɗibar abin cin,cikin natsuwa tace "Open your Mouth", bb musu ta bude bakinta in da Kyawawan haƙoranta farare tarrr wanda suke dauke da Teeth gave babba, suka bayyana .

Fara bata Abin cin tayi,duk in zata bata sai ta mata umarni da ta bude bakinta, har suka gama, suka dawo palon suna fira ita kuma tana gurin Yara.

A sati na biyu da yin Sallah gaba daya suka tattare suka taho Ƙasa Nigeria,a babban filin jirgin garin Abuja suka sauka, wato International Airport, kai tsaye Babban gidan Yaah Shehi da yake garin suka nufa, dan dama duk zuwa Nigeria ta nan yake sauka,sai ya huta na 2 days kafin ta wuce Masarautarsu.

Yaf-yaf haka ruwan sama yake sauka a garin, gashi ya wani lullume, yy duhu alamar hadari ne sosai a garin.

suna shigowa cikin gidan bayan sun zazzauna a palo , aka kece da ruwan sama mai ƙarfi sosai, gaba daya Sawwa sai ta fara jinta cikin wani yana yi na shauƙi, Yarinyar da bata cika walwala ciki mutane ba, amma ta fara doka murmushi, kamar mai.

wanda hakan yake nuni da cewa taba masifar son ruwan, kuma da dukkan alamu kamar Akwai wani abu da take gani a duk lokacin da ruwa yake sauka dan zata je ta ringa ƙoƙarin shiga ruwa sai Sadiyyerh ta dauketa.

bayan kowa ya natsu a palo, suna Addu'ar saukar ruwa, ita kuma ta sulale bb wanda ya ga lokacin da ta fice waje, tana fita ba tare da tunanin komai ba ta shige cikin ruwan tana dan jujjuyawa ciki.

ruwan ne ya duketa sosai, wanda ya haddasa mata shiga wata rayuwar ta daban, lokaci daya ta ji ƙafafinta na wani irin kwankwatsa, zamewa ta fara yi zata koma cikin palon, amma ina ƙafa ta riƙe, zubewa a gurin tayi, dan danan sai ga zazzaki mai zafin gaske, sai fisge-fisge, cikin abibaɗan da ba zasu wuce 10 ba ta fita hayyacinta,ko magaba bata iyawa, bata iya miƙewa ko rarrafe.

Miƙewa Sadiyyerh tayi zata haye sama, fara duddubata tayi, bata ganta cikin Yara ba, da sauri tace "Ina Dolly ?", gaba daya hankullansu ya dawo gareta, kowa yace bai ganta ba bb kuma wanda ya ga in da tayi.

kai tsaye tayi waje dan tasan zata aikata shiga ruwa, tana fita ta hangeta kwance ƙasa, da gudunta ta ƙarasa gareta, cikin hamzari, ta fara jijjigata tana mai kiran sunanta, da shiga Palon gaba daya, gaba dayansu suka yo kanta, hankali tashe ganin Yarda ta riƙota kamar marar rai.

jijjigata suka hau yi gaba daya, ai tuni su Amah suka ruɗe, a ruɗe Amatul-Azez ta wuce sama, tana kwaɗawa Yaah Shehu kira, "Uncle! Uncle!! Uncle!!!!", ta ƙarasa faɗa da karfi, dai dai ya fito daga wanka yana sanye da Ash din Jallabiya, yana tsaye gabcn mirror yana tsane kanshi da towel ta banko ƙofar Bedroom din.

jiyowa y yana kallonta, ganin yarda take kuka, tana kuma nufasa, yasa ya dakata da abun da yake yi, "Uncle Sawwa ce , gata chan ", ta faɗa tana nuna baya,yana yin yarda Yarinyar take kuka da shiɗewa ne yasa ya fahimci ba lafiya, da sauri ya zari key ya fito yana riƙe da hannunta.

tun kafin ya ƙara so palon ya gane Asalin abun da yake faruwa, cikin sauri ya ƙarasa gurin, yana zuwa yy sama da ita, ba tare da ya tsaya ba yy waje, duk mara mishi baya suka yi, Amma kafin su ƙaraso gurinshi, tuni ya jaa mota da kanshi yy waje.duk shishiga suka yi tare da mara mishi baya.

gudu yake tsulawa kan titin ta yarda yay musu rata, suka kasa cin masa, sai dai suka bi bayanshi, kai tsaye Asibitin da aka fara treating dinta nan ya nufa da ita,Cikin Sa'a kuma ya tarar da Wannan Dr din dai ne, cikin hanzari ya ƙarɓeta ya shiga da ita ciki .

bayan hour 1 Dr ya fara fitowa daga cikin room din da aka shiga da ita, bayan fitowarshi Nurses suka fara tururuwan fitowa suma.

Yaah Shehi da yake zaune a kan wata farar kujera da take ajiye a gaban room din ya miƙe, yaba kallon Dr din, hannu ya bashi suka yi musabaha, kafin yace "muje Office", kallon su Ayyana yy kafin su wuce ciki.

Zama kan kujerar da take kallon ta Dr yy,ya naɗe ƙafarshi daya kan daya, yana dan kallon Dr din, numfashi ya fesar kafin yace "me yasa aka barta ta shiga cikin ruww bayan an sa irin Abubuwan da suke tare da ita, yanzu gashi Ammonia dinta ta tashi sosai , ya kamata a ringa kulawaa da ita sosai, duk da dai nasan kasan komai game da cutar amma gaskiya sai an ƙara kula sosai, dan wannan cutar tana da haɗari sosai a game da lafiyarta, musamman ma ita da take Yarinya Under age, gashi kuma bayan wannan cutar tana da wasu daban-daban h....... [4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: SAI HKR DON WLH ZAKU GA TYPING ERROR DA YAWA, DAN BAN SAMU NAYI EDITING BA, YAU KUMA NAJI INA SON YIN TYPING NE KAWAI, SHI YASA NACE BARI MUDAN RAGE HANTSI DAN NASAN YANZU KUWA NA NAN YANA BIN INUWA😂

*P. 29*.

Da Bissimillah Shehi ya zura ƙafarshi daya waje, ta dan jima a haka kafin ya zaro dayar da gan-gan jikinsa gaba daya , rufe motar yay tare da bata baya, a hankali ya fesar da wani narkakken numfashu, a hankali ya furta "Alhamdulillah Yaa Allah! Alhamdulillah!", ya faɗa yana mai lumshe idanunshi, kusan two minutes suna haka kafin ya waresu Chan sama, ya jima yana kallon guri daya kafin ya dauke idanunshi daga kallon gurin, Sadiyyerh da Sawwa tuni sun wuce ciki, ya yin da shi kuma ya nufi Masallaci, dan lokacin Sallah ya gabato sosai , yaba zuwa ya tarar da ruwa ajuye cikij wata galleliyar buta fara tarr ko zane babu a jikin buta, gefe ya matsa ya zauna da bissimillah! a bakinsa ya jaawo butar ya fara Alwalarsa kamar yarda shari'a ta tanadar.

har ya gama tama zaune daga gefe cikin wasu kayan fulani na saƙa, farare tarr masu masifar daukar ido, fara ce tar in da farinta har wani rawaya-rawaya take, tana da dogon gashin kai wanda aka mata kalar kitson Fulani da yake kwantowa har gaban goshi, gashi nan baƙi siɗik , sai sheƙi yake , tana gashin gira sosai, da manyan idanu farare masu masifar daukar ido. tana da dogon hanci mai kyau wanda tsarinsa ta dace da fuskarta, tana da ƙara min baki sosai, idanunta na kan Shehi har yay Alawar ya gama, tana zaune gefensa, shi kam abun da yake gabansa yake da dan sauri-sauri kuma cikin natsuwa kasantuwar yarda iska take kaɗawa kamar zata tafi da mutum, yana idarwa ya miƙe yay cikin Masallacin da sassarfa, yana zuwa gaba daya kowa ya matsa ya bashi guri ya shiga gaba.

cikim golden Voice dinshi ya tada Sallah, tare da fara rairo karatun Al-qur'ani mai girma a cikin Suratul Tahreem! , ƙuwwa da ihu tare da sowa ne ya fara fitowa daga sassan masarautar, ya yin da rugugin Hadari da ihun ya ƙara daukar cikin Masarautar har wani girgiza-girgiza take, lokacin da za'a tafi Sujjadar farko a lokacin ne kuma aka tsinke da wani kalar ruwan sama,mai masifar karfi da ƙara,wanda ya shafe tarihin gaba daya wasu koke - koke da iface-ifacen da ake yi cikin Masarautar bayan gama Sallah Asr din , ya gyara zamansa yana mai tasfihi ga Ubangiji Talikai , idanunshi lumshe ya jingina da bango , kai kace barci yake, Alhalin idanunshi biyu, shiru kawai yay yana saurarar ruwan da take sauka mai karfi da ƙara, An shafe 1 hour ana wannan ruwan kafin ya dan fara tsagaitawa,lokacin kuma ne ya fara tunanin Sawwah dan yasan in ba wani iko na Lillahi ba to tana chan ciki ruwa, duk kuwa da tasan Lalurarta amma ita dai tana kaunar ruwa, wanda har ya rasa gane wacce irin soyayya ce tsakaninta da ruwa, anan ne ra'ayinsu ya mugun banbanta, dan shi mutum ne mai kyankyami da rashin son ruwa, baya son ruwan sama ya taɓa jikinshi sam .

sai Bayan Magrib kafin ruwan ta tsagaita, amma duk da haka garin bai daine walƙiya ba, bai kuma daina cidaba ba da rugugi, bai fita ba yana nan har bayan Isha' kafin ya fito a hankali yana fesar da sanyayiyyar iska daga bakinsa, yana tafiya yana dan lumshe ido, gajiya ce a jikinshi ga wata ja'irar Yunwa da take damunsa dan rabonsa da Abin ci tun daren jiya, dan ko da safe bai ci komai ba.

A sanyaye cikin siririyar murya Yay Sallama cikin palonshi, Sawwa da take tsaye gurin kujera tana zazzare ido tayi karfin halin karɓa masa Sallamar gaba daya jikinta na dan cira alamar sanyi ya fara ratsa bargon jikinta, yana yin yarda tayi magana kawai da sanyin da muryarta tayi, ta tabbatar mishi da ta shiga cikin ruwan, kuma da Alama sai da ta faki ido kafin ta shiga dan babu kowa cikin palon, jinjina kanshi ya dan yi, yana mamakin wace iriyar Yarinya ce da bata jin magana, sam bata jin maganarsa in zai sa doka so dubu zata karya , ya hanata shiga ruwa ba daya ba, ba biyu ba amma taƙi dainawa.

Haka kawai Zuciyarsa ta raya masa, ya dan barta yau da halinta taji yarda ciwon jikinta yake sosai, in taji taji yarda abun yake may be ba zata kara bari ruwa ya tareta a wani gu ba balle ta shiga ciki, anan cikin palon ya barta ya hayewarsa sama dan dama bai ko kalleta ba , tun bayan shigowarsa.

zamewa tayi in da take tsaye ta zauna tana jin ƙafufunta na mata wani mugun kwankwatsa, ƙafafunta ta riƙe da hannayenta gaba daya naman jikinta na wata iriyar rawa na ban mamaki. kamar saukar Aradu haka ciwon ya mamaye jikinta gaba daya yana wata kwankwatsa da cira kamar zai zazzalo ƙasa, a hankali hawaye suka shiga silalo kata akan kumatunta, gashi ita dai irin Silent killer din nan ce, ko abu zai kasheta ba zata yi magana mai karfi ba, miskilancinta da izzarta abun mamaki ne sosai, dan irinyarda take tafiyar da lamurranta sai du'a.

ta dade sosai a gurin tana cikin mawuyacin hali, hawaye nata silali mata daga cikin idanunta. A hankali yake saukowa daga kan upstair yana sanye da Jallabiya Ash colour da tayi masifar hawa da fatar jikinta, ta mishi kyau sosai, gashin kanshi ya sauko har gaban goshinshi, cikin sanyin hali yake tafiya, ga jikinshi da yake fitar da wani sihirtaccen kamshi mai sanyaya zuciya, ƙafarsa sanye da slippers mai kyau da taushi.

idanunshi a kanta ya fara saukowa daga saman, yana dan jijjiga kanshi, har ya sauko, numfarfashi yaji tana fitarwa masu kama da dafarar mutuwa, hakan yasa da dan sassarfa ya nufo gurinta, yana zuwa ya ɗagota da hannayensa, tare da saɓeta akan kafaɗarsa, bai ko tsaya ba yay sama, da ita. Yana zuwa bedroom dinsa Bathroom ya shiga, kai tsaye ya shamfiɗeta cikin zazzafan ruwan da ya sarki masu zafi sosai.

numfashi ta dan jaa a wahalce, tana mai lumshe idanunta, ta jima sosai cikin ruwan kafin ta fara jin jikinta yana dan saki, hannayenta da suka lallakwashe suka sassaki, ba tare da damuwar komai ba, ya fitar da ita a ruwan ya cire mata kayan jikinta da suka jiƙe, ya sake haɗa wani ruwan ya wanke mata jikinta sosai ya ƙara gasata, kafin ya fito da ita, sauri-sauri ya shiryata cikin wasu fararen kayan sanyi masu kauri sosai ,har da safar ƙafa da hannu ya sanya mata, sai da ya gama, kafin ya nufi fridge dinshi, sachets din magunguna ya fitar da wata allura da ruwa mai dan rangwamen sanyi, tun da ya fito da Magungunan da Allurar Zuciyarta ke ɗatace, tayi kicin-kicin da fuskarta, yarda kasan an aiko mata da sakon mutuwa.

takowa ya shiga yi gurinta, kallo daya ta mishi ta dauke kanta daga kallonsa, wani gamsasshen murmushi yay ta gefe daya, wanda yay sanadiyar lomawar Beautiful point dinsa, ganin kamar zata juyo yasa yay saurin mayar da fuskarsa yarda take yama ƙara haɗeta , cikin natsuwa ya fara ɓallar magungunan har ya ɓaɓɓali wanda zata sha, sun kai guda goma Cikin glass cup ya tsiyaya ruwa mai rangwamen sanyi, ya miƙa mata , juyowa tayi ta kallesa kamar za tayi kuka, dauke kanta tayi, "riƙe!", ya furta yana ƙara miƙa mata, sulalewa tayi ta kwanta kan bed dinsa, kafin a hankali ta furta "Ci Abin ci"dan kallon inda take ya yi, kafin ya ajiye Komai kan stool .fita yay daga bedroom din, bai dade ba ya dawo hannunshi dauke da dan madaidaicin Plate.

jaan stool din yay ya kwashe komai , ya ajiye gefe ya zauna, ajiye plate din yay a ƙasa kafin yace "tashi!", a hankali ta miƙe tana kallonsa, nuna mata Abin cin yay yace "Ci . kizo ki sha" ya fada yana daukar laptop dinshi, wadda take charge a gefe, operating dinta yay, ya fara dan dudduba wasu abubuwa da suka shafi aikinshi. A hankali ta shiga cin Abin cin kamar mai cin magani, tana ci tana gyangyaɗi , wanda ita ta ƙirƙirarwa kanta barcin duk dan kar ya mata Allurar ya kuma bata magani, dan sam bata so.

bai Ankare ba sai da ya gama abun da yake kusan 10pm yana juyowa yaga har ta gyara kwanciyarta a inda ta kwanta tana barcinta cikin kwanciyar hankali, girgiza kanshi ya yi, Allurar ɗazun ya mayar cikin fridge ya fito da wata daga cikin wani dan kwali, tayi sanyi sosai , haɗata ya yi, ya zuƙa a Syringing , dagota yay, tare da zame Wandon kayan jikinta , da *"BISSIMILLAH"* ya daura tsinin Allurar a jikinta, ya tsira mata, a firgice ta farka , tare da sanya kuka, sai da ya juye mata gaba daya ruwan Syringing kafin ya zarw mata Allurar a hankali, yana zamewa ya mayar da hannunshi kan gurin da ya mata Allurar ya shiga murza mata gurin a hankali, yana jin yarda kukan nata yake ratsa gaba daya kunnuwanshi.

cikin gajiyawa da kukan da take, ya saukota daga kan kafadarsa, yana kallonta, idanunta na lumshe , amma a haka take yin kukan , ga hawaye nata zuba, a hankali ya sanya tafin hannunshi mai laushi da tsantsi ya shiga goge mata hawayen idanun nata,a hankali ta shiga jaan ajiyar zuciya,har ta tsaya da kukan nata sai dai ajiyar zuciya.

zameta yay ya ajiyeta gefe daya, bathroom ya nufa, bai jima sosai ba ya fito yana goge gashin kanshi da yake linkif da ruwa, a hankali ya zame ƙaramin towel din da ya sanya a fuskarsa wanda yake goge ruwa,in da yake jin motsi yabi da idanu, zaune ta ganta tsakiyar bed dinshi, ta nannaɗe ƙafafunta, ta bowl a hannunta, tana shan kankana da madarar da ta haɗa, tana yi tana kallon laptop dinshi da ta sanya cartoon ,murmushi ne kan fuskarta. ƙarar bude bathroom din da taji, ne yasa ta dago idanunta, ido biyu tayi da Yaah Shehi, da sauri ta sauke kanta ƙasa tana sanyayyan murmushi .

taɓe bakinshi ya dan yi,ƙafin ya wuce gaban mirror yana ci gaba da goge kansa, Abun busar da gashi ya jona , ya fara busar da gashin kansa, sai da ya gama tsaf kafin ya mulke gashin kan nasa da mayuka kala-kala masu ƙara taushi da ƙamshin gashi, lotion dinshi ya shafa, kafin ya bi da turarenshi na Huge Boss, wani ɗan ƙofa ya bude ya shiga, bai jima sosai ba ya dawo da wani kayan barci farare masu taushi da santsi sun mugun lafewa a jikinsa, zagayowa yay ta gurin da take zaune, laptop din gabanta ya dauke tare da kallonta da lumsassun idanunsa, A hankali yace "baki gaji ba ?", ƙifta ido ta dan yi, kafin ta gyara Zamanta kan bed din da take zaune, tana mai wasa da hannayenta tace "a'a!", watsa hannayensa yay alamar bai damu ba.

Kai tsaye ya wuce gurin Ibadarsa, tankwashe ƙafafu yay , tare da daukar Al-qur'ani mai girma ya fara raira ƙaratun Al-qur'ani mai girma , da muryarsa mai dadin sauraro. Gyara kwanciya Sadiyyerh tayi tana mai sauraron karatun nashi wanda kai tsaye yake huda dukkan wata ƙafa ta jikinta yana shiga, ji take kamar a kanta ake karatun , hakan ne yasa ta lumshe idanunta tana mai sauraronsa. har bata san lokacin da barci ya dauketa ba, sai guraren 2am kafin ya tashi daga gurin da yake zaune bayan ya yi.

Addu'o'i sosai, idanunshi ya kai in da ya kwantar da Sawwa da take barcinta hankali kwance sai fitar da sassayan numfashi mai cike da zalar ciwon da yake nuƙurƙusar gabbanta take,miƙewa yay, bai tsaya ba sai wuce in da take, hannayensa biyu yasa ya dauketa. A hankali ya bude ƙofar da zata sadashi da palonshi, durum palon yake babu yawaitar haske kasantuwar gaba daya na'urorin cikin palon a kashe suke, ta tsakiyar kujerun da suke zube a palon ya bi, tare da ƙarasawa wani ƙofa da yake kallon ƙofar bedroom dinshi, buɗe ƙofar yay ya shiga, kamar dai palon shima ɗakin bashi da yawaitar haske sosai amma akwai blue light , wanda ya dan haska ɗakin.

ta cikin wannan ɗan hasken da Ya rage cikin ɗakin na shiga ƙarewa Ɗakin kallo, babban ɗakine sosai, mai dauke da royal bed, wardrobe daga bango har bango, side drower mirror , stool da dai sauran kayan karikitai, wasu manya manyan Elagement ne na pics din wata ƙyaƙyawar Yarinya ,mai kyan gaske kamar Aljana, tana cikin wani ɗan gadon Yara hannunta a bakinta, alamun tana tsotsa, tana sanye da light blue din kayan sanyi na Yara masu kyau, hatta da showel dinta ma light blue ne. dayan Elagement din kuwa, tana cikin showel ne a lokacin ba zata wuce 2 months ba, gashi ne linkif a kanta, ta kanannaɗe fuskarta da hannayenta,wanda yasa ba'a iya ganin komai na fuskarta daga lips dinta sai siririn karan hancin kawai ake iya gani.

Sauran pics din kuma a mabanbantan gurare aka mata shi, wasu a park wasu a garden , wasu a mall -mall wasu super market duk dai pics din babu wanda Yarinyar tayi sama da 3 years , kuma daga yarda aka zazzagaye pics din da kalolin fure da abubuwa zaka gane kaunar Yarinyar ga mamallakin ɗakin, a hankali ya ƙarasa gefen bed din da yake lulluɓe da light blue din bedsheet ya kwantar da ita, Addu'o'i ya shiga mata sai da ya gama kafin ya jaa mata duvet ya rufeta , manysn labulayen ɗakin ya gyara mata,ya ƙara gyara mata windoors , ajiyar zuciya ya ji ta jaaa. idanunshi da suke a narke ya daga tare da ɗan kallonta na seconds kafin ya fice yana , fesar da sanyayan numfashi.kulle mata bedroom din yay tare da wucewa nasa.

yana tura ƙofar bedroom din ya hangi Sadiyya zaune ta tankwashe ƙafafunta hannayenta akan cikinta tana dan yatsina fuskarta. jin ƙarar bude kofa yasa ta dan dago tare da zuba mishi idanunta, haɗa idanu suka yi, cikin gaggawa ta zare idanunta daga cikin nasa. cikin bedroom din ya shiga takawa, yana sob iso bed din, zama yay gefen bed din yana mai nazartar yana yin da take ciki don kallo daya yay mata ya gane akwai abun da yake damunta.

Kan bed din ya hau dakyau tare da nannaɗe ƙafafunsa yana mai binta da kallo. jaawota yay kusa da shi tare da kama kafaɗunta yasata yarda zata fuskancesa, haɓɓarta ya dago don ta kallesa, amma sai ta sun kuyar da kanta, domin matsawar ta kalleshi to fa sai idanunta sun fallasa masa Abun da ke damun zuciyarta har ma da gangar jikinta.

numfashi ya fesar, tare da kishingiɗa daga zaunan da yake, ya lumshe idanunshi, ba tare da ya kulata ba, ganin ya basar ne yasa itama.........

Isanatu tace a muku Addu'a😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂 [4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 30*

Ta kwantar da kanta akan kirjinshi, cikin hikima ta zura hannunta cikin rigar jikinshi tare da murza kwantaccan gashin kirjinshi da yake fitar da wani sihirtaccan kamshi mai mugun sanyi da kwantar da hankali, kafaɗunta ya dago tare da tsurawa fuskarta da tayi wani jaa lokaci daya ido, cikin hikima da baiwar da Allah ya masa yake nazartar ta, cikin sa'a ya samu nasar sanya ƙwayar idanunshi cikin natajuya narkakkun idanunshi yay cikin nata, kai tsaye ta gane Abun da yake nufi na tambayarta" ya ya dai!", kwaɓe fuskarta tayi tare da manna fuskarta da faffaɗan kirjinshi wanda ya bayyana sakamakon bottom din rigar da ya dan zare, gaba daya hannayensa ya nutsa cikin tufkakkiyar sumar kanta da take fitar da wani sihirtaccen kamshi, sai sheƙi take, a hankali ya shiga zaro hannunshi wanda hakan yay sanadiyar warwarewar tufkar gashin da tayi, zare hannunshi yay dai-dai da warwarewar gashin nata ya bazu har kam fuskartagaba daya gashin ya bazu ya rufe mata fuskarta.

yatsunshi yasa ya shiga tattare gashin da ya rufe mata fuskarta, tsam ya rugunmeta a jikinshi, yana shaƙar kamshin jikinta mai dadi da kwantar da hankali. ɗagowa tayi gaba dayanta ta afka jikinsa, kumatunshi ya tallafe tare da karkatar mishi da kanshi kamar yarda tayi, ba zato yaji ta manna lips dinta kan nashi tare da ziro harshenta tana lasar lips dinshi, a hankali ya lumshe idanunshi, tare da sake mata ragamar rayuwarsa gaba daya, ita kuwa cikin tsantsar buƙatuwa ta ci gaba da bidasa.

kusan 10 minutes tana sarrafa mishi jikinshi,kallonta kawai yake , ganin duk jikinta yay sanyi ne yasa ya saki wani ja'irin murmushi, baya yay da ita tare da binta ya fara sarrafata , cikin salon burgewa da kwantar mata da hankali, har sai da ya tabbatar mata da samun natsuwa kafin , yay wata iriyar Ajiyar zuciya mai tattare da jaan numfashi mai ƙarfi.

numfashi ta shiga saukewa,tare da jaaan bargo ta rufe jikinta da shi, shi kuwa mikewa yay ya shiga bathroom domin tsarkake jikinsa, bayan ya fito ya umarce da itama ta je ta tsarkake jikin nata, kafin ma ya gama shiryawa wasu daga cikin masallatan cikin gari an fara kiraye-kirayen Sallah Asuba, hakan yasa cikin sauri-sauri ya gama shirinshi cikin wata farar jallabiya ya daura Alƙyabbar da ta zamana kamar Ibada sanyata, turare ya faffesawa jikinshi, tare da zura slipper dinshi yay waje da sauri, don lokaci ya yi mugun tafiya

sosai.Sannu! Sannu.....!

haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin dadi da ba dadi ba, lokaci ya tafi sosai rayuwa tana gudu sosai, in da abubuwa suka shuɗe da dama.

Cikin Ikon Allah kuma Sadiyya ta ƙara samun wani cikin, wanda yake mugun wahal da ita, bata ko iya magana bata cin Abin ci, bata iya aikatawa kanta komai, sai kwanciya. kamar kullum Yau ma kwance take, tayi ruf da ciki, tunanuka ne birjik a ranta, wanda har bata ji shigowar Yaaah Shehi ba da yake bakin ƙofa ya naɗe hannayensa yana kallon yarda wasu hawaye suke zubo mata. a hankali ya taka ya shiga cikin bedroom din , har ya zauna a gefen bed dinta bata sani ba.

hannayensa yasa ya jawota gareshi, tare da daura kanta akan cinyoyinsa, sai a lokacin ta ji shigowarsa, nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke, tare da kara ƙanƙame hannunshi da ya raɓa a gefen wuyanta, cikin sarƙaƙƙa murya yace "Kuka! kuka!! kukan dai har yanzu!..?", ya fada yana mai zuba mata idanu, kafin tai magana Sawwa ta shigo cikin ɗakin, cikin shigar riga da wando masu kyau da suka dan kamata, an mata kalaba ƙanana ta zubota kan ta babu ko dan kwali, tayi wani kalar girma sosai in ka kalleta zaka yi zaton ta kai 10 years ma, gefenshi ta zauna tare da daura kanta akan kafaɗarsa ya zamana Sadiyya ta daura kanta a cinyarsa ita kuma ta daura a ƙafaɗarsa, a hankali tace "Abie wai Ammyna mutuwa za tayi ?", jim ya dan yi kafin yace "waya faɗa miki ?", jiki a mugun mace tace "kullum tana faɗa min wai rayuwarta ba mai tsayi bace ta kusa ta tafi ta bar mu", ta faɗa kwalla na cika mata idanunta, riƙe hannuta Sadiyya tayi, kafin tai magana Shehi yace "aa wasa take miki" ya faɗa yana dan mayar da idanunshi kan Sadiyya, kallonshi ta dan yi kafin tace "Uhmmm a jikina fa nake jin hakan, ina jin rayuwata ta kusa zuwa ƙarshe , mutuwa zan yi !", ta faɗa tana dan murmushi tare da shafa cikinta da ya fito sosai , a ido ma kawai ka kallesa kasan zai iya yin 8 months dan yay girma sosai har ya fara sauko mata. "tana kan kowa", ya faɗa cikin dan rashin damuwa, murmushin da ya bayyana kyawawan haƙoranta wanda kamar an ƙara musu fari tayi tare da cewa "ba zaka gane hakan ba sai bana nan, fata na dai ka riƙemin Amanata , ka bata kulawar da ni ban samu ba a gurinka, ka tarairayeta, Amanarmu ce", gashin girar shi ya dan shafa kafin yace "ki tafi da ita kawai man", ya faɗa cikin dan gatsali, murmushin takaici tayi dan gaba daya sam ta lura bai fahimci mai take ji bane, kuka Sawwa ta sanya tana cewa "bana so ki tafi! Abieh ka faɗa mata man" , ta faɗa tana girgiza mishi hannunshi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull