Kenza eBookz

Arman maleek book 1 complete - Chapter 24

Arman maleek book 1 complete - Chapter 24

Arman maleek book 1 complete Chapter 24: Arman maleek book 1 complete Chapter 24. "so kike ki san ko wace ke ?,kina son sanin more inform dangane da ke ?,…

4,492 words

"so kike ki san ko wace ke ?,kina son sanin more inform dangane da ke ?, kina son sanin real Family dinki ?, to ki saurara " , numfashi ya ja kafin yace "Ke din Ƴa ce ga wani Hamshaƙi kuma Mashahurin Malami, wanda ya Amsa sunansa Malami kuma Limami wanda gaba daya duniya ake matuƙar Alfahari da shi, ni kai na a gurinsa nayi karatu domin shi din Aminin Abbuena ne, Dan kasuwa, gefe daya kuma Hamshaƙin Ɗan siyasa, wanda y gaji Sarauta gaba da baya, sannan kuma gaba daya duniya ake matukar girmamawa da jin maganarsa, Yana da Mata daya da Ƴa kwalli daya kamar rai, ke dai ba. yana da tarin dukiya mai yawa, wanda har hakan yasa ake neman daukar ransa da ta iyalansa domin a gaji dukiyar , Maƙircin gidan Sarauta da Siyasa ne yasa yake matuƙar tsoron ko ya fita nan da chan, kuma shine ya rabasa da Asalin gidan Sarautarsu wanda a lokaci aka so a basa Sarki, ƙalubale da kuma kitumurmurar da ake yi ce ta sa ya tsallake Masarautarsu ya fito waje , An sha mishi tallar mata daban daban, Amma shi duk basa burgesa domin yasan ba don Allah suke sonsa ba, don Abun da Allah y hore masa suke son sa. hakan yasa Ya tsallaka Ƙasa mai tsarki in da ya ci gaba da harkokinsa a chan , daga chan kuma ya wuce Indiya in da a chan ne ya haɗu da matarsa Wato Mahaifiyarki, har suka yi Aure, a lokacin ya manyata sosai don zai iya 40 years, haka suka ci gaba da Rayuwarsu in da sai da suka yi shekara 17 da Aure kafin Allah y Azurtasu da Samun Haihuwa, a lokacin ni na Amsa haihuwar , Domin a lokacin ina Amsa Sunan Cikakken Likita, sannan kuma Cikakken Mlm......... [5/30, 4:27 PM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: PART 4.CHAPTER 6.

*PART 49*

Tun da Allah yasa na yi Arba da Ƴar Ubangiji y jarabceni da kaunarta , sai dai bayan na dauketa na naje na mata wasu Aune-aune na girgiza sosai da ciwon da naga Yana damunta , domin Abu na farko da na gani, Ciwon zuciya ne, wanda na san na gado ne dan Mahaifinta ma yana da shi, bayan an daurata akan magungunan da suka dace, aka ci gaba da kula da ita, duk kuma bayan sati ake zuwa ana duba mata lafiyar jikinta, wadda garkuwarta tai sanyi sosai.

Bayan Shekara ne kuma na dai na Aiki a Asibiti na koma Internal Supervisor , ban cika zama guri daya ba, sai dai ƙasa-ƙasa.

Sai dai lura da yay ina kaunar Ƴar a kullum ko ban masa maganarsa ba, sai ya min mgnrta, har ta fara magana, some time yakan kira ko mahaifiyarta ta kira , a bata ta min mgn, wata irin shaƙuwa da juna muka yi, ya zama kullum sai mun ji muryar juna.

Har lokacin kuma basu je Nigeria ba, duk da wutar da Ahlin Mahaifinta suke hura masa, akan yaje musu da Ƴa ko Ɗan don basu san ma kalar da aka haifa ba, domin su gansa.

Kamae yasan irin tuggun da suke shirya masa, sai ya kasa zuwa, ya share da maganganunsu, don yasan su ɗin mugaye ne yasan duk wani abu za su iya yi donin suga bayansa, don so da dama ya su kan yi hkn Allah ne kawai yake tsaresa.

Lokacin da Ƴar Nahla ta cika Shekara biyu, muka shirya zuwa Nigeria ni da shi, domin akwai wani Abun da zamu gabatar mai muhimmanci sosai, hakan yasa su suka tafi daga chan India ni kuna na tafi daga Saudi akan zamu Haɗu da Shugaban Ƙasar nan Nigeria wanda yake kan Mulki yanzu da Mahaifina don Aminan Juna ne.

Ranar da na Sauka a Nigeria su kuma kwanansu biyu ranar, ina sauka muka yi waya da shi, akan zai je gidan Ambassador shima, bayan mun gama wayar aka daukoni daga Airport zuwa Asibitin Valli da yake nan cikin Garin Abuja, domin ganawa da wani likitana akan wani ciwo na Musamman kuma na Sirri da yake damuna, bayan na gama ziyarar da na kai wa Dr na fito , naga wata Motar Ambulance da take cikin Asibitin ta shigo, dan tsayawa na yi ina son ganin wanda za'a fito daga cikin Ambulance din", idanunshi da yay jaa kamar hawaye zasu fito daga ciki, sun yi wani ruwa-ruwa ya lumshe, yana daura hannunsa akan goshinsa da kan sa yake wani Annamimin ciwo, kamar zai tarwatse.

"A lokacin Abun da na gani ya so tarwatsa min tunanina domin Mahaifinki sa yace min gashi chan zai je Gidan Ambassador ne na gani kwance cikin jini an fito da shi, gefen kafadarsa yana ta fita da jini , Alamar Harbi, Matarsa kuwa a goshi aka sameta, shi ina da tabbacin zai iya rayuwa SBD kafada ne, amma ita kam, ina da yaƙinin 1 second bata kara daga inda aka harbeta ba ta rasu, sai kuma ke da kifewar motar da tayi ya haddasa , sawa jijiyar ganinki ta samu matsala, lafiyar jikinki ma ta samu matsala , bayan an ceto Rayuwarki ke da shi ne, kuma ya Umarce ni , ni da Dr din da muka kula da Lafiyarku, akan mu Bayyana cewar Allah ya mishi rasuwa shi da Ahlinshi gaba daya, Sannan nan ta ke , yay waliyina Dr din yay waliyinki, aka daura mana Aure sannan ya danƙamin Amanarki, ya kuma Umarceni da kar na bayyanawa kowa ko ke wacece domin maƙiyansa da suka so kasheki Allah bai so ba, zasu iya dawowa gareki idan suka ji kina da rai, na kuma riƙe Amanar domin ko a cikin Ahlina bb wanda na bayyanawa Asalin ko ke wacece domin gudun Matsala, shi kuwa , bb wanda yasan ida yake a yanzu sai ni, domin na kan je mu haɗu mu tattauna , Wannan shine taƙaitaccen tarihinki", ya fada ba tare da ya bude idanunsa ba, ita kuwa sai kallonsa take da hawaye cike da idanunta, riƙe hannunsa tayi cikin kuka tace "Abieh ka kai ni gurin Daddyna don Allah, na gaji da gorin da ake min na gaji, ina son naga Mahaifina na Asali nima, " ta fada tana jijjigasa, ware idanunsa yay, cikin sanyin magana yace "Kin yarda zaki ci gaba da zama da ni a matsayin mijinki Abun Alfaharinki, kin yarda da ni a matsayin garkuwarki, ki yarda da ni a matsayin mai kare miki haƙƙinki da ci gaba da kulawa da ke har ƙarshen rayuwarki, ki ci gaba da zama da ni, kamar yarda nake share miki hawaye tun kina ƙaramarki na zama akan kafadata za kiyi kuka ya zamana ni ne nan mai share miki hawayenki, na tabbata ba zaki yi nadamar zama da ni ba, zan mayar da ke Sarauniya, wadda zata zama Abar kwatance a duniya baki daya, k.." da sauri ta ɗaga mishi hannu, kanta a ƙasa ta fara cewa "taya zan fara zama da Mariƙina kuma Mahaifina a matsayin Mijina, taya zan karya Alƙawarin da nawa wanin ka, bana ji ko na yarda da soyayyarka a matsayinka na Mahaifina ya zamana ina baka kulawar da ta dace, domin ni akwai wani a raina, akwai wanda ya raini soyayyarsa a zuciyata, akwai wanda na Alƙawartawa Rayuwata da kula da ni, na mishi Alƙawarin Aure ba zan iya karya Alƙawarin da na masa ba na kasance tare da kai Abieh ka yafe ni, ba don bana son ka ba, domin a rayuwata bb abun da bake so fiye da kai, bani da Buri na in Auri miji mai kwatankwacin Halayarka da komai naka, har na kan ce wata ranar, ina ma ace kai ba mahaifina bane, da duk hanyar da zan bi domin mallakarka zan bi, Amma ni bazan iya Aurenka nayi zaman rayuwar Aure da kai ba a matsayin mahaifina, domin ni kallon Uba nake maka , kuma har Abada bazan taɓa dai na ma kallon mahaifina ba, ba kuma zan daina cema mahaifina ba, ka yafe ni Abieh", ta fada tana miƙewa fuskarta jagab da hawaye, idanunta na rufewa take tafiya, don bata taɓa kuka irin na kwana biyun nan ba, wanda yasa ko gani bata yi sosai idanunta dishi-dishi take gani, har ji take kamar za su samu matsala, sai wani zut-zut suke mata, da tattaɓa bango ta fita daga cikin ɗakin, tana fita juwa ta fara diɓarta, bata Ankare ba ta ji ta ƙasa........ [5/30, 4:27 PM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: PART 4. CHAPTER 4.

*P. 47*

Wata tsawa ya dakawa Ayyana daga chan ƙofar shigowa palon, kamar wani zaki haka yake takowa cikin palon idanunshi sun yi jaajir , yana fesar da wani huci, cikin faɗa ya shigo cikin palon, nuna Ayyana yay da hannu cikin ƙufula yace "Wannan wani irin abu ne ?, mai yasa kike haka me ?, ƙiri-ƙiri kike nuna banbanci kike son raba daya biyu, kina babba Amma kin zama Babbar kawai, to ba zan lamunta ba, yanzu wannan Ƴar abar har ta isa ki ringa faɗa mata wannan munannan maganganun ?, tun ba yau ba dama na lura da Abubuwan da kike mata na rashin kyautatawa, ki sani kamar yarda suke cikin gidan nan, haka ita ma take, ke ta wani fannin ma ta fisu matsayi nesa ba kusa ba,ko yau suna iya barin gidan nan, Amma ita , ba zata taɓa barin sa ba har Abada, don haka ki gane matsayinta, sannan ki tsaya da wannan shashancin na ki ", ya fada ranshi ɓace, bai ko tsaya bi tz kan Ayyanar ba, ita ma kuma Sawwar bai tsaya bi ta kanta ba.

Bata iya cewa komai ba don tasan ita ta jaawo komai, kuma tun da ya fara ko saurararta ɓa ba zai ba, don shi kafin ya hau yana da matukar sauƙin kai , kuma yana da girmamawa, da mutuntawa, Duk Abun da za kayi kar ka bari ka ƙurosa, domin bashi da dadi ka ƙurosa, kuma ko waye zai iya silleka tas har in ka biyo ta hanyarsa, daga ita har Yaranta jikinsu sukuku haka suka zauna cikin palon.

Shirye-shiryen Birthday dinta,wanda Month din da kuma Satin duk suka tsaya, sai abubuwa take shiryawa, tana kuma cikin matuƙar farin ciki sosai don Jaahan dinta yana gab da bayyana mata kansa, don dama Yay mata Alqawarin cewar ranar Ƙarin shekararta zai bayyana a gareta.

"Uncles ban ga kuna wani shirye-shirye ba, " Zayn ne da ya sauka daga kan bakarsa, yace "Biki za'ayi a gidan ne ko mai", ta gefen ido ta hararesa kafin tace "Birthday na gobe man", ta fada tana dan tura baki, dafe kanshi yay tare da cewa "Oh god!. Wlh gaba daya na Sha'afa, kice gobe akwai rakashewa, " ya fada yana yar dariya, jinjina kanta tayi tare da cewa "Sosai ma kuwa, yanzu ma zan tashi, ina son naje na ƙarasa Siyayyata", ta fada tana miƙewa.

"Okay to shirya yanzu sai na yi dropping dinki Kasuwar don nima fita zan," ya fada yana danna wayarsa,da sauri ta miƙe ta nufi Bedroom dinta, bata wani jima sosai ba ta gama shirinta, lokacin ma su Amah sun fito gaba daya suka rankaya kasuwar, Ajiyesu yay ya wuce Abunsa, shiga ciki suka yi, duk wani abu da suka san za su yi Amfani da shi a gurin birthday din, da kayan sawar da za su yi Amfani da su, daga nan suka wuce gurin yin cake suka yi order, suka je gurin masu decoration suka mishi magana, akan yaje yay musu decoration kuɗinsa suka biyasa suka fada masa Address din gidan, daga nan kuma gyaran jiki suka wuce, sai bayan Magrib kafin suka gama komai Driver dinta da Abieh'nta ya samar mata wanda zai ringa driving nata ta kira, bai wani jima ba ya zo , suka tattara suka koma gida.

Ko da suka koma gida, har lokacin Masu Decoration din gurin da zasu gabatar da Birthday din basu gama ba, Sallamarsu tayi akan gobe su dawo su ƙarasa yiwa gurin kwalliyar ƙayatarwa, a gajiye suka shiga cikin gida, zubewa tayi akan kujera a matuƙar gajiye, wucewa suka yi ciki domin gabatar da Sallar da ta wucesu ita kuwa tana zaune bata damu ba, sai latsa wayarta da take yi.

12..na bugawa Ta ki ƙarar Saƙo a wayarta, har ta kwanta ta jaawo wayar, text ta gani, da sauri ta buɗe Alert din dai da ta saba gani mai girgizarwa ta gani, sai dai fa wannan ya fi ko wanne tsoratarwa, kafin ta gama tunani ta ji ring da sauri ta dauki wayar, "Happy Birthday to you My Pinky", ya fada a hankali, cikin sanyayyiyar muryarsa da ya saba mata magana da ita, shiru tayi bata Amsa ba, a hankali ga furta "Pinky!", nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke,cikin kaɗuwa tace "Mai yasa kake son ƙassara min rayuwata ne ?, mai yasa kake sob zautar da ni ?, na fara zarginka a yanzu, an ya ba wani abu kake nema a tare da ni ba ?, taya zaka ringa min kyautar tsagwaron kuɗaɗɗe irin haka, KO kana son jamin bala'i ne a gurin Abieh'na ?, na san duk ran da ya ga irin wannan alert din a wayata zai iya kashe ni", ta fada a ruɗe, "Come Down pinky, bb abun da Abieh'nki zai miki , kuma ni ba da wata manufa nake miki hakan ba, Wlh da zuciya daya nake miki duk Abun da nake miki, kuma ko wani naga zai miki wani abu sai inda karfina y ƙare domin zan iya kashe duk wanda yace zai taɓa min mutunci Bcouse I.." shiru yay bai ƙarasa Abun da yake son faɗa ba.

kasa magana tayi tama son ya faɗin Abun da ya fara ƙoƙarin furtawa, Sallama yay mata ya kashe wayarsa. shiru tayi tana jin kamar wani abu na taɓa zuciyarta, dakyar ta samu barci yay Awon gaba da ita.

Washe gari! Tana tashi ta ci ƙaro da Wasu Furanni a gefen fuskarta, Blue da fari, masu masifar ƙamshi, An daureta da wani Sarƙa ta zinari, sai wani dan rubutu a jikin paper din da aka maƙale Abun "FOR YOU MY FUTURE WIVE PINKY", ta gani rubucs a jiki.

Sai wani Dan Jotter da ta gani a kusa da shi, da sauri ta dauka ta fara karantawa, kalaman soyayya ne masu dadi da sanyayya zuciya, bayan ta gama karantawa ta maqale paper din a kirjinta ta matsa, tana murmushi mai daukar hankali, a hankali ta furta wasu kalmomi biyu zuwa ukku da ni dai ban ji mai ta ce ba na dai ga bakinta na motsi.

Tun da sassafe suka ta shi , dasawa suka yi daga inda suka tsaya, don akwai abubuwan da basu kaarasa ba, tun bayan Zuhr komai an gama, guri ya dau sheƙi da walali ta ko ina , bama kamar ta baya inda za'a gabatar da Abun sai Sam barka .

Tun kuma bayan Zuhr din suka fice zuwa gurin Make up, sune basu dawo ba, sai kusan magrib bayan Magrib din ma, bayan hallarar kowa, su Amah sun riga ta dawowa Sakamakon sune da tarbar Baƙi duk da cewar dai ba wasu mutane suke gayyata ba, iya yan gida ne kawai suka gayyata sai tsurarun mutane.

sai bayan fara Programs , wata Sabuwar mota Fil ƙirar Benz Fara ta danno kai cikin gidan, bata tsaya ba sai da tazo dai dai gurin da aka shimfiɗa jaan carpet din da kai tsaye zai sadaka da kam kujerar wadda ta tara taron. da gudu wasu Guard biyu suka buɗe motar, sai da ta gama shan kamshi kafin ta zuro ƙafarta wadda ta sha wani ubansun takalmi da yay bala`in ƙarɓar ƙafar, dayar ƙafar ta ziro kafin ta fito da sauran gangar jikinta gaba daya.

Gaba daya mutanan gurin tashi suka yi tsaye suka zuba mata idanu , bb abun da yake fitowa daga bakinsu sai "Tubaraqallah Maa sha Allah! Wowww!", don tayi kyau bb karya, don ko maƙiyi sai ya yaba, sanye take da wasu Yar Ubansun Blue din Gown , mai masifar kyau wadda gani daya zaka mata kasan cewar ba ƙananan kuɗaɗɗe aka kashe dominta ba, har waau duwatsu ne masu sheƙon diamond a jikin Rigar, kanta ya sha gyara sosai an sa mata wata Hular Zinari an daure mata an mata gammo , tayi kyau sosai irin kyan da baki ma ba zai iya furtasa ba.

Tunda ta fito take faman rarraba idanunta, tana kallon mutanan gurin daya bayan daya, kamar mai son ganin wani abu, har ta ƙarasa gurin zamanta suna tsaye sai da ta zauna kafin ta suka zauna suma, kamar shagulgulan biki haka aka gabatar da Abubuwan, sai dai ita sam hankalinta baya jikinta, sai rarraba idanunta take yi tana kallon gefe da gefe.

har aka tashi taron bata ga abub da take son gani ba, har aka zo yanka cake, su Amah ne suka ta ya ta yankawa, bayan sub yanka suka bata, itama ta basu, kafin dukkansu suka kora da Lemu.

Gift aka fara bata, tana Amsa da yalwataccen murmushi akan fuskarta, duk wanda ya bata sai ya tafi, har kowa ya gzma tafiya.

Juyawa ta yi gabas, Arewa, kudu da Yamma , Amma bata ga kowa ba, hawaye ta ji ya fara zubo mata, da sauri ta zaro wayarta a cikin yat jakarta, ganin shine yasa ta dauka da sauri, "Uhmm mai yasa kike ɓata min wannan Cute make up din da hawaye ne ?, shin mai ma yasa Sarauniyyar mata yin kuka a irin wannan ranar mai matuƙar muhimnanci a gareta ?", ya fada yana dan sakin sanyayyan Murmushi.

"Uhmm-uhmm ni ba ruwana da kai. don mai zaka ce min Yau zaka bayyana kan ka a gareni Amma sai kawai na ga shiru ?", ta fada tana tura cute mouth dinta da ya sha Red jan baki, "juyo bayanki to!", ya fada a hankali, da sauri ta juya bayanta, mutum ta gani ya juya bayan daga chan nesa da ita, bata iya hango ko waye, Amma tana iya Bakaken Suit dinsa, wanda ya kamile gaba daya kamilallan jikinsa, ta dan hasken da ya rage a gurin take iya hango faffaɗan bayansa . Sumar kansa da take luf ta bazu a bayansa, da sauri ta tattara gaba daya kasan rigarta , ta ruga a guje ta nufesa, cikin wani irin shauƙi da kauna, tana zuwa ta rungume bayansa, cikin tsananin jin dadi, ta jima a bayansa, kafin ta sakesa, fuskarta da yalwataccen murmushi ya kama kafaɗunsa, zata juyo da shi.

A hankali cikin wani Slow motion ga kuma ƙarar waƙar da DJ ya saki, ya fara juyowa, kanta a ƙasa ya juyo, tana ɗago da kanta, tayi saurin jaa baya idanunta a warwaje, cike da kaɗuwa da tsananin tashin hankali ta dafe kirjinta, numfashinta na ƙoƙarin Fusga ta furta............

😌

Sai Amin Comment da yawa, in ba haka ba sai nai two days ban ƙara post ba🌚 [5/30, 4:27 PM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: PART 4. CHAPTER 7.

*PART 50*

Ƙarar faɗuwar Abu ya ji, da sauri y miƙe ya nufo palon, yashe ya ganta a ƙasa, "innalillahi wa inna'illaihi raju'un" ya furta yana mai yin kanta da wani irin sauri, da sauri ya dauketa yay waje da ita, tun daga cikin palonsa, yake kiran sunan Zayn-Maleeq da karfi,Abun da duk ya tsorata gaba dayan yan cikin gidan suka fito da gudu, "Lafiya Hamma.?", ya fada yana kallon Sawwa da take hannunsa, wani kallo ya masa tare da cewa, "kana ganinta a hannuna, har ma ja tambayi lafiya, mota zaka dauko", ya fada yana yin waje da sauri, kasancewar key din motar na hannunsa yasa ya bi bayansa da sauri.

"wani Asibiti zamu je ?", ya fada yana hawa kan titi sosai, "Mafi kusa" ya faɗa yana kallon fuskarta,hannayensa ya haɗa da fuskarta ya zamana ta tallafo gefe da gefen fuskarta , ya tsareta da idanunsa masu tsananin haske sosai, har suka ƙarasa Asibitin bai dago ba, don gani yake Zayn-Maleeq sam baya sauri, suna ƙarasawa ko parking bai jira ta gyara ba ya saɓeta yay ciki da ita yana kiran Dr .

kafin Dr din ma tazo shi ya shiga cikin Ɗakin da za'ai treat dinta a ciki, anan ya tarar da Dr din da Nurses , da Alama wasu suka gama bawa taimakon gaggawa, Shimfiɗeta yay kan ɗan bed din mararsa lafiya, da kasan ya fara dubata kafin Dr da Nurses su taho su fara taimaka masa, shine karfin gaba daya Aikin, basu sha wahala sosai ba suka samu damar dawo mata da numfashinta, sauran aikin suka bar masa, shi ne yasa mata drip da sauran Allurorin da suka kamata a mata, bayan ya gama ya zauna a gefenta ya riƙe mata hannu yana kallonta, sai lokacin aka bawa Zayn-maleeq da yake waje damar Shiga cikin ɗakin , "ya mai jikin ?" ya fada yana kallon fuskarta, A hankali ya jinjina kansa Alamar da sauƙi,shiru duk suka yi sun dade sosai a gurin kafin Zayn yace "Bari naje Hamma da safe na dawo", ya fada yana ya kallonsa, "sai da safe", ya fada ba tare da ya juyo y kallesa ba, "ka samo mana kayan Amfani .Sbd Safe", ya fada bai kallesa ba, jinjina kansa yay ya fice.

hannunta ya riƙe cikin karaya sa damuwa, cikin wata iriyar murya yace "Why! why Nahleerh don nai zaki min hk ? kinsa tun lokacin da na ke dakon soyayyarki ? , kin san Adadin kaunar da nake miki ?, don mai zaki yankewa kan ki wannan hukuncin, ina da yaƙinin bb Namijin da zai baki kular da zan baki, zan kaunace ki har karshen rayuwata, zan baki fansar rai na, zan kula da ke kamar kwai, ba zan taɓa bari kiyi kuka ba, zan kula da ke fiye da tunanin mai tunani", ya fada yana kifa kanshi da jikin gadon da take kwance.

Hannunsa aka dan girgiza, ɗagowa ya yi, idanu biyu suka yi da juna, lumshe idanunta tace "Ruwa!", da sauri y miƙe ya fita, bai dade sosai ba ya dawo da kwalbar ruwa faro, ɓalle bakin gorar yay, ya sanya mata robar a lips dinta da suka bushe, sai da ta sha ruwa sosai kafin ta zame bakinta.

yatsunsa ya daura akan lips dinta ya fara shafawa a hankali, cikin sauri ta mayar da idanunta ta lumshe, idanunta ne suka fara zubar da hawaye, "mai yasa kike zubar da hawayenki ?, duk a kai na kike wannan kukan ?, bakya so na ?, kin tsaneni ko ?, " da sauri ta juya kanta ba tare da ta bari ya ƙara wata magana ba, fahimtar bata san yana mata magana yasa ya tsuke bakinsa, daran ranar yarda suka ga rana haka suka ga dare, ita dai tashin hankali darashin natsuwar hankali ne suka hana ta barci, shi kuwa fargaba ce da tsinkewar zuciya yake fama da ita.

Washe gari .

ko da suka tashi bb wanda yay wa wani magana, kowa harkokinsa yake, yana son ya mata magana, amma lura da yat vata so yasa ya ƙyalleta don a duniyar nan yanzu bb abun da ya tsana irin yaga ranta ya ɓaci, sai lallaɓata take yi, yana nan nan da ita, ita kuwa ganin hakan yasa take ta butsarewa tana lalata.

Satinta daya aka sallameta, har kuma lokacin cikin tausar zuciyarta yake akan ta Aminta da Aurensa, ita kuwa ta buga ƙasa ta haɗe gabas da Yamma kuɗu da Arewa tace bb wannan maganar, ita har gobe Ubanta ne kuma bb yarda za'ayi Uba ya Auri Yarsa.

Haka suka dawo gida, izuwa lokacin bb wanda bai san Alaqar da take tsakaninsu ba, a cikin dan Ƙaramin Ahlin Yaah Shehi, wanda ita su he kawai suka sanan wace Sawwama wadda a yanzu ta koma Nahleerh.

Zaune take tana latsa waya, duk abubuwan dubiya sun bi sun dameta, duk da tana samun kula a gurin Jaahan Amma hankalinta baya kwance, sai tayi ta jin tsinkewar zuciya, da fargaba, ji take kamar zata rasa wani abu, ko zata samu wani abu.

Ƙarar motarshi ta ji, dan dakatawa ta yi da latsa wayar, jin kamshin turarensa na Hugw boss yasa ta miƙe da sauri, yana kawo kai cikin palon tana mikewa , da sauri ta wuce palon ta, yana kallon lokacin da ta shige ciki, girgiza kansa yay ba tare da yay magana ba ya wuce bedroom dinsa.

da sauri ta buga Ƙofar Bedroom dinta ta shige , zaune ta samu Amatullah a gaban mirror dinta tana fesa turare, ajiye turaren tayi tare da cewa "lafiya kuwa ?", shiru tayi ba tare da ta amsa mata ba , ganin hakan yasa tayi shiru da bakinta ba tare da ta ƙara cewa komai ba.

Sai kusan Magrib ta fito daga Bedroom din ta fesa wankan wani hamshakin material Yellow da ya saje da fatar jikinta, tayi daurin mai hawa hawa, da ya zauna ɗas a kanta, tayi kyau sosai ta koma kamar baƙuwar balarabiya, sai kamshi take ga takalminta plate mai kyau, Chewing gum ta sa a bakinta mai kamshi Apple , tana fitowa ta hangesu chan kan dining , da sauri Umma Jakadiya tace "Yawwa Nahleerh zo ki kai wa Yaah Shehi Abin cinsa Yau ya yi Azumi , ga kuma Abun buɗa bakin sai yanzu aka gama", ta fada tana tunkarota, kamar ta kurma ihu haka ta miƙe, miƴa mata tray din mai cike da coolers da flask da sauran Abubuwa, ƙarɓa tayi ta wuce .

Cikin Natsuwa ta tura ƙofar palon ta shiga da Sallama daga chan cikin palon aka Amsa mata , cikin wata iriyar murya mai sanyu da dadi sosai, wadda har sai da ta ji gabanta ya faɗi.

Har cikin palon ta ƙarasa ta ajiye tray din a gabansa, ba tare da tayi magana ba, ta yunƙura zata miƙe ta fita ba tare da tayi masa magana ba.

Hannunta ya jawo , da sauri ta saki dan ihu idanunta a lumshe, ajiyar zuciya tayi lokacin da ta ji ta sauka akan jikinsa, gentle ya daura yatsunsa akan lips dinta ya fara zagayewa, cikin natsuwa, idanu ya ƙurawa Lips din , yana kallon yarda suke wani glowing ga wani taushi da suka ƙara, ji yake kamar ya sumbaci lips din nata.

bai san lokacin da ya biye Abun da zuciyarsa take ayyana masa ba, sai dai ya tsinci lipa dinsa akan nata, sai da hakan ya faru kafin ta farga da abun da ya faru, sai kuma ya tsinci kansa da kasa cire lips dinsa da nasa, itama wani banbaraƙwai taji wai namiji da suna Hajara, bata ankare ba taji ya jaa lips dinta na ƙasa ya fara kissing cikin matuƙar zallar rashin sabo, da kuma ɗar-ɗar kasa hanasa tayi sai wasu azababbun hawaye masu wani irin zafi da suke zubo mata, zuciyarta na wani irin luguden bugawa, jikinta sai kyarma yake,

Rashin sabo da rashin sani , fargaba , tashin hankali, tsinkewar zuciya ne suka sanyata rumtse idanunta ta kasa budewa sai hawaye da suke zubowa daga cikin idanunta, test din da ya ji da wani magnet da yake ta ƙara rikeshi yana manna lips dinsu ne yasa ya kaaa sakinta, duk da ya ji yarda jikinta yake kyarma ga kuma yarda hawayenta suke jiƴe gaban Farar Jallabiyar da ya sanya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull