Arman maleek book 1 complete - Chapter 22
Arman maleek book 1 complete Chapter 22: Arman maleek book 1 complete Chapter 22. rausayar da kansa yay kafih yace "Alhaji Auta Baita ka manta da…
4,381 words
rausayar da kansa yay kafih yace "Alhaji Auta Baita ka manta da gwagwarmayyar siyasa ne ?, ai duk wanda yake cikin siyasa dole ya iya tuggu da Makirci , Asirce-Asirce har ma da Tsafi, ko da baka iya ba ka haɗu da wanda suka iya dole ne kai ma ka iya , ina tare da ku ma ban iya Tuggu ba ai sai na bar Jam'iyya", ya fada yana dariya, gaba dayansu jinjina kai suka yi domin sun san, Wani sharrin sai Siyasa , ko baka iya hassada, Mugunta, Tuggu, Makirci da Asirce-Asirce da tsafi ba sai an koya ma.
"hakan na nuni da cewa lallai kai rainon Jam`iyyar Fata-fata Party ne", ya fada yana masa jinjina, murmushi yay cike da jin dadin karɓar shawararsa, domin shi yake son yin takara a shekarar, shi yasa ya dage sosai domin yaga gaba daya Abokan Takararsa sun faɗi saura shi daya ya rage.
©©©©©©©
"Bro's kar ka mata haka, a gani na abun da ta maka bai kamata ace kayi ramuwa da haka ba, ina ma laifin ka rama marin da ta maka, amma wannan Acid din sam bai kyautu da ace ka zuba mata a Fuska ba, kar ka manta ita din mace ce mai kuma rauni,hakan zai iya Affecting na life nata ", Mansoor ya fada cikin Yar damuwa. taɓe bakinsa yay cike da son Aiwatar da mugun nufin da yake son aikatawa a kanta yace , "Uhmmm ai in ban lalata abun da take taƙama da shi ba har Abada rai na ba zai daina zafi ba, na tsaneta,mai kaunarta ma na tsanesa, a public ta yarfa ni, ta wulaƙanta ni, ta ƙasƙantar da ni, ta wofintar da ni, duk mutuncina da ake gani yanzu ya zube, ai Wallahi in ban wulaƙantata ba zan iya kamuwa da ciwon zuciya", ya fada cikin tsantsar ƙunar rai, da ɓacin rai.
"tunani zaka yi in su Umayma da Junaina aka watsawa ya zaka ji a ranka ?, sai ka duba ka gani itama ai Ƙanwar Wani ce, ka duba lamarin nan da kyau ni ban baka goyon bayan yin haka ba gaskiya", ya fada yana juyawa ya tafi, bayanshi ya bi da harara, tare da cewa "duk wanda yay ai masa, ko sune suka min haka sai na lalata musu rayuwa ballanta wata yar tsallan baɗage, yar tasha. ƙasƙantatta. mai rawa a club", ya faɗa yana miƙawa Yaron da yake gabansa, wanda tsaf na shaida fuskarsa daya, daga cikin Yaran fa suke Zuwa Club din 5 Star Club ne, bayani y ƙara masa yarda zai yi komai ba tare da ya samu matsala ba, bayan ya gama chake masa kuɗaɗɗe ya tafi Abunsa.... "Wa kike bari yana taɓa jikinki ?", tambayar ta daki dodon kunnanta, cikin Azama da tsorata ta ɗago dara-daran fararen idanunta ta zuba masa su cike da tsantsar firgici da tashin hankali, wanda zaka iya fuskantar hakan a kallon farko da ka mata, duj yarda taso ga son ɓoye tashin hankalinta da kaɗuwar da tayi kasawa tayi, domin karara yake hango rashin gaskiya a idanunta. yana yin yarda ya daure fuskarsa bb wasa ne yasa basira kwance mata , dama ita ba iya karya tayi ba, sam bata da basirar karya tun tana Yarinya da tayi karya ake kamata.
Rasa yarda zata yi da rayuwarta tayi, gashi ta san tun da ya fara mata wannan tambayoyin tasan da wasu ma a ƙasa ba su kaɗai bane, hakan yasa gaba daya ta tsure, ta kuma san ta kaɗe har ganyenta, "Abieh ni bb wanda na bari y taɓa min j...... Marin da ya yarfa mata ne, yasa ta datse laɓɓanta ba tare da ta shirya ba, sam ba tayi Expecting mari daga garesa ba, Abun da bai taɓa mata ba ko da wasa, balle har ya zamana dagaske, lallai tasan yau akwai gurmi cikin gidan domin tunda aka fara da mari, to kafin a ƙare killan sai dai da duka, "ni zaki wulaƙanta ?. ni zaki ƙasƙanta . sunana kike son ɓata min .? irin tarbiyar da na baki kenan ., irin sakayyar da zaki min kenan, ina tufka wasu suna min warwara, to bari kiji in ma faɗa miki daga Yau ki sani Ni Maleeq Ina da A.........
```Washhhhh Hannu na!✍🏽```
Sai kuma mun haɗu a wani jiƙon.....
End Of Book 3
07033371851
[5/30, 4:27 PM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: https://chat.whatsapp.com/JW31VMMW0W66mKkNGkr5s4
PART 4.CHAPTER 1.
*P. 44*
"Ki Sani ni Maleeq, in dai ina da iko a kan ki to kin bar Jami'ar Oxford har Abada,ke ko da ziyara ba na Haramta miki zuwanta, don nasan shigarki cikinta ne yay sanadiyyar Lalacewarki, har kika bari Kare da Doki, suke kai hannuwansu jikinki, ke kuma kamar wata marar ilimi da lissafi har kika bari wasu suke ribantarki, a tunanina duk in da kika shiga ba zaki yar da tarbiyarki ba, ba zaki bari wasu abubuwa suyi kutse wa rayuwarki ba, kin ban kunya wlh", ya fada cikin tafasar rai da hali irin na ɓacin rai, da wani maƙoƙon baƙin ciki da yake son fitowa daga maƙogwaronsa.
Ta kasa Magana ta kasa kuka, tana dai dage da kumatunta, tun da ta kafe guri daya da idanu taƙi daukesu, da gudu ta tashi ta ruga bedroom nata, ta sa key. faɗawa kan gado ta yi ta saki kuka mai karfi, ranta take jin yana mata zafi, tunani ta fara yi don mai ma zai mata wannan fahimtar ba zai zauna ya duba abun da ya jefata wannan halin ba, ba zai yi tunanin hakan ba halinta bane, wayarta ta ji tana ring da sauri ta dauka don ta san shine kawai zai iya fuskantar halin da take ciki, tana son ta faɗa masa Abieh'nta ya tsaneta ya daina shiga cikin Al'amurranta, tana dauka ta ƙara fashewa da wani kuka mai nuna zallar damuwar da take cikin rai, ƙarfaffar Ajiyar zuciya yay , kamar ta mayunwacin zakin da ya yini Farauta bai samu komai ba sai yanzu ya samu Abin ci, irin Ajiyar Zuciyar da Yaran kan yi a lokacin da suka ci kuka har suka gode Allah, irin Ajiyar da masoyi kan yi a lokacin da ya dauki tsawon lokaci bai ji muryar Masoyiyarsa ba, Ajiyar zuciya ta zallar marari da muradi.
"Mai sa yanzu duniya ta juya min baya ne ?,mai yasa Abieh na ba zai fuskanci duk abun da nake ba halina ba ne, ba ɗabi'u na bane , ba da son rai na bane ?,mai yasa ba zai gane cewa Ƙaddarar da bata wuce lokacinta bane ya faɗa min, a tunanina zai dauki ƙaddara akan komai da zai sameni, mai zai sa yamin gurguwar Fahimta ?, mai zai sa ba zai fahimce ni ba ?,mai yasa ba zai sani a jikinsa yay lallashina a lokacin da nake tsananin buƙatar lalashinsa ?, mai zai sa ba zai zauna da ni ya ji damuwata ba ? kawai ya dauki karan tsana ya daura min, Abin da bai taɓa min ba yau ya min, Abieh'na ko kallon da bai kamata ba bao taɓa min ba,balle faɗa bai taɓa min, Amma Yau Abieh yasa Hannu ya mareni , yamin faɗa, ya zazzageni Abieh yana kirana da Marar Ilimi. gaba daya duniyar ina jin na ƙuntata bana son zama a cikinta, don in ba a zauna dani an lalashe ni an kwantar min da hankali ba, an nema min maganin matsalata, a ganina duka ko zagi ba zai ba, kuma ba zai sana dai na abun da nake ba, ni kai na nasan kaddara ne, kuma bata wuce hawa kam kowa ba, Amma mai yasa shi din bai fahimci hakan ba ?", ta fada kamar zata shiɗe tsabar kukan da take ga magana da take cikin kukan, wanda hakan yay sanadiyar da numfashinta yake yin sama har kamar zai tsaya.
Cike da damuwa cikin ɗaɗɗar muryarsa da bata taɓa jinta a magana ko lallami ba sai dai y mata waƙar soyayya mai kwantar da hankali wadda a iya ita da yake mata ne yake sama mata da kwanciyar hankali, har take jin ta mishi kuakyawar shaƙuwar da take jin sa har a ranta, "baki san Dalilinsa na yin hakan ba, baki da hujjar da zaki tuhumaisa akan ya mareki ko ya dakeki, domin shi yasan abin da yake, kuma ba zai taɓa lafiyar kyakyawar fuskarki haka nan ba, na tabbatar da ransa ne yay mummunan ɓaci akan abun, sannan kuma yake ganin kaman laifinki ne, Amma ki dai na tunanij cewa kamar ya tsaneki ne, Abieh'nki mai tsananin kaunarki ne, mai ƙoƙarin kare nauyin da yake kan sa, yana yin hakan ne domin ki tsira da mutuncinki, har Abada shi din mai kaunarki ne ",cikin kasa fahimtar mai yake son ta gane tace , "So! .A da de in ka faɗi haka bazan musa ba, amma ban da yanzu, in faɗan so ne, kai mai zai hana kana min ?, sai shi . ko don yana taƙamar shine ya haifeni, ai bai zama dole ya tsara min zanan ƙaddarata,da tun kafin a Haifeni aka gama zazzana min ita ba, wannan ai salon wulaƙan...." tsawar da ta gigitata wadda tasa tayi saurin janye wayar a kunnanta yay mata.
cikin Kakkausar murya yace "ban san haka kike ba , Mahaifin naki kike ƙoƙarin faɗawa haka ?, Ashe dama baki da Ɗa'a , ina ganinki a mai ilimi wadda tasan haƙƙin Iyaye a kanta ashe ba haka bane , tun da kika faɗawa Mahaifinki haka bb wanda ba zaki faɗawa haka ba kenan, to kiyi gaggawar janye dukkan kalamin da yake bakinki sannan kiyi gaggawar tuba , sannan kuma kiyi gaggawar zuwa ki nemi Yafiyarsa, " yana faɗar haka ya kashe wayarsa.
Iya Damuwa da tashin hankali ranar ta shigesu, duk in da ta waiwaya da niyyar ta ji sanyi bb ƙofa, in ta waiwaya cikin gida ga dai Abieh'nta Amma bb sauƙi a garesa ga kuma Jaan dinta shima bb sauƙi a garesa, don tun bayan kashe wayarsa bata ƙara samunsa ba, gashi ta kasa zuwa ta bawa Abieh'nta haƙuri, don matuƙar tsoronsa da ya riga ya gama tasiri a zuciyarta take ji, gani take in taje gurinsa kamar zai duketa ne.
Abun da bata Sani ba kuma shine, tun bayan Abun bai fi da 4 hours ba ya bar ƙasar zuwa Nigeria Sakamakom kiran Gaggawa da ya samu daga gurin Mai Girma Shugaban Ƙasar Nigeria Saif-Wazeer. hakan yasa Ya bi Jirgin 12pm , 4pm tayi masa a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Lokacin da zai je , manyan Motoci ya tarar suna jiran zuwansa, yana zuwa aka daukesa sai Villa , wato Gidan Gwamnati, bayan gama karramasa da basa Abun taɓawa, bai wani ci sosai ba ya barsa, Direct kuma Babban Ɗakin taron da yake cikin Villa aka nufa da shi, in da gaba daya wasu ƙusoshin Gwamnati da suke ƙasar sun hallara,kama daga kan Yan Majalissu, Chiyamomi, Ministoci, Gwamnoni da Wakilai, dukkan dai wanda yake da hannu da shuni, wanda ake damuwa da su a Siyasance suna gurin.
Sosai Kujerar da aka basa a matsayin gurin zama ta basa Mamki sai dai bai ce komai ba, sannan gaba daya Yan Majillissun da suke gurin kallonsu yake daya bayan daya, a cikin su 10 bb wanda bai halarta ba, Amma shi bb wanda ya faɗa masa da wani Meeting sai ma kiran Urgent da ya samu, bayan An buɗe taro da Addu'a aka yi duk abun da ya dace a yi kafin fara taro. Mai Girma Shugaban Ƙasa Saif-Wazeer me ya fara taro kamar haka , "to takara na gabatowa, kuma kamar yarda kuka sani , wannan ita ce tenuwata ta ƙarshe, wadda daga ita kuma sai dai na ƙara riƙe wani Muƙami ba dai na Shugaban Ƙasa gaba daya ba, kamar yarda kuka sani, duk Wani Shugaban Ƙasa yakan tsayar da wanda yake son ya fitar a matsayin Ɗan Takararsa, sai dai kuma in bashi da ra'ayi ko kuma shi wamda ya tsayar din bashi da Interred akan hakan, sai kuna a zaɓi wani da ban." numfashi ya fesar a hankali kafin yace. "Ni a Matsayina na Shugaban Ƙasarku, na Fitar da Ɗan Takarata,wanda ina da tabbacin in sha Allahu zai yi komai kamar yarda ake buƙata kuma ba zai taɓa bamu kunya ba, Ba kowa bane Ɗan takarar ta mu face...", dan shiru yay yana ƙarewa mutan gurin kallo wanda suka ƙagu sosai da su ji wa zai ce, ban da shi wanda har lokacin ranshi a ɗatace yake, doh rabi da kwatar hankalinsa baya gurin, yana chan wani gurin daban.
"ba kowa bane Face Maleeq!", da dan sauri ya ɗago don an yi mugun Surprise dinshi da Abun don sam bai yi tunanin hakan ba, don shi Matsayinsa na Dan Majalissa ne sannan kuma Mai bawa Shugaban Ƙasa Shawara akan harkokin da suka shafi Al`umma, ƙoƙarin Shanye mamakin da ya gama kasheshi yay, don ko bai son Abu bai yarda, ya nuna a Bainar Nasi ba ,balle kuma wannan lamarin da yake da girma sosai.
Gaba daya gurin ne ya ɗinke da surutun mutane, wasu suna cewa basu yarda ba, wasu kuma suna farin ciki da hakan, don sun san mai sob talakawa ne, kuma ba zai bari ayi handama da babakere da duƙiyar mutane kamar yarda Sauran suke ba, buga tebur ya dan yi kafin yace "in ku so. in ma ku ƙi, ga takardar Takararsa nan, kuma komai da ya danganci takardunsa bb wanda bai haɗa ba, kama daga kan takardun Makaranta, Takardun Lafiya, da duk wani abu da ake buƙata , duk ƙa'idar da ake so na tabbatar ya cika sa, don haka shine Ɗan takarar Jam'iyya, kuma an haramtawa kowa da yake cikin Jam'iyya fitowa takara bayansa", ya fada yana miƙewa cike da izza, ya bar gurin, "Wannan ba Adalci bane, sai kace har yanzu ana mulkin Sojoji da baka isa kayi magana ba , kama ta yay aji ta ɓangaren Yan Majalissu donin jin ra'ayoyinsu", wasu daga cikinsu suke ta faɗa, wasu kuma sai zuwa suke suna masa Congrats shi dai bashi da bakin magana don an riga da an kashe masa jijiyoyin jikinsa.
Yana gurin har kowa ya fita ya barsa, saƙon Shugaban ƙasa ne ya ƙara riskarsa akan yana son ganinsa, bb yarda ya iya haka ya miƙe ya tafi. "Sam nasan ban kyauta maka ba, Amma Abun da nai na yi dai dai, domin tun kana Yaro nake yawan jin Mahaifinka na zancen dattakunka da mutuntawarka, da baiwarka, ban tabbatar da haka ba, sai da ka shigo sahun Yan Majalissa, shi yasa na zaɓeka a matsayin wanda zai yi min Mai bada shawara, domin na sanka da hamgen nesa tun kana ƙarami, to Alhamdulillahi, nasan gaba daya wata nasara da aka cimma a cikin wannan ƙasar tamu kai ne *SILA* ,kai ka tsaya tsayin daka, na ganin komai ya tafi Successfully , na san in kai ne akan kujerata za ka yi fiye da Abun da na yi, zaka mulki Al`umma cikin Aminci da Adalci, hakan yasa na gama maka duk wani Abu da ya kamata , ban nemi ko shawararka akan hakan ba, sai dai duk abun da na tsara da Yawun Mahaifinka a ciki, sannan bama buƙatar Sisin Ƙwabonka har a gama wannan takarar, kar ka ce komai dob Allah, na san in sha Allahu komai ba zai gagara ba", ya ƙarasa fada yana mai daure masa gaba daya jijiyar jikinsa, wanda yasa ya kasa cewa komai, ya zauna jigidun, yanz nazarin Wannan Uban nauyi da Jarfar da ake son haɗasa da shi.
A saninsa dai mulki ba ƙaramin bala'i bane, ko da an barsa haka, balle yanzu da yake da Manyan Abokan Karawa , wanda suke ƙwari sosai a cikin Siyasa, don su kawar da mutum, ko su salwantar da shi b wani abu bane, dakyar ya iya bude bakinsa, kamar yarda nai tsammani maganar tasa ba tayi wata tsawo ba sosai, cikin girmamawa yace "A gaskiya His Excellency kwata-kwata ban da Interred akan hawa wannan babban matsayin, ga masu so da yawa,ni a gani na gwara a basu, ƙillan su yi fin abun da ma ake tunanin zan yi"ya fada cikin biyayya.
Murmushin manya yay kafin yace "Uhmmm a ganin ka kenan, Amma a zahirance gaba dayansu ba zasuwa Ƙasa wani aiki ba, sakin jiki za suyi su yi handama da babakere akan dukiyar Al`umma wanda hakan sam ba kyautawa bane, Amma ka je kayi shawara dai", ya faɗa cikin mishi sha'awarar Abun sosai.
Godiya ya mishi ya fice don yana da flight din 9pm don duk dare a England yake son ya kwana, gobe kuma su wuce Saudi. yana gaf da Missing Flight dinshi , suka ƙarasa don har an rufe ƙofa ma, Sanarwa ta samu Sashen Jirgin da su buɗewa "Ɗan Baiwa kuma Limammin Limamai Ƙofa", ai kuwa cikin sauri aka bude masa ya shiga Special Side aka kai sa shi daya.
Bai Sauka a England ba sai 1am, yana zuwa ya samu Motocinsa sun zo daukarsa, shiga yay suka wuce gida, tun daga Parking Space ya lura da cewar bata gidan, haka ya shiga cikin gidan bb in da bai duba na Amma bai ganta ba, ranshi y ƙara ɓaci sosai, cikin ransa ya ƙara Ayya na cewar "Bama gidan take kwana ba kenan ? wani guri da ban take zuwa ta kwana.
©©©©©©©©
Yana yin da take ciki, da kuma yarda ɓacin rai da damuwa yay mata katutu, yasa 10 nayi ta shirya cikin kayanta wanda ta saba sawa Crazy Jeans , da Riga Ƴar ƙarama , sai takalmo da jaka , sai manyan wayoyinta guda biyu. Motarta Ƙirar Lexus x 360 , ta faɗa . cikin sauri ta tayar da motar tayi gaba.
Kamar kullum ba'a Ansa kuɗin Shigarta ba tana zuwa suka yi Shaking Hands da mai tsaron ƙofa ta shige ciki. tun da ta shiga take ganin baƙin fuskoki da sam hankalinta bai kwanta da su ba, Amma da yake bb wanda ya damu da wani yasa ta ware ta shiga harkokin gabanta, yau ko kaɗan ba tayi rawa ba, dai Uban Giyar da tasha, da sauran abubuwan mantar da tunani da ta sha.
12am ta tattara gaba daya kayanta , ta yo hanyar fita tana tangaɗi ita da friends dinta Biyu iya ta ukku, haka suka fito suba behaviours irin na Yan shaye-shaye, wasu Maza Biyu ne suka biyu bayansu, cikin sassarfa, har sun kai gurin Mota suka ji An musu Magana, Juyawa sukaa yi domin ganin mai maganar, Wani Bala'ittacen Sanyi suka ji ya ratsa fuskokinsu kamar wanda aka zubawa Ruwan Sanyi kafin daga baya wani raɗaɗi mai gigita tunani ya ɓaiɓaye gaba daya fuskokinsu da Ƙwanyarsu ma gaba daya, duk cikin sun biyun bb wanda yay salati sai Ihun da suka ƙwandama wanda ya mamaye gurin gaba daya, ita daya ce ta yi ƙoƙarin fusgo Salati dakyar .........
Past of All . zan iya cewa Yanzun muka fara fa. don Labarin nan mugun yawa ne da shi😂
07033371851
P.R.O ƳAR LELEN ROYAL STAR🫰🏾🥰 [5/30, 4:27 PM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: PART 4. CHAPTER 2.
*P. 45*
Kafin Securities su yi wani Yunƙuri Samarin su gudu. kafin Adawo kansu gaba dayansu sun suma, hakan yasa gaba dayansu basa a cikin hayyacinsu aka tafi da su Asibiti, Cikin gaggawa Aka karɓesu Sbd Munin Lamarin.
©©©©©©©
Gaba daya kasa Natsuwa yay, hakan yasa ya fito palo ya zauna, TV ya kunna yana dan kallo yana duba Agogon hannunsa, 2 na bugawa aka sanyo Labaran Duniya, Labarin da aka fara haskawa ne ya daukar masa Hankali, don batun Siyasar Ƙasar ce da ake ta taƙaddama a kai ake yaɗawa. gyara zamansa ya yi, don yana jin dadin Labaran, bayan gama nuna wa ne kuma, aka fara nuna Abubuwan da suka faru masu daukar hankali a cikin Babban Birnin Ƙasar.
Kamar daga Sama Aka nuno Abun da ya faru da su a TV , ƙara wara idanunshi yay Sosai yana kallon Abun da ake haskawan, tabbas Fuskarta ce ake haskawa a Tv da bayanin Abun da ya faru da ita, hajijiya ce ta shiga ɗibarsa, dakyar ya samu ya dafa bango, "innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un!, Hasbunallahu wani'imal wakeen!, Allahumma Ajrni fi musibati!",yake maimaitawa bakinshi na rawa, numfashinshin na wani crack , Addu'ar da yake ta maimaitawa ce yasa ya fara jin sauƙin Abun, bai tsaya sanya Alƙyabba ko rawani ba, ya figi key din motarsa ya fice, ko jiran Driver dinshi ya zo bai yi ba, shi da kansa ya bude motar ya shiga, a mugun Speed ya ɗibeta yay waje , ikon Allah ne kawai ya kai sa Asibitin Amma ba wai don yana cikin cikakkiyar natsuwar yin Driving din da ya manta rabon da ya yisa ba.
Bai tsaya ko ina ba sai babban Asibitin Birnin , a irin wannan mummunan Haɗarib yasan dole Emergency room za'a kai su, hakan yasa bai sha wuya gurin cewa zai duba word ba , dama yasan Asibitin ciki da bai, lokacin da y ƙaraso gurin Lokacin Dr Naufal Abokin Yaah Shehi na karatu, tun lokacin da yake Secondary ya fito daga Roon din, sanye da kayan likitoci da Alama ma shine Dr din, farin ciki ne ya bayyana a fuskar Dr Naufal na ganin Shehi, cikin Azama ya nufesa tare da cewa "A'a wa nake gani kamar Maleeq", kasa Amsa masa yay don baya cikin natsuwarsa, hankalinsa gaba daya a tashe yake bashi da burin da ya wuce ya je yaga halin da take ciki, ganin kamar baya cikin natsuwarsa yasa Dr Naufal din cewa "Wani kazo dubawa ne ?", da sauri ya ɗaga kai kafin da kyar yace "Ƴata na daya daga cikin wanda haɗarin Acid din nan ya sama", da sauri y riƙe hannunsa kafin yace "har da ita a ciki ?, innalillahi!", ya fada yana dafe kai.
Wata narkakken madarar tashin hankali ne ya ji ya ƙara ƙwaranyo masa, riƙe hannun Dr din yay cike da tashin hankali, idanunsa sun kaɗa sun yi jaajir SBD Tsananin tashin hankali, "zo mu shiga", ya fada yana yin gaba, a hankali cike da mutuwar jiki ya shiga ɗaga ƙafafunsa, tun daga farkom shiga ɗakin jikinka zai yi sanyi , tsoron Allah zai ƙara kama ka. Yara ne a cikin Ɗakin wanda ba su wuce sa'aninsu ba gasu nan kwance kan gadaje , duk haɗarin Acid ne, ya samesu, bb kyan gani gaba daya sun koma wata iriyar halitta ta daban.
wata Ƴar Corner suka shiga, suna shiga ya jaa ya tsaya, idanunshi a lumshe ya ma kasa kallonsu, gaba daya fuskokinsu naɗe suke da Bandage , hannayensu sanye da ƙarin ruwa mai dauke da sinadaran kashe zugi da sa barci domin su samu sauƙi Azabar da suke ji.
Nishi ya ji ƙasa ƙasa, da Alamar kamar ana magana chan ƙasa sosai, don in ba ma kunnuwanka suna da ji sosai ba ba zaka iya jin mai ake cewa ba. Da Sauri ya ware idanunsa, ya kalli gefensa in da yake jin Abun, ita ma dai kamar Sauran tana kwance ne ruf da ciki , bayanta naɗe da bandage , an naɗesa. da sauri ya nufeta hannanunta na dama da bb drip ya kama , cikin tsananin tausayi ya kira sunanta , a hankali ta ware dara-daran idanunta da suka ƙanƙance suka koma jajaye tsananin Azaba . , Zirrrrrr wani siririn hawayen Azaba ya zubo mata, fuskarta gaba daya tayi jaaa har kamar jini ya kwanta na tsananin Azaba, ita kam bb in da Acid din ya sameta a fuska, Amma gaba daya bayanta ya daddare , tun daga wuya har karshen bayanta, cikin ransa Yay Hamdala, kallon Allurar barcin da aka sa mata ya kalla, girgiza kansa yay , ƙarfin jininta , Allurar tayi ƙarama ba zata iya sanyata barci ba sai babbar Allura, fadawa Dr din kalar Allurar da za'a sanya mata yay, da sauri y fita dan yasa a kawo Allurar, komawa yay ya zauna yana riƙe da hannunta, kanta ya fara shafawa cikin natsuwa, wanda hakan ya fara rage mata raɗaɗin ciwon da yake masa.
lumshe idanunsa yay yana jin kamar a jikinsa ciwon yake, Dr din ne ya dawo da Allurar a hannunsa, da sauri Ya ƙarɓa ya zuƙa a Siringi ya sanya mata a cikij ruwan da yake liƙe da hannunta. Aikuwa Ruwan na fara shiga cikin jikinta barci ya fara fusgarta, gyara mata yay yarda zata ji dadin kwanciyar, kafih kace kwabo barci mai mugun nauyi ya dauketa.
bayan ya tabbatar da cewar barcin nata yay nisan da tashinta ba yanzu ba, ya miƙe suka fita da Dr Naufal suna magana, Office dinsa suka shiga, gurin Zama ya nuna masa ya zauna suka dan fara magana sama-sama , kallon Dr din ya yi, cikin ɗan Neman Alfarma yace "Dr ina son please a chanja mata Room in da hali a mayar da mu Aminity , Sbd gurin Chan bashi da kyan shiga Sannan idanun mutane sun yi yawa", ya fada yana kallonsa.
"in dai kana so mai zai hana a maka haka, dama duk cikinsu nata ya fi sauƙi, sai dai rashin sanin nata yasa muka barta a chan cikin Yan uwanta wanda Abun ya faru da ita. kuma zamu iya chanja mata gurin da bb mutane sosai, SBD kai. bari na kira, sai a chanja matan". ya faɗa yana danna wayar gabsnsa, ba'a jima ba aka dauka, Umarni yay musu da su dauketa su chanja mata Ɗaki, haka kuwa aka yi, Aka mayar da ita Chan wani sashe na musamman in da bb yawan mutanan da suke wucewa ma, ba kuma kowa ake kaiwa chan ba sai mai gata. haɗaɗɗan guri ne sosai, don in ka shiga ma ba zaka dauka a cikin Asibiti kake ba, zaka dauka ma wani Estate ne gurin, sbd tsabar haɗuwarsa da kyansa, gashi gurin aka mishi kamar wani part part .
Da sassafe ya fita , zuwa gida a hanyarsa ta zuwan ne traffic light ta tsayar da shi, masu irin siyar da Jaridar nan ne, suka yo gurin motarsa, dan zuge glass ya yi, y kira daya,kuɗi y miƙa masa ya karɓi guda daya, don yana son ganin Abun da yake faruwa a Majalissar Ƙasar , Ajiyewa Ya yi a gefansa , sakamakon basu hanyar wucewa da aka yi, hakan yasa bai duba Jaridar ba, bayan ya je gida ya na daukar Abun da ya kai sa ya fito ya koma Asibitin, Guraren Goma na safe ta fara motsawa , na Alamar ta farkawa, A hankali ya matsa kusa da ita , kanta ya shafa , jin alamarsa a kusa da ita yasa ta bude idanunta.