Arman maleek book 1 complete - Chapter 23
Arman maleek book 1 complete Chapter 23: Arman maleek book 1 complete Chapter 23. Kiran Dr yay ya faɗa masa ta farka, shi kuma y aiko Nurses duk abun da ya…
4,430 words
Kiran Dr yay ya faɗa masa ta farka, shi kuma y aiko Nurses duk abun da ya kamata a mata aka mata, aka shiryata Neat , kafin suka fice, ganin jikin da sauri ta dsn tashi da karfi, yasa hankalinsa ya dan kwanta, ba kamar da da bai ga farkawarta ba, TV ya kunna, ya matsa kusa da ita yana bata Tea, bata sha da yawa ba ta cire kanta ,zufa na tsatsafo mata, Abin da ya faru da su aka fara haskawa, da kuma baɗalar da suke yi cikin Club din har da Video din rawarta, bayan an gama haskawa ne aka yi allah wadai da Abun , tun da aka fara nuna Abun ta ɗukar da kanta Ƙasa shi kuwa wani kallo ya mata,bai kuma ƙara bi ta kanta ba.
Wayarsa ce tayi ring, yana dauka Ayyana tace "Maleeq kama kallon Abun da ake Yaɗawa a Media da sauran Gidajen redio da TV kuwa ?, Yarinyar nan tana son zubar mana da mutunci da ƙima, yanzu mai Amfanin duk wannan ? , ko so take duk in damuka shiga a ringa mana tofin Allah tsine ?, dama don tayi wannan baɗala yasa ta zaɓi ta tafi wata ƙasa tayi karatu, A gaskiya to har i dan zata ci gaba da wannan halin ,to fa zata dai na Amsa Sunan Sawwama Arman Maleeq, SBD mu yan mutunci ne , sai dai ka sama mata wani sunan da zata ci gaba da Amsawa,amma ba na Ahlinmu ba", tana gama faɗar haka ta kashe wayarta.
ko 1 minutes ba'ayi ba sai ga kiran Lamurɗe , bayan sun gama gaisawa yace "kaga Abubuwan da suke yawo a Duniya kuwa ?, mai Yarinyar nan take son zama ne ?, tana so ta ɓata mana Zuri'a ne ?, tana so ta ɓata mana Sunan Masarautarmu ne da Mutuncinmu ?, to ka ƙwaɓeta don sam ba zamu lamuncin hakan daga gare ta ba,ba ita ba ko kai ne kake son kawo mana tashin tashina to fa za muyi iya bakin ƙoƙarinmu na ganin mun horeka", cikin dan ƙasa da murya da ladabi , yace "Ayi mata Afwa Lamurɗe in sha Allahu ba zata ƙara makamancin hakan ba", ya fada cikin ladabi bayan sun gama wayar ya juyo gareta cikin ƙuluwa yace "kin kyauta Allah saka da abun da kika yi, ai dai kin zaɓi mutuncina ya zube ko ?, kin zaɓi da ki lalata min suna ?, kin zaɓi da a ringa kallonki a matsayin mai tazubar, marar tarbiya, kije kiyi ai ga Alhaki man ya fara bibiyarki tun ba'aje ko ina ba", ya fada yana kawar da kansa gefe ba tare da ya ƙara kallon inda take ba.
kasa magana tayi don bata da bakin magana, sai dai idanu,da ta gaji da wawwaresu sai ta lumshesu bata san lokacin da barci ma yay Awon gaba da ita ba, tunanin Abubuwa shima . bata wani jima ba sosai ta farka a barcin da wani irin futsari sosai, chan ta hangesa kan kujera, a Hankali tace "Abieh!", shiru yay bai Amsa ba, hawaye me suka zubo mata, cikin muryar kuka tace "Abieh!!", juyowa ya yi, y kalleta.
Langaɓar da kai tayi cikin alamar tausayi tace "Abieh'na don Allah", ta fada hawaye na zubo mata , da sauri y dauke kansa daga gareta ya mayar kan TV , kamar ba zai tashi ba kuma sai y taso,akanta ya tsaya, cikin kakkausar murya yace "Me ?", ƙasa tayi da kanta,kafin tace "zan yi futsari ne", ta fada a hankali, "ki tashi kije kiyi man", ya fada yana ƙoƙarin barin gurin, da sauri tace "ai bazan iya bane", watsa hannayensa yay Alamar ita ya shafa.
"Don Allah ka kai ni", ta fada tana kuka sosai, wani abu ya ji ya tsirga masa har cikin ransa, cikin lokaci ƙanƙani tausayinta da dama yana cikin zuciyarsa ya bayyana ƙarara a zahiri, da kansa ya taimaka mata ya kaita tayi futsarin ya dawo da ita, zama ya yi a gefenta, hakan kuma ne ya bata damar daura kanta a ƙafarsa, cikin ƙasa da kai da ƙasƙantar da shi, cikin karamar murya ta bada haƙuri tace "For give me Abieh pls kayi hkr ka yafe min, fushinka a gareni babban bala'i ne a gareni, kayi hkr ka yafe min,in sha Allahu bazan ƙara ba", ta fada wasu hawaye masu ɗumi yana zubo mata.
ɗumin hawayen ne ya tabbatar mishi da saukarsu, cikin dan tausayawa ya daura hannunsa akanta yana dan shafawa yace "it's Okay na yafe miki", ya fada yana gyara mata kanta a jikinsa, wani sanyi ta ji har cikin ranta, a hankali tace "Ngd Abieh", ta fads tana dan kallon fuskarta, murmushi yay mata , sosai ta ji dadi don ta tabbatar da y ƙuran kenan.
Yinin ranar haka ya ringa kula da ita, da tayi motsi zai ce, "me kike buƙata ?, ko me ne ne?, ita kuwa sai dai tace bb komai, in kuma akwai ta faɗa masa, haka suka yi sati a Asibitin ana kula da ita sosai, izuwa yanzu Abubuwa sun fara yin Sanyi , Abubuwan da ake yaɗawa ma sun yi san yi sosai .Ɓangare guda kuma Soyayyarsu suke bugawa ita da Jaaahan dinta, wanda har yau ya ƙi ya bayyana mata kansa sai faman ɓoye mata yake, ita ma bata damu da ta gansa ba , don kullum tana hasasosa a cikin tunaninta dama mafarkinta gaba daya, ba zata fito tane tabbas sonsa take ba, amma tabbas akwai wani abu mai kama da haka da take ji a kansa.
Ranar da suka cika Sati biyu ranar Aka Sallameta , sakamakon kan jikin da take dashi yasa ciwon Yay saurib warkewa duk da ba ko ina ya warke ba, Amma ta ji sauƙi sosai, ranar kuma suka bar Ƙasar Izuwa Saudi don yace 1 hour bata ƙarawa a cikinta, ko da suka koma kowa ya chanja mata ba kamar da ba, Zayn ma da yake yawon shige mata da Yanzu bb ruwansa da ita, Ayyana kuma Ɓacin ran Abun da tayi yasa ta dai na kulata,Umma Jakadiya kuma bata Ƙasar ta koma Nigeria su Amah ma ba kasafai suka fiye zama Ƙasar ba, sai kuma Khaleeda wacce take cin karanta bb babbaka, ta faffake komai.
Kwance take cikin palonta tayi ruf da ciki tana shan iska SBD ciwonta da ya fara chaɓewa sakamakon Sanya rigar da take ɗamamma ta yini da ita, yasa ya inda ya bushe duk zufa ta jiƙa ya fara chaɓewa, hakan yasa Abieh'nta hanata sa riga sai dai ta zauna da Boom Shot sai dan towel da zata rufe kirjinta ta gaba, waya ce saƙale a kunnanta, ta ɗaga ƙafafunta sama sai faman zuba shagwaɓa take, iya son ranta, shi kuwa sai biye mata yake yana rarrashinta kamar wanda bashi da Abun yi.
kamat an tsikareta tace "Uhmmm ga tambaya", daga chan Side din ya Amsa mata, "Wai ni baka zuwa aiki ne ne ?" murmushi yay mata kafin yace "mai yasa kika tambaya ?", shiru ta dan yi kafin tace "naga kullum baka ce min ka tafi office ko kasuwa kana gida kullum", dariya mai daukar hankali yay kafin yace "to ni da nake tare da Babban Arziki kamar ke neman kuɗin mai zan ?, ai ina kwance nake jin kuɗi ta ko ina", cikin rashin fahinta tace "ban gane ba kamar ya ?", "ooooh surutunki yay yawa Dolly", turo baki tayi kafin tace "sai na faɗawa Abieh'na", kwaikwayon muryarta yay kamar yarda tayi mgn ya maimaita, sanyayyiyar dariya tayi kafin tace "to naji din, sai kuma tambaya ta gaba", daga chan yace "ina sauraranki". "Shekarunka nawa ?, kuma ya kamanninka suke ?", jim ya dan yi kafin yace "ki fasaltani da Abieh'nki kawai har shekarun ina jin za muyi dai-dai". tura baki tayi kafin tace "Tab ni kam bana son na Auri Tsoho", dariya ya yi kafib yace "Yarinya na kama ki zaki gane kuranki ba dai ni ne tsohon ba?, " "aa ni fa ba haka nace ba, " ta fada yana boye dariyarta, "ai baku shi ke yanka wuya,naki ya yanka wuyanki", za tayi magana, taji an turo ƙofa da sauri ta sanya wayar ƙasan fillo ta tashu zaune, tana kallon ƙofar , Abieh'nta ta gani yana shigowa da waya a hannunsa, fuskarsa kadaran kadahan, zare ido ta fara yi, don ta tabbata ya ga waya a kunnanta, Alamar tana waya, Alhalin kuma ya gargaɗeta, hakan yasa tsoro kamata, miƙa mata wayar ya yi, da sauri ta ƙarɓa ta kara a kunnanta, muryar Umma Jakadiya ta ji, haukan yasa taji wani dadi y kamata, cikin murna tace "Granny!", dariya tayi daga chan ɓangaren, gaisawa suka fara yi da tambayar bayan rabuwa,su ɗan jima suna wayar kafin su gama.
Lokacin ya fice daga side dinta ya tafi nasa, da sauri ta tafi kai masa wayar, zaune ta samesa a palonsa daga shi sai jaallabiya ga daura ƙafarsa kan Stool yana kallon TV, tana zuwa ta zauna akan ƙafarsa ta mika masa wayar ba taare da tayi magana ba, "ke da waye kike waya ɗazun na kiraki na ji line busy?" . cikin inda inda tace "Wa..ya kuma Abieh ? ina jin dai sai dai network", kallon da ya sanyata yin shiru yay mata ba tare da yace komai ba.
"Kutumar Uba. Yau nake ganin bariki a cikin gidan Aurena, wannan wani irin bala'i ne, ka dauki baligar Ƴa ka daura akan cinyarka, Tsabar Iskanci da Lalata, wannan ai ya wuce Iskanci sai dai Ace Kwar........ [5/30, 4:27 PM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: PART 4. CHAPTER 3.
*P. 46*
"Wannan ai ya wuce Iskanci sai dai Ƙwartanci, yanzu kai don Allah baka ji kunya ba, azo a tarar da kai dauke da wanin Baligatun Saratun Bunsusun din akam ƙafarka, kamar wannan ko mijinta ai tayi girma ya dauketa balle kai da kake matsayin Mahaifi ko da yake ai mun gane komai Mahaifin Bogine domin Ƴar tsuntuwa ce, wa ya sani ko Zaman Dadiro kuke dama, Tsintacciyar Mage dama an ce bata taɓa zama mage, k..." kafin ta ƙara magana ya dauketa da wani zazzafan tagwayen maruka wanda suka sanya ta ganin roɗi-roɗi gaba daya jinta da ganinta ta tsaya na wani lokaci.
da Lalube ta zauna a ƙasa, don ji take idanuwanta kamar zasu faɗo, fuskarta kamar an jajjaga tarugu an zuba mata tsabar jaan da tayi ga wani raɗaɗi da ake mata, buɗe idanunta tayi tana wawwaresu gefe da gefe take kallo da alama ma bata gani faba daya, sai rarraba idanu take, baƙin idanunta gaba daya yay sama, farin ya mamaye yarda kasan zata suma.
Abin ka da farar fata ga kuma ƙari da bleaching Fuskarta ta koma kamar danyan nama, yana fesar da zazzafan numfashi , mai tattare da fushi da ɓacin rai, hannunshi ya nuna mata, sai dai ya ma kasa magana.
sai da tayi lafiyayyan 5 minutes kafin ta dawo cikin kyakyawan hankalinta, don a da haukan wucin gadi tayi,cikin kuka da takaicin Abun da ya mata, ga na Bin kansa da ya bata Haƙkinta tun bayan Auransu Amma Abu ya faska, duk iya yinta da tayi ta biyawa kanta buƙatarta,na mugun kwaɗayinsa da take domin cimma wata manufarta, Amma Abun ma gaba daya taki tashi, ko ta tashi an zo gab da Al`amari sai Abu ya koma ya kwanta yarda kasan jiƙaƙƙan Tsumma, duk da haushin hakan da take ji yasa take Abubuwan nan haka.
"Allah ya isa tsakanina da kai, Allah ya isa na cin Amanata da kake yi, ka rasa da wa zaka yi kwartanci sai da jiƙar jiƙarka SBD kai baka da kunya ma a Fasiƙanci, har gobe har jibi bazan fasa faɗar cewa ita din Tsintacciya bace , wadda bata da Asali wulaƙanttata, ƙasƙantatta, mara gata da galihu kuma sai dai ka zaɓi daya tsakanin ni da ita", ta fada cikin kuka sosai, tana goge bakinta in da ya fashe jini na zuba.
"kije na sake ki saki daya ", . "ba zaka sake ni saki daya ba Wlh sai dai ka sake ni saki Ukku, Mata maza kawai , bsn da kaɗɗara da son zuciya ma mai zai sani zama da kai ?, ba gwara na zauna na ma da mace Yar uwata ba, wadda nasan ba zata Amfaneni da komai ba, don duk daya kuke a idona kai da ita,", zafi da Ɓakin cikin kalamanta garesa yasa ya girgiza kai cikin kasa Control na kansa yace "kije na kara sakin ki , saki daya " ya fada yana yin han yar Bedroom dinsa , bai ma tsaya jin wasu surutan iskarta da take yi ba , Cakumo wuyan Sawwa tayi ta riƙe kam tana zaginta da tsine mata tare da faɗa mata baƙaƙen maganganu,tana kiran ta da Tsintacciya, ita dai sam bata ma fahimtar mai take cewa ,kallonta take yi kallo irin na wadda ta zare ko wadda bata da hankali ma gaba daya.
Shaƙe wuyanta tayi sosai, har ta fara ganin dishi-dishi , daga baya ta ji an shaƙeta an ƙara sharara mata mari, cillar da ita yay chan gefe, cikin zuciya ya nuna mata hannu, tare da cewa "kika bari hannunki y ƙara taɓata, Wlh sai kin gane baki da wayau dabba kawai, kin dauka ban san duk abubuwan da kike aikatawa bane ?, sarai nasan duk abun da kike yi, sanin hakan ne ma yasa na na kasa haɗa shimfiɗa da ke, domin ba zan iya sa jikina a juji ba,domin ke kin zama shaddar kasuwa, banza jahila , wannan din da kike kira tsintacciya marar Asali ta fi gaba daya Ahlinki matsayi da ƙima da daraja, kuma ta fiki so dubun dubayya, Shashsha" ya fada yana jaan hannun Sawwa ya nufi bedroom dinsa da ita. ita kuwa da rarrafe ta fita daga cikin palonsa don gaba daya bata gani idanunta sun rufe .
.
Fusgeta yay daga hannunta, ya hankaɗata har ta bugu da jikin gini, kanta ne ya fashe ya fara zubar da jini, a tsorace Sawwa ta kalle sa , Amma bb Abun da yake sai jaan hannunta, fita yay da ita, Side dinta ya kai ta ya kulleta kafin ya fice daga gidan, haka Khaleeda ta gama haukanta da fashe-fashe ta tattara ta tafi gidansu. su kuwa Yan gidan ko da suka dawo bb wanda ya bi ta kan wata Khaleeda don dama ta jima sosai bata shiga sabgarsu, hakan yasa suka tattara suka watsar da ita. Bayan ya je Asibiti gurin Abbue sun yi magana sosai, da idanu don da su suke magana tun da shi bashi da bakin magana, Yana nan kuma Jaddi ya kirasa daga Australia, bayan sun gaisa ya tambayesa kowa, kafin ya daura da mishi bayanin wani mai magani da yaji Sabo, sai da ya gama tas kafin yace "Kana sane da ban san tsubbu da bokanci dai ko ?", ya fada cikin sigar da suka saba magana a tsakaninsu.
"Wannan ba tsubbu bane ko bokanci, Malamin Addini ne don Traditional medicine ne, ku da kun saba Canfa komai", ya karashe da tsokana, murmushi yay tare da cewa ", dama dai mun gama haɗa Visa dinmu ta komawa gida Nigeria , gaba dayan mu, kuma ina son in naje chan , zan zo nan gareka, don ina son muhimmiyar magana da kai ", ya fada a hankali yana lumshe idanunshi, fatan Alkhairi da fatan sauka lpy yay masa kafin ya kashe wayar.
Kwana Biyu tsakani kuma suka tattara izuwa Nigeria bb wanda aka bari gaba dayansu suka tafi, ko da suka sauka Masarautarsu sun ga yan chanje-chanje sai dai ba wani abun damuwa bane da hakan. An sabunta fentin Gidan gaba daya, Sannan sun samu tarba mai kyau, Wulaƙancin Jaddi kuwa bata dai na ba sai ma Abun da yay gaba, Duk ta bi ta daurawa Sawwa karan tsana, ya zamana ko ruwa Yarinyar bata isa ƙwaga a gabanta ba, ta fara mata masifa da faɗa ga gori, abu kaɗan tace "Tsintacciyar Mage kawai", ko a ce "Tsintacciya!", tun bata riƙe kalmar ba, SBD wahalar da Hausa take mata wadda bata saba da ita ba sosai, har ta riƙe sunan sosai a bakinta, tun Abun baya damunta in ta faɗa har ya dawo damunta.
Suna Zaune ita da su Amah suna fira, Ayyana na gefe wadda har yau ba wai ta sake mata bane, don ko gaisuwarta kamar a dole haka take Amsa mata, suna cikin fira sai ta cewa Amaturrahman ", Amma Tsintacciyar Mage ce", ta faɗa irin bata san mai hakan ke nufi ba, don ita ba wai tana fahintar hausar bane, aa kawai dai tafi riƙe hakan ne akan komai , cikin jin zafi da faɗa Ayyana ta fara mata masifa don mai zata kira Amaturrahman da Tsintacciyar, Alhalin ita ce ma nan tsi tacciyar, wadda bata da Asali, ta in da take shiga ba tanan take fita baa. zafin kalaman Ayyana ne suka sa wasu hawaye masu masifar ɗumi suka zubo akan fuskarta ita dai ta rasa Abun da tawa Ayyana kwana biyu da take nuna mata ƙi irin haka....
ni kam da bazan post din nan ba, Sbd ban yi typing sosai ba, har na kwanta naga dai bari na muku , don da bb gaba daya ko yane gwara a taɓa [5/30, 4:27 PM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: PART 4.CHAPTER 5.
*P. 48*
Cikin tsananin tashin hankali, kaɗuwa da firgici ta juya bayanta, tare da rufe idanunta ruf, don wata iriyar jiri take ji kamar zata faɗi, Cikin Takun Ƙasaita da isa, ya tako ƙafafunsa, har ya zo inda take, cikin natsuwa ya sanya gaba daya hannayensa ya juyota, A hankali ta furta "Abieh mai kake yi anan ?", ta fada cikin wani yana yi, A hankali ya dan gyara tsayuwarsa kafib yace , "Babu . ke fa ?", da sauri ta jujjuya kanta, tare da cewa, "bb komai kawai na hango mutum ne anan bayan naga kowa ya gama tafiya, Ashe kai ne ", ta fada tana sosa gefen hannunta, jinjina kansa yay kafin ya ce "To wuce ki shiga gida," ya fada yana juyawa in da yake.
Da sauri ta juya tana tafiya tana waiwayen bayanta , bai ƙara kiran wayarta ba sai da ta gama shirin barci gaba saya zuciyarta na ɗatace ta ji ring nasa, kamar ba zata ɗaga ba kuna sai ta dauka, shiru tayi bata ce komai ba, shima kuma bai ce koman ba, dob yasan ranta y riga da ya ɓaci, A hankali ta furta "Am Sorry Dolly ", ya furta cikin sanyi, "Sorry for what ?", shiru y dan yi kafin yace "Disappointment!", taɓe bakinta tayi kafin tace "Hmmmm",.
"Na so na zo sai naga kamar bai dace ba, tunda gaba daya Ahlinki na gurin, in suka tambayeki waye ni fa", kai tsaye ta furta "Mijin da nake son Aura", murmushi ya yi mai sauti, "Ko ban isa Auren bane ?", ta fada ba tare da ta kula da mai take faɗa ba sai da ta gama faɗar, "Uhmmm lallai Yarinyar ta girma har da zata iya faɗar haka", "Am 20 years , kaga kuwa na gama girma ma", dariya ya dan yi kafin yace "Uhmmm lallai na ga Alama", haka suka ci gaba da fira har zuwa wani lokaci, suna cikin fira ta ji nocking Ƙofar, a hankali ta ce mishi "ina dan zuwa", ta fada tana ajiye wayar ta nufi gurin ƙofar da ake bugawa.
Da sauri ta basa guri kan ta a ƙasa, tare da cewa ''Barka da dare Abieh", jinjina kansa ya yi, kafin yace "Zo!", ya fada yana wucewa, A hankali ta bi bayansa, har zuwa Part dinsa, tun daga ƙofar shiga Part din komai na wuta yake kashe har suka shiga cikin palon, bb haske, sai da suka je tsakiyar palon, ƙafin haske ya mamaye gaba daya Palon, A hankali ta shiga ƙarewa Palon kalli, wanda ya sha kwalliya mai daukar hankali, duk kuma in da ta waiga Pick dinta ne ta ko ina.
Murmushi ne ya suɓuce mata, ta shiga daukar Balloon masu zanan heart a jiki wanda colours nasu , favorite colours dinta ne, kamar daga Sama ta ji an ce "Will you marry me ?"ta ji maganar ta daki dodon kunnanta, da sauri ta juya bayanta, a a zaune ta hangesa idanunsa a lumshe kamar ba shi yay maganar ba.
juyar da kanta tayi ta ci gaba da kallon Balloons din , cikin wata sanyayyiyar murya ya ƙara cewa "Sawwameerh Maleeq Abdul-Azez Arman Maleeq Sarki zaki Aure ni ?", ya fada wannan ƙaro idanunsa a kanta, da sauri ta ɗago idanunta cikin madarar zallar ƙiɗima, ta maimaita Abun da ya faɗa, jaa baya tayi ganin ya miƙe yana takowa zuwa inda take,cikin idanun juna suke kallo tana baya yana biyota, har ya samu nasarar cin mata , riƙe mata hannayenta yay yana kallon cikin tafukan hannayenta yace "Zaki tallafi Rayuwar Abieh'nki ki Auresa ki zauna da shi har zuwa ƙarshen rayuwarsa?", da sauri ta fusge hannunsa tana kallonsa, yarda zuciyarta take bugawa, haka shima tashi take duka, da sauri tace "Ban fahinta ba, ban gane ba, mai kake son faɗa Abieh ?, kai fa mahaifina ne mai zai sa ka ringa min wannan maganar",ta fada muryarta na rawa.
Hannayesa ya zubasu akan waist nata ya riƙe, yarda yay kusa da ita ne, yasa har yake iya juyo yarda jikinta yake wani karƙarwa da cira irin ta mutumin da ya gama kaɗuwa, da firgici, cikin ƙasalalliyar maganarsa, da muryarsa Temporary ya furta " Debbo am!'', har cikin ranta ta ji yarda yay maganar, hakan yasa ta ƙara rumtse idanunta zuciyarta na wani tsinkewa, gani take kamar Mafarki take yi, ji take kamar a Tunanin Iskarta hakan ke faruwa, ina ma ace a Mafarki hakan ke faruwa, Mahaifinta yake cewa, zata Auresa, wannan wani irin bahaggon Yanayi take ciki, don gaba maganar tasa ta sanyata a cikin matsananciyar damuwa, tasa zuciyarta na Barazanar Tatwatsewa, tunaninta yana ƙoƙarin Gurɓata, wani ɓara Gurbin Yanayi yana mamaye gaba daya Yana yin da take ciki.
Guiwarta a sace, ta fara sulalewa ƙasa cikin matuƙar tashin hankalin da ba'a sa masa rana, kafin ta kai ƙasa, yay saurin sanya guyawunsa, a inda nata zasu sauka, tana yij ƙasa ta daura guyawunta akan nasa ƙafafun, fuskokinsu na facing juna, hancinsu ya kusa haɗewa, haka goshinsu, har suna iya juyo yarda suke fesar da numfarfashi , ita tana fesar da numfashin zallar kaɗuwa da tashin hankalin da yake barazanar dauke mata da numfashi, shi kuma yana kallonta ne, tare da fitar da Numfashi mai dauke da zallar so da shauƙi, hakan ne ya ƙara haifar da Natsuwar Zuciyarsa, wanda ita kuwa, in har ta ce tana jiyo Alamar natsuwa ma tayi ƙarya, gaba daya ta dilmiya ne cikin tsananin tashin hankali da firgicin da ya damula mata lissafi.
Hawaye masu zafin gaske ne suka zubo mata, muryarta na rawa ta buɗe bakinta, "Why ?, Why ? me yasa ? nace mai yasa ?" ta fada har lokacin idanunta na zubar da hawaye kuma bata buɗesu ba, "Me yasa ka zaɓi ka sani cikin ƙunci da damuwa ?, mai yasa kake son tarwatsa min farin cikina ,sannan ka tarwatsa min rayuwa gaba daya, don mai zaka ce kana sona Alhalin kana Mahaifina, kana son ka ringa wasa da hankalina da tunanina, don mai ?, nace mai yasa kamin haka ?", ta fada da kuka sosai, gaba daya nadama da dana sani ce suka rufesa, "Kana matsayin Mahaifina kake min wasa da hankali har haka ?, ka fito min da wata suffa ta daban , Mai yasa haka Abieh ?, yanzu ya kake so nayi da rayuwata bayan na gama zurfi a son wani daban ?,,taya zan iya fara Rayuwa bb Jaan , shi nake so nake da burin Aure, Bana son ka Abieh kai mahaina ne ,bb Aure a tsakaninmu, kai ne ka haifeni, ko ba kai ka haifeni ba, bazan iya Auren wanda yake da matsayin Uba a gare ni ba, Sannan yanzun nan nake son ka faɗa min wace ni ?, mai yasa ake kirana da Tsintacciyar Mage, Tsintacciya, mai yasa kowa yake hantarata, so nake ka faɗa min Real FAM dina , su waye Iyayena na gaskiya ? wace ni ?, mai ma'anar Sunan Tsintacciya ? mai tsintacciyar mage take nufi, ? sam na kasa fahimta ji nake kwakwalwata kamar zata tarwatse" , ta fada tana riƙe kanta da hannayenta bibbiyu, gaba daya shima ya ruɗe, Abun da yake rufewa Tsawon shekaru 17 , a yau rana tsaka yana neman tarwatsewa, Nadamar mai yasa yay mata wannan maganar ma gaba daya yake, mai yasa komai ba tashi warwarewa ba sai yanzu, "Innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un!", ya furta yana rumtse idanuwansa gaba daya cikin zallar firgici da fargaba ga wani bugun zuciya da yake ji.
"K...k...ka..fa..da min...wa ce.....niiiii!", ta fada numfashinta na fusga sosai kamar wadda zata shaƙi numfashin karshe, cikin tsoro ya fara girgizata , "ke..! kee..!! ki dakata kar ki suma tsaya..Sawweermah" ya fada yana girgizata sosai, Amma inaaa, tashin hankali yaƙi y barta sai da ta kai ga ta suman, da gudu ya nufi Fridge ya sauko ruwan sanyi mai sanyi sosai har y fara ƙanƙara, duk da ya san illarshi a jikinta, amma hakan ba zai hana ya sanya mata ba sa boda ta dawo hankalinta.
Shafa mata hannunsa mai dauke da danshin ruwan da ya dangwala akan fuskarta, shiru bb motsi, ƙara shafa mata ruwan ya yi, sai da yay mata gaka sau ukku kafin ta jaa numfashi da karfi, idanunta a lumshe ta furta "Ahlina! Ahlina!! Ahlina!!!", sau ukku ta faɗi hakan kafin ta tsuke bakinta, gaba daya hankalinsa ne ya tashi don shi bai ma san ko mai zai ce mata ba,ba wai game da Ahlinta ba, aa Karfaffiyar Alaƙar da take tsakaninsu. wadda duk SBD ita Wannan halin y faru da ita.
"Tashi ki zauna na miki bayanin Ahlinki", ya fada da kyar yana danne Abun da yake ƙoƙarin tokare masa numfashi, a hankali ta bude idanunta, taimaka mata yay ta jingina da jikin gado, nannauyan Numfashi ya jaa kafin yace "Yanzu kina son ki nuna min ni ban isa komai naki ba, har da kike neman Asalin Iyayenki , Abun da yau tsawon shekara 17 kike son ki tone yau rana tsaka, kimin Alqawarin zama da ni ko da na faɗa miki komai da ya danganci Ahlinki, in ba haka ba zuciyar Abieh'nki zata iya tarwatse", ya fada yana zuba mata idanu.
girgiza kanta tayi cikin hawayen da ya wanke mata fuska gaba daya tace "aa Abieh , tun da ka furta maganar chan naji kawai ina son sanin wace ni ?, wanda baka taɓa zaunar da ni ka faɗa min ba, a da ban damu da sanin wace ni ba, Amma A yau da ka faɗa min maganar nan sai na ji ina son sani ", ta fada tana haɗa Hannayenta biyu.