Kenza eBookz

Arman maleek book 1 complete - Chapter 21

Arman maleek book 1 complete - Chapter 21

Arman maleek book 1 complete Chapter 21: Arman maleek book 1 complete Chapter 21. Ko da jirginsu ya sauka, haka ya ci gaba da zama, kanta na kan cinyarsa,…

4,429 words

Ko da jirginsu ya sauka, haka ya ci gaba da zama, kanta na kan cinyarsa, tana barcinta cikin natsuwa da kwsmciyar hankali, shi kan sa idanunsa a lumshe suke kamar mai yin barci, sai dai bakinsa sam bai gushe da Ambaton Allah ba, kusan 1 hour da saukarsu, wata Ma'aikaciyar cikin jirgi ta shigo gurinsu, cikin harshen turanci tace "Ƴallaɓai jirgin ya jima da sauka amma baku sauka ba, ko lafiya ?", hannunsa ya daura kan lips ɗinsa Alamar ta yi shiru kar ta tasheta, cikin burgewa take kallon yarda yake gyara mata kwanciyarta cikin kafa-kafa don kar ta tashi, "Best Couple!", ta furta da murmushi sosai. kallon ƙasa-ƙasa yay mata, tare da mayar da idanunsa a kanta.

hannunta ya dan danne mata, cikin barci ta turo baki tare da furta "Uhmm-Uhmm Abieh!", ta furta a shagwaɓe tana ƙasa manna kanta a mararsa kamar zata shige ciki, "Sleeping Beauty!", ta ƙara furtawa, motsi ta dan yi , hakan yasa ya kalleta , cikin bada Umarni yace "get out", ya furta cikin natsuwa da kamilalliyar muryarsa mai cike da haiba mai tattare da kamala da natsuwa tare da sanin ya kamata.

Rusunar da kanta tayi cikin rarrashi tace "A fito lafiya", ta fada tana saurin ficewa ganin ransa ya dan ɓaci, Agogon hannunsa ya kalla, cikin dan fesar da numfashi ya daura tafin hannunsa akan fuskarta, ɗumin hannun na dan ratsata ya fara kiran sunnanta "Babyluv! Babyluv!! Luv!!!", ya furta a hankali, ita ma cikin natsuwa da shagwaɓa ta fara buɗe idanunta, wsnda suke cike taf da barci , idanunshi ya dan bude a kanta, cikin salon magana yace "za mu zauna ne a ciki ?", sarai ta gane mai yake nufi sai ta ƙara langwaɓar da kanta tare da kifawa akan cinyarsa, ya zamana kirjinta gaba daya yana kan cinyarsa, jikinsa ne ya fara rawa sosai, duk yarda ya so ga sai-saita kansa kasawa yay, sai ya rumtse idanunsa sosai, yana kiran sunan Allah , kafadunta ya kama ya ɗagota, tare da zubawa fuskarta idanu, cikin shaƙaƙƙar murya da bata fita sosai yace "tashi mu tafi gida", zubawa fuskarsa idanu tayi, da sauri ya dauke idanunsa daga kanta, don ya fuskanci yarda yake da fasahar fahimtar abubuwa daga kallon idon mutum itama nata idanun suna kallo mata abubuwa da dama, miƙewa tsaye yay, tare da baza Alƙyaɓɓarsa, ya rufe dukkan jikinsa, hannunta ya kama suka fito, kanshi a kasa suke tafiya , sai kara baza Alƙyaɓɓarsa yake gani yake kamar shi daya mutanan da suke gurin suke kallo kuma kamar sun san mai yake ɓoyewa.

Motocine sosai a gurin na gani na fada,na bugawa a jarida 16 ya bude mata ta shiga, shiga shima yay, ganin tana niyyar komawa jikinsa yasa yay saurin jawo Jakar laptop dinsa,ga daura akan cinyarsa, a ƙoƙarinsa na son danne abun da yake ƙoƙarin fallasa sirrinsa.

kanta ta jinginar akan kafadarsa,numfashi ya ci gaba da fesarwa cikin gajiya da abun da yake damunsa, suna shigowa layin ta ringa bin gidajen gurin da kallo yarda kasan ta shekara biyar bata zo Anguwar ba, gidanta take ta kallo, ganin an chanja mishi fenti an yi masa saɓaɓɓin abubuwa sosai, sai da suka shiga cikin gidan ta kallesa cikin farij ciki da zumuɗi tace "Abieh gyaran nan fa", watsa hannayensa yay , yana kallon beautiful point dinta da yake lomawa ciki , saboda murmushin da ta kasa ɓoyewa, fitowa suka yi suka shiga cikin gidan , komai da yake cikin palon an chanja mata shi, ya koma pink da fari , Favorite colour nata, ko ina ta shiga bi da kallo, duk in da ta kalla sai ta ga wani wanda zai sa ta farin ciki.

ga manyan Pics nata ita da shi, wani ita daya wani ita da shi da Sadiyya lokacin tana ƙarama, wani su da su Amah ,wasu gaba daya Ahlin , wasu ma bata san an dauketa ba. tsayawa ta yi tana kallon wani pic da yay mugun bata mamaki, tama tsaye a compound din gidansu na Saudi, daga ita sai wata Yabidaddiyar rigar barci, tana tsaye ta daga kanta sama ruwa na dukan fuskarta, tayi wani murmushi da ya bayyana kyawawan fararan haƙoranta da suke a jere.

ta jima tsaye a palo kafin tayi bedroom nata, tana tana ɓudewa pic na farko da ta fara cin karo da shi, pic dinta na Jarintaka , da ya yi bala'in kyau , komai na bedroom din kuma Blue ne da fari, ɗaki yay abun sai godiya, karo na ba adadi ta saki wani yalwataccen murmushi mai nuna jin dadi, bathroom shige tayi wanka , bayan ta fito ta shirya cikin kayanta da ta saba sawa, riga da wando, sai dai yau wandon palazzo ne , wanda ta daura sa har kan ciki, ya bayyanar da hips nata.

cikin sauri ta shirya, ƙara min gyale ta sa, da wani glass Gucci pink yay mata kyau sosai, hand bag ta dauka da shoes duk pink ta fito, kwanƙwasa ƙofar da yake tayi, daga ciki aka ce "shigo", tura ƙofar tayi , daga bakin ƙofa tace "Abieh ina da Lecture yanzu , bari naje ", ta fada daga bakin ƙofar da take.

"Zo!", da sauri ta shiga ta zauna a gefensa, tana kallon takardun da yake dubawa, kallonta yay tare da cewa, "buɗe bedside drawer din chan", da sauri ta je ta bude , tana kallonsa, "dauko key'n ciki ," daukowa ta yi tana kallonsa, fuskarta da murmushi sosai don tasan motar ta ce, da gudu ta ruga bai an ƙara ba yaji ta faɗa kirjinsa, ta wani rungumesa, cikin hawayen farin ciki , tace "Wayyo Abieh ni kam yau kana kashe mi da farin ciki, saɓaɓɓin kayan gida, sabuwar mota, saɓɓin kaya, sabuwar waya, komai sabo, I Love you so much Abieh, i love you!! love you more , ina kaunarka , kaunar da ban san iyakarta ba, ina kaunarka fiye da yarda nake son komai a rayuwata, Abieh mai zan ma na saka maka, "cikin hawaye tace "bari da abun da zan saka maka da shi sai dai nace , Allah y shirya maka Uzuri'arka, Allah y dai-daita kanta, Ubangiji ya ƙare maka su, ya hana shaiɗan cin galaba a kansu, Allah y shirya maka niiiiii", ta fada da karfi tana ƙara rungumesa.

Murmushin wautarta , da kuma dadin Addu'arta yay, cikin farin ciki yace "Ameeen thumma Ameesn y Ar-rahman rahimeen, Allah ya shirya min gabanki da bayanki, Allah yasa ki dai na shigar nan da kike ki koma shiga irin tamu , ya kuma bani ikon ƙara riƙe Alƙawarin da na dauka" ya fada yana dagota tare da kissing na goshinta, da sauri ta sakesa tayi waje tare da cewa "sai na dawo Abieh", tana faɗa ta yi ficewarta. .

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya satinsa daya ya koma Saudi, sakamakon kiran gaggawa da ya samu daga gurin Sheikh Abdurrahaman Ibn Aliyu , hakan yasa ya tattara ya koma yana mai mata fatan Alkhairi.

©©©

Zaune take a palo tana kallon wani tafseerinsa da aka sa a TV , hankalinta gaba daya ya dauku akan kallon TV'n ta ji wayarta tayi ƙara alamar shigowar Saƙo, har ta share ta jawo wayar, saƙon da ta gani ne yasa ta tashi zaune tana ƙara kallon wayar, alert ne na 500M , duba sunan wanda ya tura mata kuɗin tayi, babu suna, babu sunan bank, cike da mamaki take kallon wayar , ta dai san bata yi da Abieh'nta zai tura mata kuɗi ba, gashi wannan account din ma personal Account ne, ko Abieh'nta bai san da shi ba, number bank dinta ta kira, bayan ta musu bayani suka ce, sai da aka yi sunyi ƙoƙarin dubo wanda ya turo kuɗin amma basu samu wani Details akansa ba, bank din da aka turo kuɗin ma bana ƙasar bane don basu da irin Bank din a ƙasa, godiya ta musu ta kashe wayar, jikinta a sanyaye.

Bata da Lecture ranar SBD Week End ne, hakan yasa ta shirya zuwa Super Market , tafe take a motar ta, ta ƙure volume na karatun Al-qur'ani , cikin zazzaqar muryarta take bin karatun, tana sanye da Abaya Maroon colour ta yane kanta da gyalen Abayar, ta sanya ta kalmi baƙi da jaka baƙa, hannunta na sanye da Agogo, parking tayi a babban super market din ta fito sai da ta rufe motar ta shiga ciki, tana tafiya cikin natsuwa, Manyan turaruka masu dadi da mugun tsada ta siya, manyan Abubuwa ta siya masu tsada sosai, kama daga kan abun da zata sa har wanda zata yi Amfani da shi.

bayan ta gama ta dawo gurin biyan kuɗi, wayarta ta shiga dannawa, tana dan tauna chewing gum, bayan ya gama haɗa kayan yace "Madam 5M ne kuɗin", jakarta ta buɗe ta fitar da ATM dinta ta miƙa masa, ƙin ƙarɓa yay, kallonsa tayi tare da cewa "karɓa ka cire", girgiza kansa yay tare da cewa, "ai wani mutum ya biya, gama chanjinki", ya fada yana miƙa mata dollars na England, raper , da sauri ta matsa cikin tsorata tace, "Hey Malam Are you a mad , ya zaka bani wannan Uban kuɗin daga zuwa Siyayya, ko kana yankan kai ne, waye wannan mutumin haka ", cikin yar dariya yace ", Madam cewa fa yay na baki chanjin nan in kin gama siyayyar k...", wani gigitaccen mari ta sakar masa, cikin ɓacin rai tace "am i your Age mate ? ina tambayarka kana min dariya, sai nasa a daureka , in da har ka mutu iyayenka ba zasu san in da kake ba Stupid" ta fada cikin tsawa, don ta mugun tsorata da kuɗin, zasu iya kai wa 100M a kuɗin mu na nan Nigeria, cikin tsorata yace "Sorry Madam , i don't no Even his name, bazan iya gane ko waye ba, yay sa face mask a fuskarsa", ya fada jikinsa na rawa, cikin mugun tsoro da ɓacin rai, ta fice bata ko tsaya ta ƙarɓi kayan ba, yana kiranta tayi banza da shi.

bata tsaya ko ina ba sai gida, tana zuwa ta yi parking a parking space ta wuce ciki, turus tayi ta tsaya a palo, tana bin kayan da suke ajiye a ƙasa kallo, ƙarasaww tayi ta shiga duba kayan, da sauri ta jaa baya sai kuma tayi waje, kiran get man ta shiga yi.

da gudu y ƙaraso, cikin fada tace "ina kiranka ka bar ni kamar mahaukaciya", cikin ladabi yace "Sorry Maa", bata kulasa ba tace "waya kawo kayan palon chan ?", cikin rashin sani yace "wane kaya ?", kayin ya farga ta daukesa da mari, cikin ƙufala tace "ina tambayarka kana ƙara tambayata ?", ta fada tana kallonsa, idanunta sun yi jaajir, cikin rashin sani ga kuma zafin marin da yake ɗawainiya da shi yace "ban sani ba wlh, bani bane, kuma tun bayan fitarki babu wanda yazo", da gudu ta nufi ciki hankalinta a tashe, tana shiga tayi karo da wani dan Box mai kama da gift , da sauri ta fara budewa . farar paper ce ts fara faɗowa daga ciki. da sauri ta dauka ta fara karantawa.

mai yake shirin faruwa da ita yau ne ?. mai hakan yake nufi ?. shin waye yake mata abubuwa iri-iri haka,? waye yake ɓarin kuɗinsa haka ?. ku a ganinku waye wannan...

Mu haɗe a Comment Section , [5/15, 7:47 PM] I'm His Mrs: PART 3.CHAPTER 7.

*P. 42*

"Pinky!" ta gani a rubuce, kanta ne yay mugun daurewa, sauran akwatin ta shiga dubawa, wani kyakyawan zoɓene mai ɗigon Diamon , y tsaru iya tsaruwa, ya yi kyau sosai, "i hope zaki so kyauta farko daga gare ni", ta gani a jikin wata Ƴar takarda da aka ajiye a gefen zoɓe, zube zoɓen tayi ta wuce sama da gudu ba tare da ta dauki komai daga cikin kayan ba,.

Wasa wasa haka ta ringa ganin saƙuna da kyautuka, na ban mamaki kullum da salon da za'a fito mata da shi, har abun ya dai na bata tsoro sai mamaki, na irin duƙiyar da ake ta narkar mata, gashi yaƙi ya bayyana kansa ko shi waye, gaba daya kuma duk kaysn da aka kawo bb abun da ta taɓa, suna ajiye a guri daya.

©©©©©

Zaune take cikin shigar da ta saba yi, kanta ba dan kwali, kallo takea Wayarta, lokaci daya ta ji yana yin ta yana chanjawa, wata kyakyawar Atishawa mai karfi ta yi, maimakon Ambaton Sunan Allah da neman gafara, sai ta ƙyaƙyace da dariya, dandanan idanunta suka shiga numshewa kamar mai jin barci, baya ta shiga yi har ta kwanta luf kan kujera, tana jin gaba daya jikinta ya mutu, gashi ta kasa Ambaton sunan Allah ko kaɗan, don gana daya jikinta take jin yay mata nauyi, ta kasa daga ko ina har bakinta ta kasa ɗagashi tayi magana, kamar wadda aka daka ko ruwa ya ci haka tayi luf tana sauraron saɓɓin lamurran da suke shigar mata kwanya da ma tunani baki daya, tana ji Wayarta tana ring a kusa da ita amma ta kasa daukar wayar sai binta da take da kallo har ta tsinke, sai da aka jera kira biyar tana kallo ta kasa dauka. ta jima a gurin yana yin bai saketa ba sai da tayi barci mai nauyin gaske kafin abun ya saketa. sai dai gaba daya jin ta take tamkar wata sabuwar halitta.

ƙiri-ƙiri tana ganin lokacin Sallah yana wucewa amma ko niyyar tashi ta je tayi bata yi ba, wasa-wasa lokacin Sallah ya ringa wucewa Amma tana gurin bata tashi ba, sai dare ta tashi ta tafi Bedroom dinta, yau ko shirin barci bata yi ba da kayan jikinta ta kwanta, ƙin ɗaukarta barcin yay tayi ta juye juye, amma da kyar ya dauketa. 12 na cika,kamar an Mintsineta ta tashi, ji tayi A duniya babu abun da take son yi irin rawa, rawar ma a Club , da gudu ta tashi ta shiga Bathroom wanka tayi, ta fito tana tafiya tana tsane jikinta, da sauri sauri ta fara shiryawa don jin zuciyarta take tana azalzalarta jikinta kamar ana hura mata wuta, cikin 10 minutes ta shirya cikin wani mini skat , sai wata riga mai ƙaramin hannu da ta sauko mata har kan cibiya, bata dauki gyale ba sai gyara kanta da tayi ko wayarta bata dauka ba ta figi keyn mota tayi waje, Sabuwar Motarta ta dauka, tun daga parking Space take matsa horn har bakin get, Get man kuwa tun horn din farko ya bude mata get don yasan masifarta, yanzu ta fara masa faɗa, yanzu ta koyi masifa , kowa tsoronta yake.

Tana hawa titi Motocu suka shiga matsa mata hanya, saboda yarda take tsula gudu , gashi duk wanda ya kalli motar yasan dole wani ƙusan Gwamnati ne ko wani Hamshaƙin mutum a ciki, kai tsaye 5 Star Club ta nufa, in da tasan na Manya ne, shigarshi ma sai ka zube Maƙudan Kuɗaɗɗe an baka Ticket kafin ka shiga, tana zuwa ta bada kuɗi aka bata ticket ta shige, tun daga ƙofa kiɗan yake ɗibarta, har ta shiga ciki, tana shiga gurin ido ya dawo kanta, don dole ma ɗiyar wani Hamshaƙi ce tunda aka ganta gurin , dan babu Yaran Talakawa , Futsararru kuma Ɓarayin Yaran Masu kuɗi ne da suka gagari maganar Uban kowa, masu ɗibar Kuɗaɗɗen Iyayyensu suje su yu facaka da su, tana shiga aka shiga kallonta , ita ma kallon kowa take dai-daya tana dan Nazartarsu, kafin ta ƙarasa shiga ciki, wani Matashin Yaro mai ki da kyau , kuɗi amma kallo daya zaka masa kasan Christan ne, sakamakon cross da wasu ƙacoci da suke jikinsa, ya tsaya a gabanta, "Hi ! am Joseph Michel .And You ?" ya furta yana miƙa mata hannu, hannunsa ta kalla ta kalli fuskarsa, gutun murmushi tayi kafin tace "Hllo!", tana fadar hk ta shigs ciki, in da aka tanadar domin yin rawa ta nufa, a hankali ta fara rausaya jikinta, ganin yarda take rawar ne cikin sigar jaan hankali yasa DJ din ya sanya wata Waƙa mai dadin gaske wadda duk yarda kaso ga ƙin mayar da kai ka jita sai ka rausaya, ai kuwa zagewa tayi sosai tana rawa, tuni maza da matan da suke gurin suka rufa mata baya, suka ringa rawa, in da zata samu ruwa ta shiga duddubawa, kamar daga sama aka miƙo mata wani cup , karɓa tayi don taga abun cikin cup din yay mata kama da da ruwa, hakan yasa ba tare da wani tunani ba ya kafa kanta, wari da ɗacin da ta ji ne yasa ta ɗan dakata, sai dai kamar an kwaɓa Abun cikin bakinta, haka ta juyesa, mai kuma mata lokaci ba gurin shigewa cikin cikinta, zare cup din tayi tana matse fuska, saboda ɗacin Abun har ya wuce Misali , cikin ƙanƙanin lokaci ta fara ganin bibbiyu, hakan yasa ta fara laluɓen gurin ficewa daga Club din, tana fita ta faɗa motarta .

Ikon Allah ne kawai ya kai ta gida lafiya, don idanunta har rufewa suke, ko da ta ƙarasa gida dakyar ta iya fitowa daga mota ta shiga ciki, a ƙasan palo ta kwanta, da sauri ta miƙe tana yunƙurin Amai, Aman ta fara bulbulawa marar wanda bb komai a cikinsa sai wani irin tsami da warin giya da yake tashi, tana gamawa ta faɗi nan sai barci.

Cikin Abun da ba zai wuce Sati ba gaba daya rayuwarta ta hargitse, komai nata Ya lalace, bata Sallah bata salati School ma ta dai na shiga komai ya taɓarɓare mata, ga zuwa Club don bb ranar da zata shuɗe bata jee ba,don yanzu ma ta zama Top Popular , in taje bata bada kuɗin shiga take shiga,kuma komai take son sha na daga kayan shaye-shaye za'a kawo mata banza, yanzu bb abun da bata sha na kayan shaye-shaye, ita da ko Abokai mata bata da su Amma yanzu tayi Abokai har da Maza. da da ko hannunta bata bari Namiji da ba Muharraminta ya taɓa ba, yanzu hannun maza har kan west nata ,Ɗabi'unta gaba daya sun chanja, ita da bata da raina mutane ko girman kai duk ta koya, ita kanta abubuwan na damunta amma babu yarda ta iya, tana son bari Amma abun ya faskara, gashi Abieh'nta ya yi ƙaurawa garin, sai dai y kirata, da kuma ya gama jin lafiyarta zai kashe wayar, ya daina janta a jiki yarda zai fahimci damuwarta duk da tabbas ya ji alamar tana da damuwa, amma ya rasa abun da yake daukar hankalinsa ko ya rufe masa baki ta yarda yake kasa tambayarta.

Zaune take tsakiyar palonta, da Kwalaɓe a gabanta, hawaye ne ke fita a idanunta, zafi take ji a cikin zuciyarta amma ta rasa wache Addu'a ce ma zata karanta ta yaye ƙunci da damuwa , A hankali ta fara jin kukan wayarta, da sauri ta tashi ta nufi bedroom dinta, don ƙarar wayar kawai ta ji ta san wanda yake kira.

ko da ta dauki wayar faɗawa tayi kan bed, ta kara wayar a kunnanta, ba tayu magana ba, haka ma wanda ya kiran bai yi magana, numfashinsa mai sanyi da saujar da natsuwa ya shiga fesa mata, cikin sanyi da son kwantar mata da hankali, yake mata wata sanyayyiyar waƙar larabci mai dadi, cikin golden voice nasa, mai sanyi gaske, don ba da ban kar tayi karya ba da zata ce, muryarsa ta fi ta Abiehnta dadi, domin a duk lokacih da take neman natsuwa, da ta tuna ɗaɗɗaɗar muryarsa da yarda ta iya kalami mai dadi sai ta ji duk damuwarta ta gushe, wani barci mai dadi na zuwar, mata har mamaki take yi, an ya ba Aljani bane ?, gashi harshenta yana mata nauyi a gurin tambayarsa shi waye ?.

Shima kuma bai taɓa gaya mata shi waye ba, wata magana bata taɓa haɗasu ba, sai dai in tana cikin damuwa, to shine mai zama da ita , mai yaye mata damuwar da ta shiga, Allah bai taɓa haɗa fuskokinsu ba, amma a yanzu tana ji ya fi kusanci da ita, har tana gani kamar shine wanda ya fi sanin halin da take ciki yanzu .cikin ƙanƙanin lokaci ta fara jin damuwarta na wucewa, wani sanyi na ratsa gaba daya zuciyarta , wata natsuwa na saukar mata, wata kamala da ilhama take ji.........

Sorry for the Shot typing. da babu gwara ba dadi🤭

PART 3 CHAPTER 8.

*P. 43*

Kamala da Ilhama take ji a cikin jikinta, sai da ya tabbatar da tayi barci Numfashinta na sauka cikin natsuwa dai daya, kafin ya kashe wayar , numfashi ya jaa cike da tarin damuwar halin da take ciki, tabbas yasan ba haka halayenta suke ba, sannan yasan ƙaddara ce aka ƙaddarceta da ita, yasan dama dole in Allah y ma baiwa ta wani ɓangaren,to fa tabbas dole ya jarabceka ta wani ɓangaren, kamar dai Mahaifinta, yana da sannaya kansa sosai, shi masani sannan mai tafseerin Al-qur'ani ne,Sannan Limami a ƙasa mai tsarki , ƙasar da ta fi ko wace ƙasa a duniya, ƙasar da Manzon Allah y rayu, tsawon shekaru. yanzu y ƙara tabbatar da cewa bb wanda y fi karfin Jarabta ta faɗa masa, sai dai kayi roƙon Allah yasa komai ya zamana ya zo da sauƙi.

Muskutaww yay kan katafaran gadonsa mai kyau, gaba daya ɗakin zagaye yake da pics nata kala kala, wani tana tsakiyar filin rawa, wani tana tsaye, wani tana zaune, wanda ya fi daukar hankali, tana tsaye ta dan juya ba, tana gyara gashin kanta da ya zubo mata akan fuskarta, kuma bb daya da tasan ana mata , duk ba tare da saninta aka dauka ba, kan kirjinsa ya daura photon ya matsesa a kirjinsa yana fesar da numfashi mai sanyi cike da natsuwa.

Bata farka ba sai da ta fara jiyo kiran Sallar Assalatu, tun kiran farko ta farka, sai dai ta kasa tashi tana gurin har aka gama kira aka shiga Sallah, har aka tada bata miƙe ba, tana dai kwance tana son miƙewa, Amma wani nauyi take ji ya danneta, wanda yasa ta kasa tashi tana dai nan kwance har aka fito, sai da gari ya yi haske sosai kafin ta tashi, bathroom ta nufa, wanka tayi da Brush ta fito palo, tsayawa tayi tana kallon yarda palon gaba daya y hargitse , cikin dan sauri ta shiga tattare kayan da ta baza a palon, gaba daya kwalaɓen gurin ta tattarasu ta sanya a, shara gyara palon tayi, cikin ƙanƙanin lokaci,ya dawo kamar ba wanda yake a hargitse ba.

Zama tayi a Palon tana tunanin mai zata samu ta sawa cikinta, ƙaramar wayarta ce ta fara ring, da sauri ta dauka don ringtone nasa ma da ban yake, kwanciya tayi kan kujera,cike da natsuwa da kuma shagwaɓe tace "Chuɓaɗo!", ta fada idanunta na cika da hawaye, "ka manta da ni gaba daya, naka damu da halin da nake ciki ba, baka damu da ina da damuwa ko bana da ita ba,baka damu da kazo ka ganni ba, kira na ma baka yi , an zo an kawo ni nan an bar ni ni daya,ina Maraicin Ammyna na tabbatar da tana raye ba zata bar ni nayi nisa da ita ba, ba zata bar ni a gantale ba, zata yi iya iyawarta na ganin ta ji damuwata ", ta faɗa fuskarta sharkaf, "in kin gama ki buɗe min ƙofa", ta ji ya fada cikin sanyi sosai, yana kashe wayar, duk a tunaninta wasa yake hakan yasa, bata tashi daga in da take ba ta ci gaba da kukanta.

ƙara kiran wayar,kamar ba zata dauka ba ta dauka, cikin kaushin murya yace "kika ƙara minti daya baki buɗe ƙofar nan bana shigo zaki raina kan ki", y ƙarasa fada cikin dan fushi, da sauri ta nufi ƙofar ta bude, tsaye ta gansa,cikin shigarshi ta kamala mai kara masa haiba da kamala a ko yaushe, "Abieh!", ta fada tana fadawa jikinsa, kasa riƙe kukanta tayi ta saki kuka da karfi kuka mai nuna A'lamar zallar kewa da shaƙuwa da kuma muguwar damuwa, mai tunkeshe rai , hannayensa ya daura a bayanta yay Hug nata Very tight , yana jin kukanta har cikin ransa, jin sa yake yana masa wani kuɗa a cikin kunnuwansa, tana daya daga cikin matan da yake mugun girmamawa, ya kuma tsani ganin ko ɗigon damuwarsu balle ɗigon hawayensu, cikin damuwar da ya tsinci kansa a dalilin ganin ta ta damuwar, ya ƙarasa da su kan kujera, zama yay tare da saurata akan kujera, ya riƙe kafadunta yana kallon yarda hawayenta masu daraja, abubuwa mafi tsada a gurinsa, yana kallon yarda suke zuba, tarba hannayensa yay hawayen na zuba a cikin hannunsa, cike da matsananciyar damuwa yace " Sweetie honey pie mene kike kuka ?", ya fada yana cire mata hannunta akan idanunta da take kuka kamar Yarinya, ƙara shigewa jikinsa tayi, tayi luf ,jikinta na dan rawa, hannunsa ya dan sanya a wuyanta cikin damuwa yace "kukan nan ya fara sawa sa miki zazzaɓi, in ba kiyi farin ciki da zuwana ba, sai na koma", ya fada yana ƙoƙarin miƙewa, da sauri ta riƙeshi tare da goge hawayenta tace "na dai na Chuɓaɗo!", ta fada tana kallonsa, murmushin gefen baki da ya lomar da Dimple din sa da yay matuƙar ƙara masa kyau ya yi, shagala tayi da kallonsa, shima idanu ya tsura mata, yana hango wasu sauye-sauye da yawa a jikinta da ɗabi'unta ma gaba daya, "Honey Pie!", ya Ambata muryarsa a kamile cike da haiba da kamala da tsananin dattaku, ya fada yana zama kusa da ita, cikin sanyi tace "Merri!" ta fada a hankali tana haskesa da fararen idanunsa.

Juyo da ita ya yi, yarda zata fuskancesa, ya riƙe hannayenta Alamar Maganar da za suyi mai matuƙar Muhimmanci ce, jaan numfashi ya yi cikin rashin makamar kama maganar da zai mata, gaba daya zuciyarta itama ta tsinke sai wani dar dar take ji wani tsoro na musamman take ji da fargaba, duk da bata san maganar da zai mata ba.

©©©©©©

"Yanzu gaba Daya Rayuwarta ta tarwatse, sai kuma musan yarda za muyi mu buga Mujallar da zata Yaɗu gaba daya kasa, ta yarda zamu fallasa Asirin abun da Ƴarsa take aikatawa, da haka zamu lalata takararsa, don duk wanda yaji abun da take aikatawa ba zai yarda ya zaɓesa ba, hakan kuma zai yi sanadiyar cireshi a majalissa, kaga mun lalata dukkan wani ƙarfinsa a gwamnatance, sannan kuma mun jefi tsuntsu biyu da dutse daya kenan", Alhaji Sammani ya fada yana dariyar Mugunta.

"Kaiiiii gaskiya Alhaji Sammani kai mugu ne, duk wanda ya faɗo hannunka sunansa Sorry, in kana wani abun har mamaki kake bani ni ban ma san a ina ka koyi tuggu iri-iri haka ba," Alhaji Auta Baita ya fada yana kallonsa cike da mamakin irin tuggun da ya iya haɗawa haka.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull