Arman maleek book 1 complete - Chapter 19
Arman maleek book 1 complete Chapter 19: Arman maleek book 1 complete Chapter 19. kujerar da take kallon tata ya zauna, a hankali ya fesar da numfashi daga…
4,380 words
kujerar da take kallon tata ya zauna, a hankali ya fesar da numfashi daga cikin bakinsa, cikin dan marairaice murya tana rawa yace "mai yasa kike son wahal da tunanina da kuma hankalina, kina fa wahal da shari'a da yawa, *IDAN BA KE* kin sani bb ni , bazan iya rayuwa in ba ki ba.
Table din da yake gabanta ta buga cikin tsawa tace "Yaa Isa haka Uncle Zayn. wannan wace iriyar magana ce ka keyi ?, are you in your Right Sense kuwa ?,ni kake kalla ka kewa maganar soyayya har ma kake maganar Aure, shin wai ko ka manta matsayina a gurinka ne ?, ni fa Yar Wanka ce Uwa daya Uba daya, taya kake tunanin aurwn Yar wanka ?, ko a Addinin Yahudu ba'a wannan balle a cikin Addininmu na Musulunci . ko kana so mu kafurce ne ?, kama dai na wannan maganar don yarda ba zaka iya Auren Yar cikinka ba,ba kuma zaka iya Auren Amatullah ko Amaturrahman ba, haka nima babu Aure a tsakaninmu, ko da kuwa a kwai Aure tsakaninmu , to ka ƙaddara a ranka Ni ```SAWWAMA ARMAN MALEEQ ABDUL-AZEEZ MALEEQ SARKI bazan taɓa Auren ZAYN MALEEQ ABDUL -AZEEZ MALEEQ``` SARKI ba, har ƙarshen numfashina, ta faɗa tana ajiye Spoon din hannunta tayi gaba abun ta.
Tun farkon fara maganganun nata, yana tsaye step din karshe na Upstairs yana kallonsu Daga gurin don dai ban san mai suke tattaunawa ba, daga dai yarda yaga yana yinta yasan sam ba magana mai dadi bace suke faɗa.
maimakon tayi ciki sai tayi waje chan, shi kuws Zayn kan shi ya kifa da jikin dining yay shiru, ji yake zuciyarsa na masa ƙuna,bai son mai yasa Yarinyar take son tarwatsa masa tunaninsa ba.
maimakon ya ƙarasa cikin palon sai ya koma ciki kawai, bai san mai ya haɗasu ba kuma baya son sanin koma mene ne.
***
"Abieh na yanzu tafiya za kayi ni daya zan zauna ?", ta fada idanunta na tara hawaye, shafa kanta yay tare da cewa "Uhmm dama ai ba kullum za kiyi ta ganinmu kina rayuwa da mu ba, dole wata rana mu kauce. dole wata rana ki zauna ba tare da ni ba, fata na dai zaki yi komai yarda na faɗa miki", jinjina kanta tayi cikin tsananin shaƙuwa tace "In sha Allahu Abieh", "Good!", ya furta yana mai sanya hannunshi cikin Aljihun Alƙyabbarsa.
key din wata falleliyar mota mai azabar kyau ya fitar daga Aljihunsa, cikin kulawa ya damko hannunsa ya damƙa mata key din tare da cewa "ki kula bana son ganganci bana son wauta, ki tsare mutuncinki, ki sanya a ranki kullum da ko yaushe kamar ina gabanki ne, domin tsaron da zaki samo ko da kina gabana bazan baki kamarsa ba", jinjina kanta tayi, tare da rungumesa tace "thank you so much the best Papa Ever!'', ta fada tana murmushi.
juyawa ya yi ya ƙara gyara Alƙyabbar jikinsa da kyau, waje ya yi, ita kuwa ta koma ciki, tana jura ƙafarta palo tayi ki ciɓis da Zayn, da sauri ta dauke idanunta, wani maƙirin murmushi ya saki kayin yace "yanzu Aka fara wasan SAWWAMA ARMAN MALEEQ ABDUL-AZEEZ MALEEQ SARKI.......
AYI MIN AFWA NA RASHIN YIN TYPING DA WURI GASHI KUMA GUNTU, WLH WANI DAN PROB NE AKA SAMU, AMMA YANZU NORMAL IN SHA ALLAH [5/15, 7:47 PM] I'm His Mrs: PART 3.CHAPTER 3.
*P. 38*
Haka Yinin ranar ta kasance wani sukuku, ita dai bata san mai yake faruwa ba, amma dai tana jin nauyi a ranta, tana kuma jin wani iri na daban kamar dai wadda wani nauyi ya hau kanta, lokacin Sallar Juma'a nayi, ta fito daga kitchen ta nufi Bedroom dinta, bathroom ta shiga, tayi wanka ta fito , daure da towel babba . da daya a hannunta tana goge kanta mai yawa da tsawo, sai faman gogewa take amma har lokacin lingif yake da ruwa, gaban mirror ta isa, cikin kasala da wani irin yana yi da ya saukar mata, ta fara shafa lotion dinta, komai da take a hankali take yinsa, har ta gama, cikin wata dakakkiyar Shadda Baƙa tasha ɗinki mai kyau, ta shirya, yanzu kam shiri tayi wanda yafi na ɗazun kyau, cikin Adon Zinari mai matuƙar daukar hankali, wanan karon har da Legs Chain ta sanya.
jikinta a Sanyaye ta fito daga side dinta zuwa babban palo, tana fitowa gaba daya idanunsu ya dawo kanta, "Wowwwwww Daddy's Gal kin ga yarda kika yi wani kyau na musamman yadda kasan Amarya", ta fada tana kallonta, dan murmushi ta mata kafin tace "Thanks!", ta fada tana zama kan kujerar da Zayn ya jaa mata,shiru ta zauna kan dining din ta kasa taɓa komai duk da cewar ita ce tayi kusan rabi na aikin amma ta kasa taɓa komai, Umma Jakadiya ce tace "Chef Sawwa ki ci Abin cin mana", ta fada tana tura mata plate din Fried Rice, wadda taji kayan haɗi sosai, tayi kyau tayi wara-wara.
"Toh", ta fada tana sa Spoom cikin Abin cin Amma ta kasa ci, haka kowa ya gama cin Abincin sa amma ita tana zaune,ko Spoon daya bata yi ba, miƙewa tayi ta wuce side nata, wayarta ta dauka tare da danna masa kira, har ta gama ring bai dauka ba, kafin ta ƙara kiransa ya kirata "Abieh na!", ta faɗa kamar zata fashe da kuka,magana yay daga chan ɓangaren, cikin hawayen da suka suɓuce mata , tace "Abieh ban san mai yake damuna ba, ina jin zuciyata na min nauyi, tana tsinkewa nama kasa cin Abin ci, gaba daya jikina babu dadi", ta fada tana fara shasheƙar kuka.
"ki zo yanzu ina part dina", ya fada cikin tattausar murya tare da kashe wayarsa, mayafin kayan ta dauka, tare da ficewa tana goge idanunta da Tissue , da Sallama ta shiga cikin palon nashi, chan ciki shima ya Amsa mata, tare da ware idanunsa, kallonta ya yi, sosai ya gano damuwar da take tare da ita, tun kafin ta isosa ya ware mata hannayensa,da gudu ta ƙarasa garesa tare da shigewa jikinsa ta saki kuka a hankali, sosai ya sanyata a jikinsa ya rungumeta, bayanta ya shiga dan duka a hankali cikin sigar lallashi, don yasan yau kam ya yi kaifi , don ma bata san matsayinsa a gurinta ba da sai ta fi haka damuwa.
lips nasa ya manna kan tattausar fatar kunnanta, a hankali ya fara hura mata iska cikin natsuwa da son kwantar mata da hankali, "wai me ne ne ?", ya tambaya a gajarce, tura kanta ta kara yi a jikinsa kafin tace "Abieh bana cikin walwala ta ban san mai yake damuna ba, gaba daya bana jina a cikin dai-dai ji nake kamar Ana niyyar rabani da wani abu nawa, like dai abun da naji da Rasuwar Ammyna haka nake ji a yau din nan", ta fada tana lafewa.
"babu wani Abu da zai faru da izinin Allah, kawai dai garkuwa jikinki ce ina ji ta gaji", ya fada yana dan shafa wuyanta da yatsarsa daya, hancinsa nakan sumar kanta da dan kwalin ya riga da ya cire daga kanta, cikin iya lafazi da tausasa harshe yace "Chuɓaɗon Abieh!", cikin kasalar da take ƙara sauko mata ta furta "Na'am Abieh", ta fada tana wasa da wuyan rigarsa, "A yanzu wani nauyi da girma ya kara hawa kan mu ni da ke, na san kin san komai ba sai an tsaya duguwar magana ba, a da kina Amsa sunan Iyalina ke daya, to a yanzu kin tashi daga ke daya kun zama ku biyu, Ma'ana na sama miki wata Sabuwar Mahaifiya wadda nake tunanin zata tsaya ta riƙeki tsakani da Allah, zata miki dukkan abun da kike so wanda kuma kwatankwacin kalarsa Ammynki zata miki, duk da nasan ba son Auren nan kike ba, amma ki danne zuciyarki ,ki dauketa a matsayin mahaifiya, wadda zata kula dake a ina nsn ko bana nan, ki mata biyayya kwatankwaci yarda zaki min ko zakiwa Ammynki, ina haɗaki da Allah kar ki bari naji wata rigima ta tashi daga gareki, dukkan wani abu da take so ki mata domin a zauna lpy, haɗin kan *IYALINA* shi na fi fiye da komai a rayuwata, kin san irin yarda nake jin ki a raina, ban yi haka domin na ƙuntata miko ba, ko kin gaza da wani fanni ke da Ahlina na kula da ni, aa sai dai ni Babban Malami ne kuma Limami, daɗin daɗawa Shekaruna sun yi jaan da ya kamata ace ina da mata, domin kar hakan ya zama abun wani tunani ko magana, yasa nayi Auren nan amma sam ba da son rai na ba, fatan zaki Amsa Zaɓin da nai miki na mahaifiya sannan zaki mata biyayya dai dai gwargwado", hawaye na zubowa daga idanunta, ta jinjina kanta tare da cewa "In sha Allahu Abieh , Allah y bada Zaman lafiya da Zuri'a Ɗayyiba" ta fada tana , miƙewa ta fita da sauri, dan wani mugun abu take ji yana taso mata har rufe idanunta yake.
Tana shiga Side dinta ta kulle ƙofar palo ta shige chan cikin bedroom shima ta kulle, kuka ta saki mai ƙarfi sosai tana fadawa kan bed, cikin tsananin kuka da murya da bata fita tace "Why Abieh! Why!!, Aure !", ta fada cikin kiɗima da ƙara gigita.
Tsaye Amaturrahman tayi tana kallon yarda take kuka mai cin rai, kukan da tunda Uwar da ta haifeta ta kawota duniya bata taɓa yin kamarsa ba, ko kukan da tayi na mutuwar Ammynta bai kai haka ba, da iya gaskiyarta take yin kukan tana jifa da duk pillows din jan bed din da pillows din suka ƙare, ta nufi mirror fashe-fashen ƙwalabe ta shiga yi, cikin tashin hankali Amaturrahman ta matsa gareta, ganin ta jiwa hannunta ciwo jini sai zuba yake, cikin faɗa tace "mai kike aikatawa ne haka kamar marar hankali ?, an ya kina cikin natsuwarki kuwa ?", ta fada tana jijjigata , cikin zafin rai ta dago tare da dauketa da wani gigitaccen mari mai azabar zafi, dama gata da zafin hannu, tuni fuskar Amaturrahɓan tayi jaajir.
Cikin jin haushi itama ta dauketa da kyawawan tagwayen maruka, masu gigitarwa, wanda yasa ta kifa, cikin faɗa da ƙaraji tace "kin dade baki kashe kan ki ba, Mahaukaciyar banza, da wannan haukan naki kike tunanin bazai Aure ba, in bai yi Aure ba da ke zai zauna ?, in ba masifa ba ma ban taɓa ganin in da Ƴa take da Azababban kishi akan Ubanta irinki ba, ya zaki ce ba zai Aure ba, Al halin gaba daya duniya tana koyi da shi ne ?, va mace daya ba huɗu zai yi da izinin Allah", "Yaa isheni haka, na gaji da jinn wannan mugayen kalaman naki, ki fita ki bani guri kafin na miki lahani", ta fada cikin ihu da faɗa idanunta sun wani rufe, ƙofa ta nuna mata, tare da cewa "ki fice min a Ɗakina na ce ", ta fada tana nuna mata hanya.
"Mtswww Mahaukaciya kawai", ta faɗa tana ficewa, ƙofar ta buga mata, Rai ɓace ta fito cikin babban palo, tana huci, "lafiya ?, ina Sawwaman ?", ta fada tana kallon bayanta, shiru tayi bata ce komai ba, "ba magana nake miki ba ?", Ayyana ta fada tana daka mata tsawa, cikin fushi da tura baki tace "tana part dinta tana hauka", da mamaki tace "Hauka !, hauka fa ?", ta fada tana ƙara dubanta, "Hauka mana Ayyana, wai dan mai Abien ta zai yi Aure shine take ta fashe-fashe, dan na mata magana shine ta mareni, ni ma na rama", zaro idanu waje tayi tace "kika rama", ta fada tana miƙewa, da sauri ta matsa tare da cewa "Ayyana ita ce nan fa ta fara marina ni kuma naji zafi na rama"ta fada tana kallonta.
"You are very Stupid wlh, don ta mareki shine zaki rama, saboda baki da hankali, to bari na baki labari ba ke ba har ni Ubanta zai iya cewa zai dukan saboda na duketa", zaro ido tayi tare da cewa, "Ayyana baki ga abun da take ba har fa ta jiwa kanta ciwo" ."Oh God!", ta fada tana nufar side nata.
bude ta samesa, da sauri ta shiga, tana zuwa ta tarar da ita yashe ƙasa, bakinta da hancinta na zubar da jini, "Innalillahi wa Inna'ilaihi raju'un Hasbunallahu Wani'imal wakeen", ta fada tana daura hannayenta biyu a kanta, "Maleeq! Maleeq!! Maleeq!!! Maleeeeeeeeeeeeeeeq!!!!", ta ƙarasa fada da mugun karfi tana banka ƙofar palonsa, cikin sauri ya miƙe tsaye daga in da yake yana cewa "lafiya Ayyana ?", cikin gigicewa, tace "ba lafiya ba, ga Sawwama chan ta faɗi jini na fita hancinta da bakinta", cikin mugun kiɗima da razani yace "Whatttt Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un", ya fada yana nufar hanyar fita daga palon cikin gudu-gudu.
Yashe yz tarar da ita, cikin sauri ya dauketa yay waje da ita, da gudu Ayyana da Umma Jakadiya suka rufa masa baya, suna fita kuma Zayn na yin parking din mota a dai-dai ƙofar babban palon gidan, dawowarsa kenzn daga fitar da yay, ko fitowa bai a motar ba , ya ga Shehi riƙe da ita , da sauri cikin tashin hankali ya bude masa mota sanyata yay ya shiga da gudu ya juya kan motar suka nufi babban Asibitin garin, cikin sauri suka ƙarɓeta, suka shigar da ita Ɗaki na Musamman kasantuwar dama sun san damuwarta, yasa basu sha wahala sosai ba gurin gane abun da ya ke damunta ba, duk da dai abun ya yi ƙamari, sai da suka dauki awa 2 cur a kanta kafin aka samu dai-daituwar numfashinta, ƙarar Ƙofar da suka ji ne ya dawo dasu hayyacinsu, da sauri Yaah Shehi da yake chan nesa ya matsa gurin ƙofar, Dr Irfan ne ya fara fitowa sai Dr Salmah da take bayansa, sai kuma nurses da suke binsu a baya, gaba Dr Salmah tayi , Dr Irfan kuwa shine ya tsaya,bayan sun gaisa sun tambayesa ya take yace musu da sauƙi, yace "Abieh dinta fa ", da sauri Ayyana tace "gashi chan!",ta fada tana nuna sa,"okay bari naje",ya fada yanz nufar Shehi shima kuma lokacin ya nufosa, a tsakiya suka haɗu, Masabaha su ka yi, jerawa suka yi zuwa office fin likitan.
bayan sun zauna ne, yace "fatan dai ba babbar Matsala bace ta sameta ko ?", ya fada cikin tsantsar damuwa, don ita ce rauninsa, numfashi ya sauke tare da cewa "Eh to ba dai matsala bace sosai, Zuciyarta [5/15, 7:47 PM] I'm His Mrs: PART 3.Chapter 2.
*P. 37*
Murmushi mai narkar da zuciya ta masa,kafin tazo dai-dai kunnansa tace "Uhmmmm ina nan ina jiranka Zayn-Maleeq duk lokacin da ka shirya ina shirye, kasa a ranka duk abun da za kayi to zan yi mafiyinsa", ta fada tan yi kamar zata shiga jikinsa, da sauri ta kauce tayi gaba abunta,bayanta ya bi da kallo, kafin ya fice.
A hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya, dadi da ba dadi ba, ita dai kullum tana kan karatunta,bata taɓa gajiyawa ba, sannan tana mugun mayar da hankalinta kan karatun, duk kuma abun da ya shige mata duhu tana browse nasa , in bata fahimta ba ta kira Abieh ya mata ƙarin bayani , a haka har suka tafi hutun Semester, ta shirya kayan tsaf domin zuwa hutu.
lokacin da ta isa Saudi daga England sai ta tarar da baƙin Abubuwa cikin gidan, ga shirye-shirye da ake tayi, bata dauki komai da shirin da ake yi ba, don ta dauka domin zuwanta aketa abubuwan, sai dai Abun da ya bata mamaki har baysn kwana biyu da zuwanta ana ta shirye shirye, gaba daya gidan an masa fenti, an chanja masu furniture,komai sabo aka sa musu, hatta da kayan Sawarsu an chanja musu, ga wasu sababbin fuskoki da take gani a cikin gidan sai dai bata wa kowa magsnar ba,kasantuwar gajiyar da take tattare da ita .
Zaune take A palo, hannunta riƙe da Phone nata tana daddanawa, ƙafarta na kan stool , ga plate din yankakkun fruits da cokali fuck akan cinyarta, tana sanye da wata tsadaddiyar Abaya mai kyan gaske kalar Coffee , kanta babu dan kwalli sai wani ƙananun kalaba da aka mata wadda ta zubo har kan kirjinta , sai kamshi take bulbulawa hankalinta kwance, wasu manyan mutane ne suka shigo cikin palon da Sallama, Amsa musu Sallamar tayi tana kallon fuskokinsu, cikin rashin sani don duk baƙin fuskoki ne ta gani, gurin zama ta nuna musu, bayan sun zauna ta kira aka kawo musu Abun motsa baki, bayan sun taɓa suka ƙara gaisawa,kallon rashin sanin da suka ga tana musu ne yasa daya daga cikim su tace, "baki gane mu ba ko ?", jinjina kanta tayo alamar "E!". "dama ba lallai ki ganemu ba, amma mu mun sanki Sawwama Arman Maleeq ko ?". lumshe idanunta tayi ta buɗe kafin tace "haka ne", "Good!".
"Abieh'nki muke nema, yana gida ko ?", a hankali tace "Eh yana nan, bari na kira muku shi", ta fada tana miƙewa zuwa side dinsa, "Wannan ce Munafukar Ƴar tasa", da alamar jimami tare da jaan doguwar Ajiyar zuciya dayar tace "Uhmmmmm na ganeta ai ." ƙara kallon bayanta tayi kafin tace, "lallai dole Khaleedah ta dage , don wannan zata iya rabata da Uban ma", ta fada tana jinjina kanta,wani makirin murmushi tayi kafin tace "Uhmmmm kina tunanin zamu zauna ne ?, to dama daga chan ma Kakar Ƴar shiri take a kanta, kin ga faɗuwa tazo dai-dai da zama ", Jinjina kanta taa ƙara yi kafin tace "irin wa'innan ma ko Tuggun aka musu bays kamasu", "uhmmm zai sai in baki kai su in da ake share kuka ba", ta fada tana kallonta.
A hankali ta shiha cikin palonsa da yake da dan duhu, ba sosai ake ganin cikin ɗakin ba, kasantuwar duk wasu kayan wutan da yake side din a kashe yake, ga manyan labulaye a sassake, sai kamshin Room freshener da ya haɗe da kamshin turarenshi Palon yake,"Abieh! Abieh!! Chuɓaɗo! Chuɓaɗo!!". Ta furta tana dai-daita tsayuwarta cikin palon nasa, bata jima da tsayuwa ba taga haske ta ƙasan ƙofar bedroom dinsa, hakan yasa ta nufi Bedroom din, tsaye ta tarar da shi, yana dai-daita zaman hiramin kansa,dan kallonta yay, kafin ya dauke kansa daga kallon nata, "Abieh wasu mutane sun zo ganinka", ta fada tana kallon carpet din da yake shimfiɗe a ƙasan bedroom din.
"Je ki kawosu palona", ya fada yana fesa turarensa na Huge Boss, "Tom!", ta fada tana yin waje, tunda ta fito daga side dinsa, suka dai na ƙus-ƙus din da suke a tsakaninsu suka fara mata murmushi, fuskarta babu yabo babu fallasa tace "muje yace ku shiga", miƙewa tsaya suka yi, hanyar side nasa ta nuna musu, sai da suka yi gaba kafin ta biyosu a baya, don hakan take jin bata yarda da mutanan ba.
Kan kujerun palon suka zauna, ita kuwa sai ta wuce bedroom domin faɗa masa ta cika umarninsa, dayar ce ta ƙara taɓo daya tare da cewa "ji fa wai Ƴa ce da shiga Bedroom din Uba gaba gaɗi haka bb wani neman Izini, sam ba daraja cikin Al-amurran nan", gauron numfashi daya ta jaa tare da cewa "bb daraja kam, wannan balugatun Ƴa a gaban mutum tana wannan irin shiga, ga ba kunyar shiga ko ina, Allah dai y kyauta", kafin dayar tai magana suka fito tana gaba tana bayansa, suna tafiya ƙaf da ƙaf , taku daya ne a tsakaninsu.
da Murmushi kan fuskarsa ya ƙaraso cikin palon, cikin tsananin mutuntawa yace "A'a su Hajiya Abida sannunku da zuwa", ya fada yana zama kan kujera, murmushi suka yi tare da Amsa masa, kafin wani yay wata magana, da zauna a gefensa kan kujerar da ya zauna, jikinsu na gugar jikin juna, kallon juna suka yi tsakanin wadda aka kira da Hajiya Abida da dayar,yana yin yarda suka kalli junan ne, sai Shehi yaji wani iri, alama ya mata da ta tashi, basarwa tayi kamar bata san mai yake nufi ba, ƙyaleta yay dan tun da tai hakan yasan ba zata tashi ba, "Muna son mu yi magaba da kai", Hajiya Abida ta faɗa tana kallon Sawwa da ta dauke kanta ta mayar kan phone nata tana daddanawa, wanda a zahiri zaka dauka ma bata jin mai suke faɗa, A baɗini kuwa sarai tana jin duk abu da suke faɗa.
"Zaku iya yin maganarku ai ba matsala", ya fada yana tattara musu dukkan natsuwarsa, kallon Sawwama suka yi, shima kallonta yay kafin ya kallesu, "ba wata matsala kuyi maganarku", ya fada yana kallon fuskokinsu, numfashi suka sauke kafin su shiga yin maganganun da suka kawosu.
tun da suka fara magana numfashinta yay sama, ta dai na fahimtar komai bata ji bata gani, wani hazo-hazo take ji yana luluɓe idanunta, wani abu mai nauyi ya tsaya mata a kirjinta.
Fahimta da lurar da yay da yana yin da take ciki ne, yasa ya taƙaita maganar da suke da cewa "An jima ma yi magana da ita", ya fada yana dan jingina bayansa da jikin kujera, gane dai y taƙaita musu magana ne ba tare da sun gama baya, alamar ya gaji ko wani abu makamancin haka yasa suka mishi Sallama suka fice.
Ya dade sosai yana kallonta bayan fitarsu, Amma ya gaza fahimtar damuwarta ta me ce ce, hannunta ya riƙe yana kallonta, kallonshi tayi, da sauri kuna ta dauke idanunta ta miƙe ta fice, alamae A fusace take ko kuma tana fushi mai tsanani , gyara zamansa ya yi , yana kallon bayanta, a hankali ya lumshe idanunsa, ƙarar wayarsa ya ji, sai dai bai mayar da hankali akan hakan ba, sai da aka yi kira har ukku a na huɗu ne ya dauki wayar, *Jadda* ne yake yawo akan screen din wayar, sai da yay jim kafin ya dauka, kafin tai magana yace "lafiya?", ya faɗa a taƙaice, daga chan ɓangaren cikin wutar tsana tace "ni kake tambaya lafiya ?, to Uwarka Yahudu da Wannan Naƙasashen Uban naka a kai , Dan iskan Yaro", cikin takaici na ta kasa chanja halayenta yace, "ko mai kayi da jaki dai dole sai ya ci kara", ya ƙarashe fada da dan jaan tsaki, "Ubanka da Uwarka ne Jakan , Eh nace sune jakai, akwai sauran magana ko babu", ta faɗa cikin tsawa mai tashin kai, wanda yasa yay saurin matsar da wayar daga kusa da shi.
"na gaji da jin wannan haushin naki, in kina da abun faɗa ki faɗa in kuma babu ki kashe", ya fada yana kallon gefensa, "cewa nai ka tattaro wannan tsintacciyar magen ka dawo da ita nan, don ban son ganinku tare, kuma Umarni ne ba shawara ba", cikin tsantsar ɓacin rai yace "Sannu Uwata",cikin sauri tace "dai na haɗa ni da wannzn gantalalliyar matar da babu Allah a ranta, Allah y tsareni da shiga cikin Ahlin Yahudu, kuma na faɗa maka ka dawo da wannan Tsintacciyar don bama mu sani b ki Shegiya ce tske zaune tare da mu", cikin tsawa yace "Yaa Isa Jadda kada ki ƙara sheganta min ita, domin ba shegiya bace, da Ubanta da kuma Asalinta da na tabbatar in aka bibiya tama fiki Asali, kuma dawowa da ita bazan dawo da ita ba, babu daya dan Ahlina da zai dawo nan, ku dai da kuke mayatar Sarautar kuje kuyi, kuma ku zauna a cikinta, amma ba dai mu ba, " yana gama fadar haka yaa ja wata kwata tare da kashe wayar.
Sororo tayi da wayar a hannunta jin yw kashe, ita ma kwatar tayi tare da cewa "Shegu masu jaajayen kunnuwa, da sannu gaba dayanku sai na farraƙaku,na Tsani Ahlin Aminatu bazan taɓa kaunarsu ba, sai na tabbatar da lalacewar farin cikinsu gaba daya, sai na sa sun fara tantalbaɗeɗe, sai sun zama Abun kallo da Wulaƙanci, ko zan yi yawo tsirara sai na wufubtar da su", ta fada tana gyara zamanta, cike da ɓacin ran maganganun da ya gaggasa mata.
Wasa-wasa abu yay ƙamari tsakanin Sawwama da Abienta , bata bari su haɗu, daga zaran taji fitarsa zata fito pali, daga zaran ya dawo kuma zata dawo bedroom ba zata fito ba har sai ya ƙara fita, tun babu wanda ya fahimci halin da ake ciki har kowa ya fahimta.
yanzu haka suna palo suna fira, kamar daga sama suka ji Ƙarar dirar motocinsa, da sauri kamar ƙiftawar ido ta ɓace daga cikin palon tayi bedroom, da Sallama ya shigo cikin palon, ganinsu zazzaune yasa ya shiga binsu da idanu, yana kallonsu daya bayan daya, amma babu ita a cikin palon, numfashi mai zafi ya fesar kafin ya shige ciki, ba tare da ya biya gaisuwar da su Amah suke masa ba, alamar dai baya cikin natsuwarsa.
"Baki fahimci wani abu ba ?", Ayyana ta raɗawa Umma Jakadiya da take kusa da ita, jinjina kanta tayi kafin tace "na fahimci kamar babu jituwa tsakanin Uba da Ƴar a kwana biyun nan". "nima Abun da na fahimta kenan, kuma shi na lura yana son ganinta amma ita bata ko bari su haɗa hanya". numfashi Ayyana ta saki kafin tace "bari naje naji", ta faɗa tana yin hanyar ɓangaren Sawwama, ko da ta je palo a bude tsaf dashi kamshi sai tashi yake, direct bedroom dinta ta nufa, a rufe ta jisa, hakan yasa ta fara ƙwanƙwasawa, daga chan ciki Sawwama cikin muryar damuwa har kamar kuka-kuka take tace "Waye", "ni ce"Ayyana ta fada tana gyara tsayuwarta.
da sauri tasa tissue ta goge hawayen idanunta ta nufo ƙofar, budewa tayi, tare da bata hanya, shiga tayi kafin ta biyo bayanta, gefen gadonta ta zauna , kafin ta zauna itama a gefenta, cikin kulawa, tace "mai yake damunki ?", ta fads tana dubanta da kyau, "babu !" ta faɗa a taƙaice, jinjina kanta tayi kafin tace "mai yasa kike fushi da Abienki ?", kallonta tayi, sai kuma ta saukar da idanunta a hankali tace "ni ba fushi nake da shi ba ", ta fada idanunta na tara hawaye.
"Dube ni da kyau kin san ni ba Yarinya bace, taya na ganki kina kuka, bakya son shiga cikin mutane, kullum ki shige ɗaki bakya zama,bakya zuwa Gurin Abienki , kamar ma kowa kina fushi da shi amma kice babu komai", ta fada cikim fada-fada.
"Ayyana ban so", ta fada hawaye na zubo mata, duk ta ruɗe don ita sam bata kaunar faɗa gwara ka duketa da ka mata faɗa, numfashi ta fesar kafin cikin sai-saita murya da karyar da muryarta tace, "Okay! Okay !! zo jikina ki faɗa min mene damuwarki", ta fada tana bude mata hannayenta.