Kenza eBookz

Arman maleek book 1 complete - Chapter 20

Arman maleek book 1 complete - Chapter 20

Arman maleek book 1 complete Chapter 20: Arman maleek book 1 complete Chapter 20. da sauri ta shige jikinta,tare da sakin kuka, sai da tayi mai isarta…

4,442 words

da sauri ta shige jikinta,tare da sakin kuka, sai da tayi mai isarta kafin tace "Wai Abieh ma ne zai yi Aure", sakin baki Ayyana tayi tana kallonta,cike da mamaki,murmushi ta saki kafin tace "baƙya son ya yi Auren ne ?",cikin sauri ta daga mata kanta, jinjina kanta tayi kafin ta gyara zamanta da kyau, tace "Uhmmmmm! Amma dai kin san a matsayinsa na Babban Malami kuma Limami ga tarin shekaru ai ba Mutuncisa bane zama Babu Aure, ko kin fi son ayi ta zaginsa ana ce masa tazuru ?", girgiza kanta tayi, "to kin ga dole ne tay Aure ko don gudun ruɗun shaiɗan", tura bakinta tayi kafin tace "to ma duka nawa Abien yake ne", yar dariya Ayyana tayi kafin tace, "Eh nawa yake mana, Amma kuma ko dan ke da kike gabansa ai ya kamata yay Aure domin shine mutuncinsa da naki gaba daya, ko kina so a ringa ce miki Ƴar Tazuru ?", "to ina ruwan wani da Rayuwarmu ma", ta fada tana kwantar da kanta a cinyar Ayyana.

"ke dama ai ba zaki gane ba, yana da Shekaru da Dukiyar da ba Mace daya ba biyu ba, ba ukku ba , ba huɗu ba ke in ana mace goma yana da dukiya da Arzikin da zai kula dasu ci , sha, tufa da komai na more rayuwa zai iya musu, sai kuma ya zauna babu Aure", "ni dai wlh bana so, in naji ana mishi maganar Mace Zuciyata nauyi take min", ta fada hawaye na zubo mata" Babbar Magana, Dan sanda yaga Gawar Soja", Ayyana ta faɗa cikin ɗunbin mamaki da dan firgici, "Ayya dai Ayyana ya da cewa haka kuma ?".ta fada tana kallonta.

"Babu komai.Amma dai y kamata ki gyara irin halayar da kikewa Abienki , duk ya shiga cikin damuwa, baya cin Abin ci, duk ya rame ya zube kamar ma baya da lafiya", zaro ido haɗe da dafe kirji tayi, kafin ta miƙe ta fice daga ɗakin da sauri, duk kiran da Ayyana take mata bata ko waiwayo ba balle ta saurareta, girgiza kanta tayi kafin tace "Allah y kawo shiriya", ta fada tana miƙewa ita.

"Abieh na!", ta fada tana kwala mishi kira, sanyayyan numfashi ya sauke, yana mai lumshe idanuwansa, tsaye yake cikin bedroom dinsa, yana sanye da jallabiya Ash , wadda ta mishi kyau sosai, kanshi yana sanye da hula tashi da ƙwaƙwa, turare ne a hannunsa yana fesawa, har ta shigo cikin bedroom din bai ko juyo ba, da gudu taje bayansa ta rumgume bayansa, ta saura kanta a faffaɗan bayansa, ta zagaye hannayenta akan kirjinsa, ta manna kanta sosai a bayanta tana sauke numfashi.

"Abieh Fushi kake yi da ni ne ?", ta fada tana ƙara riƙeshi, shiru ya mata bai juyo ba, bai kuma Amsa mata ba , ta gabansa ta dawo , ta riƙesa "to Abieh duk ba kai bane, " janyeta yay da jikinsa kafin yace "da nayi miki mai ?", tura bakinta tayi gaba tare da cewa "kace za kayi Aure man", da mamaki ƙarara yake kallonta, cikin dan mata kallon ƙasa-ƙasa tace "ba ji nayi wsnnan matan na faɗa ba", ta fada tama zama kan bed dinsa.

"ina takardar da muka yi Yarjejeniyyar bazan Aure ba ?, in ban yi Aure ba, so kike nayi ta zama da Babbar Ƴa a gabana kamar ke?, ni ba Aure ke ba Aure ?". "Ai ni ban ce dama kar kayi ba", ta faɗa tana juya bayanta.

Taɓe baki ya ƙara yi, kafin yace "to ki fita a idona", ya fada yana tattara wayoyinsa ya sanya a cikin Aljihunsa, takalminsa yasa ya jura Alƙyaɓɓarsa zai fice, da sauri ta biyu bayansa, haɓar Alƙyaɓɓarsa ta kama ta riƙe tana binsa a baya, "Abieh wai dagaske Auren zaka yi ?", ta fada cikin damuwa, bai juyo ba yace "a'a!" ."Abieh ba maganar wasa ba fa", "quit Surutun ya isan", ya fada yana daura yatsarsa manuniya akan lips dinsa.

shiru tai bata ƙara cewa komai ba, a palo ta zauna shi kam ya fice Abin sa.

Ranar Juma'a, da sanyin safiya ya fito cikin shirinsa,mai kyan gaske yau ya yi wani irin kyau na musamman , fuskarsa sai sheƙi take ga wasu Yan ubansun kaya daya ya sha, yarda kasan Ango haka ya fito yana fitar da wani sahihin kamshi na musamman yarda kasan an bulbula masa gwangwanayen turaruka, haka yake kamshi,a palon sa yaci karo da ita , itama cikin shiga ta musamman shigar da ba kasafai ta cika yinta ba, riga da Skat ne jikinta na Atamfa Chiganvi mai golden a jikinta, ɗinki ya mugun tsaruwa ya zauna das a jikinta, ga wani dauri na musamman da tasha, dauri mai tashin kan Maza Musamman ma Masu gida, wato Ture kaga tsiya, ta sha Sarkar Diamond da Yan kunnanta da zoɓɓa, ga wata Agogo mai kyau ta sha, ga dan haƙorin Makkanta sai walwali yake, ta ko ina ta juyawa walali take, gaba daya ta haska ko ina.

Tray din Break fast dinsa ne a hannunta, kallonsa tayi cikin kula da tsantsar shaƙuwa irib ta Uba da Ƴa tai murmushi tace da cewa "Maaa sha Allah Tubaraqallah Abiena kayi kyau sosai, yadda kasan Ango", ta ƙarasa fada da yar dariyarta, tattausan murmushi ya sakar mata shima,kafin yace "kema kin yi kyau yadda kasan Uwar gida", jujjuya kanta tayi kafin tace "Uhmmm Uhmm ni kam bana son Uwar gida Amarya nake so", ta fada tana dan ɗiɗɗira ƙafafunta, jaan kumatunta yay kafin yace "haka nan zaki dauka kuwa", ya fada yana ƙoƙarin raɓawa gefenta ya fice, da sauri ta zubar da duk maganganunsa , tace "Abieh Break fast din ka fa", ta fada tana ajiyewa akan stool , "ooh ina son zuwa wani guri ne yanzu".

cikin tura baki tace "Abieh ni fa na sha wahala na girka maka har da yankewa ma nai a hannu amma zaka ce a'a", ta fada tana tsaresa da idanunta, "nace miki ina sauri fa, ki barsa" ya fada yana ficewa, bayansa ta bi izuwa palo , sai dai kafin ta zo ya fice.

Zama tayi ranta a Matuƙar Ɓace kasantuwar wannan ne karo na farko da tayi girki yace mata aa shi yasa duk ta damu, ranta kuma ya ɓaci.............. [5/15, 7:47 PM] I'm His Mrs: PART 3.CHAPTER 4.

*P. 39*

"Maganar dai ta Zuciyarta ce, in ba zaka manta ba shekarun baya an mata Aiki A Zuciyar, to Ciwon ne yake son ya tashi, sakamakon ƙillan wata Hatsaniya da suka samu ko kuma wani abu da aka faɗa mata wanda ya dukar mata zuciya, Amma zamu ci gaba da treat nata Zata samu sauƙi in sha Allah, "numfashi ya sauke kafin yace "to dama Dr wani lokaci ma jini ya zobo mata ta hanci, ina ta so nazo muyi magana amma ban samu halin zuwa ba",jinjina kansa yay kafin yace "babu wata Matsala a wannan jinin domin haɓo ne, zata iya yin sa ko wani lokaci is normal", ya faɗa yana kallonsa, sansayayyan numfashi ya sauke a ƙoƙarinsa na son ɓoye damuwarsa da nuna ita din ce rauninsa, sai dai tuni Dr din ya harɓo jirginsa, cikin kula yace "kamar dai yarda aka saba a ci gaba da kula da sosai, madamar aka ƙara mata irin haka har ta faɗi to ba makawa zata iya rasa rayuwarta, yanzu bari na rubuta muku magunguna da duk abun da ake buƙata aje a nemi mana" ya fada yana rubutu a jikin wata paper,bayan ya gama ya basa, ƙarɓa yay ya fito daga office din. anan ya tarar Ayyana tana tawa Amaturrahman faɗa kan abun da ya haɗata da Sawwama, tun kafin ya iso ya fuskanci abun da yake faruwa, cikin zafin rai ya ƙaraso gurin, babu wanda ya ji zuwansa, sai ƙarar marukan da suka gigita kowa da suka ji.

Cikin razani da tsoro gaba daya suka ɗago idanunsu domin su kalli wanda akawa wannan marukan, zuɓe suka ga Amaturrahman ta faɗi, tana riƙe da fuskarta, idanunta a rufe , don tama kasa budesu, lokaci daya fuskarta tayi wani irin jaaa sosai, har wani jini ne ya kwsnta akan fuskar. cikin faɗa Umma Jakadiya tace "kana da hankali kuwa ?, yaushe zaka ware kawa wannan yar taliliyar Yarinyar mari da wannan hannayenka, kana sane babu kyau marin fuska musamman ma ta mace, amma kayo burus da hakan", cikin ɓacin rai ba tare da ya ji kiran da take masa ba ma, yay waje.

Ɗagota Umma Jakadiya tayi tana rarrashinta, Ayyana kuwa, dauke kanta tayi kamar bata ga abun da yake faruwa ba, cikin rashin damuwa da abun da ya faru tace "dama ai na faɗa mata, ta roƙi Allah kar Maleeq yasan abun da ya faru, don zai iya mata fin haka in dai akan Sawwa ne", ta faɗa tana watsa hannayenta alamar bata damu ba.

"Haba Ayyana da hankalinki fa wayaukin kike faɗar haka, maimaikon ki lallasheta", kallon Umma Jakadiyar tayi kafin tace "to Umma ni mai zan mata, ai tasan bashi da dauke kai akan Yarsa , zai iya hkr akan komai amma ban da abun da za'a mata,don haka ni babu ruwana", ta fada tana miƙewa, cikin kin fa sata ta shiga.

Shafa Skat dinta tayi ba wai har da gutun futsarinta, idanunta da suka yi jaaajir har bata gani ta buɗe dakyar, sai yanzun tasan cewar kuka ma rahma ne, wani bala'in yafi gaban ka masa kuka,Rarrashinta ta ci gaba da yi,a chan cikin ɗakin kuwa ,har dare bata farka ba, tana kwance kamar gawa, iya kaɗuwa da tsorata Amaturrahman tayi, shi kan shi gogan ya mugun tsorata sosai da lamarin , ya kasa matsawa ko nan da chan, yana gefenta akan kujera, idanunsa akan drip din da aka sa mata, in ya kalli drip din sai ta kalli fuskarta, da ta dashe lamar babu jini sosai a jikinta. "Bari naje gida" Ayyana ta fada tana kallonsa, jinjina kansa yay ba tare da yace komai ba , ficewa tayi , shi kuwa, kusa da ita, hannunta da babu drip a jiki ya riƙe yana kallonta, A hankali ya laura lips dinsa akan goshinta ya mata kiss, gangarowa yay kan hancinta ya mata kiss , lips dinta ya ƙurawa idanu, a hankali , ya sa tongue dinshi, ya lasa lips dinta da suke a bushe , a hankali ya shiga dan tattauna lips dinta ta yarda banzai mata zafi ba, kuma zata ji dadin lips din, idanunshi a lumshe, yake suba mata yawon bakinsa a nata, haka yake shiga take haɗiyewa.

cire lips dinsa yay da sauri daga kan nata, yana kallon fuskarta cikin wani yana yi na musamman , ganin drip din jikinta ya ƙare ne yasa ya cire mata na ........

SAM TYPING DIN BAYA MIN DADI , WAYAR TA KOMA KAMAR SABUWA SAI WAHALA NAKE SAI NA RUBUTA WATA KALMA SAI TA KOMA WATA SAI KA GOGE KA RUBUTA WATA BABU DADI ABUN😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭 [5/15, 7:47 PM] I'm His Mrs: PART 3.CHAPTER 5.

*P.40*

*TUN SUBH YAU BAN KOMA BA DON NA MUKU POST , ƳAN GATANA🤩🥰. NASAN KUNA MIN UZURI PLS KU CI GABA DA MIN DON ABUBUWA SON SHA MIN KAI🥹 AMMA IN SHA ALLAH KOMAI YA KUSA DAI-DAITA.......*

Ya yi dai-dai kuma da ƙarewar drip din jikinta hannunta ya kama ya shiga cire mata wanda y ƙare tare da sanya mata wata ƙaramar roba, wasu manyan allurori ya mata cikin ruwan, wanda take suka sai-saita bugun zuciyarta ,daga nan kuma ya fara ƙirgen lokacin farkawartaawa daya nayi da sa mata ruwan ta fara motsa ƙafarta , lura da hakan yasa ya matsa da gareta, tattausan hannunsa ya daura akan goshinta cikin kula sosai, ya fara kiran sunanta cikin sanyi sosai, A hankali wasu zafaffan hawaye suka fara gangarowa daga gefen idanunta, cikin damuwa da sigar lallashi ya shiga goge mata duk hawayen, "ki daina wannan kukan , kin san babu ƙarfi a jikinki " ya fada yana dan juyota, hannunshi ta wanchakalar ta juya, ta ci gaba da zubar da hawayenta, yay maganar duniyar nan tai banza ta ƙyaleshi, har Ayyana ta dawo bata kulasa ba, haka ya tafi ya barta da ita.

*WASHE GARI*

Wan shekarar ma haka ta faru, tama jin kamshin turarenshi ta rufe idanunta, bata ƙara buɗesu ba sai da ta tabbatar da ficewarsa. wasa-wasa lamari yay ƙamari, kwata-kwata bata bari su haɗa ido, da ya shigo zata rufe idanunta ita da buɗewa sai ta tabbatar da bayanansatin ta daya currr a Asibitin kafin aka bata takardar Sallama, Zayn-Maleeq ne ya je ya daukosu daga Asibitin, lokacin da suka dawo gida lokacin gidan babu kowa,kowa ga tafi hada-hadarsa sallama Ayyana ta rafka, sai da tayi ukku kafin a Amsa mata daga chan ciki, a hankali ƙarar takun takalmi ya shiga gauraye gurin, lokacin da zata iso gaba daya sun yada zango a palon .

Da murmushi akan fuskarta ta kalli Ayyana tare da cewa "barka da dawowa Ayyana" ta faɗa cikin babbar muryarta da tasa Sawwama buɗe idonta daya ta kalli Matar, da sauri ta ƙarasa bude dukkan idanuwanta ta kalleta, Mace ce a tsaye zororo babu gaba ba baya, sai Uban fari , irin farin nan da bashi da kyau,farin rashin godiyar Allah ga halittar da ya maka, wato na bleaching , ba laifi fuskarta na da dan kyau, don Balarabiya ce .

"Ya jikin ?" ta fada tana kallon fuskar Sawwama da take tsanarta ta mamaye dukkan gaɓɓan jikinta , miƙewa tayi ta wuce Side dinta ba tare da ta Amsa mata ba, kallon bayanta taxi sao kuma ta kalli Ayyana murmushi ta mata kafin tace "ina ga jikin ne bari na bita" ta fada tana bin bayanta don sam bata ji dadin abun da tayi ba , kwata tayi kafin tace "kiyi naki ki gama kutumar ubanki zan ci la'ada waje",ta fada tana gyara zamanta akan kujera .

"Sam abun da kika aikatan nan baki kyauta ba, taya tana miki mgn amma kika yi shiru kika ƙyaleta, kina tunanin Abieh'nki zai ji dadi in yaji maganar nan", shiru tayi ba tare da ta amsa mata ba, don yanzu ta koyi jin zafin kowa, haka ta ƙare maganarta amma ta fita bata daga kai ta kalleta ba.

Anan inda take bata matsa ba barci mai nauyi ya dauketa, sai maraice liƙis ta farka, wanka tayi, kamar yarda ta saba, ta sha wandonta baƙi iya guiwa ta daura farar riga , ribbon ta sa ta daure kanta dashi, wata ƴar bandana mai fiffike a gaba baƙa ta sanya ta mata kyau sosai, sai ta koma kamar Ƴar Baby, baƙin plate shoes ta sanya, ta fito daga bedroom nata, haka ta fito sai baza kamshi take. A zaune ta tarar da su,Amaturrahman nawa Amatul-Azeez kitso , Ayyana da Umma jakadiya da Sayyid-Maleeq ,Abdul-maleeq na zaune suma, firar su suke yi ƙasa-ƙasa.

Cikin Natsuwa ta zauna akan wata kujera da ta banbanta da ko wacce da take cikin palon, kujerar babba ce gata da kyau, kamar an mata Yarfin Zinari a jikinta ,tana zama suka fara mata ya jiki cikin kulawa, haka ta shiga Amsa musu suma , bayan an gamawa Amatul-azeez kitsonta ta kalli Amaturrahman "nazo kimin ?", ta fada kamar ba ita tayi maganar ba, "ki bari ki samu ƙarfin jikinki kafin", Ayyana ta fada tana kallonta, girgiza kai tayi kafin tace "na gaji da ganin kan a haka Almost 1year ban kitso ba" ta faɗa a hankali, bata ƙara cewa komai ba ganin haka yasa ta matsa, da Bissimillah ta fara mata kitson,an yi kusan rabi ya shigo cikin palon, bayan sun gama gaisar dashi, ya samu guri kan kujerar da ta tashi ya zauna yana facing nata, kitson da ake mata yake kallo don yay kyau sosai.

har aka gama yana zaune , kan ya shiga kallo yana furta Maa sha Allah a ransa, Khaleedah ce ta fito daga sashenta sai wani yauƙi take, ta sha Abaya ruwan ƙasa, ta mata kyau ba laifi sai dai fa a tsaye take ba lanƙwasa, zama tayi kan kujerar da yake zaune, gaisar da su Ayyana tayi ba tare da damuwa da sabgarta ba suka Amsa mata suna masu mayar da hankali kan aikin da suke, cikin markewar murya tace "D zan je a wanke min kai da kitso, kaina ya fara damuna"kallon ƙasa-ƙasa ya mata kafin yace "Amaturrahman ta miki man, ai ta iya",ya fada ba tare ds ya kalleta ba.

Cikin fargaba tace "a'a akwai in da nake zuwa" ta fada tana kallonsa, bai dameki ba kenan", ya fada idanunshi a lumshe, "please!", ɗaga mata hannu yay alamar ta masa shiru, tashi tai ta fice ranta babu dadi, sa nin ba'a sa masa baki a lamarin Iyalinsa yasa duk suka jaa bakinsu suka yi shiru.

Haka dai har aka yi sati da dawowar Sawwa daga Asibiti ta samu sauƙi sosai, amma yanzu ta rage zaman palo saboda Khaleedah wanda yasa ta tsani zaman gidan ma gaba daya, ana haka ya fara mata shirye-shiryen koma Schooldinta, har izuwa lokacin bata wani kulasa, shi kuwa neman shiryarsu yake ta ko ina ,hakan yasa ya shiga mata siyayya kala-kala har sabuwar waya ya siya mata duk da kuwa cewar ta hannunta bata yi komai ba don dawowarta ya chanja mata, tayi murna da siyan wayar amma bata ko nuna masa a fuska ba, ƙarɓa tayi tare da yin godiya ta wuce Abun ta", dafa kansa yay cikin tsananin damuwa da yake gab dawa rayuwarsa illa, numfashi ya fesar kafin ya furta "Yaaaah malikul mulk!", ya furta cikin sigar damuwa ,baya ya yi ya zauna akan kujerar bayansa .lumshe idanunsa yay, yana kiran sunan Allah,zama yaji an yi a gefensa, hannunta yaji yana shafa gemunsa, shiru yay, kamar mai barci , kan kirjinsa ta kwanta, tana ƙoƙarin cire masa rawanin kansa.

ƙarar fashewar Abu wanda yasa yay saurin buɗe idanunsa suka ji, miƙewa tsaye yay da sauri, ganin tayi saurin juyawa ta nufi hanyar side dinta, zuciya a ɗatace, kanshi ya dafe cikin wata juyawa da take yawo dashi sakamakon rashin cin Abin cin da yake. riƙe hannunsa tayi tare da langaɓar da kanta akan kafadarsa , tana ƙoƙarin cusa hannunta cikin jallabiyar jikinsa, da sauri ya zameta daga jikinsa ,yay hanyar bedroom, kafin ya shige ta biyo bayansa da sauri .

Yana shiga yana shiga , amma ta nemesa sama ko ƙasa bata gansa ba, da sauri ta nufi bedroom shima bayanan,gaba daya ɗakin ta rewaye ciki da bai amma bayanan. cike da tsoro ta jaa ta tsaya, a baƙin ƙofa tana ƙarewa ɗakin kallo, "to ko dai Aljani ne ?", ta Ayyana a ranta, "inaaaaaa mutum ne . to amma ina ya shiga haka ?", ta ƙara faɗa tana ƙara duddubawa , da sauri ta fice sakamakon wani mugun tsoro da ya kamata.

©©

"Ya za muyi da wannan Shegen Yaron ne da yake da niyyar tarwatsa mu, so yake ya babbake ko ina, yanzu in ba sharri ba taya Auta Baita zai mana wannan Cakwakiyar, gamu cikin Ministers da Yan Jam'iyya wanda muka dade muna bautawa Ƙasa da jam'iyya , bai zaɓemu muyi takarar President ba sai wanchan Chakuricicin karan larabawan zace wai shi zai fito taƙara, Yaron da kwata-kwata bai san me takarar ba ma . bai san jam'iyya ba. bai san ya wahalar Siyasa take ba. bai san gwagwarmayya da ake sha da siyasa ba, amma har ace shi zai fito takara, a gaskiya da sakyal an bawa mai kaza kai", Alhaji Audu sigidi ya fada rai ɓace.

"Uhmmmm wai a ina kuka samu wannan baƙin labarin ?, wanda yake barazanar tarwatsarmin da zuciya ", cikin ƙufula Alhaji Sammani yace "kutumar bala'i ai wallahi ba zata saɓu ba, duk wahalar da muka yi ta tashi a tutar babu kenan ?, duk wahal da kanmu da muka yi akan jam'iyya ya tashi a banza kenan ? ba zai yiyu ba wlh ". "ba kumfar bakin nan ba ku bamu shawara ya zamu yi yanzu, tunda ai da sauran zaɓe, kafin ya ƙaraso mun gama duk shirinmu, wata ƙil an ma tsayar da dayanmu ", ya fada yana binsu daya bayan daya da idanu.

"ko zamu kirasa ne mu zauna da shi". Kallon baka da hankali gaba daya suka mishi kafin daya a ciki yace "tab to kai Alhaji Baushe zan mai zamuyi da shi ?, muma tonawa kanmu asiri ta yarda za'a ga maitar mulkinmu a fili, " ya fada yana jinjina kansa fuskarsa jaajir.

"ina tunanin Abun da ya fi so zamu, raunata, in muka yi haka zai bamu guri tabbas", Alhaji Sammani ya furta , "kafin nazo ban nasa an bincika min komai da ya danganci rayuwarsa, " "Good Job gaskiya Alhaji Mugu kana ƙoƙari" Alhaji sammani ya fada yana jinjina masa. gyaɗa kansa yay.

"Da rauninsa ya kamata muyi amfani gurin Rusasa, domin ta wannan sashen ne kawai za muyi galaba a kansa tabbas" ya fada cikin zalan ƙeta,"Rauni! Rauni!! rauni kace ?, ai kuwa yana da babban rauni a rayuwarsa wanda har muka taɓa raunin nan dole zai girgiza ", da mamaki suka kallesa sai dai bb wanda yay magana, "Ƴarsa !", wani kallo suka masa "nasan zaku ce taya Ƴar zata zama rauninsa ?, to dai Ƴarsa ita ce raunin duka Ahlinsa domin suna sonta fiye da yarda suke son kansu, Yar ta kasance tana da cutar Anemia sannan a wani ɓarin tana dauke da ciwon zuciya , wanda har aka mata aiki a lokacin da tana da shekara 3 a duniya, har kuma yanzu ciwon bai saketa ba, don kwanannan ma tayi ciwo a kansa", ya fada yana sauke numfashi.

"A yanzu dai tana da shekara 19 don ta kusa kulle Ashirin, tana kuma karatu a jami'ar Oxford da yake a England , har zuwa yanzu Abun da Ƴarsa take so shi yake mata, kuma komai take so shima yana so,Ina ga ta kanta ya kamata ace mun fara, domin zai fi mana saurin rusuwa", ya fada yana kallon fuskokinsu gaba daya, cike da gamsuwa tare da miƙa kai suka ce "Lallai wannan zancen naka haka yake, kuma ka sama mana hanya mafi sauƙi da zamu rusasa, "Alhaji Dan Kaka da yake gefe baice komai ba yace "a gaskiya Alhaji Sammani bala'i ne , yanzu duk a kwana daya da yini ka tattaro wannan bayanan ?", murmushin gefen baki yay kafin yace "to ni din na wasa ne ?"da sauri ya girgiza kansa, cikin muryar Mugunta yace "Faɗa da Aljani ba riba" ."Tabbas!". haka suka ci gaba da mugun ƙullinsu, in da wanda sukewa ma bai san suna yi ba, don shi sam abun baya kansa baya cikin Al-amurransa don ba ƙadan ya washi mulki ba, ko na masarautarsu da ya zama dole baya ra'ayi balle kuma wani.

©©©

Tsaye yake tsakiyar babban palo, yana darawa tsintsiyar hannunsa Agogo yana sanye da Captan Jallabiya milk sai wata Alƙyaɓɓa Brown da takalmi shima brown kansa naɗe da Rawani, fuskar nan tayi fayau ya ƙara haske sosai, ramewar da yay tasa idonsa ya dan burma kaɗan, Sunan Allah ne a bakinsa, wani ƙarfaffan numfashi ya jaaa cikin rauni da zallan damuwar da yanzu ta zame masa abokiyar rayuwa, sai dai in ba farin sani ka masa ba ,ba zaka taɓa ganin hakan ba.

Gaba daya hannayenta ta zuba kan kirjinsa, ƙamshin turarenta na wani fusgarsa, ga kuma wani yanayi na musamman da yake jinsa ciki yau din...........

Kuyi hkr in kunga Errors , don yanzu sai a hkl ga kuma hidima, shi yasa yanzu ban cika hawa online din ba ma sosai [5/15, 7:47 PM] I'm His Mrs: PART 3.CHAPTER 6.

*P. 41*

Zameta yay daga jikinsa da sauri tare da matsarwa gefe ya kame , marairaice fuskarta tayi,dauke kan sa yay gefe, yana fesar da numfashi, "sannu da fitowa Daddy's Gal", ta furta da murmushi kan fusksrta don haka taji suna faɗa mata, kuma da alama tana son sunan, bata ko kalli in da take ba, "Abieh!" ta furta tana danne abun da yake taso mata na ganinsu tsaye a tare, bai Amsa mata ba, amma tasan gaba daya hankalinsa yanzu ya dawo kanta, "lokaci na ƙurewa", ta fada tana ficewa waje, wani kallo ta bita da shi tana Ayya na yarda zata ci uban Yarinyar. "uhmmm" ya furta tare da yin gaba, wani takaici ne ya kaita bango , wato ya ma fi karfin ce mata ya tafi sai dai ya ce mata wani "Uhmmm!", mai Yar da Uban suke nufi da ita ne, Yar cin 'Daci Ya ma haka, da wane zata ji ?. Cikin natsuwa yake taka Steps din fita daga babban palon har ya fito, gurin mota ya nufa. tun da ya fito itama ta kuresa da kyawawan idanunta tana kallonsa tana jin kaso 77 na damuwarta yana tafiya.

Yana ƙarasowa gurin ta dauke idanunta daga kan sa, ta mayar da hankalinta kan wayar, ƙusa da ita ya zauna, rufe motar aka yi daga waje, bayan an tabbatar da zamansa a cikin motar, cikin natsuwa Driver ya fara tafiya da mota har suka fice daga gida. hannayenta taji ya riƙe tare da matsowa da ita kusa da shi, jikinsu na gugar juna, cikin ƙasa da murya yace "kina Azabtar da Abieh'nki , baki damu da halin da zai shiga ba , in mutu ko in yi rai ke babu ruwanki", ya fada yana wasa da yatsun hannunta, hawayen da suke ƙoƙarin zubo mata ta fara ƙoƙarin mayarwa. "ko da yake in na mutu ma baki da damuwa", ya fada yana sakin hannunta ya jingina da jikin mota, idanunshi a lumshe, kan cinyarsa ta kwantar da kanta, hawaye na zubo mata, tace "Abieh ni kam na kasa jurewa , bana jin zan iya zaman fari ciki a cikin wanchan gida, zan koma England kawai , ko ka kai ni wani guri," ta fada cikin Asalin kishi, shafa kanta yay cikin son kwantar mata da hankali, ya manna lips dinsa a kunnanta, yana fada mata magamganu masu kwsntar da hankali , da sanya sanyi a cikin zuciya, Abun ka da Shaƙuwa da sabo tuni ta watsar da komai suka ci gaba da fira, har aka iso Airport , lokacin da suka isa bai fi minutes a rufe jirgi ba ma, cikin sauri suka wuce ciki. suna shiga aka rufe ƙofa, ba da jimawa ba kuma jirgin ya tashi.

Hannunta na sarke da nasa, kanta akan kafadarsa suna fira, har barci ya fara daukarta, gyara mata kwanciya yay don ta fi jin dadin yin barcin sosai, ai kuwa ba jimawa barci mai nauyi ya dauketa, don dama ta jima bata barci , damuwa ta hanata saƙat, ko ta fara barcin bata iya mai nisa zata farka, shima bai san lokacin da barci mai nauyin gaske ya daukesa ba, duk da A zaune suke, amma sun yi barci mai dadi da nauyi, wanda suka dade ba suyi irinsa ba, har sai gab da saukarsu ya farka ita kuwa har suka sauka bata farka ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull