Kenza eBookz

Arman maleek book 1 complete - Chapter 18

Arman maleek book 1 complete - Chapter 18

Arman maleek book 1 complete Chapter 18: Arman maleek book 1 complete Chapter 18. a hankali ya ci gaba da wawware idanunsa yana kallon cikin gurin,…

4,487 words

a hankali ya ci gaba da wawware idanunsa yana kallon cikin gurin, idanunshi ya ƙurawa Zayn da yake gaban wata tamfatsetsiyar baƙar mota ,suna fitowa , wasu tsala-tsalan motoci biyar suka shigo gurin, baƙaƙe biyu a gaba biyu baya, sai farar mota ƙirar Benz a tsakiya , sai walwali motocin suke, har gabansu suka tsaya, cikin sauri aka buɗe musu motar da take tsakiya, ita ce ta fara shiga sai shi, rufe motar aka yi driver ya jaaa, a tsare motocin suke tafiya, kan lafiyayyan titin ƙasar , babu cikowar wucewar motoci sosai. , nasu na gaba ta Zayn na baya, shima drivet ne yake jaansa cike da natsuwa , a haka suka shiga wata katafariyar Anguwa mai kyau da tsari, titin Anguwar ma kansa abub kallo ne, don gaba daya gefe-da gefen titin flowers ne masu kyau a jere, an wani irin yalwata gurin dasu, Anguwar tayi kyau sosai, gashi ko ina a kulle, babu kuma yawaitar mutane masu wucewa a gurin.

tunda suka shiga wani layi da yafi ko wane layi da suke cikin Anguwar, suka rage speed din motocin , suka koma tafiya slowly, har suka ƙarasa kofar wani gida na Alfarma , horn aka yi, a take get man din gidan ya bude ƙofa ya leqo ganin masu gurin ne, yasa da saurinsa ya bude musu ƙofar, da gudu motocin suka sulala cikin farfajiyar gidan mai girman gaske.

sai da suka ƙarasa babban parking space din cikin gidan kafin suka yi parking, da sauri aka bude musu motar, kasantuwae akwai gajiya a tattare da su yasa basu tsaya wata-wata ba suka fito daga cikin motar cike da muguwar gajiya suna fesar da numfashi, gaba Shehi yay ita kuma tana biye da shi, kafin Zayn ya ƙaraso tuni sun shige ciki, har Upstaira suka hau, nuna mata wani bedroom da yake kusa da wanda ya shiga ya yi, shigewa tayi da sauri, don tun tashinta yau bata jin dadi ga kuma alamar zuwan baƙonta da take ji, gashi kuma ma taji kamar zubowarsa, da saurinta ta shiga bathroom din da yake cikin bedroom din, sauri sauri ta cire kayan jikinta, gabanta ne ya faɗi "Subhanallahi!" ta furta lokacin da idanunta suka hasko mata , period dinta da ya zubo a pant dinta.

cikin rashin karfin jiki da kalasa, ta fara wanke fatar jikinta tana sakin sanyayiyyar iska daga bakinta, sauri-sauri ta gama wankan ta daura babban towel ta fito, da gudunta ta nufi Bedroom dinsa, tun daga ƙofa ta fara kwala masa kira "ABIEH! Abieh!! Abieh!!!", ta ƙwala kiran da ƙarfi lokacin da ta shiga bedroom dinsa, a tsaye ta samesa gaban mirror yana taje sumar ƙansa , a baƙin ƙofar ɗakin ta tsaya, ta cikin mirror ya hango yarda ta wani yi rau da idanunta, juyawa yay gaba daya ya kalleta, alama ya yi mata da me ne ne ?, hawayen cikin idanunta ne suka zo, lips dinsa ya dan tsotsa a hankali yana kallon fuskarta da ta koma wani iri .

"Abieh wlh kuwa ni bana son Abun nan, kawai a ɗinke min gurim yinsa na huta", ta fada tana turo baki, dan ware idanunsa yay, alamar da hankslinki kuwa, chan ciki ya furta "Chappp!", " kullum in yazo cikin fargaba da ciwo nake, yanzu haka jin marata nake kamar zan mutu", ta fada tana dafe cikinta, "Zo!" ya furta chan ciki.

A hankali ta fara takawa gurinsa, tana zuwa ya ware mata hannayensa, shigewa tayi cikin jikinsa ta rumtse hannayenta , sanyayyan numfashi ya fesar, tare da dan lumshe idanunshi, turo ƙofar da yaji ne yasa yay saurin saketa tare da mayar da ita bayansa ta yarda ba'a iya hangota.

Zayn ne ya turo ƙofar bedroom din ya shigo, daga chan baƙin ƙofa yace "Hamma bari na dan fita", jinjina kansa yay alamar to, ficewa yay, sai da yw fita ya matsa daga gabanta yana fesar da iska, a hankali ta furta "Abieh da buƙatar na gyara jikina", ta fada tana kallon ƙafafunta , miƙewa yay ya jura Alkyabbarsa cikin natsuwa ya furta "ki jirani anan", ya fada yana ficewa.gefen bed dinsa ta zauna.

bai jima sosai ya ba ya dawo, hannunsa riƙe da manyan ledoji guda biyu, saman carpet da yake gwfen gado ya ajiye ledojin, da sauri ta matsa gurinsu dan ta matsu ta gyara jikinta, ledar farkon ta fara dubawa, ta ko yi sa'a pad din Besense Sanitary pads , mai guda 30 - 30 guda ukku ne, sai set din pants masu jikin net, kala-kala masu kyau , da tsada, da sauri ta zari dai-daya ta shige bathroom din da sauri .

sai da ta ƙara gyara jikinta kafin ta shirya cikin wata Abaya mai masifar kyau da ya siya mata, tsaf ta fito cikin kayan, sai dan ramewar da tayi , tana fitowa tace "Abieh yunwa", harararta ya dan yi kafin tace "ai gani. sai ki cinye ni", ya fada yana dan danna ƙaramar wayarsa, "A...." bai bari ta ƙarasa ba ya nuna mata dayar ledar da ya shigo da ita, da sauri ta nufi ledar,budewa tayi, kamshin lafiyyan Abin ci ne ya bugi hancinta, lumshe idanunta tayi tare da furta "Yummy!", da sauri tayi bissimillah ta fara cin Abin cin cikin natsuwa, yarda take tauna Abin cin ma kansa abun kallo ne, komai cikin natsuwa take yinsa, tana yi tana lumshe idanunta, ta ƙasan idanunsa yake kallonta, bata ci da wani yawa ba ta tsame hannunta tare da furta "Alhamdulillah!", kallon Take away din Abincin yay ya kuma kallonta, a yatsine yace "mai kike nufi ?", langwaɓar da kanta ta dan yi ta dan yi luuuu da idanunta, cikin natsuwa da muryar shagwaɓa ta furta "na ƙoshi", ta fada tana dan lasar lips dinta da harahenta, da sauri ya dauke idanunshi daga kallonta, numfashi ya fesar, da sauri ta je jikinsa ta zauna, da sauri ya ware idanunsa, zameta yay daga jikinsa,cikin dan ruɗu yace "mai yasa bakya jin kunyar hawa jikina ne ? ke baki san kin girma bane ?", ya fada yana haɗe ƙafafunsa tare da baza, Jallabiyar jikinsa, ta bude sosai cuno baki tayi gaba cikin sakalcin da shi daya take iya yiwa, maganar ma bata damu da yi da kowa ba, amma a gabansa Zabiya take komawa , "ni kam ban girma ba, ko yaushe a gabanka Ƴar Jaririya nake jina, kuma nasan ba zan taɓa girma ba, ba kuma zan ji kunyar hawa jikinka ba ko a gaban wa", jijjiga kansa yay cike da tarin mamakin Yarinyar, chan ciki Ya furta "Allah y shirya!", da sauri tace , "Ameeen", gyara zamansa ya ƙara yi yana duba litattafin Hisnul muslum, da yake hannunsa.

Kwance yake kan Gado idanunsaca lumshe, bakinsa bai gusa da Ambaton sunan Allah ba, ɗira ƙafarta tayi cikin shagwaɓa tace "Abieh ina zan yi barci ?", bayanshi ya nuna mata, ba tayi tunanin komai ba, ta afka kansa, tare da kwanciya luf a bayansa, "Yaaah Ilahi! Yaah Allahu!! , Yaaa Ar-rahman raheemin!", ya furta lokacin da yaji saukar ta akan jikinsa, jikinsa na wani irin rawa, ya zameta daga jikinsa, da sauri ya yi waje, miƙewa tayi tana kallon bayansa da ya shige, watsa hannayenta tayi.

Bedroom din da ya nuna mata ya shiga, bai tsaya ciki ba, bathroom ya shige cikin mugun kiɗima, kanshi ya sakarwa ruwa, lumshe idanunshi yay yana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya, masu zafin gaske, "Wayyo Allah!", ya furta chan ciki, yana mai sanya hannayensa cikin sumar kansa ya bazata, ta zubo har bayansa gaba daya ta liƙe masa a bayansa da gaban goshinsa, yana haɗa hanya ya fito daga bathroom din, bed ya faɗa, cikin minutes din da basu shige biyar ba wani zazzafan zazzafi mai masifar zafi ya rufesa, abu kamar wasa ƙaramin Alamari ya fara zama gaske.

A hankali ya fito daga bedroom din da ya kwana, yana tafiya yana baza Alƙyabbar jikinsa, kamar mai san ɓoye wani abu, idanunshi da suke muci-muci ya ware sosai, lokacin da ya fara buga ƙofar Bedroom din da take, chan ciki ta furta "Abieeeeeeeh!", ta furta chan ƙasa cike da mawuyacin hali, da sauri ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, ɗurkushe ya ganta gaban bed, tayi amai duk ta ɓata jikinta, gaba daya jikinta babu ƙarfi, da sauri ya ɗurkusa gabanta, faɗawa jikinsa tayi, wasu hawaye na zubo mata, jijjigata ya fara yi yana dan dukan bayanta a hankali jin tana ƙara yin kakarin Amai, hannunta ta riƙe, muryarta na shaƙewa ta furta "KIRJINA ABIEH zan mutu , K........ [4/29, 12:32 AM] salmeertsanisalman: *P. 35*

"Kirjina Abieh , wayyo zan mutu!", ta fada idanunta nayin kamar zata suma da sauri ya dagata daga inda take ya yi bathroom da ita, cikin jacuzzi ya sanyata, da sauri ya sakar mata ruwa mai sanyi ganin tana niyyar Sumar masa , doguwar ajiyar zuciya ta sauke , a hankali numfashita ya shiga dawowa jikinta, ƙarfaffan numfashi ya jaaa , kafin ya furta "Alhamdulillahi!", shi ya shiga taimaka mata har ta gyara jikinta, kasantuwar rashin ƙarfin jiki da take fama da shi, jingina ta ya yi da ƙafadarsa suka fito,lokacin da suka fito lokaci ya riga da ya ƙure,cikin hanzari ya shiryata, hijab ya sa mata, ya shiga gaba ta ba bayansa kaɗan, hala suka yi Sallar kamar zata faɗi, hijab ya sa mata, ya shiga gaba ta ba bayansa kaɗan, hala suka yi Sallar kamar zata faɗi, suna idarwa ta kwanta a gurin, da sauri ya jawota jikinsa, zafi sosai yaji jikinta.

*Washe gari*

Washe gari bayan an idar da sallan asuba ya had'a mata tea mai kauri ya bata tasha, bata jima ba kuwa bacci mai nauyi ya dauketa......

Ba ita ta farka ba sai wuraren goma na safe, wanka tayi ta shirya cikin simple abaya Wanda ya amshi D'an madaidaicin jikin ta, ya kuma yi mata kyau, babu komai a fuskarta sai gloss din data shafa wanda ya bawa lips din ta daman shining, hakan ko yasa fuskarta fitowa d'ass da ita, ta fito asalin fresher (waye ga JJC) direct school sukayi bayan ta d'an tab'a break-fast......

Basu samu wani tangard'a ba, ya gama mata komai saboda sanenne ne, hakan yasa basu bata lokaci ba, don har café sukaje suka biya na biya sukayi printing ma printing daga nan kuwa sukayi gida.......

***

D'agowa tayi ta bude idanun ta da suke lumshe tun dazu akan Zaid, Wanda lokaci daya ta fara masa kallon mai juyeyyen tunani ko kuma dai kawai ta ce Mara hankali, don yafi dacewa da hakan.

Cikin nutsuwar da Allah ya mata Wanda lokaci d'aya ya nemi gushewa saboda mamaki da kuma al'ajabin da maganganun Zaid suka haifar mata a lokaci guda ta ce.

"Amma dai kana cikin hankalin ka ba wai ka tabu bane? To kai ina ka taba jin ance maka akwai aure tsanani na da kai? Kana kanin mahafina? Kace kana so na? Uhmmmm lallai kam amma sai wallahi sai na gayawa Abieh, daga haka ta mike tayi cikin daki ba tare da ta amsa ko da kira d'aya cikin wadanda yake kwala mata ba, don ita Jin abun take Kaman mafarki, wai kanin mahafin ta ne zaice yana sonta so irin na aure,? ai gwara Abie yazo ta fad'a masa yasan me zai masa ko Dawanau ta kama ai sai a kaishi don wannan ba lafiya ba, da wannan tunanin ta tattara zancen ta wartsar tayi shirin baccinta......

Har ta kwanta, taji abun ya tsunkeleta, kwata tayi cikin jaan tsaki tace "Lallai ma Uncle Zayn din nan. ~SO~ , Aure Uhmmm", ta faɗa tana juya kwanciyarta , amma gaba daya abun duniya ya addabawa rayuwarta , da ta juya sai ta ji maganarsa tana mata Amsa quwwa, ta jima bata yi barci ba, sai da kyar ta samu ya dauketa.

Dadewar da tayi bata yi barci bane kuma ya haddasa mata, rashin tashi da wuri, wanda yasa Shehi yin tunanin ko ciwonta ne ya kuma tashi, cikin saurinsa ya tura ƙofar bedroom din, da sauri ya komaya juya bayansa, ya zamana bayanshi na kallon cikin ɗakin gabanshi kuma na kallon ƙofa, "Hasbunallahu wani'imal wakeen!"ya furta yana mai lumshe dukka idanunsa, cikin dan ruɗu, da sauri ya buɗe ƙofar ya fice, itama A diririce ta faɗa Bathroom don duk abun ta ɓata taɓa bari ya ganta a yarda ya ganta yanzu ba, "innalillahi!", ta furta tana mai sawa ƙofar lock ...

kasa fitowa tayi daga cikin bathroom din, ta kusa 1 hour , kafin ta fito duk a ɗarare, sauri-sauri ta shirya, tunani take ta yi,ya ganta a yarda take ko kuwa dai hasashe ne take da ya ganta, tunda dai ko idanunsa bai ɗago ba ya juya bayansa, in kuwa ya ganta da kunya mai zai yi tunani kenan ?, tayi sakacin da Mahaifinta har yaga surar jikinta a yana yin da bai kamata ba ko kuwa ?, tunane-tunane ta shiga yi, har da ta barsa akan bai ganta ba, nan take ta bar abun a inda ya faru, jin cikinta na kira mata ciroma ne, yasa ta fita palo, tana tafiya tana tattare gashin kanta da ya bazo mata, numfashi take fesar wa a hankali, tana shaƙar daddar iskar hadarin garin da ta haɗu da sanyin AC da aka kurewa gudi cikin palon ya dauki wani irin ɗari na musamman mai haɗe da kamshin turare mai dadin gaske, kanta a ƙasa har ta zauna kan kujerar dining, komai yana a shirye, duk kuwa da cewa babu mata a gidan, amma komai tsaf , kuloli kuwa sun fi biyar, da flask da abubuwa komai na shirye tsaf-tsaf gurin ,sai kamshi girki.

Cup ta dauka, ruwan zafi mai haɗe da kayan kamshi sai tashi yake ta zuba , wanda ta zuba bai fi rabin cup din ba, ta ajiye, madara ta bude da sugar da millo, zubawa ta shiga yi, bayan ta gama ta motsa , wata Ƙaramar kula ta dauka, budewa tayi, kyakyawan farfesun kayan ciki ne ya bayyana, yatsina fuska tayi, tare da rufewa ta matsar da kular gefe, wata ta ƙara budewa, farin mulmulallan tuwan danyar shinkafa ne , ya bayyana ya samu tuƙi mai kyau, an mulmulesa a leda, daya ta dauka, ta sanya akan plate din da yake gabanta, wata kula ta bude , haɗaɗɗiyar Miyar Egusi ce ta bayyana, ta sha Ogun da ganda ga kifi zuƙul-zukul , tayi wani irin kyau , ga mai ya kwanta a sama gwanin burgewa, tuni miyanta ya tsinke, serving Spoon ta sanya ta zuba miyar.

A hankali ta shiga cin Abin cin kanta a ƙasa, amma a jikinta take jin an tsaya mata a ka kuma ana kallonta, tun tana jin idanun basa damunta har ta fara jin idanun suna mata yawa a jikinta,cikin natsuwa ta dago ds kanta ta kalki direction din da take jin ana kallonta, tsaye ta gansa cikin shigar suits , ya kame ya yi wani irin kyau , sai kamshin Black Oud yake, cikin kamewa ya shiga takowa, fuskarsa a haɗe, alamar babu wasa, kallo daya ta masa ta dauke kanta, tare da ci gaba da cin Abin cinta cikin natsuwa kamar yarda ta fara.

ya Zauna a kujerar da take kallon nata, amma bata dago ba, cikin kamewa, ya fesar da iska daga cikin bakinsa, kana kallon idanunsa kasan bai samu isassan barci ba, ga kuma alamar kuka duk sun kumbura sun yi jaa. kamar ba zai yi magana ba yace "jiya ina kiranki kika share ni ko ?", ya fada yana murza zoɓan Zinarin hannunsa.

Jiimmm ta dan yi, kafin ta cire spoon din da yake hannunta, ta dan kallesa, kamar yarda ya kame fuskarsa itama sai ta kame tata, cikin iya sarrafa harshe da salon magana, wadda zan iya cewa gadonta tayi, tace "Ayya Uncle Zayn, naga kamar baka cikin hayyacinka ne shi isa na baka guri ka dan dawo dai-dai", ta faɗa tana kurɓan tea din da yake gabanta, kafin ya ƙara yin wata magana ta tashi ta shige ciki.

Da Misalin karfe 11pm taji wayarta na ring, daga ring din da taji kawai ta gane mai kiran, cikin sauri ta dauki wayar, cikin shagwaɓa ta furta "Chuɓaɗo!', cikin dan gajiyawa, yace "ki shirya 11:30 kina da Lecture , zan tura miki sauran bayanan ta Gmail yanzu", yana faɗa ya kashe wayarsa, cike da murna ta miƙe ta faɗa banɗaki domin sake yin wanka, tana fitowa ta bude Gmail dinta , ai kuwa saƙonsa ya baɗo cikin wayar, da sauri ta fita tana ƙara duba abun da ya turo mata, sauri-sauri ta fito daga cikin palon gidan ta nufi parking space in da Driver yake jiranta, tana shiga ya jaata zuwa School din, tun da suka shiga farfajiyar makarantar take ƙarewa makaranta kallo, ciƙe da shauƙi, don zaƙuwa, suna zuwa tsakiyar makaranta tawa driver Umarni da ya sauketa, Umarninta yabi ya tsaya, fitowa tayi cikin shigarta ta yau da kullum dogon wando ta sanya, Royal Purple ya sha yanka (crazy) sai farar T-Shirt , sai kuma ta daura baƙar Falmara wadda ta zo mata har kusan guiwa, wani kyakyawan takalmi Royal Purple Benigna Paten Tuscany Leather da yay wa ƙafarta cif-cif gwanin kyau , ga wani ɗan Ubansu Legs Chain da tasa na zinari a ƙafarta daya.

ga wani mayen glasses No Respect da ta sha, gaba daya gashin kanta ya sha gyara da kalolin mayuka masu kyau, an yi oiling din ƙasan , yay wani macaroni-Macaroni gwanin kyau, daga chan sama kuma an yi fixing dinshi ya kwanta har gaban goshinta, siririn mayafine fari a kanta, sai Agogon Rolex na mata, mai kyau cif da tsintsiyar hannunta, sai zaɓɓan Zinarai masu kyan gaske, kyakyawar hand bag dinta, ya ƙarama tana maƙale a hannunta, sai kuma wayarta da take dayan hannunta. sanyayyiyar iska take shaƙa mai wadda tayi mata dadi sosai.

tafiya ta fara cikin natsuwa, gaba daya idanun Yan makarantar ne ya dawo kanta, da ace yau ta fara fitowa cikin mutane, ko yau ta fara shiga cikinsu, da zata mugun firgita da yanayin kallon da ake mata, kai in ma aka yi rashin sa'a da mace ce mai tsoro sai ta ringa jin fargaba ko ma ta ringa harɗewa, amma ita tsaf take takunta kamar yarda ta faro daga gida.

Tana tafiya tana duddubawa har taga Department dinsu, har cikin class dinsu ta shiga, sai dai babu kowa, dan zama tayi ko zata ga wani yazo, ta bisa izuwa Theater din da zasu yi Practical din da suke dashi amma shiru, har 12 tayi, ganin haka yasa ta fito tayi tana dube-dube amma bata ga Theater din ba, wasu Mutane biyu ta tare, da sauri suka daddare don dayawansu tunani suke ko Aljana ce don kyanta har ya zarta inda ake tunani, sam wani lokacin sai ka dauka ba mutum bace musamman in tana yin wasu abubuwan.

don kanta ta gaji da yawon da take ta zauna, a mugun gajiye, wayarta ta fitar daga cikin jakarta, kira ta danna masa amma tana ring bai dauka ba, sai da tayi masa kira biyu bai dauka ba, Innalillahi! kamar za tayi kuka ga yunwa da ta fara ƙwaƙular mata hanjin cikinta, tana cikin tunanin abun yi, taji kiransa cikin wayarta, da sauri ta dauka, tana kara wayar a kunnanta ta sakar masa kuka, numfashi ya fesar daga chan ɓangaren.

"Wayyo Allah na Chuɓaɗo!, gantalewa ta gama samuna ni kam", ta fada hawaye na zubo mata, "lafiya ?", cikin shagwaɓa tace, "uhmm uhmmm to ba na kasa gane Theater din ba, gashi kuma na kasa samun wanda zai kai mi, kowa ma tsorona yake", dan murmushi ya saki, don yasan za'a rina tunda Driver yaga ya masa yarda abun ya kasance .

"Me ?", "Abieh Wlh kazo ka dauke ni," ta faɗa tana ƙara sakin kuka, "Okay¡ okay! gani nan", ya fada yana kashe wayar, anan ta ci gaba da zama har ya ƙira wayar.... 07033371851

END OF BOOK 2

*P. 36*

"Abieh!", ta faɗa a gajarce a kuma gajiye, numfashi ya fesar kafin yace "ga ni!" yana faɗar haka ya kashe wayar, da sauribta dauki Hand Bag dinta da mayafinta da ya zame tayi waje, chan ta hango motarsa nesa kaɗan da class nasu, da sauri ta ƙarasa motar dan babu abun da take so yanzu sama da ta ganta gida ko jikin Abienta, kafin ta ƙarasa ma ya bude mata gaban motar, hakan yasa ta gane shi da kansa yazo daukarta ba Drivet bane, tana zuwa ta shige, motar yawa key suka bar cikin makarantar, idanunta na kansa, kamar bata taɓa ganinsa ba, don ya mugun mata kyau, yana sanye da shigarmu ta gargajiya, shadda Gizner fara ƙar sai daukar ido take, da hularsa Zanna , da ta zauna ras a kansa, sajansa da gemunsa sai ƙyalli suke, fuskarsa tayi wani fayau gwanin kyau, ga Tabon Sallarsa ya ƙara wani baƙi sai sheƙi yake abun da ya ƙara fito da fuskar tasa kenan, ya gyara gemunsa ya zubo har kusan kirjinsa sai kyallin yake yana saukar idanu, kasa dauke idanunta tayi daga kallonsa don ya mugun mata kyau, ji take kamar ta dauwama tana kallon kyakyawar fuskarsa, wani shauƙi na musamman yana mamaye jikinta da zuciyarta, ji take wani abu mai kama da mashi kamar yana sukar ƙahon zuciyarta, ji take ta tsani wata mace wadda ba ita ba ta raɓesa, wani yana yi na daban take ji game da shi, wanda yasa idanunta suka tara wani hawaye na musamman wanda shi bai zubi ba kuma shi ga shinan ya tsaya cikin idanunta kamar zai zubo, hakan yasa idanunta wani narai-narai , ga wani sheƙi da blue din ciki yake, farin kuwa har wani madara-madara yake tsabar kyan da suka yi"Ƴar Abieh!", ya fada a hankali, idanunshi na kan titi "Abieh!", ta furta itama har lokacin idanunta na kansa, "Wannan kallon fa ?", lumshe idanunta tayi ta bude a kansa cikin tsananin shauƙi da shaƙuwar da take tsakaninsu tace "Youlook so Good , cikin wannan kayan", ta fada tana manna hannunta da sajen fuskarsa, lumshe idanunsa ya dan yi kafin ya budesu, still akan titi yace "Uhmmm!"."kasan me ?", ta fada tana daura hannunta akan hannunsa da yake kan wani dan tudun abu mai kama da pilow da yake gefen site dinshi, "Uhmmm sai kin faɗa!" jim ta dan yi kafin tace "kana kyau a cikin kayan Malam Bahaushe".taɓe baki ya dan yi kafin yace "ke ma da zaki sa zasu miki kyau", tura bakinta tayi tana cewa "ni kam sam basa min kyau bana son su", ta fada tana sarƙe hannunta da nasa, "kin kuwa kusa dai na sa wannan ɗin don sam bana son su, kawai sa boda ban son ranki ya ɓaci shi yasa ba bari kike sawa, amma Soon zaki dai na", ya fada yana tsotsar lips dinsa, "Abieh dai", dan kallonta yay, kafin yace "Chuɓaɗo dai", dan murmushi tayi kafin tace "bana son kayan nan, nafi sakewa a cikin wannan idan nasa wannan ina ji na a taƙure, infact ina ji kamar ba irin Asalin suturata ba kenan" taɓe baki ya ƙara yi kafin yace "Shaiɗanci dai" "Abieh Shaiɗanci kuma", ta fada tana kallonsa, "Eyyi Man in ba shaiɗanci ba ya mutum zai ce baya son Suturar da zata rufe mishi tsiraicinsa, wadda zata ƙara fito da kamalarsa, kayan Hausawa sun fi ko wane kalar kaya kyau da dadin Amfani sun kuma fi ko wane kaya rufewa mutum jikinsa,suna ƙarawa mutum mutunci,ƙaramci, kwarji ke har da farin jini,Amma ku Yaran zamani gaba daya kun yi fatali da wannan, aa yau in an ganku da kayan sawa to Eglish Weres ne"."Abieh sun fi dadin sawa fa, " "dama zasu fi dadin sawa mana tunda suturar shaiɗanu ce, ai shi ya kawo muku ita"."ni kam dai Abieh bana son kana kira min Shaiɗanun nan,ka dai san Addu'ar Iyaye bata da Hijabi, in kuma so kake in zama Shaiɗaniyar na buwayeka shi kenan", ta fada tana langwaɓar da kanta gefe.

Dungure mata kanta yay, kafin yace "ni kam dai bana son ki zama Shaiɗaniya, don nasan kika zama ni kawai zaki fi Buwaya, kuma nine kawai zan juri kiyi tamin rashin jin, Amma soon na kusa gajiya in kika yi rashin ji na ringa zaneki tunda bakya ji", dariya mai daukar hankali ta saki, shagala yay da kallonta, har suka kusa haɗa ido, da sauri ya dauke nasa idanun, "Abieh Duka fa ?, ai ni Yanzu na wuce duka, tun Ina ƙaramata baka duke ni ba sai yanzu da na girma," ta fada tana kallon hanya.

"Ai dai ni bana son dukan Yara ne, Amma tunda kin girma yanzu zan fara ɗurmanki tunda dai kina rigima", luuu ta dan yi da idanunta kafin tace "Abieh!", dan kallonta ya yi ba tare da ya Amsa mata ba.

"Abieh Ai dai ban yi rashin ji ba, Ammyna ta fini rigima", ƙasaitaccen murmushi ya saki kafin ya ce, "Uhmmmn lallai Yarinya, Halee Dubu kuma ai ƙarshe ce, Rigimarta bata da iyaka, in ta fara rigima sai na ji kamar na dauko bulala, Shagwaɓɓaɓa kuma Sakalalliya ta, bata jin magana sam, duk rigimarki ƙafarta baki kama ba, duk da dai kin dauko wasu abubuwan, sai dai ba duka ba , ita tana fira da mutane, tana fara'a da kowa, bata sa kaya irin wannan, kullun da shigar Hausawa, in kin ga tasa wasu kaya to Abaya ne " . "to ni kam dai Abieh kushe ni kake kana yabonta", ta fada fuskarta bb alamar murmushi.

Shiru yay bai ƙara cewa komai ba , don yasan zata iya yin fushi daga wannan yar maganar, har suka ƙarasa gida bata yu magana ba shima kuma bai yi ba, kowa ɗakinsa ya nufa,sauri-sauri tayi wanka ta fito, cikin wata Abaya mai kyau, ta yane kanta da gyalen tana tafiya a harɗe daga ka ganta kasan ba saba sa kayan tayi ba kuma bata jin dadin kayan, haka ta nufi Dining A hankali ya fara haɗa tea mai dan kauri , A hankali ta fara sha tana dan lumshe idanunta, kular da take gefe ta jaawo, lafiyayyan farfensu kayan ciki ne a ciki, da sauri ta rufe kular don bata cin kayan ciki ita kam , wata kular ta ƙara budewa, nan kuma lafiyayyan tuƙaƙƙen tuwan danyar shinkafa da ya gaji da tuƙuwa yay wani irin mul-mul ne ya bayyana, cikin hamzari ta fito da tuwon kwara daya, ta rufe kulan, kulan miya ta bude nan kuwa haɗaɗɗiyar miyar kase ce ta bayyana, tayi wani irin kyau a ido, ga naman da bandar kifi zuqul-zuqul a ciki, miyar tayi kyau sosai,zubawa tayi a gefen tuwan ta sanya Spoon ta fara cin Abin cinta hankalinta kwance.

ko 5 Spoon bata yi ba ta fara jin idanun mutum na yawo a jikinta, bata dago kanta ba don tasan ko waye, kwana biyun nan haka yake mata wannan game din, duk kuwa da yasan bata son idanu a kanta amma shi ksm ya laƙanci haka, idanun mutane a wasu lokuttan suna da mugun tasiri a kanta, so da dama bata jin komai in ana kallonta, wsni lokacin kuma takan rasa natauwarta in ana kallonta, ita dai rayuwarta baina-baina ce ita ba mai son takura ba ita kuma mai takura, haka take tafiyar da rayuwarta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull