Arman maleek book 1 complete - Chapter 31
Arman maleek book 1 complete Chapter 31: Arman maleek book 1 complete Chapter 31. Basu bari an basu wahala ba kuma suma basu bawa Shari'a wahala ba don sun…
3,006 words
Basu bari an basu wahala ba kuma suma basu bawa Shari'a wahala ba don sun san dubun su ta gama cika, tunda aka riga aka ganesu bb wata sauran daukaka da zasu ƙara yi, sun san daga ranar irin ta yau sun gama tozarta, hakan yasa suka faɗi iya kacin gaskiyarsu, sun san hukuncin kisa ne, to ba su ma jaa magana ba, don suna son su mutu da dan Sauransu ba tare da an wahalar musu da Gangunar jikinsu ba.
Tattara gaba daya Shaidun da suka bada da kansu da wanda aka nemo da sauran Abubuwan da duk ya kamata, aka maka su Ƙulliya domin gabatar da Shiri'a kowa ya san matsayinsa, Ƙulliyar ma da aka kai su, basu bata wahala ba suka Amsa tuhumar da ake musu domin su samu sauƙi da Rangwame akan Hukuncinsu, sai dai bb wani sassauci bb sauƙi , hukuncin kisa aka yanke musu, har da taran Maƙudan kuɗaɗe domin kula da wanda suka jinyatar , don Nahleerh ma tun da ta faɗi take Asibiti tana fama.
Haka suka bada tarar da aka chajesu, bada jimawa ba kuma aka yanke musu hukunci da Aka zartar musu da shi, Shi kenan kuma babin gaba daya Azzaluman Nigeria Manya-manyan har ma da na Ƙananan wanda suke ganin Ubayen gidajensu suna bin bayansu ya rufe, don yanzu bb wanda yake daure musu gindi.
A hankali yake buɗe idanunsa har ya budesu tangaram akanta, tana zaune kusa da shi hannunta na riƙe da nasa tana kallon Shiri'ar da ake gabatar wa a Kotu, dan motsa hannunsa ya yi, hakan yasa ta mayar da gaba daya hankalinta a kansa, cikin kulawa da wata natsuwa da ta shigeta cikin kwana biyun nan da ta gansa a kwance kamar a yi magana ya Amsa bb magana, bb motsi ma mai kyau komai sai An masa, hakan yasa tsoron Allah ya shigeta, dukka wani wasa da yake cikin kwakwalwarta ta ciresa, ta dauki niyyar kulawa da shi da mulkinsa, domin ta zamar musu Garkuwar Ƙarfe.
"Sannu Abieh", ta fada So quit , ba kamar yarda ta saba sakalcinta, da shagwaɓarta ba, "kana bukatar wani abu , ko akwai inda yake maka ciwo ne", ta kara faɗa, kafih ya dawo daga duniyar tunanin Abun da ya sameta har ta chanja a gaba ki daya ba, hannunta ya rumtse cikin kula ya buɗe bakinsa dakyar yana jin kansa na masa wani irin ciwo, yace "Babu", ya fada jikinsa na dan rawa.
Dr ne ya shigo ya ƙara dubasa yay masa dukkan abun da yake buƙata, kafin ya fita, bayan kuma drip din hannunsa ya kare ta kara sanya masa wani, haka suka ci gaba da zama har dare duk da ita ma dai jikinta ba dadi yake mata ba dauriya ce kawai.
Cikin dare jikinsa ya dauki wani irin zafi na ban mamaki yarda kasan zai ƙona mutum haka jikinsa ya yi, duk yarda ta kai da dauriyar ta rungumesa kasawa tayi ta sakesa tana kuka sosai cikin juka take cewa "Na gaji bana so, dududu kwananka nawa da karɓar mulkin da har ake son Sabauta ka, ba zai yiyu ba, madamar Wannan Abubuwan basu dai na faruwa ba wlh sai dai ka bar Mulkin nan, don ba Sarauta bace da za'ace duk rintsi kai ne zaka gajeta, haaaba don Allah , wama ya sani ko wani mugun Abun aka sake yi maka, yanzu ji jikinka, ji yarda nama jikinka yake tafarfasa", ta fada tana kuka sosai.
da sauri ta nufi Office din likita, ta fada masa duk abun da yake faruwa "Oh God!, akwai matsala tunda har limite din ya kai haka, " ya fada yana ficewa da sauri, sun sha wuya sosai kafin zazzaɓin ya sauka, a cikin darwn Yawa Forma President magana, akan sai an mishi Juyen jini domin jininsa ya riga da ya lalace dole sai an chanja masa wani , sai kuma an kai sa China domin chan ne kawai za'ayi aikin ba tare da an samu wata matsala ba.
Cikin tashin hankali ya sanya aka haɗa musu jirgi na musamman wanda zai daukesu su kaɗai ya tafi da su, chan din ma kafin su ƙarasa za'a gama komai na aikin domin ana zuwa dashi za'a shiga ɗakin Theater din da shi, kafin ma su tago an gama tura musu dukkan wasu bayanansa, kalar jininsa, waye shi da dukkan abun da ake so.
Asubar Fari jirginsu ya ɗaga ko su Ayyana ma basu san da tafiyar ba, sai dai wayar gari suka yi suka ji har sun tafi, Ƙasa gaba daya ta ruɗe da rashin lafiyar Sabon Shugaban Ƙasa, sauƙar Al-qur'ani aka shiga yi masa da Sadaka akan Allah ya basa lafiya, wasu daga cikin Yan ƙasa masu Kaunarsa ma har da Azumummukansu , do fatan Allah ya basa lafiya.
Suna zuwa b wani ɓata lokaci aka tafi da shi Ɗakin da za'a mishi aikin, bayan gama dukkan wasu abubuwan da suka kamata, aka fara mishi juyen jinin, ana ɗibar nasa ta hannu daya, dayan kuma ana sanya masa wani.
Haka aka fitar mishi da wani irin jimi, wanda sai ka rantse in har baka sani ba kace ba na Dan Adam bane, SBD yarda yake Baƙi sosai, ya chanja kala gaba daya kamar ba jini ba.
Cikin sa'a aka fito da shi, jikinshi ya yi wani sharrr, alamar jini mai kyau yana yawo a jikinsa, Ɗakin hutu aka kai sa, Wata Nurse aka damkar wa Haƙƙin kula da shi, a madadin Nahleerh sam bata fahimci hakan ba,in ma yana buƙatar wani abu to ita ce zata mishi.
Zaune yake ƙafafunsa a ƙasa, ya jingina da jikin bango idanunshi a lumshe ta shigo cikin ɗakin, tsareshi da , tana son yi masa magana, amma bata son ya buɗe idanunsa domin bata gaji da ganinsa ba, A hankali ta buɗe Bathroom ta fito, daga ita sai Towel tana tsane jikinta da yake zubar da ruwa, turus tayi ta tsaya tana kallon Bachainiyar da ta tsaresa da idanu bata ma ko san fitowarta ba daga Banɗaki.
Kishi ne ya turnuƙeta, wasu hawaye masu zafi ne suka shiga tsiyayo mata, ga Uban ciki a gaba bata jin zata iya Fitina da shi, amma ko ya ne sai ta koyawa Yarinyar Hankali, tsawa ta buga mata kafin tace "Ubanki kika tsaya kallo mayya, tsinanniya masu tsafe-tsafe to ƙurwar mijina ƙur da kike kallonsa mun fi ƙarfinko domin mun sha tabara mun sha Yaseeen, mun yi Wanka da Ayoyin Ubangiji , bb wani abu nake da zai tsarata mu, fita ki bar Ɗakin nan kafin na kasheki", ta fada cikin dan Abun da take ji daga chainanci don yau da gobe ta wuce wasa.
Tsorata tayi da yarda take balbala mata ruwan masifa ta fice da sauri har tana haɗawa da gudu-gudu, "kai kuma na dawo kan ka, da ka wani sakar mata jiki tana kallonka, in sonta kake yi ko Aurenta kake son yi ai ba sai kayi haka ba, fitowa zaka yi ka faɗa min, ban san ma mai yasa maza baku da Amana ba, " ta fada tana kuka.
Ruɗewa ya yi, yana rarrashinta amma sai botsarewa take, sai kuka take tana cewa ya saketa , tunda har zai Bari wata tazo tana kalle masa jiki amma ko ya yi magana ya barta, daƙyar da siɗin goshi ya samu ta daina kuka da masifar da take masa, bayan ta gama kafa masa Sharruɗa, da kanta taje tace wa Dr ita bata Buƙatat wata nurse wadda zata kular mata da miji ita kaɗai zata iya kula da Abinta, da yake ta zayyane masa abun da ya faru, sai hkr yake bata akan ba zata kuma ba,, zama a sama musu mai kula da shi namiji na Musamman "da yafi dai", ta fada tana ficewa, numfashi ya jaa don in da sabo sun saba da Fitinarta, ba kamar in suna Yarensu, sai tayi ta zaginsu tace suna haɗa kai zasu kashe mata miji, sai sun yi Turanci suke samun Salama, tunda kuma ta fara iya Yaren shi kenan kuma ta kafa musu Ƙahon Zuƙa, dole sai sun yi Fira, ko basa so haka nan suke biyeta.
Watansu Daya a ƙasar ya gyagije ya yi wani irin kyau ita ma ba'a barta a baya ba, tayi kyanta Abunta suna samun gamsasshiyar kulawa daga gurin Likitoci, sun yi wani irin Mugun sabo da su, don har binsu gidajensu take, suje kasuwa suje ina ne, cikin wata dayan nan ta zaga kusan Rabin Chaina haka nan sai ta ƙirƙirar musu tafiya, ga jikinta da ba dadinsa take ji ba Amma haka take yawo kamar ta ci ƙafar kare.
Bayan sati biyu suka tattara yanasu-yanasu suka bar ƙasar zuwa ƙasarsu Nigeria, cike da kewar Mutanan Chaina, da suma suke Kewarsu, suna komawa suka shiga yin aiyukansu gadan-gadan, don ko Gombe basu koma ba sbd yarda lokaci ya tafi sosai, kusan 2 months da hawansu Mulki.
Bayan wata daya da Dawowarsu Ranar wata Juma'a ta tashi da naƙuda, cikin sa'a Allah ya sauketa lafiya ba tare da ta sha wata wahala ba sosai, Sai kuma Allah ya Azurtasu da samun Ɗa Namiji, kar ku so ganin Ɓarin Ƙafa a gurin Maleeq.
Sbd Tsananin Mirna har ya rasa inda zai sanya Rayuwarsa, a ƙaron farko na rayuwarsa Allah y azurtasa da samun ƙaruwa, Ƙaruwar ma ta Ɗa Namiji, yarda yake ririta Ɗan da Uwar Ɗan ma abun kallo ne, duk wanda ya zo sai y tafi da zanxen yarda yake kula da Matarsa da Ɗansa, ko kuɗa baya kaunar ya ga ya sauka a kansu.
Tun daga ranar da aka haihu ake gashe-gashe , soye-soye, ciye-ciye da lashe-lashe, in kaje gidan ranar kwana biyu zaka dauka ranar ne suna, SBD yarda aka kawo mai gashe na Musamman, Sa da raguna aka kayar aka fara gasawa, Abin ci kuwa, bb wanda bai ci ya tafi da shi ba, Restaurant na Musamman aka bada Aikin Abin ci daga ranar da aka haihu har bayan suna, kullum sai an kawo Abin ciccika kala-kala, sai a lokacin ne Mahaifin Nahleerh ya zo Nigeria, lokacin da ya je ga danginsa sun matuƙar mamakin ganinsa, don su a Zatonsu Ƙashinsa ya jima da yin fari a Kabari, nan da nan suka zo suna neman Afwarsa da Yafiyarsa akan Abun da suka mishi, anan ne suke faɗa masa sune suka yi Sanadiyar Haɗarinsa wanda a shi ne ya rasa matarsa, a lokacin da suka basa bayanin nan ji ya yi baya kaunarsu a rayuwarsa, baya son su SBD yarda suka yi sanadiyar Ajalin Abu mafi soyuwa a rayuwarsa, yarda suka yi ƙoƙarin Halakasa akan Abun da ya zage ya nema da karfinsa, da Jarumtarsa, Wasu mutanan Ababen mamaki ne sosai, wai baka san lokacih da mutum ya sha wahalar nemansa ba, bakasan wani tudu wani gangare mutum ya faɗa ya nemi Abun sa ba, Amna kazo rana tsaka kace zaka ƙwace masa ta ko wanne Hali, dakyar suka samu ya yafe musu.suka koma kamar da.
Ranar suna ne kuma Yaro ya ci Sunan Abu-Maleeq , Amma suna kiransa da Yareema wansa zaɓin Mahaifiyarsa ne hakan.
Ranar an ci an sha , an gyatse, bb wanda yaje sunan nan bai fita da niƙi-niƙin kayan Arziki ba, don manyan Jakunkuna aka ringa rabawa, masu dauke da photon Baby da Mamarsa da Babansa, duk kuma cikin jaka daya, akwai Atamfa, mai photon Baby, Shadda da Lass, sai Hijab takalmi , Al-qur'ani da Chasbaha sai kuma dadduma, Yajin Jego da kuma Naman suna, sai Stickers din baby, kaya da ririƙin Arziki, Aikwa mai jego ma ta samu Abubuwan duniya, wanda har aka kasa Iya ƙirga mai ta samu, Ɗaki daya sai da aka cika su da kayayyakin Baby, Turame da saursn Abubuwan da ake samu na Suna, Keys din mota kuwa ta samu a ƙalla ba Aƙasaru ba kusan Biyar, Wadda Maleeq ya damƙa mata ranar da ta haihu, sai wadda Mahaifinta ya bata, wanda Forma President ya bata, sai kuma Zayn ya bata daya Sayyid daya, sai kuma Abdul ya bata kyautar Kujerar Hajj da Umrah.
Company ma ta samu Biyu bayan wanda Maleeq ya mallaka mata, Mahaifinta ya bata, sai kuma Kakanta wanda ya Haifi Mamarta ta bata , Abubuwan duniya dai ta samesu , har ma ta rasa yarda zata yi da abubuwan, sai kawai ta sanyasu gaba ta saki kukan farin ciki, yanzu a duniya bb abun da bata samu ga, sai dai tayi ta bautar Allah ya sadata da rahmarsa a Lahira, Da Sallama ya shigo Ɗakin, da babyn da yake maƙale a ƙafadarsa yana dan ƙananun kuka, Ɗagowa tayi ta kallesa, yana zama gefenta ta faɗa kansa, tare da kara fashewa da kuka, ruɗewa ya yi, ya shiga tambayarta lafiya , cikin kuka ta ce "Abieh na gama samun Duniya , yanzu mai nake nema na jin dadi da Allah bai mallaka min ba, ina ji a rayuwata na fi ko wacce mace sa'a a duniya, Allah y azurta ji da miji kamili mai tsaron Allah, mai Arziki, ya bani Mahaifi Mai kaunata, ya Azurtani da Samun Ɗa, ya Azurtani da tarin Dukiya, wadda har na rasa yarda zan da ita, komai na Alatu ina da shi bb Abun da na nema na rasa, ni mai zan ce da Allah yanzu" murmushi ne ya suɓuce masa kafin ya furta "Alhamdulillah!. A duk lokacin da Allah ya ni'imtaka da ni'imarsa bb abun da yake so sai ka mishi godiya,yana cewa, idan na muku ni'ima ku gode min ni kuma zan ƙara muku , don haka ki ci gaba da gode masa " Rungumesa tayi tare da furta "Alhamdulillahi Allah!, Alhmdllhi Ala kulli Halin, Alhmdulillah!", sumbatar goshinta ya yi, tare da daura mata babyn akan cinyarta, "yunwa yake ji ki basa ya sha" cikin natsuwa ta fara feeding din Yaron tana shafa sumarsa da ta kasance irin ta Larabawa, bata da maraba da ta Mahaifinsa.
BAYAN SHEKARU HUƊU.
Bayan Shekaru huɗu, aka ƙara basa Takarar Shugaban Ƙasa , domin yin tazarce, Amma ya fito yace "wanda ya yi ma Allah ya sanya masa Albarka, zai bai mulki ya koma chan gargajiya wato Sarauta" mutane basu ji dadi ba musamman ma talakawa, wanda suke jin dadin mulkinsa, bb cuta bb cutarwa, yana yin konai cikin Adalci baya bari a Zalunci Talakawa, ya tsaya tsayin daka gurin ya ga ya murƙusar da Azzalumai, inda bai tsaya ba sai da ya amsa sunansa na *DODON AZZALUMAI*.
Haka ya tattara ya koma Masarautarsu da Matarsa da Ɗansa wanda ya yi girma sosai, wanda daga shi kuma basu sake samun haihuwa ba.
Bayan ya koma aka nadasa Sarkin garinsu, don Lamurɗe lalace ya tsofe, Halin da suka aikata shi da Jadda ne yake tambayarsu, dukkan wani Haƙƙi da suka san sun dauka yanzu Allah yake kankaroshi a jikinsu, da Baƙunanau suke tona Asirin Abubuwan da suka aikata, tun daga kan na Sarki Mahaifinsu Lamurɗe da suka kashe har kan Abdul-Azeez Sarki mahaifin su Maleeq da suka sabauta har Mahaifiyarsu da suka yi sanadiyar mutuwarta, da makirce-makircen da suka ringa ƙuƙƙulawa, Abubuwan da suka aikata kare ma baya ci ba.
BAYAN SHEKARA GOMA.
A cikin shekaru Goman nan Abubuwa da yawa sun faru masu dadi da mararsa dadi, ciki har da Mutuwar Abdul-Azeez Sarki, Mutuwar Jadda har ma da ta Lamurɗe, da ta Ayyana, da ta Khaleeda ma matar da Ya Aura, wadda Aid ce tayi sanadiyar mutuwarta , Su Amatullah da su Zayn Gaba daya sun yi Aure, sun Auri wasu dangin Mahaifiyarsu.
Yana Zaune cikim Ɗalinshi yaga Mutum ya bayyana a gabansa, idanunshi ya ɗago tare da zubasu akan wadda ta bayyanar, cikin sanyi ta gaisheshi, bayan ya Amsa ne , ta bayyana masa Itace wadda suka haɗu da Sadiyya a Saudi lokacij dabtana da rai har ta mata karyar cewa ita matarsa ce , haka ta kwashe dukkan abun da ya faru a ranar ta faɗa masa, tare da nemansa afwa a madadin Sadiyya da karyar da tayi Sanadiyar Sonsa da take, tana gama maganarta ta ɓace Ɓat.
Slippers dinshi ya sanya ya fito palo, zaune ya sameta da Yar Yarinyarta da take shayarwa, kusa da ita ya zauna yana kallonta, a hankali ya kalleta, kashe mata ido ya yi, murmushi tayi tare da cewa "Alhamdulillahi Allah da ya Azurta ni da Mahaifina a matsayin miji, da na yi garaje tabbas da na Tamka Mummunan Asarawa Wadda Humaida(Yar gan-gan) ta kusa tabkawa akan Humaid, da kuma nayi gaggawa to ba shakka da na zama AMARYAR ZAMANI, Amma da ban yi gaggawa ba, sai ka zamemin Yaya Omar na Hamideert(Rashin Uwa ne Sanadi), wanda muka Rikiɗa muka zama Yan uwa tamkar Nazlah daHameed dinta, Yarda Kasan Khair da Muneebat dinsa, muma haka RAYUWARMU A Yau ta riƙiɗa ta zama Abun kwatance, bayan Tsayin lokaci kuma Sai Allah ya Azurtamu da *ƁOYAYYAN YAREEMA* (My New book), wanda yake ɓoye kansa , ya fi ganewa zama shu daya akan ya shiga cikin mutane, daga shi kuma sai Allah ya ci gaba da Azurtamu da Yara kala-kala masu Albarka, ga kuɗi, mulki, ilimi , bb Abun da zamu ce da Allah sai Alhamdulillah!, Alhamdulillahi Ala Ni'imatul Islam.
ALHMDLLH ALLAH, ALHMDLLH,Ina mai kara Jaddada Godiya ta ga Mai sama, wanda ya bani ikon yin Labarin nan har na gama sa cikin nasara da tarin Albarka, ba'ace ba'a fuskanci Ƙalubale ba, Amma Alhamdulillahi, Ina Roƙon Allah da ya yafe mana dukkan wani Kusa-kuran da yake ciki, gyaran da yake ciki kuwa Allah ya Albarkace sa, sannan ya bamu ikon gyarawa, Sai kuma mun haɗu a cikin Sabon Littafina mai Taken *Ɓoyayyan Yarima*, karo na Farko da nake son gwada littafin Yaƙi, domin muma a dama da mu a harkar, ba wai a zauna guri daya ba, kullum basirarka na gu daya, za'a dan matsa wani fanni a ji yane😂, fatan zan samu Magoya baya fiye da wanda na samu a wannan Book din, #400 ne shima, Amma duk wanda ya Siya Arman Maleeq zai bada #300, domin duk wanda ya karanta wannan book din ina matuƙar girmamasa. za ku iya paymant dinku yanzu, duk dai mai buƙata zai iya tuntuɓata, ga kuma number Account nan 1499884120 UMMA SALMA SANI. ACCESS BANK . daga Karshe ina mai cewa .
*Bissalam*
P.R.O SALMAH🤙🏽